Waleed yatashi ya isa” ta goge mata fuska, sannan takoma kitchen din store ta shiga tadauko wata kula wanda abinci ke ciki da goran zobo da spoon tafito tazo gabanta tabude kulan tana kallon fuskanta tace “nasan harda yunwa kikeji, ci abinci ki kinji yarinyata mai kyau, Maman Waleed” Mama taja hancinta dan murmushi Safeerah tayi tasa hannu ta karbi kulan ta bude rice wanda tun abincin rana ne sai spaghetti tamata murmushi, Mama tace “ci maza” karban cokali tayi ta sa hannu ta cire mayafin datai rolling ta ijiye, Masha Allah tanada gashi garda na hauka baki sidik kaman na yar buzuwa danma tai parking tayi donut da yawan gashinta yasa yayi kato sosai, kanta a gyare tsaf yana sheki, Mama ke gyaramata dan bata zuwa saloon, bata saka relaxer, batada kiba but tanada kirji sosai acike ga hips daya fito from yanda ta zauna, abincin ta debo cikin spoon takai bakinta, ijiyan zuciya Mama ta sauke now this is her daughter, Safeerah ta that never jokes with food, cikeda so tace “toh ba’amin murmushin ba ko girkin beyi dadi bane”? Murmushi tayi mai kayatarwa takasa magana sabida yanda abincin yacika baki, Mama tace “maza cinye bari naje nakai abinci falo” yunkurawa tayi zata tashi Mama tace “koma ki zaune kici abincinki zan iya komi” Mama ta wuce ta shiga kitchen, binta da kallo Safeerah tayi ta sauke ijiyan zuciya In sha Allah saita zama wani abu ta kwashe iyayenta, abincin ta shiga ci tana sauke ijiyen zuciya duk yawan abincin nan tasss ta cinye ta ci nama tasha zobon ta mike tsaye dan an fara kiran magrib tabude kofa tashigo kitchen din tahada duk wanke wankan data gani ta wanke tsaf tana cikin mopping taji kukan Waleed cikin muryan bacci da muryan rashin iya magana yace “Um…….myyyyyy” dasauri ta jingina mop din tayi kofa zata bude taji Momma ta dakama Mama tsawa. “Kifita dashi daga falon nan mana bakiga Salma na waya bane, yaro sai shegen katon murya kaman gardi”bude kofan tayi dayake Mama na nan dinning tana gyara plates da flask tana jijjiga Waleed abaya yana ganin Maman sa yawani fashe da kuka yana musu mutsun kwantowa yazo wajenta dasauri Mama tayi kitchen din tashiga kwantoshi Safeerah na murmushi tana washe fararen kananun hakoranta masu kyau cikin muryan yara tace “Waleely oyoyoo, ayoyooo” ta karbi yaron yawani rungumeta yanakai hannu yana taba mata boobs yana wani irin rigima Safeerah takama hannunsa takai baki tace “kul, kul, kul bana hanaka ba, tututuuu not good Waleed” tama hannun kiss sai yayi dariya na one second yahau kuka kuma, Mama tace “kuje daki kimasa abinci yasha, akwai tuwo ki gwada basa ko zaici” gyadama Mama kai tayi tace “bari nakarasa mopping din saimu tafi” Mama tace “barshi zanyi jeki basa abinci kinsan ba kirki Waleed yakeda shi ba idan yanajin yunwa zai kusan rusa mana gidan nan ne da kuka”.
💫ITS NEVER TOO LATE💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 8️⃣
TOM INA AMARE WAYANDA HARYAU BAKI TABA TASHIN KAN MEGIDA KIN BURGESA BA?🤭
INA KUMA UWARGIDAYE DA BASU IYA HARKAN ABUNBA BAKIDA CAPACITY😀 HAJIYATA BAKI KAWO LIGHT 💡 AKAN GADO??? TOH INA MUKU ALBISHIR DA BUDE SABON CLASS MAI SUNA COITUS JUNCTION WATO MANHAJAR RAGADADA🎊
ZO AKOYA MIKI NANAYE DA AYYARAYE DA ZAI BIRKITA LISSAFIN OGA💃
CLASS DIN WATA DAYA NE REGISTRATION IS 3K🔥
wa.me/+2347012181461
Kankame Waleed Safeerah tayi tana murmushi jin abinda Mama tace tanamai kiss a farin kumatun shi mai nama tace “kaji abinda Mama tace ko Waleed wai ka iya kuka, oya to banda kuka muje muje dan Lukuti na” tabude kofan kitchen din tafice dashi Mama tabisu da kallo tana murmushi Waleed har yasa ta mance ranta abace wani kuncin ma Waleed ke rage mata shi. BQ tawuce wanda yake dan karamin flat tabude kofan falo ne dakeda wasu old chairs aciki ga carpet akasa sai kitchen sai dakuna biyu Mama na daya ita an bata daya da sauri tawuce kitchen dinsu ta duka tana zaunar dashi akasa cus is very clean cikin lallashi tace “yauwaaa zauna kaga Ummy tama Walely abinci yanzun nan ko” tana ijiyesa zata mike ya kurma uban ihu kukan dayake rikewa tuntuni daman magiya kawai yake yasakesa da kyau saiga hawaye, idan kaga Waleed na kuka mai hawaye is either an dakesa ko yanajin yunwa ta tsani taga hawaye a fuskansa sabida bala’in tausayi yake bata, da sauri tadaukesa tace “kai Waleed toh dena kukan yunwa ne! Ishiru ishiru” dasauri ta kunna heater na water kettle dake kitchen dinsu tabude wani drawer wanda abincin yara ne, ga Aptamil, Gerber rice, Friso Gold, Cerelac, tarasa mesa haryau Waleed yaki yarda yaci normal abinci saidai yataba idan yaga dama ya dandana but abincin nan sune abinda yakeso yayi kuma considering as food, ko yadaure yaci tuwo is as if cikinsa bai dauki tuwo as food ba sai yaci this food, yanason tea ma yanasha but tea baya rikesa, tun Waleed na yaro suke fama dashi kan lamarin abinci, budewa tayi taga Gerber rice dinma yakusan karewa haka madaran Aptamin din, duka baifi idan ansha yanzu yasha gobe da safe maybe darana yasha yakare ba kenan, hadamai tayi a gurguje sannan tadaukeshi tafito falo jikinsa har rawa yake ta shiga basa tsaf ya shanye tabasa ruwa yasha sannan yasauka yafara wasa anan tsakiyan falon itakuma tawuce kitchen ta wanke plate nasa da spoon tabude drawer tadauko Frisogold da cerelac ta duba duk suma baifi sha biyu ba, ijiyan zuciya tasauke, maida komi tayi tafito takalleshi har yaje gaban tv yana taba wayoyin wajen tace “kafara aiki ko toho muje muyi salla” ashagwabe yace “Ummyyyy” yarike wayan dasauri tace “noooo Waleed bani kaga” karba tayi takama hannunsa tace “muje” binta yayi suka wuce dakinsu yar katifa number 1 ce a kasa am shimfida zanin gado mai kyau akai, dakin yayi kyau yana kamshi, wucewa tayi bayi shikuma yafara guje guje tayo alwala tafito ta shimfida dadduma dasauri Waleed yazo yashiga gabanta tayi murmushi tace “Allahu Akbar” daga hannunsa yayi shima yace “Aaaaa Ab bar” shi adole yana salla tayi dariya ta kabbarta salla da kyau abinta tanayi yana binta ta sallame zai tashi tace “bakace astagfirullah ba” tare sukai zikiru ba’ada salla sannan yatashi yadauki wani toy car nasa yana wasa sai binsa da kallo take tana kan dadduman, seeing Waleed makes her happy, koda yaushe inhar yaci abinci ya koshi baida rigima yunwa kadai ke sakashi rigima, saikuma idan sun dakesa achan flat din, she loves her little Boy ita karan kanta batasan iya dadin son datakemai ba, but Waleed is her everything.
Saida akai isha’i tayi sannan tai shafa’i da wuturi ta mike tace “Waleely wankan dare taho” dasauri yazo ashagwabe yace “Ummyyyyy” hancinsa taja tace “kai wai bakason wanka ko” daukansa tayi tashiga ciremai kaya da pampers tace “wlh saikayi” tamai chakulkuli yahau dariya itama tana dariya tawuce dashi bayi tamai wanka tamai brush sama sama tafito dashi, ledan pampers nasa taje Huggies shima baifi guda 10 ba tadauki daya tazo tasamai taciro kayan bacci tasamai da kyar cus so yake yayi wasa shirya Waleed is war on its own, sannan tabarsa nan ita takoma bayi tayi nata wankan tafito daure da towel looking damn fine tasa wani rigan bacci har kasa tazauna ta dauki wayanta Oppo tabude first bank account nata taduba duka duka 15k gareta ta shiga Opay tanada 3,200 shiru tayi 18200 bazai isheta ba, tasai cerelac sauran bazai isheta tasai madara ba balle ma ayi maganan pampers, “Mamaaaaa” taji muryan Waleed a falo yana kiran sunan Mama batamasan sanda yafice ba that means Mama tazo flat nasu, tashi tayi tafito falo Mama harta dauki Waleed tanamai wasa dan Mama is his favorite person, ganin Safeerah yasa Mama ta kalleta tamata murmushi tace “karki damu Allah bazai taba hanamu abincin da zamu ba Waleed ba kinji” murmushi tayi bataso Mama ta damu hakan yasa tace “a’a Mama ni ban damu ba, jekiyi wanka kihuta Mama” Mama tace “tom” tasauke Waleed tace “samai cartoon kiga ya kalla” murmushi Safeerah tayi tace “Gotv yayi expire” Mama tace “kuma nagaya ma Shamsu yace zaiyi ina ganin ya mance” dasauri tace “zan samai awayana kawai” saita dauki Waleed din tashiga YouTube tasamai cartoon a wayanta aiko yayi lamo ajikinta yana kallo yakai hannunsa zai taba kirjinta tace “kul bana hanaka ba wai” denawa yayi yacigaba da kallo har sai wajajen 12 yayi bacci dan har Baba yashigo kallo yake.
Around 12 wani mota yashigo gidan parking akayi wani matashi da zaiyi 34yrs haka tareda Salma suka fito daga motan suna kama da Salma sosai, hararansa tayi tace “I will tell Momma kahanani magana da AJ” tsaki yaja yace “wlh nakara ganinki a club sai ranki yabaci akan mema Momma zata barki kifice da daddare eh” ranta abace tace “motana fa” “is being taken care of nasa akawo miki” yawuce abinsa Salma kaman zata hadiye zuciya ta mutu tabisa abaya suka wuce flat nasu sama tawuce tana tafiya tana cika tana batsewa tawuce dakin Momma tabude kofa ba sallama tareda kunna wuta kawai tafashe da kuka adaburce Momma dake bacci ta farka. “Salma wat is it”? Cikin fushi tace “Ya Shamsu ne Momma” da dan fada Momma tace “Shamsu!” Yana kokarin shiga dakinsa jin Momma takirasa saiyazo yashigo dakin, yakalli Salma dake kasa tana kuka sai kawai yahau dariyan iskanci Salma cikin kuka tace “Momma kingani ko” cikeda takaici Mom tace “wai me haka Shamsu bazaku banni na huta ba yara biyu rak dana haifa sun hanani kwanciyan hankali, you know this girl nada asthma why are you doing this to her” yana dariya yace “Mom a club na ganta fa with some bad girls metakeyi a club” kallon Salma Mom tayi, Salma tace “shima meyakeyi a club besides ma ai azaune yaganni” nunata yayi yace “look at dressing na jikinta Momma jean da wannan rigan pls ba dankwali akai sannan she was talking to one bad guy fa Mom dana sani sosai AJ and he’s friends with Abbati” dasauri Momma tace “wani Abbati”? Shamsu yace “Abbati dai Baban Waleed, duk wanda ko yake click din su Abbati ai ba mutanen arziki bane” cikeda damuwa Momma tace “kwarai Salma banason ki tareda mutanen Abbati kindaiga abinda yama yar uwanki Safeerah” mikewa tayi ta turo baki tace “ai kinfi kowa sanin waye Abbati kika hada aurensa da Safeerah! Ni da gatana babu wanda ya isa yamin abinda akama Safeerah wlhy so kuma chanza maganan, besides ma we just becomes friends 2days ago a Nile is not like aurensa zanyi but he’s just so cute and handsome ya iya gayu wlh ga accent kaman bature” Shamsu yace “kingani ko Momma” hararansa tayi cikeda rashin kunya tace “baruwanka dani allow me to leave my life am an adult” tayi kofa fuuu tafice yabita da kallo saikuma ya kalli Momma yace “wlh zan tattaka yarinyar nan asthma kesa nake ragamata fa” cikeda lallashi da lallabawa Momma tace “zo Shamsu kyale Salma yarinya ce” tahowa yayi yazauna abakin gado tace “da gaske AJ abokin Abbati ne”? Gyadamata kai yayi yace “yes wlh Momma, all they do is abuse girls, ko lokacin nan i warned you kan Abbati kikace bazaki iya gayama kawarki No ba tunda tazo gidan nan taga Safeerah taji tanaso ta aurama danta kuka kama kuka hada aure look at her yanzu da yaro da yaki daukan responsibility nashi saidai muke komi”.
💫LOKACI BAI KURE BA💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 9️⃣
Ahankali Momma tace “yanzu dai mubar maganan yaya ake ciki? Kama abokin naka maganan? I mean IT da Safeerah zatayi”? Dan tsaki yayi yace “wlh Momma I hate yanda kikesa nake wahala unnecessary sabida this your brother da family nasa haba I got better things to do” cikeda lallabawa Momma tace “so kake ayi dani ace na maidasu yan aiki agidana banma yarsu komiba? Ko yanzu ma ubanme Aunt dinku ta gwagwalada batace ba, dole nayi using school na rufe bakin kowa kodon abinda yasami yarinyar so please kayi?” Gyadamata kai yayi yace “yes yace nakawota though yayansa shine owner of the company yana China he’s expecting zai dawo ko yau ko gobe besides his brother baida matsala zai yarda even though basu taba barin yan IT a company su ba, in nutshell dai she can start yayansa ma hardly comes to the company kinsan soja ne, so shine ke komi kuma komi ke hannunsa” ijiyan zuciya Momma ta sauke tace “yauwa Shamsudeeni godiya nake babban mutum” tashi yayi daga gadon yace “good night Momma”.
**
Around 8:30 nadare yashigo gidan this time around bai bari sojoji sun kawosa ba, parking yayi yana kallon motocin dake compound din yafito anatse sai lafiyayyen kamshi yake yazare bakin glasses na idanunsa ya ijiye a mota yarufe yawuce flat nasu yabude kofa da sallama yashigo cikin falon wani attajirin magidanci ne a falon wanda zai iyakai 65yrs cikin manyan kaya tareda wani mai kama da shi da zaiyi 60yrs a gefensa suna magana ga kayan abinci agabansu sai kaninsa Auwal dake gefen Ammi laptop kan cinyansa yana tabawa, dakatar da magana magidancin yayi murmushi ya gauraye fuskansa yace “Sojoji” cikeda girmamawa ya sunkuyar da kansa ya maida kofan yarufe yazo har gabansa yadan duka yace “Baffa barkanku da dare, ina yini Dad” mugun kallo mai kama dashi yamasa yace “kaga daman dawowa daga Chinan? Ai dakai zaman ka saika dawo rannan daurin aure” dasauri Babban yace “waikai baka gajiya da fada daga dawowan yaro?” Tabe baki yayi yadauki jarida yabude yana karantawa, Baffa ya shafa kansa yace “ka sauka lpy, barrack kaje ne hala?” Gyadamai kai yayi alamun eh batare dayayi magana ba, Baffa yace “sannu da zuwa Salim, Ya shirin bikin” anatse yace “Alhamdulillah Baffa” Ammi tace “zokaci abinci” ahankali yace “okay” saiya wuce dinning dasauri Auwal yabisa Dady yadan sauke jaridan kasa yabisa da kallo kafin ya kadakai yasake bude jaridan yana dubawa, Auwal yace “Yaya akwai kanwar wata Abokina Shamsu dazatayi IT a company mu, I know kace no yan IT but please Yaya kaga nariga nacemai yes” dan kallonsa Salim yayi fuskan nan tasa ba walwala, Ammi dake zubamai abinci tace “tundazu yaketa nanata maganan nan Son, I told him daya sanar dakai kafin ya yarda but tunda kanwar Abokinsa ce ka yarda please na san Shamsu yana zuwa gidan nan he’s a nice boy kaji Son” ta shafa kansa, sauke jaridan Dady yayi yajuyo yakallisu yace “kazo company na kayi aiki ka makale ana yayanka gashinan kullum cikin roko kake kaman me bara” dukansu kallon Dady sukayi hatta Ammi bataji dadin maganan ba Baffa zaiyi magana Auwal ya jirasa yace “common Dad sau nawa zan gayamaka company Yaya is my dream, I studied architecture a school, mexanyi in your company when my brother open my dream company and gives me to manage” yayi maganan yana murmushi yana kallon Yayansa dake juya spoon, magana Daddy zaiyi Baffa yace “kafi kowa kewan yaron nan dabaya gari yanzu yadawo zaka fara” shiru Dad yayi bai kara magana ba.
Kansa Ammi ta shafa hakan yasa yadago yakalleta murmushi ya sakan mata kadan yadan lumshe idanu yabude sai yaja bowl of soup din gabansa yasaka spoon ciki yadeba zaikai baki saiya kallesu ganin duk shi suke kallo da Ammi da Auwal yasa yace “is there something in the food”? Kwashewa da dariya Auwal yayi yace “wlh Ya Salim baka iya cracking jokes ba badadi kai sojoji babu abinda kuka iya”, murmushi Ammi tayi tace “ci abincin ka mun dena kallonka” taja kujera ta zauna kusa dashi, kaiwa bakinsa yayi anatse yaci sannan yakalli Auwal yace “she can start” dunkule hannu Auwal yayi cikeda jin dadi yace “yesssss!” Ammi tai murmushi tace “thank you Salim” gyadamata kai yayi cikin muryansa kasa kasa yace “tell him within the week zanzo for supervision idan naga anything ba daidai ba I will fire both him and Paresh and nobody will use you to beg me Ammi! It won’t work” Ammi takalli Auwal dake dariya tace “kadaijiko”? Dasauri yace “I manage everything to perfection bazaka ga komi ba sai alkhairi Yaya, wannan uban salary da kake biyaba how can I joke da wajen cin abinci na” dan hararansa kadan Salim yayi yace “silly boy” shiru yamusu bai kara tankasu ba yacigaba da cin abinci while Ammi da Auwal na hira, Dady da Baffa na nasu a falo, bai wani ci sosai ba yadauki mug na coffee yamike baice musu komiba ya wuce stairs yashiga hawa Ammi tabisa da kallo, anatse yake tafiya kaman yana inspecting ko’ina dakin dake gaban na Ammi yawuce hannunsa yadaga yayi knocking so daya dudda kannensa ne baya taba fadawa dakinsu kai tsaye he respect privacy nasu, bude kofan akayi autansu ce Lubna batai wata wata ba kawai ta rungumesa tana washe baki dan tana bala’in son yayanta tace “Yaya kadawo? Oyoyooo” Ameerah da kanta ke a tsefe gashin kam acinye tazo itama tana murmushi akunyace gabanta na faduwa tayi hugging nasa tace “Yaya sannu dazuwa, Yaya kaga gashina duk yakarene saisa nasaka” Calmly yet strictly yace “is that ur excuse na yin abinda Allah yahana”? Dasauri ta girgizamai kai, anatse yace “Allah ya tsinema mai karin gashi, get ready I will take you to supermarket gobe to get the best hair products that helps with hair growth” gyadamai kai tayi tana murmushi tace “thank you Ya Salim”suna mugun tsoron sa but again kuma suna mugun sonsa, he’s just the best and very sweet but you need to be open minded before ka fahimce sa inba hakaba zaka dauka ya tsaneka ne, kusan 1min suna ahaka yace “ku cikani” dariya dukansu sukayi suka sakeshi wucesu yayi yashigo dakin Lubna ta kulle kofa duk suka biyosa bai zauna kan gadonsu ba saiya wuce gaban dressing mirror nasu ya zauna yayi crossing leg yanashan shayin ahankali yanabin ko’ina da kallo kaman wani invigilator this is just him haka yake, akwai observing environment nasa, he’s very very security conscious, gadaje biyu ne a dakin daya na kallon daya ga bra da pants akan gadon Lubna kallo daya yamusu yadauke kai yace “wat are those underwears doing saman gadonki Lubna?” Dasauri tayi wajen ta kwashe komi tawuce wardrobe nasu tabude tana sawa ciki tace “Yaya sunmin kadan ne Ammi tace nahada nafito dasu” wayansa ne yahau ringing da sauri Ameerah tazo wajen tace “Yaya Anty Nanah ne?” Kallonta yayi saiyasa hannu yaciro wayan ga sunan Nanah a screen din dasauri Ameerah tace “can I talk to her Yaya?” Dasauri itama Lubna tace “Yaya nima I want to talk to her” wayan yaba Ameerah yamike yace “idan kun gama ina wajen Ammi” yawuce yafice daga dakin yashiga dakin Ammi, Ammi na zaune saman gado hannunta rike da wata yar takarda yawuce yazauna kan coach na dakin yace “ina yini Ammi” murmushi tamai tace “yaushe zaka gidansu Khadija?” Dan shiru yayi Ammi ta tsaresa da idanu ahankali tace “Salim” dago kansa yayi yakalleta anatse yace “zanje” Ammi tace “before this week runs out kaje, kudan tattauna kaji me da me take bukata da babu na biki, get to know her, Nanah yar mutunci ce ga hankali da kunya, this is duk abubuwan damuka duba ni da mahaifinka muka hada aurenku kajiko” gyadamata kai yayi yace “okay” zata sake magana Ameerah tashigo rikeda wayan tace “Yaya ga Anty Nana” Ammi tace “Khadijah ce bani ita” dasauri Ameerah tawuce tabama Ammi wayan, Ammi tasaka wayan a speaker tace “Yar Albarka” akunyace tana murmushi kasa kasa tace “Ammi na ina yini ya gajiya yakuma karfin jiki? Ina Daddy na”? Ammi tace “Alhamdulillah duk muna nan lpy, Dadyn ki na falo, ya su Mama?”Nanah tace “Alhamdulillah Ammi, Ammi daman gobe inaso namiki burabusko na aiko miki dashi Ameerah tacemin kina sonshi sosai da miyan hanta” murmushi sosai Ammi tayi kana gani kasan maganan yamata dadi tace “gaskiya ne inaso kam sosai amman karki wahalar da kanki” dasauri tace “duk abinda zan miki ba wahala bane Ammi in sha Allah gobe zan miki” Ammi tace “shikenan Allah yayi albarka” ahankali tace “Ameen Ameen agaida Abba, saida safe Ammi” Ammi tace “Allah tashemu lpy” tabama Ameerah wayan tace “ungo ba yayanki” karba tayi tamike ta kaimai wayan karba yayi yasa hannu ya katse wayan yamike yayi kofa Ammi tabisa da kallo, hannu yasa zai bude kofa Ammi tace “I really love this girl Salim!” Chak ya tsaya batare daya juyoba, Ammi tace “she’s my choice and choice na mahaifinka, yarinya yar gidan mutunci, she’s those type of girls that will keep familyn ka together, tanason kanninka da yan uwanka duka, tana son mahaifiyarka da mahaifinka, this is dream of Everyman yasami perfect wife that have no any problem or issues with his family” shiru yayi baice komiba kusan 10secs kafin ahankali yace “good night Ammi” yabude kofa yafice.
💫LOKACI BAI KURE BA💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 🔟
Bude kofa yayi yafito daga dakin ya sauko kasa Daddy kadaine a falo yana bude wasu files yana signing ga glass a idanunsa Baffa yariga yatafi, anatse yace “saida safe Dad” dagokai Daddy yayi yakallesa yace “kaima saida safe Alhaji Salim” bude kofa yayi yafice batare daya kara wata magana ba Daddy yasake kadakai yadauki files yacigaba da signing dayake yi.
Wayansa ne yafara ringing cirowa yayi daga aljihu Nanah ce, katsewa yayi yakirata back ringing daya ta daga tace “Baby dan Allah ka kulani wlh kewanka nake” baice komiba ahankali chan yace “ya su Mama”? Ahankali tace “fine tanachan falo kasan yan uwanta har sun soma zuwa daga Katsina, Baby sai maganin mata aketa bani” tayi maganan tana rage murya, yace “wat is that”? Yayi tambayan da zuciya daya, baya wani hira da ita itakuma babu abinda takeso kaman taga yana zance da ita, bala’in mahaukacin son Major Salim take gani take she’s the luckiest girl on earth, ga kudi, ga kyawu, ga gayu, ga ji dakai, ga aji ga ilimi, lankwasa murya tayi tace “Baby kagani ko idan za’ama mace aure an samata rana ana bata magunguna haka dake gyara jiki, suna cire ciwon sanyi, suna saukar da ni’ima ajikin mace kuma zaisa miji yayi na’am da ita zakaga idan an tashi bikin Ameerah da Lubna za’a basu maganin mata” yace “I don’t think Ammi tasan shi” dan dariya Nanh tayi yau wlh yabata dariya wato namiji namiji ne, kasa daurewa tayi tace “Baby wlh I love you so much, ina mugun mugun sonka! You are so innocent, I can’t wait to officially zama matarka, I promise I’m going to be the best wife to you” wayan na kunnensa baice komiba yakai dakinsa yacire wayan a kunne yasa a speaker ya ijiye kan gado yana rage kayan jikinsa jin shiru tace “zakazo ka ganni gobe?” “No” yabata amsa atakaice kafin ahankali yace “let’s see within the week” kaman zatai kuka tace “okay” anatse yace “I have to shower, daganan zan shiga gym” murya chan kasa tace “zaka kirani kagama?” Ahankali yace “okay!” Yasa hannu ya katse yawuce closet nasa ya ijiye kayan daya cire yadauki wani short na nike da singlet na nike black yasaka hand gloves yasa sneakers yafito yasauka kasa yabude wani daki gym ne yahau kan treadmill yafara gudu na bala’i kaman a highest yasaka yakai kusan 20min sannan yasauka yayi press up yadaga karfe yadaga rope kafin yaje punching bag yasaka fighting gloves, one of his hubby is boxing he loves it a lot, yayi punching bag sosai kusan 2hours yabata sannan yagama yana zufa sosai yakalli agogo is 12:20 yafito yawuce sama, kaya yacire yafada bayi yayi wanka yafito he wants to smoke but bayayi agidansu kwata kwata out of respect for iyayensa kwanciya yayi agado alkawarin dayama Nanah yatuna hakan yasa yadauki wayan even though yana tunanin tayi bacci yakirata but harya katse bata daukaba hakan yasa ya katse wayan ya ijiye yayi shiru tareda lumshe idanu he’s just seeing that little girl face data taimakeshi as usual dan babu ranan da baya gani yazo bacci, he’s not sure takai 16yrs ma she will not pass 15yrs, this is 5yrs probably yanzu she’s 20yrs haka, there’s this guilt dayake feeling koma ina take yanzu aduniya itada iyayenta shiya sakasu in it, shi ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 15