mutumin looking really really scared, cikin zakakkiyar muryansa data dishashe sabida azaba yace “hide me please! Kasheni sukeso suyi!” Daidai an buga kofar gidansu kofar yayi wani irin kara kaman an karyata ma hakan yasa da sauri ta juya tashiga kalle kalle tagama rudewa batamasan mezatayi ba, idan taki taimakonsa aka kashesa itama tanada hannu a kashe musulmi dan uwanta kuma wuta zata shiga, tabarsa tasan tsaf zasu kasheta rasa abinyi tayi ta kallesa saikuma tayi hanyar dakinta tace “ka zo” dasauri yabita yana kallon ko’ina wardrobe da Mama takawo mata dakin tabude wanda ba wani abune ciki ba tajuyo ta kallesa tace “shiga na boyeka anan” gyadamata kai yayi yashige ta maida kofan da sauri tarufe daidai samarin da sunfi Allah kadai yasan adadinsu sun fado falonsu, rawa jikinta yafara ganin suna tahowa zasu shigo dakin kuma bataso su shigo zasu iya ganinsa sai kawai ta zare hijabinta ta yar akasa mutumin cikin wardrobe din na kallonta tadan ramin wardrobe din, takai hannunta bayan riganta tashiga jan zip dinta kasa ahankali kadan kadan gabansa na faduwa yace “wat is this girl trying to do” yaga wani black tabo mai girma a ta right side na kafadanta daidai samarin na daga labulen dakin wani irin ihu ta tsala tareda dukawa da sauri tace “Mamaaa!” Wanda ke kan gaba ya fizge labulen cikin muryan yan ta’adda yace “dalla gafarachan Malamai ku koma baya bakuga yarinya na kokarin cire kaya bane kuke dage mata labule” dasauri ta dauki hijab nata tasaka jikinta nawani irin rawa kaman tanajin fitsari kirjinta kaman zai tsage ganin mutanen nan ba alkhairi bane, dan daban yajuyo ya kalleta ganin dukta tsorace yamata murmushi da black lebensa na taba yace “yanzu kika dawo daga makaranta Feerahn Mama?”Gyadamai kai tayi dan tasansa sarai dan makotansu ne ya gagari iyayensu, tace “eh Ya Anas” wani narkewa zuciyansa yayi yasake washe baki yace “wani bai shigo gidan nan ba?” Girgizamai kai tayi ahankali tace “babu kowa agidan yanzu nadawo na karbi makulli wajen Mama Uwale nabude gidan Mama wai sunje dubiya chan gabari” juyawa yayi believing yarinyar yace “tohh sai ajuya bai shigo nan ba eh ya ne mu ware, yarinya karama ce agidan kanwarmu Safeerah, Mamanta ma sunje dubiya, aware” samarin suka fara fita yajuyo yakalleta tasauke kanta kasa gabanta har bugawa yake tsanagen tsoro yasake washe baki yace “karki damu babu wanda zai kara shigowa karkiji tsoro babu wanda ya isa yatabaki a layin nan, bari muje agaida Mama” gyadamai kai tayi ahankali gabanta na faduwa ya wuce gabanta sai faduwa yake bana wasa ba takai kusan 5min ahaka sannan ta tashi tafito falonsu ko’ina yayi datti sun tattaka musu har kujeru da takalma tawuce tafito ta taho zaure gabanta na faduwa taga neighbor nasu tace “kinga Safeerah kulle kofa ki garkame sakata Allah ya tsaremu daga sherin mutanen nan kinga yanda suka juyamin gida, wlh nagaji da unguwan nan ina dalili kullum cikin tashin hankali muke rufo kofarku nidai” gyadamata kai tayi ta maida kofansu tarufe ahankali tasaka sakata na sama dana kasa sannan tajuyo har lokacin kirjinta racing yake tashigo falonsu tamaida kofa tarufe tasaka sakata zata wuce sai kawai tayi wajen dan karamin freezer su tabude taciro goron ruwa, tadauki rubber cup dake saman fridge din ta tsiyaya ruwan sanyin a cup din tawuto tashiga dakinta tawuce wajen sip dinta tabude ahankali tadan koma baya adan tsorace ta kallesa, ijiyan zuciya kawai yake saukewa yama kasa motsi sai hura iska yake a hannunsa dake masa wani irin azaba, ahankali tamikamai ruwan da hannunta, juyowa yayi yakalleta saiyasa hannu ya karbi ruwa ya tsaya kallon cup din saikuma yakai ruwan baki ya kwankwade within seconds duktana tsaye tana kallonsa kana ganinta kaga matsoraciya yamika mata cup din yace “karamin” karba tayi tajuya takoma falo tasake debo ruwan takawo mai ya karba ya kwankwade yabata cup din, karba tayi tana kallonsa, ahankali tace “nabaka abinci”? Juyowa yayi yakalleta sai yakasa magana sai kallonta daya tsaya yi hakan yasa Safeerah tajuya tawuce wajen gadonta dan karamin kulan abinci ta da spoon dinta tadauka tajuyo tazo har wajen wardrohe din still kallonta yake tashiga bude kulan da sauri ta duka ta ijiye marfin a kasa tasaka spoon sannan ta matso wajen ta mikamai, dafadukan shinkafa ne na manja da baimaji sosai ba kana ganin abincin kasan struggling food ne wanda marasa kudi talakawa ne suka dafa, yayi jim yana kallon abinci batare daya amsaba hakan yasa cikin sanyin muryanta tace “dazafi kaci kanajin yunwa” Jaye idanunshi yayi daga abincin yakalli hannunsa yace “no kici I’m not hungry! Kin dawo daga school, so eat” dukawa tayi ta dauki marfin flask din ta rufe ta ijiye a gefe takara kallonsa hannunsa yake kallo ga bakinsa da gefen fuskansa jini, asanyayye Safeerah tace “konaka suka soma yi da wuta?” Gyadamata kai yayi batare daya kalleta ba, murya chan kasa tace “Allah sarki, Allah kadai keda ikon yin hukunci da wuta ba dan Adam ba, meka musu?” Batare daya kalleta ba har lokacin yace “na kade wani achan express na kaisa asibiti aka basa magani shine nace ya gayamin gidansu na kawosa ina zuwa kawai suka tareni and then this, is like kaman sun sanni is set up nazo kano for wani government project ne!”
💫ITS NEVER TOO LATE💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 3️⃣
TOM INA AMARE WAYANDA HARYAU BAKI TABA TASHIN KAN MEGIDA KIN BURGESA BA?🤭
INA KUMA UWARGIDAYE DA BASU IYA HARKAN ABUNBA BAKIDA CAPACITY😀 HAJIYATA BAKI KAWO LIGHT 💡 AKAN GADO??? TOH INA MUKU ALBISHIR DA BUDE SABON CLASS MAI SUNA COITUS JUNCTION WATO MANHAJAR RAGADADA🎊
ZO AKOYA MIKI NANAYE DA AYYARAYE DA ZAI BIRKITA LISSAFIN OGA💃
CLASS DIN WATA DAYA NE REGISTRATION IS 3K🔥
CHAT ME UP AND JOIN NOW wa.me/+2347012181461
Natsuwa Safeerah tayi tana kallonsa ya mugun bata tausayi, wani iri zuciyanta kemata irin inama ita watace ko tanada wani karfi tayakesu, yan anguwan nan haka suke kaman ma dagangan suke zuwa titi dan abugesu su samu nama ga hannunsa ya kone ga gefen fuskansa duk jini sai kawai taji kuka yazo mata tadaura hannunta kan fuskanta tafashe da kuka ahankali tana tabe baki, awani irin hankali yajuyo yakalleta jin sautin kuka why is she crying? Ya tambayi kansa, yana kokarin magana saiyaga ta jaye hannayenta fuskanta gabaki daya ya jike da hawaye, cikin muryan kuka tace “kuma Allah saiya saka maka azzalumai kawai, kayakuri kaji, akwai Allah, one day duk Allah zaiyi maganin su sun dauka sunfi karfin kowa basusan cewa babu wanda yafi karfin Allah ba” takarasa maganan tana kallonsa another set of hawaye na zubomata sai yakasa magana ma kawia ya tsaya yana kallonta, tashi tayi har lokacin goge hawaye take yana kallonta tawuce tabude jakan school nata ta zazzage komi, tanada gauze, bandage, spirit, hydrogen da auduga, kwasowa tayi tazo wajen wardrobe din tace “kafito” ahankali yafito tanunamai kullin kayan wankinta dake wajen daure a zani zama yayi ahankali yana sauke ijiyan zuciya, tajuya tafita daga dakin tadauko zuma tadawo tazo dan nesa dashi takallesa da idanunta da sunyi ja sabida kukan datayi suka hada ido, hannunta tadaura a kirjinta tace “kagani farin uniform na nurses ne ajikina ko, ina zuwa makarantan Nurse ban kware ba, zanyi jamb nashiga asalin nursing a university abinda nakeso nazama kenan” tai wani murmushi daya bayyana dimples nata masu kyau da fararen hakoranta, takallesa tace “ban kware ba but na iya abubuwa kadan amman zaka bari nasamaka magani a haka?” Kallonta yayi na kusan 3secs sai murmushi takemasa hakoranta yan kanana kaman na children saiya dauke kai baice komiba, dasauri tace “dan Allah ina ganinka ahaka kuka kake sani” tai wani rau da fuska zata fashe da kuka kallonta yayi ganin hawaye yataru a idanun nata sai ya gyadamata kai kawai alamun eh, da sauri tabude spirit da auduga ta dangwala ta dan taho dab dashi but saitaji gabanta na fadi takasa komi sai wani firrr take da idanu yakalleta ganin takasa kana gani kasan bata tabayiba, ijiyan zuciya ya fuzar ahankali yace “do it” yanuna mata gefen goshinsa dake jini, gyadamai kai tayi ta kai hannunta dake rawa ta goge ciwon goshin ya runtse idanu da sauri sauri ta tsaya tace “dazafi ko sannu” saita matso dab dashi tacigaba da goge blood din tana kallon black face nasa daya runtse idanu yanda yabata tausayi yasa kawai saita huramai iskan bakinta a goshin wani irin bude idanu yayi yajuyo yace “wat are you doing?” Kasa magana tayi tai fiki fiki da idanu yace “ki barshi banso” dasauri tace “yakuri baram karaba wlh tausayi kabani naga kanajin zafi” akufule yace “namiki kala da abin tausayi?” Girgizamai kai tayi sai ta turomai baki ta kwabe fuska zatai kuka dauke kai kawai yayi yace “cigaba” dasauri tacigaba tai maza tagama ta manna bandage awajen sannan tazo wajen hannunsa takalla ya kone sosai a hannun yama fara bororo, bala’in tausayi yabata, tasan kawai dan shi namiji ne yasa yadaure amman a konaka haka da bala’in zafi gashi yayi bororo, sheshekan kuka dayaji yasa yajuyo da fuskansa gently, yarinyar yaga ta tasa hannunsa agaba tana kallo tana kuka batare data taba hannun ba, sai yayi shiru kawai yana kallonta sai kuka take tana gogewa da bayan hannu, calmly yace “ahaka zaki zama Nurse?” Kaman jira take tafashe da kukan da kyau cikin kukan tace “banson naga anacin zalin mutum, sabida sunga bakada karfi kai kadaine su sunada yawa saisu azabatar dakai haka, kaga nataba konewa akafa” dawani irin sauri ta gyara zama ta daga kafar damanta tazare white sock na kafan da sauri tanuna mai wata yar karaman tabo haka na kuna, kafanta very clean ga dogayen yatsu looking damn beautiful dan akwai ragowan jan kunshi akansu tace “lokacin Mama na koyamin girki tace na tafasa wake naje zan juya ruwan ya zubemin akafa saida nayi kwana bakwai ina kuka sabida zafi, kaiko wuta fa suka samaka nasan kalan azaban wlh, is not fair sai Allah ya sakamaka” he’s in extreme pain da maybe da wanine da yanzu yasume sau uku, but shirme da surutun this little girl is diverting attention nasa, on a scale of 10 tasa he’s only feeling 4% azaba, ganin da gaske kukan take yasa gently yace “stop crying and treat me Miss Nurse” washemai baki tayi tace “kaika fara kirana Nurse amman Nurse Safeerah zakace, sunana Safeerah Shu’ibu idan na girma na bude asibiti na ai zaka dinga zuwa ina dubaka ko, nine nurse dinku ko”? Gyadamata kai yayi kadan alamun eh, zuman ta dauka tace “dana gama school danayi admitting naka ma ni, but bakomi zan gayama Mama yau nasami first patient” tabude zumansu tashiga shafawa ahankali kai tsaye batare dataji wani tsorobae idanunsa a lumshe amman hakanan yabude kadan yadan kalleta tana shafamai zuman hawaye na ciko mata a idanu, kasan the thing is hurting her, saikuma ta turo baki irin na yara dake jin tausayin abu tasake fashewa da kuka mara sauri, for the first time sai yayi murmushi dudda yanajin azaba yace “abinda aka koya muku a school din kenan, kina treating patients kina kuka”? Dasauri ta kallesa saitakai bayan hannu ta goge fuskanta tass tace “banso naga an zalinci wani, kaji proper hospital duk sai an cire skin dinnan, hannunka zai zama mai tabo, kayakuri kaji”gyadamata kai yayi yamike tsaye dasauri ta mike tace “ina zaka?” “Zan tafi” ya amsa batare daya kalleta ba dasauri ta shiga gabansa tana zaro idanu tace “suna nan ko’ina su Anas Magu, dan Allah karkaje kabari Baba yadawo saiya fadi yanda za’ayi ya fitar dakai batare da an ganeka ba” shiru yayi yace “aramin wayanki i lost mine” ahankali tace “banda waya Baba yace naci jamb zai siyamin nafara university da waya” kallonta yayi sai yadan fuzar da iska kana ganinsa kasan yadamu ganin haka yasa tace “naje gidansu Maman Uwale na aro maka?” Gyadamata kai yayi, ahankali tace “to koma ka zauna” komawa yayi yazauna saita juya ta duka takarasa zare dayan takalmin kafanta tafita yabita da kallo kafin yabi dakin da kallo, kusan 3min tayi tadawo gidan takara kulle kofansu sannan tashigo dakin a kwance tagansa kaman baida lafiya yana ganinta da kyar yadago yamika mata hannu tabasa wayan karba yayi yashiga saka wasu number yakai wayan kunnensa yace “ya sunan layin nan” dasauri tace “yan kwalta bakın kasuwa karshen layi” magana taji yayi turenci ne but kuma kaman numbers yake kira saikuma sunan layinsu daya kira yazare wayan a kunnensa yamika mata karba tayi tajuya tawuce takai tadawo ganinsa kwance kaman baya numfashi yasa tayi wajen ta tsaya kansa tana lekasa ganin baya motsi yasa ahankali tace “Yaya, Uncle, Malam, bawan Allah” but baiyi motsi ba kawai saita fashe da kuka tace “nashiga uku shikenan sunja mutum ya mutu agidan mu, mezan ce? Mesan gayama su Mama da Baba? Innalillahi? Na shiga uku ni Safeerah yazanyi?” Hawaye ya gangaro daga idanunta ya diddiga akan fuskansa, bude idanunsa yayi ahankali ya kalleta da sauri ta dakatar da kukan tace “na dauka ka mutu ne” cikin karfin hali dan bala’in rashin lafiya da zazzabi yakeji yace “haka aka gayamuku ana mutuwa a school?” Zaro manya manyan idanunta dasukai jaaaa tayi ta kallesa batai magana ba, murya chan kasa yace “kinci abinci?”
Girgizamai kai tayi ahankali yace “to dauka kici” murya chan kasa tana kallonsa tace “to katashi kazauna banso ka mutu tsoro nakeji” shiru yayi saiya taso cikeda karfin hali ya zauna ganin she’s really scared itakuma saita zauna anan gabansa kan tiles ta kallesa ganin yazauna da kyau yadan lumshe idanu yasa tajawo kulan abincinta tabude ahankali tasa spoon, ciko spoon din tayi da kyau ta hangame baki tasa abincin dasauri ya kalleta yana kara zaro idanu baitaba ganin loma haka ba, gabaki daya hankalinta yakoma kan abincin dan shegen yunwa takeji tun kokon safe sake ciko cokali tayi takai bakinta tana jan hanci saiya manta da zazzabin dayakeji ya tsaya kallonta, 7good spoons tayi ta cinye abincin dake kulan tasss takai hannu cikin kulan tana tsince yan few rices dasuka rage takai baki kaman bata koshi ba yace “kinajin yunwa haka why did u give me abincin ki?” Dasauri ta kalleshi tace “sabida bakada lafiya ni zan iya hakura ai nasha koko kafin naje school, kuma nasai kosan rogon da hamsin din da Baba yabani kudin mota nadawo da kafa, kafa kuma Mama tadawo zamuyi girki tare” ahankali yace “mesa bakihau mota ba”? Murya chan kasa tace “yunwa nadingaji a school wlh” for the second time yayi murmushi ahankali, dasauri tace “laaaa murmushi kayi? Fuskanka baki kirin ba’a ganewa” shiru yayi baice komiba ya lumshe idanu, tayi shiru tana kallonshi ganin yana zufa saita juya da sauri tawuce gadonta tadauko mafici tadawo tashiga fifitashi, bude idanu yayi kadan sabida sanyin dayaji kan hannunsa dake zugi zaiyi magana sukaji jiniya da kukan motocin yan sanda ga sahun ana gudu ana watsewa dawani irin sauri ta jingina da sip gabanta na faduwa sosai, yadan kalleta yace “are you scared”? Zaro manyan idanunta tayi ta girgizamai kai tama kasa magana, chan taji ana diddirkowa ata kofar gidansu arude tace “tashi kashiga wardrobe” buga kofar gidansu taji anyi arude tazabura tace “tashi ka shiga ciki bari naje nagani”.
💫LOKACI BAI KURE BA💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 4️⃣
TOM INA AMARE WAYANDA HARYAU BAKI TABA TASHIN KAN MEGIDA KIN BURGESA BA?🤭
INA KUMA UWARGIDAYE DA BASU IYA HARKAN ABUNBA BAKIDA CAPACITY😀 HAJIYATA BAKI KAWO LIGHT 💡 AKAN GADO??? TOH INA MUKU ALBISHIR DA BUDE SABON CLASS MAI SUNA COITUS JUNCTION WATO MANHAJAR RAGADADA🎊
ZO AKOYA MIKI NANAYE DA AYYARAYE DA ZAI BIRKITA LISSAFIN OGA💃
CLASS DIN WATA DAYA NE REGISTRATION IS 3K🔥
watsapp me to join wa.me/+2347012181461
At this point bayama iya magana sabida azaban dayake ji har zuwa heart nasa, cikeda damuwa ganin he’s suffering tace “karkaji tsoro kaji” lumshe idanu yayi yabude su akanta, hannunta ta daura a kirji tace “ni Nurse Safeerah will protect you, duk wanda zai kasheka saidai yafara dani first” tawuce kofa jikinta na rawa yabita da kallo da idanunsa da sunfaramai dishi dishi, cambass dinta yaga ta dauka tarike a hannu tadaga sama irin dashi zata kwada musu idan sune, fitowa zaure tayi sai alokacin ta gane gidan makociyarsu ake bugawa da karfin gaske ana cewa. “Open the door is Soldiers” haba jin haka yasa wani karfi yazoma Safeerah tunda ga hukuma sune zasu iya taimakon bawan Allahn chan su fito dashi batare da an kashesa ba, yarda kambass din tayi ta shiga bude kofansu da saurinta, tana budewa taga sojoji anan lungunsu sunfi guda talatin ga manya manyan bindigogi a hannayensu dayasa taci cikinta ya daure daidai itama Maman Habiba nabude kofa gabanta na faduwa, ganin sun kallo Safeerah dukansu yasa tafashe da kuka tace “banine ba” tanuna cikin gidansu tace “dan Allah ku taimaki wani bawan Allah dasuka kusan kashewa yana cikin gidan nan” dasauri duk suka kalleta Babban cikinsu yace “lead d way” dasauri tajuya takoma ciki suka biyota har cikin dakinsu, ana ganinsa sojojin sukai kansa da gudu. “Sir Sir” kawai suke fada amman baya hayyacinsa, daukansa sukai yadan bude idanu kadan yabi kowa da kallo sai kuma ya lumshe idanun ruf arude sukace “Sir” Babban yace “let’s move” sukai waje dashi Safeerah ta bisu da gudu ba takalmi kafanta, ta tsaya gaban lungun gidansu, motocin sojoji sunfi goma tagani sunyi layi, bude mota akayi ana kokarin sakashi yabude idanunsa kadan yakallota, duk cikin uban sojojin nan da mutanen anguwa da aka fiffito ita kadaine wearing white, no shoes a kafafunta, those eyes looking reddish, sunyi ja, she looks like an innocent angel, bakinsa ya shiga motsi amman haka aka sakasa amota sukaja motan da mahaukacin gudu, sauran sojoji suka tsaya dan saisun nemo wayanda sukai this act suci ubansu, daidai wani mutum dabazai wuce 50yrs ba baida jiki siriri ne sosai ga furfura a fuskansa rikeda wani jaka yazo wajen ya tsaya gefenta yace “meke faruwa anan Safeerah? Ina takalmi”? Kafin tai magana wani soja yace “Ke!” Wani firgicewa Safeerah tayi saida tarike Baba gam tace “na….na’am” sojan yazo ya tsaya gabanta fuskansa ba rahama yace “agidanku akaga Oga meya faru? Waya tabamana Oga”? Wlh tsabaragen rudewa batasan sanda tace “Anas Magu ne!” Wani kallonta Baba yayi yana salati aransa, Babban Sojan yayi ihu yace “Soldiers!” Atare suka amsa “Yes Sir!” Cikin bacin rai yace “I don’t care idan zaku juya anguwan nan up side down kushiga house by house, afitomin da koma waye Anas Magu” Baba yawani fincike Safeerah yayi cikin gida da ita, makociyarsu nabiyosu tace “hauka kikayi Feerah? Ke kinsan wani rigima kika sa kanki kuwa dake da iyayenki, aiko wanda basuci nasaran konawa ba kika boye, ku zasu kona amadadin sa”? Fashewa da kuka Safeerah tayi brain dinta kwata kwata bai gayamata meta aikata ba sai yanzu kuma tsaf tasan yanzu bala’in nan kansu zai dawo kuwa, Baba yace “wai meke faruwa ne ma tukunna?” Makociyar su tabasa labari daga farko zuwa karshe hankalin Baba yatashi sabida yasan su waye mutanen nan, sukai charko charko a tsakar gida suna kallon Safeerah dake kuka ba kakkautawa, ana ahaka Mama tadawo wata yar dattijuwan mata da bazata wuce 40yrs ba tace “meya faru ne kaga yanda sojoji ke ma yaran unguwan nan kuwa awaje” tai maganan tana kallon Safeerah dake kuka, nan Baba yagaya mata komi itama tsoro yashiga jikinta duk sukai charko charko ana kallon Safeerah makociyar tace “uhmm Allah ya takaita fitinan nan, nidai gaskiya zaman unguwan nan yazo karshe bazan iyaba, Allah dawo da Malam, sai anjiman ku” tawuce tafita, Mama takalli Safeerah tace “ni banki boyesa dakikai ba, amman mesa zaki kira sunan Anas basaikice baki Sani ba, ke kina girma kinki wayau” Baba yace “dan Allah bita ahankali meta sani eh guda nawa take dakike expecting tayi abu kaman adult, zo taho Mamana” tasowa tayi tazo gefen Baba ta kankamesa tai zuru zuru sabida tasan tai laifi, ahakadai sukasa abincin dare, sai wajajen 10 nadare sojojin sukabar unguwan sun tafi da mutanen dasuka kama but not all still anbar few sojoji a unguwan, da kyar Safeerah tai bacci Mama ma haka Baba dai yakasa runtsawa dudda an tafi dasu yasan ways na yan unguwan nan.
Yana kwance a falo yaji an dirko gidan da sauri yamike yashige daki yataso Mama yaga yamata tawuce dakin Safeerah su rufe kofa tawuce tarufe kofan, Baba yaji ana dirkowa soyake yabasu hakuri yarsa tai kuskure amman yarinya ce, yafito yana kokarin kunna torchlight kafinma yayi magana suka shiga yimai duka baji ba gani Baba salati kawai yake, Mama tasaki Safeerah data rungume ajiki jin karan bugun da akema Baba tabude kofa tafito Safeerah tasa ihu na bala’in tana kuka dan tabiyo bayan Mama ganin dukan da akama Baba, suna ganin Safeerah daya yazabura yayo kanta yace “zonan dan durun Babanki” “Mamaaaaa” Safeerah tai ihu tana kankame Mama, Mama tace “kuwa Allah kuyakuri Safeerah sa’ar kanninku ce, yarinya ce tayi shirm….” Ture Mama yayi ya fizgo Safeerah Baba yatashi da duka karfinsa ya turesa ya maida Safeerah daki yaja kofa ya tsaya gaban dakin yace “ku rama akaina karku tabamin karaman yarinya, ransu baci yayi suka shiga dukan Baba Safeerah na ihu tana kuka jin yanda ake dukan Baba Mama ma haka, before u know it aka tashi a unguwan, warwas suka sumar da Baba suka sama gidan wuta Safeerah da Mama na daki, sukabar gidan, Safeera da Mama suka bude kofa suka fito suna tari, kamo Baba Mama tayi suka fito dashi waje wuta ci yake sojoji suka iso, karban Baba sukayi suka sa amota Mama da Safeera suka shiga kaisu wani asibiti sukayi suna saukesu suka juya komawa unguwan, aka karbi Baba akace su ijiye dubu dari ko biyar babu ajikinsu ko sun koma gida ma an sama gidan wuta, wayan Baba Mama tacire daga aljihun jallabiyan sa tana kuka, Number Yayar Baba Kubura dake Abuja takira, ta sanar da ita komi dake faruwa, Mama Kubra ranta yabaci tadinga masifa ta tura kudin kawai ta aiko driver yadaukesu, wuraren 6 na safe driver ya iso haka aka cire Baba daga treatment aka sakasa a mota Mama takama hannun Safeerah dake kuka mugun zazzabi ya rufeta suka shiga motan kawai aka wuce dasu Abuja.
Bayan 5yrs!!!
💫IT’s NEVER TOO LATE💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 5️⃣
Bayan 5yrs
Tampatsetsen gidane mai lafiyayyen kyau, kalan yan gayu da abubuwan zamani, gidan nada girman gaske irin gidajen nan ne da kana ganinsu kasan sai wane da wane ne keda kalan gida haka, ga securities biyu dake sanye da wasu bakin uniform na wajen gate tsaye kaman gumaka, anata aikace aikace a gidan kaman akwai wani event, masu fenti nayi, masu gyaran flowers nayi, ga motoci dayawa parke a compound din.
Wata hamshakiyan mata ce zaune a hadadden parlour dayaji kayan duniya tana sanye dawata shadda dayasha aiki wuyanta da kunnenta duka zinare ne, waya na kunnenta tana magana while wata haka na zaune agabanta tana samata kunshi akafa, sai wasu yammata haka masu kyau su biyu zaune a falon da bazasu wuce 21yrs ba dayan kuma maybe 23-24yrs dukansu suna kama da Maman kagansu farare tass dasu, zare wayan mahaifiyarsu tayi daga kunnenta hakan yasa babban yarinyar tace “Ammi I can’t believe finally Yayan mu is getting married wai har an tafi kai akwatin auren sa yau” dayan karaman tace “I cant wait to see him yaushe zai dawo ne Ammi”? Murmushi matan tayi tace “he said yau” zatai magana wata mata sanye da uniform na Chef tafito daga wani babban kitchen tazo gaban matan tace “everything is ready Madam” gyadamata kai Ammi tayi tace “ok, sannunku da aiki” matan tawuce.
Tundaga nesa security ya hango motan sojoji na tahowa bayanta kuma yaga wata arniyan mota 2024 GLK baka kirin taji uban tinted itama tana tahowa, dasauri yabude gate da yanzun nan daman ya rufe, shiga ciki motocin sukayi, parking motocin akayi sojoji guda biyu sanye da uniform dake motocin sojojin suka fito suka kame, bude gaban GLK akayi wani matashine yafito wanda bazai wuce 34yrs ba haka, baki dashi yana sanye da shadda mai ruwan toka ga waya a kunnensa yana magana, bude kofan flat nasu akayi yammatan biyu suka fito karaman tafito da gudu ta taho tanajan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 15