Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jazamusu, banda yaransa dayasa sukai bincike sama da kasa shi da kanshi saida yayi tattaki yaje garin yaje layin but gidansu is still burnt, even though that neighbor nasu ta sanar dashi ba’a kona dasu ba but anma Babanta shegen duka sunje asibiti daganan ne basu kara dawowa ba he went to the hospital akacemai an basu bill but basu dawoba bakudi, his mind is not at ease baitaba samun abinda ya tsaya mai araiba sai this, murya chan kasa yace “where are you!? Nurse Safeerah!” Yayi maganan ahankali yadan fuzar da iska yajuya gefe yakai hannu yana kunna side lamp yana kashewa lost in thought. Yarinyar is the most brightest girl he’s ever seen in his life, the kindest, she has the most precious heart, she saved his life, zuman data shafamai was wat saved his hand not hospital, yakasa manceta the way she genuinely cried for him sabida taganshi in pain no one has ever done that ko iyayensa though baisani ba maybe dan baitaba wani major ciwo bane, but this particular guy makes a huge space a zuciyansa, sabida her kindness, free spirit and care, he just wanna know she and her parents are fine! He wants to take care of her! Support her, and gives her whatever her heart desires, gashi duk ba’asan daga ina sukeba, har school da aka cemai Babanta na koyarwa wani primary school haka yaje school dinma basu da information na background na Babanta cus is not standard school principal din dai tacemai yan Maiduguri ne, ahaka bacci yayi awon gaba dashi. ** Mama tashigo dakin ta tadata da kyar ta tashi zaune takalli Waleed dake bacci abinsa one thing about him baya tashi da wuri dan baya bacci dawuri itakuma bata samin enough bacci dan bata isa tayi bacci ba sai Waleed yayi duk kalan gajiyan jikinta yanzu ma da kyar ta tashi, bayinsu tawuce ta shiga brush tafara yi sannan tayo alwala tafito tasaka hijabi tayi sallan asuba, one thing is tunda suka dawo gidan nan batada karfi da ikon zama kayi azkar bayan salla saidai kayi a tsaye dan zasuje main flat girki da gyaran gida, mikewa tayi ta linke dadduma tana enchanting morning zikir nata tazo wajen gado tadan lullube Waleed sannan ta shafa fuskansa tana murmushi tamike tabude kofa tafito tabude kofa tafice, flat din tashigo duk suna bacci basa tashi sai around 9, 10, 11 wata rana har 12 ma ko 1 na rana, kitchen tawuce taga Mama awajen tafara hada abinci tace “Mama kibarshi zanyi komi” murmushi Mama tayi tace “wuce kije ki koma bacci Waleed bai barki kinyi bacci dawuri ba” murmushi tayi she has the best Mom wlh, Mama zata iya dauke duk wani wahalan duniya dan kawai ta huta, tazo wajen Maman tasa hannu ta karbi waken tace “kosai za’ayi”? Murmushi Mama tayi tace “eh da kunu, sai pepper soup na kayan ciki gashinan cikin pressure pot, tunda kin karbe girkin bari na gyaro gidan ni” dasauri tace “Mama duk zanyi w…” hararanta da Mama tayi yasa bata karasa maganan ba tadauki tsinstiya tafice itakuma tashiga aikin tana tunane tunane yanzu haka Baba na chan compound yana wanke cars, watering plant, gyaran grass and sweeping, tsayawa tayi gaban sink din takalli window gari yasoma haske takalli sama azuciyanta tace “Ya Allah baka bacci, I know Mahaifina baida sana’a yanzu baima da hanyar yin sana’ar sabida idanunsa baya gani sosai ko gidan nan sabida he’s familiar with the sorroudings ne saisa yake komi, Mama na is helpless woman da batai karatu ba, I’m all they got Ya Allah! Look at our lives slaving for people da basa appreciating namu ko mana godiya they said this is our payment na ciyar da mu dasuke” tadan fuzar da iska tace “Ya Allah karka dawwamar damu ahaka! Ka yantar da iyayena, kabani source na taimakonsu, duk inda zanje IT Ya Allah kasa suna biya nasami wani kudi” hawaye ne ya sauko idanunta takai bayan hannu ta goge tacigaba da aikin sosai, Mama tagama gyaran falon ta duka tana saka turare taji karan bude kofa dasauri tajuyo Momma ce sanye cikin wani bubu mai mayafi ga charbi a hannunta tanaja fuskanta ahade kaman wacce ke shirin dambe takalli Mama ta zubar, Mama tamata murmushi taduka cikeda girmamawa tace “barka da saukowa Mama Kubra, ina kwana” “kiramin yarki” Momma tafadi awulakance tashi Mama tayi tawuce kitchen tabude kofa tace “kizo Safeerah ana kira” hannunta ta goge tarage gas tabiyo Mama suka fito ganin Momma tawuce ta duka tace “ina kwana Momma” kallon banza Momma ta mata dasauri Safeerah tasauke kanta kasa, Momma ta tabe baki tace “anyways jeki shirya 8 Shamsu zai kaiki inda zaki fara IT, kibar aikin Uwarki takarasa” wani abu Safeerah taji a kirji ta daure ahankali kanta na kasa tace “Momma zan iya gama komi before time aiki yama Mama yawa gakuma Wale…..” “Feerah!” Mama takirata cikin kakkausan murya dayasa Safeerah tai shiru bata karasa maganan ba, Mama tadan gyara magana tace “yaran yanzu basu iya magana ba wani shirme kike gaya haka Safeerah”? Kada kafa Momma tayi tana kallon Mama tace “ke Amina nizaki gwadama makirci? Ohhh wato ke kin kasa gayamin a fuskana aiki yamiki yawa sai ki turomin yarki” dasauri Safeerah tace “Momma wlh bahak…….” Hannu Momma tadaga mata sama sannan takalli Mama tace “na ciyar da mijinki na ciyar dake, na ciyar da yarku na ciyar da jikanku, nine tufafinku, abin shanku, kunzgunku, abincin jikanku, nine makarantan diyarku private university, kin dauka ina kashe uban kudin nan zan bar masu aiki agidan nan ne? Menene amfaninku? Shu’aibu kanina ne jini daya kuma, da babuni da ina zaku? Sabida na rufamuku asiri namuku rumfa da sutura eh shine zaki bama yarki sako aiki yamiki yawa?” Ahankali Mama tace “kiyakuri Mama Kubra kuskure ne kawai da shirmen yara yasa Safeera…..” “Shu’ibu! Shu’aibu!” Momma tashiga kiran Baba ranta abace kaman daman jira take daga tsakar gida ya amsa yashigo gidan da gudu hannuwansa duk kumfa yana tsiyaya anan falon Momma tamai wani kallon banza da takaici tace “shashasha bakasan zaka goge hannu kafin kashigo min falo ba” runtse idanu Safeerah tayi zuciyanta namata daci yanda ake zagin mata iyaye agabanta, Baba dasauri yashiga goge hannuwansa ariga yace “yakuri Mama Kubra, gani kin kirani” cikin fushi tace “Matarka Aminatu tayomin aike da yarku yanzu take sanar dani wai aiki yama uwarta yawa” dasauri Baba yace “Subhanallahi wani irin magana ne haka nakeji Aminatu, Safeerah” Mama zatai magana Momma ta dakamata tsawa tace “lemme finish”Mama tai shiru, Momma tace “dan haka ka tattara matarka da yarka da jikanku kubarmin gidana yanzun nan” faduwa gabansu yayi dasauri Safeerah takalleta tace “Momma dan Allah kiyakuri” Mama tace “Mama Kubra dan Allah kiyi hakuri wlh aiki baimin yawa ba” Baba ya zube yana hada hannu yace “Mama Kubra wanake dashi banda ke? Ina kikeso naje? Taya zan fara? Ga makanta? Bara kikeso naje nayi” cikeda rashin mutunci tace “sai me toh akanka aka fara baran, sabida na rufamuku asiri sai ahaumin aike, mara mutunci kawai butulu daku marasa godiyan Allah matsalan talakawa kenan kamusu dare su maka rana” lumshe idanu Safeerah tayi hawaye na zubomata this is the reason why she never talks take hadiye komi, cus everything she says affect parents nata more, they are being humiliated, abune ya tsayamata a kirji ganin yanda suke begging Momma tana duramusu zagi baki tabude zatai magana kawai sai zuciyanta ya karaya ta fashe da kuka sosai tace “Momma dan Allah kiyakuri, wlh wlh Mama bata aikoni komiba, baki fahimci maganata bane dan girman Allah kiyakuri” Ijiyan zuciya Momma ta sauke tana kada kafafu tace “okay zan salllami masu gadina! Shu’aibu ka tattara matarka da yarka ku koma dakin masu gadi dake gate dagayau kaine zaka dinga bude gate tunda na kore ka bawai kanada wajen zuwa bane” dasauri Baba yace “naji na yarda” zuciyan Safeerah ya mugun sosu, bude kofan sama akayi Salma tafito dawani mahaukacin kayan bacci ganin su Mama duke gaban Momma a falo yasa ta harari Safeerah tace “yarinya sai mugun hali kuma saidai aiki ya kashe Uwarki da Ubanki yanzu suka fara, yazama gateman your mother kuma our cook and maid die da bakin ciki, in kinyi zuciya ke nemo naki kudin kawai an dawo gidanmu ana cinye mana kudin gadon da Baban mu ya barmana, kai Baffa dalla tashi kafita” tashi Baba yayi ahankali yajuya yawuce idanun Safeerah suka kada sukai ja. EPISODE 1️⃣1️⃣ Momma itama ta dakama Mama tsawa tashi kibar nan kekuma wuce kije ki shirya kafin nasa Shamsu ya tattakamin ke” da gudu Safeerah tayi kofa Salma tabita da kallo saikuma tazo wajen Momma tazauna tace “Wlh Momma I hate Safeerah, I hate her ta uban Yaya ma tafini kyau”?Dasauri Momma tajawota jikinta Salma ta kankameta ashagwabe, Momma tace “wat are you saying Salma? Yarinya fara kal dake inake ina hada kanki da black skin Safeerah haba haba, ai sama taiwa yaro nisa saidai yadaga fuska ya kalleta” shafa gashinta Salma tayi tace “Momma harda gashi tafini fa” dasauri Momma tace “Kin fita keda kesa relaxer jibi gashinki common stop the comparison kina ragema kanki daraja ne, the kind money kike spending on your body why will you compare kanki damai shafa alayyadi”? Turo baki Salma tayi ta bala’in jin dadin maganan mamarta tai blushing ta gyara zaman kanta a cinyan Momma tace “you’re the world best Momma”. Dakinsu Safeerah tabude kofa ta shiga idanunta sunyi jaa, waje tasamu akujera ta zauna hawaye na saukowa daga idanunta tana gogewa da bayan hannu, ita kadai tasan metakeji azuciyanta, itafa da ace ita suke zagi, suke ciwa mutunci, suka maida jaka wlh bazata damuwa as long as iyayenta nada martabansu da kimansu, mesa Momma da yaranta this small Salma ke zagin mahaifinta da mahaifiyarta? Why? Wlh kawai tausayin su Mama takeji kuma harda bataso taja musu fitina dasaitama Salma dukan da akace ta zagi Baba bazata karaba, marasa tarbiya kawai da girmama na gaba dasu, she hated gidansu na Kano sabida yan daban anguwansu but yanzu she rather lives there sau dubu da wannan rayuwan gidan na Abuja wani kalan kaskanci iyayenta ke facing? Zata nemi aiki da zai taimaka mata tarike iyayenta da danta, saikuma tai shiru nawa ne kama haya? Nawa abinci? Asibitin Baba, abincin Waleed? How can she do all of those? Itada batada any qualification, takai almost 20min kuka take sannan ta tashi ahankali ganin seven yayi tawuce dakinsu tabude kofa ta kalli gado Waleed na bacci abinsa zuwa gaban gadon tayi ta duka takai hannunta tashafa kan Waleed murya chan kasa tace “Waleed pray for Ummy kaji! I don’t want this life for you my Baby” tai maganan ahankali takai dayan hannunta ta goge fuskanta sannan ta mike tawuce bayi ta watsa ruwa a gurguje tafito Vaseline nata ta shafa ta warware gashinta da sauri gashin yazubo saura baifi 2inches yakai waist nata ba gashin baki sosai ta shafa man kitso tadan taje sannan tasake packing tai donut da bakin sannan tabude sip din tanada tufafi ba laifi tun na akwatin ta na zamanin aurenta ne, wani blue atampa tadauko gown aka maga ta saka sannan ta dauki sky blue gyale mai duwatsu masu kyau babba taciro sannan tayi dauri taciro file na credentials nata datai photocopy tadauki bagpack nata tasaka sannan tasaka flat shoe tafesa body spray nata mai dadin gaske tafito, tajuyo ganin Waleed na bacci still tafito tabude kofa tafito tsakar gida tayi kyau sosai wlh gata da tsayi ba sosai ba dai, she looks so good, flat din tawuce tabude kofa ahankali Momma tagani da Shamsu suna zaune a dinning suna breakfast ya shirya tsaf cikin kananun kaya duk suka kalleta karasawa wajen tayi tace “Ya Shamsu ina kwana” wayansa yadauka da car key yamike yace “muje ke I have somewhere to be kina batamin lokaci” gyadamai kai tayi Mama tafito daga kitchen rikeda kula Safeera tace “natafi Mama” Mama bata kalleta ba gudun kar ace tai laifi tace “adawo lpy” Safeerah tajuya tabisa suka fito compound Baba ya wanke motarsa tsaf yana kara gogewa sai sheki motar take suka taho wajen, yayi murmushi yace “an fito sannu da kokari Shamsu nagode sosai, Safeerah sai an dawo ko, ayi addua, Allah bada sa’a” Ameen Safeerah ta amsa ciki ciki dan fushi take da Baba, Shamsu bai tankaba yashiga motan itama tashiga gaba yaja motan aka bude musu gate suka fice, saida suka shiga kan titi cikeda isa Shamsu yace “saura mukaje ki disgani! This is number one biggest construction company a Nigeria kaman irin su Julius Berger haka suke, suna gina titina, railways, estate etc, this people are bastardly rich, the Maradis kenan! Kudinsu gado sukayi tundaga zamanin kakannin kakanni and gasu all of them are bless, Babansu shine Maradi Jet co yana harkan jirage he’s the only person a Nigeria dake kawo jirage yana saidawa yana bada shatter, sai dansa shine mai Maradi construction din nan Babban Soja ne kaman wasa yabude this construction company boom sun zama global, bama ya iya managing abokina dawani Indian Man Paresh ke mishi managing company, sai kanwarsu Layla tana auren dan shugaban kasan Nigeria sai sisters dinsa biyu da basuyi aure ba lemme even tell u I’m trying to see yanda zan samu daya na aura sabida family mu yazama so powerful but that big brother nasu baya wasa and seems he doesn’t like me, nafara magana da Lubna yahanata tacemin school zatayi she blocked me so dan haka banso ki kofsani, mind your business kiyi aikinki kibar wajen kidawo gida, wlh if you do anything dayasa aka kirani I will kill you Safeerah u hear me” yadaka mata tsawa gyadamai kai tayi tace “naji Ya Shamsu” company sukakai yanada girma tsaresu akayi a gate saida Shamsu yakira Auwal yasa aka barsu suka shiga company is so big ga manya manyan motoci na goni daban daban parked a big space din, parking yayi inda ake parking sannan yafito ahankali Safeerah tabude motan tafito wani iri jikinta yamata saitaji wani irin tsoro da anxiousness irin wanda kakeji din nan idan kaje sabon waje tafiya Shamsu yafara hakan yasa tabisa tana tafiya ahankali suka shiga building din, receptionist ne a lobby din saiga wani status na ginin gida da titi anyi komi me kyau is just a work of art ta tsaya tana kallo Shamsu yafara tafiya jin shiru yasa yajuyo ganin ta tsaya tana kallon abun yasa yaji kaman ya dura mata ashar amman ba dama a kufule yace “Safeerah!” Firgigit Safeera tajuyo da kanta ta kallesa yamata wani mugun kallo ta taho da sauri kanta akasa suka wuce 2nd floor wani office da aka rubuta CEO suka wuce secretary tace “are you Mr Shamsu?” Dasauri Shamsu yace “yes yes” murmushi tayi professionally tace “welcome Sir, Mr Auwal is expecting you” tayi maganan tana bude musu office Shamsu yace “thank you” ya shige Safeerah biye dashi ta shiga tana zaro manya manyan idanunta tana kallon office din da bata taba ganin me kyau dinsa ba ga wani mutumi zaune gaban table yana magana dawasu ma’aikata dasuka karesa hakan yasa tashiga bin ko’ina na office din da kallo kaman bakauya while Shamsu yasami kujera yayi zamansa comfortably, shikuma Auwal ya sallami ma’aikatan suka juya sai alokacin idanunsa suka sauka kan wata yar yarinya dayabi da kallo tundaga kan kafafunta har zuwa saman kanta Shamsu yataso cikin murmushi yace “Boss Auwal mutumina” suka wani kashe hakan yasa Safeerah ta natsu takallesu Auwal yace “Shamsu wai har yanzu kaki aure” Shamsu yace “kai kayi”?Suka kara kwashewa da dariya sannan suka saki hannun juna Auwal yakoma yazauna yakalli Safeerah yace “Sister ka ce”? Kallon Safeerah yayi datazo wajen table din da sauri gabanta nadan faduwa tace “ina kwana” shiru yayi yana kallonta saita sauke kanta kasa, murmushi Auwal yayi yace “you remind me of Lubna kanwata haka takeda tsoro, sit down please” yanuna mata kujeran gaban table din zama Safeerah tayi ahankali, Auwal yace “give me the necessary document” bagpack nata tabude taciro komi tadago kanta tamikemai karba yayi yashiga dubawa saiya dan dago yasake kallonta kanta akasa saiya kalli Shamsu yace “kacemin kanwarka” dan sosakai Shamsu yayi yace “kaga surname dina da nata daban ba well kasan Momma da kwashe kwashe woman of people, wani brother ta tadauko daga chan Kano da iyalansa itane cinsu shan…..” katsesa Auwal yayi yace “I get she’s your cousin Sister” dan yatsine fuska Shamsu yayi baiyi magana ba, saiya sake murmushi yakalli Safeerah da kanta ke kasa yace “welcome to Maradi Construction Company Malama Safeerah” dan dago kanta Safeerah tayi takallesa saita gyadamai kai anatse tace “thank you Sir” zaro idanu yayi yace “wani Sir call me Yaya Auwal tunda ni abokin Yayanki ne can I see designs naki” gyadamai kai tayi tasake bude jakan taciro wani files ta basa ya karba, to be honest she’s an average designer bawai ta iya zanen hauka dinnan dazasuyi wowing naka bane, nothing special, Shamsu shima na ganin zanen yayi tsaki yace “danasan baki iya zane ba daban kawoki nan ba doluwa kawai” dan kallonsa Auwal yayi yace “don’t be harsh Bro! Duk ahaka muka fara muma ai it’s okay! She will get better with time” yakalli Safeerah da kanta ke kasa yace “don’t mind Yayanki, you are trying, naga 6weeks zakiyi ko”? Gyadamai kai tayi yace “okay zansa secretary dina takaiki HR department zasu danyi magana dake sannan su kaiki inda yadace dake dazakiyi aiki pay, attention and learn bazaki samu problem dakowa ba, for me the only thing da zaisa nayi fada dake is late coming, this is one of the strongest rule na company nan we don’t tolerate late coming, be punctual okay Safeerah” gyadamai kai tayi ahankali, Shamsu yace “wai ke wawiyan inane baki iya magana bane ko bakinki na ciwo”? Dasauri tace “toh naji Yaya Auwal” Shamsu zai kara magana Auwal ya danna wani bell yayi kara hakan yasa aka bude kofa secretary tashigo tace “I’m here Sir” files da komi na Safeerah yabata yace “take her to Mr Gorge HR, he will take it from there” “yes Sir” karba tayi takalli Safeerah tace “let’s go beautiful Miss” dan murmushi kadan Safeerah tayi tamike tsaye tabita suka fice, ganin Auwal yabita da kallo yasa Shamsu yadanyi gyaran murya dasauri Auwal ya kallesa, Shamsu yace “don’t mind me I’m grumpy sabida bacci bai isheni ba Momma tace saina kawota nan, ga yarinyar da shegen shirme dudda tayi aure harda d’a” dasauri Auwal yace “Matar aure ce Safeerah”? Girgiza kai yayi yace “no bazawara ce! Mijin ya saketa, tanada yaro that’s almost 3 now” ahankali Auwal yace “ayyah that’s sad” Shamsu yayi murmushi yace “but kasan Salma ba my BabySis she’s still very single she’s only 22yrs” dan shiru Auwal yayi yana kallonsa part of the reason baiyi making Shamsu a close friend ba dudda tare sukai Havard University a kasan waje sabida halinsa ne yanada wasu halayya da ya tsana he’s strongly against, this less than 5mins sitting yayi abubuwa da dama da bayaso from yanda yayi treating Safeerah, see rayuwan nan not all fingers are equal, akwai masu kudi akwai talakawa but why will u be feeling special sabida kanada kudi kaman kafi talaka? Look at the way yake treating yarinyar sabida yaga yana kallon Safeerah yadauka sonta yake shine harya faramai tallan sister sa taciki Salma, dan murmushi yayi yace “wooooh ahh ni inada Babe dina zamuyi aure soon ma jira nake agama na Ya Salim” Shamsu yadanyi wani disappointing smile bai kara maganan ba sukayi hira kadan Auwal yasake yin baki hakan yasa Shamsu yatashi yamai sallama yatafi. EPISODE 1️⃣2️⃣ Mr Gorge was so good to her, she must be special dan basu taba accepting yan IT ba, ko yan NYSC, he was kind to her yamata explaining komi tunda IT ne kuma 6weeks zatayi dau zata dinga yin one week a each department sabida tasami vast knowledge on how construction companies work, yace this week she will start with Marketing/Customer Care Service Department yatashi tabisa abaya suka koma first floor wani babban daki that looks like classroom yabude yashiga tana biye dashi mutanen office din sunkai 15, kowanne gaban laptop ga chair mai kyau ga coffee machine da water dispenser, ga TV, ga telephones dayawa wasu na waya, very fine office kaman wani conference room duk aka bisu da kallo cikin murmushi yace “we have newbie, she’s here for 6weeks IT, her name is Safeerah Shu’ibu let’s welcome her” tashi dukansu sukayi suna tafi duk kunya yakama Safeerah banda school nasu bata taba zuwa organization ko kampani haka ba, tayi murmushi kadan tadanja gyalenta tana rufe bakinta kaman wata yar kauye tama kasa magana balle ta gaidasu, wata mata tazo wajen yar babba haka tana sanye da abaya kafin tai magana Mr Gorge yace “meet head of this department Madam Maimuna” ahankali Safeerah tace “ina kwana” murmushi tamata takai hannu ta karbe gyalenta daga wajen baki tace “welcome to my dept Safeerah, don’t be shy, lets go to your sit” takama hannunta Safeerah tabita taja mata kujera ta nuna mata ga laptop awajen tace “zauna” zama Safeerah tayi ahankali ta sauke jakanta Gorge yawuce yafita Madam Maimuna tawuce wajen coffee machine tasaka paper cup tamata coffee tadauki wani cookie daganan pantry takawo ta ijiye gaban table na Safeerah dasauri Safeerah ta kalleta murmushi tamata tace “have some coffee and calm yourself down i will be back to give you proper orientation nai assigning miki task” gyadamata kai Safeerah tayi tawuce ta tafi, bakaramin dadi taji ba sai tadan fara natsuwa kowa kuma yacigaba da aikinsa babu mai wani kallonta. Wuraren 11 ya shigo falon, Ammi natare dawata bakuwa makociyarsu ce, ahankali yace “ina kwanan ku” Ammi tace “ka fito zokai breakfast” girgizamata kai yayi yace “sauri nake Ammi I have meeting with Paresh and Auwal, where are the girls?” Murmushi Ammi tayi tace “sun tafi school” juyawa yayi yace “natafi Ammi” “adawo lpy Allah bada sa’ yabude kofa yafita, anatse yake tafiya wajen wata black Lamborghini Urus yaje yabude motan yashiga yadauki black glases dinsa yasaka sannan yaja motan gateman dinsa na gaidasa rage gudu yayi yasa hannu a dayan seat na motan yadauki bandir daya na yan 500 dake Wajen yabasa sai godiya yake yawuce yatafi. Wuraren 12 yakai company nasu kwata kwata shi baya parking anan waje, wajen parking motarsa yaje a kasan basement yadan dade cikin motan sannan yafito sai wani uban kamshi yake yawuce yafito direct wani elevator dake wajen ya shiga daya kaisa 3rd floor yafito yawuce wajen wajen wani off office dake wajen gawata secretary dake aikinta awajen bamata lura dashi ba, kamshin turarensa dataji yasa tadago kanta dawani irin sauri tamike tsaye tace “welcome back Sir, it’s so good to see you” batare daya kalleta ba yace “thanks I need coffee please” “coming right up Sir” office dinsa yabude yashiga that looks like a suite ya mahaukacin hadu wucewa yayi yazauna yashiga bude files da aka ijiye mai awajen dan ansan yau zaizo ya kunna desktop din yakalli agogon sa he needs to be in barrack by 2 yanada meeting yau da Lieutenant General, glasses na idanunsa ya zare akai knocking kofa yace “common in” Auwal ne yayi wani murmushi yace “welcome Boss” “thanks” ya amsa yana duba files din, aka sake knocking wani dan india ne yashigo sanye da suit zai iyakai 45yrs yace “welcome Boss” “thanks Mr Paresh” yafadi still reviewing files din saiga secretary ta shigo tace “Sir your coffee just the way you love it” ta ijiye agabansa yace “thanks Miss Becky” murmushi tayi tajuya tafita, yadauki coffee yakai baki ya kurba ya ijiye sannan yakalli Auwal yace “mergin na gross profit namu yayi decreasing compare to last year, what happen?” Yanda yake magana bazaka taba dauka Auwal kaninsa bane babu wani wasa is just a strict work conversation, bayani Auwal yashiga yi yana hadawa da report na accounting department, meeting din yakaisu har zuwa one but it was productive suka fito dan zuwa salla shida Auwal suka jera sai gaidasa ake duk randa ya shigo idan zai tafi he gives them lot of money araba so ma’aikatan sa loves him die, nan masallacin su

Chapter 5 of 15