Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
20k idan zaki tafi gobe saina baki saiki hada da 15k dinki ki samowa Waleed dan abincin daya sawwaka da pampers ko irin me guda goman nan ne” shiru tayi ta tsare Mama da idanu tana kallonta, Mama tace “menene kike kallona haka?” Hannun Mama takama ta jujjuya tana kallon uban shedan yanka wasu sun warke wasu basu warke ba, takai hannunta ta taba kashin wuyan Mama, da fuskanta da duk yayi wrinkles, sai hawaye yafado idanunta dasauri Mama takai hannu ta share mata tace “zaki fara yauma ko? Kina wani duddubani kaman patient, duk randa kike neman kuka abinda kikeyi kenan” Lips dinta ne suka fara rawa tace “Mama na tambayi wajen IT ko zasu bani aiki parmanently na tara albashina na kama mana gida mubar nan?” Tsareta Mama tai da idanu sai kuma tai murmushi ganin yarinta tace “yaro man kaza, shi aikin dakike magana akai ba su suka samo miki ba”? Ahankali tace “eh dudda haka amman ai basune masu kampanin ba” Mama tai murmushi tace “ko dubu dari ake biyanki bazaki iya rikemu ba Safeerah mubar maganan ma dan Allah, kinyi tunanin makarantan ki? Mahaifinki duk wata wata yake zuwa checkup na idanu da hawan jini, ga Waleed very soon zai shiga 3yrs za’a sashi makaranta dole, abincin sa fa, pampers waye waye, I know kin damu but u can’t do this Safeerah!” Rushewa da kuka sosai Safeerah tayi dayasa Waleed yazo wajen da gudu yana leko fuskanta Mama tace “wai me haka Safeerah kinga zakisa yaron nan kuka ko zo Waleed” Mama ta daukeshi yafashe da kuka yana kallon Safeerah data kasa daina kuka, Mama tace “wlh banson wannan halin kawai saiki tasani agaba kina kuka ba’a miki komi ba eh” cikin kuka Safeerah tace “Mama nagaji da ganinki ahaka nagaji, kullum daga safe har dare aiki kike, kin zama yar aikin wasu da ba’a miki godiya sai zagi da cin mutunci, while Baba an maidashi mai gadi da wanke mota ana zagin mahaifina kullum agabana, Mama mubar nan ko barane muje muyi yafimin da this life we are doing here, school din banaso lets leave Mama dan Allah” Safeerah kuka Waleed kuma Mama tama rasa wazata lallasa sai kawai itama tafashe da kuka tace “Safeerah yakikeso nayi eh? Ina kikeso nasa kaina naji dadi? Ni yar rikoce banmasan iyayena ba Babana yarasu kafin ahaifeni mahaifiyata wajen haihuwana tarasu yar rikoce wajen yan uwan Babana, wahalan danasha wajensu bana shan kalansa anan, mahaifinki shiya ceceni ya aureni sukace sun yafeni banda kowa sai mahaifinki duk inda zaisa kafa zan saka tawa sabida yabani gatan daban taba samun kalansa aduniya ba, wannan shine hallaci duk runtsi duk wahala ina tareda shi, dagani har mahaifinki sabida ke muke zaune anan nothing is important arayuwanmu face ke da Waleed as long as zaman mu anan zaisa ki cigaba da samun education Waleed na samin abinci da kulawa fakat mu karmu samu mun hakura bakomi, stop crying we are doing this for you, no condition is parmanent watarana sai labari, zagi da cin mutunci baya kari, dan Salma ko Shamsu ko mahaifiyarsu sun zageni it’s okay, watarana ko ance suyi bazasuyi ba, abinda nakeso is just focus on school naki, kigama IT dinki and become somebody, as for Waleed zan kula miki dashi as long as I’m alive kinji, please karki bari Babanki yaji maganganun nan kar BP sa yatashi ya isa zo nan yarinya na nasan badadi ana zagin miki iyaye amman kiyakuri kinji Feerah na” Mama ta rungumota zuwa jikinta lamo tayi jikin Mama haka shima Waleed yayi lamo yana kallon mahaifiyar tasa dake kuka Baba yadade gaban dakin tsaye dan yaji komi sai kawai yawuce yakoma waje yabuga tagumi, yasan watarana sai labari shi bayajin kyashin yima yayarsa Kubra komi sabida takula da lafiyarsa, tasaka yarsa a makaranta da sauransu, kawai baitaba sani yayarsa Uwa daya Uba daya zata iya maidashi mara daraja dan aiki mai wanke mota ba da gadi tana zaginsa da cimasa mutunci gaban iyalansa ba, shi yasan da shine mai hali Kubra tazo garesa bazai taba maida rayuwanta haka ba, zai iya kwashe iyalansa sunbar nan ba but tunaninsa shine aikin me zai samu baya gani? Tayaya zai rikesu? Mama Kubra ta cutar dashi sosai kawai baiso yayi magana ne sabida zumunci amman bazai taba mance lalata yaruwan yarsa datayi ba ta auramata dan shaye shaye mai duka. Basu dawo gidan ba sai wajen 12 tuni Safeerah tai bacci anan falo shima Waleed haka, Baba yafito daga uwardaka yafito yazo yabude musu gate, driver ke tuka Momma da Salma dake baya suka shigo ya maida gate yarufe yabiyo motan Momma ta sauko yace “sannu da zuwa Mama Kubra” kallonsa tayi sannan takalli driver ta tace “kai zaka koma BQ yanzu” cike da girmamawa yace “toh Hajiya” Salma tayi gaba batare data gaida Baba ba tace “ka daukomin kayan dinki na a boot” Momma tace “ka tsaya kana kallona bakaji abinda Salma tace bane” ahankali yace “naji” bude booth yayi yadauki jakan dinki yawuce flat Momma biye da shi har bene yashiga hawa Momma tace “nasan ba hankali gareka ba ka ijiye agaban dakinta baka shigo ba” daga ciki Salma tai kwafa tace “yashigomin daki bana gaura masa mari ba hmmmm” Baba baice komiba yawuce ya ijiye gaban dakin Momma tayi dakinta tace “ka kashe wutan ko’ina” anatse yace “toh” Yasauka yakashe wuta yawuce yafita. EPISODE 1️⃣5️⃣ Washe gari da sassafe Safeerah ta tashi ance ba’ason latti bayan tai salla ta taho flat tas tashiga share share tana azkar ahaka ta gyara ko’ina tasa turare 7 har yayi Mama tace “maza jeki wanka” wucewa tayi taje tai wanka wani black abaya tasaka yau is simple abaya babu wani kwalliya ajikinsa dan stones dake jiki sun dade da fita tun na akwatinta ne shima rigan, closed abaya ne black but a goge, tasaka wasu hook earings farare masu kyau Mamane tasayo mata su a kasuwa, batama tsaya gyara gashinta ba gyalen kawai tayafa aka tadauki jakan bayanta ta goya tafito she smells good very mild, Mama tries dasai mata yan turaruka da khumra haka da yan kudinta tasaka flat shoe black tafito, wucewa tayi zataje flat Baba dake shigowa gidan baiso yauma takara tafiya da bakin ciki yace “wuce kitafi” dasauri tajuyo tace “Baba ina kwana” hannunsa yasa a aljihu yaciro 10k yamika mata yace “gashi ki hada da wanda mamanki tabaki ki sayoma Waleed abinci da pampers saiki cire na mota kisai abinci kuma kici” murmushi tayi tace “toh Baba nagode Allah kara bude, jama’a Babana yafi nakowa principal Baba” dariya Baba yayi yace “uhmm Principal da ba idanu yanzu” murmushi tayi tace “da nazama Nurse dana maka magani” yanayin fuskan Baba chanzawa yayi sabida burinsa kenan Safeerah tazama Nurse, wucewa Safeerah tayi tafice yabita ya tsaya a kofar gida tafiya tayi harta fita wajen layinsu tasami keke tahau yakaita bakın junction tasami mota yakaita har layin wajen aikin sannan tatako daga junction zuwa company 8:05AM tashigo kampanin kafin takai ciki was 8:09 zatai hanyar office nasu receptionist tace “you need to sign in Miss Safeerah” gyadamata kai tayi tazo tai signing receptionist din na kallonta ahankali tace “you’re very pretty Miss, I love this plenty hair on your forehead” kallonta Safeerah tayi sai kuma akunyace tace “thanks” ta ijiye biro tajuyo tawuce zuwa office tabude tashiga Madam Maimuna na desk dinta, ahankali tace “morning” sannan tawuce wajen Madam Maimuna dake kallonta tana murmushi adan kunyace tace “ina kwana Anty”? Murmushi tamata tace “lpy lau ga files naki jeki karasa sai na koya miki next abu, before then get coffee or tea, anjima da rana zamuje canteen muci abinci Oga yace kowa yadinga zuwa cin abinci bill on him, anytime Oga Salim ke gari enjoyment kawai akeyi a kompany, jiya yabada kudi araba naki na hannun Mr George” gyadamata kai tayi ahankali tawuce ta zauna tafara aiki. Wuraren 12 yashigo company cikin wata army green motan kana ganin motan kasan na soja ne tundaga plate number, Parking akayi chan aka bude kafansa na sanye cikin boot din sojoji me ruwan kasa yafito anatse yana sanye cikin wandon sojoji daya zauna ajikinsa tsaf, ba rigan sojoji mai common flag ne ajikinsa ba wani green riga ce mai v neck data kama jikinsa tsam har 6packs dinsa kana gani yayi stocking da rigan gawani arnen belt na sojoji a waist nasa hannun rigan gajerenne so kana ganin muscles dinsa a murde sosai, idanunsa sanye da bakin glases sosai, kansa ba hula sumansa sunyi wani irin kyau ka gansa sai kwarjininsa ya cika maka ido maida motan yayi yafara tafiya anatse few employees nasa na gaidasa instead ya shiga ta basement ta main entrance ya shiga dasauri receptionist din tace “welcome Boss” dan gyadamata kai yayi yawuce yashiga hayowa staircase anatse yana bin ko’ina da kallo har yaje fourth floor a staircase ko gajiya baiyiba office dinshi yawuce secretary dinshi na biyosa ciki tace “welcome Sir, coffee or tea Sir?”Batare daya amsata ba yawuce ya zauna yasa hannu ya kunna desktop nasa sannan yace “none, excuse me” dasauri tace “yes Sir” tajuya tafice fuzar da iska yayi kawai yaja keyboard yayi logging into ystem din he have access to everything na company shi, direct CCTV camera file ya shiga yana shiga office office ya shiga office din customer care ya tsaya chak yana kallon Safeerah dake aiki ga file a hannunta tana cikawa, there’s something he’s feeling, he just wanna take care of this girl and repay her kindness, baitaba haduwa da y’a mace data tsayamai arai like she ba, he doesn’t know how to help, and also yanajin nauyi yaje yafara mata bayanin waye shi da yanda yasanta da menene menene, he just wanna get to know her first, zooming camera yayi yana kallonta da kyau kaman tana gabansa, ringing wayansa yashigayi batare daya jaye idanunsa daga screen dinba yadauki wayan yakai kunnensa yayi shiru yana kallon screen din. “Ina kwana Baby” yaji muryan Nana, yace “how are you” “gani nan banida lpy” “meke damunki”? Yayi tambayan yana zoooming system din ganin Safeerah tamike yanabin ta tawuce wajen Madam Maimuna, Nanah tace “marana ke ciwo” ahankali yace “sannu go and see Dr ki karbi magani” murya chan ciki tace “Mami taje office, babu kowa agidan sai ni kazo ka kaini dan Allah” hankalinsa gabaki daya nakan system din yace “I’m kind of in the middle of something right now, but get ready I will send John yazo yakaiki” muryanta ba dadi tace “okay nagode” “Allah sawaka” yafada ahankali yana zare wayan ya katse yadan cire idanunsa kadan daga system din yayi dialing wani number da akai saving da John yakai wayan kunnensa yamaida idanunsa kan System daidai Safeerah na juyowa rikeda wani paper a hannunta datake dubawa looking so serious daidai John yadaga yace “Sir” murya kasa yace “I need you to pick up Madam akaita clinic” anatse yace “okay Sir” katse wayan yayi ya ijiye yana kallon screen din chan yadaga wayan office nasa yakai wayan kunnensa Hajiya Maimuna ta dauka zata fara gaidasa yace “I need report na feedback na client namu na last month” dasauri tace “yes Sir” anatse yace “give the newbie tasameni a parking space awaje I’m going out” dasauri tace “angama yallabai” ijiye wayan yayi yakashe system din yadauki wayansa yafito daga office Secretary tamike tsaye dasauri, yawuce this time lift yashiga yasauka kasa yafice yaje wajen motansa ya jingina da motan yayi folding hannunsa a kirji ya tsare kofan entrance da idanu cikin dark glases nasa yana jiran yaga fitowanta, ahankali Safeerah tai pushing door tafito rikeda file a hannunta Madam Maimuna tace “Oga yana waje yana jiran file din” batasan ko Oga Yaya Auwal ko Ogan daya dauketa a mota ba tana bude kofan ta hango mutumin jiya sanye da kayan sojoji yayi folding hannu a kirji, kaurin muscles dinshi zaikai dan hannunta sau ashirin halan, wannan duk wanda yama duka saiya mutu, wani irin kwarjini yamata tunda tamai kallon farko bata karaba tasauke kanta kasa tarike wuyan gyalenta da hannu daya da iska ke neman fincikewa dan batai rolling ba tashigo tahowa, tundaga yanda take tafiya yake kallo exactly the way she walks when she was 15yrs old, fuskanta ya tsare da kallo yana kallon gaban gashinta daya nuna sosai sabida iska tana tahowa wani iri jikinsa yahau masa da he can’t really explain kafin dan bugawa da kirjinsa yayi cus he just can’t deny she’s damn pretty kaman lokacin, yanzu she looks cuter ma, he keeps picturing fuskanta 5yrs ago sanda tana kuka tana cemai karya mutu, karasowa tayi gabansa tadan bar tazara a tsakaninsu dudda haka saida yaji mild feminine kamshin datake that’s so peaceful yaji kawai hankalinsa ya kwanta kanta adan kasa ahankali tace “ina kwana, head of department tace nabaka this file” kaman karta dena magana she sounds so girly, so feminine, she speaks like mace, that feminine energy grip his all 5senses, he loves when a woman act and behaves like one, not all those strong independent Goddesses of what a man can do a woman can do it better, yadan kalli gaban sumanta dake nunawa sosai batare da ya karbi file dinba yace “meya sami kallabin ki ko hula gashinki ke nunawa haka?” Dasauri tadan kallesa dasauri ta sauke kanta sabida fuskanshi ba rahama gawani glass kaman mugu, takai hannunta tadaura gaban kanta saita jawo gyalen gaba sosai murya chan kasa tace “sauri naitayi na manta banyi rolling agida ba” “Do something about it!” Yafadi da so much authority kaman wani Babanta ko yayanta, dan sake dago kanta tayi ta kalleshi dasauri tamaida kanta kasa tace “to” hannunsa yamika mata alamun tabasa basa tayi ahankali ya karba tajuya da mugun sauri zata wuce “did i say u can”? Dawani irin sauri tajuyo taga kaman ita yake kallo ta glasses din maida kanta kasa tayi shikuma yashiga bude file din batare daya kalleta ba yace “gyara veil din properly” dan kallonsa Safeerah tayi ganin ba ita yake kallo she felt some type of way, haka Bosses ke behaving da ma’aikatan su ko wannan daban ne? Hakanan sai jikinta na gayamata kaman he’s trying to protect her ne saitaji kaman da ace tanada brother he will be just like him, ahankali ta gyadamai kai saitadan juyamai baya takalli side ta warware gyalen tafara kokarin rolling dan dago kansa yayi yakalleta daidai iska yakada gyalen yahango uban gashinta datai donut dashi ga keyanta wasu gashi dayawa sun kwanta lub sunyi kyau kaman yar jaririya, that earing a kunnenta looks beautiful kaman wata babydoll wani irin yirrrr jikinsa yayi da sauri yadauke kai, rolling gyalen tayi ta chusa akasan wuyanta ya zauna daram tajuyo taga har lokacin duba file din yake ta maida kanta kasa, dago kansa yayi yakalleta hakanan jiyayi breath nashi yadanyi seize dasauri yasaita kansa rolling din yamata kyau she looks like yar Arab yamika mata file din yace “tell her I need na October I will collect the two together gobe” gyadamai kai tayi tasa hannu zata amsa gently kasa kasa yace “you look modest when you’re properly covered!” Saiya saki file din yabude mota yashiga yaja hakanan kasa tafiya tayi for a while kafin da kyar ta fara tafiya tana maimaita kalmomin dayayi mata, you look modest when you’re properly covered! Office takoma tabada sakon duk suka fito tare salla sannan suka wuce canteen yau taci abinci takoshi suka dawo. Kiran John ne yashigo wayansa hakan yasa yadanna kiran yayi connecting da mota John yace “Sir they want to admit shine nace nakira nagaya maka” shiru yadanyi ahankali yace “I’m coming” katse wayan yayi yay kwana wani private clinic yawuce babban gaske awaje yaga John yana jiransa shima yana sanye da uniform yana gamında ya kame anatse yace “at ease soldier, let’s go” wucewa sukayi ciki sama direct wani private room sukayi har zuwa gaban dakin John ya tsaya a waje yace “this is the room” ahankali yabude kofan wata kyakkyawan yarinya fara kaman balaribiya ce kwance kan gadon tana sanye da atampa gown da gyale an makalamata drip yarinyar akalla zatai 26yrs haka tana ganinsa tawani narke tana kallonsa kaman yanda yake kallonta ya maida kofa yarufe yataho gaban gadon ya tsaya tareda folding hannunsa akirji yana kallonta sosai dayasa ta sauke idanunta kwarjinin sa yayi yawa hannunsa yamika yadauki file dake saman table ahankali yace “when did u start having painful period”? Cikin muryan marasa lafiya tace “just this month” chat nata ya karanta ya ijiye sannan yasake kallonta ahankali yace “sorry” gyadamai kai tayi kaman wata yar yarinya daidai lokacin aka bude kofa wata macen Dr tashigo tace “barka da zuwa yallabai” kai tsaye yace “tell me everything wat is wrong with her” ahankali doctor tace “don’t worry matarka is going to be okay is just period i will keep her on observation zuwa anjima idan ya lapa saina sallameta” gyadamata kai yayi yace “okay thanks” yasake kallon Nanah dake kallonsa ahankali yace “kinci abinci?” Girgizamai kai tayi, yace “me kikeso?” Narkewa tayi sosai tace “Boba tea” gyadamata kai yayi yajuya yafice tareda rufo kofa cikeda farin ciki Nana tawani yunkuro suka kashe itada Doctor tace “yesss! Thank you Habibty” takoma dasauri ta kwanta jin ana kokarin bude kofa yashigo Dr tace “okay bari naje please kar abarta ita kadai” gyadamata kai yayi tawuce tafita tarufe musu kofa yasake kallonta itama shi take kallo yawani kara kyau looking damn fresh weather China yamai kyau, so take yazauna kusada ita abakin gadon amman yana tsaye kaman soja oh sojan ne fa, ahankali tace “kazauna Babe” girgiza mata kai yayi yace “no I’m okay like this” zuciyanta bai mata dadi ba ahankali tace “sorry I know kana wajen aiki i made you worry” calmly yace “just focus on yourself ba matsala” gyadamai kai tayi tai lamo she’s just thinking of mezatayi that will make him come to her she wants to somehow cire veil nata atampan data saka ana ganin boobs nata sosai dan wuyan rigan yasauko kasa sosai, ringing wayansa yayi hakan yasa yakai hannunsa aljihun wanda yaciro wayan ganin KB ne yasa yakai wayan kunnensa yace “wats the outcome KB”? Dan ijiyan zuciya tasauke jin da namiji yake magana ba mace ba takai hannunta tadan ja gyalenta yafadi awuyanta tana wani serious juyawa gyalen zai rabu da ita yafice daga jikinta, gashinta a tsefe ba laifi tayi parking nasa an tsaga an raba biyu tasha relaxer abinta jin yana magana kaman he’s ending the call yasa tawani kama cikinta ta tashi zaune ta kifa kanta a guiwa tayi wani nishi datasa ya katse wayan yadan duko da kansa gently yace “Nan……” bai karasa kiran sunan nataba sabida yanda Nanah tadago kawai tayi hugging nashi gyalenta na fadawa gefe kawai tafashe da kuka sosai tace “Babe zan mutu ciwoooo” shifa wani irin mutum ne bayason any form of body contact da matan daba muharraman sa ba even though Nanah zai aura batariga tazama matarsa ba hannayenta yakama yacirota daga jikinsa yace “just lay down hold on lemme get the doctor” ya kwantar da ita duk tana kallonsa ko sau daya bai kalli kirjinta ba, da kyar ta kwanta yajuya kawai yafice daga dakin ran Nanah yamata ba dadi instead of yayi hugging nata back and pet her mtsww waje yafita yakira Doctor da kansa sannan yadaga waya Mom yakira tana dauka yace “Mom can you call Maman Nanah she’s in the hospital sick no one is here” dasauri Mom tace “ohh no how is she wait bari na fara kiran Mamanta tukunna” ya katse wayan bai kara komawa dakin ba har saida wata mata tashigo asibitin, Lecturer ce tana sanye da lace ubansu tana ganin Salim tace “ohh sannu da kokari Salim yanzu kana tsaka da aiki ta dagoka” sauke kansa kasa yayi yace “bakomi yanzu zan koma zan dawo anjima idan ba’a sallameta ba Allah kara sauki” kafin tayi magana yawuce John yabisa abaya murmushi matan tayi tawuce dakin tana bude kofa suka hada ido da Nanah dasauri tace “ina mijina Mommy”? Maida kofa tayi ta taho wajen gadon tace “yatafi yace idan ba’a salameki zuwa anjima ba zai dawo” dan tsaki tayi ta cisge drip din Mamanta na kallonta saikuma kai tsaye tace “bangane ba Nana Khadija me kikeyi haka?” Dan turo baki tayi tace “ni lafiya na kalau da Besty nahada baki” “and why did u do that Nanah”? Akufule tace “Toh Mommy tun yaushe yadawo yaki zuwa yaganni, Mommy he’s not romantic at all, baya nan nan dani, kullum nike kiransa, he acts so cold towards me, kawai i just wanted his attention and affection saisa” ran Mommy baci yayi tace “to dan you wanted his attention sai kibi ta route din rashin lafiya? Are you okay kuwa at all Nana?” Kaman zatai kuka tace “Mommy baya rawan jiki akaina fa saini” dakuwa Mommytamata tace “kinci ubanki kaga yarinya kin dauka kowa ya iya shirmen hauakan nan nan da mata? Akwai abinda kika rasa? Kin taba cemai kinason abu baiyiba”? Nana ta girgiza kai, Mommy tace “bada baki daya kikace kina asibiti yazo ba kafin yan uwanki ma suzo yabar aikinsa jibesa da uniform ajiki akwai care and affection dayafi haka? Ku yaran zamani sai kunga maza na kawo flowers yana tura that long epistle of love message shine so ko well guess wat Nana? Men like Salim don’t have that time, he’s rich I mean wealthy with a successful career, sannan shiba yaro bane dazai dinga wasting tima nasa unnecessary nonsense, kawai, yau duka duka bikin naku saura 14days, kika kara gwada abu haka saina saba miki wlh tashi mutafi wawiya kawai” tashi tayi ta yafa gyalenta suka fito sukaje office na Besty ta Rahama itama Mommy ta wanke ta tass sannan tace “nawa bill din”? Rahma tace “ai yabiya komi” Mommy takalli Nanah datai smiling tace “you see harda boba tea yasiya miki” tanuna hannunta dake rike da Boba tea tace “you don’t know how lucky u are nonsense girl” suka wuce suka tafi. EPISODE 1️⃣6️⃣ Karfe 4 na yamma daidai suka tashi Safeerah tafito yau saida ta tsaya tai sallan la’asar sannan tafito tasa kafa ahanya, tana fita bakin express tasami motan Wuse market ta shiga da sauri suka tafi she knows Wuse Market sabida itada Mama suna zuwa chefanen kayan abinci duk karshen wata, shiga tayi tafara tsayawa tacire kudin account nata tass sannan taje shagon yaran just cerelac ta iya siyamai da Aptamil sai tasaimai pampers mai guda 24 kudin yakare tass sai 3k dazatayi transport komawa gida dashi dakuma zuwa aiki gobe ko 30min bata bata a kasuwan ba tafito tashiga mota zuwa area su tashiga Keke daya kaita bakin GRA din aka sauketa abakin layinsu sannan ta sauka tashiga tafiya tana goye da jakan bayanta sai ledan hannunta da pampers ke ciki da abincin gwangwani tana tafiya taga an bude gate na gidansu motan Ramla yafito wuceta Ramla tayi fit da mugun gudu, Safeerah ta tabe baki aranta tace “aikin kenan” tawuce gida abinsu awaje taga Baba tai murmushi tabude ledan tadauki tomtom guda uku tace “Baba na sayo maka tomtom a kasuwa” murmushi yayi ya karba yace “ke Mamana kudin dazamu lallaba mu siama Waleed abinci kike sayamin tomtom, yanzu abinci guda nawa kika iya kika saya da kudin”? Murmushi tayi tace “madara da cerelac sai pampers, karka damu Baba zamuyi managing su kuma namayi tunani Baba mudena biyewa Waleed ya koyi cin abinci gaskiya lokaci yayi Baba, idan yawuni bai sami abincinsa ba zaici abinda aka dafa agida” hade giran sama da kasa Baba yayi yace “dako na sassaba miki karki kuskura kiyi haka, yaro ne nan gaba aka basa abincin yaran ma bazai karba ba, komi lokaci ne karki takura sa” dan murmushi tayi tace “ni shikenan Waleed ya kwacemin Babana” dariya Baba yayi sosai yace “Mamana daban ne araina, Safeerah na yar albarka, Allah ya haska rayuwanki” ahankali tace “Ameen Baba nagode” “shiga gida toh” wucewa tayi tabude gate ta shiga, Baba da Mama na mugun son Waleed, dakinsu na gate tashiga ta ijiye ledan tarage kayan jikinta tafada bayi wanka tayi dayake yau batajin yunwa ba abinci tafara nema ba, fitowa tayi ta shirya cikin wata

Chapter 7 of 15