Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Salim yabude zaiyi magana Dad yacemai “get out before I loose my temper dan zan sabamaka sosai” wucewa Salim yayi wajen kofa haryasa hannu zai bude kofan ya tsaya yajuyo yakalli Dady calmly yace “Dady I know kai mahaifina ne saisa natako zuwa nan na sauke hakki nabaka hakkin ka, I am an adult that can make decision about my life, I don’t need you kamin aure zan iyayi dakaina, I am simply here dan na sanar dakai zan auri Safeerah and make her my wife today!” Yana maganan yajuya yabude kofan yafice Baffan sa yagani agaban office din ya tsare Salim da idanu murya ciki ciki dan ransa Salim yace “ina yini Baffa” yawuce abinsa bai jira amsan sa ba yasauka kasa yakai wajen parking yana kokarin bude motansa akace Salim, juyowa yayi Baffan sa yagani hakan yasa ya tsaya Baffa yazo wajen yace “Salim mesa zakama mahaifinka wannan furucin? Wani aure kake shirin yi bayan ana shirin bikinka Salim”? Ahankali yace “Baffa ni yaro ne? Bashi zai ciyarmin da matar dazan aura ba, he think sabida yahani zan hanu, idan bazaku nemanmin auren ba zan nemi wasu sujemin, i am tired of the way Dady ke treating dina kaman ba shi yahaifeni ba, he was never there for any decision nawa daman, why did i even come here today thinking zai yarda? Baffa stay out of this sai ajjima” yabude motansa yashiga yaja abinsa yatafi, juyawa Baffa yayi yakoma office na Dad yashiga har lokacin yana tsaye yana huci yace “Yaya kaji maganan banzan da Salim yake gayamin? Is because ka lallabani that year na hakura ban kira an koresa daga camp na soja ba, look at what this boy becomes today eh” Baffa baice komiba yawuce fridge na office din yabude yaciro ruwa ya tsayaya a glasscup yazo yamikamai yace “sha” karba yayi yakai baki ya kurba ya ijiye cup din Baffa yace “zauna to muyi magana Aliyu” zama Daddy yayi ahankali yadan sauke ijiyan zuciya, Baffa yace “kadaisan yanda nake yabanka in terms of sauraron yara da biya musu bukatunsu ko” runtse idanu yayi yace “nasani amman abinda Salim yazo dashi ba me yuwa bane Yaya kagane, bikinsa saura kwana goma yazo dawata magana kumama bazawara zai aura haba” Baffa yace “to menene a bazawaran eh?” Dasauri Dady ya kallesa hannu Baffa yadagamai alamun ya isa yace “calm down kawai kaduba zancen, auren nan kaika hada dakazo mai da maganan baice a’a ba, yanzu yazo maka da tasa saika yarda kaima me aciki he’s matured enough to hold both of them, kadena treating Salim kaman wani yaro” wani kallo yama Baffa yace “yanzu anma yar karaman Nana adalci?” Baffa yace “shi fa namiji mijin mata hudu ne kowa yasani sabida baka yiba doesn’t mean is wrong, bagani da mata biyu ba” Dady yace “ai kaga har yau bana shiri da amaryar ka Uwargida ce tamu” murmushi Baffa yayi yace “dan Allah ka saurari yaron nan stop trying to control Salim the more kanayi the more yana kufce maka” sosai yakalli Baffa yace “ba’a haifi yaron dabazan controlling ba, mubar maganan cus I will never ever support auren nan wlh kuwa”. EPISODE 2️⃣7️⃣ 5 na yamma za’a shiga aikinsa around 4 yashigo hospital din yau tukasa ake aka budemai baya yafito yana sanye da kayan sojoji, wucewa cikin hospital din yayi zuwa dakin yayi knocking tareda Sallama Mama tabudemai tace “Salim shigo” shigowa yayi yakallesu yace “ina yinin ku, ya karfin jiki Baba” atare sukace da sauki, kujera Baba ya nuna masa yace “zauna Salim” zama yayi ahankali yana tunanin ina Safeerah da Waleed basa dakin, dan shiru Baba yayi chan yace “mesa kake taimakon Safeerah Salim? Mahaifiyarta ta sanar dani komi hartakardun filayen an nunamin, in everything this is the only question nakeda shi, na ganka naga mutum mai amana da fadin gaskiya, aiki za’a shiga dani bansan ko zan fito da raina ko akasin haka ba, Salim ka gayamin mesa kake taimakon Safeerah”? Shiru Salim yayi kaman yana tunani sai chan yakai hannunsa na dama yadaura akan hannunsa na haggu ya yacire bitirin hannun rigansa yaja hannun rigansa sama gabaki daya har zuwa muscles dinsa da ananne rigan taki matsawa sama, hannunsa na haggu a kone fatan takoma mai tabo gabaki daya dinnan Mama tace “Subhanallahi kataba yin hatsari ne tabon kuna nake gani haka gabaki dayan hannunka? Meya sameka haka?” Dago kansa yayi yakalli both Mama da Baba ahankali yace “shekaru biyar da suka wuce abin yafaru” sai yayi shiru yace “lokacin ina mata kin lieutenant a soja nazo kano wani aiki ina gudu a titi wani yaro kawia ya shigomin da gangan bayan na kaisa asibiti yace na kaisa gida ina shigowa layin naga kawai an taru akaina an kaini wajen taya aka kulleni” yayi shiru yadan lumshe idanu kaman he’s remembering something ahankali yace “I dont know meya faru but nasan Allah ne kawai ya kubutar dani daga wutan data faraci takama hannuna rigata ta kone na gudu awannan babban unguwan gidanku na fada!” Yayi shiru Baba saiya shiga kokarin mikewa zaune da kyau Mama na rikesa, cikeda mamaki yace “kaine mutumin da Safeerah taboye agidanmu lokacin nan?” Ahankali Salim yace “nine Abba, bayan an tafi dani nayi sati a ICU na shaki hayaki sosai na wahala dan saida nayi wata daya a hospital inajin sauki babu wanda na fara nema aduniya sai ku!Saida na hargitsa anguwan nan da Kano ina nemanku ana kuma nemanmini ku” yayi shiruu yace “nadade ina neman ku dan na godema Safeerah da iyayenta amman ban ganku ba, kullum Safeerah na raina ranan daya kawai naganta a kampanina!” Baba da Mama sukai murmushi Baba yace “Allah kenan! Iko saina Lillahi!” Ijiyan zuciya yasauke saikuma yadago yakalli Baba da Mama dasukai shiru duk suna kallonsa ahankali yace “nasan this is not the right time! Baba ni ba yaro bane shekaruna 39 ina neman arba’in in few months time, dan haka Baba inaso kubani auren Safeerah!” Atare Baba da Mama suka kallesa, Mama tace “Salim nasan kaganta da d’a amman dudda haka hakkine mu gayamaka bazawara ce fa Safeerah, ta taba aure, tayi zaman aure na watanni shidda, tanada yaro Waleed dake neman shekaru uku he is 2yrs 7months” gyadama mata kai yayi yace “nasani Mama! Zan aureta ahaka, ko tanada yara goma zan aureta, zan rike yaran kuma idan za’a bani, sannan zan riketa itama amana Safeerah tamin komi ita Allah yaturo ta ceci rayuwana!” Mama da Baba sukai shiruuu, sauke ijiyan zuciya Salim yayi yace “Banbata gidan nan danta aureni ba! Kafin namata maganan aure nabata gidan bata amsa ba, I only use auren sabida nasamu ta amsa kyautan, Abba badan komi namata kyautan nan ba saidan hallaci sanadina gidanku aka kone is only right na maisheku gidanku dan Allah ku karbi gidan Abba” Baba yayi shiru yana sauraronsa Salim yace “Abba agidan mu nine babba inada kanni hudu daya na miji uku mata, daya tayi aure, biyu na gida basu yi ba, Abba inason kannina sosai especially matan sabida sunada rauni, all I want is na kula dasu, bazan taba cutar da Safeerah ba, zan kula da ita zan killace ta, kome zanma Safeerah bazan taba iya biyanta abinda tamin ba, shekaru biyar kenan ina nemanta ido rufe yanzu da Allah yahadani da ita bazanso takara kufcemin ba, ina so na auri Safeerah Abba!” sun mugun natsu da Salim the way yake maimaita yanaso ya aureta is so deep for him da kana iya gani a kwayan idanunsa dudda mutum ne shi mai wuyan ganewa, dudda bawai sun sanshi bane but yashiga ransu, banda haka ya nada natsuwa sannan ba yaro bane kaman su Abbati dan babu abinda yara suka iya sai shirme da yawon party, ga uwa uba gidan chan sunce kar Safeerah takara dawowa sannan yayarsa daya sani kaman yanda taki sayo abincin Waleed makarantanta ma ba maganan shi yanzu, to da wannan wahalan ba gwara sun aura mata Salim mai sonta ba, wanda yadade yana nemanta, shima yagaji da halayyan yayarsa zai shiga gidan da aka bawa yarsa tunda sadakinta ne da kyauta ne bazai zama comfortable ba but yanzu natane aure yabata, as long as yarsu is safe burinsu yacika, and yaga Salim can give yarsa that safety da babu wanda zai kara hantarar ta. Anatse Baba yataba hannun Mama kamawa tayi ta matse alamun ta yarda hakan yasa Baba yace “mun yarda dakai, ni mahaifin Safeerah nabaka auren ta, ina fita daga asibiti katuro magabatanka mu daura aure banson hayaniyan biki albarka nake nema a wannan auren nata karo na biyu kaji Salim! Karikemin Mamanah amana, bana wasa da yarinyar nan ina matukar son Safeerah ita kadai Allah yabani, tanada taurin kai da kiriniya amman Safeerah tafi kowa kirki aduniya tanada zuciya mai kyau, nabaka aurenta Salim, Allah yamuku Albarka!” Ahankali Salim yace “Ameen Abba nagode!” Shigowa Dr Isa yayi da surgeon yace “Baba ka shirya? It’s time” murmushi Baba yayi yace “na shirya Mamana na masallaci tanamin addu’a ba tsoro araina muje Doctor, saina fito Salim” Gyadamai Kai Salim yayi yace “Allah baka lpy Abba”. EPISODE 2️⃣8️⃣ Saida aka shigar da Baba operation room sannan yabar Mama kadai awajen yafito shi baije wajen masallacin ba but daga inda ya tsaya yana hango masallacin. Hangota yayi tafito daga masallaci she is still with that hijab, day 3 kenan she’s still wearing the same thing stubborn girl, eyes nata sun sabe today but har yanzu basu gama washewa ba saida tafito tajuya tai wani dan karamin murmushi tamikama Waleed hannu alamun yazo da sauri yakama hannun yana wasa slippers nata tasaka tajuyo tafara tafiya out of nowhere wani mutum haka yatare gabanta yaga yana mata magana hakanan Salim yaji abu just hit his heart, kuma sai yaji zafi sosai kaman ciwo does he have heart problem ne? Ya tambayi kansa saiya juya zai koma ciki ina yaji in all levels yakasa kawai saiya juyo yasake kallonta bawai murmushi take ko magana ba but ta tsare mutumin dake mata magana da manyan idanunta ko kyaftawa batayi amman shi bata iya kallonsa haka kawai yaji bazai iya daurewa ba cike da izza yashiga tafiya one one kaman daga sama suka gansa awajen gaban Safeerah ya tsaya yama mutumin wani mugun kallo yace “lafiya!” Wlh ayanda muryansa yafito ba mutumin kadai ba har ita Safeerah saida gabanta yafadi gashi yamata wani babba agabanta sosai, adan daburce mutumin yace “tambaya nakeyi daman kan war……” “meya sami securities dinchan dabaka tambayesu ba kana tambayan matan aure!” Dasauri mutumin yace “ayakuri yallabai, ayakuri Oga” yajuya da sauri yawuce daidai Waleed nawani irin dirlowa daga hannun Mamansa yakama hannunsa yace “ayoyooooo” juyowa yayi yakalli Waleed dakawai ganinsa yasa yaji bacinran yabace dan karamin smile yasaki yace “Hello Finest boy Waleed, come here” yawani daukesa ya rungume yana kallon Safeerah daharta sauke kanta kasa, murya ciki ciki tace “ina yini” bata jira amsar sa ba tawuce dasauri ta tafi ta shiga ward din binta yayi da kallo she still walk kaman da. 7 aka fito da Baba an saka bandage a fuskansa. Yana asibitin har isha’i awajensa Waleed yayi bacci sannan yadawo dashi yamusu sallama yatafi koda Mama tace taje tamasa sallama fitowa tayi but taki zuwa chan tadawo daki, kallonta Mama tayi tace “zo Feerah” zuwa tayi ta zauna gefen Mama, hannunta Mama ta kama tace “Salim yagaya miki waye shi?” Girgizama Mama kai tayi alamun a’a, ahankali Mama tace “dazu kina masallaci Babanki ya tambayesa mesa yake taimakon mu, shine yake gayamana shine mutumin da kika taimaka kika boye lokacin nan!” Tunda Mama tafara maganan kirjin Safeerah ke bugawa none stop, Mama tace “yanuna ma ni da Babanki hannunsa gabaki daya hannun tabon kunane haryau bai dawo daidai ba” wani irin kallon Mama Safeerah take, murmushi Mama tayi takai hannunta ta kama fuskan Safeerah tace “yace yanemeki sama da kasa bai ganki ba not until rannan dakikazo company sa aiki” Mama tai shiru tace “ni da mahaifinki mun aminta da auren mun yarda, and mun yanke shawaran zamu shiga gidan tunda sadakin ki ne, da kyautane da munji wani iri, ga idanun Babanki anyi aiki yana warkewa zai nemi koyarwa we will live good babu wanda zai kara zaginmu, abinda nakeso dake yanzu is kidage da addu’a, Allah yasa Albarka a auren, Salim ba yaro bane abinda yasa muka karajin natsuwa dashi kenan, thank you Safeerah for saving us” Mama tayi rungumeta kankame Mama tayi tunani sunmata yawa aka daman shine mutumin nan? Saisa yadinga kallonta the first day daya ganta in his company, daman shine? But yanzu yafi girma. ** Yau kwanan Baba five a hospital din Alhamdulillah yaji sauki ras idanun dazu aka bude da safe yana gani ras saidai sun kankance but Alhamdulillah, tun after rannan operation din Salim baizo ba sabida wani work trip daya tafi to France na just 3days but kullum yana aiko sojoji akawo musu daily need, yasayama Safeerah 5abayas yabada akaimata saida Mama tai da gaske sannan tasaka kayansa. Yau aka sallami su but Dr Isa yace Salim yace ajirasa zaizo yakaisu gida duk suna zaune, Safeerah tasaka daya daga cikin abayan daya sayamata black yanada stones yamata kyau ajiki sosai dankwalin abayan ta yafa, Waleed short ne ajikinsa na jean dawani blue riga mai kyau da takalmi yayi kyau sai wasansa yake a tsakar dakin sun hada komi nasu tsaf, suna zaune akai knocking tareda sallama hakanan gaban Safeerah yafadi jin muryansa dasauri ta gyara gyalen kanta da kyau tana rufe gashinta, Mama tabudemai Waleed na ganinsa ya jefar da Cheese na hannunsa yadaga hannu yazo dagudu yace “ayoyooooo” daukan Waleed yayi dasauri yayi murmushi kadan yace “Finest Boy Waleed” kankamesa Waleed yayi Mama tace “ai sai ka barsa ko hannunka duk cheese zaka bata masa kaya” dasauri yace “Mama barsa bakomi” yashigo dakin batare daya kalli Safeerah da kanta ke kasa ba yayi wajen Baba yana mika masa hannu cikeda respect yace “Abba ina yini, idanu sunyi kyau” Dan dariya Baba yayi yana feeling very free with Salim yace “ai saiyau nake ganin ka da kyau, Salim kam Masha Allah” dan sunnar da kansa kasa yayi maganan Baba tasa yadanji kunya kadan yace “bari nasa akai kayan mota sai mu tafi” yajuya yakalli kofa yace “come in Boys” sojoji guda biyu suka shigo suna daukan yan kayansu Mama tazo inda Safeerah take zaune kan kujera, duka ta dakamata a sace Safeerah ta kalleta da sauri, wani harara ta mata irin bata iya gaisuwa ba, adan hankali Safeerah tace “ina yini” batare data kalleshi ba, shima bai kalleta ba yace “lafiya lau” yace “Abba Bismillah muje” Baba yace “asibiti ba dadi jama’a” yasauka ahankali yake tafiya Salim dake rike da Waleed na je rawa dashi suka fito, Mama ta kalleta tace “ke da bakin hali baki iya gaisuwa ba ko” kaman zatai kuka tace “Mama magana fa yakeyi saisa ban iya nai gaisuwan ba fa” Mama tace “muje mai kunnen kashi” murmushi tayi suka fito itada Mama. Sunakai wajen motan ijiye Waleed yayi akasa shiya rike Baba cus baida karfi sosai yasaka sa abayan mota Safeerah da fitowansu kenan tareda Mama tadan saci kallonsa he’s so gently da mahaifinta, Mama ma tabisa da kallo sai tadan sauke ijiyan zuciya wlh she loves Salim for yarta sosai, karasawa wajen sukayi itama ta shiga baya, adan kunyace Safeerah tashiga gaba, shima yashiga Waleed na jikinsa ya kunna motan yaja har zuwa estate din Baba da Mama nata kallon ikon Allah sabida basu dauka a irin waje haka yabawa Safeerah gidaba, wlh estate din yafi GRA su Momma kyau sau dari, ga gidajen iri daya sak, saima dayayi parking gaban wani hadadden gida ga flowers anyi decorating wani mini garden, ga bike na yara da ball yasa awajen wanda she is sure bata gani the other day ba, yanzu wannan hamshakin gidan Safeerah ta karba jama’a? Kashe motan yayi yabude yafito yazagayo ta bangaren Baba yabude masa kofa, fitowa Baba yayi Mama ma haka, itama Safeerah jikinta yadan mata wani iri amman tadaure tabude motan tafito taciro key dake yar jakan hannunta ganin ko kallonta Salim bayayi wasa yake da Waleed abinsa yasa tai wajen kofa su Baba na kallonta tabude tajuyo ta kallesu saikuma takasa magana, Salim yace “mushiga ciki Abba” shiga Baba da Mama sukayi duk suna kallon gidan this is the moment of disbelief awajen gidan nan nasune yanzu? Su? Suka zauna afalon dayake a gyare, Salim yasauke Waleed yace “remember don’t cry zanje office okay” gyadamai Waleed yayi, gently yace “je Ummi tasa maka cartoon” dan satan kallonsa Safeerah tayi jin abinda yafadi yamike tsaye yace “sai anjiman ku Abba” har yayi kofa Baba yace “Salim” dasauri Salim yajuyo yace “na’am Baba” ahankali Baba yace “gobe kazo da magabatanka adaura muku aure ba amfanin bata wani lokaci tunda nasami lpy” faduwa gaban Safeerah yayi sosai jin abinda Baba yafada, Salim yadan gyadamai kai yace “toh Abba”. EPISODE 2️⃣9️⃣ Wani haske kalaman Baba sukasa yaji aransa, deep down yanaji kaman yawani fizgo gobe tayi, he just wanna hear those golden words an daure tsakanin Salim Ibrahim Maradi da Safeerah Shu’ibu, rabonsa da gidansu yau kwana nawa dayana France ko sau daya Ammi bata kirasa ba maybe Dady yafada mata, sai kawai yawuce gidansu, parking yayi yafito flat nasa yawuce shower yafada tun yana ciki yaji wayansa na kuka karasa wanka yayi yafito jin wayan na kuka again yasa yatafi wajen wayan, ganin Ammi ke kiransa yasa yadaga wayan muryanta ba dadi kwata kwata tace “kazo ina dakina” bata jira amsawan sa ba ta katse wayan, ijiye wayan yayi shima yacigaba da shiryawa, wani 3quater yasaka wando yasaka, yasa t-shirt mai dogon hannu, slippers yasa sai kamshi yake yafito, flat nasu yashiga yaga Lubna da Ameera a falo suna tattare souvenirs dasuka hada na bikinsa dasauri sukace “sannu da zuwa Yaya” wucewa yayi bai amsasu ya gyadamusu kai ganin abubuwan dasuke hadawa yasa yatuna da auren da za’amai yawuce dakin Ammi yayi sallama yabude dakin Ammi ya shiga, Auwal yagani aciki da Layla kanwarsa datai aure yarta daya Meenal, Ammi yagani tahade rai sosai tana kallonsa, Layla tamike da murmushi sosai kan fuskanta tace “Yayaaa yau kwana na biyu ina gida banganka ba wayanka baya shiga” hancinta yaja yayi murmushi yace “i was in France” Auwal yace “ya hanya Yaya”? Anatse yace “Alhamdulillah” yana tahowa cikin dakin rike da Layla data basa side hug yasami waje yazauna yakalli Ammi yace “ina yini Ammi” Ammi bata amsasa ba sabida yanda ranta yake abace tace “kullum rannan duniya complain na mahaifinka is baka girmamasa, bakada respect menene menene, I see complain nasa baseless kawai yacika korafi ne but slowly na soma yarda da maganar sa yanzu” tai shiru, cikin tsantsan bacinrai tace “me nakeji haka daga bakin Dadynku Salim?” Dan lumshe idanu yayi yabudesu yace “me yaran nan keyi anan Ammi”? Yayi maganan yana musu wani kallo hakan yasa duk suka tashi zasu fita Ammi tace “nina kirasu kudawo nan cus enough is enough” tsayawa duk sukayi Auwal yazauna kan hannun kujeran da Salim ke zaune kai din, Layla tazauna gefensa ahankali, Ammi tace “wat kind of embarrassment is this Salim? Few days to your wedding, gobe zasu fara events one week to wedding, Bazawara zaka auro ana zaune lafiya harda d’a fa?” Sauke kansa yayi kasa, Ammi tace “I’m talking to you kamin banza menakeji me hadinka dawata bazawara datazo IT company? Because she saved you and so?” Da dan zafi kan muryansa yace “wat if sonta nake Ammi? Wat if all this years I’ve fallen for her tun sanda ta taimakamin I’ve beeen searching for her? Dan naganta yanzu ta taba aure tanada yaro does that change anything Ammi? I am a Man yaushe karin aure yazama wani laifi ko wani abu? What am I doing wrong Ammi”? Cikin fushi Ammi tace “everything you are doing is wrong Salim, mahaifinka daya hada auren nan zaka kunyata? And yes it does matter sabida you are too small ka auri bazawara not to even mention ta taba haihuwa bayan ga budurwa wacce bata taba aure ba ce zaka aura” dan runtse ido yayi he hates d name da ake referring Safeerah dashi, Ammi tace “inba magani tamaka ba ga budurwa zaka aura yarinya danya shakap yau biki saura kwana takwas kace kai bazawara zaka aura kuma”? Ahankali yadan dafe kansa dake sarawa yace “wat do you want yanzu Ammi? Why did you call me here”? Cikin fushi Ammi tace “kabar maganan wani aure, Salim ran Babanka yabaci sosai, already kullum cikin damuwa nake da yanda baku jituwa kaidashi kun dawo goshi da keya, ka kama kai auren nan he will never forgive you, saisa na kira kanninka su saka baki, don’t ruin relationship dinka da Mahaifinka sabida wannan auren kaji Son” Ammi tadan sassauta murya tace “I hate yanda baku jituwa dakai da mahaifinka please respect his wish, give this girl kome takeso ka rabu da ita and face Nana Khadija kaji” ahankali Salim yace “I can’t Ammi!” Ba Ammi ba har kannensa kallonsa sukayi, Ammi tace “ni kake gayama you can’t?” Ahankali yace “da ace zan iya da tun last five years na hakura da nemanta, not a day goes by da banayin tunaninta, now that I’ve finally seen her kuma I can’t let her go, I’m really very sorry Ammi but I can’t grant this wish naki, Daddy needs to accept I’m a man, and I own my life, he should respect wish dina and yadena dictating mini my life! I am 39 Ammi not 13” yamike tsaye yajuya zai fita Ammi cikeda mamaki Salim tace “Salim!” Tsayawa yayi chak batare daya juyoba, Ammi tace “tun yanzu kafin ka aurota kafara nunamin ban isa ba ko?” Wani iri yaji sosai ahankali yace “baku taba kawo abu kuce nayi nakiyi ba, even Nanah ban muku gardama ba dakukace na aureta, but ni nakawo kunce a’a, and it’s too late nariga nabiya sadaki! And gobe za’a daura auren so I can’t back out now!” Kowa na dakin kallonsa yake da mugun mamaki ran Ammi ya matukar baci dataji yarinyar ma zai fara aure before Nana, da kyar ta daidaita muryanta tace “okay shikenan kaje kai aurenka dayake zabinka but kasani ba yawuna ciki, and as long as ina raye ni matarka daya nasani Nana Khadija, bazan taba accepting koma wace yarinyar da zaka auro ba” shiru yayi yay jimmm maganan ta tabasa sai kawai yabude kofa yafice daga dakin Layla tai wajen Ammi da sauri tace “Ammi please calm down dan Allah, Yaya baitaba disobeying dinku ba, ku fahimce sa kadan, haba Ammi kinfi Dady fahimta fa kinji Ammi na” Ammi da ranta yabaci tace “karki gayamin maganan banza Layla” ahankali Auwal yace “but Ammi Layla is right, Yaya baitaba gardama da ku ba, even though bayason Nanah I saw it but ya yarda sabida zabinku ce, ni banmasan Safeerah ce yarinyar ba but rannan daya ganta naga yanda yake kallonta, bantaba ganin Yaya yakalli wata mace aduniya like that ba wlh, ku barsa ya aureta, Ammi tsakani da Allah bai kamata kuna gayama wanda is approaching 40 wat do and wat not to do ba, yanzu idan kuka hanashi aurenta shaidan ya shiga ransa da aurensa yaje yanabin yarinyar fa eh Ammi? Kunada kason zunubi, kidena biyema akidan Dady dan boko bayason aure aure, as long as zaiyi adalci, he’s capable bamu zamu tayasa ciyar da su ba let him have his way, Ammi badan yarinyar nan ba da yanzu kullum muna kukan rashin Yaya yarasu? So koma menene he owe her his life Ammi kinji” shiru Ammi tayi jikinta yayi sanyi tace “Nanah fa? That girl is so innocent she’s just 25 ina zata iya dawata bazawara? How will she feel 7days to bikinsu rannan da ake event na kauyawa day wanda zata aura na chan yana auren wata eh, Small girl zai aurowa Bazawara” Auwal yace “to ai Nana ta girmi Safeerah ma Ammi, Safeerah is just 20, kuma Nana tafi Safeerah girma da wayewa da komi ma babu wanda zai cutar da Nanah” Layla dake shafa Ammi tace “toh kinmaji Ammi calm down, yariga yasa ransa look at how serious he is da maganan so unlike Yaya, kika hanasa zaiyi abinda

Chapter 12 of 15