suna wajen kusan 10min yakara knocking tareda bude kofa Waleed da kansa ya shigo rike da sweet da chocolate ga cake yamai waving hannu yace “babyeeee” shima Salim yace “byeeee” Mama tace “angode Salim sai anjima” wucewa yayi Mama ta kalli Safeerah tace “bazaki je kimai godiya ba” ahankali tamike dan bataso takara batama Mama rai, Mama tadauki Waleed itakuma tabude kofa tafito basa awajen dasauri tashiga tafiya tafito yana kokarin bude mota yaga tafito kallonta yayi saida takusan zuwa inda yake yabude motan yashiga yazauna, wajen window sa taje tasa hannu tai knocking, sauke glass kasa yayi kadan yamata wani kallo yace “get in bana magana da mutane awaje” yaja glass din sama abinsa bata ganin komi kuma, dan jim tayi sai kuma tajuya tazagayo ahankali tabude motan batare data kalleshi ba tashigo tazauna taja kofan tarufe, tasauke kanta kasa tashiga wasa da yatsunta ahankali, motan yayi shiru, chan tadago kanta tadan kalleshi ganin ita yake kallo da sauri tamaida kanta kasa kirjinta na dukan uku uku tacigaba da wasa da yatsunta murya chan kasa tace “thank you for everything” tayi shiru murya kasa kasa tace “Allah saka da alkhairi, Allah kara budi da matsayi da daukaka, thank you” dan lumshe idanu Salim yayi yabude har cikin ransa yaji dadi but yayi shiru, dan shiru tayi tanaso tayi magana but tana tsoro sannan she feels idan batayi ba kaman she’s taking advantage of him ne azamanin nan waye zai kashe maka kudi haka, ba’a tambayi Mama ko kwandala in this big hospital ba only mean yabiya komi, dan dago kai tayi ta kalleshi hada ido sukayi da sauri tamaida kanta kasa su wai sojoji haka sukeda kallo, tana wasa da yatsunta maganan na mugun mata wuyan fita tana kuma fargaban fadamai but haka tadaure amman tai kasa chan da muryanta sabida tsoro da shakkan sa tace “nawa ka kashe mana ni da Waleed dakuma kudin asibitin Baba? In sha Allah I will work hard and pay you koda kadan kadan ne, uhmmm nawa ka kashe?” Tai maganan ciki ciki wlh kalaman ma basu fito da kyau ba tsabagen tsoro dakuma fargaba, kusan two minutes taji shiru hakan yasa tadan dago kanta kadan faduwa gabanta yayi ganin wani mugun kallon dayake mata dayasa taji hanjin cikinta ya kada tamaida kanta kasa tawani yunkura dasauri takai hannu da gudu zata bude kofa ya danna lock wlh batasan sanda tace “kay…….kaya kuri idan maganata ta bata maka rai”dan daidaita muryansa yayi dan maganan datamai yabatamai rai yace “I will be back anjima da daddare for an answer game da maganan dana miki!” Gyadamai kai tayi not herself why is he insisting about auren nan ita she hates aure, kai tsaye yace “get out!” batasan sanda tabude motan da sauri ba har saida kofan yadaki next car dake wajen tafito da sauri tamaida kofan ta rufe, reverse yayi dasauri yabar wajen tabi motan da kallo idanunta sunyi ja sannan tawuce takoma cikin asibitin takoma tashiga dakin nurse tazo da takarda tabata tai signing tafice Mama ta kalleta sosai tace “meya ce?” Faduwa gabanta yayi jin tambayan da Mama tamata sai lips dinta yahau rawa Mama ta tsareta da idanu ahankali tace “cewa yayi wai bayan an sallamemu mu koma gidansa daya kaini nida Waleed jiya dukanmu muyi zaman mu wai yabani gidan shine nacemai a’a banso” tai shiru Mama dake kallonta tace “sai yace mene?” Kallon Mama tayi batasan mesa gabanta ke faduwa ba murya chan kasa tace “yace tunda inada girman kai bazan amshi kyautansa ba wai zai aureki yabani gidan a matsayin sadaki yabani zuwa dare nayi tunani” Mama na kallonta tace “wani shawara kika yanke Safeerah?” Dasauri takalli Mama tace “Mama mesa kike min tambaya haka?” Mama na kallonta tace “aure nabiyu ne wannan kinada yancin zaban miji dakanki” bata fuska tayi tace “Mama ni bazan kara aure ba harna mutu zanyi tunani nasan inda zamuje idan an sallami Baba” Mama tadade tana kallonta sai bata kara cewa komiba.
EPISODE 2️⃣4️⃣
Waleed shima bacci yayi dan yayi ciye ciyen nan Mama ta kwantar dashi kan lafiyayyen couch na dakin.
Motsi Baba yayi hakan yasa daga Safeerah har Mama suka taso da sauri Safeerah tai wajen muryanta yayi rauni sosai tace “Baba Baba kanajina gani nan” bude idanunsa Baba yayi ahankali yadan gani dishi dishi but he was able to know Safeerah ce murya chan kasa yace “Mamana kin dawo? Ina Waleed?” Fashewa da kuka Safeerah tayi kawai ta rungume Baba sosai tace “Baba kayakuri dan Allah, Baba baran karaba kayakuri I’m sorry kaji Baba, sabida nine rashin lafiyanka yatashi ko, baram kara tadamaka da hankaliba kaji Baba” hannunsa yadaga ahankali taredayin murmushi dan gaskiya yasami sauki yace “ai kaganta ga kiriniya ga iya kuwa, Feerah rigima, ya isa toh bar kukan haka” ya shafa bayanta Mama ta tsaya tana kallonsu kai Baba na son Safeerah bana wasaba to ko don ita kadaice yarsa oho amman baya wasa da Safeerah dagosa Safeerah tayi tana dago gadon ya zauna tace “meke maka ciwo yanzu Baba?” Girgiza kai yayi yace “ba abinda ke min ciwo Alhamdulillah inama dan gani baga Waleed chan ga kujera ba” yanuna Waleed dake bacci, Mama ya kalla yace “waya kawoni asibiti”? Yayi tambayan sabida yasan ba Mama Kubra bace wannan dake fushi dasu ahankali tace “Salim ne yakawo ka” shiru Baba yayi yana tunani yatuna sanda yazo yana masa maganan Safeerah daidai nan Dr Isa yazo Baba yaduba tsaf sannan yayi murmushi yace “bansan ko Major Salim ya gayamuku ba, inhar kanaso zaka bamu yardan ka muna kyautata zato zamu iya maka aiki a idanunka da sababbin technology mu dasuka shigo tsaf zaka iya gani, Major Salim yariga yabiya kudin aikin consent naka kawai mukeso dazaran BP ka yasauka sai ayi fixing time ashiga surgery Baba” tunda Dr Isa yafara magana kowa na dakin kallonsa yake especially Safeerah da kirjinta yahau bugawa batada burin da ganin Baba ya dawo, wayan nan idanuwan sune suka tankwafar da Baba yakasa samin sana’a muguwar yayarsa na yanda taga dama dashi, Baba yaje school yayi FCE he’s such a good teacher idanunsa suka dawo he can look for teaching job again har ranta taji dadi, Baba yadan kalli Mama sabida shi kudin ne aransa sai cin kudin Ogan yarsa suke but saiyaga Mama ta gyadamasa kai hakan yasa yace “to likita kunada consent dina a ina zanyi signing?” Wata takarda yasan karba daga hannun nurse ya matso yasa a hannun Baba yasamasa biro Baba yayi signing, Dr Isa ya karba yace “I will monitor you zuwa gobe idan BP ka yazama stable za’asa lokaci na aikin” gyadamai kai yayi yace “an gode likita, Allah saka da alkhairi” juyawa yayi yafice, Mama takalli Safeerah tace “kinyi salla wai ke yarinyar nan” girgizama Mama kai tayi, Mama tace “tashi kitafi masallaci kiyi salla” tashi tayi ba musu tawuce tabude kofa tafita ta rufo zata wuce saitaki ta tsaya dan yanda Mama ta korata when she can simply pray adaki is somehow kunnenta tasa jikin kofan muryan Mama taji cikeda damuwa tace “Yayarka nata kiran wayanka Malam nasaka wayan silent banso yarka maraji tagane, sakon ta ya shigo ta aiko maka da sako a message” wayan Baba ya kalla cikeda damuwa yace “mita fada a sakon?” Shiru Safeerah taji Mama tayi sai chan tace “waya baka izinin shigomin dawani kato gida? Gidanka ne ko gidan ubanka ne? Gidana ake shigomin da wasu batare da izinina ba to bari kaji zumunci yaci uwarsa da ubansa tunda baku da godiyan Allah dakai da matarka kuma ku kama sahu kubi yarku ko kofar gidana kada ka kara zuwa inba hakaba saina maka wulakanci wanda harka mutu bazaka mantaba munafuki shashasha” Mama ta sauke ijiyan zuciya ta kalli Baba tace “yanzu ina zamu Malam? Ta ina zamu fara gamu da y’a, gamu da jika? Kano zamu koma da ake nemanmu akashe? Inamu ina zaman Abuja? Ko an maka aikin ma a ido kafin kasami aiki it takes time a zamanin nan damuke, bazan maka karyaba nadamu Malam” murmushi Baba yayi saiya rungumo Mama yanada danne damuwa yace “kidena damuwa ni nasan Allah bazai barmu ahaka ba, ya isa dan Allah karki kuka yarinyar nan tazo ta gane” wani kalan nauyi Safeerah taji zuciyanta yamata sai kawai ta tashi wajen kofan tawuce masallaci salla tayi tasa goshinta akasa takuma yi shiru kunya takeji tamayima kanta maganan aure after abinda tagani a auren, saita kasa rokon Allah komi ta taso kawai ta zauna har akai asir tayi sannan tadawo, tana bude dakin taga wani soja aciki yakawo basket dake dauke da manya manyan kulan abinci ga gwangwanin cerelac da madara a gefe aikin Salim ne, why is he so good to her? Meya yakemata alkhairi haka for mutumin da sau biyu sika hadu on Monday and Tuesday what is happening? Godiya Mama tama sojan yajuya yafita tabude kulan dan wlh yunwa takeji, tuwon shinkafa ne da miyan kuka mai kifi da kaza da man shanu, sai jellof rice da chicken tace “mezan sama ka Malam” ahankali Baba yace “tuwon yabani sha’awa” samai tayi ya karba yafara ci sai kallonsa Safeerah take Mama ta kalleta tace “ke bazaki ci ba” ahankali tace “anjima zanci” duk son abincinta dakuwa yamata yawa she loose apatite.
EPISODE 2️⃣5️⃣
Shi daman iyayensa sun sani ko yana gari baiwani cika zama gidansu ba sai idan yaga dama ko Ammi na kewansa he’s always fighting da Daddy so he’s avoiding him, gidansa na barrack yawuce bayan yatashi daga office, wanka yayi yasaka simple yadi brown jumper ce dinkin, Hermes slippers yasaka na maza yafito yana zuba uban kamshi, wata envelope dake kan table na falon yadauka yabude yaciro takardan yakalla sai kawai yamaida cikin envelope din yarike yafito yashiga mota, super market yabiya yayi sayyaya mostly for Waleed ne da irin kayan tea yasaka a booth yakoma gaba yawuce hospital wasu soja yabama kayan akai dakin ya tsaya yayi isha’i a mosque yayi magana da Dr Isa yana basa update kan lafiyan Baba.
Duk suna dakin Mama na goye da Waleed da akeso yayi bacci dan rigima yake saiya fita waje wasa yamafara gyangyadi while Safeerah na magana da Baba akai knocking Mama tawuce tabude kofa soja ne yashigo da uniform da leda yace “good evening Oga yace na kawo he’s coming” ya ijiye yajuya yafita Safeerah tai shiru tana kallon kayan kaman yanda su Baba keyi tace “zan maidamai abun yayi yawa” Baba ahankali yace “ke kul babu kyau maida kyauta” bata sake magana ba almost 20mins akai knocking tareda sallama gabanta kawai yafadi jin muryansa, Mama tace “shigo Salim” bude kofan yayi yashigo Safeerah takasa kallonsa ya gaisa da Mama yama Baba yajiki, Baba yace “Salim dawainiyan nan batai yawa ba? Toh mungode Allah amfana, nagode kwarai Allah ya saka da mafificin alkhairi” kansa yasauke kasa yace “Allah kara lafiya Baba, kadinga cin abinci akai akai sannan karage damuwa Baba, duk batada amfani” Baba kadakai yana yabawa da natsuwan Salim da hankalinsa yace “ba shakka haka maganan ka take Salim, Allah yayi albarka” anatse Salim yace “tom Allah saida safen ku Allah baka lafiya Baba” sosai Baba yaji dadin addu’an yace “Ameen Ameen Salim nagode sosai” juyawa yayi yasaci kallon Waleed dake bayan Mama karaf Mama ta lura murmushi tayi tace “abokinka yayi bacci da yanzu yafara binka” sunnar dakai kasa yayi yace “saida safen Mama, zanzo gobe da yamman In sha Allah” Mama da Baba sukamai godiya, Baba shi kawai yanason yaron wlh hakan yasa yakalli Safeerah yace “baki iya gaisuwa bako, anyways ke jeki masa godiya” ita sai yanzu tasan bamatayi gaisuwa ba, mikewa tayi tawuce tana bude kofan tagansa tsaye gefen kofan saida gabanta yafadi, kaman daman ita yake jira yayi gaba abinsa tabisa abaya dudda bataso taje har waje ya shige mota kin shiga motan tayi hakan yasa yasauke glass yamata wani kallo dasauri tashigo tamaida kofan tarufe, Envelope yadauka yamika mata yace “take this” dago kanta tayi takalli abinda yake bata but kallon dayake mata yasa tasaka hannu ta amsa ahankali gabanta na faduwa yadauke kansa yakalli kofa yace “that is the house papers!” Dasauri ta kalleshi shima juyowa ya kalleta da kyau wani irin kwarjini yamata dasauri ta sauke kanta kasa chan yace “remember i made this offer since naga baki son kyauta it hurts your ego” yasake shiru chan for the second time today yace “marry me Safeerah!” Wlh gabanta faduwa yayi da karfi akwai yanda kalman ke fita daga bakinsa yake shiga kunnenta, why is he so adamant about ya aureta, yanda kirjinta ke bugawa saitaji gumi yasoma keto mata, he sees and noticed yanda take tsoronsa if he wants zai iya tsoratata now and hear ta yarda da zancen auren but baison haka, shi ko bata auresa ba yariga yabata gidan har ransa, he’s just using the gidan ne as excuse he really wants to marry her, dudda baida tsoro but deep deep chan chan kasan zuciyansa baisan mesa ba he’s scared kartace bazata auresa ba, kotace ta yarda ta karbi kyauta basai sunyi aure ba, he’s just praying kar her little brain dinta yayi wayon gayamai haka, shi kansa baisan mesa he just wanna make her his ba, baitaba feeling haka for Nana ba, but look at the way yakeso wata tace ta yarda zata auresa.
Calmly yace “I told you nabaki zuwa dare for final decision naki, here are the papers kirike gidan nan amatsayin sadakin ki” dasauri tadago kanta takalleshi gabanta na faduwa batason aure, dan rage muryansa yayi yace “a musulunci mace can decide to collect anything as sadaki, zamanın Annabi akwai wacce aka bawa takalmi a matsayin sadaki, akwai wacce aka koyama suratul Fatiha a matsayin sadakinta!” Baki Safeerah tabude dake rawa sosai zatai magana hannu yadaga mata hakan yasa maganan ta makale a wuyanta yace “I am not forcing you, aurena is your decision! I just wants to help you! I don’t need anything from you kome azuciyanki, kome kike tunani cus nasan kin taba aure, all of that bana bukatan komi, I just simply wanna help, and it all depends on how far you can go for parents naki! And Waleed” sosai gabanta ke faduwa, everything nadawo mata especially messege da Momma ta turo dasuka boye mata basu fadamata ba, rashin hankalinta da haukanta yasa all this yafaru dasu su Baba yanzu suma are stranded like her, byro dake gefen wajen ta tsare da idanu kafin ahankali tamika hannunta dake rawa sosai tadauka wani irin boyayyen ijiyan zuciya Salim yasauke daya rasa ta mecece, envelope din tabude tajawo papers din tafito dashi murya chan ciki that sounds kaman tana kuka tace “bana gani” kunna mata wutan motan yayi ta kalli papers din saikuma ga agreement da aka rubuta sadakin Safeerah ga signing dinsa yayi saura nata, hawaye ne yadauko daga idanunta ya sauka kan papers din ya tsareta da idanu he knows she is scared, she’s troubled, tana cikin tsoro what if abinda yasameta ada yakara samunta a aurensa yasan she is signing this papers sabida babu yanda zatayi ne sabida her parents needs it so somehow zamata iya ji kaman he is taking advantage of condition nata ne, but is not like that, he wants to protect her with everything and anything in him, he wanna become her shield and make her untouchable, he wants to give her everything and anything she ever wanted in her life, he will bring back that happy Safeerah ta 5yrs back and remove this sadness and pain daga zuciyanta.
Karasa signing tayi saita ijiye papers din ahankali da pen din kan cinyanta, takai hannu ta goge fuskanta tass sannan batare data kalleshi ba tadauki papers din ta mikamai ahankali tace “na yarda zan aureka”hannunsa yasa ya karbi takardun yace “ok” sannan yazare aggreement din yamaida takardun gidan envelop yadauki key gidan yasa acikin envelop din yace “your house papers and key Madam Salim!” Kaman jira take rushewa da kuka tayi kaman yar yarinya tasa hannu ta karbi papers din tajuya tabude kofan motan dasauri tafita ta maida kofan tarufe ta wuce ciki tana share fuska ya tsaya yabita da kallo harta shiga kafin ya sauke ijiyan zuciya ahankali ya kunna motan yayi reverse yafita daga hospital din tadade a lobby asibitin saida fuskanta ya washe sannan tawuce dakinsu tabude kofa ahankali Baba yayi bacci sabida alluran dayake kai ga Waleed kwance gadon kusada Baba yana bacci, Mama na zaune kan kujera tana jiranta file din ta ijiye kan drawer tazo kusada Mama tazauna jikinta duk yayi sanyi, Mama tace “menene a file din?” Kasa dagokai tayi ta kalli Mama, anatse Mama tace “Safeerah!” Dago kanta tayi idanunta sun cika da hawaye Mama tace “nace menene an envelope din chan?” Hawaye ne ya sauko daga kan idanunta tace “takardun gidan na amso, zan auri Salim Mama!”
EPISODE 2️⃣6️⃣
Yau duk wani schedule nasa he cancelled it inda ma ake bukatan sa he makes sure yayi assigning soldiers dazasuyi representing nasa, kwata kwata baya so yama Dad maganan nan agida dan shi wani irin mutum ne da yanada principles, ya tsani yana magana da wani another person from nowhere yashiga maganan, baison ya tunkari Dad da maganan yazama case, ko Ammin sa ko kannensa su jiyo su shigo zancen cus Dad can shout, so he decided to meet mahaifinshi a kampaninsa, Maradi Private Jet and Co.
Yau wata benz yadauka fara yayi parking kusada inda motar mahaifinsa yake a special parking space nasu yana sanye da very simple yadi mai bala’in tsada off white, ba hula akansa saidai yasaka dark shade yawuce ciki sai gaidasa ake, maybe throughout this year this is the second time yake zuwa kampanin nan, direct elevator yashiga yayi sama yadan fuzar da iska yana gyara murya haryakai floor da zasa kofan yabude yafito, yana kokarin shiga office na mahaifinsa Daddy nafitowa sanye da suit da mukarrabansa abaya yana magana dasu da turenci, ganin Salim yasa yadakata looking extremely suprise yace “Son!” saiya juya ya kalli ma’aikatansa yace “kuje start the meeting without me I will meet you half way” anatse Salim yace “Dady kaje meeting din I will wait” dasauri Daddy yace “no, no, meeting can wait not my Son muje” cikin office nasa suka wuce mai kama da office na shugaban kasa while ma’aikatansa nafita, maida kofan Salim yayi yarufe gabansa yadan buga bawai na tsoro ba cus gaskiya baida tsoro kawai na baisan yanda Dady zai dauki zancen bane sabida his father is just like him, halinsa yadauko, saisa basa taba jituwa, zama Dady yayi bayan yacire jacket na suit nasa yayi hanging ya zauna yace “yesss to wat do I owe this visit yau babban soja Salim yazo office dina, uhnnn remind me of that your tittle ko matsayi” yayi maganan yana kallon Salim yana daura yatsansa kan lips nasa kaman mai tunani yace “i remember Major! Barka da zuwa Major Salim!” Kansa ya sauke kasa baisan mesa Dady is like this with him ba more like bullying but baiso yakira abin bullying, Dady hates yazama soja with passion so all this years he uses it to make him feel bad, ahankali yakai hannunsa yadan sosa kai Dady sa dan boko ne sosai, gasa dan gayu baya tsufa, yanda yake lurada kansa har mamaki yake bama mutane, calmly Salim yace “good morning Dad” batare da Dad ya amsa ba yace “mekazo nema wajena? Meya kawoka my company, kana garin nan amman saikaga dama kake zuwa gida ka kwana, tunda kadawo daga China I saw you once, skip the formalities I know ba gaisuwa yakawoka nan ba, what is it Muhammad Salim?” Yanda Dady ke kallonsa ido cikin ido haka shima Salim ke kallonsa cikin wata yar murya that is straight and directyace “Dady I’ve seen that girl” Babansa na kallonsa kur bayako kyaftawa yace “the one that saved you five years back sanda aikin sojanku yakusan hallakaka”? Hada lips nasa yayi ya gyadamai kai yayi yace “eh Dady she comes to my construction company for IT this week anan na ganta” Dady yace “okay nice run her a check, idan baka da kudi I can tell my accountant yayi running check din”dan shiru yayi yasauke kansa kasa, Daddy yakara natsuwa sosai yana kallonsa yana nazarinsa. “I’m not here for check Dad” ahankali Daddy yace “Salim” dago kansa Salim yayi ya kallesa, Dady yace “then what are you here you indai ba check ba?” Ijiyan zuciya ya fuzar cikeda dakewa yace “she’s going through alot Dady all because of me, har aure aka mata 6month mijin yasaketa, she has a son yanzu” cikeda rashin kulawa da nuna baiga wani abuba or important na story ba yace “and? I just said run her a check, sponsor the boy to school idan kanaso unless there’s more, but money can solve any problem datake ciki” sauke kansa kasa yayi yayi shiru na kusan 1min kafin anatse yadago kansa yakalli mahaifinsa da kyau yace “inaso na aureta Dady!” Yanda maganan tasauka akan Dady baisan sanda yamike tsaye yabuga table na gabansa sosai yace “wat nonsense!”gently Salim ke kallon mahaifinsa, hade fuska Dad yayi dan ransa yayi masifan baci yace “just 12 ne ko 11days to aurenka kazo kanamin maganan zaka auri wata chan da bansan daga ina take ba, sabida wannan aikin sojan ya maida mana da yara marasa tsoro ko shakkan iyayensu, an kekashe muku zuciya you feel zaka iya tarana da kowace kalan banzan zance, look at what becoming a soldier ya maidaka!” Daddy ya nunasa da hannu yace “look at you Salim very heartless emotionless wicked man!” Dan sauke kansa kasa Salim yayi baice komiba, Dady yacigaba da banbanmi. “Za’a fara shagulgulan bikinka nan da 3days is something wrong with you Salim koko yarinyar tamaka asiri ne”? Yakalli Salim yana jiran amsa amman baice komiba, Dady yace “are you that heartless ka kasa tunani how Nana Khadija will feel few days to bikinku mijinta na zuwa da maganan zai auri wata? You know me very very well I don’t believe in polygamy ban yarda da aure dayawa ba, babu abinda yakai mace daya zaman lafiya da kwanciyan hankali, yaranka su taso kansu ahade, can’t you see mahaifiyarka? She’s always happy sabida batada competitors, she’s fulfilled and satisfied, I make sure na sama maka auren one of the best, my childhood friend Haruna, Yar Niger ya aura, buzuwan yarinya that is very educated she’s just 25 ana maganan bikinku kana kawomin wani maganan banza da wofi, well listen to me, I’m not in support of this, babu abinda kakeso aduniya da ban makaba, kayi degree harda MBA kazo kasameni kanason soja, nahanaka bakaji ba zan iya using other means to stop you from becoming a soldier but ban hanaka ba I let you have your way regardless, kasameni kanaso ka bude companyn ka, al’adan tundaga my grandfather yara works a company iyayensu kai kace no kafi karfi kayi aiki awajena fine ban hanaka ba kabude, ko kana Nigeria baka cika zama gida ba sai barrack ban hanaka ba, you are 39 all this years ban dameka dakai aure ba dudda mates naka sunyi sai yanzu ka kawomin maganan banza da wofi! Ban yarda ba at all nagayamaka” baki Salim yabude zaiyi magana Dady yanunamai hannu yace “quiet! I don’t wanna hear a word, and I will consider nida kai bamu taba magana on this topic ba kajini stand up and get out of my office!” Ko motsi Salim baiyiba yakalli Dady sosai dake kallonsa, Dady yace “ohh bazaka fitaba! Nayi kadan na kora Nigerian Army Major out of my office ko”? Ahankali Salim yamike yajuya yafara tafiya Daddy yace “nonsense!” Chak ya tsaya saiya juyo yakalli Babansa yace “Dad kataba tambayana for once ko inason Nanah Khadija? Koko na amince da aurenta?” Cikin fushi Daddy yace “sabida ba yardanka ko amincewan ka nake nema ba Salim! Khadija is my choice diyar aminini na and dole ka aureta, moreover kai ka kalli wannan zuciyan taka dake cike da wickedness da rashin da’a nada space na soyayya ko san mutum? Of course I know bakason Nana Khadija sabida mutum like you is not capable of loving anyone a riga an cire emotion dinnan a filin yaki!” Baki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 15