An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
A hankali take tafiya domin ba sauri take yi ba, duk da dai magriba ta kusa amma ta san zata kai gidan nasu kafin a fara kiran sallar. Karar wayarta ce ta katseta, ta dan rage sauri a tafiyar tata sannan tayi kokari ta zaro wayar daga jakarta. Tayi murmushi bayan da ta ga wanda yake kiran nata. Ba tare da bata lokaci ba ta amsa wayar ta kara a kunnenta.
'Hey Babe.' Ta fada tana wani rangwada kai tare da juya kwayar idonta kamar dai ga Babe din a gabanta tana kallonsa.
'Mai kyau, ya kike?’ Ya fada daga daya bangaren.
'I'm fine. Yanzu nake dawowa daga school gashi nan na kusa shiga gida.’
'Oh, nima yanzu na mayar da su Afaf gida wajen Hajiya. Mun je shopping ne and I bought a few things for you nake so na kawo miki later. Is that ok?’
'Yes Babe, kai ma ka san ina nan idan dai kaine kake son ganina. Ya yarana? Hope suna lafiya?’
'Alhamdulillah ga su nan. I just can't wait to have you so we can all live in one place na huta da visiting yarana.’
'Aww! Kada ka damu, very soon in sha Allah. We will talk more about it idan ka zo in dha Allah don yanzu zan shiga gida ka san Mommy ta hanani waya a kan hanya.’
Yayi ‘yar dariya yace ‘Kuma fa hakane, to sai mun hadu.’
Suka yi sallama suka ajiye wayar.
Da sallama ta shiga gidan tana ta fara'a kamar wadda aka yiwa wani babban albishir. Babu kowa a parlor din sai Mommy tana shirin tashi ta shiga sallar Magriba. Bayan ta amsa sallamarta tace ‘Yau kuma haka kike tafe kina tallan macleans?’
'Kai Mommy! I'm just Happy.' Ta fada tana dariya.
Ta wuce dakinsu yayinda Mommy ta shige nata dakin.
Tana sane da yanda take tafiya tana murmushi din kuma tana jin dadin hakan. Idan dai a kan Mistapha ne fiye da haka ma zata yi. Muryarsa kawai take bukatar ji ta shiga farin cikin da baya misaltuwa. Wata bakwai da suka wuce suka hadu, amma saboda yanda ya iya soyayya da tarairaya ya shiga zuciyarta kamar wanda suka yi shekaru a tare. Da ya sami yanda yake so ma da tuni an daura musu auri don shi a shirye yazo, itace take dan dakatar da shi don tana so ta gama level 1 kafin ayi mata auren.
2
Sai dai a daren jiya Baffanta ya sanar da ita cewa ta gaya masa ya turo maganar aurensu.
Ta jefa Jakarta a kan gadonsu wadda ta fada kan kanwarta Nabila. Nabila ta make jakar ta ja tsaki tace ‘A’a, must you be stubborn?’
Tayi dariya tana cewa ‘A tashi dai a yi sallah.'
Ta matsa gaban wardrobe ta fara kokarin cire kayan jikinta.
………
Kamar yanda yayi mata alkawari ana idar da sallar isha'i ya iso gidan nasu. A tsakar gida suka zauna inda ta saka musu kujerun roba a rumfar mota, ta ajiye karamin tebur a tsakanin kujerun wanda ta dora ruwa da lemon roba masu sanyi a kai.
Bayan sun gaisa suka dan taba hira, hirar da a mafi yawancin lokuta itace take yi shi binta kawai yake da kallo yana murmushi yana bata gajerun amsoshi.
Mustapha kenan; haka yake kamar wani basarake, komai nasa a hankali sannan kuma bisa tsari. Wannan ya sa yake kara burgeta.
Ta dauki ruwan robar da ta ajiye ta bude ta mika masa tana cewa ‘Ko ruwan baka sha ba Yallabai.'
Yayi murmushi yayinda ya karbi ruwan yana cewa ‘Kuma kin san kishirwan nake ji ba, don tun daga gida muke waya da su Afaf har na zo nan suna ta surutu duk sun gajiyar dani.'
'Kai haba, surutun na su nawa yake?’ ta fada tana dariya.
Suka cigaba da hirarsu har zuwa lokacin da ya tashi tafiya wajen karfe tara. Sai da ta raka shi bakin motarsa kafin tayi masa sallama sannan tace ‘Baffana yace na gaya maka mutanen gidanku zasu iya zuwa maganar aurenmu ranar asabar mai zuwa.’
Take fara'ar sa ta kara fadi, ya dubeta kamar ya rungumeta yana ta murmushin da itama yake saka ta murmushi. Yace ‘Allah Khadija! Kai amma na ji dadi wallahi, in sha Allah ranar asabar din kuwa zasu zo da kudin aure da sadaki gaba daya.’
Tayi dariya ‘Kai garaje, saurin me kake?’
'To ai na kula bakya tausayina, so kike kiyi ta ja min rai kina barina sauro yana cinyeni saboda zance.’ ya fada da murya kamar ta mai shagwaba.
Tayi dariya ‘To kwanan nan zaka huta in sha Allah.'
Sukayi sallama cike da farin ciki bayan ta sanar da shi gidan kakanta inda nan ne zasu je maganar auren nata.
Cikin walwala yake tukin lokaci zuwa lokaci yana yiwa kansa murmushin ji dadi saboda wannan labarin da Khadija ta sanar da shi. Watansu bakwai kacal da haduwa amma ya nutsu da hankalin yarinyar kuma ya yaba da tarbiyyar gidansu, ya tabbatar zata kular masa da su Afaf kuma zata tsaya a kan tarbiyyarsu ba tare da wata mugunta ba.
Wata takwas kenan da rasuwar matarsa Asma'u, wadda itace ta haifa masa yara hudu; Afaf mai shekaru goma sha daya, Habib mai shekaru tara, Nasreen mai shekaru shida sai Shukra mai shekaru uku. Ba wani rashin lafiya tayi ba, haka kawai da daddare tace kanta yana ciwo don haka a gaba ya sakata sai ta sha kwayar Panadol sannan ta kwanta; sai dai da yake kwananta sun kare haka aka wayi gari sai gawarta. Yayi matukar bakin cikin rasuwar Ma'u kuma ya ji tausayin kansa da yaransa, gaba daya rayuwarsa ta tsaya saboda rashin Ma'u.
Tunda aka kwana uku da rasuwar Asma'u mahaifiyarta ta tattara yaran ta tafi da su gida aka cigaba da kula da su. Can yake zuwa kullum ya daukesu ya kaisu makaranta idan an tashi ya mayar da su. Ana kula da su sosai kuma suma suna jin dadin zaman gidan sai dai shi ya fi so ya rayu tare da yaransa. Da farko ya so ya kwashesu ya kaisu gidan yayarsa; tunda mahaifiyarsa ta tsufa da yawa ba zasu sami kulawa ba a wajenta. Amma sai mahaifiyar Ma'u tace ba zata bayar da yaran ba. Sun so su sami matsala domin da kwashesu yayi ba tare da izininta ba ya mayar da su gidan Yayar tasa, sai da manya suka shiga cikin maganar aka yi yarjejeniya a kan idan yayi aure zai je ya debi yaransa. Don haka ba karamin dadi yaji ba da Khadija tace an bashi izini ya turo.
Ya riga ya sanarwa Khadija idan ta tare zai dawo da yaransa kuma tayi na'am da hakan. Shiyasa ma wasu lokutan yake kwasosu ya kai mata su har suka saba sosai. Yayi mata bayanin irin kaunar da yake musu da kuma yanda yake so ta dinga kula da su kamar ita ta haifesu; kuma ta yi na'am da hakan. Don ko a yanzun ma tana kokarin wajen hidimarsu da jansu a jiki ga kyaututtuka, gashi wata ran da kanta take masa waya ya kawo mata su.
Duk da ya riga ya je gidan mahaifinsa da safe amma a daren ma haka ya koma cike da farin ciki ya sanar da mahaifinsa cewa iyayen Khadija sun bashi damar ya turo. Mahaifinsa yana zaune a kan kafet a dakinsa ya dubeshi bayan ya gama sanar da shi inda za a kai kudin yace ‘Shikenan rigimar yara ta kare ko, ga amarya ga yaranka sai ka sami natsuwa.’
Yayi dariya ya sunkuyar da kai.
Daga baya yayi musu sallama ya wuce gidansa cike da farin ciki.
_____
Kamar yanda aka yi alkawari ranar Asabar 18th February, 2020 waliyyan Mustapha suka sami karba ta girmamawa a gidan kakan Khadija. Bayan sun gaisa an musu maraba suka gabatar da sadaki N100,000 da kuma kudin aure N50,000. Baba Sani kanin mahaifin Khadija ya sa hannu ya karbi kudin ya matsa ya ajiyesu a gaban mahaifinsu Alhaji Baba. Cike da fara'a da murmushi Alhaji yace ‘Ma sha Allah, Allah ya sa albarka Allah ya nuna mana.’
Gaba daya mutanen dake wajen suka amsa da Amin.
Baba Safiyanu wanda Yaya ne a wajen mahaifin Khadija yayi gyaran murya yace ‘Alhaji ni ina ga tunda ga sadaki an kawo kuma ga waliyyan ango ai sai kawai a daura auren nan yanzu. Yanda abubuwa suke tafiya rufe garin nan fa za ayi, tunda ka ga kasashen duniya suna ta rufewa fa. COVID 19 din nan ana maganar ta shigo kasar nan sosai, ko da wanne lokaci za a iya shiga lockdown.’
Alhaji yace ‘Ikon Allah, kace abun ya zo mana kenan. To Allah ya tsare mu da zuri'ar mu.’ ya dubi waliyyan Mustapha yace ‘To idan a shirye kuke sai a daura auren ai, nan da sati mata sai suyi bikinsu su kai amarya kafin ace an kulle kasar.’
Cike da murna Alhaji Muhammad wanda shine Babba a waliyyan ango yace ‘Ah ai mu a shirye muke, hakan ai ya fi sauki Alhaji, Alhamdulillah Alhamdulillah. Shi Mustapha ai a shirye yake, lefe ma da sauran kaya duk gobe sai mata su zo su kawo.’
Nan da nan suka gyara zama, Baba Sani ya kirawo mahaifin Khadija ya sanar da shi wanda shima a take ya amince, sannan ya kirawo makota da wasu daga cikin dangi. Suma ‘yan uwan Mustapha suka sanar da shi ya taho shi da abokansa mutum biyu. Kafin minti talatin guest room din Alhaji ya cika da mutane ana ta murna.
Ba tare da bata da bata lokaci ba aka daura auren Khadija da Mustapha.
—------
Tana kwance a parlor dinsu a kan doguwar kujera tana chatting a waya yayinda kanwarta Nabila take zaune tana kallon TV; kaninsu Ahmad ya shigo parlor din da gudu yana ihu ‘Ta zama matar aure, Ya Khadija ta zama matar aure…’
Zumbur ta mike daga kujerar yayinda itama Nabila ta mike tana cewa ‘Kaifa kana da matsala, don Allah ji yanda ka firgita ni.’
Khadija tace ‘Wai me kake cewa ne?’
Yana dariya yace ‘Wallahi an daura miki aure da Mustapha yanzu a gidan Alhaji.'
Ta bude baki tana kallonsa cike da tsananin mamaki. Nusaiba ta daki kafadarsa tace ‘Kai Ahmad kaji tsoron Allah.'
Yace ‘Wallahi da gaske nake, kirawo Baffa a waya ki tambayeshi.’
A take Mommy ta fito daga daki rike da waya jiki a sanyaye, Ahmad ya kalleta yace ‘Mommy ai an daura auren Yaya Khadija ko?’
Ta daga kai tana cewa ‘Eh, yanzu Baffanku yake gaya min an daura auren.’ ta juya ta dubi Khadija tace ‘Khadija kin zama matar aure.’
Ta fada kan kujera kamar wadda aka tura, to murna zata yi ko me? Bata taba zata za a daura aure yau ba, ta zata za ayi yanda aka saba; a kawo kudin aure a zo a sa rana sannan a shirya biki a nutse. Shikenan yanzu ta zama matar Mustapha? Ikon Allah.
Ta kai hannu ta shafa kwarmin idonta inda taji danshi; kwallace ta fado. To kukan me takeyi? Murna takeyi ko kuwa tsabar mamaki ne?
Nabila ta zauna ta doro hannunta a kafadarta tana kallon Mommy tana cewa ‘To Mommy sai mu fara shirin bikin kenan ko kaita kawai za ayi haka?’
Ta banka mata harara tana cewa ‘Sai kace wata kaza?’
Mommy tace ‘Uhm, sai dai mu jira Baffanku ya dawo muji.'
Ta koma daki ta barsu a nan.
____
To Yaya? Me kuke tunanin zai faru? Ga amarya ga ango, kuma ga lockdown a hanya.
Gaba daya tunanin Khadija ya tsaya, wannan daura auren da aka ce an yi mata yana nufin nan da ‘yan kwanakin zata tare a gidan Mustapha. Fatanta daya Daddy ya bari ayi biki don gaskiya tana son biki.
Karar wayarta ne ya katse mata tunani, tana kallon wayar tayi murmushi “My love” shine sunan da tayi saving lambar Mustapha da shi.
'Hello.' ta amsa murya kasa-kasa.
Muryarsa zakwai cike da farin ciki yace ‘Ya na ji ki haka? Ko ba kya farin ciki ne? Alhaji ya hutar da mu, kinga next weekend kawai sai a kawo min amarya ta.’
Tayi dariya ‘I was just not expecting it to happen today, but Alhamdulillah. Ai babu abinda ya fi zama da masoyi dadi.’
'Hakane. So me kike bukata na bikin, ki sami Yaya Mama kuyi lissafi zuwa an jima sai ki gaya min na turo miki ta account dinki. In sha Allah ranar Tuesday za a kawo lefe.’
'Ok, hakan yayi.’
'Common, ni ina so na ji muryarki tayi zaki zakwai kamar tawan nan.’
Tayi dariya ‘Ka kirawoni in an jima kafin nan na sha zuma zaka ji zakin da muryar zata yi.’
Suka yi sallama ta ajiye wayar ta koma ta kwanta a kan gadon cikin sanyin jiki.
Dab da azahar Yaya Mama ta karaso tare da yaranta Anisa da Jawad. Itace Babba a ‘yayan gidan su Khadija. Bayan ta gama tsokanar Khadija ta shige daki inda ta tarar da Mommy tare da kanwarta Anti Naja'atu suna ta tattauna bikin; don Baffa ya sanar da su a shirya a yi biki ranar asabar da Lahadi idan an gama sai a kai amarya.
Bayan ta gaishesu ta zauna suka cigaba da tattaunawa a kan bikin.
Jimawa kadan Yaya Mama tace ‘Ni wallahi Mommy tausayi ma Khadija take bani, Allah ya sa dai da gaske yake sonta kuma ya cigaba da kula da ita. Ga yara har hudu yana shirin hada mata da su, ai sai a hankali.’
Anti Naja tace ‘Kada ki damu ai mace komai kankantarta raino baya gagararta.’
Mommy tace ‘Yaran ma fa yana kawosu nan wajenta, kamar suna da tarbiyya da saukin hali ma.’
'To kin ji ma. Kada kiyi mata magana ma ki sa ta zata wani tashin hankali ne don na ganta tun da aka ce an daura auren nan jikinta yayi sanyi.’
Haka suka gama tattaunawarsu suka tashi.
………..
Ranar Lahadi bayan Magriba aka shirya Khadija a ka kaita gidan Mustapha
Bai zo da abokansa ba sai mutum daya wato Badaru, ba tare da bata lokaci ba suka sallami kawayen amarya Badaru ya kwashesu.
Bayan ya rufe gidan ya dawo ya sameta tana ta faman share hawaye. Ya zauna ya lallasheta har tayi shiru sannan sukayi Sallah ya bude musu abincin da ya zo da shi suka ci. Da kansa ya kwashe kayan da suka gama cin abincin sannan ya dawo ya sameta a zaune a inda ya barta.
'Yauwa, tunda mun koshi taso na nuna miki gidan naki kafin mu kwanta.’ ya fada yana murmushi.
Ta mike a kunyace, har sun kama hanyar fita daga dakin ya juyo ya dubeta yana murmushi yace ‘Bari mu fara daga nan, nan ne dakinki.’
Tayi murmushi murya kasa-kasa tace ‘Ok.’
Ya wuce ta bishi a baya ya nuna mata ragowar gidan; bayan dakinta sai dakinsa sai kuma dakin yara inda nan ne kuma dakin baki. Sai kuma parlor guda daya da dining area a dai-dai kofar kitchen.
Bayan sun gama zagayawa ya kashe fitulun sannan suka wuce dakinsa inda zasu kwana.
……….
Ranar da Khadija ta cika kwana uku da tarewa a ranar bakin danginsa da suke ta zuwa ganin amarya sun lafa, don tunda gari ya waye babu wanda ya zo har azahar tayi. Suna zaune a parlor suna hirarrakinsu aka fara kiran Sallah, ya mike yana cewa ‘Bari naje masallaci na dawo.’
‘Ok, by then nima nayi sallar nayi serving lunch.’ ta amsa itama tana mikewa.
Tayi masa a dawo lafiya ya fice ita kuma ta shige kitchen.
Kafin ya dawo ta yi Sallah ta gyara kwalliyarta sanna ta jera abincin a kan dininga table. Yana dawowa tayi masa sannu da zuwa sannan ya zauna a dining table ta zuba abinci suka fara ci. Fried rice ne tare da sauce din hanta da salad, daga gefe kuma ga hadadden zobo. Shiru sukayi kowa yana ta kai loma, sai da Mustapha ya kusa cinye abincin nasa sannan ya ajiye cokalinsa ya dauki zobon da ta zuba masa a kofin tangaran ya kora. Yana ajiye kofin ya dauki cokalinsa yana gyara abincin ya dubeta yana cewa ‘Umm! Kin iya girki fa.’
Tayi dariya tace ‘Ai da na zaci santin kurma kake da ka kasa magana.’
'Au ashe ma sa min ido kika yi.’ ya fada yana sake cika baki da abincin.
Tayi dariya itama ta cigaba da cin abincin.
Bayan ya hadiye na bakinsa yace ‘Ina ga ai ya kamata in an jima muje mu debo su Afaf ko? Tun da suka ji an kawoki suke ta zumudi.’
Ta kalleshi tana wasa da cokalinta a kan abincin saboda ta riga ta koshi, tace ‘Babe ai na zata za a barsu sai mun dan huta, kaga shekaran jiya fa na tare. Ko gajiyar biki ma ai ban gama hucewa ba.’
‘Haba, ai sai ku huta tare, kin san suma fa they missed home don tunda mahaifiyarsu ta rasu rabonsu da gida.’
'Allah sarki, ni kaina ina dokin dawowarsu nan but babe please ka bari koda zuwa next week ne na dan gama kwance kayana.’ ta fada da muryar magiya da lallashi.
Ya ture farantin gabansa ya sake cika kofinsa na zobo, ya dan gatsina fuska yace ‘Ok, amma dai ba zasu ji dadi ba. Dazu muka gama waya da su suna ta dokin dawowa wajenki.’
Ya mike ya nufi wajen TV yayinda itama ta mike ta fara tattara kwanukan tana cewa ‘Allah sarki, in sha Allah next week da ni zamu je mu daukosu kaga daga nan ma sai mu biya gaba daya mu gaida Mommy mu gaida su Hajiya sai mu dawo gida.’
'Umm!’ ya amsa yana canza channel din TV.
Ta cigaba da kwashe kwanukan tunani kala-kala yana yawo a kwakwalwarta; ta yi zaton yana dokin kasancewa da ita, ta yanda zai bari su dan kara fahimtar juna kuma su more amarcinsu kafin ya dauko yaran amma shi yana maganar yau. Babu kananan yara a gidansu amma kusan kullum suna tare da yaran Yaya Mama, ta san yara ba zasu bari ta mori amarcinta ba tunda su rayuwarsu suna bukatar kulawa ne kullum. Musamman tunda ga Shukra mai shekaru uku kacal. Sati dayan ma da tace a kara kawai dai daurewa tayi don ita da a tunaninta ta sami kamar wata uku a gidan kafin ya kawo mata yara tunda a can ma inda suke ana kula dasu. To amma bata da wani zabi, zuwa next week din sai ta bishi suje su dauko yaran.
…….
Ana fara kiran magriba yayi alwala ya dauki mukullin motarsa, ya sameta a kitchen tana tsugene a tsakiyar kitchen din tana tuka tuwon shinkafa. Motsinsa ya sa ta saurara da tukin tuwon ta juyo, ta dubeshi tace ‘Fita zaka yi? Ko masallaci zaka je?’
'Eh, daga masallacin zan wuce na dubo yara sai kuma na wuce wajen Hajiya.’
Ta dan langabe kai ‘Babe ai da ka dawo, nima sai na shirya muje na gaida Hajiyan.’
'No ki bari next week zamu je tare.’ Ya amsa yana duba wayarsa.
Ta saki tukin tuwon ta mike ta nufeshi da niyyar ya rungumeshi, sai dai ya dan kauce don haka ta gefe ta rungumoshi. Jikinta ya dan yi sanyi ta sumbaci kumatunsa tace ‘A dawo lafiya Babe, I will wait for you idan ka dawo sai muyi dinner tare. Ka gaida su Hajiya.’
'Ok.' ya amsa sannan ya fice.
.........
A parlor ya sami Daddy, bayan sun gaisa suka dan taba hira. Daddy yace ‘Wai ka debo yaranka kuwa?’
'Ban debo su ba, tace a bari sai zuwa next week idan ta gama hutawa.’ Yana wani kau da kai.
‘To babu laifi; Amma fa idan ka daukosu to ka saka ido, ka san mata yanzu basa son riko. Idan baka yi wasa ba haka za a mayar maka da yara kamar almajirai a gidanka.’
'In sha Allah zan kula, duk da ma na kula kamar bata da muguntar.’
'A'a, basu fa da tabbas, kai dai ka sa ido. Kuma ka dinga bincikar duk motsinsu.’ Ya fada yana nuna shi da yatsa.
Suka dan sake hira sannan ya shiga wajen Hajiya inda ya samesu ita da Yaya Jidda suna hira; da yake ita gidanta kusa da gidan ne wataran ma sai an yi sallar Magriba take zuwa.
Bayan sun gaisa suka cigaba da hirarsu gaba daya. Jimawa kadan Yaya Jidda tace ‘Musty ina amarya? Tsohuwar sirikar taka ta baka yaran ko har yanzun ba zata bayar ba?’
Ya gyara zama yace ‘Haba, sai kace ita ta haifa min su ai dole ta bani su.’
Hajiya tace ‘Sai yaushe zaka dauko su?’
'Tace wai a bari ta huta zuwa next week, don ni da yau ma na so a daukosu. Yanzu ma idan na fita zan je na kai musu biscuits din da na saya musu.’
Yaya Jidda tace ‘Wai wacece tace a bari ta huta? Khadijan?’
Yace ‘Eh, tace wai a bari ta huta ta gama ware kayanta kafin a kawo su.’
'Kai Musty! Yanzu kai har ka bata dama su da gidan ubansu sai ta ga dama za a kawosu, to me tayi ya gajiyar da ita har take bukatar hutu.'
'To nima dai haka na gani, amma dai zan ga yanda zamu yi.’ Ya fada yana kauda kai.
Hajiya tace ‘To ka dai dinga kula sosai don kada ta dinga cutar da su, ka sa ido sosai don yanzu mata ba tausayi ne da su ba.’
Yaya Jidda tace ‘Musamman gashi tun yanzu ta fara iyayi da kafa dokoki, a jira ta huta kafin a kawosu gidan ubansu.’
Haka suka gama hirarrakinsu suna jaddada masa ya sa ido sosai kada Khadija ta cutar da yaransa; yayi musu sallama ya wuce gidan iyayen Ma’u wajen yara. Sai da ya tsaya a hanya ya saya musu yoghurt da gasasshiyar kaza sannan ya wuce.
Yana shiga bayan sun gaisa da Mama ta turo masa yaran suka sameshi a guest room. Suka karbi kajin da yoghurt suka kaiwa Mama; wadda ta riga ta saba idan ya kawowa yaran abu to ba zai bata ba sai dai ya bawa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 25