Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a lokacin. Ya kalli plate dinsa; ya riga ya ci da yawa sannan kuma sauran duk ya dame da sauce. Cike da damuwa ya cewa Naja ‘Ko wannan zaki ci naje na dubo.’ ‘No, kada ka damu. Ku ci abincinku akwai bread a kasa zan je na ci.’ Ta juya ta fice daga parlor din ba tare da ta surareshi ba. A fusace ya nufi dakin Khadija, tuna kafin ya fara buga kofar ya kirawo sunanta. Ba tare da bata lokacin ba ta amsa sannan ta taso ta bude masa kofar, ko a fuska bata nuna masa ta san tayi laifi. Ya shige cikin daki ya kalli abincin da take ci a gefen dadduma yace ‘Ya zaki taho nan ki kama cin abinci ki bar mutane? Kuma kina ji nace ki bata abincin itama.’ Duk yanda ta so abi maganar a hankali bai samu ba, domin yanda yayi mata wannan tambayar da isa da gadara take taji duk wata kara da zata iya yi masa ta bushe. Ta kalleshi ta kawar da kai sanna ta wuceshi ta koma ta zauna a gaban abincinta inda ta taso sannan tace ‘Gani nayi kun cike table din, abincin kuma babu tunda ni ban soya dankali da ita ba. Me kake so na bata?’ ‘Ai tun jiya nace ki dinga saka abincin a can don kowa ya ci kuma kika amsa ko? Me yasa ne kike so ki dinga raina ni a gaban mutane? Saboda me nace ki bata abinci ba zaki bata ba zaki shigo nan ki bar mutane?’ Ta kula dai duk wani zille-zille ba zai yi mata ba, ta kalleshi suka hada ido tayi murmushin yake mai dauke da takaici sannan tace ‘Kwana kusan talatin tayi a gidan nan tana girki bata taba bani ba, kuma tare kuke cin abinci kai da ita da yara baka taba cewa a kirawoni naci abinci ba; ko da yake ko ka kirawoni ma ba ci zan yiba tunda nima na iya girkawa. Kayi hakuri ba zan hada girki da matarka ba itama kar ta hada dani, duk wanda ya girka yaci shi da maigida da yara kawai.’ PAGE 177 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta mika hannunta ta dauki fork a kan plate din da yake gabanta ta fara wasa da shi tana kokarin tokare takaicin da yake taso mata yana neman ya sakata kuka. ‘Wai ke me yasa ban isa na gaya miki magana kiji bane Khadija? Ko..’ ‘Ita da ka gaya mata ai ta ji har ta bani abincin, ko da yake ita ka dauka mutum shi yasa kake nema mata abinda zata ci. Ni da babu wanda ya damu da rayuwata ina nan kake fita ka siyo muku abinci ka sakata a gaba ita da yaranka ku cinye ba tare da ko rabona an bani ba. Ban yi magana ba, shine kuma yanzu za ace ni zan bata abinci; to ta cigaba da jirana taga idan zata ci abinci.’ Ta gyara zama ta jingina da bango ta kawar da kai. Ya rasa abinda zai gaya mata saboda tabbas ya san duk abinda ta fada gaskiya ne, sai dai a wancan lokacin ai laifi tayi masa na kin amincewa ta kula da yara don haka bai ga dalilin da zai sa ya bata abincin da ya siyo ba bayan taki ta girka. Ba tare ya ce mata komai ba ya fice daga dakin don a yanda ya san Khadija da taurin kai sai dai ya datse igiyar auren nan amma ba zata yi abinda yake so ba. Sai dai tabbas idan ta cigaba da gwada masa taurin kai irin wannan zai datse igiyar auren ya huta, taje can gidansu ta cigaba da taurin kan. ……….. Haka ya karasa shiryawa zuciyarsa babu dadi, don ko dakin Najan ma bai shiga ba suka fice tare da Habib suka tafi daurin aure. Yana ficewa itama ta gama shiryawa, ta kulle dakinta da parlor dinta gaba daya. Ta hada mukullanta da wanda ta cire daga jikin nashi keys din duka ta jefa a jaka don bata so ko shi ya bude mata waje idan bata nan. Ta goya Hammad ta tasa Hafsa a gaba, suna saukowa kasa ta shiga parlor din Naja inda ta jiyo hayaniyar yaran, ta dubeta da fara’a tace ‘To Anti ni na fita, zan je gidanmu ne in sha Allahu zan kwana biyu. Sai ranar litnin zan dawo.’ Ta juyo ta yi mata wani kallo na raina sanna tace ‘A dawo lafiya.’ Shukra ta tashi da gudu ta kama hannunta tace ‘Anti gidan Mommy zaki je?’ Ta shafa kanta ‘Can zan je Shukra, sai ranar Monday zan dawo.’ Ta langabe kai tana cewa ‘Kai Anti ina son zuwa fa, kwana biyu ban je wajen Anti nabila ba fa.’ PAGE 178 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) ‘Ai kin ga Monday akwai school ko? Shi yasa ba zan tafi dake ba. Amma idan zan koma ranar da babu makaranta zan tafi dake kin ji.’ Haka ta tsaya ta lallabata sannan ta wuce. 000000 Haka rayuwarsu ta cigaba; duk yanda ya so Khadeeja ta dinga binshi dakinsa gaba daya taki. Don haka bashi da zabi duk daren da yake bukatarta sai dai ya bita dakinta su kwana, idan bai je ba sai dai kawai ta leka dakin nasa tace masa sai da safe. Sau da dama ya sha kyaleta yaga ko zata biyo shi amma da zarar ta shiga dakin tace masa sai da safe sai tayi ficewarta. Da farko duk ranar kwananta idan bai ya bukatarta yayi kwanciyarsa a dakinsa haka yake kwana shi kadai, amma tunda Naja ta gane sai ta dinga bibiya; idan ta sameshi shi kadai sai tayi kwanciyarta a nan da uzirin laulayi. A zatonsu Khadeeja bata sani ba; sai dai ita din ta zabi tayi shirune tunda ta san yana yin hakan ne don ta hakura ta koma kwana dakinsa. Ita kuma har ga Allah gani take yi babu yanda za ayi ko wa take aure ta kwana gadon da yake kwana da wata matar; musamman Naja wadda bata tsanar wata mace kamar ita ba. …….. Tunda Khadeeja ta dawo daga gida kuma sai laulayi ya saka Naja a gaba. Haka zata wuni jikinta babu kwari, abinci kuwa to idan dai itace ta dafa ba zata iya ci ba dole sai dai ya siyo mata wanda zata ci. Yau Khadeeja take fita daga girki don haka a wajenta shi da yara suka ci abincin rana. Ragowar abincin ranan shi ta diba ta zuba a flask ta ajiye musu ita da Hafsa saboda ta huta shiga kitchen da daddare. Tana zaune a parlor tana bawa Hammad nono ya shigo parlor din, bayan ta amsa sallamarsa ya zauna kusa da ita. Sai da ya gama kame-kamensa yace ‘Da-Allah kiyi abincin dare gaba daya saboda Naja bata da lafiya, kin san na gaya miki ciki ne da ita kuma yana bata wahala.’ Ko da dai bata zata abinda ya zo fada kenan ba amma tana jiran wannan din ma domin tu tuni yara suka gaya mata Najan bata da lafiya kuma ta fahimci menene ciwon. Ta cire Hammad daga nono ta saka shi a kafada tana cewa ‘Ai kuwa ka ga yau ba girki zan yi ba ga ragowar abincin rana can shi na ajiye zamu ci da daddare. Allah ya bata lafiya.’ PAGE 179 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ya sake bata rai ‘Khadeeja, da-Allah ki bari. Yarinyar nan bata da lafiya ko abincin ma ita bata iya ci, kuma ba ita nace ki yiwa girki ba. Ni da yara zaki girkawa, idan ta sami lafiya zata karbi girkinta.’ Ta kwantar da Hammad a gefenta sannan ta fuskanceshi gaba daya don bata cikin yanayi na son zance, tace ‘To ai cikin ba wani abu bane, ko ka manta ne? haka na dinga hadawa da cikin da komai duka da karancin shekaruna ga rashin mataimaki. Ita kuwa yanzu ka ga tana ma da mai aiki; ai babu wani abu da zai gagareta. Idan dai kwana ya zagayo kaina in sha Allahu zan yi kamar yanda muka saba.’ A fusace ya kalleta na dan lokaci sannan yace ‘Yanzu kenan ke babu halin ace kiyi wani abu sai ki tuno abinda ya faru shekarun da suka wuce? Kuna zaune tare a gidan kina kallon bata da lafiya nace kiyi girkinta amma kina nema kice ba zaki yi ba? Wai ke me kike son zama ne? babu wanda ya isa ya tankwaraki kenan saboda zaman kanki kike yi ko me?’ Ta sunkuyar da kai murya kasa-kasa tace ‘Ba haka bane, kawai dai nima mutum ce, yanda aka yi min na zata haka ake yiwa mutanen da ake so shi yasa nake so ko yaya ne ayi adalci.’ Bata saurari abinda zai fada ba ta mike ta dauki Hammad a hankali saboda bata son ta tasheshi ya fara bacci, ta wuce dakinta ta barshi a nan. Yanda tayi wannan tafiyar ya tabbatar ko me zai yi ba zata saurareshi ba; wanda hakan yake nufin shi da yaransa zasu shiga halin rashin samun kulawa na tsawon wata takwas har Naja ta haihu, sai dai su sami kulawa kwana biyu kwana biyu kuma a barsu a gantale. Babu yanda za ayi ace ya dauki wannan kuma a halin yana da mata biyu. A yanda cikin nan yake wahalar da Naja kuma dole Khadeeja ce zata dauki wannan hidimar har zuwa lokacin da zata haihu. Sai da ya gama lissafinsa sannan ya mike ya fice, kai tsaye dakinsa ya wuce ya dauki mukullan motarsa. Bai zame ko ina ba sai gidansu Khadeeja; baya son kai kara don ya kulaita ko ya kai kararta ma goya mata baya zasuyi, sai dai yanzu bashi da wani zabi da ya wuce hakan. Ya ci sa a yana shiga gidan Baffa yana shirin fita, a nan bakin gate ya tsaya yayi masa bayanin halin da ake ciki. PAGE 180 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Cike da kulawa Baffa ya jijjiga kai yace ‘Subhanallahi, to Allah ya bata lafiya. Yanzu ka ga fita zanyi amma in sha Allahu idan na gama abinda nake zan zo har gidan na sami Khadeejan. Kada ma kace mata zan zo, ka kyaleni da ita zan zo na sameta ka ji. Ai daya daga cikin amfanin karin auren kenan daya ta taimakawa daya a irin wannan yanayin.’ Suka yi sallama kowa ya nufi inda zai je. PAGE 181 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ba shi da tabbacin abinda Baffa zai yi a kan wannan matsalar amma dai yana saka ran Baffan zai fahimceshi ya saka Khadeeja ta dinga taimakawa Naja, a kalla a lokutan da bata da lafiya; idan ba haka ba menene ribar mata biyun ga namiji. Bata samu tayi sallar isha’i a kan lokaci ba don haka har wajen 8:30pm tana zaune a kan dadduma, Hammad yana wajen Habib wanda yake zaune a parlor dinta yana kallon TV. Ta so ta jiyo muryar Baffanta suna gaisawa da Mustapha a tsakar gida, amma da yake bata sa rai da zuwan Baffan ba sai kawai ta zata kunnenta ne ya jiye mata ba daidai ba. Tana nan zaune Mustapha ya turo kofar dakin ya shigo da sallama, bayan ta amsa sallamarsa yace ‘Baffan Mommy ne yazo, gashi nan a parlor na.’ Da mamaki ta kalli Mustaphan da alamomin tambaya a fuskarta, tace ‘Baffana?’ Yayi ‘yar dariya saboda yanda ta tambaya sannan yace ‘Baffan Nabeela dai.’ Itama sai ta dan yi dariya tare da mikewa tsaye; kwata-kwata bata yi zaton kararta Mustapha ya kai wajen Baffa ba. Ta yi zaton zuwa yayi ya ga sabon gidansu kamar yanda take ta faman rokonsa tunda suka tare yazo ya ga gidan. Nan da nan ta tashi ta fice don zuwa ta taryi Baffan nata. Sai da ta shiga kitchen ta jera ruwa da lemo a faranti sanna ta fito, ta dubi Habib wanda yake zaune a parlor din yana rike da Hammad tace ‘Yaya ku taso ku gaida Baffa gashi nan a parlor din Abbanku.’ Tana shiga parlor din ta sameshi da Shukra da Nasreen yayin da Abban nasu yake zaune daga gefe a kan kafet; yanayi zaman da Mustaphan yayi kawai ta kalla ta sha jinin jikinta. Ko da bai kai kararta gida ba to tabbas ta san a wannan dan zaman da Baffan yayi ya gaya masa laifinta. Ta karasa ta ajiye ruwan a gaban Baffa a daidai lokacin da Naja wadda itama ta shigo ta gaisheshi take ficewa daga parlor din. Ta zauna daga gefen kafarsa sannan ta gaisheshi ya amsa cike da girmamawa. Sai da ya gama raha da yaran sannan ya zaro sababbin kudi a aljihunsa ya bawa kowa naira dubu sannan ya sallamesu suka wuce suka barsu daga shi sai Khadeejan da Mustapha. PAGE 182 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ya dubi Khadeeja yayi gyaran murya sannan yace ‘Deeje, garin yaya kika ce ba zaki taimaka ki karbarwa abokiyar zamanki hidimar gida ba bayan bata da lafiya? Haba Khadeeja, hakan ai shine zaman tare tunda dai Allah ya hadaku.’ Ta yi shiru ta sunkuyar da kai tana tunanin ta inda zata fara, inama da Baffa ya zo da Mommy. To ta ina zata fara gayawa Baffa yanda Mustapha yayi mata lokacin tana nata laulayin? Kuma ya za ayi ta gayawa Baffa cewa ita bata bin Mustapha dakinsa kuma duk ranar da bata bishi dakinsa ba Naje yake kira ta tayashi kwana? To ai Baffa ma sai dai ya sake yi mata fadan kin zuwa dakin miji domin tabbas abu ne da haka aka saba; kuma ta sani mata biyu ne da kakanta mahaifin baffa. Wanda da wayonta kafin dukansu su rasa ta san matan ne suke zuwa dakinsa. Wannan kam ai sai dai ta kara kai karar kanta. Muryar Baffa ce ta katseta yana cewa ‘Deeje me yasa ba zaki taimakawa abokiyar zamanki ba?’ Ta dan yi firgigit kamar wadda aka tasa daga bacci sannan tace ‘Uhm Baffa wallahi nima daurewa nake ina yin hidimar ranar girkina, tunda ga jego ina yi sannan kuma ina zuwa aiki.’ ‘Eh, ai wannan ba zai gagareki ba tunda kinga da ace ke kadai ce a gidan ai duka zaki hada ko?’ Suka yi shiru na dan lokaci sannan daga baya tace ‘Baffa nima fa haka nake hada nawa laulayin da aikin gidan babu wwanda yake tayani. Kuma ka ga Baffa akwai mai aiki fa wadda zata iya yi mata duk abinda take so idan tayi mata bayani.’ Baffa ya dan yi murmushi sannan yace ‘Na fahimceki Khadeeja, amma dai kiyi hakuri ki karbar mata aikin. Tunda kin ga yanzu kema idan kika kuma samun wani cikin ai zata karbar miki ko? Kiyi hakuri Deeje, bana son taurin kai da yawa. Allah zai baki lada har kashi biyu, ladan biyayya wa miji da kuma ladan taimakon ‘yar uwarki musulma wadda take neman taimakon naki. Kiyi hakuri kin ji, tunda ga yarinyarki nan tana taimaka miki ki zauna lafiya tunda dama yara duka naki ne tun kafin ma a aurota.’ Haka Baffa ya dauki lokaci yana bata hakuri, daga karshe kuma ya bata umarnin lallai ta taimakawa Naja ta karbi hidimar gidan. PAGE 183 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid Innar su Amal Bayan ya mike duka suka mike gaba daya, a nan yayi sallama da Khadeeja yace ta koma ciki. Suka fice shi da Mustapha wanda yayi masa rakiya har wajen motarsa sannan yayi masa sallama ya tafi. Ya san ko da ya koma wajenta a yanzu ba zata saurareshi ba sai dai ma ta gaya masa maganganun da baya son ji, don haka ya wuce wajen Naja tunda dama kwananta ne. ………. Har turiri take ji yana taso mata a kirjinta saboda tsabar yanda zuciyarta take tafasa; sai da tayi da gaske sannan ta kai kanta dakinta ba tare da tarushe da kuka ba. Ya za ayi ace ta karbarwa naja girki saboda kawai tana da ciki? Bayan ita a lokacin da tana da nata cikin hakaya dinga barinta da duk wata hidima yana hana yaranshi su tayata. Sannan kuma idan tayi magana ya dinga nuna mata cewa laulayi ba komai bane kamar ma dai itace take son nuna raki. Yanzu kenan haka zata kwashe wata takwas ko tara tana kula da yara yayinda Naja take kwana da miji tunda laulayin bai hana idan ta sameshi shi kadai a dakin ta kai masa kanta ba? Tana shiga ta murza mukulli ta rufe kofar, sai da karasa kan daddumar da ta tashi sannan ta zube da gwiwoyinta tarushe da kuka. Shikenan ita ta zama baiwar Mustapha ne? ya iya nunawa kowa kauna da tausayi a duniya amma banda ita? Anya zata iya wannan rayuwar a gidan Mustapha kuwa? Amma ta san dole ne ta bi umarnin Baffanta, musamman da yake a gaban Mustapha ya bata umarnin. Ta kifa goshinta a kasa ta sake rushewa da kuka. ….. Ya so kwarai kamar yanda ya saba lekawa da daddare ya yiwa wadda bata da kwana sai da safe ya leka wajen Khadeeja, amma da yake bai shirya rigimarta ba sai kawai ya kyaleta suka shige daki shi da Naja suka yi kwanciyarsu. Ba karamin dadi ya ji ba da ya dawo daga masallaci sallar asuba ya jiyo motsinta a kitchen, tabbas ya san ta ji maganar Baffanta. Ba tare da bata lokaci ba ta shiryasu sannan ya fito ya kaisu makarantar. Kafin ya dawo daga kaisu makaranta ta gama nata shirin, a zaune ya sameta a parlor dinta tana karyawa. Babu yabo babu fallasa suka gaisa, sai dai daga gaisuwar bata sake ko da kallon inda yake ba. PAGE 184 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Jimawa kadan ya mike zai fice, tace ‘Idan na tsahi daga aiki zan je gidan Mommy.’ Ya dan tsaya yana kallonta yana kokarin su hada ido ko zai karanto wani abu a fuskarta, sai dai bata bashi damar ba. Daga tsayen yace ‘Ki gaishe min da mutanen gidan.’ Ya fice ita kuma ta cigaba da cin abincinta ba tare da ko da ta kalli inda ya wuce ba; gaba daya ma a halin yanzu ko son kallonsa bata son yi. ………. Tun wajen 12pm ta nemi izini a wajen aikin nata ta fice, kai tsaye gidansu ta nufa. Ta ci sa’a ta sami Mommy da Yaya Mama suna zaune a parlor suna hirarrakinsu. Bayan sun gaisa Khadeeja ta dubi Yaya Mama tace ‘A nan kika kwana Yaya.’ Tayi dariya tace ‘Ga jakata a kusa dani kina kallo amma kike min wannan tambayar, to ni yanzu ma zan tashi saboda 2pm zan dauko yara a makaranta sannan mu wuce gidan.’ Itama tayi dariyyar, ta umurci Hafsa da ta shida dakin Nabila ko taje kitchen wajen masu aikin gidan ta zauna. Tun kafin tace wani abu Mommy ta dubeta tace ‘Lafiya dai na ganki kamar a fusace, sarkin rigima.’ Ta zumbura baki ta sunkyar da kai tana kallon hannunta kamar me kunkuni, sai da ta gama zumbura bakin sannan cike da takaici tana kokarin danne hawayen da ya taso mata tace ‘Mommy ni Mustapha zai mayar ‘yar aiki, kuma Baffa ya goya masa baya.’ Mommy ta gyara zama ta fuskanceta sosai tana kallon fuskarta da mamaki sannan tace ‘Ban gane ba, kuma me kawo Baffanki a cikin mayar dake ‘yar aiki? Shi Mustaphan me yayi miki?’ Tana bude baki zata yi magana hawaye ya kwace mata, ta sa bayan hannunta ta goge sannan ta labartawa Mommy abinda ya faru. Zuwa lokacin hawayenta ya gama kwacewa yana zuba kamar ana zubar da ruwan famfo, Mommy ce ma take kokarin goge mata. Tace ‘Mommy yanzu shikenan haka zan yi wata tara ina mata hidimar gida tana kwana da miji, bayan ni haka nayi nawa laulayin ko tausayina baya ji. Ko haihuwar Hammad fa ana gama suna dole na mike na koma hidimar gidan saboda ban ma ga fuskar cewa ba zan iya ba. Amma yanzu saboda ya auro ‘yar gwal shine zan karbar mata aiki ita kuma tayi laulayi.’ PAGE 185 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Yaya Mama tace ‘Nifa gaba daya ban gane. To ke me yasa bakya zuwa dakin kike barinta taje, ai da sai kije ki yi wanciyarki a can kiga ta inda marasa kunya zasu kwana tare.’ Kafin tayi magana Mommy tace ‘Gaskiya nima dai ban gane dabarar yin hakan ba, ai dakin ya kamata ki gyara ki tare har sai kin gama kwananki.’ Ta sa bayan hannunta ta goge hawayenta sannan tace ‘Mommy ba zan iya ba, ya kwana da wata matar a kan gadon sannan nima ya kwana dani a kan wannan gadon. Watakila ma da yayi aurensa ba tare da ya ci min mutunci ba abubuwa da dama zau zo min da sauki, ama gaskiya ba zan iya ba. Tunda ko bayan ta tare ranar da zan karbi girki bayan da ta gama kwana takwas dinta na shirya tsaf zan shiga dakin, amma har magriba bata fito daga ciki ba. Lokacin shi kuma ya riga ya fita. Don haka na kyaleta na shirya masa abincin dare tunda na gama kintsawa. Amma yana dawowa ko kallon abincin bai yi ba ya sameni wai tunda ina jego na bashi kwanakin ya kaiwa amaryarsa in ya so idan nayi arba’in sai a fara rabon kwanan. Kinga kenan ita ta riga ta san ba zai bani kwnan ba shi yasa ta ki fita ma daga dakinsa. Daga wannan lokacin dakin da me dakin suka karasa fice min daga rai gaskiya. Idan yana bukatata ya sameni a dakina, kuma yana zuwa din.’ Mommy wadda take binta da kallo tana jijjiga kai tace ‘Lallai Mustapha, ni na rasa ma me zan ce. Ni fa mamakin da nake Baffanki ko gaya min bai yi zai je ba balle da ya dawo ya gaya min, watakila jiya bayan ya fita da magriba Mustaphan yayi sa’a ya sameshi a gate suka gama magana.’ Yaya Mama tace ‘Hmm! Ai komai dadinki da miji idan dai wata macen ta gifta to sai abinda kika gani. Watan hakurinki ne ya kama har ya gama yayinta.’ Mommy tace ‘To yanzu ya za a yi? Kinga Baffanki ya riga ya sa baki a maganar ba tare da kin gaya masa ainahin abinda yake faruwa ba..’ ‘To Mommy ya za ayi nayi masa duk wannan bayanin ya gane, ai ban ga alamar zai ma gane ba tunda ko a lokacin ma yace amfanin mta biyu kenan daya ta taimakwa daya. Kuma ya za ayi na zauna ina gaya masa Mustapha yana satar min kwana saboda na ki zuwa dakinsa?’ PAGE 186 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) ‘Umm, hakane kuma. To Allah ya kyauta. Yanzu kam sai dai kiyi hakuri a ga abinda hali zai yi tunda dai babu wanda zai je ya kwance maganar baffanki. Ina ga kula dayarn wanda kika yi a baya bai kashe ki ba bana jin na wata tara nan gaba zai dameki.’ Haka suka zauna suka yi ta bata hakuri; sai daga karshe Yaya Mama tace ‘Kuma kema idan kin gaji kawai kiyi pretending ki kwanta masa, wallahi da kaina zan zo na taho dake na kawowa Mommy tayi jinyarki idan kin huta kya koma.’ Mommy ta kai mata duka tana cewa ‘Allah ya shiryeki yayar kwabo.’ Suna nan zaune wajen 1:30pm Baffa ya shigo gidan da sallama, bayan ya amsa gaisuwarsu da sannu da zuwa ya dubi Mommy tana zaune a tsakiyar su Khadeeja yace ‘Gulmar wa kuke yi suka saka ki a tsakiya haka.’ Itama dariyar tayi tace ‘Ba dai gulmarka muke yi ba.’ Yaya Mama tayi musu sallama ta fice yayinda Khadeeja ta mike ta nufi dakin Mommy ba tare da tace komai ba. Baffa ya bi bayanta da kallo sannan yayi dariya ya dubi Mommy yace ‘Wannan iya rigimar karata ta kawo ko?’ Ta harareshi tace ‘Ashe ka san kayi mata laifi?’ Yayi dariya yace ‘Rabu da ita da-Allah, ya za ayi ace mutum yana da mata biyu ace daya ba zata karbi daya aiki ba idan bata da lafiya? Ai itama bata so a zauna lafiya ba.’ Nan ta kara yi masa bayanin yanda zaman nasu yake, sai dai ta kasa gaya masa cewa Mustaphan yana bawa Naja kwanan Khadeeja saboda Khadeejan bata yarda taje dakinsa. Yanda ta san shi ta san tabbas ba zai dauki wanna ba, tunda shima tashi uwar har ta koma ga Allah turaka take zuwa ranar kwananta. ……… Haka dole Khadeeja ta hakura ta cigaba da hidimar gida da ta yara. Shima Mustapha da ya gama zagaye-zagayen haka ya sameta a dakinta yana nuna mata jin dadinsa ganin yanda take kula da yaran sai dai baya jin dadin yanda

Chapter 18 of 25