Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abun pregnacy test sannan ta wuce. Ta riga ta san su Rahma suna jiranta a hostel don haka kai tsaye can ta wuce, tana ajiye jakarta a dakin ta fice ta fada toilet. Tana tsoma abin nan a fitsarinta ya nuna radau positive; wato tana dauke da ciki. Tayi murmushi tana ji kamar ta daka tsalle saboda murna, nan da nan idonta suka ciko da kwalla saboda jin dadi. A take kuma jikinta yayi sanyi da ta tuna cewa Mustapha ne yayi mata ciki kuma shine yake shirin auro matar da ta ke ikirarin zata shigo ta gyara mata zama. PAGE 124 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta sunkuyar da kai ta saki takardar a kasa sannan ta fito daga bandakin cike da damuwa. Yanayin da ta shiga dakin ya tabbatar musu da akwai matsala, don haka tun kafin ta Zauna farida ta mike ta tareta tana cewa ‘Ya na ganki haka, lafiya dai ko?’ Ta zauna a kan gado Rahma kamar wadda aka jefa, ta kalli farida suka hada ido sannan ta saki murmushe wanda yake hade da takaici tace ‘I am pregnant Farida.’ Nan da nan su Rahma da Amina da ke zaune suka dako tsalle suka fada jikinta sun ihu. Sai da suka fahimci ita bata taya su ihun kamar yanda suka saba sannan suka tsaya suna kallonta. ‘Girl, wannan ai abun murna ne na ga kamar ke baki ni dadi ba.’ Amina ta fada tana rike da hannun Khadeejan. Ta sunkuyar da kai ta zare hannunta ta goge kwallar da ta fado daga idanunta. Ta basu labarin auren Mustapha da kuma abinda ta gani da ma yanda yake boye mata. Tace ‘Ban ma san wanne zan yi ba; murna ko bakin ciki? Ni da za a zo a gyarawa zama ina zan mike kafa na fara haihuwa; haihuwar da ni ban ma tabbatar zai yi murna da ita ba. A yanzu ma gaba daya kai na ya kulle. Mommy dai tace kada na kuskura nayi masa maganar kara aurensa, na barshi har sai ya zo da kansa ya ya gaya min, a lokacin sai ayi duk wadda za ayi. Amma wallahi ban sani ba ko zan iya jurewa. Gaba daya ma yanzu ban san matsayina a wajen Mustapha ba, kuma ga ciki.’ Suka yi shiru na dan lokaci. Amina ce ta katse shirun nasu tana cewa ‘Gaskiya mutumin nan dan wulakanci ne, haba!’ Rahma tace ‘Amma gaskiya ina bayan Mommy, ki barshi kawai kada kiyi masa magana in ya so idan ya zo zai gaya miki da kansa sai ki yi masa wankin bargo tunda dai babu abinda zai sa ya fasa wannan auren da yayi niyya.’ Tace ‘Hakane.’ Nan suka daui lokaci suna bata baki, sannan daga baya Farida da Rahma suka fice suka tafi lecture din suka barsu a dakin itada Amina wadda ta tsaya ta tayata zama don tace ba zata iya zuwa lecture din ba. PAGE 125 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Duk yanda take cikin damuwa da yanda take so ta yiwa Mustapha tijara game da yanda ya boye mata maganar aurensa da Naja haka ta hakura ta danne zuciyarta. Domin ita kanta ta kasa ganin maslahar yi masa maganar; tunda dai itace baya so ta sani gara ta rabu da shi ta gani ko za a dauro auren ne a kai amarya sama jannati saboda kada ta sani. Cikin da take dauke da shi ma kasa gaya masa tayi, domin bata ga alamar yana farin cikin kasancewarta matarsa ba. Gaba daya ma cikin ya zo mata a wani lokaci ne da take jin cewa da bata same shi ba zata iya hakura da haihuwa a gidan Mustapha har sai ta fahimci inda auren nasu ya sa gaba. Ko da yake dai ta san ana cewa idan namiji zai kara aure matarsa da take gidan sai ta yi matukar hakuri; to tabbasa ta ji a jikinta cewa lokacin nata hakurin ne ya kama yanzun. Da kansa ya kula da yanda take mu’amalarta kwana biyu cikin kasala gashi bata ma son magana, don haka ya tasata a gaba ya kaita asibiti. A nan aka tabbatar masa da cewa tana dauke da ciki sati shida. Suna zaune a mota yana tukosu a hanyarsu ta dawowa ya dubeta yace ‘Kin gani ko, kin sami cikin a kwanciyar hankali ba tare da kinje nemansa a asibiti ba ko? Allah ya sa dai ba mai wahaka bane?’ Ta dan yi gajeran murmushi tace ‘Smin ya Allah.’ Suka yi shiru na dan lokaci, ya dubeta yace ‘Wai ya naga duk kin yi wani shiru ne? kamar ba abin nema ne ya samu ba?’ Ta kawar da kai tana murmushin yake tace ‘Bana jin dadi ne, bacci ma nake ji.’ Ta kwantar da kanta a jikin kujerar motar ta rufe ido, don haka shima ya kyaleta ya mayar da hankali a wajen tukinsa. …… A haka Khadeeja ta dage ta cigaba da mu’amalarta tana yin duk wata hidima da ta saba. Ko a wanne yanayi ta tashi haka take daurewa tayi duk wata hidimarta don bata shirya drama da Mustapha ba. Ta riga ta san idan dai tana numfashi a gidan nan to duk wata hidima da matar gida take yi ba yafe mata zai yi ba; don haka ta daure ta cigaba da dagewa tana yi. Musamman da yake duk wani aiki da ta saba yi a gidan ta riga ta koyawa Rashida kuma ta iya sosai, gashi yarinyar bata da kyashi ko daya, don haka abubuwa suka zo mata da sauki sosai. PAGE 126 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Sai dai fargabarta daya iyayen Rashida suna maganar ko da wane lokaci za a iya zuwa a dauki Rashida saboda aurenta ya kusa; duk da dai an ce za a kawo mata kanwarta to amma ta san akwai aiki. Haka ta cigaba da rayuwarta tana goyon cikinta. A hankali ta fahimci lokutan da yake zuwa zance wajen naja, kuma da yake shi yake kaita makaranta da ta shiga motar take gane Naja ta fita a motar ko kuma sun fita tare. …….. Daidai lokacin da zasu fara jarrabawar karshe a lokacin cikinta ya shiga wata na takwas; ga hidimar gida, ga karatu kuma gashi tana kokarin hada project dinta. A dai-dai lokacin ne kuma Mustapha ya gama gyara gidansa wanda yake fatan da zarar sun koma za ayi bikinsa da Naja. Sau biyu yana kaisu gidan ita da yara, kuma duka zuwa biyun sai ta tambayeshi ko aure zai yi ne yake yin gidan kamar d zubin mata biyu. Amma duk lokacin da ta tambaya sai yace mata ko da zai yi auren to ba yanzu ba; ta rasa gane dalilin da yasa yake son boye mata aurensa da Naja. Don haka ma ta daina tambayarsa gaba daya. Ranar asabar ce kuma tun dare ya sanar da ita da safe yara su shirya zai fita dasu, don haka tun wajen tara na safe ta bayan da suka ci abinci ta sallamesu ta koma ta kwanta. Ya dai ce mata gidan Hajia zasu je kuma suma yaran haka suka gaya mata; amma a ‘yan kwanakin nan yana yawan fita da yaran ranar da babu aiki yace wajen Hajia zai kaisu. Ta riga ta gane wajen Naja yake kaisu, sai dai bata ga dalilin da zai sa tayi masa magana ba tunda ‘yayansa ne sannan kuma gaya musu da yake suce mata gidan Hajia suka je su yake cutarwa ta hanyar koya musu karya. Gaba dayansu suka fice banda Habib, wanda dama ya riga ya saba duk lokacin da za suyi wannan fitar shi baya binsu. A gida yake zama tare da Khadeejan da Rashida. Sai wajen karfe biyar na yamma sannan suka dawo, lokacin ta riga ta gamamabincin dare ta zuba a flask tana kwance a daki. A dakinta yaran suka sameta tana kwance tana hutawa, suka sanar da ita sun dawo. Shukra kuwa sai ta wuce ta haye gadon ta kwanta kusa da ita tana cewa ‘Bacci kike yi Anti?’ PAGE 127 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta dan matsa jikinta tana gyara kwanciya, Khadeejan ta dan gyara kwanciyarta tana kawar da Shukran daga cikinta. Tayi dariya tana cewa ‘Na matsa ko Anti, kada na lotsewa kanina hanci.’ Tayi dariya saboda itace ta saba gaya mata hakan a duk lokacin da take son kwanciya a jikinta tunda cikin ya fara girma; domin Shukra yarinya ce mai son jikin tsiya kuma ta samu Khadeejna bata tureta. Tace ‘Yauwa, ashe dai kin gane. Kada a dinga ce miki yayar mai lotsttsen hanci.’ Suka yi dariya gaba daya; Shukra ta ci gaba da wasa da hannun Khadeejan guda daya yayinda Khadeejan take rike da daya waya a daya hannun tana chatting. Jimawa kadan cike da damuwa tace ‘Anti.’ ‘Umm.’ Ta amsa ba tare da ta bar abinda take yi ba. Tace ‘Gaskiya ni ba zan koma wajen Anti Naja ba, a wajenki zan zauna ko?’ Ta ajiye wayar tace ‘To wa yace zaki koma wajen Anti Naja kuma? Ai muna nan tare, ko ba gamu ba a gidanmu.’ Cike da damuwa tace ‘Ai itama tace aurota Abbanmu zai yi ta dawo gidanmu. Amma sai mun koma sabon gida. Shine yau da muka je wajenta take cewa Yaya Afaf idan ta tare duk wajenta zamu koma. Gaskiya ni dai ba zan koma ba ko?’ Ta dan yi shiru tunani yana nema ya birkita kwakwalwarta; duk da bai gaya mata ba ta san yana kai yaransa wajen Naja, amma maganganun da Najan take gayawa yaran basa kama da maganganun da ya dace a gaya musu a daidai wannan lokacin. Sai dai ta san babu yanda zata yi tunda shi ya bata dama. ‘Anti.’ Muryar Shukra ta katseta tana kiran sunanta. Bayan ta amsa Shukran ta cigaba cikin damuwa ‘Tace saura wata biyu ta tare, gaskiya idan ta zo ki gaya mata ni a wajenki zan zauna ba a wajenta ba. Kuma ma na ji tana gayawa Yaya Afaf idan an koma sabongida sama take so kece a kasa, na gayawa Yaya Afaf mune a sama mu dake tace min wai daAllah can. Gaskiya kia gaya musu mune a sama.’ ‘Hmm! Zan fada musu Shukra, ai mune a sama kada ki damu.’ Ta cigaba da surututa tana bawa Khadeeja labarin irin abubuwan da suke yi idan suka je gidan Naja. PAGE 128 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Duk da Khadeeja bata yi mamakin jin cewa Naja ta san da sabon gida ba amma ta yi mamaki da ta ji cewa har Naja ta zabi part din da take so yainda ita kuma har yanzu bai ma gaya mata ita da wata matar zasu zauna a gidan ba. Ta kasa gane dabarar da Mustapha yake jin yayi da yaki gaya mata zai yi aure; amma dai zata cigaba da binsa taga karshen wulakancinsa. Ko da yake a ‘yan kwanakin nan ma yanda yake kara tubure mata ta tabbatar da tana biye masa da kullum sai sun yi fada. To sai dai bata da wannan lokacin tunda ga project dinta wanda take so ta gama kafin su fara jarrabawa wanda tana fatan Allah ya sa kada haihuwa ta zo mata har sai tayi final paper. Haka ta ajiye wannan ma a ranta tana jiran ranar da zata titsiye Mustapha tunda haka ya zaba. …….. Tun kafin su fara jarabawa ya sanar da ita idan ta haihu aka yi suna aka gama zuwa barka zasu koma sabon gida, saboda baya so aje a bata masa gida. Itama tsarin yayi mata don haka ba tare da wata matsala ba ta amsa. Kuma kamar yanda ya bata umarni ta fara hada kayanta da zata tafi da su duk da cewa ya gaya mata ya saka sabbin furniture a gidan. Ranar da zata yi jarrabawar karshe ya kama yara suna hutun makaranta, kuma sai 2pm zasu shiga paper. Don haka yace idan babu matsala yanaso ta shirya da wuri su tsaya a sabon gida taga furniture din da ya siyo in ya so sai ya ajiyeta a makaranta shi da yara su wuce wajen Hajia. Ta riga ta gama karatunta don haka tun wajen sha daya ta shirya suka shiga mota gaba dayansu suka kama hanya. Saman gidan yana dauke da parlor guda biyu karami da babba da kuma dakuna guda uku sannan da kitchen, daki daya da parlor suna tare da juna wanda dama ya sanar da ita nan ne nashi part din. Kasan kuma parlor ne guda daya, sai dakuna guda biyu wadanda suke kusa da juna sai kuma wani dakin guda daya wanda yake gafe, sannan kuma da kitchen. Parlor din kasan duk a nan aka sauke furniture din; duk da kusan kowanne yana cikin kwalinsa. Suna shiga suka dan yayyage kwalin ita da yara suka gani. PAGE 129 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ya dubeta yana nuna dakunan kasan yana cewa ‘Sai ki zabi a wane dakin za a saka miki gadon, in ya so daya dakin kuma sai a dauko gadonki na tsohon gida a saka.’ Ta kama hanyar sama tana cewa ‘Eh hakan ma yayi; dakin wanda yake jikin nakan sai saka min sabon gadon a nan in ya so na kusa da shi sai a gyarwa ‘yan mata na ko? Shi kuma Yaya Habib sai a bashi wannan na kasan.’ Shukrace kawai ta biyota shi yana tsaye a inda yake. Ta dan juyo tana cewa ‘To kazo muje mana ka gani.’ Yayi ‘yar dariya yace ‘Na zata zaki fi son wadannan dakunan na kasa ai, kin ga sun fi girma. Kuma ai ina ga zai fi min privacy ace dakinki yana nan kasa a madadin yana kusa da nawa idan kin yi baki ina jiyoku.’ Tayi dariya tace ‘Haba dai, kuma don nice duk fadin gidan nan sai na rasa wajen sauke baki sai bedroom? Ai dama sama ba wajen saukan baki bane tunda nan kasan ma da parlor. Amma dai can ne dakina, in ya so idan ma baka so yaran su hau sama za a iya barinsu a kasa.’ Shukra tace ‘Gaskiya Abba mune a sama mu da Anti, in ya so ita Anti N…’ Kafin ta karasa Afaf ta katseta cikin daga murya tana cewa ‘To baki ji me Abban yace ba, kasan ya fi girma ne da space.’ Khadeeja tace ‘To mu dai ba ma son kasa, muna sama abin mu.’ Ta ja hannun Shukra suka haye saman. Habib wanda yake tsaye a kusa da Abban nasu ya dubeshi yace ‘Haba Abba, dama ai sama na Anti Khadija ne.’ Kallon da Abban yayi masa ya sa ya kawar da idonsa da sauri ya waske yana cewa ‘Bari naje na tayasu zabn dakin.’ Haka ya hakura shima ya bisu saman inda khadeeja ta nuna masa dakin da yake jikin nasa tace shi take so, dayan kuma wanda yake gefe daya sai a barwa yara. Bashi da wata hujja da zai bata a kan hanata daukan dakin sama, kuma har yanzu baya jin ya shirya gaya mata cewa zai kara aure, ya fi so sai ta haihu tukunna saboda kada ma yaji tausayinta idan tace zata tayar masa da hankali. Haka suka gama zagayensu a cikin gidan sannan suka shiga mota suka nufi BUK don su kaita. PAGE 130 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Har suka isa makarantar bata daina mamakin Mustapha ba; ta kasa gane sai yaushe zai daina yi mata wannan karyar. Kuma ta kasa gane dalilin da yasa yake fifita bukatar Naja da son zuciyarta a kan tata, amma dai haka zata cigaba da biye masa ta ga gudun ruwansa. ……… Kwanansu biyu da gama jarrabawa Khadeeja ta haifi yaronta, don haka ko kwana bata yi a asibiti ba aka wuce da ita gidanta. Sai daga baya aka kawo mata Anti Binta wadda kanwa ce a wajen Mommy. Tun a asibiti Mustapha ya sanar da su ya sakawa yaro suna Muhammad; sunan Baffan Khadeeja. Daga baya Nabila tayi masa lakabi da Hammad. Nan da nan aka shiga hada-hadar shirya bikin suna; kuma alokacin Mustapha ya sanar da ita idan an yi suna da sati biyu zasu koma sabon gida. Ranar kwana biyu da haihuwa Mustapha ya sameta a dakinta da daddare, tana zaune a gefen gado da baby a cinyarta tana kallosa tana murmushi. Ya ajiye shopping bag din dake hannunsa sannan ya zauna akusa da ita ya shafa kan baby yace ‘Shikenan kuma kin mayar min da yaro abun kallo kamar wata TV ko?’ Tayi ‘yar dariya tace ‘To ina laifi, ina yaba halittar Allah ne.’ Ya matsar da ledar kusa da ita yana cewa ‘Ga wannan ‘yan office dinmu ne suka bayar a kawowa Baby.’ Ta karba ta dan buda ta leka sannan ta mayar ta ajiye tana cewa ‘Mun gode, Allah ya saka da alkhairi. Ai dole Muhammad ya kawo tukuici tunda an yi masa takwara.’ Yayi dariya. ‘Wannan ma ba na Muhammad bane, sauran ma’aikatna ne dai. Shi yace sai gobe zasu zo da matarsa.’ ‘Allah sarki mun gode, Allah ya bar zumunci.’ Suka dan taba hira sannan ya fita. Yana fita ta dauki ledar ta zazzage kayan; rigunan Baby ne masu kyau da tsada guda biyu, sai set din kayan sanyi guda daya, set din huluna da kuma sar din kayan wasa. Ta tabe baki ta mayar da kayan cikin ledar, jikinta ya bata wannan kayan Naja ce ta bayar don haka ko burgeta basu yi ba. Rawar kan da yake yi da ya shigo da kayan kadai ta isa ta sa ta san cewa daga wajen Naja kayan suka fito. Ta tsani yarinyar gaba daya ta tsani ta tuna ta, bata ko son jin sunanta. Haka ta ajiye kayan da niyyar da zarar an gaya mata haihuwa itama zata yi barka da su. PAGE 131 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Lafiya kalau aka gama taron suna; musamman da yake Khadeeja ta kawar da kanta daga abubuwa da yawa. Domin hatta abincin sunan Yaya Jidda cewa tayi ya basu zasu yiwo su zo dashi, shi kuma ya hau kai ya zauna. Tunda taga haka ta gayawa Mommy kada su yiwo gayya da yawa, sannan baffa ya basu kudi suka shirya nasu abincin wanda suka taho da shi. Ko da Yaya Jidda ta gansu da kulolin abincinsu sai ta soke duk wani wulakanci da ta shirya yi musu, haka aka gama taro kowa ya watse lafiya. Bayan kwana biyu tana kwance a dakinta tana hutawa da daddare wayar Mustaphe ta shigo; ta riga ta san yana cikin gidan don haka ta san kiranta yake yi. Haka yake yi tunda Anti Binta tazo; baya shiga dakinta sai dai yayi mata waya ita ta sameshi a dakinsa. Ba tare da bata lokaci ba ta mike ta nufi dakin. Ta karasa ta zauna a gefen guda kusa da shi tace ‘Gani.’ ‘To sannunki da zuwa.’ Ya fada yana bin idonta da kallo yana kokarin karanto yanayinta. Tayi murmushi tace ‘Godiya nake, a bani abinda aka kawo min.’ Suka hada ido na dan lokaci, ya dauke nashi idon ya dan cije lebe sannan yace ‘Ya shirin tashi, saura kwana biyar fa.’ ‘Ai ni na gama shiri, makota ma duk na gama sallama da su. Sai mun tare zan yi musu kwatance su zo ganin gida.’ ‘To da kyau.’ Suka yi shiru na dan lokaci; ita tana sauraronsa don ta kula da magana a bakinsa yayinda shi kuma yake ta sake tauna maganar bakin nasa yana tunanin ta inda zai fara. Ya kalleta suka hada ido yayi gajeran murmushi, itama ta mayar masa da murmushin. Cikin sanyin murya yace ‘Um ki yi hakuri ki saurareni kuma ki fahimci maganar da zan gaya miki.’ Ta kalleshi na dan lokaci da mamaki a fuskarta tace ‘In sha Allah.’ Ya sake gyaran murya sannan yace ‘Um Khadeeja aure zanyi, don maganar da nake miki ma saura sati biyu a daura auren. Idan mun tare a sabon gida da sati daya itama zata tare.’ Suka hada ido, tayi murmushi sosai sannan ta zare hannunta daga nashi tana cewa ‘Allah sarki, abun ya zo kenan. Toh Allah ya sanya alkhairi. PAGE 132 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Bude baki yayi yana kallonta saboda tsabar mamakin yanda ta nuna halin ko in kula da maganr tasa kamar dai wadda yake cewa gobe litinin a ranar lahadi. Ta mike zata fice ya rike hannunta yana cewa ‘Um wani abun kike yi ne kike saurin tashi.’ Ta koma ta zauna tana cewa ‘A’a, na zata ka gama maganar da zaka fada din.’ Ya dan sunkuyar da kai saboda gaba daya ya kasa hada ido da ita, wannan halin ko in kula din da ta nuna yasa duk ya firgice; gaba daya ta goge masa haddar kalaman da ya tsaro don ya bata hakuri. Cikin sanyin murya yace ‘Um baki ma tambayi wacece wadda zan aura ba.’ Ta dan yi dariya tace ‘Oh, Naja ce mana. Ko ka fasa auren nata ne?’ A jigace ya amsa ‘Itace.’ Ta daga gira cikin halin ko in kula tana shirin mikewa tace ‘Allah ya sanya alkhairi.’ ‘Um, wai dama kin san zan yi auren ne ko naga kamar kin sani tun tuni.’ Tayi ‘yar dariya ta koma ta zauna tace ‘Na sani mana, ko bai kamata na sani ba?’ Ya jiijiga kai ‘No, ina dai mamaki ne.’ Suka yi shiru na dan lokaci. ‘To don Allah wa ya gaya miki?’ Muryarsa ta katse mata tunani yana tambaya. Tayi ‘yar dariya tace ‘Oh, ka san fa na dauka kai ka gaya min; ashe ba kai bane. Ina jin dai a cikin wadanda ka gayawa ne kace kada su gaya min aka sami wani ya gaya min.’ Ya sunkuyar da kai domin ya kasa hada ido da ita; wato duk wannan tsawon lokacin ashe kallonshi kawai takeyi duk abinda yake boyewa ta sani. Ba karamin mamaki yayi ba. Kafin yace wani abu suka jiyo kukan Hammad daga cikin gidan, don haka ta dubeshi tace ‘ka ji yarona can yana kuka, bari naje na gani.’ Ta fice ba tare da ta saurari amsarshi ba. PAGE 133 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Tana fitowa daga dakin ustaphan ta tarar da Anti Binta a parlor tana ta jijjiga Hammad, tun kafin ta karasa wajensu tace ‘Yunwa yake ji, zo ki bashi ya sha.’ Ta karbeshi ta shige dakinta Anti Binta tana biye da ita. Haka ta daure ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro har ta gama bashi nono suna hira da Anti Binta. Sai da ya sha ya koshi sannan ta mikawa Anti Binta shi tana cewa ‘Gashi Anti Binta, bandaki nake son shiga.’ Ta karbeshi ta mike tana cewa ‘To muna can dakin yara muna hira da mutuniyata.’ Ta fice ta ja mata kofa sannan ta mike ta shige bandakin don ta san idan dai tana cikin dakin nan wani sai ya zo nemanta, idan kuma ta rufe da mukulli za ayi ta fama tambaya. Tana shiga bandakin ta turo kofar ta jingina a jikin kofar, take hawayen da take rikewa suka kwace kamar an kunna famfo. Ta hada tafukan hannayenta ta rufe fuskarta tana jijjiga kai, saboda tsabar takurar da zuciyarta tayi har wani daci take ji a bakinta. Yaushe Mustapha ya raina ta haka? Wannan ma ya fi karfin raina ya koma wulakanci. To me yasa yayi mata haka? Daman can baya sonta ne ko kuwa son da yake mata ne ya kare? Bata taba tunanin zata auri miji ta zauna ita kadai ba amma dai ta dauka idan ka auri mutum zai cigaba da girmamaka yana ganin mutuncinka har karshen tarayyarku. A halin yanzu ta rasa wanne zatayi; murna ta haihu itama ta sami yaro ko kuwa jaje zata yiwa kanta tunda ko babu komai wannan yaron da ta haifa zai karawa alakarta da Mustapha tsawon rai. Bata san tsawon lokacin da zata iya dauka tana jure wulakanci irin wannan da Mustapha yake mata ba, amma dai ta san tabbas ba zata iya jurewa har abada ba. Gashi shi ba dukanta yake ko zagi ba, wani irin wulakanci ne yake mata yana nuna cewa komai normal ne, kuma a mafi yawancin lokuta ma idan tayi magana sai a dinga nuna mata haka maza suke. Domin kowa ce mata kawai yake idan dai namiji ne bata ga komai ba. Ta barwa Allah al’amarinta kuma zata jira su tare ta ga yanda yanayin zaman zai kama; amma tabbas idan aka cigaba a haka bata jin zata iya zama da Mustapha. PAGE 134 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) zuwa yanzu kuma duk wasu alamu sun nuna mata cewa ba zai taba yi mata adalci ba

Chapter 13 of 25