Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ana kula da su dai ko?’ PAGE 21 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta tambayeshi. 'Ah Alhamdulillah, gaskiya tana kokari.’ Ya fada cike da fara'a. 'To ai haka ake so, Allah ya sa ta dore.’ Tun a bakin gate yayi honk, gaba daya yaran suka fito banda Nasreen. Habib ya tayashi bude gate, bayan ya shigo da motar gaba dayansu suka yi masa sannu da zuwa. A nan suka fara gaida Yaya Jidda, bayan ta amsa tace ‘Ina Nasreena?’ Afaf tace ‘Tana ciki tsifa Anti Khadeeja take mata.’ Suka wuce gaba daya suka shiga gidan; kafin Khadeeja ta amsa sallamarsu Nasreen ta fizge kanta wanda saura daya a gama tsefeshi ta tashi tana share hawaye tace ‘Abbaaa.’ ta fada tana zumbura baki. Da sauri ya rungumeta ‘Ya haka na ganki wujiga-wujiga? Wa ya taba ki?’ Shukra ta tintsire ta dariya ta daga slippers din da aka ajiye tace ‘Kukan tsifa take Abba shine Anti zata zaneta da slippers, kaga nawa Anti yalash din ko kuka ban yi ba har aka tsefe yanzu za mu je saloon smma banda ita. Anti tace tunda bata so a taba kanta askeshi zata yi kamar na Yaya Habib.' 'Sannu da zuwa Yaya.’ Khadija ta fada tana karkade jikinta. 'Yauwa.' ta amsa ba yabo babu fallasa. Ta kare musu kallo tana kokarin zama tana cewa ‘To yanzu Kuma tsifar ce sai an yi zaniya ni ‘ya su?’ Kafin Khadeeja tace wani abu Afaf tace ‘Anti wallahi idan aka biye mata sai an yi sati ana wannan tsifar, kullum haka ake fama da ita.’ Khadeeja tace ‘Ai ba a ma yi zaniyar ba ta bari an tsefe.’ Ta tsuguna ta gaida ita yayinda shi kuma ya ja hannun Nasreen din suka shige ciki. Sai da ta kawowa Yaya Jidda ruwa sannan ta bi shi dakin. Tana shiga ta sameshi a tsaye yana cire kaya yayinda Nasreen take kwance a kan kujerar dakin, kafin tace wani abu yace ‘Wai me yasa ne sai an yi duka sannan za a yi tsifar? naga tun tuni dama ana mata kitson ban taba ji an doketa ba.’ Tace ‘Yanzun ma ba a doketa ba, ko Nasreen? Ta dai ki tsayawa a tsefe ne na takurata na tsefe mata, amma ba ayi duka ba.’ Ya kawar da kai ‘Ni dai bana son dukan yara, don Allah duk abinda yaro yayi kada a dokar min shi. Uwarsu ma bata dukansu, bana bari gaskiya.’ Ta sunkuyar da kai cikin kosawa tace ‘In sha Allah za a kiyaye.’ PAGE 22 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta ajiye masa ruwan da ta kai masa tana cewa ‘Lunch dinka yana nan a table.’ sannan ta fito ta barshi a dakin. Bayan ta dawo parlor din ta tarar Yaya Jidda tana ta yiwa Afaf tambayoyi, ta wucesu ta shige kitchen. Ta tsaya a tsakiyar kitchen din gaba daya kanta ya kulle; daga shigowarsu suna nema suce ta doki Nasreen, to yanzu haka suke so a bar Nasreen din ta dinga yawo da kanta? Gashi Afaf tace makarantarsu ana duba kitso duk ranar Monday. Ta jijjiga kai ta karasa ta dauki saucer ta zuba cake da cin-cin ta debo lemo a fridge ta jera a tray ta kawowa Yaya Jidda da yaranta, bayan ta ajiye a gabanta tace ‘Ya wajen su Hajiya?’ 'Lafiya kalau.’ Ta amsa ba yabo babu fallasa. Sukayi shiru sai surutun Afaf da take ta bawa Naja labari. Shukra ta matso ta kwanta a jikin Khadeeja tace ‘Anti nima lemon.’ Ta shafa kanta ta dubi Afaf tace ‘Yaya ki dauko mata lemon wanda babu sanyi.’ Ta mike, har ta kama hanyar kitchen din Yaya Jidda tace ‘Ku ba zaku sha lemon ba?’ Afaf tace ‘Ai da shi muka je school.’ Shukra tace ‘Anti tace idan an kawowa baki abinci mutum ya daina cewa zai ci, ni ma dai kawai lemon zan sha.’ Khadeeja tace ‘Ki dauko muku lemon idan kuna so.’ Jimawa kadan Abbansu ya fito daga dakin ya wuce dining ya zauna ya fara cin abinci; yana cikin cin abincin ya juyo yace ‘Kai Habib kun ci abinci ne?’ Yace ‘Tun dazu Abba, acici har tayi round 2.’ Ya fada yana zungurar Nasreen. Khadeeja ta mike ta shige daki, don gaba daya jikinta yayi sanyi. Ta kula kiri-kiri neman laifinta ake yi; kamar ma Yaya Jiddan zuwa tayi ta binciketa. Ta karasa ta zauna a kan gadonta ta zuba tagumi. Bayan ya gama cin abincin ya shiga daki ya fito da mukullin motarsa, ya dubi Khadijan yace ‘Idan kun shirya muje na Kai ku saloon din.’ Gaba daya suka fice harda su Yaya Jidda, ya ajiyesu a hanya sannan ya wuce. ……… Tun daga wannan lokacin kuma sai Yaya Jidda ta mayar da shi dabi'a, duk Juma'a sai ta zo gidan. Haka zata zauna a parlor tayi ta kare musu kallo tana kula da duk wani motsinsu, ga tambayoyi wadanda idan ta gama yiwa yaran zata bi Khadeeja da neman karin bayani. ......... PAGE 23 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ranar talata ce Kuma a ranar Khadeeja take sa ran zata koma makaranta, tun dare ta sanarwa Mustapha. Ya amsa mata ba tare da wata matsala ba. Haka ta tashi tun kafin asuba ta shirya yaran tsaf, suna tafiya makaranta tayi Maza tayi wanka sannan ta dan rage aiki don tana da lecture 9am. Bayan sun gama breakfast ta mike daga dining table tana tattara plates din tana cewa ‘Babe bari na saka hijabi na sai kayi dropping dina a school.’ Yace ‘Ok, but kada ki bata lokaci don kada ki makarar da ni.’ Kusan a lokaci guda suka fito daga dakin kowa a shirye, sun kawo tsakiyar parlor ta dubeshi tace ‘Yau Kai zaka dauko yara ko? Don ni Ina da lectures 9am to 4pm.’ Ya dan bata rai cikin nuna damuwa yana cewa ‘I thought Zaki dawo ki daukosu, kin san ni sai 5pm nake tashi daga wajen aiki.’ 'To ai ka ga nima sai 4pm.zan tashi, Kuma I can't miss these lectures don last week ma ka ga ban je ba. Gara dai ka sami wani ya dauko su kawai.’ Ya Bude motar ya zauna yayinda itama ta zauna a kujerar gaba, yace ‘To ai ko an daukosu ma wajen wa za a kawo su tunda ba kya gidan?’ 'Haka ne fa, most days ma lectures dina har 4pm ne.’ Suka yi shiru na dan lokaci; gaba daya ma shi ya manta tana wata makaranta. Yanzu ya take so yayi da yaran? Wa zai daukosu Kuma wa zai zauna da su? Wannan ai shine an gudu ba a tsira ba. Muryarta ce ta katse masa tunani tana cewa ‘Babe ka ga da muna da Mai aiki sai ta daukosu ta shiryasu su tafi islamiyya kafin na dawo; musamman idan Babba ce.’ Cikin jin dadi yace ‘kwarai kuwa, zan yiwa Yaya Jidda magana sai a sami Mai aikin kafin next week.’ 'No, ka bari idan na yiwa Mommy magana zata sa a sami kla garinsu, mutanen suna da Amana sosai ga aiki.’ Ba tare da ya kalleta ba yace ‘Ki bari tukunna idan aka rasa a wajen Yaya Jidda sai a gayawa Mommy din.’ Bata ji dadin wannan maganar ba Kuma ta san da ya kalleta da zai gane sai dai son zuciyarsa me a gabansa; don haka sai kawai tayi shiru. Bata son abinda zai hadata da Yaya Jidda don gaba daya matar ta fice daga ranta, ta kula kamar tana neman laifinta ne ido rufe. PAGE 24 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) A bakin department kawayenta Maryam da Jamila suka tareta, ana ta ihu ana murna ga amaryar Babe. 9am to 11am suka fito daga lecture, wanda zai yi musu 12pm to 2pm ya aiko aka gaya musu ba zai zo ba. Don haka suka wuce hostel dakin su Maryam. Suna shiga Khadeeja ta nemi waje ta kwanta, Jamila ta tabata tace ‘Ke da zaki bamu labarin amarci Kuma sai ki kama wani bacci.’ Ta bige hannunta tana cewa ‘Barni wallahi baccin da yake kaina ya fi na wata guda.’ Maryam tayi dariya tace ‘Barta Jamila, kin san kwanan ibada takeyi.’ Haka sukayi ta hirarrakinsu a kanta tana ta faman bacci. Har suka gama hirarrakinsu tana bacci, don haka basu tasheta ba suka fice sayen abinci. Basu dade da fita ba ta farka, bayan ta wanke fuska ta yi alwala tayi Sallah. Ta zauna a kan dadduma tana tunani; tun ba ayi nisa ba ta gaji da auren Mustapha. To amma tana son shi, matsalarta kawai yaransa kuma da yanda ba zai bari tayi musu tarbiyya ba. Kusan tun da ya kawo mata yaransa bata huta ba, wannan baccin da tayi ji tayi kamar an dauke wani dutse da ta dade tana dakonsa. Ko Ina a jikinta ciwo yake, fatan ta kawai a samo Mai aikin nan ko zata huta. Duk da tana tsoron a kawo Mai aiki daga gidan Yaya Jidda; gani take kamar CCTV camera ce kawai za a kawo mata. Tana zaune tana wannan lissafin wayar Yaya Mama ta shigo; bayan sun gaisa tace ‘Ya na ji ki haka ne amarya? Ko bacci kike yo ne?’ 'Wallahi Ina hostel Yaya, kin ganni gyangyadi na gama.’ 'To ya maganar Mai aikin, tunda dai gaskiya aikin gidan nan ya fi karfinki ga yara hudu.’ 'Ya ce yayarsa zata kawo mai aikin.’ 'To ai shikenan, duk daya ne. Kawai dai idan ta zo sai ki sa ido, kada ki bari ta shisshige miki; ke ko a cikin gidan ki kula kada ki kuskura ki dinga barinta tana shigar Miki daki, kitchen da store ma duk ki kula da motsinta. Yaran ma ki dinga kula da alakarta da su idan ba haka ba sai ta zame muku fitna.’ Yaya Mama ta fada. Cikin sanyin murya tace ‘To Yaya.' Yanda taji muryarta Bai gamsar da ita ba tace ‘Ko da wata matsala ne?’ 'No, ba wani problem. Ni ga ni ma a school na dawo sai yamma zan koma gidan.’ 'Ok, Mommy ma tace min kun je weekend.’ PAGE 25 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) 'Eh.' Suka dan taba hira daga baya sukayi sallama suka ajiye wayar. Khadeeja ta bi wayarta da kallo kawai sai ji tayi tana hawaye; tayi kewar gida sosai, gaba daya a yanzu ma bata san me take so ba, kawai dai ta gaji. Motsin su Maryam ya sa ta share hawayenta ta basar. …….. Kwana biyu da yin maganar kuwa sai ga mai aiki; dattijuwa ce Baba Habit. Yaya Jidda da kanta ta kawo ta. Sai da ta tafi sannan Khadeeja ta nuna mata dakin yara inda a nan zata dinga kwana. Ta nunnuna mata aiyukan kafin yaran su dawo daga islamiyya. Nan da nan ta fara ba tare da nuna wata kyuya ba, ga shi tana da hanzari wajen yin aikin. ______ 'Yan kwanakin nan gaba daya bata jin dadin jikinta, gaba daya bata San me yake damunta ba. Ranar laraba ce, tana jin Mustapha yana tashinta daga bacci kafin asuba yana cewa ‘Ki tashi yara zasu makara fa.’ Ta juyo tana yanutsa fuska tace ‘Babe bana jin dadi wallahi, daga kwancen nan ma ni jiri nake ji ga headache. Bana jin zan iya tashi yau.’ Ya Mika hannu ya taba jikinta yana cewa ‘Subhanallah, me yake damunki?’ 'Nima ban sani ba.’ ta amsa muryarta na rawa. Ya matsa ya leka fuskarta, sai kuma ya sauka daga kan gadon yana cewa ‘Bari na gama da yara sai na kaiki asibiti, amma ki daure ki tashi ki shirya.’ 'To, ka bari gobe ma je asibitin mana.’ 'No, yau zamu je kin ga ana maganar za a saka lockdown saboda COVID 19 idan aka rufe ban san lokacin da za a bude garin ba. Gara muje mu gama komai a siyo Miki magani yanzu haka malaria ce.’ Ya fada sannan ya fice daga dakin. Baba Habi ce ta shirya yaran, duka da kasancewar ita bata iya girki ba haka suka hakura Afaf ta nuna mata ta dafa musu indomie. Bayan sun Sha shayi da burodi ta zuba musu indomie a lunchbox. Duk yanda ya so ga komawa baccin bayan asuba ranar haka ya hakura ya zauna a parlor din yana taya su shiryawa. Bayan ya Kai su makaranta ya dawo ya shirya, ya taimaka Khadeeja itama ta shirya suka wuce asibiti suka bar Habi a gidan. Suna zuwa likita ya tabbatar musu da cewa ciki ne da ita, aka bata magungunan suka taho. PAGE 26 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Kafin su Isa gida sai da ya siyo magungunan, suna dawowa ya mikawa Baba Habi magungunan yayi mata bayani. Ya shiga dakini inda Khadeeja take kwance ya tsaya a kanta yace ‘Ki daure Habi ta hada miki abinci ki ci ki Sha magani, shine zaki ji dadin jikinki. Kin ga wadannan magungunan ita Ma'u idan tana sha ko laulayin kirki bata yi, haka take ci gaba da harkokinta har ta haihu.’ 'Yanzu zan fito ai.’ Yayi mata sallama ya tafi office. Indomie din dai Baba Habi ta dafa mata sannan ta shiga dakin ta taso ta, ta Sha maganin ta dan ci abinci sannan ta koma ta sake kwanciya. Kafin Habi ta dauko yara daga makaranta ta dan ji kwari, zuwa dare rashin kwarin jikin ya ragu don da kanta ta lallaba tayi musu tuwo miyar kuka. ……… Kwana biyu laulayin ya yiwa Khadeeja sauki don tana dagewa tana shirya yara makaranta kuma tana shiga kitchen tayi abinci da taimakon Baba Habi. Ranar laraba suna zaune a parlor da magriba ita da yara da Abbansu; tana zaune a tsakiyarsu tana yi musu homework yayinda shi kuma Abbansu yake zaune a kan kujera yana ta faman danna waya yana kuma kallon labarai a BBC. Baba Habi ta fito daga dakin yara da sallama, bayan Khadeeja ta amsa sallamarta ta tsuguna daga gefe ta dubi Khadeeja tace ‘Uwar dakina ina so zuwa gida gobe, naji ance za a kulle garin. Zan je na dubo yarana idan na kwana daya sai na dawo kafin a rufe garin.’ Abbansu ya dago kansa daga kallon wayar yace ‘Baba ai da kin bari muga abinda hali zai yi tunda kin ga itama Khadeejan bata da lafiya.’ Ta juya Kai ‘To ai Yallabai kafin a kulle garin, na baro yara gara naje na dubo tunda ana maganar idan an rufe garin za ayi watanni kafin a bude.' Kafin yayi magana Khadeeja ta dubeshi tace ‘Ka bari take ai na dan ji sauki, gara taje ta dawo kafin a rufe garin ga azumi ma yana tahowa.’ 'Hakane.' Ya amsa ya cigaba da abinda yake yi. Gari yana wayewa bayan ya dawo daga kai yara makaranta ya bawa Baba Habi kudin mota Khadeeja kuma ta hada mata abinda zata bata ta kama hanya a kan jibi zata dawo. A ranar da daddare aka sanar da total lockdown a Nigeria, an Hana duk wata zirga zirga sai dai kowa ya zauna a gida. PAGE 27 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Da farko Khadeeja tayi tunanin idan ta sami ciki Mustapha zai yi doki kuma ya bata kulawa ta musamman kamar ko wacce amarya, sai dai ga mamakinta hakan baya samuwa. Wani lokacin ma sai ta ga kamar bai san ma tana da ciki ba ko kuma ba da son ransa ta sami cikin ba; halin ko in kula din da yake nuna mata yayi yawa. Tunda aka saka lockdown sai ya zamana kullum suna gida ita da shi da yara, ta so sosai taje gida ta wuni kafin a kulle garin amma bata sami dama ba. Duk da haka kullum sai sun yi waya da Mommy da Yaya Mama; don tun satin da za a fara lockdown su Nabila suka zo mata wuni da suka je gida suka gayawa Mommy ciki ne da ita. Don haka kullum da safe sai ta kirawota ta duba ta. ………. Hayaniyar da su Afaf suke yi a gidan ba kadan bace don haka idan gari ya waye ko gyangyadi bata samu tayi; ko ta fara baccin ma haka za ayi wata hayaniyar a tasheta. Bata gane yanayin da jikinta yake ciki, ita dai kawai ta san tana shan wahala. Kullum jikinta babu kwari gashi bata son cin abinci, gashi kullum cikin jin bacci take. Ga hidimar yara, wadda duk ranar da ta nuna ba zata iya ba haka Mustapha zai yi ta kunci yana kin kulata. Haka take dagewa tayi duk wani abu da ya kamata. —---- Kullum wuni suke kallon TV saboda ana samun wuta sosai, idan dare yayi kuma Abbansu ya tada inji su cigaba da kallo. Ita dai bata isa ta canza channel ba don da ta canza za a fara kuka wanda bata son ji sanna kuma a take ubansu zai fito yayi magana. Ta gaji da zaman haka barkatai don haka ta daure take saka yaran a gaba suyi karatun kur'ani. Da safe a jagwale take tashi don haka ta san ba zata iya da safe ba. Amma kullum bayan sallar azahar idan sun ci abincin rana sai ta kashe TV din kowa ya dauki kur'ani ta biya masa. Nasreen ce kawai bata son zama don haka sai Khadeeja ta kyaleta saboda a halin yanzu na zata iya ba. Amma har Shukra ake biyawa karatun. Duk wani motsinsu idonsa a kai, da zarar ya ji wata hayaniya ko ya ji su shiru zai leko ya duba. Kullum yana kwance yana faman latsa waya. Yau ma haka suka tashi tun asuba suke ta guje-guje, TV kuma dama tana kunne don da zarar wani ya kasheta za a yi korafi. PAGE 28 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Shinkafa da wake ta dafa da manja da yaji; bayan sun gama cin abinci kowa yayi Sallah ta saka su a gaba kowa da kur'aninsa. Sai da suka yi tilawa sannan ta karawa kowa aya biyar amma banda Nasreen. Ba zata iya surutu ba saboda yanayin jikinta da kuma yanda yawu yake yawan taruwa a bakinta, sannan kuma idan ta daga murya tana mata fada Abbansu baya so. Don haka sai ta kyaleta, suna zaune gaba dayansu sun kewaye Khadeeja suna karatu, harda Shukra; amma Nasreen tana zaune a kan kujera ta zuba kayan wasa a gaba tana yiwa ‘yar tsanarta kitso. Shiru yaji sai muryoyinsu kadan-kadan suna karatu don haka ya taso ya fito parlor din. Ya kare musu kallo sannan ya sami waje ya kwanta a kan 3-seater. Ya dubi Khadijan yace ‘Ita Nasreen ba a biya mata karatun?’ 'Tace sai ta gama yiwa ‘yar tsanarta kitso.’ ta bashi amsa ba tare da ta dubeshi ba. Nasreen tace ‘Na ma iya karatun Abba, kitson nan nake so na gama tukunna.’ Yayi dariya ya cigaba da danna wayarsa. Bayan sun gama karatun ta koma daki ta kwanta su kuma suka cigaba da kallonsu na TV. ……… A kwance take a gefen gadon da alawar tomtom a bakinta saboda yawu, ya zauna a kan kujera. Ta juyo ta kalleshi ta koma ta cigaba da kwanciyarta don bata son magana. Jimawa kadan ya kirawo sunanta, ta amsa sannan ta juyo. Ya kalleta yace ‘Wai me yasa bakwa karatun ne da Nasreen?’ Tace ‘Bata so ne, ni kuma ba dadi nake ji ba shi yasa ba zan iya surutu da ita ba kawai na kyale ta.’ ‘Ya kamata idan ma wani abu kika saka a ranki game da Nasreen ki cire, duk abinda zaki yiwa yaran nan kiyi musu gaba daya kuma kiyi musu adalci. Ina kula komai zakiyi sai ki kyale Nasreen, idan banda haka ya za ayi ace Shukra ma da bata shiga islamiyya ba kina biya mata karatun amma ita Nasreen kin yi banza da ita.’ Tunda ya fara zancen ta mike ta zauna akan gadon tana kallonsa, maganganun da take so ta fada masa suna da yawa sai dai tana bude bakinta yawu ya cika bakin. Ta taune ‘yar guntuwar tomtom din ta hadiye da kyar, ta tabe baki ta kawar da kai kawai tace ‘Kayi hakuri za a gyara.’ 'Ya kamata dai ki dinga yi musu adalci don dukansu ‘yayana ne.’ ya fada. PAGE 29 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta zame ta kwanta zuciyarta har turiri take saboda takaici; shi yake hanata takurawa Nasreen, shi yake nuna baya son a dinga yi musu fada amma kuma yanzu yana mata maganar ba a karatu da ita. To ya zata yi da ita? Ita adalci ne wannan yake mata da zai ce ta dinga yiwa ‘yayansa adalci? Ta share kwallar da ta gangaro a idonta tayi kwafa. Jimawa kadan ya tashi ya fice daga dakin. ……… Wannan wunin da kowa yake yi a gida ba karamin takurawa Khadeeja yake yi ba; tana cikin laulayi sannan ga hidimar gida da ta yara. Wuni suke cin abinci don haka gidan kullum kace-kaca ga wanke-wanke baya yankewa. Wasu lokutan tana samu ta danngyara amma wasu lokutan haka take kyalewa saboda ba zata iya ba. Yau kwana biyu kenan dan almajiri da ta dauka yake zuwa yayi mata wanke-wanke da sharar tsakar gida bai zo ba; bata sani ba ko suma lockdown din ya shafe su don da dai suna fitowa tunda makarantarsu nan cikin unguwa take. Gidan gaba daya yayi kaca-kaca don kitchen har warin lalatacce abinci yake yi. Suna gama cin abincin safe Abbansu ya mike ya shige daki. Nan da nan ta saka yaran a gaba suka tayata suka fitar da wanke-wanken suka kai fanfon waje, ta turasu waje ta gyara cikin gidan tsaf. Tana yi tana hutawa tana tofar da yawu, zuwa karfe goma na safe ta gama. Ta fito tsakar gidan ta tara yaran a waje daya, ta dubesu tace ‘Afaf muje fanfo ni da ke mu wanke kwanukan can, kai kuma Yaya Habib dauki tsintsiya ka share compound din nan, ka fara daga kan baranda. Nasreen da ke da Shukra ku tsince toys dinku ku zuba a kwando, duk wadda bata tsince ba ba zan bata sweet ba.’ Nan da nan kowa ya fara aiki. Ta saka kujera a bakin famfo tana wanke kwanukan Afaf tana mata dauraya. Sai da suka cika karamin kwando da kwanukan ta kirawo Habib wanda ya kusa gama sharar tace ‘Ya Habib zo ka dauki wannan kwandon ka kai kitchen ka kwashe kwanukan a kan sink sai ka dawo da kwandon mu cigaba da zubawa.’ Ya dauka a nufi cikin gidan; a kan baranda suka ci karo da Abbansu yana fitowa. Ya dan ja baya don ya bawa Abban hanya ‘Kai ina zaka da kwanuka haka.’ 'Anti ce ta wanke zan kai mata cikin gida.’ PAGE 30 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Yana daga kansa ya hango Afaf a tsakiyar kwanuka suna ta wanke-wanke ita da Khadeejan. A fusace ya karasa wajen, cikin tsawa yace ‘Ke Afaf me kike a nan? kalli yanda kike jika jikinki sai kin gama kiyi ta mura.’ Ya dubi Khadeeja yace ‘Ina yaron naki?’ Ta tofar da yawun bakinta a gefe sannan tace ‘Kwana biyu bai zo ba, nima ban san dalili ba.’ Ya dubi Afaf wadda ta cigaba da aikinta ba tare da ta kula da shi ba, ya daka mata tsawa yace ‘Ki fita daga cikin ruwan nan nace, me kika iya?, sai sanyi ya kama ki kina ta faman jika jiki. Fice kije ki canza kaya kuma kada ki sake fitowa nan.’ Ta dubeshi tace ‘Kwanukan ne da yawa, ni din kuma ba dadi nake ji ba idan muka gama gaba daya zata canza kayan ai.’ Habib ya karaso ya ajiye kwandon yana cewa ‘Anti gashi.’ Ya juya ya cigaba da shararsa. Abbansu ya sake dakawa Afaf tsawa don haka ta fice daga wajen wanke-wanken ta shige gida. Har ya bude baki zai cigaba da magana ya hango Habib yana kwashe shara ‘Kai Habib wa ya saka sharar nan?’ Yace ‘Anti ce Abba, ai na ma gama kwashewa zan yi.’ 'Ajiye tsintsiyar nan ka shige cikin gida ka bani waje.’ ya fada a fusace. Ya jefar da tsintsiyar ya shige gidan. Ya juya kan Khadeejan wadda take cigaba da wanke-wankenta yace ‘Wai me kika mayar da yaran nan ne? Habib ne zai iya share wannan tsakar gidan ga kura ga komai. Itama Afaf din wannan uban ruwan ai sai tayi mura. Ke kika ce a bar mai aikinki ta tafi gida, da kin bari ai da yanzu tana nan; sannan kuma ki dinga basu aikin da ya fi karfinsu? Bana son irin wannan; bana son ki dinga yiwa yaran nan kallon wasu manya, ki dauke su kamar ke kika haifsu shine zaki iya yi musu adalci. Idan an ji wani almajirin yana bara sai a kirawoshi ya karasa wannan aikin ko kuma tunda kun kusan gamawa ki karasa zuwa gobe a sami wani almajirin.’ Ko kallonsa bata yi ba ta cigaba da wanke-wankenta, ya ja tsaki ya juya ya nufi cikin gidan. Ta share hawayenta ta cigaba da wanke-wankenta. Ba zata iya dogon

Chapter 3 of 25