Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yaran a hannunsu su su kai mata; sannan suka dawo wajensa suna ta murna don su sun shirya kayansu tsaf yau zasu tafi wajen Anti Khadija. Hakan yayi masa dadi don dama hakan yaso. Nan da nan suka sheka cikin gida suka fara fitowa da kayansu, Anti Nihla kanwar Ma'u ta taya su duk suka fito da akwatunansu. Mama ta fito ta sameshi, bayan ta zauna tace ‘Ga mutanena nan tunda suka ji uwarsu ta tare sun kasa zaune sun kasa tsaye fa, ni da mukayi da su sai an kwana biyu amma ka ga suna ganinka sun fara fito da kaya. Kayan nasu ma fa wasu suna wajen wanki.’ 'Wallahi kuwa, ai babu komai daga baya sai na zo na karbar musu sauran, kuma ma ai zasu dinga zuwa in Sha Allah.' Ya bata amsa. Haka aka gama fitar da kayan aka zuba masa a mota ya kwashe su suka kama hanya, suna ta murna zasu je wajen Anti Khadija. ……. Tunda ta gama tuwo tayi Sallah sai ta yi wanka ta shirya cikin bum short dinta da wata figalalliyar riga, ta sha turare sai kamshi takeyi ga gidan ma tayi fes da ko ina ta kunna turaren wuta kamshi sai tashi yake a hankali. Tana kwance a kan three-seater tana danna waya ta jiyo motarsa ya bude gate yana shigowa, ta tashi zaune ta dan gyaggyara tana jiran ya shigo ta taro shi daga bakin kofa. Mintuna kadan ta fara jiyo motsinsu a kofar shigowa parlor, ya zura mukullin yana kokarin budewa yana cewa ‘Afaf rike hannun Shukra na bude kofar.’ Ta dan yamutsa fuska tana kokarin ta gane shi da su waye; tas ta jiyo muryarsu gaba daya. Ta dan rikice kadan tana mamakin dalilin da yasa ya taho da su bayan ya amince sai next week. Ta jiyoshi yana zare mukullin daga jikin kofar; ta kalli jikinta yanda take kusan tsirara. Ta yi wuf ta zaga bayan kujera daidai lokacin da yake sako kai cikin parlor din, ta dauki jilbab dinta wanda yake ajiye a saman kujera ta saka. Tana karasa saka jilbab din suka shigo da gudu bayan ya shigo, suka hada baki gaba daya ‘Anti Khadija, Anti Khadija.' Suka karasa da gudu suka rungumeta suna murna. Haka ta yashe baki tana amsa gaisuwarsu, ta dauki Shukra tana cewa ‘Shukra baby, ya Mama? Kin barota tana kuka ko?’ Cikin muryarta ta gwaranci tace ‘Ba kuka take ba, ta ce ma na gaisheki.’ 'Ina amsawa.’ Ta ajiyeta ta kama hannun Habib tace ‘Ya Habib, welcome.’ Ta kalli Mustapha suka hada ido, yayi sauri yace ‘Sun ki barina na taho sai da suka biyo ni, ga kayansu nan sai ku shigar.’ 'Uhm, bari mu gani.’ Ta amsa murya kasa-kasa. Ta dauki babban akwatin nasu ta ja ta nufi dakin yaran tana cewa ‘Afaf dauko wannan jakar mu iai daki.’ Afaf ta kama jakar tana kokarin dagawa Abbansu yace ‘Ke ajiye jakar nan ba zaki iya dauka ba.’ Suna tsaye a dakin a gaban wardrobe tana tambayar Afaf ina jakar Abbansu ya shiga dakin dauke da jakar, yace ‘Ga ta nan, gani nayi ba zata iya daukowa ba na dauko mata.’ Ta yi ‘yar dariya tace ‘Haba dai, Yaya Afaf ai ba raguwa bace, jakar ma da babu nauyi.’ Sukayi dariya gaba daya, ya ja yaran suka fice daga dakin suka barta ita kadai tana kokarin samarwa akwatin kayansu waje. Bayan ta ajiye akwatin a kusa da mudubi ta dan ja baya ta kare wa dakin kallo; komai tsaf yake tunda an share lokacin da ana kafi sai dai ba a shimfida zanin gado ba a kan babban gadon nasu. Bata san a ya suke kwana ba kafin a aurota amma dai tana jin a kan gadon suke kwana duka. Ta fito ta samesu a parlor sun baje suna kallo suna ta yiwa Abbanau surutu. Ta dubesu tace ‘Bari na ciro hijabin nan Afaf sai ki tayani mu gyara dakin.’ Abbansu yace ‘Wannan ce za tayi wani gyaran daki? Babu abinda ta iya fa.’ Tayi ‘yar dariya tace ‘Bari ka gani.’ Ta shige dakinta; tana shiga ta cire hijabin ta jefa kan gado, ta karasa gaban wardrobe ta bude tana duban babban rigar da zata saka. Wani malolo ya tokare mata makogoro saboda takaici; to ta ina zata soma? Haka kawai ya kwaso mata yara a wannan daren. Da ya gaya mata ma ai da tuni ta gyara dakin. Ta ja gajeren tsaki a Fili. Motsin shigowarsa ne ya katse mata tunanin, ya nufota yana cewa ‘Na zata a nan dakinki zasu kwana ai.’ Ta dan goge idonta ta juyo tana cewa ‘No, gara kawai na gyara musu dakinsu tunda babu wata kura da yawa a dakin sai su kwanta a can.’ Ya dan tabe baki ‘Ok, ammma dai za ki dinga zuwa kina dubasu ko?’ 'Eh mana wannan ai dolene.’ Ta amsa tana dan juya jikinta. Ya juya ya fita ba tare da ya ko kalli jikin nata ba. Ta kalle jikinta ta dan murgude baki; yau dai kwalliyarta ta tashi a aikin banza kenan. Ta janyo babbar riga a wardrobe din ta saka, ta sa hula ta rufe gashinta sannan ta fito. Kai tsaye ta wuce kitchen ta dauki tsintsiya da parker, ta fito parlor din ta dubesu tace ‘Taso Afaf, maza mu gyara dakinku ku sami wajen kwanciya.’ Ta wuce ta barsu, a tunaninta yarinyar zata biyo bayanta. Sai dai har ta shiga dakin ta fara kokarin sharewa babu motsin tahowarta, ta dan dakata da sharar da takeyi ta kwala mata kira. A maimakon yarinyar ta amsa sai Abbansu yace ‘Abinci muke ci.’ Ba tare da ta amsa ba ta sunkuya ta cigaba da sharar, har ta dan yi nisa a sharar sai kuma ta tuna cewa yayi abinci suke ci fa; to wanne abincin? Tuwon da ta tuka da shinkafa gwangwani 1 da Rabi din ya tasa yaransa a gaba suke cinyewa? Bayan ta gaya masa zata jirashi ya dawo su ci abincin dare tare? Tuwon ma da gaba dayansa malmala uku ne ta tuka saboda ta san miyar ba zata isa su ci dumame ba. Har ta ajiye sharar ta nufo parlor din sai kuma ta tuna idan ta zo me zata yi a kai, don haka sai kawai ta cigaba da sharar ta tana fatan Allah ya sa su rage mata tuwon. Ta share dakin ta karkade ko ina sannan ta shimfida zanen gadon da ta dauko daga dakinta. Ta kalli dakin taga ko ina yayi tsaf, sannan ta dauko sharar da ta kwashe ta fito. Suna zaune a kan dining table suna ta cin tuwo shi da ‘yayansa, kafin tayi magana Abbansu ya dubeta yace ‘Yauwa dan karo mana tuwon nan Habib bai koshi ba, ga Shukra ma kamar zata kara.’ Ta dan zaro ido tace ‘Wai kun ciye na flask din?’ 'To nawa yake, ai bashi da yawa.’ Kafin ta bada amsa Nasreen tace ‘Kuma miyar tayi dadi Anti.' Ta yi murmushin yake tace ‘Shikenan dama na dafa, ko nima ban ci ba.’ Habib yace ‘Abba nifa ban koshi ba, dama bamu ci abincin dare ba lokacin da muka taho gashi mun manta bamu karbo kazar mu ba a wajen Mama.’ Abbansu ya dubeta yace ‘Yanzu ya zakiyi da Habib? Yunwa yake ji.’ ‘Akwai ragowar bread sai mu raba ni da shi mu sha da tea, don gaskiya yanzu ba zan so dora tukunya ba.’ ba tare da ta saurari amsarsu ba ta wuce kitchen da sharar a hannunta. So take ta sami waje tayi kuka ko taji sanyi a ranta, don haka ba tare da ta kalli wajen ba ta jefa sharar ta juya sink ta fara wanke hannunta. Abbansu ta jiyo a bayanta yace ‘Khadeeja, daurewa fa zakiyi ki dafawa Habib Indomie don shi baya cin bread kuma kinga ai ba ya kwana da yunwa ba.’ Ta kalleshi suka hada ido tace ‘Babe na gaji ne wallahi, nima ina son tuwon amma na hakura zan ci bread.’ Ta dan saurara tana kallon yanda yake kara hade rai, sai kuma cinkin sanyin murya tace ‘Amma Afaf ta zo na kunna mata cooker ta dafa musu Indomie din.’ Ya kalleta shekeke yace ‘Wai ke me kika dauki Afaf ne she's only eleven babu abinda ta iya na aikin gida. Idan ta girma dai ta koya but ki daure kawai ki dafa masa.’ Ta juya ta bashi baya saboda hawaye ne yake Shirin kwace mata, ya juya ya fice ya bar mata kitchen din. Ta share hawayenta ta sauko da tukunya karama ta zuba Indomie din da ruwa da komai ta kunna wuta ta dora. Ta koma ta jingina da sink ta tsaya ta kafa tagumi; yanzu shikenan har ta gama amarcin, ko awa biyu yaran nan basu yi da zuwa ba amma sun gundireta, anya kuwa zata iya wannan rayuwar. Ko da yake dai yanzu suka zo ta san basu fahimceta ba itama kuma bata fahimcesu ba; amma dai zata dorasu a saiti kwanan nan. Tana cikin juye Indomie din suka shigo kitchen din suka wanke hannuwansu, sai dai abinda ya bata mamaki babu wanda ya dauko plate din da yaci abincin ya kawo kitchen din; duk a dining table din suka baro mata. Ta gama juye Indomie din ta mikawa Habib bayan ya gama wanke hannu. haka ta fito ta kwashe kwanukan daga dining su kuma suna zaune suna kallon TV. Ta hado shayi ta dauki guntun bread dinta ta wuce daki. Bayan ta gama shan shayin ta dauko kofin ta fito, tana isa gaban sink din zata ajiye kofin ta ga Indomie din da ta dafawa Habib ko rabi bai ci ba kuma ga dukkan alamu ya koshi kenan. 'mtsewww' ta ja tsaki a Fili. Ta wanke hannunta ta fito daga kitchen din. Har zata wuce daki Abbansu yace ‘Kizo ki shiryasu sun fara jin bacci kinga 10 har ta gota.’ Ta juyo ta dawo, ta dauki Shukra wadda ta riga ta fara gyangyadi Afaf, Habib da Nasreen suka bi bayanta. Sune suka nuna mata kayan baccinsu ta taimaka musu duk suka yi brush sannan suka shirya, ‘yan matan gaba daya suka haye gadon. Ta kalli gadon taga ma ba zai ishesu ba don haka ta koma dakinta ta dauko katifar da aka kawo mata saboda baki ta shimfidawa Habib a kasa. Ta gama tsaf zata kashe musu fitula Nasreen yace ‘Anti ba a kashe mana fitila sai mun yi barci.’ Ta mayar da fitilar ta kunna musu sannan ta fice daga dakin, ta wuce Abbansu a parlor ta shige dakinta. Ta riga ta gaji sosai don haka itama kayan bacci kawai ta saka ta rufe dakin nata ta wuce dakinsa, ta kwanta ta rufe idonta. …….. Lokacin da Khadeeja ta fito daga dakinsa ya zata dakinsu Afaf zata koma don su kwana tare, amma sai ya ga ta shige dakinsa. Ya tashi ya shiga dakin yaran inda ya tarar dukansu sunyi bacci, don haka ya kashe musu fitilar ya fito daga dakin. Ya kashe fitilun falon ya shige daki. Tana kwance a kan gado kamar ma bacci takeyi, don haka ya kyaleta. Bayan ya gama shirinsa ya kwanta, ya mika hannu ya tabata, ta juyo ta bude ido tace ‘Babe, ka shigo?’ 'Um.' Ya amsa a gajarce. Ta fara kokarin matsowa jikinsa, ya tashi zaune yana cewa ‘Kin baro yara su kadai, kin ga daga nan ma ai ba lallai ki jiyo motsinsu ba. Ni da na zata ma tare zaki kwana da Shukra a dakinki fa, she's just 3 bata saba kwana ita kadai ba.’ Ta dan matsa ta koma inda ta baro tana cewa ‘No, they will be fine fa, ba kaga a tsakiyar yayunta na sata ba kuma duk fa sun yi bacci. Ka ga na ma saka alarm wajen biyun dare zan je na dubasu sai kuma da asuba.’ 'Uhm, amma dai da kin daure kin kwana da su din.’ 'Kada ka damu ina jinsu.’ Ta fada sannan ta gyara kwanciyarta ta juya masa baya ta rufe ido. Haka kawai zai ce taje ta kwana a cikin yara; to ai ko ‘yar da ta haifa ce shekara uku ai raba wajen kwana zasu yi. Ba zama ta fara wannan aikin ba balle ya sallamawa yaran ita. Har barci ya fara daukanta suka ji an murda kofar, ya riga ya murda mukullin da ya shiga don haka sai kofar bata bude ba. Aka kwankwasa a hankali, suka tashi zaune tare shi da Khadeejan. Kafin suce wani abu Nasreen tace ‘Abba Shukra ce ta tashi zata sha shayi.’ Ya kalli Khadeeja yace ‘Oh, na manta ban gaya miki ba tana farkawa shan tea da daddare, tunda aka yaye ta ta saba. Kije ki hada mata shayi, da ga ta sha zata koma bacci.’ 'Shayi? A wannan daren? Ko fa 4 hours basu yi ba da cin tuwo, ikon Allah.' ‘Idan baki bata ba haka zata yi ta yiwa mutane kuka har sai an bata, kije ki hado mata gobe sai ki hada ki sa a flask kafin ta kwanta.’ Ya fada yana sake bata rai. Ta daura zaninta a kirji ta sauka daga kan gadon ta fice daga dakin cike da takaici. A tsakiyar gadon ta sami Shukra tana kuka, duk yanda zuciyarta ta kai ga kuna a wannan lokacin dole ta danne fushinta. Ta mika mata hannu tana dan murmushi tana cewa ‘Ahh! Sorry Shukra, ya aka yi? Kukan me kike yi?’ Cikin shesshekar kuka da gwarancinta tace ‘Tea.’ Ta zauna a gefen gadon ta rungumeta tana shafa bayanta tana mata magana cikin lallashi ‘Ya Isa, ya isa. Da safe ke zan fara hadawa shayi kinji Baby Shukra, kinga dare yayi ko? Muyi bacci da safe sai mu sha tea ko, harda bread ma da kwai ko?’ Ta gyada kai alamar eh, amma fa hawayenta ya ki daina zuba harda shesshekar. Ta cigaba da shafa bayana tana lallabata yayinda Nasreen ta koma ta kwanta har bacci ya fara daukanta. Abbansu ya ya turo kofa ya shigo dakin, Shukra ta leko ta kafaradar Khadija cikin shessheka tace ‘Abba tea zan sha.’ Ta kwace daga jikin Khadijan ta sauko ta taho wajensa, ya rage tsawo ya dauketa ya rungumeta yana cewa ‘Ya isa, Anti bata baki shayin ba?’ 'Tace sai da safe.’ ta fada tana shessheka. Ta mike ta rungume hannuwanta a kirjinta ta kalleshi da fuskar tausayi tace ‘Babe, ka barni da ita zata koma bacci kuma a hankali zaka ga ta ma daina farkawan shan shayi da daddaren. Ka barni na lallabata idan tayi bacci zan taho.’ Kallonta yake da mamaki a fuskarsa, sai da ta gama sannan yace ‘Yunwa fa take ji, haka zata kwana da yunwa. She's only 3, idan ta girma da kanta zata daina duk yayyenta ma haka barsu take raininsu.’ Cikin kosawa tace ‘Kai dai ka barni da ita mana, I promise you she will be just fine.’ Ta karaso kusa da shi, ta mika hannu ya dafa kafadarta yana cewa ‘Kin ga, ki yi hakuri ki hado mata shayi kada ki sakata kwana da yunwa tunda bata saba ba. A hankali zaki ga da kanta zata daina.’ Murya kasa-kasa tace ‘Ohkk!’ Ta wuce ta barshi a nan ta nufi kitchen; tea at 1pm, wannan wane irin tashin hankali ne? Idan da ya kyalesu ta san tabbas zata rabata da wannan shan tea din amma har wani cewa yakeyi kada ta barta da yunwa. Ta karasa kitchen din ta hado mata tea a kofi ta daukonta fito. Tana zuwa ta sameshi zaune a gefen gadon ragowar yaran duk suna ta baccinsu yayin da yake zaune rungume da Shukra; har bacci ya fara dibanta amma tana shiga ya dagata yace ‘Yauwa Baby tashi ga shayinki.’ Ta tashi tana muttsike ido, ya mike tsaye ya nunawa Khadijan wajen ta yana cewa ‘Zauna sai na ajiye miki ita idan kin gama bata tayi bacci kya taho.’ Ya ajiye mata ita a kan cinyarta ta fara bata shayin sannan ya fice ya barsu. Bayan ta gama bata shayin ta sakata tayi fitsari sannan ta kwantar da ita ta dan jijjigata bacci ya fara kwasarta sannan ta wuce dakin. Ko da ta shiga dakin ya riga yayi bacci, don haka ba tare da ta kunna fitila ba ta lalubi waje ta kwanta a gefen gadon. Motsin kwanciyarta ne ya farkar da shi, ya dan matso ya rungumota ta baya yana sumbatar bayan wuyanta. Ta dan motsa tace ‘Mmmm!’ Yace ‘Kin San gobe yara zasu school ko? Sai ki tashi da wuri don ki shirya su.’ A take jikinta yayi sanyi; gaba daya ma ta manta da wannan tunda ita ta riga ta sanar da kawarta su yi mata attendance ba zata koma ba sai tayi sati. Ya cigaba da lalubenta tana kokarin zamewa, saboda ita gaba daya ma komai ya fita daga ranta; a halin yanzu ma kuka take son yi. Sai dai haka ta hakura ta barshi yayi yanda ya so sannan ta kwanta tana fargabar yanda zata tashi nan da awowi kadan ta cigaba da hidima. Ana fara kiran assalatu ya tasheta daga bacci, sai da tayi da gaske sannan ta iya saukowa daga kan gadon. Tayi alwala ta wuce kitchen tunda da dan sauran lokaci kafin a tada Sallah. Ta tsaya a tsakiyar kitchen din tana tunanin inda zata fara; a hankali dabara ta fado mata; macaroni da sauce zata dafa musu in ya so sai ta dafa indomie da kwai suyi breakfast. Nan da nan ta dora sannan ta debo tsofaffin flasks dinsu da ta gani a store ta wanke sannan taje tayi Sallah. Ta zata idan ya dawo daga masallaci zai tsaya ya tayata shiryasu amma ga mamakinta sai ya wucesu a parlor ya koma daki ya kwanta ya cigaba da baccinsa. 7:15 am ta gama komai duk ta yi musu wanka sun shirya, suka zauna a dining table ta kawo musu abinci ta zubawa kowa Indomie da dafaffen kwai guda daya. Daga fuskokinsu ta san ba indomie suka so ci ba, suna cikin cin abincin yayinda ita kuma take zaune a table din tana bawa Shukra a baki Nasreen ta kalleta tace ‘Anti da ma dankali da kwai kika soya mana.’ Ta kalleta tana murmushi tace ‘Saboda kar ku makara shi yasa nayi sauri na dafa Indomie, but in sha Allah weekend idan babu makaranta sai a soya muku dankali kin ji. Yanzu maza ki cinye kafin Abba ya fito ya kai ku school.’ Suka cigaba da cin abincinsu. Jimawa kadan Abbansu ya fito yana rike da mukullin mota, suka hada baki gaba daya suka gaisheshi. Bayan ya amsa yace ‘Maza ku gama mu wuce a school kada ku makara.’ Ya kula da ragowar kwai a plate din kowa banda Habib, ya dubeshi yace ‘Kai ina naka kwan.' Yace ‘Shi na fara cinyewa Abba.' Nasreen tace ‘Abba ni ina son dankali, Anti tace ba za a dinga soya dankali ba sai weekend.’ Ta langabe kai kamar abun tausayi. Ba tare da ya kalli Khadeejan ba yace ‘No, za a dinga soyawa kada ki damu, maza ki ci abinci mu tafi.’ Tana jinsu ta kawar da kanta, don sai dai idan shi zai dinga tashi ya soya ita bazata iya soya dankali da sassafe ba. Nan da nan suka gama; Habib ne ya fara mikewa har ya juya tace ‘Dauke plate dinka da cup din ka kai kitchen.’ Ya dauke plate din ya tafi da shi, suma ‘yan uwan da suka ga haka kowa idan ta mike sai ta dauke plate dinta ta wuce da shi. Suma ‘yan uwan da suka ga haka kowa idan ta mike sai ta dauke plate dinta ta wuce da shi. Suka karasa shiryawa suka fice tare da Abbansu. Kafin ya dawo ta soya dankali da kwai ta jera a dining table sannan ta wuce daki; wanka zata shiga sai kuma ta tuna ko da ta yi wankan dai kitchen zata shiga tayi wanke-wanke ga shara, don haka taga gara ta bari idan ta gama aikin ta yi wankan. Sai da yayi wanka ya shirya sannan ya fito a shirye, kai tsaye ta riga ta shirya abincin a dining table don haka suka zauna. Yana bude kwanon yace ‘Sai da suka tafi kuma kika soya dankali? Sun fi son soyayyen abinci idan zasu tafi school.’ Ta dan langabe kai ‘To ai Babe ba zan iya soya wani abu before 7am ba, da ace ma dai ina da mai aiki ne. Amma hakan ma weekend zan soya musu in sha Allah.’ ‘To ai da kin bari sai weekend din ma ci gaba daya, yanzu idan sun dawo ai zasu ga bawon ba dadi ai kuma ma Shukra zata gaya musu tunda ita taci. Mai aikin ma kuma za a dauka.’ 'Uhm.' Suka cigaba da cin abincin ba tare da kowa ya ce komai ba. Gaba daya ma abincin sai ya fice daga ranta; kenan duk abinda ba zata bawa yaransa ba baya so ita ta ci. Haka tunani kala-kala suka yi ta yawo a kanta. Ya gama cin abincin ya fice ya barsu ita da Shukra. Sai wajen 10am ya kirawota a waya, bayan ta dauka yace ‘Mantawa nayi ban gaya miki ba idan 1pm tayi sai ki je ki dauko yara daga school.’ Ta dan yi shiru don ta zata shi zai daukosu, tace ‘Ohk, but zan iya zuwa a kasa?’ 'No, kin san school din ai ba nisa sosai amma dai ku hau a dai-daita sahu sai ki tafi da Shukra.’ 'Ok.' Suna gama wayar ta mike ta dora abincin rana don ta gama da wuri. Lokaci yana yi ta dauki Shukra suka tafi suka dauko yan makarantar. Suna dawowa bayan sun huta ta shiryasu suka tafi islamiyya. Dab da magriba ya dawo. Bayan ya huta yana zaune a parlor shi da yaran tana jiyoshi yana tambayar Afaf abinda aka yi da baya nan, an dauko su da wuri daga school? Sun ci abincin rana? Me suka ci? Sun makara a islamiyya? Haka dai ya cigaba da tambayoyinsa tana kitchen tana jiyosu, kamar ta fito tayi magana sai kuma ta share ta cigaba da abinda takeyi. PAGE 20 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) A haka suka karasa satin nan tana bakin kokarinta wajen kula da yaran nan gaba dayansu. Ranar Juma'a suna gida da yake yara babu islamiyya; ranar ne kuma suke gyara gashin yaran mai kitso zata zo. Tun da wuri Afafa ta tsefe nata kan, ita kuma Shukra da yake tun suna makaranta Khadeejan ta tsefe mata babu wanda ya ji kansu. Tun da suka gama cin abincin rana take faman lallaba Nasreen ta bari a tsefe mata amma har aka kusa kiran la'asar guda biyu suka tsefe. Bata son a taba gashinta kwata-kwata don haka taki ma zama a tsefe. Khadeeja ta kamo hannunta tace ‘Zo kin ji Nas, kin ga fa Shukra zata fi ki kwalliya tunda ta tsaya an gyara mata nata.’ Ta zauna, har an fara tsifar ta zame kanta ta matsa tana zumbura baki. Afaf tace ‘Anti wallahi idan baki zare mata ido ba haka za kiyi ta fama da ita, sai ayi sati ana tsefe kanta a gidan Mama.' Ta cigaba da lallabata amma sam ta ki tsayawa; don haka ta kama hannunta ta zaunar da ita tana cewa ‘Idan kika sake tashi sai na zaneki Nasreen, ko na sa almakashi na aske gashin kan ya koma kamar na Yaya Habib.' Ta dubi Afaf tace ‘Yaya Afaf dauko min slippers mai zafi idan bata tsaya an tsefe ba zaneta zan yi.’ Da sauri Afaf ta dauki slippers ta zo ta ajiye a gaba Nasreeen wadda ta fara shesshekar kuka tana fizge-fizge. Khadeeja ta dan rike gashin tace zan dake ki fa Nasreen, ki rufe min baki bana son jin kukanki.’ Nan da nan ta hadiye kukanta tana shessheka aka cigaba da tsifa Shukra tana mata dariya. ………. Daga masallacin Juma'a ya wuce gida don ya gaida Hajia, da ya gaisheta sai ya wuce gida don Khadeeja tace idan ya dawo zai kaisu saloon ita da yara a wanke musu kai da yamma kuma akwai mai kitso a makota dama ita take musu. Yana shiga gidan ya sami Yaya Jidda da yaranta biyu ‘yan mata Naja da Farida, bayan sun gaisa gaba daya Yaya Jidda ta dubeshi tace ‘Gidanka fa zamu tafi yanzu ni da yara, Hajia tace muje mu dubo su Afaf.' Yace ‘To ai sai ku tsaya mu tafi, don nima gaisawa kawai zamu yi na wuce.’ Kafin minti goma sun gama, suka shiga mota ya ja su suka kama hanya, suna tafe suna hira. 'To ya yaran?

Chapter 2 of 25