Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sanye da uniform dinsu; don saida suka fara shirin makaranta sannan Naja ta sauko ta sanar da su ba zasu makaranta ba Habib ya bata Abbansu kuma ya tafi nemansa. Babu wanda ya ji shigowarsu gidan saboda Mustapha a waje ya ajiye motarsa saboda Hajia tace yanzu zata fito ya mayar da ita. Da sallama suka shiga parlor di, Nasreen ce da Shukra suna zaune a parlor din da flask din shayi a gabansu da katon bread. Sai dai sun kasa shan sahyin sun yi tsuru-tsuru. Da gudu suka mike, Shukra ta fada jikin Habib tana dariya yayinda Nasreen ta matsa kusa da Hajia. Suka karasa ciki suka zauna. Hajia tace ‘Ina Afaf?’ Nasreen tace ‘Tana dakinmu.’ ‘Antin fa da Rukayya?’ Nasreen ce ta sake sunkuyar da kai tace ‘Basu sauko ba.’ Hajia tace ‘To kije ki kirawo min ita kice ta zo.’ Shukra tace ‘Yanzu fa ta leko kuma tace kada wanda ya hau mata sama ya dameta, ko menene a jira sai ta sauko.’ Hajia ta jijjiga kai, ta kalli Mustapha. Ya dan diririce sannan yace ‘Hajia tasowa zakiyi muje saman ai.’ Ba tare da wani musu ba ta mike ta tasa Nasreen da Shukra a gaba tana biye da su yayinda Mustapha da Habib suke biye da ita. Anti Wiyya ce a zaune a kan kafet da kwanuka a gabanta suna cin abinci ita da Rukayya yayinda Naja take zaune a kan kujera tana cin nata abincin suna hira. Da yake kicin a buda yake ana hango mai aikinta da goyon baby tana goge-goge. Shukra ce ta fara shiga tana surutu don haka a fusace Anti Wiyya tace ‘To sarkin tsurku, ba cewa aka yi ku zauna a kasan ba shine kika shigo kina….’ A lokaci guda kuma Naja tace ‘Ai sai nayi maganin wannan yar…’ Sallamar Hajia ce ta katse musu zantukan, ta karsa ciki yayinda Shukra ta zagaye ta koma bayan Abbanta. Suka karasa ciki suka zauna yayinda Naja da Wiyya suka diririce. Naja tayi wuf ta mike ta kwashi kwanukanta tana cewa ‘Bari na wanko hannu.’ Ta nufi kicin cikin sauri. Itama Wiyya ta kwashi nata kwanukan ta mike tana cewa ‘Sannu da zuwa Hajia, bari na kawo miki abinci.’ PAGE 230 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Rukayya tace ‘Anti ban koshi da naman ba.’ Bata ko saurareta ba ta wuce kichin yayinda ita kuma ta tashi ta bi bayanta da sauri. Sai dai duk saurinsu kowa ya riga ya ga abinda yake cikin kwanukan nasu; farfesun kaji ne wanda suke hadawa da burodi da shayi suna ci. Bayan sun zauna Hajia ta dubi Mustapha sannan ta dubi Nasreen tace ‘Nas ku ina naku naman naga kuna cin gayan burodin.’ Tayi darya tace ‘Ba a bamu ba, dama kullum abincin sama da ban da na kasa har garama idan Abban yana nan.’ Hajia ta sake kalloshi tace ‘Allah ya sauwake.’ Naja ce ta dawo parlor din ta zauna a kan kafet ta gaida Hajia, bayan ta amsa ta dubi Nasreen tace ‘Jeki kicin ki taya Anti Wiyya ta daukowa su Hajia abinci.’ Hajia ta daga hannu tace ‘Ki ce ta barshi, ku barshi ma, abincin da naga bai isa an raba da yara ba ai ba zai isa har a bawa bako ba. Ni na ci abincina ku barshi na koshi.’ ‘A’a Hajia ai akwai, suma hawowa ne basu yi ba nake jira Jummai ta gama wanke-wanke ta mika musu.’ ‘To me zasu shigo suyi, su da zaki yi maganinsu. Ai sai dai kawai a cigaba da addua kada a wayi gari kin korosu daga gidan kamar yanda kika koro dan uwansu cikin dare.’ Hajia ta bata amsa. ‘Wallahi Hajia babu wanda ya koroshi.’ ‘Allah ne kawai zai gane gaskiya, amma dai ke kiji tsoron Allah. Kin bani kunya, wallahi kin bani kunya! Ban taba zaton haka daga gareki ba. Gaba daya mun zata zuwanki gidan nan zai sa yaran nan su sami kulawa ta musamman ashe ba haka bane. Ke da uwarki da ‘yayanki kuna sama kuna cin kaji yaran suna kasa suna fama da burodi. Kuma ma har sharadi aka kafa musu cewa kada su hawo su dameki. Kamar dai ba gidan ubansu ba.’ Suka yi shiru kamar ruwa ya cinyesu. Hajia ce ta karya shirun ta dubi Mustapha tace ‘Kai dai baka kyauta ba, yanzu rayuwar da kuke yi kenan? Su wadannan da uwarsu ta mutu kun barsu a kasa kuna sama kuna jin dadi. To kaji tsoron Allah. Kema kuma ki ji tsoron Allah. Bana jin sun taba ganin haka a wajen Khadeeja, ashe dama jira kike ku koreta daga gidan ki cuzgunawa marayun Allah.’ PAGE 231 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta sunkuyar da kai kamar wadda zata dungura. Habib yace ‘Ai tunda suka dawo daga Saudiyya aka hanasu hawowa na, dakinsu ma da koamai nasu ya koma kasa.’ Hajia ta dubi Mustapha duba na takaici har sai da ya sunkuyar da kansa cike da kunya. Ta mike tana cewa ‘Ai shikenan, amma tabbas ba zan bar wannan zaluncin ba. Kuma ko da kin ga kamar kin yi nasara to Allah yana kallonku gaba daya.’ Yaran suma suka mike, Hajia ta dubi Mustapha wanda kunya ta hanashi mikewa tace ‘Za ka samu ka mayar da ni gida ko sai ta baka izini.’ Ya mike kamar wanda aka tsikara. Naja tace ‘Don Allah Hajia kiyi hakuri. Wallahi ba haka abubuwan suke ba rashin fahimta kawai aka samu wallahi ana kula da su.’ Ta dubeta tace ‘Allah ya sa, ai nima haka nake so. Sai dai kowa yayidon Allah ai ya sani ko, Allah kuma yana sane.’ Ta wuce yaran da Mustapha suka bi ta a baya suka fice. Har suka isa gida tana faman caccakar Mustapha a kan yanayin da ta gani a gidansa kuma tana tuna masa girman hakkin yaran nan a wuyansa da shi da matarsa. Bashi da binda zai gaya mata sai hakuri kawai yake bata; shima baya jin dadin yanda gidan ya koma tun bayan rabuwarsa da Khadeeja. Ba da son ranshi ba ta mayar da yara kasa kuma wannan raba abincin ya sha yin magana a kai. Amma ta iya abun ganin ido ne kawai, idan yana nan sai tayi kamar komai normal amma da zarar ya fita sai ta tsawatarwa yaran kowa ya shiga hankalinsa. Abinci kuwa dama idan dai ba a gidan zai ci ba tabbas abincin da ake dafawa a sama da ban kuma abincin da take bawa mai aiki ta dafawa yaran da ban ne. Duk wani dadi a sama suke ci ita da yaranta da ‘yan uwanta su kansu yaran har sun saba. Gashi ta hanasu kula ubansu sosai, domin in dai yana saman nan bata barinsu su ganshi. Har sun gaji da yanda take musu sun hakura sun ma daina cewa suna son magana da shi. Haka ya karasa gidan ya ajiye Hajia a bakin gate ya dawo saboda baya son ya shiga ciki saboda ya san ba zai ji da dadi ba a wajen Alhaji. PAGE 232 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Suna fita Anti Wiyya ta fito daga kitchen jiki a sanyaye, ta zauna kusa da Naja ta kama haba tana cewa ‘Ikon Allah, kin ji mutane ko? Ko motsin shigowarsu bamu ji ba sai kace shiri.’ Ta tabe baki ‘Hmmn! Su suka sani. Dama tafiya yayi ya kai rahoto shi yasa ya bi dare su kuma basu yi tunanin su kirawo mutane su sanar cewa ya isa can ba saboda sun shirya tsiya. A kansu zata kare in sha Allahu.’ Ta mike kamar an tsikareta tana cewa ‘Bari ki gani na hada kayana na bar gidan nan kafin ya dawo ya koreni da kansa.’ ‘Haba Anti, saura sati biyu dama fa ki tafi tunda kin ce ba zaki yi mim arba’in ba. Kiyi zamanki babu abinda zai yi.’ Ta fada tana gyara zama. ‘Wallahi tafiya zan yi, da wanne idon zan kalleshi ya riga ya gama rainani. Ina nan ina yagar kaza na bar masa yara suna fama da gayan burodi.’ Ta marairaice ‘Anti idan kika tafi ma in ya dawo ai sai yace bani da gaskiya.’ Ta nufo kasa don hada kayanta tana cewa ‘Ku kwashe kalau amma ni da mijinki ba zamu sake haduwa ba in sha Allahu, ko a kwararo balle ma a gidansa.’ Tana ji tana gani Anti Wiyya ta fice ta bar mata gidan. Bata dade da fita ba Mustapha ya dawo. Yana shiga parlor din kasa ya tara da Afaf ta fito tana shan bakin shayi da burodi yayinda sauran yaran suke zaune suna kallon TV. Bayan ya amsa sannu da zuwansu ya karasa ya zauna a kusa da Shukra, ya kalli kofin shayin Afaf wanda ta ajiye a kusa da ita tana kokarin sake yago burodi. Yace ‘Ya kike shan bakin shayi Yaya?’ Tace ‘Um, babu madara a nan dama idan nayi canjin kudin makaranta ne nake siyo mana kuma yanzu ka ga ina hutu shi yasa bani da kudi.’ Takaici ya cikashi, yanzu da ransa da lafiyarsa madarar shayi ace sai Afaf ta tara kudin makarantar da yake bata ta siya sannan zasu sha. To wai ina kansa ya shiga hakan take faruwa a gidansa? Tunda yake a rayuwarsa bai taba ganin Khadeeja ta hana yaranshi wani abu da ya siyo ba, sai dai ma ya san lokutan da take sayen abu da kudinta su ci ita da yaran. To wai yaushe ma Khadeeja ta bar gidan? PAGE 233 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ba a fi wata takwas ba fa da rabuwarsa da Khadeeja amma gidan duk ya zama haka? Ita da take zama cin abinci a tsakiyar yaran balle a ce ta boye wani abu ta hana su. Ya bi fuskar yaran da kallo gaba dayansu babu wadda take da cikakkiyar walwala, tabbas yanzu ne zasu ji nauyin maraicinsu. Shi kanshi sai ya ji kwalla tana neman kwace masa, sai da yayi da gaske sannan ya mayar da kwallar. Ya dubi Nasreen yace ‘Nas dauko min kofi nima na sha shayin.’ Ta tashi ta shiga nan kichin din kasan ta dauko masa tsohon kofin tangaran ta kawo masa da sugar a ‘yar roba. Ya kalli kofin duk ya dafe ya dubi Nasreen din da ta ajiye kofin yace ‘Kije sama ki dauko min wani kofin mai kyau.’ Tace ‘Abba Anti Naja fa tace kada mu hau kuma wallahi idan na hau zagina zata yi in nayi magana tace na mata rashin kunya, sai dai ko yaya Afaf taje ta dauko.’ Haka ya karbi kofin ba don ya so ba ya hada bankin shayi ya sha tare da ragowar burodin da suke ci. Sai da ya gama sannan ya tashi ya haye sama domin ya shiryo ya fita aiki. …….. Ta ji dawowarsa tunda ya shigo da motarsa, sai dai da ta ji shiru ta saka rai ya tsaya a wajen yaransa don ya kara jin abubuwan da zasu gaya masa a game da ita. Don haka a parlor ya sameta tana ta cika tana batsewa ita a dole kada yayi mata fada. A gajiye yake sannan bashi da karsashin hayaniya da ita, don haka ko inda take bai kalla ba ya shige daki ya fara shirinsa. A shirye tsaf ya fito dauke da jakarsa, tana nan zaune a inda ya barta. Ya dauke kai ya nufi kofa bayan ya amsa a dawo lafiyar da Rukayya tayi masa. Ta mike ta nufoshi fuska babu walwala tana cewa ‘Ga abincinka can zaka fita baka yi breakfast din ba.’ Ya kalleta a fusace ba tare da ya daina tafiya ba yace ‘Abincin da kike hana yarana? Ni na koshi ki kirawo ragowar ‘yan uwanki ku cinye.’ Ta bude baki zata yi magana sai dai kafin tace wani abu ya ci rabin kafar benen, tana nan tsaye kamar zata hadiyi zuciya ta jiyo ficewar motarsa daga gidan. Dole itama ta shirya ta fice ta tafi wajen aiki domin a hakan ma ta san sai an harareta tunda ta makara. PAGE 234 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Kansa a cike yake saboda rashin bacci ga damuwa, don haka yana shiga office din ya rufo kofar ya kwanta a kan 3-seater din da take wajen. Yana rufe ido ya fara nadama; ya aka yi ya saki Khadeeja? Ya aka yi ya bari har ta gama idda bai mayar da ita ba? Tunda dai ai da ya mayar da ita ya san bata da wani zabi dole ta zauna da shi tunda ba zata saki kanta ba. Tunda yake da Khadeeja bai taba ganin wata damuwa game da yaransa ba, gashi wata takwas kacal da ta barsu gidan yana neman ya gagareshi. A da yayi zaton Naja zata fita kulawa da su musamman yanda yaga tana nuna kauana garesu kafin ya aureta; to me ya canza mata ra’ayi har aka kai inda basu da damar da zasu ci abinda suke so a gidan ubansu? Lallai dole ya dau mataki. Haka ya wuni a office din cikin rashin sukuni; yana tunani halin da yaransa suke ciki a gida sannan kuma ga shi zuciyarsa taki ta kyaleshi da tunanin Khadeeja. Tabbas da Khadeeja tana nan da babu yanda za ayi ya wuni a office yana tunanin halin da yaran suke ciki. Domin ya tabbatar duk halin da suke ciki to itama tana cikin wannan halin a tare da su. Ya tuno lokacin da tace ba zata yi musu girki ba yanda suka gaya masa gari suka sha kuma garin ma tare da ita suka sha. Yayi dariya a fili; tabbas Khadeeja tana da rigima amma ta iya rigimarta. Ya tabbatar babu yanda za ayi taci kaza ta bar yara da bakin shayi. Haka ya zauna yana aiki yana tuno rigimarsu da Khadeeja yana murmushi shi kadai. Bai taba zaton zai yi kewara rigimar Khadeeja ba amma yanzu tabbas kewar rigimar tata yake yi. Karfe daya da rabi daidai suka idar da sallah a farfajiyar office din su. Yana shiga office dinsa ya auna a kan kujerarsa ya turata baya kadan yana juyawa ya dauki wayarsa wadda take kan tebur din ya lalubo lambarta ya dannan mata kira, ya kara a kunnensa bayan da ta amsa yace ‘Hello.’ Bayan sun gama gaisawa yace ‘Kina ina ne?’ Da mamaki a muryarta tace ‘Ina office mana, akwai wata matsala ne?’ Murya a sanyaye yace ‘No, babu matsala kawai dai ina son ganinki. Zan iya zuwa office din yanzu?’ ‘Umm! Akwai matsala ne?’ Ta sake tambaya. PAGE 234 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Yayi ‘yar dariya ‘Babu matasala fa, akwai dai maganar da nake so muyi. Zan iya zuwa, minti talatin kawai ya isa.’ ‘Ok, ina jiranka duk da dai na kusa tashi.’ Ya ajiye wayar ya mike ya dauki mukullan motarsa ya kama hanya. ……. Yana sane yaki ya kirawota da ya sa don so yake ya shiga ya sameta a office din nata, don haka bayan ya ajiye motarsa sai ya fito ya shiga gidan talabijin ya tambaya. Ba tare da bata lokaci ba aka nuna masa office din nata. A hankali ya kwankwasa kofar, daga ciki muryarta ta bashi amsa ‘Shigo a bude kofar take.’ Ya tura kofar ya shiga da sallama. Tana zaune a kan kujerar zaman mutum daya wadda take gefe guda, da jakarta a gefenta tana ta danna waya; da alama ta gama shirin tafiya gida. Bayan ta amsa sallamarsa ya mayar da kofar ya rufe sannan ya karasa yayi kansa mazauni a kujerar da take kusa da wadda take zaune a kai. Bai san dalilin da yasa ganinta ya saka shi jin dadi ba amma dai ya san ya ji dadin ganinta. Cikin girmamawa ta gaisheshi kamar babu wata damuwa a tsakaninsu. Bayan ya amsa tace ‘Allah ya sa dai ba wata matsala don tunda kace zaka zo nake ta tunani.’ Yayi murmushi yace ‘Babu wata matsala, kawai dai ina son ganinki ne.’ Ta dan yi gajeren murmushi tace ‘Uhm, to gani.’ Yayi dariya yace ‘Kamar dai kina korata.’ ‘Ba korarka nake ba, kawai dai ina son na tafi gida don wallahi na gaji.’ Ya gyara zama; yarasa ma ta inda zai fara domin ganinta ya goge masa duk zantukan da ya tsaro zai zo ya gaya mata. ‘Yara suna kewarki.’ Ya fada bayan ya gama nazarin ta inda zai fara. Nan da nan murmushinta ya kara fadi, tace ‘Allah sarki ni da Hammad ma muna kewarsu. Don ma Yaya Habib yana zuwa gidan Mommy yana gaishemu.’ Ya girgiza kai domin Habib bai taba gaya masa yana zuwa wajen Khadeeja ba, bai ma taba yi masa maganar Khadeejan ba tun bayan da suka rabu. ‘Ya Hammad? Baya kukan makaranta?’ Ya tambaya. ‘Baya yi, ka san ya hada wayon yayyinsa gaba daya.’ Ta fada tana dariya. Suka yi shiru na dan lokaci; ita duk ta kosa domin so take ta tafi gida yayinda shi kuma ya gyara zama yana kwaso hira. PAGE 236 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace ‘Khadeeja.’ ‘Na’am.’ Ta amsa tana kallonshi. ‘Wai me yasa kika ce na sakeki?’ ya tambaya yana tsareta da ido. Ta sunkuyar da kai tana murmushi, ta dago ta kalleshi suka hada ido sannan ta sake yi masa wannan murmushin nata wanda yake dauke da ma’anoni daban daban tace ‘Right question at the wrong time; amma dai zan baka amsa.’ Ta sunkuyar da kai a daidai lokacin da murmushin fuskarta ya gushe, ta dago suka sake hada ido sannan ta gyara zama tace ‘Gajiya nayi Musatapha. Ka san idan mutum wanda bai iya swimming ba ya fada ruwa to zai yi ta kokarin ganin ya fita da rai ko, amma duk dadewa zai gaji. To haka ce ta faru da ni. Soyayya ce ta saka na aureka, amma idan dai ba na manta lissafin ba tun a shekarar farko na rasa soyayyarka. Haka na dinga kokawar janyo attention dinka ko zaka fahimceni amma baka ko kalli inda nake; kai dai abinda kake so kawai shi kake so. Na hakura ina zama da kai a haka saboda I was ok with just sleeping behind you every night; sai kuma ka dauko aure. Duk wani abu da nake so daga wajenka a lokacin ka dauka ka bata ina kallo. Haka na cigaba da kokawar samun attentin dinka, ina kokarin ganin kayi mana adalci amma hakan bai samu ba. Na tuna tun ina ni kadai ma ka fara kasa yi min adalci to balle yanzu mun zama mu biyu; ni da rabin ranka. So I gave up, ba zan iya ba, na gaji da fadan da bashi da ranar karewa don na gane bana ma gabanka. Shi yasa na nemi saki kuma Allah ya taimakeni ka bani kuma ka barni har na gama idda.’ Idanuwansa suna kan fuskarta har ta gama tayi shiru, ya cije lebe yace ‘Kuma baki gaya min ba Khadeeja? How did I not see all this?’ Tayi dariya tace ‘Da wanne yaren zan gaya maka?’ Suka sake yin shiru na dan lokaci. ta danna wayarta ta kalli agogo sannan tace ‘Time yana tafiya, wallahi so nake na tafi gida don na gaji.’ ‘Oh, sorry’ PAGE 237 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid Innar su Amal Suka sake yin shiru na dan lokaci sannan yace ‘Khadeeja yi hakuri mu mayar da aurenmu, in sha Allahu haka ba zata sake faruwa ba.’ Ta mike tsaye tana dariya tace ‘Kayi hakuri Mustapha amma aure ba zan sake yi da kai ba, babu wannan zance don Allah kada ka sake yinsa. Shekarun da muka yi Allah ya amfana su kuma Allah ya sa kaffara ne amma kada Allah ya maimaita mana.’ Ya dafe kansa da hannuwansa biyu na dan lokaci sannan ya sauke hannuwan ya mike tsaye. Ta bude kofar ya fice sannan ta biyo bayansa suka fito daga office din. Suka jero suka fito harabar office din. Nan suka tsaya yana ta faman lallabata ta bari ya kaita gida amma ta ki; yana ji yana gani ta tare taxi ta hau. Sai da ya tabbatar ta zauna a bayan motar sannan ya zagaya ya bawa direban taxi din kudinta. Suka ja mota shima ya koma ya shiga motarsa ya kama hanya. Ya dai ji tace ba zata taba sake aurensa ba amma tabbas bai yarda ba, yana ji a jikinsa in sha Allahu zata yarda su mayar da aurensu. Yanda zai yi da baffa ne ma yafi damunsa domin ya san tabbas Baffa ba zai saurara masa ba. Haka har ya isa gida yana wannan tunanin, sai dai yana saka kafarsa cikin gidan ransa ya kara baci. Bai san a yanda zai je ya sami yaran ba sannan kuma ita kanta Najan yana jin haushinta do ba zai taba bata dama ta wulakanta masa yara ba. ____ Ana cikin kiran sallar magriba ya shiga gidan, don haka ko zama bai yi ba ya daura alwala ya ja Habin suka wuce masallaci. Ko da aka idar da sallar a can ya tsaya wajen magidanta unguwar suna hira, har sai da suka yi sallar isha’i sannan suka tashi daga hirar kowa ya koma gida. A parlor din kasa ya sami yaran suna harkokinsu, ya wuce ya haye sama. Tana zaune a parlor tana jiransa saboda bata son yanda tun da safe ya ki ya ko kalli inda take. Ita idan ana fada ta fi so ayi hayaniya kowa ya fadi abinda yake ransa, amma ya ma ki ya tambayeta me yasa ta yiwa yaran haka balle ta samu tayi masa bayani. Ba ta jin ya amsa sannu da zuwan da ta yi masa, idan kuma har ya amsa to tabbas ita dai bata ji ba. Ba tare da ya kalli inda take ba ya shige dakinsa. A fusace ta mike ta bi bayanshi. PAGE 238 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Yana tsaye a gaban mudubi yana rufe durowa ta shiga ta turo kofar, ta tsaya a bayan kofar ta rungume hannu tace ‘Ga abinci can a dining table.’ Ba tare da ya kalleta ba yace ‘Ki sauka da shi kasa a can zan ci ni da yara.’ ta sunkuyar da kai ‘To bari nace su hawo sai kuci a nan, duk da suma na zuba musu nasu abincin kuma duk tuwon ne dai.’ ‘Ba sai sun hawo ba ni zan sauka, ki dauka ki kai can.’ Ya fada sannan ya juya ya zauna a gefen gado. Ta karasa ta zauna a kusa da shi, ta dafa gwiwarsa ta dan marairaice tace ‘Don Allah ka bawa Hajia hakuri, wallahi abinda ta gani ba haka bane. Kai ma ka san babu yanda za ayi na ci wani abu na hana yara. Hawowa ne basuyi ba na ajiye musu nasu a kitchen kuma da ka shiga zaka gani.’ Ya kalleta shekeke yace ‘Ai ba yau kika fara ba, kuma ba yau na fara yi miki magana ba. Babu wani akuri da zan bata idan kin gyara halinki su yaran zasu gaya mata ai. Mugun halin da kike nuna musu kuma ki cigaba kada ki fasa.’ Ya mike zai fita, ta kama hannunsa itama ta mike tana cewa ‘Don Allah kayi hakuri, yaran da nake hidimarsu tun kafin na aureka kuma yanzu ribar me zan ce idan nayi musu mugunta?’ ‘Nima shine abinda nake mamaki, watakila daman ba don Allah kike yi ba ko kuma zugaki aka yi kika canza hali ni ban sani ba. Abinda na sani kawai shine kusan tun da Khadeeja ta bar gidan nan kika dage sai kin raba rayuwarki da ta yaran nan, ina kula da yanda kike kokarin ganin basu hawo benen nan ba saboda tsabar samun waje…’ ‘Don Allah ka dai wannan maganar, wallahi kai ma ka san ba haka bane. Naga dai ko gidan waye akwai part din mai gida inda ba a bari yara su shiga, amma in sha Allahu ba zan sake hakan ba tunda na ga kai ba haka ne tsarinka ba.’ Ta katseshi cikin kosawa. Ya zare hannunsa da ta rike ya mike yana cewa ‘Ki kawo min abincin parlor din kasa yanzu.’ Ya fice ba tare da ya saurari amsarta ba. Haka ta gama zumbura baki ta sauko ta kawo masa abincin nan parlor din kasa inda a zauna suka ci da yaran; duk da sun nuna msa suma tuwo aka basu irin nashi. PAGE 239 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Haka ya kafa mata dokar idan dai yana gidan to a parlor din kasa zai dinga cin abinci wajen yara, babu rokon da bata yi masa ba a kan ya bari yaran su dinga hawowa saman ana cin abincin tare amma ya ki ya saurareta. Ya kula cewa ganin saman bene take kamar wani abu na musamman don haka ya yanke shawarar bar mata saman benen ita kadai. Ya yanke shawarar a kasa zai dinga

Chapter 23 of 25