Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
surutu ba sannan kuma bata son tana biye masa suna fada a gaban yara, ita yanzu duk wani abu da zai sa ayi magana ma bata so; shi yasa ta gwammace tayi masa shiru. PAGE 31 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Sai da ta gama wanke-wanken nan tsaf sannan ta kwashe sharar, ta debi kwanukan ta shigar cikin gida. Suna zaune a parlor suna kallon TV. Tana kitchen din tana kife kwanukan Afaf ta shigo ta sameta, ta dauki kwanukan ta fara kifewa. Ta dubeta tace ‘Afaf je ki zauna ai na kusa gamawa.’ Tace ‘Bari na tayaki Anti, ai nan babu ruwa.’ Ba don ta so ba ta kyaleta sai da suka kife kwanukan gaba daya ta mayar da komai inda yake sannan ta wuce daki su kuma suka cigaba da kallonsu. Can wajen 1pm bayan sun yi sallar azahar ta fito daga daki ta shiga kitchen; tuwon alkama da miyar danyen kubewa ta dafa jiya da daddare amma duk sai suka ki ci. Da yake akwai biscuits da cake sai kowa ya ci ya sha lemo, ita da abbansu ne kawai suka ci tuwon gashi ta dafa shi da yawa. Da safe kuma da kwadayi ta tashi don haka wainar fulawa ta soya kowa yaci. Wannan ragowar tuwon shi ta dauko daga fridge ta dumama shi, ta dumama miyar wadda ta sha kaza da nama. Ta zubawa kowa abincinsa sannan ta kirawosu kowa ya dauki nasa suka zauna a table. Kallon tuwon kawai Habib yakeyi yana juyashi amma yaki ya fara ci, tana kallonsa tayi banza da shi ta cigaba da kai lomarta tana bawa Shukra don ita tuwon yayi mata dadi. Jimawa kadan ya dubeta yace ‘Anti tuwon jiya ne fa?’ 'Eh, shine, ko ci ko bari.’ ta fada a gajarce ta ci gaba da cin abincinta. Daidai nan Abbansu ya fito ya zauna a table din, ta tura masa flask da plate. Ya bude flask din ya kalli fuskokin yaran sannan ya kalleta yace ‘Wannan ai tuwon jiyane, ba a yi abincin ranar bane?’ ‘Shine abincin ranar ai, dumamawa aka yi tunda babu abinda yayi.’ Nasreen wadda itama take ta juya nata tuwon tace ‘Abba wallahi tuwon ba dadi, ni bana son bakin tuwo gaskiya.’ Shi din yana son tuwon alkama don shine ma ya sa aka yi tuwon da daddare, don haka ya zuba malmala guda ya fara ci. Ya sake duban fuskokin yaran, bayan ya hadiye lomar da take bakinsa yace ‘Yanzu ba wani abu da za a iya dafawa yaran nan, Afaf ce kawai take cin tuwon nan.’ Ba tare da ta kalleshi ba tace ‘Babu.’ Ta cigaba da cin tuwonta kamar bata san da su ba a wajen. Jimawa kadan Nasreen tace ‘Abba ni a hada min cornflakes. PAGE 32 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ya dubi Khadeeja yace ‘Akwai cornflakes ko?’ Cikin halin ki in kika tace ‘Akwai.’ 'Da Allah a hada mata ta samu ta ci kafin ayi abincin dare.’ Tace ‘To.’ Ta ci gaba da cin tuwonta tana bawa Shukra a baki, yayinda ita kuma Nasreen ta tashi ta koma gaban TV. Jimawa kadan Habib ma ya mike, ya dauki kwanonsa da na Nasreen yana cewa ‘Abba nima na sha cornflakes din kawai.’ Ya wuce ya kai kwanukan kitchen ya dawo shima ya zauna a gaban TV. Bai dade da tashi ba kuma itama Khadeejan ta gama cin nata tuwon, ta dauke kwanonta ta kai kitchen. Ta fito daga kitchen din ta wuce daki ba tare da ta kallesu ba. Tana shiga ta saka pillow ta kwanta a tsakiyar gadonta, da yake ta gaji sannan kuma ta koshi tana rufe ido bacci ya kwasheta. Bata sani ba ko ta dade da kwanciya ko bata dade ba, kamar a mafarki taji Mustapha yana dan buga kafarta yana cewa ‘Khadeeja, Khadeeja, barci ma kike yi? Kin bar yara da yunwa fa ki zo ki hada musu cornflakes ko ki dafa musu indomie.’ Ta dan janye kafarta tana kokarin tashi; kafin aurensu fa baya kiran sunanta sai dai yace ‘yan mata, mekyau ko kuma yace babe. Tayi zaton idan sun yi aure next level zasu shiga a kara mata matsayi amma zata iya cewa tunda ta shigo gidan nan sau daya ya kirawota da babe a daren da suka tare. Yanzu kam yaci duba sai ceto don gatsal yake kiranta Khadeeja. Ta gyara zama tace ‘Me kake cewa?’ 'Baki bawa yara abinci ba kin zo kin kama bacci.’ Tana jijjiga kai tace ‘Kowa fa na bashi abinci baka gani bane?’ 'Habib da Nasreen nake magana fa.’ 'Oh, ba sun ce cornflakes zasu sha ba, ai akwai a kitchen din.’ ta fada tana kokarin kwanciya. 'To ai sai ki zo ki hada musu ko?’ Ta gyara kwanciyarta a cewa ‘Wallahi babe na gaji, idan ban yi baccin nan ba ko abincin dare ba lallai na iya dafawa ba. Suje su hada cornflakes din mana ko su ci tuwon da kowa ya ci.’ 'Ya ina miki magana kina kwanciya Khadeeja, haka zaki bar min yara da yunwa.’ ya fada a fusace. Ta gyara kwanciyarta tayi banza da shi. 'Ina miki magana kina ji na fa Khadeeja bana son wulakanci.’ Ta tashi zaune, lokacin ya riga ya mike tsaye. Ta gyara zama tace ‘To me zan ce maka?’ PAGE 33 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) 'Ba zaki zo ki hada musu cornflakes din ba kenan?’ 'Hada cornflakes din ba wani aiki bane shi yasa nace su hada kawai, wallahi kaina ciwo yake.’ Ta ture abinda ta rufa da shi ta sauko daga kan gadon ta wuce bandaki saboda yanda bakinta ya cika da yawu, ta mako kofar bandakin ta tsaya a gaban sink; wallahi babu wani abinci da zata hada sai dai yayi duk abinda zai yi. Tana ji Nasreen ta leko tace ‘Abba yunwa nake ji.’ Ya ja tsaki ya kama hannun Nasreen suka fice daga dakin bayan ya maka mata kofar a fusace. Haka ya je ya hadawa yaran cornflakes din suka zauna suka ci. ……….. Tun da ya hada musu cornflakes din nan kuma sai ya shiga share Khadeeja, gaba daya ya ki kulata ko zama inda take. Ta kula da hakan don haka ita ma sai ta ja jikinta, domin bata cikin yanayin ma da zata iya saurarensa. Ko da dare yayi ma har ta kwanta a dakinta sai kuma taga rashin dacewar hakan, tunda dai bai koreta ba kuma ita ba fushi takeyi da shi ba shi kadai yake fushinsa. Don haka bayan ta kwantar da yara sai ta shirya ta wuce dakinsa ta kwanta. Can wajen sha biyun dare motsin shigowarsa ya tasheta, yana tsaye a gaban wardrobe yana saka kayan bacci. Ta sauko daga kan gadon ta wuce bandaki don tayi fitsari ta kuskure baki. Tana fitowa ta wuce ta kwanta, ta kalleshi yana zaune a gefen gadon yana dannan waya; so take ta ce masa “good night Babe” kamar yanda ta saba amma bakinta ya ki furtawa saboda yanda take cike da haushinsa. Don haka sai kawai ta juya masa baya ta kwanta. Kamar wanda yake jira ta kwanta sai ya gyara zama a kan gadon yace ‘Tashi muyi magana Khadeeja.’ Ta juyo ta kalleshi sannan ta tashi zaune ta jingine da jikin gadon; tana bakin cikin yanda yake kiranta Khadeeja gatsal sai kace shi ya yanka mata ragon suna. Bayan ta zauna ya kara tsuke fuska sannan yace ‘Bana son yanda kike yi min taurin kai da neman kawo min raini a gaban yara, idan ma wani abu ne a ranki gara ki fito ki gaya min.’ PAGE 34 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Tayi murmushin yake tace ‘To, sai dai ban san lokacin da nayi maka taurin kan ba.’ 'Dazu nace ki hadawa Habib da Nasreen cornflakes kin ki, nan kika shige bandaki kika barni a tsaye ina miki magana.’ Ta kalleshi suka hada ido ta kura masa ido har sai da shi ya kawar da kansa, ta bude bakinta wanda ya fara tara yawu tace ‘To in sha Allah zan kiyaye, amma nima don Allah ka dinga saukaka min rayuwa a gidan nan. Idan baka yi min saboda kauna ba to kayi min saboda yanayin da nake ciki tunda nima ba lafiya ce ta isheni ba duk abinda ka ga ina yi daurewa nake yi.’ Ya dan fara saukowa yace ‘Duk don na nema miki saukin ne ai nace a kawo mai aiki, kuma da ta dawo zata cigaba da tayaki. Itama mahaifiyarsu haka take kula da su ko da kuwa tana da ciki don wannan ba wani abu bane a wajen macen da ta san me take yi. Bana son ki dinga yi musu abubuwan da zasu ji maraicin uwarsu, ki rike su kamar ke kika haifesu. Shine abinda zai samar da zaman lafiya tsakanin mu.’ Ta gyada kai tana kallonsa cike da tsananin mamaki tace ‘To.’ Ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki ta tofar da yawun bakinta ta daurayo bakinta ta fito ta kwanta bayan ta kashe fitila. Tana kwanciya hawaye ya fara bin idonta; wannan wace irin rayuwa ce? Wai dama haka ake aure ko kuwa itace bata dace ba? Shikenan shi da ‘yayansa ne kawai mutane? Kiri-kiri sai a kirkiri laifi a dora mata kuma a saka ta bada hakuri. Da ya barta da yaran tabbas tayi niyyar ta rikesu kamar ita ta haifesu, domin har addu'a takeyi kada Allah ya bata ikon cutar dasu. Sai dai zuwa yanzu gaba daya sun fice daga ranta, duk wata kauna da ta tanada don ta nuna musu bata jin zata iya tunda ga dukkan alamu ma ba zai barta ba. Shi ba so yake ta nuna musu kauna ba so yake kawai ta bauta musu, bata jin zata iya hakan kuwa. ……… A cikin wannan yanayin Khadeeja ta cigaba da lallabawa tana iya kokarinta wajen kulawa da yaran da gidan gaba daya. Kwana biyar aka yi da lockdown aka bada wuni daya mutane su fita su dan yi sayayya, don haka a wannan ranar Khadija take sa ran dawowar Habi mai aikinsu tunda Mustapha yayi wa Yaya Jidda magana. PAGE 35 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Tun safe take kiran Habi amma har azahar ba a daukan wayar sai bayan azahar sannan Habin ta dauka. Nan ta sanar da ita cewa mahaifiyarta ce bata da lafiya don haka wanen mai magani suka je, sai dai ko zuwa lokacin da za a sake bude gari shine zata samu ta taho idan mahaifiyar tata ta sami lafiya. Kamar tayi kuka haka ta ji domin tana ganin kamar dawowar Baba Habi zai rage mata wata wahalar; gashi azumi saura abinda bai fi kwana goma ba. A take dabara ta fado mata, ta dauki wayarta wadda ta juye; har ta nemo lambar Mommy zata kirawo sai kuma ta fasa ta kirawo lambar Baffa. Bayan sun gaisa ta sanar dashi tana so Nabila ta zo ta tayata zama zuwa lokacin da za a sake Bude gari in ya so sai ta tafi. Sai da ya Dan yi jim sannan yace ‘Kiyi hakuri Khadeeja,ba zata zo ba, haka aure yake. Kanwarki balagaggiya ba muharramar mijinki bace gashi gidanku ba wani Kato ba, ba zai yi ma'ana ba ana wannan zaman na wuni a gida na turo miki ita. Amma dai zuwa lokacin da za a sake Bude gari zan sa Mommy ta duba Miki dattijuwa wadda zata zo idan Kuma Mai aikin naki ta dawo ma shikenan. Kin gane ko?’ 'Na gane Baffa.' Sukayi sallama ta ajiye waya. Wani malolo ne ya taho ya tokare mata makogoro saboda takaici; yanzu Baffa ba zai bata Nabila ba kenan yana wani zance? Take hawaye ya wanke mata fuska, ta dauki wayarta ta shige daki saboda kada yara su sameta tana kuka. Tana ji tana gani aka sake mayar da garin aka kulle babu Baba Habi babu Nabila, haka ta cigaba da bautawa Mukhtar da ‘yayansa babu abinda ya sauya. ………. Saura kwana biyu azumi aka sake bude garin na wuni daya saboda a dan yi sayayyar azumi. Tun da safe Mustapha ya sa ta shirya yaran ya kwashesu sai gidan Hajiya. Basu dade da fita ba aka buga mata kofa, kamar ba zata Bude ba da oda tana tunanin ko almajiri ne. Amma sai ta daure ta fito don ta bude da aka cigaba da bugawa. Tana budewa ta ci karo da Mommy tare da Nabila, Ahmad ne ya ajiyesu ya juya sai da yamma zai dawo ya daukesu. Tun a bakin gate ta rungumo Mommy suka shigo gidan tare tana ta murna. A nan parlor suka baje, ta sa Nabila ta dauko musu ruwa da lemon suna Sha suna hira. PAGE 36 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Daga baya Nabila ta tashi ta fara gyara mata gidan; ta barsu a zaune ita da Mommy suna hira. Mommy tace ‘Baffa dai yace kada a bar Miki Nabila, Mai aiki Kuma Ina ta cigitawa. Kin san yanzu duk tsoro ake ji saboda wannan lockdown din.’ 'Watakila ma yau Baba Habin zata dawo, zai iya yiwuwa ma tana can gidan Yayarsa tasa sai ya taho da ita idan zasu dawo.’ Mommy tace ‘To Allah yasa.’ 'Ya jikin naki?’ 'Da sauki Mommy, yawun nan ne bana so wallahi ga wani yawu da bana iya hadiyewa.’ 'Wannan Kam hakuri Zaki yi, Allah ya raba lafiya.’ Jimawa kadan Mommy tace ‘’yayan naki basa baki matsala ko?’ 'Babu matsala Mommy,shine ma yake sa mana Ido wallahi amma da zai barsu yaran basu da matsala.’ 'Da sauki ma idan hakane, Shima a hankali Zaki dinga nuna masa in Sha Allah zai gane idan ya ga kun hade Kai.’ 'Hmmm!’ Haka Mommy ta wuni a gidan nan tana kokarin ganowa ko da matsala, sai dai har ta tafi bata ga inda gagarumar matsalar take ba. Ta dai bawa Khadeeja shawarwari kuma da alkawarin sami mata mai aiki da zarar gari yayi lafi. La'asar tana yi Ahmad ya zo ya daukesu suka tafi. Suna tafiya ta dauki waya zata kirawo Mustapha taji ko Habi ta dawo, sai dai kafin wayar ta shiga ta jiyo motsinsu yana Bude gate don haka ta mayar da wayar ta ajiye. Tun kafin ya zauna ta kula kowa ya shigo bata ga Baba Habi ba, tace ‘Ina Baba Habi? Na zata tare zaku taho.’ 'Hm! Wai mahaifiyarta ta rasu jiya don haka ba zata dawo ba sai bayan Sallah, lokacin an yi 40 days.’ Tace ‘Subhanallahi. To don Allah kace da Yaya Jiddan ta sami mana wata saboda azumi, wallahi hidiman da yawa ga lockdown.’ Ya karaso ya a zauna sannan yace ‘Na gaya mata, ta dai ce wai wahala suke saboda lockdown tsoron baro gidajensu suke yi.’ 'To ga mu ga Allah, Mommy ma ta zo bayan kun fita itama na ce ta cigita mana.’ A ranar haka Khadeeja ta kwana cikin zulumi saboda fargabar yanda zata yi da aikin azumi. Kafin gari ya waye dabara ta fado mata, tana fatan Allah ya sa kada wani abu ya kawo matsalar. PAGE 37 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ko da gari ya waye sai wajen 10am sannan ta yiwa Mustapha bayani wanda ya bata dama sannan ta tafi gidan su Ummi; makotansu inda a nan ake yiwa su Afaf kitso. Ta samu ta roki arziki a wajen mahaifiyar Ummi a kan ta dinga zuwa tana tayata aiki zuwa bayan Sallah. Ba tare da wata matsala ba ta amince mata tunda dama ita kewa yaran kitso. Tun a ranar Umminta fara taya Khadeeja aiki, gashi bata da kuwa don haka cikin walwala suka wuni. Kullum haka zata bata abinci ta ce ta koshi sannan Kuma idan zata tafi ta zuba mata a falsak; ga alkhairi Kuma kullum tana yi mata. —---- Ranar da aka tashi da azumi Alhaji wato mahaifin Mustapha ya kirawoshi da safe ya sanar da shi rasuwar abokinsa Alhaji Rilwanu; nan yayi masa bayani cewa ai Covid 19 ce ta kashe shi don haka mutane kadan ne ma suka je jana'iza. Matarsa ma tana kwance Kuma itama COVID 19 din ake tunani don har an kaita isolation center. Khadeeja tana shiga dakin ya bata labari, tace ‘Allah ya sa ya huta. Ashe Corona din nan gaske ce.’ Da mamaki ya kalleta yace ‘Oh, ke da baki ma yarda ba kenan? To wallahi ki kula sosai don babu wahala an dauka. Ai shi yasa ma aka saka lockdown don idan dai mutane suna yawo to zasu yi ta rabata a junansu. Kina ji dai Baba Rilwanu ya rasu kuma an saka matarsa a isolation. Garama ki San wa kike bari yana shigowa gidan nan kada ki kwaso mana, especially ke da kike da ciki.’ Ta Dan zaro ido ‘Allah ma ya kiyaye, in Sha Allah we are safe.’ Suna nan zaune ya daga waya ya kirawo Alhaji yayi masa gaisuwar abokinsa, suka dauki lokaci suna waya tana jinsa yana ta amsawa da eh, ava, toh, haka har suka gama wayar. Yana ajiye wayar ya dubeta yace ‘Ai muna da Dettol ko?’ 'Eh akwai babbar roba ma kuwa.’ 'Don Allah a dinga goge duk wani surface na gidan nan da ruwan Dettol, musamman hannuwana kofa da guraren da mutane suke tabawa. Duk wani shige da fice ma a hakura da shi don wallahi corona Dina nan da gaske take, sai mutuwa ake. Gara a daina shigowa gidan kada a kwasawa yara muna zamanmu lafiya.’ Ta gyada kai ‘Hakane, ai da yake ma babu wanda yake shigowa gidan sai Ummi, itama da ta gama aikinta take fita.’ PAGE 38 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta gyada kai ‘Hakane, ai da yake ma babu wanda yake shigowa gidan sai Ummi, itama da ta gama aikinta take fita sai dai da yamma kuma nace ta dawo ta tayani girkin Sha ruwa ta tafi.’ 'To sai kun yi taka tsan-tsan.’ ……… Har azahar tana ta jiran Umminta zo ta gyara gidan amma bata zo ba. Can wajen 2pm suna zaune a parlor gaba dayansu aka buga gate. Da kansa ya tashi yake ya bude, jimawa kadan ya shigo Ummin tana biye da shi. Ya koma ya zauna a inda ya tashi. Ummi na shiga gidan Shukra ta tashi da gudu ta rungumeta tana cewa ‘Ummi na tsefewa Baby na kanta yau ita Zaki yiwa kitso.’ Ta dauketa ta mika mata hannu suka tafa tana cewa ‘Yauwa kawas, bari nayi sauri na gama shara mu zauna kitso don babynki anti yalash ce.’ Ta sauketa tana ta murna. Ta rage tsawo ta gaida Khadeeja, har zata shige kitchen Khadeejan tace ‘Shine baki zo da wuri ba yau Ummi? Gashi annfara azumi.’ 'Wallahi Anti cikin gari muka shiga.’ Da mamaki tace ‘Ke Ummi ana lockdown din kike fita.’ 'Yo Anti ai mu a kasa muke yawonmu, babu inda bam zuwa.’ 'Ai kuwa za a kamaku Ummi ko ku kwaso cutar da ake gudu.’ 'Ta masu kudi ce Anti.' Ta shige kitchen tana dariya. Bata dade da shiga kitchen din ba Shukra ta dubi Khadeeja tace ‘Anti zan Sha ruwa.’ Daga nana ta kwalawa Ummi kira ta debo ruwa ta mikowa Shukra. Kadan ta kurba har Ummin ta juya zata koma kitchen din Shukra ta kurbi ruwan ta mika kofim tana cewa ‘Na Sha Ummi tafi da shi.’ Ta karbi ruwan a Kofi ta juya ta nufi kitchen din, tana juyawa ta kafa kai ta shanye ragowar ruwan sannan ta wuce kitchen din. Mustapha ya kalli Khadeeja yace ‘Wannan yarinyar kuwa ta san me take yi? Ana maganar Corona tana abubuwa anyhow. Ta gama yawonta a gari Kuma ta zo tana daddumar abubuwa kuma har tana using utensils din yara? Corona din nan fa is real.’ Khadeeja ta kalleshi ta langabar da Kai tace ‘Kayi hakuri zan yi mata magana.’ 'To Allah ya kiyaye.’ PAGE 39 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Nan da nan Ummi ta gama aikin gidan ba tare da wata matsala ba. Bayan la'asar Kuma ta dawo. Itace tayi komai don Khadeeja kujera ta saka ta zauna a kitchen din tana gaya mata abinda zata yi, shi kuma Mustapha yana zaune a parlor shi da yaransa suna kallon TV. Kafin magriba sun gama komai Khadija ta kawo ta jera a kan carpet domin Mai gidan ya ce yau a kasa zasu Sha ruwa ba a table ba. Zobo ne mai sanyi, sai dankali da kwai, daga gefe kuma ga farfesun kaza da kuma couscous da sauce. Kafin a fara kiran Magriba ta zubawa Ummi komai ta sallameta ta tafi. Sai da aka idar da sallar Magriba sannan suka zauna shan ruwa; kowa da plate dinsa wanda Khadeeja ta zuba masa abinci ga soup bowl a gefe, ita kuma Shukra kwanonsu daya da Khadeejan. Bayan ta gama zuzzuba abincin kuma ta fara kokarin hada musu shayi. Bayan ta gama ta hada nata sannan ta dauki karamin kofi zata zubawa Shukra daga nata login, Mustapha ya dubi kofin yace ‘Wannan ba kofin da yarinyar nan ta sha ruwa da shi dazu bane?’ Ta cigaba da juyewa tana cewa ‘Shine, ai ta wanke shi.’ 'Kika sani? Bayan ruwa kawai aka Sha da kofin kuma kina zaune a nan tayi wanke-wanken, idan fa kifewa kawai fayu bayan ta gama dambara baki a jiki?’ Ta gyara zama zata mikawa Shukra shayin yace ‘Ya zaki bata, ki canza mata cup mana. Ba kya jin me nake fada ne.’ Ta kalleshi kamar zata yi magana sai kuma ta fasa; ba zata iya fara musu da shi yanzu ba domin bata ma da kwarin da zata iya doguwar magana don kishiruwa ta galabaitar da ita a wunin yau. Ta tashi ba tare da tace komai ba ta wuce kitchen, ta zubar da shayin ta dauko wani kofin ta dawo ta sake hadawa Shukra wani shayin. Haka suka gama shan ruwan ba tare da ta kula kowa ba sai Shukra da suke cin abinci daga kwano daya. ……. A kwance ya sameta a daki, ba wai bacci take yi ba kawai rufe ido tayi tana hutawa saboda yanda jikinta yake ciwo. Duk da babita tayi aikin gidan ba yau amma ta gaji, musamman da yake an yi kishiruwa. Gashi bata son ta ajiye azumin saboda ko bata yi ba ma bata iya cin abincin kirki; garama da tayi azumin ta samu bayan shan ruwa ta ci couscou ta koshi. PAGE 40 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Da sallama ya shigo dakin, ta dan juyo ta amsa sallamarsa, bayan ya zauna yace ‘Sai yaushe zaki shirya yaran su kwanta ne?’ Tace ‘Barinsu nayi da yake daren na azumi ne kuma gobe ba fita za ayi da safe ba, zuwa 10pm sai a kwanta.’ 'Ok, haka ne kam.’ Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace ‘Ina ga kiyi hakuri da aikin nan wannan yarinyar ta daina shigowa gidan nan. Ki bari a sami saukin cutar nan tunda kina ji tace cutar ma ta masu kudi ce don haka ba zata daina yawonta ba.’ Ta tashi zaune takalleshi sosai tace ‘Don Allah ka bari, wallahi nayiata magana kuma gobe ma zan sake mata magana. Ka ga ga azumi wallahi abincin shan ruwa kawai ya isheni balle ga su wanke-wanke da shara, zan mata magana na san in sha…’ Kafin ta karasa ya katseta yace ‘Ki fahimceni ba wai don bana son ta tayaki aiki bane, nima na fi so a tayaki. But she's putting all of us at risk, tunda zata ke ta gama yawonta a gari sannan ta dawo ta shigo mana gida tana mu'amala da yara da kuma ke anyhow. Bana son a sami matsala please ki sallameta kawai, idan pandemic din nan ya wuce zata iya dawowa ai.’ ‘To ya zan yi da aikin? Gashi ba dadi nake ji ba, kamar kana mantawa da cikin jikina.’ 'Ni ban ce miki na manta na, Amma aikin gidan nawa yake? Duka ba wani abu ne da zai gagareki ba fa, kina ma fa da damar ki ajiye azumin idan yana wahalar dake ba wani abu bane. Amma aikin gida ai ba abinda zai gagareki bane, itama Ma'un haka take hadawa da ciki da goyo kuma da aikin gaba daya. Amma gaskiya a hakura da shigo da kowa gidan nan for now, gaskiya. Da safe ma idan ta zo daga gate zan ce ta koma. Kiyi hakuri ki fahimceni, ke kanki you are at risk idan ta kwaso cutar nan ta shigo mana da ita gidan nan.’ Cike da takaici ta sunkuyar da kai tace ‘Shikenan, duk yanda kayi.’ Ta zame ta kwanta. Ya bude baki zai yi magana sai kuma ya ga gara ya kyaleta ta huce zuwa an jima ya sake yi mata bayani, amma ba zai iya bari ba ga halin da ake ciki kuma a dinga shige da fice a gida. Idan cutar nan ta shigo gidan ya zai yi da ita? Ya mike ya fice ya turo mata kofar. PAGE 41 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa

Chapter 4 of 25