Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta juyo ta kalli kofar ta harareta kamar shine a wajen sannan ta ja tsaki ta juya. Ta San akwai cutar to amma ai ta yiwa Ummin magana, yanzu ya yake so tayi da aikin gidan nan ga azumi? Da ma ace zai tayata aikin me ko kuma ya bari yaranshi su dinga tayata to da sauki. Amma haka zai zuba yaranshi a gaba suna zaune suna kallon TV ita kuma tana kitchen ita kadai. Ta share kwallar da ta gangaro a idonta ta gyara kwanciya; bata san yanda zata kasance ba sai dai kawai ta bari taga yanda hali zai yi goben. …….. Ko da gari ya waye Khadeeja bata ma San lokacin da Ummi ta zo ba don tun daga bakin gate ya tareta yace ta koma kada ta sake zuwa sai bayan Sallah. Sai wajen Sha daya sannan ta fito ta dan gayggyara gidan, wanke-wanke ne ma ya bata mata lokaci don yana da yawa sosai. Haka ta wankesu gaba daya a famfon waje sai da shigo kifewa sannan Afaf ta tayata. Tana gamawa ta shige dakinta ta kwanta; bata taba jin gajiya irin wannan ba a rayuwarta, gashi duk wata gaba da take jikinta ciwo take yi. Tun 3pm ta shiga kitchen ta fara kokarin hada kayan Shan ruwa; dankali da kwai zata soya sai jollof sphagetti sannan ga peppersoup din nama. Da akwai ragowar zobo na jiya don haka ba zata sake hada wani ba. Yaran suna zaune a parlor ta zo ta wuce ta shiga kitchen, tana wucewa Afaf ta bi bayanta. Ta so ta Koro Afaf din daga kitchen amma dai ta hakura ta barta, suna yin aikin. Basu dade da farawa ba Habib ya shigo kitchen din, ya kalli dankalin da aka ajiye a tsakiyar kitchen din yace ‘Anti wannan ferayewa za ayi?’ Tace ‘Eh, so nake na dora kifin nan sai na zauna na feraye shi.’ 'Kawo wuka na feraye Anti.' Ya fada yana Bude cabinet, ya zaro roba ya tara ya debu ruwa. Tace ‘Ka barshi Habib zan feraye.’ Ya sa hannu ya dauki wuka a kan sink yana cewa ‘Na iya feraye dankali fa Anti, idan na feraye miki sai ki yanka.’ Bai saurari amsarta ba ya tsuguna ya fara feraye dankalin. Afaf ta ajiye kayan miyan da ta gama wankewa a kusa da Khadeejan tace ‘Anti na wanke kayan miyan.’ 'To ki yanka mana albasar nan, Rabi slicing za ki yi rabi Kuma ki yanka kanana sai a saka a soup da fried egg.’ PAGE 42 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta dauki albasar ta wanke ta zuba a chopping board ta fara yankawa. Ba su ji lokacin da Mustapha ya karaso bakin kofar kitchen din ba; a dai-dai lokacin nan wukar da Afaf take yanka albasa ta goce ta Yanke mata hannu. Ta dire albasar ta make murya tana cewa ‘Waiyo Anti na yake.’ Da sauri ta saki abinda yake hannunta ta nufi wajen Afaf din tana murmushi cike da kulawa tana cewa ‘Sorry, garin yaya Afaf. Ki…’ Da sauri ya karasa ya kama hannun Afaf din yana cewa ‘Garin Yaya kika yanke, me ya sa kika dauki wuka?’ Ya juya ya dubi Khadijan yana cewa ‘Na gaya miki sai kin san aikin da Zaki dinga sa yaran nan Amma ke gani kike kamar kawai bana son su taya ki aiki ne. Yaushe Afaf zata iya wani yanka albasa.’ Afaf ta zare hannunta daga nashi hannun ta juya ta wanke a sink, ta dubeshi tace ‘Ya ma daina jinin Abba bari naje na daure.’ Yana juyawa ya dubi Habib wanda yake ta ferayar dankali ya daka masa tsawa ‘Ka ajiye wukar nan ka tashi, namiji da kai kana wani feraye dankali. Tashi ka bani waje.’ Ya juya kan Khadeeja wadda ta riga ta cigaba da aikinta kamar ba da ita yake magana ba, yace ‘Na gaya miki ki daina sa yaran nan aikin da ya fi karfinsu, bana so. Shi Habib ma da yake namiji me ya hadashi da wani harkar girki? Bana so.’ Bai ga alamar zata bashi amsa ba don haka ya juya shima ya fice suka barta ita kadai a kitchen din. Ta rasa me ma zata yi, ta goge fuskarta ta cigaba da aikinta. Haka ta lallaba ta gama komai, zuwa magriba ta zubawa kowa aka sha ruwa. Ta gaji iya gajiya don haka bata ma da kuzarin da zata iya wani musu da shi, ta dai riga ta gama yankewa kanta hukunci da zarar an bude gari zata tafi gidansu ba zata dawo ba sai ta haihu kuma ya dauki mai aiki. ……. A haka aka cigaba da azumi, kullum cikin wannan yanayin Khadeeja take hadawa da hidimar gidan da ta yaran tayi ta fama. Kullum sai ta yiwa Shukra da Nasreen wanka, tsarkin kashi tsarkin fitsari duk ita take musu. Duk wata fitinarsu itace me kulawa. Ga shi tana fama da Shukra wadda sai yanzu ne da suka kwana biyu ta fara hanata kashin wando. PAGE 44 MIJIN MARIGAYIYA A HAUSA NOVEL by Sakina Yazid (Innar su Amal) 'Don Allah kiyi mata a hankali, komai lokaci ne ai zata daina ne a yi mata hakuri.’ Ya fada yana shirin komawa dakin ya yiwo alwala. Ta tsuguna zata dauketa taji kanta ya biyota kamar zai fado, ta dafe goshi ta koma ta tsaye tace ‘Kai! Ba zan iya ba fa.’ Ya juyo ya tsaya ‘Menene?’ ‘Ba zan iya tsugunawa ba fa, jiri kwasa ta yake.’ ta karasa kan kujera ta zauna ta dafe goshi. Ta dubi Afaf tace ‘Bani ruwa na Sha Afaf, ga kiran Sallah nan an fara.’ Nan da nan ta cika Kofi da ruwa ta mika mata, ta Sha kadan ta jingine kanta tana rike da ruwan. Kukan Yusra ne ya katsesu tana cewa ‘Anti na daina ba zan Kuma ba, manatwa nayi daman.' Ta yunkura zata mike Afaf tayi sauri ta dafeta. Abbansu ya dubi Khadija yace ‘Don Allah ki lallaba ki wanke mata kashin nan, Wannan wane irin abu ne? Yanzu wa kike so ya wanke mata kashin?’ Afaf ta aika Nasreen ta dauko fo a toilet ta cire wandon da yake cike da Kashi ta jefe a fo din sannan ta dauke Shukran ta nufi bandaki. Ta wanke mata sannan ta dawo ta gyara wajen, zuwa lokacin Abbansu ya fito daga alwala. Ya zauna ya sha ruwa sannan ya mike zai tafi masallaci. A daidai lokacin itama Khadeeja ta dago kanta ‘A dawo lafiya.’ Yana jinta yayi banza da ita saboda yanda yake jin haushinta, Kuma tabbas sai ya kora mata bayani in an Sha ruwa. Daga yau ma ba zata sake yin azumin ba tunda dama Mai ciki tana da damar ajiyewa. Ta mike tana gatsina fuska, kawai sai gani yayi ta sulale zata fadi. Ya zabura zai tareta yayi fatali da casserole din dankali, a lokaci guda Habib ya saki jug din zobon da ya fito dashi daga kitchen ya tarwatse a wajen ya karasa kanta. Duka su biyun kafin su karaso ta zube. Abbansu ya dago kanta yana jijjigawa ‘Khadeeja, Khadeeja, Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, Khadeeja.' Ko motsawa bata yi. Ya sunkuceta ya kwantar da ita a kan three seater, ya kara gudun fanka sannan ya kunna AC. Ya cire mata dankwalin da yake kanta ya fara yi mata fifita. Yaran gaba daya suka jeru a kanta suka yi tsuru-tsuru; Afaf ta leka fuskarta ta kafadar Abbansu tace ‘Abban itama mutuwa zata yi ta barmu ko?’ 'Ke bana son rashin hankali, ba wanda zai mutu’ PAGE 45 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) A take yaran suka saka masa kuka mai ban tausayi. Afaf ta rungume Nasreen da Shukra suka hada Kai suna kuka. Habib ya taba shi yace ‘Abba ka Kai ta asibiti kada ta mutu ta barmu.’ 'Kai rufe mana baki.’ Gaba daya Shima ya rude, jikinsa har rawa yake yi. Ya janyo jug din ruwan sanyi ya jika hannunsa ya Shafa mata a fuska. Ta ja numfashi ta bude idonta, sai kuma ta mayar ta rufe. 'Khadeeja.' Ya kirawo sunanta da karfi yana jijjiga ta. Da gudu su Afaf suka karasa kanta suna kira ‘Anti, Anti.’ ‘Khadeeja.’ Ya kara kiran sunanta a firgice. Ta bude ido ta sake rufewa. Ya mike tsaye ya dan tura yaran yana cewa ‘Ku zauna na dauko mukullin mota, asibiti zan kaita yanzu, babu abinda zai sameta in sha Allahu.’ Ba tare da bata lokaci ba ya dauko mukulli ya fito, ya je ya bude kofar motar ya dawo ya dauketa bayan ya yafa mata mayafi ya wuce yaran suna biye da shi ya kwantar da ita a bayan motar. Bayan ya rufe kofar motar ya juyo ya kalli yaran yana tunani; to yanzu ya zai yi da su? Wa zai barwa su? Ya san shi kansa ma sai ya amsa tambayoyi a checkpoints gashi ma’aikatan asibitin ma kamar tsoron mutane suke balle ya kwashi yara su tafi. Ya shafa kai sannan ya sake kallonsu cike da damuwa; da ace gari a bude yake da sai ya wuce da su ya ajiyesu gidan Hajiya to amma ya san ba zai yiwu don zai yi ta bata lokaci a checkpoint. A take dabara ta fado masa. ‘Ku tsaya a nan ina zuwa.’ Ya basu umarni sannan ya fice daga gidan ya turo gate din. Yana fitowa ya karasa gidan su Ummi, yayi sa’a yana tsayawa maigidan yana dawowa daga masallaci. Bayan sun gaisa ya sanar da shi so yake Ummi ta zo ta zauna masa da yara ya je ya kai Khadeeja asibiti. Ya janjanta masa sannan ya shige gidan ya turo masa Ummin. Haka ya sako ta a gaba ya dawo gidan ya bar mata yaran ya ja motar ya nufi Aminu Kano Teaching Hospital dake Kano. ________ Yana zuwa asibitin aka nuna masa gynae emergency inda nan ne ake karbar masu ciki wadanda suke bukatar taimako na gaggawa, nan da nan suka karbet aka fara duba ta; duk da dai su kansu ma’aikatan zaka gane cewa suna cikin yanayi na tsoro saboda Covid19. PAGE 46 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) A nan wajen aka nuna masa benchi ya zauna yayinda ita kuma aka turata a kan gadon marasa lafiya aka shige da ita dakin bincike. Tana kwance a kan gadon yayinda take amsa tambayoyin ma’aikaciyar jinya sai wata ma’aikaciyar wadda taji suna kira matron ta shigo, ma’aiakciyar ta juya tana kallon matron tana cewa ‘Matron wannan fa sai an yi mata scaning, cikin nan na jikinta kamar ficewa zai yi duk da dai tace bata fara bleeding ba ama dai tana jin alamunsa.’ Matron din ta karaso ta tsaya a kanta, tace ‘Ah! Wannan ai Khadeeja ce, wa ya kawota?’ Jin an ambaci sunanta ya sa ta bude idonta a hankali, ta yi murmushi a gajiye lokacin da suka hada ido ta gane wadda ta ambaci sunan nata. Cikin sanyin murya tace ‘Anti Iyami.’ ‘Na’am, Khadeeja. Wa ya kawoki?’ ‘Muatapha ne.’ Ta juya ta kalli abokiyar aikin nata tace ‘’Yata ce ai, itace wadda mukayi biki kwanaki fa yarinyar Habiba wadda nace miki chiildhood friend dina ce.’ Da fara’a tace ‘Aaah! Allah sarki, to abun ya zo kenan haihuwa yakin mata.’ ‘Ai kuwa. Bari na kirawo Dr. Jamil ya zo ya duban min ita sai muje na kaita scanning din muga ko za a iya sallamrta a daren nan.’ Har ta juya zata fice Khadeeja ta riko hannunta, ta juyo tana cewa ‘Akwai wani abu ne Khadeeja?’ Tayi murmushin yake ta goge kwallar da ta gangaro daga gefen idonta tace ‘Kada ki sallameni Anti Iyami, ki yiwa Mommy waya ta zo ta daukeni gida zan tafi.’ Ta dan rankwafo tana shafa kanta tana duban fuskarta tace ‘Ok, kada ki damu, ki samu ki huta tukunna likita ya duba ki. In sha Allahu yanzu zan kirawota ko bata zo ba da safe idan na tashi daga aiki sai na tafi da ke gidan Mommy din. Kada ki damu.’ Ta juya ta fice yayinda Khadijan ta mayar da idonta ta rufe. Tare da likitan suka dawo, bayan ya duba Khaddej aka je aka yiwo scanning tare da Mustaphan aka dawo. Bayan likita ya duba scanning din yace cikin jikinta ya lalace fita zai yi, don haka za ayi mata wankin ciki sannan akwai allurai da ruwa da za a saka mata. Da kansa yaje ya siyo komai ya kawo sannan suka koma wajen Khadeeja tare da matron; a nan Khadeejan take sanar da shi cewa martron kawar Mommy ce. PAGE 47 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ya sake gaisheta cike da girmamawa, bayan ta amsa ta dubi Khadeejan tace ‘Likita ya ce cikin jikinki ya lalace don haka za a yi miki wankin ciki, ga magunguna kuma ya rubuta miki sannan ga drip idan an gama wankin cikin zan saka miki kinga yau a nan zamu kwana da ni da ke.’ Tayi murmushin yake, ta dubi Mustapha tace ‘Ka tafi, ka bar yara a gida. Anti Iyami zata kirawoka idan akwai wani abu tunda ka ga tare zamu kwana ma, zuwa da safe zamu yi waya in sha Allah. Matron ta fice ta basu waje. Bayan ta fice ya matsa kan Khadeejan yana saha fuskarta yace ‘Sannu, kin bani tsoro fa.’ Tayi murmushi. Ya cigaba ‘Kafin safiyar tayi sai ki samu ki yi mi message din duk abinda kike so na taho miki da shi, idan kuma Allah ya sa da safen zasu sallameki ma shike nan sai kawai na zo mu tafi. Na yi maganar abici ma Anti Iyami tace na bari zata kawo miki, but in ana son wani abu kiyi min magana sai na saka miki kudi a account dinki ko transfer ne sai kiyi musu.’ Ya sa hannu a aljihunsa ya zaro wayarta ya mika mata yana cewa ‘Ga wayarki, ba zan kirawoki ba don kada na dameki ko na tashe daga bacci, but please da kin farka ki kirawo ni.’ Ta karba tana murmushi tana cewa ‘Ok, ka gaishe min da su Yaya Afaf.’ Ya fice ya barta a kwance. Yana fitowa ya sami Anti Iyami da abokan aikinta a station dinsu, yayi mata sallama bayan ta karbi lambar wayarsa sannan ya wuce. ……… Tun a daren Anti Iyami ta kirawo Mommy ta sanar da ita halin da ake ciki, sai dai bata gaya mata cewa Khadeejan tace gida zata taho ba. Ta dai sanar da ita cewa tana hannunta idan akwai wani abu zasu ji zuwa wayewar gari. Tana tsaye aka yiwa Khadeeja wankin ciki sannan aka bata daki, ta saka mata drip da alluranta sannan ta hada mata sahyi mai kauri. Ta sakata a gaba bayan ta shanye sannan ta zuba mata shayi da kwai ta cinye sannan ta ajiye mata saucer da kankana da lemon bawo tace ta shanye kafin a jima. Ta sha tambayoyi a wajen Anti Iyami wadda take kokarin gane dalilin da yasa Khadeejan take son tafiya gida; sai dai bata sami komai ba don da a tunaninta ko Mustaphan yana abusing dinta ne. PAGE 48 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) ita kuma ta sanar da ita kawai bata da lafiya ne sannan kuma ga aikin gida da raino wanda yayi mata yawa shi yasa take son ta je gida ta huta. _______ A gajiye ya shiga gidan wajen karfe tara na dare, yana shiga yaran suka taso da gudu gaba daya tun kafin ya gama rufe kofar motar suba cewa ‘Abba ina Anti Khadeeja?’ Ya dauki shukura ya kana hannun Nasreen yana cewa ‘Tana asibita, likita ya kwantar da ita, amma gobe in sha Allahu zan je na taho da ita.’ Ya tattara su suka shige cikin gidan. Yana shiga bayan Ummi tayi masa sannu da zuwa ya sallameta ya fito ya rakata sai da ta shiga gida ta kirawo masa babanta yayi godiya sannan ya koma gida. Sai da ya biya sallar Magriba da Isha’I duk da yunwar da yake ji sannan ya zo ya zauna a parlor a gajiya, ya dubi Afaf wadda take kwance tana yin game a tab dinta yace ‘Afaf dauko min flask da kayan shayi.’ Ta mike ta shiga kitchen din, jimawa kadan ta futo dauke da kayan shayin bayan ta ajiye tace Abba babu ruwan zafi a flask ka jira na dafa maka, wanda Anti ta zuba mun sha shayi dashi mu da Ummi.’ ‘No, barshi kawai. Dauko min zobo ki kawo min ragowar abincin da kuka ajiye na ci, yunwa nake ji.’ Kafin ta bashi amsa Habib yace ‘Abba ai tun kafin ku fita zobon ya bare a nan, ka manta? Kuma dama shi kenan wanda Anti ta zuba ragowar na jiya ne.’ Kafin yace wani abu Afaf tace ‘Abba babu fa abincin ma sai dai ragowar rice and stew, gaba daya dankalin muka cinye kuma da peppersoup din, amma akwai ragowar watermelon a fridge. Ko na dafa maka indomie?’ Ya kalleta yana shafa kai na dan lokaci, ya ma rasa me zai ce mata sabod yanda gaba daya ya jigata saboda yunwa, coke kawai ya samu a asibiti da wani guntun burodi ya ci. Ya zata zasu rage abincin amma wai duk sun ciye. Muryar Afaf ce ta katse shi tana cewa ‘Bari kawai na dafa maka indomie din Abba.’ ‘No, bari na shiga kitchen din na gani.’ Ya fada yana mikewa tsaye. Ya dan dauki lokaci yana kallon kitchen din bai ma san ta inda zai fara ba; har ya dauki tukunya zai dafa indomie sai kuma ya tuna ai akwai cereal, don haka ya mayar da tukunyar ya ajiyeta a muhallinta. Ya zuba ruwan zafi a kettle ya jona PAGE 49 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ya zuba ruwan zafi a kettle ya tafasa ya hada cereal, ya ajiye ya fiddo kankana daga fridge ya yanka sannan ya dauko ya dawo parlor din. Yana zama Shukra ta matso tana dariya ‘Abba zan sha golden morn din.’ Ya bita da kallo da cokali a hannunsa; bata taba bashi takaici ba kamar a wannan lokacin don ya tabbatar sun koshi tunda gashi sun cinye duk wannan uban abincin da Khadeeja ta dafa. Ya dubi Afaf yace ‘Tashi ki dauko cereal, ki hado min da tea flask da komai na hada mata.’ Kafin Afaf ta dawo Nasreen tace ‘Abba nima zan sha.’ Don haka tana kawowa ya sa ta koma ta karo kofi, ya hada musu cereal din su biyun. Babu wadda ta sha cokali uku a cikinsu, suka tashi suka bar masa a nan. Kafin ya gama cinye nasa abincin duk sun fara gyangyadi don haka ya sa Afaf ta dauko musu kayan baccinsu ya shiryasu bayan ya rakasu sunyi brush sun yi fitsari. Bayan sun kwanta sannan Afaf da Habib suma suka shirya, Afaf ta zauna a gefen gado tayi tsuru-tsuru shima Habib sai ya hau katifarsa ya kwanta yana zare ido. Yana tsaye daga bakin kofa yace ‘Yaya dai Afaf? Ki kwanta mana, ko akwai wata damuwa ne?’ Ta jijjiga kai tace ‘Kawai tunawa nayi da Mommy, itama muna bacci ta mutu.’ Ya gaji sosai ga kansa yana sarawa, babu abinda zai iya yi musu na lallashi, ya bude baki a gajiye yace ‘In sha Allahu babu abinda zai sami Anti, kuyi addu’a ku kwanta kuyi bacci kawai.’ Halifa shima ya tashi zaune yana share kwalla ‘Wallahi Abba ni ba zan ma iya baccin ba, Allah ya sa dai kada Anti Khadeejan ma ta mutu ta barmu. Har yanzu idan na tuna Mommynmu sai na yi kuka.’ Kafin yayi magana itama Afafa din hawaye ya fara bin fuskarta, ta sunkuyar da kai ta sa masa kuka harda shassheka. Ji yayi kamar ya dora hannu a ka ya sa ihu; ina ma yaran nana zasu barshi ya huta, yanzu ya zai yi da su? Manyan cikinsu da yake ganin sune ba zasu bashi matsala ba sune suke so su hanashi bacci. Ya karasa ya zauna a kusa da Afaf ya rungumota yana cewa ‘In sha Allahu babu abinda zai sameta, ku daina kuka kuyi mata addu’a Allah ya bata lafiya. Goben nan ma zaku ga an sallamota.’ PAGE 50 A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta fara share hawayenta, Habib wanda shima ya taso ya dawo kusa da ita yace ‘Abba to ka kirawo mana ita a waya mu yi mata sannu.’ Ya zaro wayarsa daga aljihu yana cewa ‘To ai da bana son kiranta saboda kar na dameta don an yi mata allurai, ban sani ba ko harda ta bacci a ciki. Amma bari na kirawota sau daya idan ta daga shikenan idan kuma bata daga ba sai mu hakura da safe ma sake kira.’ Ya lalubo lambarta ya danna mata kira, sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan ta daga. Murya kasa-kasa tace ‘Hello.’ Yace ‘Hello, Khadeeja ba kiyi bacci ba?’ ‘Na dan yi, farkawa dai nayi kuma naji wayar tana ringing. Ai tun dazu aka gama wankin cikin har na dan ci abinci.’ ‘Sannu. Wankin cikin ba wahala kenan?’ ‘Hmmm! Akwai wahala ba kadan ba, kawai dai da an gama aka bawa mutum maguguna sai ya sami relief.’ ‘Sannu. Afaf ce dama ita da Habibi wai ba zasu iya barci ba sai sun yi miki sannu.’ Tayi murmushi mai sauti domin ta ji dadi har cikin ranta, ta tabbatar cewa yaran nan suna kaunarta kuma da zai barta da su komai nasu zai zo da sauki amma shi komai gani yake kamar zata cuce su. Muryar Afaf ce ta katseta bayan da Abbanta ya bata wayar ‘Anti.’ ‘Na’am Afaf, ya aka yi ba kiyi bacci ba.’ ‘Babu komai Anti, ya jikin naki? Ke ya aka yi bakiyi baccin ba? Tayi ‘yar dariya tace ‘Yanzu zan yi Afaf, kuma na sami lafiya don likitan ma ya ce gobe za a sallame ni.’ Suka dan taba hira sannan tayi mata sallama ta mikawa Habib wayar. Bayan sun gama gaba daya ya karbi wayar ya katse yayi mata sai da safe. Ya yi musu sai da safe suka kwanta, har zai kashe fitilar Afaf tace ‘Abba kada ka kashe mana fitilar, in an jima ka zo ka kashe.’ Haka ya bar musu fitilar ya fice. Can bayan awa daya ya gama abinda yake yana so ya kwanta saboda ya gaji ya zo zai kashe musu fitilar, yana kashewa Afaf da Habib suka hada baki a lokaci guda suka ce ‘Abba kada ka kashe fitilar.’ Da mamaki yace ‘Kai! Me kuke baku yi barci ba?’ Afaf tace ‘Abba to ni dai na kasa bacci, da ma zaka taya mu kwana.’ Habib yace ‘Eh wallahi Abba don ni wallahi tsoro nake ji.’ Takaici ya kamashi, to yanzu ya zai yi? Taya su kwanan zai yi ko kuwa barinsu zai yi a haka su PAGE 51 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Takaici ya kamashi, to yanzu ya zai yi? Taya su kwanan zai yi ko kuwa barinsu zai yi a haka suna zare ido yaje ya kwanta? Wannan wacce irin fitna ce a daren nan gashi ya gaji. Baya son barinsu su kadai don haka ya wuce dakinsa yaje ya shirya ya rufo gidan sannan ya dawo nan dakin; katifar Habib karama ce ya san ba zata ishesu ba don haka kawai ya gyarawa Nasreen da Shukra kwanciya ya dan sami waje a gefen gadon ya kwanta bayan Khadeeja ta kwanta a daya gefen. Yayi addu’a ya tofa musu sannan yace kowa ya rufe idonsa kada ya sake jin motsinsu. Tunda ya kwanta yake jin wani dan doyi haka, idan iska ta busa sai ya ji kamar doyin ya buso cikin daki idan iskar ta wuce kuma sai ya daina ji. A haka bai san lokacin da bacci ya daukeshi ba. ‘Subhanallahi!’ ya fada bayan yayi firgigit ya tashi, ya kai hannunsa ya taba inda yake kwance daidai duwawunsa yaji shi a cikin ruwa sosai. Ya daga hannun yana kallo da tsananan mamaki ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.’ Ya sake fada a fili. to fitsarin kwance yayi ko me? Gashi yaran duk sunyi bacci balle yace wni ne ya zuba masa ruwa; tunda shi dai ya san baya fitsarin kwance. Motsin Shukra da yaji a kusa da shi ne ya tabbatar masa da cewa itace tayi fitsarin, ya mika hannu ya tabata ya jita a jike amma tana ta baccinta hankali kwance. Ya kai hannu zai janye Nasreen daga kusa da ita ya jita itama a jike ‘Tab!’ ya fada a fili. Kenan duka su biyun suke fitsrin kwance ko kuwa yau suka fara? Don shi tunda Khadeeja ta tare a gidan nan sau daya ya taba ji an ce Shukra ta yi fitsari. Ya kalli Afaf wadda ita tana can ta takure a karshen gadon tana baccinta, ya danna wayarsa ya kalli lokaci yaga karfe biyun dare. Ba zai iya tashin yaran nan ba

Chapter 5 of 25