Share this page
1 / 10
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ❤️💕SO NE SILA❤️ 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* K'arkad'i banyadda ba ban Kuma laminta wani ko wata ya ya juya min labari ba ta kowa ta fuska ba tare da amince wa ta ba, yin hakan kuskureni babba dan haka a kiyaye👌🏻 Wannan labarin k'irk'irarran labari ne, ban yi da niyyar cin zarafin kowa ba. Page 1 & 2 Bismilahirrahamirrahim. Babbar makaranta ce ta mata zalla wato ( boarding school) ko wata yarinya ka kalli fuskarta daga cikin 'yan matan murna ce kwance akan fuskokinsu bisa ga alama yau suke candy. 'Yan mata ne ko wacce d'auke da jakar kayanta, wasu Kuma sun tsaya suna hotuna, wa ta budurwa da ga cikinsu na gani gefe guda tsaye ta na ta kallansu, d'aya daga cikin 'yan matan dake hotuna ta kalli budurwar dake tsaye kusa dasu ta ce. "Ke Hafsat ba za ki zo a yi Hoton da ke ba ne?." Wata daga cikinsu ta ce. "Ya dai kamata wallahi, dan ko watarana kika d'akko kin tunamu in da kin san dai had'uwa za ta yi mana wuya". Wadda aka kira Hafsat murmushi ta yi ta ce. "Tom ni dai ko ban yi hoto ba dukkanku ba zan manta fuskokinku ba ha ba tunfa a j.s 1 ta ya ma zan manta ku, kuma yawan cinku duk ina da hotunanku". D'aya daga cikin 'yan matan ta ce. "Kai Hafsat yau fa saura kwana goma sha hud'u bikinki, daga kin yi aure zaki manta da mu" Fadila ce ta yi saurin cewa. "Yauwa dan Allah ku ruk'e alk'awari dan Allah duk kuzo bikin nan kunga lokaci ya kure ba zamu samu halin zuwa gidajanku ba shi ya sa na baku cingam anan." Sun dade suna hotuna kafin su ka yi sallama kowa ya Kama gabansa, dan dama kusan duk an watse. Da ya ke makarantar bak'in titi ta ke, hakan ya sa su Hafsat suka fito suna naiman motar da za ta kaisu Bakori. Fadila kallan Hafsat ta yi ganin ba yadda ta saba ganinta ba ta ce "Hafsat wai lafiya na ganki wata kala?." Hafsat kallan Fadila ta yi kafin ta ce cikin sanyi. "Bakomai haka nan nake jina wata iri yau...." Motar da ta tsaya kusa da su ne ta sa Hafsat yin shiru. Yaron motar kallansu ya yi ya tambayesu ina za su, Fadila ce ta bashi amsa Bakori, bude musu motar ya yi suka shiga ganin yamma ta yi. Bayan sun shiga motar sun zauna Fadila ta kalli Hafsat ta ce, "Hafsat na manta ban ba su Husna cingam ba Allah ya sa kin basu?." Duk maganan nan da Fadila ke yi Hafsat ko hankalinta na kan wasu wata mota da tunda suka taho ta lura motar na binsu, kafin ta ankarar da Fadila motar ta sha gabansu. Wasu kosassun matasa ne guda uku suka fito daga motar suka sha gaban wannna motar da su Hafsat ke ciki. Daya daga cikin matasan Wanda daga ganin fuskarsa ba alamun imani ga bin diga da ke rik'e da hannunsa cikin hargagi ya ce. "Duk ku fito". Duk Wanda ke motar sai da ya fita tsayawa ya yi yana kallansu d'aya bayan d'aya, Kafin ya dakko wayarsa da ke rori ya kanga a kunnansa. Bin wayar ya yi da kallo yana kallan wani hoto wanda da alama yanzu aka tura masa shi, ya dade yana kallan hoton kafin ya dago kansa Yana bin duk Wanda ke cikin motar da kallo. Hafsat ya nuna ya ce "You follow me." waige waige Hafsat ta fara yi kafin ta rike hannun Fadila katakam tana kuka jikinta ko ina na rawa. Tsawa ya daka ma Hafsat Yana nufar inda take yana rike da bindiga ya ce "Nace ki bi yo ni ko" Hafsat duk jikinta rawa ya ke Fadila ta k'ara rik'e ma hannu katakam tana kuka sosai ta kasa matsawa ko Ina. Ganin ba za ta zo ba wannan guy din dake tsaye ya rufe rabin fuskarsa da ba alamun tausayi a cikinta, ya fara takowa zuwa inda suke tsaye. Hafsat ko ganin ya kusa zuwa gunta ya sa ta rungume Fadila ta na kuka sosai. Yana k'arasowa kusa da i'ta ya d'ora mata kan bindiya ya ce. "Muje." Fadila itama k'ara rik'e hannun Hafsat ta yi ta ce. "Dan Allah ka rufa ma ta ashiri, wallahi yau saura kwana goma sha hud'u bikinta dan Allah k..." Nunin da ya yi ma Fadila da bindigar hannunsa ya sa ta yi shiru. Haka ya tasa k'eyar Hafsat su na ji suna gani ya shigar da ita mota ya ja ya tafi yabar su a gun tsaye. Fadila na ganin an tafi da 'yar'uwarta kuma aminiyarta, Fadila ta yanke jiki ta fad'i agun a sume. Allah sarki fasinjojin motar ne su d'auki Fadila suka sata a motar su ka tafi da ita suna jimamin abinda ya faru, tare da mamaki ganin sun dauki mutum daya kacal duk yawan mutanan motar. Hafsat ko cikin motar ba abinda ta ke fad'i sai "Wayyo Allah na dan Allah ina zaku kaini wayyo Allah na. Can kuma ta fara salati da addu'a'in naiman tsari. innalilahi'wa'inna ilaihirraju'un, Allahumma rahamatuka'arju, falatakilni'ilanafsi d'arfata'ainin wa islihili sha'ani kullahu la ila ha'illah'anta" Ya kawiyu ya jabbaru." Haka Hafsat ta yi ta mai-mai tawa. Tafiya sosai su ka yi kafin ta ga sun nufi wani gida. tsayawa ya yi ya na horn, can a ka bud'e get d'in gidan wani kyakkyawan saurayi fari ne amma ba fari can-can ba k'arfafa ne sosai. Yana zuwa ya sa hannu ya bud'e murfin motar, gefan da Hafsat ta ke ya bud'e, Hafsat da saurinta cikin furgita da abinda ta ke gani ta fito da ga motar, tana bin gidan da kallo cikin tsananin tashin hankali da furgici, wata uwar kara Hafsat ta yi wadda dukkansu sai da suka toshe kunnuwansu. Daya daga cikin wa inda suka kawo Hafsat kallan guy din da suka iske a gidan ya yi ya ce "Oga na cika aiki." sarama juna suka yi sannan ya shiga motar ya ja ya suka tafi ya bar Hafsat nan dake tsaye tana zare ido cikin tsantsar tsoro da furgicin da take ciki. Wannan matashin kuwa, in da Hafsat ta ke tsaye jikinta ko ina rawa yake ya nufa, kallanta ya yi kafin ya ce, "Muje." Hafsat ga ba d'aya ganinta ya d'auke duhu-duhu ta ke gani jin kalmar da ya fura ta muje, daga k'arshe ta fad'i gun a sume. Tsaye ya yi yana kallan Hafsat kafin ya nan nade hannun rigarsa ya sabata ya nufi da ita cikin gidan. Wata kofa ya bude sai ga wani haddan falo ya bayyana, kallo d'aya za kai mai ka san an kashe dukiya aciki. Wani d'aki ya bud'e d'aya daga cikin dakunan falon ya shigar da Hafsat ciki ya kwantar da ita, kafin ya ciro waya ya yi kira, bisa ga alamu dai likita ya kira ya duba Hafsat da ke kwance ba ta san in da kan ta ya ke ba. Tsaye ya ke akanta ya yi nisa cikin tunani yana ganin abin da ya yi fa kamar bai kyauta ba, sai dai zuciyarsa ta tabbatar mai bashi da wata mafita sai wannan. Kallo ya Kai kan Hafsat dake kwance. Ya na nan tsaye ya na aikin kallanta wayar shi ta yi k'ara yana d'auka ya ce. "Ok, am coming." Fita naga ya yi sanna sai ga shi da wani sun shigo tare Wanda ko ba afad'aba daga gani likita ne, likitan kallanshi ya yi ya ce, "Muhamoud, wannan fa ? Ko Ka yi aure bamu da labari ne?." Rasa abinda zai ce mai ya yi dan haka sai ce mai ya yi " Eh, dan Allah du bata ba ta da lafiya ne." bayan likitan ya gama dubata, kallan Mahmoud ya yi ya ce. "Kamar akwai abinda ya furgitata ko, koma dai meye za ta iya farkawa ko da yaushe, amma gaskiya ka kiyaye dan ko meye ya so yin affecting heart na ta, kuma irin wanna ya na kawo heart attack." Magunkuna ya rubuta ya mik'a ma Mahmoud ya ce, "ka siyo mata wa innan ta sha za ta ji dad'in jikinta." Muhmound na nan zaune har aka kira magriba amma Hafsat ba ta farka ba, abin tsoro ya so ba shi dan haka sake kiran likitan ya yi ya fad'a mai har yanzu fa ba ta farka ba". Likitan ce mai ya yi karya damu zata farka, amma in ta Kai 3 hours nan gaba bata farka ba ya kirasa. Mahmoud fita ya yi ya je ya siyo ma Hafsat magungunan da likitan ya ce mai ya siyo ma ta ta sha. Mahamoud na fita Hafsat ta farka daga doguwar sumar da ta yi, kai ta d'aga ta na kallan d'akin da ta ke, zumbur ta mik'e tana Kuma bin dakin da kallo, sai yanzu abinda ya faru da ita ya dawo mata akai, kai ta d'aga tana kallan d'akin iri d'aya da na mafarkin da ta yi ana gobe za su yi final Exam, kai Hafsat ta dafe ta fasa wata uwar k'ara wadda dai-dai Mahmoud ya shigo falon ke nan, ya dawo daga siyo ma ta magungunan. Mahmoud da saurinsa ya k'araso bedroom d'in da ya ajeta, sai dai me ko da ya zo akakkafe ya ga idonta, wanna karan abin ya tsorata shi ga kashedin da likita ya yi mai. Kiran likitan ya yi ya fad'a mai halin da ta ke ciki". Likitan ce mai ya yi gaskiya sai dai ya zo asibitinsu ya sa mai dan yanzu yana aiki ne. Mahmoud ba yadda ya iya d'aukar Hafsat ya yi ya sata a mota ya kaita asibitin da Aminu ke aiki. Bayan ya karasa Asibitin Waya ya kira ya sanar da shi ya k'araso asibitin da ya ke private Hospital ne hakan ya sa cikin lokaci Aminu ya karaso. Duk wa ni taimako da ya kamata doctor Aminu ya ba Hafsat shi, bayan ya gama gano asalin matsalarta. Kallan Mahmoud ya yi ya ce. "Mahmoud akwai fa damuwa, dan gaskiya yarinyar nan Condition d'in da ta ke ciki fa akwai da muwa dan yanzu haka zuciyarta na da k'arancin buguwa, dan haka ya zama dole akiyaye abinda ke je fa ta a wanna halin, dan ba zan b'oye ma ba idan har ta sake shiga irin wannan halin da ta ke yanzu haka tom gaskiya fa zata iya wuce wa daga can ma'ana idan har zuciyar mutum ta kai irin wannan ma takin tom dole ne fa akiyaye yawan abinda ke sasa wannan halin." Mahmoud da fa likitan ya yi, ya ce. "Aminu yanzu me ye mafita?." Tom irin matsalar nan dai likitocin duniya sun ta fi akan abu biyu zuwa uku ke je fa mutum acikinsa, na farko damuwa mai tsanani, ko razana da wani abu, ko ganin wani abun Wanda ya tsorata mutum sosai". Shiru Mahmoud ya yi ya na tunanin ma fi ta. Likitan dafa Muhamoud ya yi ya ce, "Ba damuwa karkadamu bari in duba wani nan in dawo." Doctor Aminu fita ya yi ya rage daga Muhmoud sai Hafsat da ke kwance Muhmoud gajiya da tsayuwa ya yi ya zauna. Tsananin sanyi A.C ya farkar da Hafsat daga sumar da ta yi, inda ta farka da wani zafaffan ciwan kai, rik'e kanta ta yi jin yadda ya ke juya ma ta kamar zai tsinke. Muhmoud da sauri ya tashi ya yo kanta gudin karta tona mai asiri. Hafsat ko ganinsa da ta yi ya sa ta bud'e baki za ta yi ihu, da sauri Muhmoud ya sa hannu ya rufe bakinta, yana girgiza mata kai Yana wage-waige, kafin ya sa hannu ya ciro 'yar k'aramar bindigar da ke ajjihunsa ya saitata a kan Hafsat ya ce. "Kin san Allah idan har kika sake ki kai min k'ara sai na d'auke kanki a'asibitin nan." Kai Hafsat ke juya ma Muhmoud alamun ba za ta k'ara ba tsabar tsoran bingidar d ya saitata da ita da take yi. Muhmoud kasa cire hannunsa abakin Hafsat ya yi gani ya ke kamar za ta tara mai mutane, dan haka tun kafin ma Aminu ya zo ya zargesa tasa k'eyarta ya yi da bindiga har zuwa wajan motarsa da ya ke dare ya yi babu muta ne kuma dama can gefe ya yi parking d'in motarsa. Tafiyar da ya yi ba ta fi ta minti goma ba ta kai su gida, ka san Cewar dare ya yi ya sa abincin da ya siyo ma ta tun a'asibitin ya ba ta ya nuna ma ta d'akin da ya kaita d'azu ya ce. "Ki shiga dakin nan ki kwanta kafin ga abinci nan kici sai ki yi sallah ki kwanta, da safe za mu yi magana kin ji?". Hafsat kallan shi ta yi da idanunta da suka cika da hawaye ta ce. "Dan Allah ka taimakamin ka fad'amin waye Kai? Me na yi muku da kuka kawoni nan kuka aje? " Muhmoud kallanta ya yi ya shafi sajan fuskarshi ya ce. "Babu abinda ki kai mana, yanzu kinga dare ya yi kuma kina buk'atar hutu dan haka ki ci abinci ki kwanta gobe za mu yi magana" Ni dai wallahi ba zan ci abincin nan ba har sai kun mai da ni in da kuka d'akko ni, dan Allah ku taimakamin kurufamin asiri kubarni in tafi." Muhmoud kallan Hafsat ya yi baice mata komai ba sai dai a zuciyarsa ba ya jin dad'in kallan Hafsat a irin halin furgicin da ta ke, hannuta zai kama da sunan ya kaita bedroom d'in da ya nuna ma ta tak'i shiga ta yi saurin ja da baya ta na cewa. "Wayyo dan Allah karka tab'ani!." Cak Muhmoud ya tsaya ya na kallanta, kafin ya nuna Mata dakin da ya kaita dazu ya ce. "Baki son in tab'aki ko?." Kai Hafsat ta d'aga mai. "Ok, in dai baki son in tab'aki tom d'auki abincin nan ki je ki ci". Hafsat da sauri ta d'auki abincin ta shiga d'akin da ya nuna ma ta, Sai dai Hafsat ko da ta je aje abincin ta yi dan ita tunaninta ya bata abincin tana ci za'a shanye jininta, ko kuma ta b'ace dan haka can gefe ta aje abincin, ta tashi tana waige-waigen in da za ta ga toilet. In da ta ke tunanin toilet ne ta shiga, ta yi fitsari tare da alwallah. Hafsat Sallah kusan ta kwana yi tana rok'on Allah ya fitar da ita daga hannun azzalumannan, ahaka dai bacci b'arawo ya d'auki Hafsat. Washegari kasancewar sai gaf da asuba Hafsat ta yi bacci hakan ya sa ba ta farka ba har sai da Mahmoud ya shigo d'akin da tea d'insa a hannu, dan tunaninsa ya basa jiya da wuya in ta ci abincin da ya bata. Hafsat kwance ta ke ak'asa koma sanyi k'asan ba ta ji, in da ta ke kwance Muhmoud ya k'araso bubbuga kafarta ya yi da hannunsa ahankali , dan sosai ta bashi tausai ganin in da ta kwanta. Hafsat ko jin ana bubbugata furgigi ta tashi tana ja da baya, Muhmoud toilet ya nuna ma ta ya ce. "Ki wanke bakinki sai kisha tea ko?". Hafsat kallan shi ta yi ta ce. "Allah ba zan ci ko mai ba, sai kun mai da ni in da kuka d'akko ni". Kamar za ta yi kuka haka tai maganar". Muhmoud bindigarsa ya ciro ya nunata da ita ya ce. "Idan har kika sake musu dani sai na d'auke kanki yanzun nan". Hafsat har tana tuntub'e ta shiga toilet din ta wanke bakinta ta fito can nesa da shi ta tsaya". Muhmoud d'aukar cup d'in tea d'in ya yi ya bi ta da shi ya ce. "Amshi kishanyeshi dukka." Hafsat amsa ta yi ta kafa kai tana sha tana addu'ar da duk ta zo bakinta dan ita batayarda da tea d'in ba, Allah sarki ba ta yi rabiba ta ruga da gudu toilet d'in ta kama amai". Bayan ta gama aman tana juyowa ta ga Muhmoud bayanta ta har ta gama aman yana tsaye yana kallanta, bayan ta gama aman ne, ya d'akko sauran tea d'in ya ce amshi kisha?." Kai Hafsat ta girgiza mai ta ce. "Bazan sha ba, kuka sheni in huta dan Allah, sai dai in kasheni za ka yi amma ba zan sake cikin komai ba a gidan nan ku kasheni ya fi min sauk'i dan Allah ku kashe ni." Ganin yadda Hafsat keta wani irin abu kamar mai iska tana akasheta ya sa Muhmoud ya d'akko ruwa zai shafa mata wai shi atunaninsa ta dawo hayyacinta ganin yadda take magana". Ita ko Hafsat ya na d'akko ruwan ta kuma furgicewa dan ita a tunaninta ruwan sihiri ne aiko yana watsa mata ta sumemai. Muhmoud da kyar ya samu Hafsat ta farfad'o, sai dai hannunta dafe da kanta, cewa ta ke. "Dan Allah karku kasheni, me na yi muku?." Muhmoud jin haka rasa abin da zai cema Hafsat ya yi hakan ya sa ya d'auki motarsa ya fita daga gidan. Tafiya ta ke agajiye hakan ya sa Muhmoud sai horn ya ke ma ta amma ba ta ji ba, cikin b'acin rai ya lek'o daga motar yana kallanta ya ce. "Haba baba bakya jin horn ne?." Wadda aka kira da baba kallan Muhmoud ta yi ta ce. "Wallah d'annan na gaji ne, gashi a Katsina ban san ko ina ba na ce dan Allah koka san Unguwar ma su kud'i?." Murmushi Muhmoud ya yi ya ce "Na sa ni baba, shigo muje". Baba sai da ta shiga kuma tsoro ya kamata kallan Muhmoud ta yi ta ce. "Kai sauke ni ina za ka kai ni? ko dan kaga ban san gari ba? Tom nidin da kake gani ba sakarar tsohuwa ba ce, da wayewata bare ka yi min wayau ka saceni dan haka tun kafin in b'atama rai ka sauke ni ko kuma in tarama muta ne Wallahi a gabana sulugudeka kamar jaki ban cewa su yi hakuri, gara ma ka rufa ma kanka asiri ka tsaya in sauka in ba haka ba ka dakko ruwan dafa kanka" Muhmoud ko kallan baba be yi ba bare tasa ran zai sauke ta." Baba ganin haka ido ta fara zarewa tana cewa "Haba dan albarka Wanda ya gaji albarka dan Allah yaro ka yi hak'uri ka saukeni idan ka dubeni da kyau ko ka saidani walllahi ba kudi zanyi ba ..." maganar baba mak'alewa ta yi ganin Muhmoud ya yi horn a wani gida Wanda daga ganin gidan gidan yankar mutane ne a tunaninta" Ihu za ta yi Muhmoud ya yi saurin d'akko bindigar jikinsa ya d'ora ma baba akai ya ce "Baba ki na yin ihu zan harbeki gara ma ki yi shiru" Allah sarki jikin baba ko ta ina rawa yake cikin furgeci ta ke cewa. "Dan Allah yaro karka ka karasa gawar da ba taka ba, kawa Allah ka yi hakuri, idan ma Kai dan kinmashin ne (kidnapping) Wallahi ni talakace kurmus amma zan iya yi maka alkawari ka biyoni bashi in yi aiki in tara maka kudin fansarka in baka." Muhmoud k'asa ya yi da bindigar yana murmushi kafin ya ce "Tom baba na fasa harbeki, amma bisa ga wani sharad'i in kinyarda za ki abinda na ce?." Allah sarki baba ganin bindiga ba tare da tunanin ko wana irin sharad'i ba ne ta ce. "Yaro tunima na yi na gama komeye fadi zan yi dan Allah karka kasheni ina jinka" Muhmoud k'ara gyara tsayuwa ya yi ya ce "Baba ibinda zan sa ki idan har aka samu kuskure tom zan harbeki ne kin yadda?" Kai baba ta d'aga ta ce. "Haba yaro ko Ina aikata kuskure Kai ya za ai in aikata maka za a yi komai kake so babu kuskure ciki na yadda na amince ni dai rokona karka kasheni kasan ko Allah na kunyar mai furfura ka kalli furfurar kaina ka kauda bindigar nan in bar ganinta dan Allah." Muhamoud maida mingidar ya yi ya ce "Baba mu shiga ciki zan sanar dake aikin da za ki yi min✍🏻 Littafin SO NE SILA idan kina sonsa daga farko har ƙarshe ki kasance a channel din Fadila Sani Bakori Novels Saboda anan kawai zan rika posting nasa 👇🏻 https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r COMMENT AND SHERE PLEASE 🙏🏻 Fadila Sani Bakori ce ❤️💕SO NE SILA❤️ 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* Page 3 & 4 Mahmoud kallan baba ya yi ya ce "Baba akwai wata yarinya da za ki rik'a kular min da ita cinta, shanta, motsinta da komai nata, ma'ana so na ke ki za me mata Uwa duk wa ni abu da Uwa ke ma 'yarta so na ke kirik'a mata shi idan kuma har aka samu kuskure to fa baba anan za ki k'arashe rayuwarki" Baba cikin rud'ewa ta ce "Ba za ma asamu wata matsala ba yaro zan kula da ita kamar yadda ka ce." Haka Muhmoud ya

Chapter 1 of 10