Share this page
2 / 10
ta sa k'eyar baba har izuwa falonsa. Bayan sun shiga Kallan baba ya yi ya ce, "Baba ga d'akin da za ki zauna nan ita kuma yarinyar kinga d'akin da ta ke can, yanzu Baba ga abinci ki kai mata dan Allah ki tabbata ta ci saboda ba ta ci komai ba" Ita dai baba kallan Muhmoud ta ke yi kawai dan har yanzu zuciyarta ba ta kwanta da shi ba, haka dai ta daure zata dauki abincin da mahmoud ya ce ta kaima Hafsat. Mahmoud kiran baba ya yi har zata tura kofar dakin da Hafsat ke ciki ya ce "Baba dan Allah ki kula da ita da kyau zan rink'a biyanki, idan kuma aka samu akasin haka kamar yadda na ce miki baba tom anan gidan za ki k'arashe rayuwarki" In sha Allahu ma haka ba za ta faru ba yaro" Yauwa baba na gode, sannan Ina so ki nuna mata ni danki ne" kai Baba daga ma Mahmoud ta dauki ledar abincin Hafsat ta tafi cikin tunani. Baba cikin fargaba ta tura dakin da Hafsat ke ciki ta shiga. Zaune ta iske Hafsat ta yi ta gumi, baba da sallamarta ta karasa inda Hafsat take zaune. Hafsat ko da saurinta ta d'ago kanta jin muryar mace, Kallan-kallo suke ma junansu kafin baba ta duka daidai kusa da Hafsat ta ce. "Sannu ko, ta shi ki ci abinci kin ji?." Hafsat kallan baba ta yi bata ce komai ba. Baba cikin kakaro murmushi ta dafa Hafsat ta ce. " 'Yata tashi ki ci kin ji dan Allah?." Hafsat kalan baba ta kuma yi kafin ta ce "Wannnan dan fashin danki ne hala?" Baba da fe k'irji ta yi ta ce. "Ke 'yar nan dan Allah d'an fashi ne dama?." Hafsat tsaya wa ta yi kallan baba ganin yadda ta rud'e ta ce "Baba ba ki ban amsar tambayata ba na ce d'an fashin nan d'anki ne?." Baba k'asa-k'asa ta yi da murya gudin Kar dan fashi ya jita ta ce. "Dan Allah yarinyarta ya ki ke da shi ne?" Hafsat b'ata fuska ta yi ta ce. "Baba ni fa baki ban amsata ba har yanzu na ce ya ki ke da d'an fashin nan Kuma kin zo kina tambayata bayan tare na ganku?" Baba k'asa-k'asa ta sa ke yi da murya dan kar Muhmoud ya jita ta ce. "Wallahi yarinya ba yadda na ke da shi wajan yarona na zo nan Katsina na hadu dashi ganin kamar na kirki ne ya satoni ya kawoni nan wai in kula dake idan na kuskure a gidan nan zan karasa rayuwata." Baba ta ida maganar tana dadewa da kuka, komai ta tuna Kuma ta yi sauri ta toshe bakinta tana waige-waige. Hafsat shiru ta yi tana kallan baba kafin ta ce. "Gaskiya baba kin yi ganganci ya za ai ki biyoshi bi ki san shi ba" Wallahi yarinya fuskar shi kama ta yi min da ta muta nan kirki" Allah shi kyauta Hafsat ta ce. Baba ko kallan Hafsat ta yi ta ce. "Yarinyata baki fad'amin yadda ki ke da shi ba?"Baba ba yadda ni ke da shi sato ni ya yi ya kawo ni nan gidan ya aje ina kan hanyar da wowa makaranta, yanzu haka yau saura kwana goma sha uku bikina, nasan Iyayena na can cikin tashin hankali da damuwa suna tunanin halin da na ke ci ki" Hafsat ta idasa maganar cikin kuka. Baba goge ma Hafsat hawayanta ta yi ta ce, "Ki yi hak'uri kin ji, yanzu ga abinci nan da ya ban ya ce in kawo miki, dan Allah ki d'auka ki ci, addu'a za mu taru mu yi ta ta yi" Hafsat kallan baba ta yi ta ce. "Baba ba zan iya cin abincin nan ba ki ajeshi kawai" Duk yadda baba taso Hafsat ta ci abincin k'in ci ta yi". Baba kallan Hafsat ta yi amarerece ta ce. "Yarinyata so kike in dauwama agidan nan ko kamar yadda ya ce?"baba ki mai da mai abincin shi Allah ba zan ci ba." Baba ba yadda ta iya haka ta d'auki abincin ta nufi falon da shi sai dai ba ta ga Muhmoud ba, hakan ya sa ta sa mu guri ta tsugunna da abincin a hannunta. Baba na nan tsugun ne sai ga Muhmoud ya fito daga bedroom d'insa, kallan baba ya yi ya ce. "Baba ya naga abincin ba ta ci ba ne?"Eh yarona ba ta ci ba" Muhmoud amsar abincin ya yi ya ya shiga d'akin da Hafsat ta ke. Zaune ya iske ta hannunta d'aya ta yi ta gumi. Muhmoud tsugunnawa ya yi kusa da Hafsat ya sa hannu cire ma ta ta gumin, sannan cikin lallashi ya ce. "Ki yi hak'uri kinji, dan Allah ki ci abinci na san kina jin yunwa" Ya mik'a ma ta abincin. Hafsat kallan shi ta yi ta ce. "Ba zan ci ba wallahi har sai ka fad'a min dalilin satoni da ka yi ka kawo ni nan" Muhmoud kallanta ya yi ya yi murmushi kafin ya ce. "Hafsat, ki dauka nine kaddararki kamar yadda kika zama kaddarata, bawai na kawo ki nan dan cutar dake bane, na kowoki ne dan bani da wata mafita ne sai dai in yi hakan. Hafsat Ina so in zama masoyi miji a gareki dan Allah cikin amincewarki ba wai in tursasaki ki amince da aurena ba?" Hafsat sai yanzu ta dago ta kalli fuskarsa jin abin da ya ce kafin cikin rsantsar mamaki ta ce "Ka zama masoyina kamar ya kenan? Ban gane ba?." Hafsaar ta idasa maganar a rude. Muhmoud kamar mai ciwan ba ki ya ce "Hafsat, ina sonki so na hak'ik'a, so mai tarin yawa, na bi duk hanyar da na ke gani zan iya samunki amma abun ya ci tura, na sanki a kankanin lokaci a lokacin da kike gaf da shiga gidan wani, nasan abinda na yi ban kyauta ba amma ba daga ni bane daga zuciyata ce nakasa control dinta ta gane abinda zan aikata kuskure ne babba" Hafsat tashi ta yi daga zaunan da take ko inda Muhmoud ya ke ba ta kalla ba ta ce. "Ba sai ka fayyace min wacece zuciyarka ba iya haka da ka yi ya isa na fahimci kalar zuciyarka wadda kanta kadai ta sani, bata tunanin halin da iyayena da masoyina da duk wasu masoyana za su shiga? Tom ka yi gaggawar sanar da zuciyarka ta aikata babban kuskure sannan ta nemo masoyiyarka tun wuri tun kafin lokaci ya kure maka amma bani ba, ni Hafsat saura kiris in zama matar wani matar aure, ko ba haka bama ba zan yi soyayya da mutum irinka ba bare Kuma har in aureka, kai bari ka ji da in auri mutum irinka Wallahi gara in mutu ba aure." Muhmoud kallan Hafsat ya yi kafin ya ce "Ai ko za ki k'arashe rayuwarki a gidan nan." Hafsat cikin kuka da jin abinda ya ce ta ce "Ta Allah ba ta kaba, azzalumi macuci in Allah ya yadda sai ka na ga karshenka." Muhmoud shiru ya yi sai dai kallo daya za Kai mai ka fahimci maganganuta sun bata mai rai sosai. Amma sai ya danne ya ce "Ki d'auki abincinki ki ci" Ba zan ci ba, ba zan ci ba na ce!!." Muhmoud abincin ya d'akko ya matsa da shi kusa da ita ya ce. "Ni ba macuci bane kamar yadda kike zato watarana nasan zaki fahimci haka, ki daure ki ci abincin nan ko da kadan ne Kar ulcer ta kama ki." Hafsat ci gaba da kukanta ta yi, Muhmoud ko ganin ba za ta ci abincin ba ya sa ya d'ibo ya kai bakinta" Hafsat bige spoon d'in ta yi" Muhmoud kallanta ya yi ya ce. "Ki amsa ki ci idan ba haka ba zan Kira wa inda suka kawo ki nan su yi miki duransa." Kai Hafsat ta d'aga da idonta da ya yi ja tana kallan Muhmoud shima Muhmoud d'in ita ya ke kallo ya ce. "Da gaske nake idan Kuma bakya son nasu sai in baki da kaina, dan wallahi sai kin ci abin cin nan." Hafsat d'aukar abincin ta yi tana ci tana kuka". Muhmoud kallanta ya yi cikin kasa da murya ya ce "Dan Allah ki bar kukan mana kirki shak'e" Ya na fad'ar ha ka ya fita dan jin kiran sallar magriba da ake yi. Muhmoud ko da ya fita gidan ba shi ya dawo ba sai da akai sallar issha'i, daga can kuma ya biya ya yo masu baba siyayya. Baba ko na ganin Muhmoud ya fita d'akin Hafsat ta shiga da saurinta jin kukan Hafsat, baba kallan Hafsat ta yi ta ce. "Yarinyata lafiya dai ko me ya yi miki?" Hafsat kallan baba ta yi ta ce "Baba wai sona ya ke kuma in dai ban so shi ba anan zan k'arashe rayuwata." Baba zama ta yi kusa da Hafsat ta kamo hannun Hafsat d'in ta ce, yarinyata shawarar da zan baki in dai har ki na so ki bar gidan nan ki amice mai in da in yaga ki na son shi d'in zai bari ki koma wajan Iyayanki tom me zai hakana ki mai son k'arya ki nuna mai kina sonsa da gaske Allah bashi duk san da ya maida ke gaban Iyayanki shi ke nan." Duk maganar da baba ke yi Mahmoud na jinta zai shigo d'akin ke nan ita kuma ta fara ba Hafsat wannan shawarar. Baba ko jin Hafsat ta yi shiru kallan ta ta yi ta ce. " 'Yata baki ce ko mai ba?." Baba na tsane shi sosai Allah ni ba zan iya ko da soyayyar wasa da shi ba" Muhmoud cikin damuwa da jin furicin Hafsat ya tura d'akin ya shiga da ledoji guda biyu a hannunsa. ko kad'an bai nuna masu ya ji abinda su ka ce ba, baba ya mik'a ma d'ayar ledar hannunsa ya ce. "Baba ga wannan duk wani abu da zaku buk'ata akwai ciki" d'ayar jakar kuma ya ajeta gaban Hafsat ya ce. "Ke kuma ga wanna ki yi amfani da kayan ciki" kafin ya maida kallanshi kan baba ya ce "Baba tafiya ta kama ni gobe, amma kwana uku zan yi in dawo". Baba addu'a ta yi ma Muhmoud wadda ba takai zuciyarta ba. Mahmoud Mai da kallan sa ya yi kan Hafsat ya ce. "Sai na dawo"Allah ya sa akasheka acan." Cewar Hafsat. Muhmoud ja ya yi ya tsaya dan addu'ar ta ta ta bashi tsoro sosai ya kasa matsawa, kallanta ya yi baice komai ya juya ya fita. Bayan tafiyar Muhmoud baba fad'a ta yi ma Hafsat akan addu'ar da ta yi ma Muhmoud ta ce. "Haba ke da kike burin barin gidan nan kike mai irin addu'ar nan, nima duk addu'ar da kika ji Ina yi mai a zuciyata cewa nake ba ameen ba, sannan idan ya mutu acan d'in mu kuma mu k'arasa rayuwarmu anan ke nan?" Baba hatta gama maganarta Hafsat ba ta tanka mata ba. Baba kallan Hafsat ta yi ta ce. "Ki daure ki yi wanka naga dogayan riguna ne ya siyo mi ki sai ki canza" Nan dai Hafsat ta ta shi ta shiga toilet d'in ta watsa ruwa ta cire uniform d'in da ke jikinta dama duk ya yi datti. Yau satin Muhmoud d'aya da tafiya ke nan, tun Hafsat na kuka har ta hak'ura ta fara addu'a akan Allah ya kawo hanyar da za su bar gidan. Baba ce kullum ke masu girki duk da ita Hafsat ba wani ci ta ke ba, sai baba ta matsa ma ta. Yanzu haka Hafsat ce zaune take ta idar da Sallah tana addu'a baba ta shigo, hannun Hafsat ta kamo ta ce. "Yarinyata na samo mana hanyar da za mu bi mu gudu daga gidan nan yi sauri." Aiko Hafsat da saurinta ta bi bayan baba, suna zuwa baba ta bud'e window d'in da ya ke abud'e ta kama ta. ..✍🏻 Fadila Sani Bakori ce ❤️💞SO NE SILA❤️ 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* Page 5 & 6 Baba babu yadda ba ta yi ba ta tusa kanta cikin window amma abin ya ci tura ƙarshe ma dakyar Hafsat ta jawo kanta da ya makale cikin window. kallan Hafsat Baba ta yi ta ce. " 'Yata tagar nan kan mutum kadai zai iya fita, amma duk da haka akwai wata dabarar da za mu k'ara gwadawa je ki kitchen ki d'akko min wuk'a in b'alle mana k'ofar?." Hafsat kallan Baba ta yi ta yi dariya ta ce. "Baba wuk'a ba za ta b'alla k'ofar nan ba ai" Baba ban za ta yi da Hafsat ta ta fi kitchen d'in da kanta ta d'akko wata k'aramar wuk'a ta na naiman inda zata tusa wukar ta balle kofar. Hafsat duk irin halin da take na k'osa wa ta bar gidan hakan bai hana ta dariya ba, dariya ta kama yi ma Baba ganin ta na ta k'ok'arin b'alle k'ofa kamar wanna da wanna 'yar mi tsi-tsiyar wuk'ar" Baba kallan Hafsat ta yi ranta bace ta ce. "Yanzu 'yar nan ina k'okarin yadda zan ceto rayuwarmu ni da ke shi ne zaki tsaya kina min dariya." Koma wa Baba ta yi ta zauna ranta a b'ace. Hafsat matsawa ta yi kusa da Baba ta ce. "Baba dan Allah ki yi hak'uri Allah dariya kika ban ne" Baba kallan Hafsat ta yi ta ce "Yanzu Shike nan sai dai mu yi hak'uri mu ci gaba da zama har lokacin da Allah ya nufa mu fita" Tom Baba sai dai mu yi ta addu'a Allah ya kawo mana mafita" Ameen 'yan nan." BANGARAN SU FADILA Bayan an tafi da Hafsat fasinjojin motar suka sa Fadila a mota suka tafi cike da jimami da zantawa akan abinda ya wakana. Wani daga cikin fasinjojin ya ce "Wannan fa daga gani an dade ana farautarta, abinda zaku lura ai ita kadai suka kama." Eh tabbas hakane, saboda inda zaku lura sai da aka kirasa a waya ya duba wani abu a wayarsa kafin ya bimu da kallo alamun hoto ne aka tura masa ya ganota." Direban cikin jimami ya ce "Allah dai ya yi mana maganin wannna matsar kidnappers din da muke fatama da ita." Haka dai sukai ta zantawa akan matsalar rashin tsaro dake damunmu. Drivern motar kallan Fadila ya yi da ke kuka ya ce. "Hakuri za ki yi ki mata addu'a yanzu Ina ne gidanku mu kaiki?." Fadila cikin kuka ta ba da address din gidansu. Tana kuka ta na nuna mai hanya a haka har suka zo k'ofar gidan su. Suna zuwa Fadila ta fita tana kuka. Fadila da kuka sosai ta shiga gidansu, daga mahaifiyar Fadila har Mahaifiyar Hafsat ja su ka yi suka tsaya suna kallan Fadila. Mahaifiyar Hafsat kallan Fadila ta yi ta ce "Lafiya wai ke da abin kuka bai miki wuya Ina Hafsat din fa?." Ta idasa maganar tana waigawa bayanta ko zata ga Hafsat. Fadila ta kasa magana sai kuka, sai ga kanwar Hafsat Husna ta yi sallama ta shigo. Kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Mama wasu mutane a waje wai suna sallama da baba." Mahaifiyar Hafsat cikin rudewa ta ce "Innalillahi wa inna ilaihirrajun! Ko dai wani abune ya samu Hafsat din Fadila?." Ta idasa maganar tana sa hijab dinta ta fita cikin tsananin tashin hankali ba tare da ta jira amsar Fadila ba. Mahaifiyar Hafsat dakyar ta samu ta iya gaida mutanan da ta gani fuskarsu cike da alhini alamun wani babban al'amari ya faru. Cikin tashin hankali ta ce "Bayin Allah lafiya?." Daya daga cikin mutanan motar cikin alhinin abinda ya faru ya ce "Wallahi muna tafe tare da yaranku cikin motar nan Allah ya hadamu da masu Garkuwa da mutane suka dauke daya daga cikinsu, yanzu sai dai a yi ta addu'a akuma saurari kiransu." "Innalilahi'wa'inna ilaihirraju'un, Allahhumma ajjirni filmusibati! Sun tafi da Hafsat wallahu galibun ala amrihi." Mahaifiyar Hafsat ta idasa maganar tana fashewa da kuka ta yi cikin gida ta barsu nan tsaye. Da ya ke gidan su Hafsat babban gida ne ka fin kace me magana ta ke waye ko ina, kidnappers sun d'auke Hafsat. Nan fa yara da manya na gidan aka taru sai kuka ake. Mahaifin Hafsat ya yi sallah ma ya shigo gidan cikin kid'ima ya ke tambayar mahaifiyar Hafsat yana ya ce. "Maman Yara abinda na ji a waje da gaske ne? wai masu garkuwa da muta sun tafi da Hafsat?" Mahaifiyar Hafsat cikin zubba kwalla ta ce. "Abinda ka ji haka ne sai dai mu taru mu yi ta addu'a" Nan fa Mahaifin Hafsat cikin tashi hankali ya juya ya fita gidan wajan limamin unguwarsu ya je ya sanar dashi abin da ke faruwa a dan a sasu a addu'a. Sosai limin ya tausaya ma Mahaifin Hafsat nan ya bashi adda'o'i da dama wa in da zai rik'a yi mata in sha Allah zata kubuta cikin lokaci. A ranar duk muta nan gidan ba su yi bacci ba in ka cire k'ananan yaran gidan. Mayan gidan ko dama ba baya ba wajan kiyamullaili haka suka kwana ido biyu suna fadama Allah. Usman ko wanda a ka sa ranar auransa da Hafsat ba shi ya samu labari ba sai dare, dan mahaifiyarsa b'oye mai ta ke ta yi. Aiko cikin tashin hankali ya shi ga gidan, kallan Mahaifiyarshi ya yi ya ce. "Maman Rabi, wai da gaske ne maganar da na ke ji a gari wai 'yan kidnapping sun tafi da Hafsat d'ita?." Mahaifiyar Usman kamo hannun Usman ta yi ta ce. "Haba Babana dad'ina da kai ke nan, kanatsu mana mu yi magana"Haba maman Rabi wata na tsuwa kike so in yi Hafsat dina na hannun mutanan da basu da imani, gaskiya ni dai ba a kyau ta min ba ta ya ma ya za ai a ce matar da zan aura wani abu ya sa meta amma sai dai a waje zan ji labari." Usman na fadin haka ya juya zai fita cikin tsananin tashin hankali Wanda mahaifiyarsa bata taba ganinsa ciki ba. Da sauri mahaifiyar Usman ta kamo hannun Usman din ta ce "Haba Usman dare ne fa yanzu ina zaka?." Wajan malam gurgu zani, in fada mai kinsan ko yaran gidan gidan Alhaji Jabir da aka dauka shi ya yi abin da ya yi aka Sako yaran babu kudin fansa." Mahaifiyar Usman bata fuska ta yi ta ce "Kana da kudin da zaka bashi ne? Ko shi Alhaji Jabir din nawa kasan ya bashi, Kuma kasan dai mahaifin Hafsat ya ji haka ma fada zai maka inda kowa dai yasan malam gurgu boka ne." Usman bata fuska ya yi ya ce "Maman Rabi ni fa ko meye zan iya sai dawa in dai Hafsat zata fito, kawu Kuma da kike magana in dai bake zaki je ki fada mai ba wajan wa zai ji labari?." Mahaifiyar Usman bata fuska ta yi ta ce "Wallahi ban yadda ba yarinyar da bacin ka hada da taimako iyayanta ba za su taba baka ita ba ita ce za ka je ka Kai kudi a fito da ita to baka isa ba." Usman da sosai yake son Hafsat cikin jimami ya ce "Maman Rabi Hafsat fa ko da ace ba auranta zan yi ba Yar kaninki ce ban yi asara ba, sannan ni tunda malam garku ya sa Hafsat ta soni na yadda da aikinsa, kalli fa da yadda Hafsat ta tsanan amma lokaci guda lamari ya juya wanda har su kawu mamaki suke." Ka dai ji abinda na ce maka tana fadin haka ta juya ta tafi ta barshi nan tsaye. Usman zaune a gaban malaminsa, bayan sun gaisa ne malamin Usman ya ce. "Usman kar dai ka ce min tak'ara bijire ma?." Usman kalan malamin shi ya yi cikin damuwa ya ce. "A'a Malam ai yanzu ko mai ya dai-dai dan yanzu ma haka ka saura kwana goma sha hud'u bikinmu, tom Malam wata matsalar ce kuma ta faru, masu garkuwa da muta ne ne suka yi garkuwa da ita tom daga ni har Iyayan yarinyar babu mai kud'in da in sun sara za a basu shine na zo dan Allah a taimaka min a ku b'ito min da ita" Bokan Usman kallan Usman ya yi bayan ya gama zane-zanansa a kasa ya ce. "Hafsat za ta dawo ba tare da abinya kudin fansa ba Kuma auranka da ita zai tabbata kamar yadda na ce maka, amma Kuma ga wata gura nan dake tashi ta baibaye komai wadda na rasa daga Ina take" Usman kallan malam gurgu ya yi ya ce "Da fatan dai kuran nan ba zata shafi auranmu ba?." Bokan Usman dariya ya yi ya ce "Usman kasa fa bata karya na fada maka akwai rabo tsakaninka da yarinyar nan dan haka babu abinda zai hana auranku, yanzu haka k'urar nan da na gani sai da na Kara bincike akan auranka da yarinyar Kuma na ga babu wata matsala saidai wannna kurar da ta lillibe ko Ina, amma karka damu ka kawo dubu 200k za a yi taimakon da wowarta da na maganin kurar da na gani." Shiru Usman ya yi kafin ya ce "Shi kenan zan yi ƙoƙarin hado kudin in kawo." Gidan su Hafsat ko kullum cikin jiran kiran Kidnappers su ke amma shiru addu'a ko yinta suke ba su fa sa ba. Fadila ko ba ta da aiki sai kuka, kasan cewar tafi kowa shakuwa da Hafsat a gidan. BANGARAN SU HAFSAT KUWA. Yau Mahmoud kwanan shi goma ke nan babu shi babu labarinsa, Hafsat da Baba kullum cikin addu'a suke, sai dai zuwa yanzu Hafsat ta d'an saki ranta, dan ko aikin abinci tare da Baba su ke yi. Ma sha Allah yanzu Hafsat ta saki ranta ba kamar da ba, abu d'aya ya fi damun ta in ta tuno da Iyayanta da Usman d'inta su na can cikin damuwa akan rashinta, wannan shi ne abin da ke ta da ma ta hankali sosai. Usman zaune gaban Malaminsa ya kawo masa kudin da ya bukata. Usman cikin damuwa ya ce "Malam gashi a taimaka min saida na saida wasu abubuwa daga cikin lefan da na hada kafin na samu na hada kudadan nan, dan Allah a taimaka min." Dariya bokan Usman ya yi ya ce. "Ai kamar yadda na fad'ama Usman yanzu haka duk Wanda ya d'auki Hafsat da zarar mun yi aiki nan dolansu su sallameta ko ta kubuta dakanta dan cikin biyu za a yi daya ko dai su ji ku lallanta basa son yi a wajan zata zamar masu kamar mujiya a. Wajan, ko kuma ina mai tabbatar ma duk Wanda ya d'auke ta ko yake da sa hannu a dauketa daga zarar na yi aikin nan a daran yau sai ya makance, makatanta za ta samesu har ta baro gun ba za su ankara ba." "Yanzu Malam nan da kwana nawa za mu sa ranta?." Usman ka ban nan da kwana uku, na yi ma ka alk'awari sai Hafsat ta dawo, kai idan ma ka na so aranar da ta dawo za a d'aura auranka da ita a sakko dashi duk mai yuwu ne, kai dai ka bi ko mai a hankali" Usman sosai ya ji d'adin maganar da bokansa ya fada masa dan bai taba fada masa abu bai faru ba, hakan ya sa cikin gwarin gwiwa ya tafi gida cike da jin dadin albishir dinsa dan ya san zai iya fiye da haka ✍🏻 Comment and share please Fadila Sani Bakori ce ❤️💞SO NE SILA❤️ 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* Page 5 & 6 Baba babu yadda ba ta yi ba ta tusa kanta cikin window amma abin ya ci tura ƙarshe ma dakyar Hafsat ta jawo kanta da

Chapter 2 of 10