ya ce. "Shi ke nan Mahmoud zan yi bakin k'ok'arina yanzu tashi ka sha magani zuwa gobe in sha Allah zan ma Alhaji mu'azu magana mu tafi tare gidansu Hafsat d'in mu ji yadda za a yi." Mahmoud godiya ya yi ma Mahaifinsa sosai sanna ya tashi ya sha maganin ciwan kan kamar yadda ma haifinsa ya buk'ata.
B'angaran Nafisa ko har yanzu ba ta san maganar fasa auranta da Mahmoud ba kamar yadda Hajiya Jamila ta ce, yanzu haka waya ta ji Hajiya Jamila na yi na sanar da fasa auran na ta.
Aiko bayan Hajiya Jamila ta gama wayar ne Nafisa ta kalleta ta ce. "Mommy sai na ji kamar kina maganar fasa aure na da Broz Mahmoud ko?" Hajiya Jamila hannun Nafisa ta kamo cikin lallashi ta ce. "Nafisa ki yi hak'uri da Mahmoud dan Allah, duk wannan wulak'ancin da ya ke miki wallahi bi ki ga ko mai ba sai kin shiga gidans..." Nafisa tsaida Hajiya Jamila ta yi ta hanyar cewa, "Mommy ni dai na ji ina sonsa a haka, dan Allah ya za ai ki min haka dan Allah Mommy ni dai gaskiya ki samu Abba ki ce mai kin hak'ura in ba haka ba ma k'ila ma Yarinyar nan zai aura"
Hajiya Jamila ganin Nafisa ta tada hankalinta ya sa ta ce. "Tom shi ke nan ki kwantar da hankalinki zan samu Alhaji yau za mu yi magana shi ke nan ko?" Kai Nafisa ta d'aga ma Hajiya Jamila.
Mahaifiyar Usman ko kamar yadda ta ce za ta zo da daddare haka ko aka yi, Iyayan Hafsat na zaune kamar yadda su ka saba zama dadaddare suna hirar su suna nan zaune Mahaifiyar Usman ta yi Sallama ta shigo, bayan sun gama gaggaisawa ne ta kalli mai bi ma ta wato wan Mahaifin Hafsat ta ce "tom dama Nasiru abinda ya sa na zo duk da dai Usman bai ma gari amma ya ce gobe zai dawo, nazo ne game da maganar auran Hafsat da Usman kun san ance abari ya huce shike kawo rabon wani yanzu Kwana nawa ku ke ganin ya kamata asa auran?" Wan Mahaifin Hafsat numfasawa ya yi sannan ya ce, "tom Yaya Uwani ni aganina wan nan Abun in da duk gida ne duk yadda ki ka ce ai ya yi ko ya kuka ce ?" Ya tambabyi sauran 'yan uwan shi.
Duk kan su suka amsai mai da haka ne.
Mahaifiyar Usman numfasawa ta yi sannan ta ce. "Tom yau asabar dan haka asabar ta sama mai zuwa sati biyu ke nan" Duka amsa mata su ka yi da ya yi.
B'angaran Mahaifin Mahmoud ko washe gari kamar yadda ya yi ma Mahmoud alk'awari ya sa mu aminin shi Alhaji mu'azu akan ya raka shi Bakori naima ma Mahmoud aure.
Aiko cikin lokaci suka kama hanyar Bakori.
Cikin awa biyu da wasu mintoci su ka isa Bakori da ya ke dama Mahaifin Mahmoud ya amshi number Mahaifin Hafsat ya sa ya na zuwa ya kira shi ya sanar da shi gashi a k'ofar gidan shi.
Mahaifin Hafsat cikin girmama ma wa ya ce. "Tom Alhaji barka da zuwa amma na fit ka jirani kadan..✍🏻
Fadila Sani Bakori ce🤗
💓💞SO NE SILA💓
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
Page 21 &22
Cikin minti lokaci Mahaifin Hafsat ya dawo. Cikin girmama juna su ka gaisa.
Bayan sun gama gaisawa ne Mahaifin Hafsat ya kalli Mahaifin Mahmoud ya ce, "Alhaji mu shiga daga ciki mana"
Mahaifin Hafsat d'akin da ya ke saukar da bak'in shi ya kai Mahaifin Mahmoud.
Bayan sun Kara gaisawa ne Mahaifin Mahmoud ya kalli Mahaifin Hafsat ya ce "Tom na san dai za ka yi mamakin dawowa ta yau, wato baban Hafsat d'an wajena Wanda na ce ma shi ya tsinci Yarinyarka jiya bayan dawowata kawo Hafsat na koma gida na iske shi awani yanayi Wanda ban tab'a ganin shi ciki ba tunda na ke dashi na iskeshi hannuwanshi duka biyu dafe da kanshi wai kanshi ke ciwo kuma ya dage sai kuka ya ke kamar wani k'aramin yaro, da nabi ba asin Abun na matsa mai dan jin me ke damun shi shine ya ke rok'ona dan Allah in zo in naima mai auran yarinyarka Hafsat" Mahaifin Mahmoud shiru ya yi ya na jiran yaji ta bakin Mahaifin Hafsat.
Mahaifin Hafsat numfasawa ya yi, sanna ya ce, "Alhaji banji dad'i ba da karo k'an abinda ya riga ya fi k'arfina, wato Alhaji Hafsat dama da sa ranarta aka a ka sace ta. Yanzu haka maganar da mu ke yi da kai yau saura Kwana goma sha uku bikin Hafsat, da ace Hafsar ba d'an ''yar'uwata za ta aura ba, Wallahi Alhaji da na amshe auran Hafsat a hannun duk Wanda na ba na ba d'anka, sai dai Haidar d'and'an yayata ce, Uwa d'aya Uba d'aya".
Mahaifin Hafsat numfasawa ya yi, sannan ya ci ga ba cewa, "Alhaji ina baka hak'uri dan Allah, ka yi hak'uri, ka kuma ba d'an wajanka hak'uri, ya yi hak'uri , haka Allah ya nufa".
Mahaifin Muhmoud hannu ya mik'a ma Mahaifin Hafsat ya ce, "Wallahi ba ko mai ai duk anzama d'aya Allah ya sa hakan ya fi alkairi, ina Hafsat d'in ta ke mu gaisa? ".
Mahaifin Hafsat tashi ya yi, ya kira mai Hafsat d'in.
Hafsat ko da ba ta san mai kiranta ba, Cikin wani sabon miskilanci da ta tsira tun dawowarta ta ta h, Sai dai Hafsat ba k'aramin ma ma ki ta yi ba, ganin Mahaifin Muhmoud.
Hafsat Cikin girmama wa ta gaida Mahaifin Muhmoud, tare da tambayar shi ya muta nan gidan.
Mahaifin Muhmoud ma Cikin sakin fuska ya amsa ma Hafsat.
Hafsat ta shi ta yi ta koma d'akin Mahaifiyarta ta kwanta.
Mahaifin Muhmoud ko sallama ya yi ma Mahaifin Hafsat su ka ta fi shi da abokin sa.
Bayan tafiyar Mahaifin Muhmoud ne, Mahaifin Hafsat ya shiga d'akin Mahaifiyar Hafsat da ke ta aikin nin kin kayan su na su kola da ta yi, Mahaifin Hafsat kallan Hafsat ya yi da ke kwance kan d'an ma dai-dai cin gadon su, ya ce, "Ni ko sai inga kamar kazar-kazar d'in Hafsat ya canza tunda ta dawo , ka mar ta na da wa ta damuwa ab'oye aranta? ". Mahaifiyar Hafsat numfasawa ta yi, sannan ta ce, "Tom ni ma haka nagani, amma nai ma ta magana ta ce min wai ita ba abinda ke damunta, tom ya zan yi da ita in da haka ta ce min". "Tom shi ke nan ai, Memuna Wanda ya kawo Hafsat ne ya zo yanzu wai nai man ma yaron shi auran Hafsat, wai ba yan tafiyar Hafsat d'in yaranshi ya shiga Cikin wani hali, Wallahi Memuna banji dad'in haka ba, ina ma ace ban bada Hafsat ga Haidar ba". Mahaifiyar Hafsat kallan Mahaifin Hafsat ta yi, ta da ka ta da nin kin kayan da ta ke yi, ta ce, "gaskiya ni ma dai na so hakan dan muta nan daga gani na kwarai ne, tom ai ba komai Allah ya sa haka shi ya fi alkairi ". Da Ameen Mahaifin Hafsat ya amsa sannan ya ta shi ya fita.
Bayan fitar Mahaifin Hafsat ne, Mahaifiyar Hafsat ke jin kamar kukan mutum ku sa da ita, da ya ke dama ta gama nin ke kayan, kallan Hafsat ta yi da ta ke zaton kamar bacci ta ke, kuma yanzu ta na tunanin ita ke kukan. Mahaifiyar Hafsat Cikin d'aga murya ta kira Hafsat, ta ce. "Hafsat!". Hafsat shuru ta yi da kukan da ta ke yi.
Mahaifiyar Hafsat ko, kallan Hafsat ta yi, da ke kwance kuma tabbas ta na da tabba cin ita ke kukan da ta ke yi, ta ce, "Hafsat ta shi kizo ki sa me ni". Hafsat tashi ta yi ta na mai goge hawayanta dan ba ta son Mahaifiyar ta ta gani.
Mahaifiyar Hafsat ko, k'urama Hafsat ido ta yi, ta na kallan ta, ita kuma Hafsat d'in sai k'asa ta ke da idonta kamar wa ta muna fuka.
Mahaifiyar Hafsat kallan Hafsat ta yi, ta ce, "Hafsat kallan ni". Hafsat d'ago da kai ta yi ta na kallan Mahaifiyarta .
Mahaifiyar Hafsat Cikin muryar daga ji ka san ba alamun wa sa ta ce, "Hafsat me ke damunki?, kuma me ya sa ki kuka yanzu?, Wallahi ki ka ce min ba ko mai sai na fasa bakin ki". Hafsat rasa abinda za ta ce ma Mahaifiyarta ta yi, ga kuma rantsuwar da ta yi, idan ta ce ma ta ba bu abinda ke damunta sai ta fasa bakinta. Hafsat da ta rasa abinda za ta ce ma Mahaifiyarta ka wai sai ta fashe ma ta da kuka.
Mahaifiyar Hafsat tsayawa kallan Hafsat ta yi, dan Tabbas ta lura tun da wowar Hafsat akwai wa ta damuwa da ta b'oye aranta wadda ke damunta.
Mahaifiyar Hafsat Cikin taushin murya da alamun lallashi, ta ce, "Hafsat ni za ki b'oye ma damuwarki ko?, tom idan ba ki fad'amin ba wa za ki fad'ama wa?, fa d'amin abinda ke damunki kin ji Hafsat ni mai ba ki shawara ce". Hafsat shiru ta kuma yi dan ba ta san abinda za ta cema Mahaifiyarta ba.
Mahaifiyar Hafsat jin Hafsat ta yi shiru, ba ta ga ji ba, ta kuma cewa"Hafsat ba za ki fad'amin ba ko? ". Hafsat kallan Mahaifiyarta ta yi, ta ce. "Mama Allah nima na ji ina kuka ne ka wai amma ban san me ke da muna ba". "shikenan Allah ya yi mi ki maganin da muwarki, ba kuka za ki ba ai addu'a za ki rik'a yi, ta shi ga sallah can ankira ki je ki yi.
Hafsat ta shi ta yi kamar yadda Mahaifiyarta ta Uwarceta.
Mahaifin Muhmoud ko da ya isa gida direct falon Mahaifiyar Muhmoud ya wu ce, dan can ya ke tunanin Muhmoud . Ai ko kwance ya iske Muhmoud.
Muhmoud ko na ganin Mahaifinsa ya yi, k'arfin hali ya ta shi zau ne, kallan Mahaifinsa ya yi, ya ce. "Abba ba a dace ba ko? "? Mahaifin Muhmoud da fa Muhmoud ya yi, ya ce. "Muhmoud so da dama abinda mu ke so ba alkairi ba ne gare mu, idan mu ka yi hak'uri sai ka ga Allah ya mu sanya mana da ma fi alkairi, Muhmoud mahaifin yarinyar nan Hafsat ya yi ta kai ci sosai na hanaka auran Hafsat da ya yi, saboda ko Hafsat ya riga ya bada ta in da ba za ta kwatu ba, ya ba da auran Hafsat ga d'an yayar sa ne.
Mahaifin Muhmoud numfasawa ya yi, sannan ya ce, "Muhmoud dan Allah ka yi hak'uri da Hafsat, kuma ka yi addu'a nima zan ta ya ka, Allah ya ba ka wadda ta fi Hafsat". Shiru Muhmoud ya yi, dan shi ka d'ai ya san yadda zuciyar shi ke mai d'aci da zafi, tabbas rabuwa da masoyi na da d'aci da zugi mai rad'ad'i amma bai tab'a sanin zafin shi ya kai ha ka ba, sai yanzu da Mahaifin shi ke sanar da shi wai ya yi hak'uri da Hafsat.
Muhmoud kallan Mahaifinsa ya yi, ya ce, "Abba ina jin zafi mai d'aci a zuciyata, Abba ba zan iya rabuwa da Hafsat ba, dan Allah ka rok'an min Mahaifinta". Mahaifin Muhmoud kallan Muhmoud ya yi, muryar shi ad'an sama-sama ya ce, "Muhmoud ba zan sa ke zuwa gidan su Hafsat ba, idan ko kaga na sake zuwa tom auran Hafsat na je, dan yau saura Kwana goma sha uku auran ta da Wanda Iyayanta su ka ba ta".
Muhmoud kamar saukar aradu haka ya ji maganar da Mahaifinsa ya fad'a mai, Muhmoud cikin rud'u ya ta shi tsaye ya na kallan Mahaifinsa, ya ce, "Abba mutuwa zan yi,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, ". Muhmoud bai k'arasa abinda ya ke fad'iba ya yanke ji ki ya fad'i.
Mahaifin Muhmoud cikin rud'u ya ke girgiza Muhmoud dan ga ba d'aya numfashin shi gani ya ke kamar ya d'auke.
Mahaifin Muhmoud wa ya ya ciro ya kira Family doctor su, Ai ko ba afi minti goma ba sai ga shi ya shigo gidan.
Koda doctor ya duba Muhmoud kallan Mahaifin Muhmoud ya yi, ya ce. "Gaskiya Alhaji sai dai mu tafi da shi Hospital d'in mu, dan ya na buk'atar Emergency treatment ne"."Ok, badamuwa mu ta fi tom". Da tai ma kon doctor su ka sa Muhmoud a Mota su ka yi, Hospital da shi.
B'angaran Hafsat kuwa da daddare ta idar da sallar issha'i ke nan, k'anin ta Usaini, ya shigo ya ce ma ta, "Aunty Hafsat Yaya Haidar na d'akin babanmu wai ya ce ki je". Hafsat wa ta irin fad'uwar ga ba ce ta risketa, kallan k'anin na ta ta yi, ta ce, "ka ce mai ganinan zuwa". Duk abinda Hafsat ke yi Mahaifiyarta na kule da ita, a haka dai Hafsat ta ta shi ta fita, zuwa in da suka saba hira da Haidar.
Haidar na zaune k'afa d'aya kan d'aya Hafsat ta yi sallama ta shigo. Hafsat can d'an ne sa da Haidar ta zauna.
Haidar kallan Hafsat ya yi da fuskar shi da ta ji bleaching, ya ce, "baby kin ko ji farin cikin da na ji lokacin da ake sanar da ni dawowar ki, Gaskiya baby, ina son ki sosai dan na kashe kud'i da yawa a sanadiyar b'acewarki,tom ya kike ya ki ka ji da rashina? ". Hafsat cikin k'asa da kanta ta ce, "lafiya klau". Haidar kallan Hafsat ya yi, ya ce, Baby wai su wa ye suka sace ki ne? ". "Nima ban san su ba". Haidar kallan gefe ya yi ma Hafsat ya ce, "Baby Wallahi k'arya ki ke ta ya za ace bi ki san wa inda suka sa ce ki ba, amma shi ke nan, da fatan dai basu shiga gona ta ba ko? ". Hafsat rasa abinda za ta ce ma Haidar ta yi, dan haka sai tai mai shiru.
Shi ko Haidar jin ta yi shiru kuma mai mai ta tambayar shi ya yi, ya ce. "Baby wai ba kya ji ne, na ce da fatan dai su wa inda suka sa ce ki basu shiga gona ta ba?". Tambayar ta soma b'atama Hafsat rai dan haka sai cewa ta yi, "kai dai ka yarda da Allah ka wai". "Ok tom shikenan, yanzu me ki ke tsara mana na shirye-shiryan auran mu? ". Hafsat kallan Haidar ta yi, kamar za tai kuka ta ce, "yaya Haidar kaina ciwo ya ke, ba ri in shiga gida in kwanta". "Ayyah sannu Baby Allah ya baki lafiya je ki ki kwanta gobe zan zo in ga jikin na ki".
Hafsat na dawo wa gida ta fad'a kan gado ta kwanta ta na kuka.
Mahaifiyar Hafsat ko dama ta lura da yadda Hafsat ta shiga d'akin ya sa ta bi bayanta.
Mahaifiyar Hafsat kallan Hafsat ta yi, da ke rusa kuka kamar wadda a kai ma mutuwa, ta ce, "Hafsat me ke da mun ki ne wai?". Hafsat ta shi ta yi ta zauna ta na mai ci gaba da kukan ta ta ce, "kai na ke ciwo". "Tom ta shi ki sha magani". Mahaifiyar Hafsat ta fad'i haka ne kawai ba dan ta yadda da abinda Hafsat d'in ta ce ma ta ba, tabbas damuwar 'yarta ta ta fara ta b'ata, dan ta lura Hafsat na da wata b'oyayyar da muwa da ta b'oye aranta.
Maganin ciwan kan ta mik'a ma ta, sannan ta fi ta ta bar ma ta d'akin.
B'angaran Muhmoud ko yau kwanan shi biyar a asinitin, in da ya yi dai-dai da yau saura Kwana 7 d'aurin auran Hafsat da Haidar.
Muhmoud ko wani irin ciwan kai ne mai azaba ke damunsa Wanda ya fidda mai da hayya cin sa, abin har yasa jininsa ya hau, kuma kullum Idan aka auna shi jinin shi sake hawa ya ke, wanna shi ne abinda ya d'aga hankalin Mahaifin Muhmoud sosai, dan Muhmoud ko ga ne Wanda ke kanshi ba yi ya ke ba, tsabar ciwan kai, dan ciwan har ya tab'a brain d'in shi.
Yanzu haka Mahaifin Muhmoud zau ne Office d'in doctor, ya na tambayar shi akan jikin Muhmoud d'in.
Likitan lallan Mahaifin Muhmoud ya yi, ya ce. "Gaskiya ni banta b'a ganin ciwan kai irin wanna ba, dan abin har ya shiga cikin kwakwalwar shi, ga abin kullum mu ka auna shi sa ke ga ba ya ke, kuma duk wani tai mako da ya ka ma ta muna bashi, akwai abinda ke ta da mai hankali ko ya ke damunsa, Wanda ya sa duk halinda ya ke ci ki bai manta shi ba.
Likitan kallan Mahaifin Muhmoud ya yi, ya ce. "Gaskiya da ace zaka iya hasashen abinda ke damunsa ko ace ka san damuwar shi da ha kan ya tai ma ka sosai". Mahaifin Muhmoud kalla likitan ya yi, ya ce, "Ina zuwa doctor ".
Mahaifin Muhmoud motar shi ya hau ya kama hanyar Bakori, tun kafin ya isa ya sanar da Mahaifin Hafsat ya na zuwa.
Tsabar gudun da Mahaifin Muhmoud ya yi, cikin hour guda ya isa Bakori.
Ya na isa ya yi ma Mahaifin Hafsat wa ya gashi ak'ofar gidansa.
Mahaifin Hafsat da murmushin shi ya fita, kallan Mahaifin Muhmoud ya yi, ya ce, Alhaji ka shigo daga ci ki mana? ". Mahaifin Muhmoud kai ya girgiza ya ce. "Dan Allah alfarma na ke ne ma kara ka ni wani waje dan Allah ? ". Mahaifin Hafsat ba ta re da tunanin ko mai ba, ya shiga motar Mahaifin Muhmoud, ya ja suka ta fiiii..........✍🏻
Fadila Sani Bakori ce
💓💞SO NE SILA💓
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
Page 23 & 24
Mahaifin Hafsat shiru ya yi ya na tunanin inda Mahaifin Mahmoud zai kai shi.
Tafiya su ke yi ba Wanda ke ma d'an'uwansa magana. Sai dai mahaifin Hafsat cike yake damamakin inda Mahaifin mahmoud zai kai shi.
Tafiyar kusan awa uku suka yi ta kai su Katsina.
Mahaifin Hafsat bak'aramin mamaki ya yi ba ganin inda Mahaifin Mahmoud ya kawo shi.
Mahaifin Mahmoud ko direct d'akin da Mahmoud ya ke ya kai Mahaifin Hafsat.
Mahaifin Hafsat kasa hak'uri ya yi ya juya ya kalli Mahaifin Mahmoud ya ce, "Alhaji lafiya me ya kawo mu Asibiti lafiya?." Mahaifin Mahmoud ba tare da ya kalli Mahaifin Hafsat ba ya ce "Na sa ni". Parking din motarsa ya yi sannan ya kalli Mahaifin Hafsat ya ce "mu je ko" D'akin da Mahmoud ya ke kwance Mahaifin Mahmoud ya kai Mahaifin Hafsat.
Mahaifin Mahmoud cikin damuwa da halin da Mahmoud ya ke ciki ya nuna ma Mahaifin Hafsat Mahmoud da ke kwance daga gani kasan yana jin jiki yanzu haka hannusa dafe akansa.
Mahaifin Hafsat kallan Mahaifin Mahmoud ya yi ya ce "Alhaji ni fa bangane komai ba ka yi min bayani?." "Wannan shine yarona Mahmoud wanda muka je naima mai auran yar wajanka Hafsat, wannan jinyar gaba dayanta yana yinta ne asadin son 'yarka Hafsat ne, da na ɗauki abun kamar wasa sai da na ji daga bakin likita akan halin da yake ciki ya sa na zo na kawoka ka gani.
Mahaifin Muhmoud ya ci gaba da cewa, "Wato malam yarinyarka Hafsat bakowa bane ya saceta face Mahmoud d'ana" Na sha magakin ganin Hafsat a gidansa, dan da ace wani ya fada min mahmoud zai aikata haka Wallahi ba zan yadda ba. Kuma shi duk ya yi hakane a haukansa duk akan son da yake ma Hafsat din gudin Kar ya rasata da yake yi kasan cewar da saranarta ya santa, yanzu haka akwai yarinyar da na sa mai rana da ita amma yaki, atakai ce daima ka ga halin da yake ciki duk akan ita Hafsat din." Mahaifin Mahmoud shiru ya yi ganin yadda ran mahaifin Hafsat ya bace hakan ya sa ya dafa
Mahaifin Hafsat cikin sanyi ya ce "Tabbas na san Mahmoud ya ai kata laifi mafi muni agareka, sai dai na san za kai ma Mahmoud uziri saboda kalan rukon da ya yi ma Hafsat din sunan dai kawai ya yi kidnapping dinta ne amma Ina mai tabbatar maka ka tambayi Hafsat din ma za ka ji bai taba mutuncin Hafsat ba Wanda da ya yi hakan da ina mai tabbatar maka ba zan zo gabanka in tsaya ba ina rokonka ka ba shi auran Hafsat ba batare da na hukunta shi ba.
Mahmoud ya na son Hafsat so na gaskiya kuma so mai tsanani, saboda tabbas da ace ba da aure ya ke son yarinyarka ba da yaketa mata haddi kasan cewarsa tare da ita na dogon lokaci.
Abban Hafsat ina rok'onka da abinda na san aikata hakan zai ma wuya, dan Allah ka ceci rayuwar Mahmoud ka bashi auran Hafsat dan Allah"
Mahaifin Hafsat shiru ya yi yana ayyana yadda abun zai kasance dan ya san shi kanshi baida wata isa da Hafsat din in da ya na da yayye ga yaya Uwani ita ke yanke hukuncin duk wani abu da ya taso akan zuri'arsu baki d'aya, tom wannan kuma sai ya kasance Usman yaronta ne Kuma Wanda take ji dashi sososai.
Mahaifin Hafsat kallan Mahaifin Mahmoud ya yi ya ce, "Alhaji, Allah ya ba Mahmoud lafiya amma ba ni ke da iko akan Hafsat ba, sai dai na yi maka alk'awarin zan samu 'yan'uwana in musu magana akan halin da Muhmoud d'in yake ciki, duk yadda muka yi da su za ka ji"
Godiya sosai Mahaifin Mahmoud ya yi ma Mahaifin Hafsat, sannan ya bashi kud'i da yawa ya ce ya yi kud'in motar komawa gida, da kyar Mahaifin Hafsat ya ya amshi kud'in,
Sannan ya yi mai sallama ya tafi tare da yi ma Mahmoud fatan Allah ya bashi lafiya.
Mahaifin Hafsat bayan ya dawo gida Usani ya aika ya Kira mai Hafsat.
Bayan Hafsat ta zo giran Mahaifinta ne ta zauna tana saurare daga garesa Mahaifin Hafsat ya dad'e yana kallan Hafsat da ita kuma kanta ya ke ak'asa sanan ya ce, "Hafsat, waye ya sace ki?" Hafsat abazata ta ji tambayar mahaifin nata hakan ya sa ta dago tana kallansa, kafin ta ce "Baba, nima bansan su ba" Mahaifin Hafsat kallan Hafsat ya yi ya ce, "Hafsat su suka ce ki rufa masu asiri karki fad'ama Iyayanki shi ya sa baki fada mana ba?." Hafsat rasa abinda za ta ce ma Mahaifinta ta yi, abin da kawai ta sani ba ta son Mahaifinta naganin mutun cin Mahaifin Mahmoud ta fad'a mai d'ansa ne ya sace ta tana ganin in dai ya sani tom zai bar ganin mutuncin mahaifin Mahmoud din hakan ya sa ta ce, "Baba, kamar yadda ka ji tun farko haka ne ban san wanda ya sace ni ba" Mahaifin Hafsat tsayawa ya yi yana kallan Hafsat ganin yadda ta dage tana son b'oye laifin Mahmoud ba cin shi kuma ya riga ya sa ni, kallanta ya yi ya ce "Hafsat me ya sa bakya son in san Yaron Alhajin da ya kawo ki ne ya sace ki? Hafsat ta rud'e da jin abinda Mahaifinta ya ce hakan ya sa ta rasa abinda za ta ce ta ja bakinta ta yi shiru.
Mahaifin Hafsat ko kallan Hafsat ya yi