Share this page
5 / 10
abinda kika ce jiya." Mahmoud tea din kadai ya dauka ya ce "Wannan dinma dan ke kika yi amma bana breakfast da wuri." Tea din kawai ya sha ya aje cup din ya ce "Na gode sosai da kulawarki, fatan kin tashi lafiya." Lafiya Lau yallabai." Zan fita sai na dawo za ki min na rana." Hafsat tana murmushin yaudara ta ce "Har na dare ma idan kana so." Murmushi Mahmoud ya yi ya ce "A'a zan wahalar dake na gode, bari in tafi ko sai dawo." Tun daga wanna rana ya zama na Hafsat kullum ita ta ke masu abinci, Hafsat ko ta ci nata Muhmoud ya dawo sai ya ta kura ma Hafsat sun ci tare, Hafsat sosai suka take biya ma Mahmoud su yi fira zuwa yanzu sabon dole ya fara shiga tsakaninsu. Yau saura Kwana biyu Mahmoud ya mai da Hafsat ga ban Iyayanta kamar yadda ya yi ma ta alk'awari inda ya zamana shi kuma Mahmoud saura Kwana uku auran da Mahaifinsa ya ke son ya mai. Hafsat ga nin tafiyarta gida ta gaba bato hakan ya sa ta dage wajan k'ara sakar ma Mahmoud fuska yanzu haka tana kitchen yau mahmoud ya ce yake so ta yi masa, bayan ruwan ya tafasa ne Hafsat ta d'akko garin za ta yi talge by miske ruwan ya shek'e mata a k'afa, Hafsat cikin jin azaba da irin rad'ad'in da ta ke ji ta kashe gas d'in falon Hafsat ta koma tana zagayewa tsabar azabar da k'afar ke mata, kuka Hafsat take sosai tana yarfe hannu, ana haka ne Mahmoud ya shigo gidan da sauri ya k'ara so jin kukan Hafsat da ya yi Mahmoud cikin rud'ewa da ganin k'afar Hafsat ya ce. "Subhanallahi me ya samu kofar taki? Konewa ki kai? Bari in kira Aminu ya duba kafar" Mahmoud Aminu ya kira ya zo ya ba Hafsat magungu nan wutar Aiko Hafsat kamar an k'ara mata azaba haka ta ji da aka fesa mata maganin na ruwa a kafa, ranar Hafsat barci gagarta ya yi, babu yadda ba ta yi da Mahmoud ba akan ya tafi ya kwanta amma yaki ya ce sai ta yi barci ranar dai kusan raba dare ya yi a wajan Hafsat har sai da ya ga alamun tana jin barci kafin ya tafi ya barta. Washegari Mahmoud da kanshi ya shiga kitchen ya hada ma Hafsat tea ya kawo Mata, babu yadda Hafsat ba ta yi ba ya bata ta sha da kanta ba Amma Mahmoud ya ki ya ce "Yi hak'uri ai kinga ban taba ciyar da Kai ba in ba yau ba da baki da lafiya. Hafsat gauda Fuska ta yi ta ce "Ai a kafa ne ciwan ba a hannu ba." Ni dai ki ta shi kisha dan Allah" Hafsat ganin Mahmoud ya bata rai ya sa ta tashi ta je ta wanke bakinta kafin ta zo ta zauna. Mahmoud miko cup din ya yi bakinta, Hafsat amsa ta yi tana turo baki a haka har ta sha rabi sannan ta kauda kai ta ce " Allah na k'oshi." Mahmoud shanye sauran ya yi sannan ya kalleta ya ce "Babyna bari zan amso miki wani magani yanzu zan dawo" Mahmoud Fita ya yi dan amso ma Hafsat maganin. Muhmoud ya fita da d'an dadewa sai ga wata farar mota tana ma mai gadin mahmoud horn, mai gadin sanin na cikin motar da ya yi ya sa cikin sauri ya bud'e mai get d'in, kafin cikin girmamma ya gaidashi, ganin gidan zai shiga har zai ce mai mahmoud ya fita sai ya yi tunanin ai kila ma sun yi waya hakan ya sa ya yi shiru. Mahaifin Mahmoud kai tsaye ya bud'e k'ofar falon ya shiga. Hafsat na kwance akan caution din falon tana mikar da kafar da ta kone, Kai ta dago da sauri jin muryar da bata Mahmood ba . Hafsat da mamaki yake kallan Hafsat wadda Hafsat ta yi saurin dukar da kanta tana✍🏻 Fadila Sani Bakori ce ❤️💕SO NE SILA❤️ 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*By https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* Page 15 & 16 Hafsat tsabar tsorata da ganin Mahaifin Mahmoud ya sa bata sansan da ta tashi daga kwancan da ta ke ba. Mahaifin Muhmoud ko Innalilahi wa inna 'ilaihir raj'un ya ke mai-mai tawa. Hafsat ko ganin yadda Mahaifin Mahmoud ya sha mamaki da daganinta ya sa jikinta ga ba d'aya ya fara rawa. Mahaifin Mahmoud kallan Hafsat ka wai ya ke cike da mamaki da al'ajabi dan bai taba tunanin mahmoud zai iya aje mace a gidansa ba dan shi kallan da yake mai ko budurwa ma bashi da ita, dan yama rasa abinda zai ce mata, cikin danne yadda ya ke jin zuciyarshi na yi mai ya ce "Ina Mahmoud dinfa?." Hafsat gaba d'aya jikinta rawa ya d'auka ta fashe da kuka Maimakon taba ba mahaifin Mahmoud amsa, sosai ta rude ganin kallan gyamar da yake Mata. Mahifin mahmoud da yake mutum ne mai zafi tsawa ya daka ma Hafsat kafin cikin wani irin fushi ya rufe Hafsat da duka, saboda a rayuwarsa ya tsani ya ga mace tana irin wannna rayuwar ba kamar ita Hafsat din ba da ya ganta yarinya karama hakan sai ya bata mai rai sosai hakan ya sa ya rufe Hafsat da duka dukanta yake sosai kamar wata yar cikinsa yana cewa "Dan ubanku iyayanku sun baku tarbiya iya iyawarsu amma kunki kunbujire masu ku yan isa." Mahaifin mahmoud bugun Hafsat yake sosai yana cewa "Saura Mahmoud din shi ma zai zo ya saman, idan ma kin rasa ma fadane ni zan gyaraki yau dinnan." Hafsat ko kuka take sosai tana naiman ceto tana cewa "Wallahi ba laifina bane, ba da son raina nake zaune ba." Mahmoud bayan ya dawo tun da ya ga motar Mahaifinsa a gidansa gabansa ya fad'i dan yasan halin Mahaifin nasa da zafin rai sosai, mahmoud cikin faduwar gaba ya idasa cikin gidan sai dai tun kafin ya bude kofar falon ya ji yo ihun Hafsat. Mahmoud cikin rudewa da fargaba ya idasa falon, Mahmoud cikin rashin sanin abinda ya aikata ya rik'e hannun Mahaifinsa cikin tsantsar tashin hankali yana cewa. "Abba dan Allah ka yi hak'uri ka saurare ni Wallahi bata da laifi nine mai laifi." Marin da Mahaifin Mahmoud ya wanka ma mahmoud ne ya sa Muhmoud yin shiru tare da sakin hannun shi. Mahaifin Muhmoud cikin bacin rai ya nuna Mahmoud da hannu ya ce "Mahmoud wanna ita ce tarbiyar da na ba ko? Dama wanna shi ne dalilin da ya sa ba ka son yin aura ba ka son ai ma maganar aure, saboda kana ganin wannan ita ce rayuwa mai kyau ko?" Mahmoud shiru ya yi kansa k'asa dan yama rasa ta ina zai fara yi ma mahaifinsa bayani. Mahaifin Muhmoud Cikin daka tsawa ya ce, "Mahmoud na ce wanna shi ne dalilin da ya sa ba ka son ai maka ko maganar aure ko?" Mahmoud cikin rashin sanin abinda zai ce ya ce, "Abba Wallahi duk abinda kake tunani bashi bane, hasali ma ita bada son ranta take zaune nan ba." Mahaifin Mahmoud murmushin takai ci ya yi ya ce, "Mahmoud ni za ka raina ma hankali ko? Ni za ka mai da yaro k'arami?." Mahaifin Mahmoud na kai haka ya juya zai bar gidan ranshi b'ace sosai wanda mahmoud a iya tsawan rayuwarsa bai taba ganin bacin ran mahaifin nasa ba kamar yau. Mahmoud da sauri ya rik'o hannun Mahaifinsa ya tsugunna gaban Mahaifinsa ya ce "Abba ka saurare ni dan Allah in maka bayanin komai Wallahi abinda kake zargi ba haka bane". Mahaifin Mahmoud wani kallo ya yi ma Mahmoud Wanda ya sa Mahmoud bashi hanya bai shirya ba. Mahmoud ganin in harfa yabar mahaifinsa ya fita a wannan halin da ya ke tom ko mai zai iya faruwa, hakan ya sa Mahmoud ya ce "Abba wallahi Allah d'aya Wallahi ban tab'a ai gata zina a Rayuwata ba dan Allah Abba dan Soyayyarka da shugaban halitta ka tsaya ka saurare ni" Mahaifin Mahmoud jin irin ran zuwar da Muhmoud ya yi ya sa ya dawo falon dan jin mai Mahmoud zai ce mai. Guri ya samu ya zauna, sannan ya kalli Mahmoud ya ce. "Mahmoud na riga nasan waye kai tun kana yara, amma yanzu abin da idanuna suka gani ya sa ni a kokwanto, amma zan tambayeka kar kai min k'ary ya ka ke da yarinyar nan? kuma me dalilinka na zamanta gidanka?" Mahmoud cikin fargaba da tsoran mahaifin nasa ya ce "Abba, babu wata alak'a da ke tsakanina da Hafsat, hasalima bisa tursasa watace ta ke zaune gidan nan" Mahmoud shiru ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Abba Hafsat ita ce yarinyar da na aika anemamin auranta alokacin da ka je ummara, amma na san ka ji labari gun amininka Alhaji lawai?." Mahaifin Mahmoud cikin mama ki ya ke kallon Mahmoud sanna ya ce, "Mahmoud shine da suka ce ba za su baka auranta ba ka sato ta ka ka wota gidanka ko-ko ya akai?." Mahmoud cikin inda-inda ya ce, "A..b..ba Wallahi na rasa yadda zan yi ne alokacin shi ya sa, amma yanzu haka jibi zan mai da ta gaban Iyayanta" Mahaifin Mahmoud kallan mamaki ya ke ma Mahmoud ya ce, "Mahmoud da ace wani ne yaban labarin nan ya ce za ka aikata haka Wallahi da ba zan yarda ba amma sai gashi na gani da idona, yanzu mahmoud da hankalinka da tunaninka ka ka sato mace ka aje gidanka Ka wai dan ka na sonta, yanzu ka na tunanin Iyayanta za su kyaleka ne? ka aikata kuskure mafi girma arayuwarka kuma Allah ba zai barka ba dan hak'in Iyayan yarinyar nan kad'ai ya isheka bare kuma ita kanta yarinyar, ni kaina kalli dukan da na yi mata akan rashin sani?." Mahifain Muhmoud mai da kallan shi ya yi wajan Hafsat da ke kuka cikin lallashi ya ce "Yi hak'uri kin ji, na yi miki haka ne cikin rashin sani, inane gidanku?" Hafsat d'ago da kanta ta yi ta ce "Ni 'yar Babori ce" Mahaifin Muhmoud salati ya hau yi ya ce. "Mahmoud yanzu daga Bakori ka dakko yarinyar mutane har nan Katsina?." Mahmoud mai ke damunka ne? ko dai ka fara shayeshaye ne bansani ba?" Mahmoud shiru ya yi yana soka k'eya dan shima sai yanzu ya ke ganin girman laifin da ya aikata. Mahaifin Mahmoud kallan Hafsat ya yi da ke kuka tun k'arfinta ya ce, "Dan Allah ki yi hak'uri kin ji da kai na zan mai da ke gidanku, yanzu haka tafiya ce ta ka mani sai nan da Kwana uku ko biyar zan dawo kuma da hannuna na ke son in kai ki ga ban Iyayanki dan haka ki yi hak'uri yanzu za ki koma gidana da zama daga na dawo zan kai ki gaban Iyayanki kin ji?" Kai Hafsat ta d'aga mai. Mahaifin Mahmoud kallan Mahmoud ya yi ya ce, "Mahmoud na d'aga auranka da Nafisa sai next week saboda tafiyar da ta kama ni yau d'in nan zuwa Cameroon. Mahaifin Muhmoud mai da kallan shi ya yi ga Hafsat ya ce, "Yi hak'uri kin ji ki bar kuka yanzu tashi in kai ki gidana ki zauna kafin in dawo daga tafiyar da zanyi in sha Allah Kwana uku zanyi daga na dawo zan mai da ke ga ban Iyayanki da hannuna. Hafsat tashi ta yi tana share hawan idonta. Haka Mahaifin Muhmoud ya tasa Hafsat gaba har wajan motarsa ya bud'e ma ta back ta shiga. Mahmoud ko da ya zamana kamar wani dolo binsu ya yi ta yi abaya ya na gani Mahaifinsa ya ja motarsa ya tafi ya barshi gun tsaye. Mahaifin Mahmoud gidansa ya kai Hafsat falon Hajiya Jamila ya kai ta, lokacin Hajiya Jamila na zaune ita da Nafisa a falon, Mahaifin Mahmoud sallama ya yi ya shigo da Hafsat da ke biye da shi a baya. Daga Hajiya Jamila har Nafisa kallan Hafsat kawai su ke, Hajiya Jamila Mahaifin Mahmoud ta kalla ta ce, "Alhaji wannan fa daga ina?" Ta fad'a tana nuna Hafsat da ke gefe guda a rakub'e. Mahaifin Mahmoud kallan hajiya Jamila ya yi sannan ya ce, "ki sameni a falona mu yi magana" Yana kaiwa nan ya juya ya fita daga falon Hajiya Jamila. Hajiya Jamila kusan tare da Mahaifin Mahmoud suka isa falon nashi, ko zama bata bari ya yi ba ta ce. "Alhaji ina jinka daga ina muka samu bak'uwar?" Mahaifin Muhmoud numfasawa ya yi tukun ya ce cikin sanyi murya, "Jamila Mahmoud ya yi abinda ya ban mamaki tabbas da ace wani ne ya ban labarin abinda Muhmoud ya ai kata Wallahi da ba zan yarda ba, wato Jamila Wannan Yarinyar da kika gani Mahmoud ne ya satota ya kai ta gidansa tana zama wai yana son ta, kuma anriga anba da ta ga wani fa tsabar hauka irin ta Mahmoud" Hajiya Jamila cikin k'osawa ta ce. "Tom yanzu nufinka ka kawo ta nan ne mu zauna tare ko-ko?" Mahaifin Mahmoud sanin halin Hajiya Jamila da ya yi ya sa ya d'aure fuska ya ce. "Jamila na kawota ta zauna nan ne kafin in dawo daga tafiyar da zanyi da kaina zan kai ta gaban Iyayanta, dan Allah Jamila kar in ji wata hayani dan Allah har in daw.." Hajiya Jamila katse Mahaifin Mahmoud ta yi ta hanyar cewa, "Alhaji kai ma ka san zaman Yarinyar nan ba abu bane mai yuwuwa in da ka san Nafisa na gidan nan, kuma ka san ba ai mata adalci ba haba dan Allah ta ya za ta ji d'ad'i ma ace mijin da zata aura ya sato wata suna zaune tare gida daya Kai ma dai kasan haka ma bai dace ba." Mahaifin Mahmoud ganin Kiran abokin tafiyarsa ya sa ya ce "Jamila dama ba amincewarki nake nema ba" ya na kaiwa nan ya nufi Falon Hajiya Jamila. Hafsat na zaune gefe guda a rakub'e, Nafisa ko ko kallo Hafsat ba ta issheta ba. Mahaifin Muhmoud kallan Hafsat ya yi ya ce. "Zo mu je ko?." Hafsat tashi ta yi ta bi bayan Mahaifin Mahmoud, Mahaifin Muhmoud gudin fitina part d'in Mahaifiyar Mahmoud ya kai Hafsat ya ce. "Ki yi hak'uri kin ji ki zauna nan har in dawo akwai ko mai da za ki buk'ata anan har in dawo." Yana kaiwa haka ya fita daga part d'in. Mahaifin Mahmoud Falon Hajiya Jamila ya koma ya ce. "Jamila na tafi sai na dawo" Ciki-ciki Hajiya Jamila ta amsa mai. Bayan Mahaifin Muhmoud ya tafi ne Hajiya Jamila ta kalli Nafisa da ke charting a wayarta ta ce. "Nafisa hankalinki kwance charting ma ki ke abunki ko?" Nafisa ko jin haka da sauri ta d'ago ta ce. "Mommy lafiya? Ni yanzu in ba aure na da Broz Mahmoud aka fasa ba me zai d'aga min hankali" Hajiya Jamila kallan baki da hankali ta yi ma Nafisa ta ce. "Tom waccan Yarinyar da ki ke gani wadda Alhaji ya zo da ita yanzu tom budurwar Mahmoud ce kuma akanta ya ke wulak'anta ki har ya ke nuna be son auranki" Nafisa da fe k'irji ta yi ta ce. "Na shiga uku Mommy kina nufin wannan munafukar Yarinyar da Abba ya fita da ita budurwar Broz Mahmoud ce?" In ji wa ya ce mi ki fita ya yi da ita? Tom ta nan part d'in Uwar shi ya ajeta" Nafisa tashi ta yi daga zaunan da ta ke ta ce. "Mommy me haka ke nufi? Dan Allah ki je ki kore ta" Hajiya Jamila kallan Nafisa ta yi ta ce. "Nafisa ai ni yanzu Alhaji sai ya ga laifina amma ke za ki je ki mata jan ido ki koreta da kanki" Nafisa tashi ta yi ta nufi part d'in da Mahaifin Mahmoud ya aje Hafsat. Allah sarki Hafsat ko tunda Mahaifin Mahmoud ya fita ya barta ta ke aikin kuka dan bata tab'a jin ta tsani Mahmoud ba kamar yau. Zaune ta ke ta kifa kanta jikin caution sai kuka ta ke Nafisa ta shigo falon. Nafisa kallan rainin hankali ta ke ma Hafsat, inda ita kuma Hafsat bata ma sanda Nafisa a gun ba. Nafisa cikin isgilanci ta d'ago kan Hafsat ta ce. "Dan uwarki me ye had'inki da Broz Mahmoud? Da har Abba ya kawo ki nan gidan da zama" Hafsat kallan Nafisa ta ke kamar wata wawiya. Nafisa cikin d'aga murya ta kuma cewa. "Dan Ubanki ba da ke nake magana ba? Na ce me ye had'inki da Broz Mahmoud?." Allah sarki Hafsat ita ko tama za ci Nafisa k'anwar Mahmoud ce Hafsat cikin jin zafin yadda Nafisa ke zagin Iyayanta ta ce. "Malama kar ki kuma zagar min Iyaye in da ba sa'anninki ba ne ba" Nafisa da idonta ya gama cika da kishi kallan Hafsat ta yi ta ce."Eh tabbas ba sa'annina bane taya sakararrun iyayanki dama za su zama sa'annina zo ki fitar Mana daga gida malama" Nafisa ta wani fusgo Hafsat. Hafsat ture Nafisa ta yi ta waneta da mari cikin zafin rai ta ce "ko da wasa karki kuma zagar min sunan Iyaye idan ke biki san darajar na ki Iyayan ba ni na san darajar nawu Iyayan" Hafsat ta ture Nafisa daga jikinta Wanda ya yi sanadiyar kan Nafisa ya bugu da caution. Aiko Nafisa cikin jin zafin yadda kanta ya bugu ta fasa k'ara dama tunda Nafisa ta taho Hajiya Jamila ta bi yo bayanta ta tsaya bakin kofar falon ta na jin duk abinda ke faruwa. Hajiya Jamila jin k'arar da Nafisa ta yi ya sa ta shigo falon da saurinta. Nafisa ko na ganin Hajiya Jamila ta fasha kuka ta rik'e kanta.. Hajiya Jamila ko ganin haka Hafsat ta jawo ta kama da bugu kamar dama jira take tana cewa "Dan Uwarki shi Mahmoud d'in ya d'aure miki gindin da ki ke ganin har kin isa ki ai kata haka" Haka Hajiya Jamila da Nafisa suka taru su kai ta bugun Hafsat, Nafisa na cewa "Shigiya akanki yake ta wulak'anta ni zaki ci ubanki kila ma asiri kikai mai." Hafsat ko tsabar wahala hak'uri ta dawo ba su Hajiya jamila. Turo k'ofar da a ka yi ne da k'arfi ya sa Hajiya Jamila juyowa da sauri dan ganin wa ne ne. Mahmoud cikin tashin hankali ya yo kan Hafsat. Hajiya Jamila da Nafisa da sauri suka matsa gefe guda ganin irin rud'ewar da Mahmoud ya yi ya sa Hajiya Jamila da Nafisa suka lallaba suka fita. Mahmoud ko kwata-kwata bata su ya ke ba cikin rud'ewa ya kamo Hafsat. Hafsat ko ture Mahmoud ta yi ta ce cikin kuka. "Na tsane ka Wallahi! Na shaneka ban tab'a tsanar abu kamar ka ba a rayuwata, kalli kalar rayuwar k'ask'ancin da ka jawo min." Hafsat na kai wa nan ta fad'a kan Caution d'in ta na matsanancin kuka. Mahmoud gaba d'aya ya ma rasa me zai yi me zai ce ma Hafsat ta fahimce shi tsugunnawa ya yi cikin muryar nadama yana cewa " hak'ik'a ni na san mai lafine a gareki Hafsat ba ni da bakin da zan baki hak'uri sai dai in ce dan Allah ki yafemin kin ji?" Hafsat shiru ta yi da kukan da ta ke yi tana mai share hawayanta. Mahmoud tashi ya yi ya shiga toilet ya had'a ma Hafsat ruwan zafi sanna ya dawo falon ya kalle ta ya ce. "Hafsat dan Allah ga ruwa mai zafi ki je ki yi wanka za ki ji d'adin jikinki" Hafsat ita kanta ji tai tana buk'atar wankan ko za ta ji d'adin jikinta hakan ya sa ba tare da ta ce ko mai ba ta ta shi ta nufi hanyar toilet d'in. Mahmoud cin motar shi ya je ya dakko ma Hafsat jakar kayanta da ta zo mata da ita. Mahmoud na nan zaune sai ga Hafsat ta fito tana d'angyasa k'afa. Mahmoud saurin kallan k'afar Hafsat ya yi ya ga sun fama mata kunarta sosai ta gwalje. Mahmoud tashi ya yi ya koma hannun Hafsat ya zaunar da ita kan Caution d'in. Mahmoud kallan Hafsat ya yi cikin tausayawa ya ce. "Me ya hadaki dasu ne?" Hafsat kallan mahmoud ta yi ta kauda kanta can gefe. Mahmoud kallan ta ya kuma yi ya ce. "Hafsat me ya hadaki da du Nafisa, nasan dai kila a haukarta kishi take da ke kinsan itace yarinyar da Abba zai hadani aure da ita". Hafsat kallan Mahmoud ta yi ta ce. "Dama ba k'anwarka ba ce?"Ba k'anwata ba ce 'yar k'anwar matar Mahaifina ce, tunda ta dawo da ita gidan nan da zama ni kuma na bar zaman gidan, kuma ni dama ba wani jituwa mu ke ba da ita matar Abba. Meye silar fadan naku ne?" Hafsat kwashe duk yadda su ka yi da su Nafisa ta fad'a ma Mahmoud. Mahmoud Kai ya girgiza kafin ya tashi ya nufi bangaran Hajiya Jamila. Hajiya Jamila suna zaune ita da Nafisa ta kalli Hajiya Jamila ta ce. "Mommy Allah ya sa ta ji tsoron abinda muka yi mata ta tafi." Hajiya Jamila wani kallo ta yi ma Nafisa sanna ta ce. "Ki kwantar da hankalinki ko ya dawo babu abinda zai far.." Hajiya Jamila bata idasa maganar data ke ba ta ji sallamar mahmoud. Nafisa na ganin mahmoud ya yo kanta ta yi tsalle ta koma bayan Hajiya Jamila. Hajiya Jamila ganin Mahmoud na yowa bayanta kallan shi ta yi ranta ab'ace ta ce. "Bansan wulakanci me kake nufi har bayan nawa za ka zo ka bugeta kome?" Mahmoud bai saurari abinda Hajiya Jamila ke ce mai ya yi kan Nafisa.... ✍🏻 Fadila Sani Bakori ce 💓💞SO NE SILA💓 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* Page 17&18 Mahmoud dukan Nafisa ya ke tun iya k'arfinsa. Hajiya Jamila rud'ewa ta yi ganin irin yadda Mahmoud ke dukan Nafisa ga shi daga ta je za ta amshi Nafisar sai ya d'aga bulalar kamar zai zabga mata. Idan ka ji yadda Hajiya Jamila ke ihu za ka d'auka Mahmoud ga ba d'ayan su ya had'a ya ke bugu. Hajiya Jamila ihu ta ke tana cewa. "Wallahi Mahmoud ka raunata min 'ya sai na yi shara'a da kai." Mahmoud bai kula abin da Hajiya Jamila ke cewa ba kamar ma zugashi take. Hafsat tunda Mahmoud ya fara bugun Nafisa ta ke jiyo Ihunta, Hafsat na son fitowa amma tana jin tsoro gashi ta kasa natsuwa jin yadda take jin ihun su Nafisa. Wani ihu Hajiya Jamila ta kurma Wanda ya sa Hafsat fita da gudu ta yi part d'in su. Hafsat ba k'ara min rud'ewa ta yi ba ganin yadda Mahmoud ke bugun Nafisa cikin tsananin tashin hankali Hafsat ta yi kan Mahmoud ta rikesa sosai tana kuka tana cewa " Dan Allah ka yi hak'uri ka rabu dasu Mana." Dan ita Hafsat ta dauka har da Hajiya Jamila mahmoud ya hada yana bugu." Mahmoud jin yadda Hafsat ta ci kwikwiye shi tana kuka ya sa ya jefar da dankon hannunsa kafin ya ce "Allah ya sa ko kazata na kawo gidan nan ki Kara kulata." Mahmoud na kaiwa nan ya ja hannun Hafsat suka fita. Hajiya Jamila rungume Nafisa ta yi tana lallashinta ta ce "Ki yi hak'uri Nafisa Wallahi bebigi banza ba sai ya yi nadamar bugun ki da ya yi. Haka Hajiya Jamila ta dage sai ba Nafisa hak'uri take. Nafisa dai bata ce komai ba, haka ta sha kukanta daga karshe barci ya kwasheta. Hajiya Jamila cikin takaice ta dakko wayarta ta Kira mahaifin mahmoud ta fadi masa karya zalla akan dukan da Mahmoud ya yi ma Nafisa. Mahaifin Mahmoud cikin mamaki ya ce "Yanzu Mahmoud ne ya

Chapter 5 of 10