Share this page
3 / 10
ya makale cikin window. kallan Hafsat Baba ta yi ta ce. " 'Yata tagar nan kan mutum kadai zai iya fita, amma duk da haka akwai wata dabarar da za mu k'ara gwadawa je ki kitchen ki d'akko min wuk'a in b'alle mana k'ofar?." Hafsat kallan Baba ta yi ta yi dariya ta ce. "Baba wuk'a ba za ta b'alla k'ofar nan ba ai" Baba ban za ta yi da Hafsat ta ta fi kitchen d'in da kanta ta d'akko wata k'aramar wuk'a ta na naiman inda zata tusa wukar ta balle kofar. Hafsat duk irin halin da take na k'osa wa ta bar gidan hakan bai hana ta dariya ba, dariya ta kama yi ma Baba ganin ta na ta k'ok'arin b'alle k'ofa kamar wanna da wanna 'yar mi tsi-tsiyar wuk'ar" Baba kallan Hafsat ta yi ranta bace ta ce. "Yanzu 'yar nan ina k'okarin yadda zan ceto rayuwarmu ni da ke shi ne zaki tsaya kina min dariya." Koma wa Baba ta yi ta zauna ranta a b'ace. Hafsat matsawa ta yi kusa da Baba ta ce. "Baba dan Allah ki yi hak'uri Allah dariya kika ban ne" Baba kallan Hafsat ta yi ta ce "Yanzu Shike nan sai dai mu yi hak'uri mu ci gaba da zama har lokacin da Allah ya nufa mu fita" Tom Baba sai dai mu yi ta addu'a Allah ya kawo mana mafita" Ameen 'yan nan." BANGARAN SU FADILA Bayan an tafi da Hafsat fasinjojin motar suka sa Fadila a mota suka tafi cike da jimami da zantawa akan abinda ya wakana. Wani daga cikin fasinjojin ya ce "Wannan fa daga gani an dade ana farautarta, abinda zaku lura ai ita kadai suka kama." Eh tabbas hakane, saboda inda zaku lura sai da aka kirasa a waya ya duba wani abu a wayarsa kafin ya bimu da kallo alamun hoto ne aka tura masa ya ganota." Direban cikin jimami ya ce "Allah dai ya yi mana maganin wannna matsar kidnappers din da muke fatama da ita." Haka dai sukai ta zantawa akan matsalar rashin tsaro dake damunmu. Drivern motar kallan Fadila ya yi da ke kuka ya ce. "Hakuri za ki yi ki mata addu'a yanzu Ina ne gidanku mu kaiki?." Fadila cikin kuka ta ba da address din gidansu. Tana kuka ta na nuna mai hanya a haka har suka zo k'ofar gidan su. Suna zuwa Fadila ta fita tana kuka. Fadila da kuka sosai ta shiga gidansu, daga mahaifiyar Fadila har Mahaifiyar Hafsat ja su ka yi suka tsaya suna kallan Fadila. Mahaifiyar Hafsat kallan Fadila ta yi ta ce "Lafiya wai ke da abin kuka bai miki wuya Ina Hafsat din fa?." Ta idasa maganar tana waigawa bayanta ko zata ga Hafsat. Fadila ta kasa magana sai kuka, sai ga kanwar Hafsat Husna ta yi sallama ta shigo. Kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Mama wasu mutane a waje wai suna sallama da baba." Mahaifiyar Hafsat cikin rudewa ta ce "Innalillahi wa inna ilaihirrajun! Ko dai wani abune ya samu Hafsat din Fadila?." Ta idasa maganar tana sa hijab dinta ta fita cikin tsananin tashin hankali ba tare da ta jira amsar Fadila ba. Mahaifiyar Hafsat dakyar ta samu ta iya gaida mutanan da ta gani fuskarsu cike da alhini alamun wani babban al'amari ya faru. Cikin tashin hankali ta ce "Bayin Allah lafiya?." Daya daga cikin mutanan motar cikin alhinin abinda ya faru ya ce "Wallahi muna tafe tare da yaranku cikin motar nan Allah ya hadamu da masu Garkuwa da mutane suka dauke daya daga cikinsu, yanzu sai dai a yi ta addu'a akuma saurari kiransu." "Innalilahi'wa'inna ilaihirraju'un, Allahhumma ajjirni filmusibati! Sun tafi da Hafsat wallahu galibun ala amrihi." Mahaifiyar Hafsat ta idasa maganar tana fashewa da kuka ta yi cikin gida ta barsu nan tsaye. Da ya ke gidan su Hafsat babban gida ne ka fin kace me magana ta ke waye ko ina, kidnappers sun d'auke Hafsat. Nan fa yara da manya na gidan aka taru sai kuka ake. Mahaifin Hafsat ya yi sallah ma ya shigo gidan cikin kid'ima ya ke tambayar mahaifiyar Hafsat yana ya ce. "Maman Yara abinda na ji a waje da gaske ne? wai masu garkuwa da muta sun tafi da Hafsat?" Mahaifiyar Hafsat cikin zubba kwalla ta ce. "Abinda ka ji haka ne sai dai mu taru mu yi ta addu'a" Nan fa Mahaifin Hafsat cikin tashi hankali ya juya ya fita gidan wajan limamin unguwarsu ya je ya sanar dashi abin da ke faruwa a dan a sasu a addu'a. Sosai limin ya tausaya ma Mahaifin Hafsat nan ya bashi adda'o'i da dama wa in da zai rik'a yi mata in sha Allah zata kubuta cikin lokaci. A ranar duk muta nan gidan ba su yi bacci ba in ka cire k'ananan yaran gidan. Mayan gidan ko dama ba baya ba wajan kiyamullaili haka suka kwana ido biyu suna fadama Allah. Usman ko wanda a ka sa ranar auransa da Hafsat ba shi ya samu labari ba sai dare, dan mahaifiyarsa b'oye mai ta ke ta yi. Aiko cikin tashin hankali ya shi ga gidan, kallan Mahaifiyarshi ya yi ya ce. "Maman Rabi, wai da gaske ne maganar da na ke ji a gari wai 'yan kidnapping sun tafi da Hafsat d'ita?." Mahaifiyar Usman kamo hannun Usman ta yi ta ce. "Haba Babana dad'ina da kai ke nan, kanatsu mana mu yi magana"Haba maman Rabi wata na tsuwa kike so in yi Hafsat dina na hannun mutanan da basu da imani, gaskiya ni dai ba a kyau ta min ba ta ya ma ya za ai a ce matar da zan aura wani abu ya sa meta amma sai dai a waje zan ji labari." Usman na fadin haka ya juya zai fita cikin tsananin tashin hankali Wanda mahaifiyarsa bata taba ganinsa ciki ba. Da sauri mahaifiyar Usman ta kamo hannun Usman din ta ce "Haba Usman dare ne fa yanzu ina zaka?." Wajan malam gurgu zani, in fada mai kinsan ko yaran gidan gidan Alhaji Jabir da aka dauka shi ya yi abin da ya yi aka Sako yaran babu kudin fansa." Mahaifiyar Usman bata fuska ta yi ta ce "Kana da kudin da zaka bashi ne? Ko shi Alhaji Jabir din nawa kasan ya bashi, Kuma kasan dai mahaifin Hafsat ya ji haka ma fada zai maka inda kowa dai yasan malam gurgu boka ne." Usman bata fuska ya yi ya ce "Maman Rabi ni fa ko meye zan iya sai dawa in dai Hafsat zata fito, kawu Kuma da kike magana in dai bake zaki je ki fada mai ba wajan wa zai ji labari?." Mahaifiyar Usman bata fuska ta yi ta ce "Wallahi ban yadda ba yarinyar da bacin ka hada da taimako iyayanta ba za su taba baka ita ba ita ce za ka je ka Kai kudi a fito da ita to baka isa ba." Usman da sosai yake son Hafsat cikin jimami ya ce "Maman Rabi Hafsat fa ko da ace ba auranta zan yi ba Yar kaninki ce ban yi asara ba, sannan ni tunda malam garku ya sa Hafsat ta soni na yadda da aikinsa, kalli fa da yadda Hafsat ta tsanan amma lokaci guda lamari ya juya wanda har su kawu mamaki suke." Ka dai ji abinda na ce maka tana fadin haka ta juya ta tafi ta barshi nan tsaye. Usman zaune a gaban malaminsa, bayan sun gaisa ne malamin Usman ya ce. "Usman kar dai ka ce min tak'ara bijire ma?." Usman kalan malamin shi ya yi cikin damuwa ya ce. "A'a Malam ai yanzu ko mai ya dai-dai dan yanzu ma haka ka saura kwana goma sha hud'u bikinmu, tom Malam wata matsalar ce kuma ta faru, masu garkuwa da muta ne ne suka yi garkuwa da ita tom daga ni har Iyayan yarinyar babu mai kud'in da in sun sara za a basu shine na zo dan Allah a taimaka min a ku b'ito min da ita" Bokan Usman kallan Usman ya yi bayan ya gama zane-zanansa a kasa ya ce. "Hafsat za ta dawo ba tare da abinya kudin fansa ba Kuma auranka da ita zai tabbata kamar yadda na ce maka, amma Kuma ga wata gura nan dake tashi ta baibaye komai wadda na rasa daga Ina take" Usman kallan malam gurgu ya yi ya ce "Da fatan dai kuran nan ba zata shafi auranmu ba?." Bokan Usman dariya ya yi ya ce "Usman kasa fa bata karya na fada maka akwai rabo tsakaninka da yarinyar nan dan haka babu abinda zai hana auranku, yanzu haka k'urar nan da na gani sai da na Kara bincike akan auranka da yarinyar Kuma na ga babu wata matsala saidai wannna kurar da ta lillibe ko Ina, amma karka damu ka kawo dubu 200k za a yi taimakon da wowarta da na maganin kurar da na gani." Shiru Usman ya yi kafin ya ce "Shi kenan zan yi ƙoƙarin hado kudin in kawo." Gidan su Hafsat ko kullum cikin jiran kiran Kidnappers su ke amma shiru addu'a ko yinta suke ba su fa sa ba. Fadila ko ba ta da aiki sai kuka, kasan cewar tafi kowa shakuwa da Hafsat a gidan. BANGARAN SU HAFSAT KUWA. Yau Mahmoud kwanan shi goma ke nan babu shi babu labarinsa, Hafsat da Baba kullum cikin addu'a suke, sai dai zuwa yanzu Hafsat ta d'an saki ranta, dan ko aikin abinci tare da Baba su ke yi. Ma sha Allah yanzu Hafsat ta saki ranta ba kamar da ba, abu d'aya ya fi damun ta in ta tuno da Iyayanta da Usman d'inta su na can cikin damuwa akan rashinta, wannan shi ne abin da ke ta da ma ta hankali sosai. Usman zaune gaban Malaminsa ya kawo masa kudin da ya bukata. Usman cikin damuwa ya ce "Malam gashi a taimaka min saida na saida wasu abubuwa daga cikin lefan da na hada kafin na samu na hada kudadan nan, dan Allah a taimaka min." Dariya bokan Usman ya yi ya ce. "Ai kamar yadda na fad'ama Usman yanzu haka duk Wanda ya d'auki Hafsat da zarar mun yi aiki nan dolansu su sallameta ko ta kubuta dakanta dan cikin biyu za a yi daya ko dai su ji ku lallanta basa son yi a wajan zata zamar masu kamar mujiya a. Wajan, ko kuma ina mai tabbatar ma duk Wanda ya d'auke ta ko yake da sa hannu a dauketa daga zarar na yi aikin nan a daran yau sai ya makance, makatanta za ta samesu har ta baro gun ba za su ankara ba." "Yanzu Malam nan da kwana nawa za mu sa ranta?." Usman ka ban nan da kwana uku, na yi ma ka alk'awari sai Hafsat ta dawo, kai idan ma ka na so aranar da ta dawo za a d'aura auranka da ita a sakko dashi duk mai yuwu ne, kai dai ka bi ko mai a hankali" Usman sosai ya ji d'adin maganar da bokansa ya fada masa dan bai taba fada masa abu bai faru ba, hakan ya sa cikin gwarin gwiwa ya tafi gida cike da jin dadin albishir dinsa dan ya san zai iya fiye da haka ✍🏻 Comment and share please Fadila Sani Bakori ce ❤️💞SO NE SILA❤️ 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* Mahmoud kallan Hafsat ya yi ya ce. "Ki je ki kwanta sai da safe" Yana kai wa nan ya tafi ya bar Hafsat nan tsaye. Hafsat ma data gaji da tsayuwa ta fitaya ta yi ta kwanta sai dai Hafsat yadda ta ga rana haka ta ga dare dan ga ba d'aya ta kasa bacci cikin tsananin tashin hankali take ace baba ta tafi ta barta. Washegari Baba da wuri ta ta shi ta shiga kitchen ta yi musu abin karyawa, Baba na gama wa ta shiga ta yi wanka abinta kafin 8:00am Baba ta gama duk wani shiri kafin ta shiga dakin Hafsat, zaune ta iske Hafsat ta yi ta gumi, Baba breakfast ta mik'a ma Hafsat ta ce. " 'Yata ta shi ki karin kumallo" Hafsat kallan Baba ta yi ta ce. "Baba ba zan ci komai ba ni dai bana so ki tafi ki barni gidan nan" Haba 'Yata dan Allah karki haka mana yunwa fa ba abu ba ce mai kyau, Kuma ai baki ga tafiyar tawa ba ki Ki jira ki gani kila ya ce mu tafi tare. Ke ce tun farko na baki shawara akan ki aminta da soyayyarsa amma kika ki da yanzu kila ya maida ke gidanku ma. Shi aure da kike gani muk'addari ne na Allah idan Allah ya nufi ba zaki auresa ba komai zai yi saidai ya yi ya yi hakuri, haka Kuma idan Allah ya kaddari aure tsakaninku Kuma ke ma saidai ki yi hakuri" Allah shi kyauta Baba in auri d'an fashi Allah ya yi min tsari da auran mutum irinsa.." Mahmoud da ke bakin k'ofa duk ya ji abinda Hafsat ta ce da sauri ya k'araso d'akin in da Hafsat ta ke ya nufa tsugunnawa ya yi ya na kallan Hafsat kafin ya ce. "Hafsat da gaske kallon d'an-fashi ki ke min?" Jin Hafsat ta yi shiru Muhmoud fi ta ya yi bayan ya dawo ne ya mik'a ma ta I'd card d'in sa ya ce. "Hafsat ba dan fashi bane kamar yadda kika dauka ni soja ne, dan na d'akko ki shine ki ke min kallan d'an-fashi?" Eh mana ai bani kad'ai ka sato ba kuma Wanda ba d'an-fashi ba ba zai iya satar muta ne ba ni abinda kai min meye shi? Akan me zaka d'akko ni ka kawo ni gidanka ka aje? Wai dan ka wai kana sona wanna ba hujja ba ce kuma bata haka ake nuna so ba, dan haka d'in da ka yi daga ni har Iyayena za mu d'auke ka amatsayin mafaraucin mutane kai ne ba wai masoyina ba. Sanna ka sa ni daga ni har Iyayena da duk wa ni masoyina ba za mu tab'a ganin haskenka ba" Hafsat na kai wa nan kuma ta kama kuka. Muhmoud kallan Hafsat ya yi ya ce. "Hafsat idan duk duniya zasu taru suce ni makiyinki ne ni nasa ba haka bane, saidai nasan akwai lokaci zai zo wanda kema zaki shaida Mahmoud masoyi ne agareki na hakika shaida ni masoyin ki ne na hak'ik'a. Allah ya nufa sai a k'urarran lokaci zan sanki Hafsat, ban tashi saninki ba sai alokaci k'urare lokacin da ake sanar dani kwanakan bikin ki na duba bani da wata mafita wadda ta wuce abinda na aikata saboda za a dauki rabon wani gida ne akai wani gida" Baba jinjina Kai ta yi kafin ta ce " Amma yarona a Ina kasan Hassatu bayan na ji ta ce ita bata sanka ba? Kuma na ji ka na cewa ak'urarran lokaci ka santa?" Baba na raka wani abokina ya biya ma kanwarsa d'in Neco anan naga Hafsat a ranar na santa, wallahi baba kallo d'aya na yi ma Hafsat lokaci guda Allah ya d'ora min son ta, Amina kanwar abokina ita muka tambaya ko ta sanki nan ta ke fad'a mana ta sanki tom gurinta ne ma mu ka samu labarin auranki da za ai bayan sati biyu da candy dinku. Duk da Amina ta fad'amin haka ban sare ba na amshi address d'in gidanku alokacin Mahaifina ba ya nan sai dai abokinsa ne ya je gidanku naima min auranki amma sai dai hak'uri aka ba shi aka sanar da su saura kwana kadan bikin ki, wannan maganar sosai ta tada min hankali tun ina ganin abin kamar wasa har ya nai mi kwantar da ni, bansan ko dan ban taba mai da hankali a al'amuran soyayya bane abin ya zo min a haka, sai da na zamana ko abinci bana iya ci Wallahi, barci ya fara kaurace ma idona anan na fahimci so mai girma nake ma Hafsat baba, saboda ni ba komai ke hanani barci ba, ba kasafai ake gane damuwata ba amma hatta mahaifina sai da ya fahimci Ina cikin damuwa, Wallahi Baba na yi iya k'okarina akan in ga na hak'ura da Hafsat amma abin ya ci tura ganin ba ni da wata mafita ne ya sa na yanke wannan shawara na ka wo Hafsat nan gidan ko zata fahimci na fi wanda zata aura kaunarta" Baba sosai ta ji sausayin Mahmoud, kallan shi ta yi ta ce. "Tom, duk da haka amma ni da za ka ji shawarata a matsayin ka na Wanda ba murarramin Hafsat ba akwai da muwa ka zauna daga kai sai ita yau da gobe sai Allah shed'an zai iya ratsa tsakanin ku ka yi hak'uri ka mai da Hafsat gaban Iyayanta idan rabonka ce za ka aure ta dan ba mai auran matar wani, ko iyayan Hafsat za su yi fushi dakai duk sansa suka fahimci kaika dauke musu 'yarsu ba za su amshi hujjarka ba gaskiya" Muhmoud kallan Baba ya yi cikin sanyi ya ce. "Baba wallahi ba zan iya mai da Hafsat gida ba gashi da bakinki kin ce iyayan Hafsat ba za su dauki hujjata ba. Amma na yi miki alk'awarin zan rike Hafsat da Amana ba zan cutar da itaba daidai da rana daya ba in sha Allah har izuwa ranar da Hafsat zata fahimci son da nake mata ta waiwaye gareni da zuciya daya ta gaskiya." Hafsat jin haka ya sa ta fashe da kuka ta na cewa "Allah ba zan zauna ba ko ana so dole ne ni babu ranar da zan soka gara ma ka barni in tafi gidanmu." Hafsat fashewa da kuka ta yi sosai tana hade hanna yanta waje guda ta ce ma Mahmoud "Dan Allah ka taimaka min kar ka bari baba ta tafi ta barni". Baba kamar za ta yi kukan itama ta kalli Hafsat ta ce "Dan Allah Yar nan ki bar cewa haka, Kinga yayana za su shiga wani hali na rashina." Mahmoud rasa abinda zai ce ya yi ya dade a haka kafin ya kalli Baba ya ce. "Baba ki shirya in kai ki da wuri" Baba kallan Mahmoud ta ce "Nama shirya tun d'azu" "Ok tom ta shi mu tafi" Baba ta shi ta yi Hafsat ma tata shi ta rik'e Baba tana kuka sosai tana cewa. "Dan Allah Baba karki tafi ki barni wallahi ba zan iya zama ni kad'ai ba, dan Allah Baba ki taimakeni dan Allah mu tafi tare" Allah sarki Baba kuka take itama dan sai ta ji ba dad'i da zata tafi ta bar Hafsat tasan koba komai Hafsat na rage damuwa ganinta a gidan, gashi babu damar ta roki Mahmoud ya bar Hafsat su tafi tare itama ya ce ya fasa. Baba dafa Hafsat ta yi ta ce. "Ki yi hak'uri Hafsat zan dawo matukar yayaran sun yadda" Baba ba gaskiya ba ne ni nasan ba za ki dawo ba" Hafsat bin baba ta yi tana kuka sosai, Babu yadda Baba ba ta yi da Hafsat ba ta sa ke ta amma Hafsat tak'i, Muhmoud da ke tsaye kallan Hafsat ya yi ya ce. "Ki saketa ke ma zan maida ke gida" Hafsat Maimakon ta saki baba k'ara rik'e Baba ta yi. Babu yadda Muhmoud bai yi da Hafsat ba ta saki Baba amma ina abun ya ci tura dan ta rirrike Baba ko ta ina. Mahmoud da k'arfin tsiya ya fusge Baba daga hannun Hafsat ya ce. "Baba yi sauri ki fita" Baba da gudu ta fita daga falon ta tsaya farfajiyar gidan tana goge hawaye. Hafsat ko rik'e rigar Muhmoud ta yi katakam ta na kuka kamar wata zautatta. Mahmoud babu yadda bai yi ba Hafsat ta Sakai amma taki tana cewa "Wallahi sai dai mu fita gidan nan tare ni ba za a barni ni kadai ba." Hafsat ta hauka ce ma Muhmoud. Muhmoud duk yadda zai yi Hafsat ta sa ke tak'i sakin shi ga shi shi kuma bai son sa ma ta k'arfi daga k'arshe dai da ya ga dagaske fa take ba sakin shi za ta yi ba hakan ya sa dole ya ja hannunta da k'arfi ya kai ta bedroom d'inta ya turata ciki rufeta ciki kafin ya sauke ajiyar zuciya ya fita ya samu baba daike waje tana sharar hawaye. Mahmoud da kwatancan Baba ya kai ta malumfashi har kofar gidanta. Lokacin da suka isa babbar yarinyar Baba na gidan cikin murnarta ta tari Baba yarinyar Baba kallan Muhmoud ta yi ta ce. "Inna wannan fa?"Wanan shi ne Wanda ya tai ma ke ni bayan na je na kasa gane gidan Usaini" Godiya sosai yarinyar Baba ta yi ma Mahmoud. Muhmoud kallan Baba ya yi ya ce. "Tom Baba ni zan koma na gode sosai Allah ya saka da alkairi" kafin Muhmoud ya ciro kudi masu yawa ya ba Baba. Baba amsa ta yi ta yi ma Mahmoud godiya sosai ya tafi. Muhmoud ya na da wowa daga kai Baba ba shi ya dawo gida ba sai dare. Hafsat ko tun tafiyar Baba ta ke kuka kuma har yanzu Babu abinda ta ci sallah kadai ke ta da ta, kafin dare zazzab'i ya rufe Hafsat. Muhmoud ko lokacin da ya shigo gidan ya so zuwa ya duba Hafsat amma yana jin tsoran karta ce sai ya mai da ta gida in da ya ce ma ta zai kai ta itama, hakan ya sa yana da wowa ya tafi ya kwanta duk da sosai ya so ganinta amma yana jin tsoron Hafsat din dan ta bashi tsoro dazu. Kafin safiya jikin Hafsat ya yi za fi sosai. Muhmoud ko ya na tashi ya ci karo da sakon Mahaifinsa akan ya na son ganinsa hakan ya sa yana gama shirinsa ya nufi d'akin Hafsat dan ya ganta, sai alokacin ya tuna da rufe ta d'in da ya yi, lokacin da zasu tafi da Baba, Muhmoud kwance ya iske Hafsat ta lillib'e dukka jinkinta tsabar zazzab'i jikinta ko ina rawa ya ke. Muhmoud da sauri ya k'arasa in da ta ke bud'e rufar da ta yi ya yi sai dai jikinta ko ina rawa ya ke saboda zazzab'i, Muhmoud cikin da muwa da halin da ta ke ciki ya ce. "Subhanallahi mai ke da mun ki haka ? Ayyah ki yi hak'uri kin ji lokacin da na dawo na yi tunanin kin yi bacci ne meke damunki?" Hafsat da ya ke ta kanta ta ke ko in da Mahmoud ya ke ba ta kalla ba bare ya sa ran za ta ba shi amsa. Muhmoud ganin yadda Hafsat ke rawar sanyi ya sa ya kira Aminu a waya, cikin lokaci k'an-k'ani ya iso duba Hafsat ya yi sanna ya kalli Mahmoud ya ce, "Mahmoud Ulcer ce ke da mun ta, sannan kuma gaskiya ita ta sakar mata zazzabin nan." Magungunan ya rubuta ma ta da alurai Muhmoud ya je ya siyo. Wajan yin allura ne fa Hafsat ta ce ita fa ba za ai ma ta allura ba duk yadda doctor Aminu ya so yi ma ta dan zazzab'in ya sau ka amma ta k'i, Dole suka rabu da ita, bayan likitan ya gama duba Hafsat ne ya fita, Muhmoud ya d'akko Magungunan ya bata Hafsat ko in da Muhmoud ya ke ba ta kalla ba ta ce. "Ni dai ba zan sha ba Allah har sai ka mai dani gidanmu" Muhmoud cikin tausasa murya ya ce. "Tom na ji kisha maganin zan mai da ke in da kinga dai ai ba za ki tafi haka da zazzabi ba ko?" Hafsat da sauri ta ta shi daga kwancan da take ta ce. "Dan Allah da gaske ka ke za ka mai da ni gidanmu idan na sha?" Eh zan mai da ke, amma sai kin shanye duka magungunan nan kinga lokacin kin ji sauk'i sosai" Muhmoud d'aukar magungu nan ya yi ya bud'e ya ba Hafsat d'aya ba yan d'aya haka ta amsa ta sha. Bayan Hafsat ta gama

Chapter 3 of 10