Share this page
9 / 10
daga falon mahaifiyar Hafsat kamar a rude yake hakan ya sa ya bi bayansa ya kirasa. Usman juyowa ya yi yana goge hawayansa, mahaifin Hafsat cikin rudewa dan yayi tunanin wani abu ne ya samu Hafsat ya ce "Usman, me ya samu Hafsat din?." Usman fashe ma mahaifin Hafsat da kuka yi dama kiris yake jira. Mahaifin Hafsat hannunsa ya kama ya shiga dashi dakinsa, bayan ya zauna ne ya ce "Usman me ya faru?." Usman kamar mace yana kuka ya ce "Kawu, Hafsat ta ce bata sona wani take so wai Kona aureta gangar jikinta na aura ba ita ba." Mahaifin Hafsat shiru ya yi kafin ya dafa Usman din ya ce "Ka yi hakuri Usman ka ji, nina san watarana Hafsat za ta soka, idan aka furta Mata irin kalaman nan da ta yi maka aka ce ita ta yi sai ta yi fada da Wanda ya furta mata su, ka yi hakuri Kar ma ka tada hankalinka duk shirman banza ta ke yi daga ta ga an daura auran zata hakura." Mahaifin Hafsat sai da ya kwantar ma Usman hankali kafin ya barshi ya tafi. Haka gidansu Hafsat aka ci gaba da shirin biki dan har cincin da dibulan duk an yi. Mahaifiyar Hafsat da duk ta rasa sukunin rayuwa ganin halin da Hafsat ta sa kanta. Yanzu haka kanwar mahaifin Hafsat din ce ta shigo dakinsu Hafsat din tana cewa "Ni dai tasan ubanta zanci Wallahi barinta aka yi shi ya sa har take iya bude baki ta ce ba ta son Usman din. Hafsat zaki tashi game kunshi nan tana jiranki ki zo ai miki ko sai na ci ubanki." Cewar kanwar baban Hafsat din autarsu kenan. Hafsat komotsawa ba ta yi ba dan ta kanta take, jikinta gaba daya ba karfi idan ta tashi juwa take gani. Kanwar mahaifin Hafsat duka ta maka ma Hafsat din ta ce "Ba za ki tashi ba dan ubanki." Hafsat ido ta bude tana kallan gwaggon tata. Ita kuma ganin Hafsat din kamar duk iskanci ne abun da take yi hakan ya sa ta sa hannu ta duma ma Hafsat din dundu a baya wanda ya sa Hafsat tashi da sauri tana rike Kai. Tsawa kanwar mahaifin tata ta yi ma Hafsat ta ce "Za ki wuce mu je ne ko saina yi miki wanda ya fi na yanzu." Hafsat da sauri ta tafi, tafiya daya biyu ta yi ta yanke jiki ta fadi a wajan a sume✍🏻 Fadila Sani Bakori ce 💓💞 SO NE SILA 💓 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* Page 27 & 28 Gwaggon Hafsat ko kafin ta tare Hafsat har ta kai kasa, cikin tsananin tashin hankali ta yi kan Hafsat din tana girgizata tana tana Kiran sunan Hafsat din. Kafin ka ce me labari ya bide gidan Hafsat ta sume, kanin mahaifin Hafsat da ya zo gwaggon Hafsat din ta kallai a hankali ta ce "Yaya Aminu, ka ka Mata mu kaita Asibiti." Kai ya girgiza ya ce "Zai zamar Mana abin surutu kin ga dai jibi ne daurin auran nan, gani nake kawai a yi ma mai chemist din kusa damu din nan magana ya dubata." Yana fadin haka bai saurari cewarta ba ya fita sai gashi sun dawo da me chemist din. Kasan cewar ya sanar dashi halin da Hafsat din ke ciki hakan ya sa ya na zuwa ya sama Hafsat din drip. Maifiyar Hafsat ko ko dakin bata shigo ba tana gefe. Atakaice dai sai da aka sama Hafsat ruwa leda biyu kafin ta dawo hayyacinta. Wan mahaifin Hafsat ganin halin da Hafsat din take ciki ya sa da daddare ya tara yan'uwan nasa kaf har da mahaifin Hafsat din ya fara magana kamar haka. "Gaskiya a yadda yau na ga Hafsat anya ko ba za mu yi kuskure ba mu ce za mu dauketa a wannan halin mu kaita gidan mijin da take ikirari bata so, ni shawarata ko dai a taru aba Yaya Uwani baki a hakura abar yarinyar nan idan akwai wanda take so ne a aura mata ko Kuma a daga bikin nan har lokacin da hankalinta zai kwanta ta yadda da auran. Ko ya kuka gani?." Aminu ne ya amshe zancan da cewa "Tabbas nima a yadda na samu labarin abun haka na ce Kar mu zo mu yi abin da zai lalata zumuncinmu da kanmu, Maimakon gyarawa mu zo mu bata, nima dai shawarata idan zai yuwu a hakuri kamar zai fi idan muka yi duba da halin da ita Hafsat din take ciki." Mahaifin Hafsat katsesu ya yi da cewa "Ni Kuma a shawarata mu yi hakuri mu bar duba halin da Hafsat take ciki mu duba zumuntarmu, saboda fasa wannan aure tamkar ruguza zumuntarmu ne, sannan idan ma ance za a fasa cikin mu wake da jarumtar zuwa ya tunkari Yaya Uwani da wannan maganar?." Aminu daga hannu ya yi ya ce "Ni, yanzu haka idan Kun yadda zan je har gida in sameta in sanar da ita halin da Hafsat din take ciki mu yi hakuri mu bata zabin ranta shi Kuma Usman ya rungumi kaddara saboda ni dai a yadda nake ganin Hafsat ko an yi auran nan ba dadint zai ji ba, gara ma ya yi hakuri ya samu me sonsa." Autarsu Jimmai sai yanzu ta yi magana ta ce "Yaya Nasiru, Tabbas na ga halin da Hafsat take ciki dan a gabana ma ta Fadi ta suma, amma fa ku Sani an yi fiye da abin da Hafsat ta yi Kuma ba a fasa auran ba an yi auran yanzu haka maganar da nake muku idan kuka ga yarinyar aka fadamu hakan da ta yi kafin auran sai Kun ce karyana, Wallahi har fiya-fiya yar nan ta sha ta ce gara ta mutu da akaita gidan wannan bawan Allah, haka aka samo rayuwarta da kyar, Kai in ta kaice muku zance tana Asibiti tana jinyar fiya-fiyar da Tasha aka daura auran, yanzu haka gatacan shiru yaranta biyar kenan." Babu haukar da yara basa yi irin haka Kuma idan aka yi auran ka ji su shiru, idan kuka ce zaku tari Yaya uwani da wannan maganar abin da zata dauka Kun fi damuwa da damuwar Hafsat fiye da ta danta Usman wanda shima jiya Yaya Uwani ke sanar dani ko abinci baya ci ya sa kansa a cikin tashin hankalin damuwar auran." Innalillahi wa inna ilaihirrajun, yanzu ya kuke ganin za a bullo ma wannan abun kenan?." Aminu cikin sanyi ya ce "Tom ni gani nake kawai a daga auran a Kara ko wata daya ne mu gani, kafin nan mu hadu mu yi ta fata baki ko ya kuka ce ?." Jimmai ta ce "Eh tom a yi hakan idan Kuna ganin hakan zai iya kawo maslaha nan gaba." Aminu ya so zuwa gidan yayar tasu sai dai ganin dare ya yi ya sa ya bari sai washe gari. Washe gari Aminu sammakon zuwa gidan yayar tasu ya yi, inda ya je ya iske mutane har sun fara zuwa 'yan nesa, nan suka gaggaisa sosai har yana tonansu, bayan sun gama gaggaisawa ne ya shiga dakin Yayar tasu shiru bata nan tambaya ya yi aka sanar dashi tana dakin Usman, dakin Usman din ya nufa inda ya je ya isketa da tea ta tasa Usman din sai ya sha. Dariya Aminu ya yi ya ce "Kai Yaya Uwani sai ka ce wani karamin yaro zaki zo ki tasashi sai ya ci abu." Cikin damuwa Yaya Uwani ta ce "Aminu Usman ya sa ma kansa damuwa so, sai ya dora ma kansa wani ciwon, daga na yi masa magana ya sa kuka kamar wani yaro wai Hafsat bata sonsa, tom karyar so dai ta kare tana sonsa bata sonsa duk ta kare in da dai gobe in Allah ya kaimu za a daura auran." Aminu ajiyar zuciya ya sauke, kafin ya ce "Ikon Allah wanan Abu ya yake faruwa haka, itama Hafsat din mafa jiya haka aka taru kanta ta sume ma mutane sai da aka Kara mata ruwa leda biyu kafin, yanzu haka akan maganar na zo, na ce Yaya Uwani kodan shi kansa Usman ya samu natsuwa da auran Hafsat din me zai hana a daga auran kafin ita Hafsat din a samu ta sakko ko..." Yaya Uwani tare Aminu ta yi ta hanyar cewa "Ya zanyi da mutanan da na gayyata waye ma ya tsiro da shawarar nan, idan za ku fasa aura ma Usman Hafsat kawai ku sanar da ni Kun fasa ba wai ku ce min za a daga aure ba, idan ba iskanci ba da Kuma rainin arziki da aka yi min taya ana gobe biki ku sanar dani wai za a daga, tom idan amincewata ka zo naima ban amince a daga auran ba, Hafsat yata ce ko ni kaina zan yi jinyar abata, idan Kuma har kuka daga auran nan Usman ko zai mutu ne Wallahi ba zai auri Hafsat ba." Tana kaiwa nan ta juya zata fita ranta tsananin bace." Aminu dama yasan hakan zai faru da sauri ya kamo hannun yayar tasu ya ce "Shi ke nan Yaya Uwani ki yi hakuri haka za a yi, za a daura auran gobe in sha Allah." Uwani kamar za ta yi kuka ta ce "Kana gani fama nake da Usman akan ya ci abinci, tun yanzu baya iyacin wani abu akan maganar nan Ina ga ance an daga ai bashi ba ni kaina sai inga kamar wayau kuka yi min na fasawa. Kullum Allah-Allah nake ayi auran nan ko na samu sukunin rayuwa hankalina ya kwanta na Usman ma ya kwanta." Aminu dai ya kasa cewa komai haka ya tashi ya dawo gida ya samu yayanshi Nasiru mai bima uwani ya ce "Na je na samu Yaya Uwani da maganar daga auran nan amma ta sanar dani idan har aka daga auran to Usman ko zai mutu ne ba zai auri Hafsat ba kamar yadda ta ce, yanzu ya kake gani?." Shiru Nasiru ya yi kafin ya ce "Aminu, duk abinda ka ga anata addu'a akai Kuma babu wani abu da ya sauya gani nake mu yi hakuri kawai idan Allah ya kaimu gobe a daura auran Allah ya basu zaman lafiya, sannan kamar yadda Jimmai ta ce nima akwai 'yar wani abokina haka aka yi Kuma yanzu haka tana gidan mijin ta zauna, itama muna fatan in sha Allah za ta yi hakuri ta zauna." Kai Aminu ya jinjina bai ce komai. Bangaran Hafsat ko Mahaifiyarta tun tana lallashinta ta gaji ta rabu da ita. Yanzu haka magungunanta ta matsa Mata ta sha kanin mahaifin nata Aminu ya yi sallama ya shigo. Zama ya yi yana amsar magungunan da kansa ya bare ya ba Hafsat, bacin ta sha ne ya ce "Hafsat, ki yi hakuri ki yi hakuri ki yi hakuri ki amshi wannan kaddarar in sha Allah zaki ga alkairin abun, dukanmu babu Wanda baya addu'a akan auran nan naki amma Kinga abun har yanzu bai canza ba dan haka kila hakan ne alkairinki ki yi hakuri kin ji bana son Kara jin Kin yi musu da kowa kin ji Hafsat?." Kai Hafsat ta daga tana fashewa da kuka ta ce "Nima Ina so in yi hakurin Baba Amma na kasa, na ka sa in yi hakurin ya zan yi in yi hakurin?." Za ki iya Hafsat, ki daure ki fitar da komai a zuciyarki ki fuskanci zabin iyayanki kin ji?." Kai Hafsat ta daga tana goge hawayanta. "Yauwa 'yar albarka Allah ya sa ki yi alfahari da auranki nan gaba, yanzu Ina me yin zane-zanan nan na hannu a kirata ta yi Mata." Kai Hafsat ta girgiza ta ce "Baba na hakura, amma dan Allah Kar a yi min kunshi bana so." Tom shi ke nan ba za a yi ba Hafsat, amma ki yi min alƙawarin zaki bar kukan nan?." Hafsat goge hawayanta ta yi tana daga mai Kai alamun ba zata Kara ba. "Yauwa Yar Albarka fada min yanzu me kike so?." Babu komai baba." Tom shi ke nan." Bangaran Mahmoud an sallamesu suna gida mahaifinsa ya sanar dashi an yi bikin Hafsat tuni, mahaifin mahmoud ya fada masa haka ne dan mahmoud ya yi hakuri da Hafsat, sai dai hakan sosai ya Kara jefa mahmoud cikin wani hali, Wanda har abinci ya gagaresa ci, sai dai sosai yake ƙoƙarin boye damuwarsa a gaban mahaifin nasa, saidai har yanzu Yana gida bai koma aiki ba dan har yanzu baya jin dadi, wani irin tari yake Wanda idan yayi kaki jini yake gani, ganin abun na naiman yi masa yawa ne hakan ya sa yau ya shirya ya nufi Asibiti, inda likita ya sanar dashi yana fama da ciwan zuciya. Mahmoud bai wani damu da lafazin limitan ba duk da ya amshi magunguna sai dai baya jin zafin ciwan dake damunsa kamar yadda yake jin zafin rabuwa da Hafsat, duk abin da yake yi daga ya tuno tana gidan wani duk sai hankalinsa ya tashi ya kasa komai. Yanzu haka fitowarsa daga office din likitan kenan wayarsa ta fara ruri na naiman agaji, dagawa ya yi yana sauraran mai Kiran. Mahmoud sai da ya dafe kirji jin abin da me Kiran ya ce ya ce "Ka tabbata abinda kake sanar min haka ne?." Mahmoud kashe wayar ya yi yana murmushi Mai ciwo. Number mahaifinsa ya Kira yana dagawa ya ce "Abba me ya sa? Me ya sa zaka sanar da ni Hafsat ta yi aure bacin ba haka bane? Gashi ban samu labarin Hafsat ba ta yi aure ba sai yanzu, sai dai na sani a korarran lokaci, Wanda yake sanar dani ya sanar dani gobe ne daurin auranta. Mahmoud ya idasa maganar kamar zai fasa iho. Kafin ya ce "Abba Zan je mu yi bankwana da Hafsat, Zan bata gudinmuwata Nima." Mahmoud na fad'in haka bai saurari abin da mahaifinsa zai ce ba ya kashe wayar. Mahmoud asibitin da yake zuwa tana kan hanya ne hakan ya sa take ya kama hanyar Bakori. Mahaifin mahmoud rasa yadda zai yi ya yi Koda ya duba karfe 5 na yamma, rasa tunanin da zai yi ya yi haka dai ya tashi ya dauki key din motarsa ya bi Mahmoud din dan ya san ba lafiya garesa ba isassa Kuma yana tsoran abin da mahmoud din zai je ya yi. Mahmoud tafiya yake yi yana tunanin yadda zai ga Hafsat, wani irin gudun ganganci yake wanda Allah ne kawai ya kaisa garin Bakori lafiya. Mahmoud bashi ya shiga Bakori ba duk da gudin da ya yi sai karfe 7 na dare. Yana zuwa ya yi parking din motarsa nesa sosai da gidansu Hafsat, kafin ya fito ya tako ya zo har kofar gidan su Hafsat din. Yana zuwa kuwa Allah ya hadasa da kanin Hafsat din Usaini. Mahmoud Kiran Usaini ya yi kudi ya fara cirowa a ajjihunsa baima san konawa bane ya basa. Usaini dama yana ta naiman kudin party da zai yi cikin jin dadi yana washe baki ya fara jero mai godiya. Mahmoud hannu Usaini ya kamo ya ce " Aikyanka zanyi gidan nan." Mahmoud ya nuna gidansu Hafsat. Usaini bude baki ya yi ya ce "Gidanmu ne ai." Mahmoud da mamaki jin ya ce haka ya ce" Kasan Hafsat?." Usaini dariya ya yi ya ce "Aunty Hafsat ai yayata ce gobe ne ma bikinta da Yaya Usman." Mahmoud dafe Kai ya yi kafin ya ce "Ka je ka Kira min Auntynka Amma karka bari kowa ya ji idan ka kirata baka bari kowa ya ji ba Zan Kara maka kudi da yawa." Usaini jin hakan ya sa da gudunsa ya shiga gidansu ya nufi dakin da Hafsat take. Mahaifiyar Usaini kallan Usaini ta yi ganin yadda ya rugo da gudu ta ce "Kai lafiyarka?." Usaini Yana washe baki ya ce"Mama Ina Aunty Hafsat?." Ya aka yi?." Mahaifiyar Hafsat ta ce tana kallan Usaini. Usaini sosa Kai ya yi ya ce "Mama abu fa zan tambayeta." Mahaifiyar Hafsat ta ce "Tana ciki." Usaini da gudunshi ya afka dakin. Zaune ya iske Hafsat kan abun Sallah ta idar da sallar magriba. Usaini zama ya yi kusa da Hafsat yana waige-waige kafin ya ce a hankali "Aunty Hafsat wani mutum a waje ya ce Wai in kiraki Kar in bari kowa ya ji, kin ga ma kudin da ya ban Kuma ya ce Idan ban bari kowa ya ji ba zai Kara min." Hafsat zubur ta tashi tana zare ido, kallan Usaini ta yi ta ce "Usaini leka min kaka ga mama na waje." Usaini lekawa ya yi ya bata nan. Da sauri ya dawo ya ce "Aunty Hafsat bata nan fito da sauri. Hafsat bin Usaini ta rika yi yana kallan Mata hanya ana haka ya hango mahaifinsa, waigowa ya yi da sauri ya ce "Aunty Hafsat boye ga baba nan." Hafsat boyewa ta yi har sai da ya wuce kafin ta fita da sauri. Usaini Yana tafe da Hafsat ya kaita har in da mahmoud ya rakube yake zaune. Tun kafin Hafsat ta karaso mahmoud ya Mike. Hafsat na zuwa ganin mahmoud abazata kawai sai ta fashe da kuka. Mahmoud kudi ya ciro ya ba Usaini Kamar yadda ya yi masa alkawari ya ce "Ka je ka yi wasa karka fada ma kowa Zan Kara maka kudi idan baka fada ma kowa ba." Usaini cikin tsananin jin dadin ya samu kudin fati ya ce "Wallahi ba zan fada ma kowa ba ko abokina habu ma ba zan fada masa ba." Murmushin karfin hali mahmoud ya yi ma Usaini. Usaini Kuma ya ruga da gudu ya tafi. Mahmoud hannu Hafsat ya kamo ya kaita in da yi parking din motarsa, bude mota ya yi ta shiga shima ya shiga✍🏻 Fadila Sani Bakori ce 💓💞 SO NE SILA 💓 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* Page 29 & 30 Mahmoud bayan ya shiga motar Hafsat ya bi da kallo ya kasa ce Mata komai ganin yadda take kuka, ga kukan nata Kara mai ciwan kai yake yi, haka dai mahmoud ya daure a hankali ya kalli Hafsat din ya ce "Hafsat, me ya faru kike kuka haka?." Mahmoud ai kamar ya zuga Hafsat ta Kuma rushewa da kuka kafin cikin kukan ta ce "Ni bana son Yaya Usman, bana son zama dashi." Mahmoud da mamaki ya kalli Hafsat dan bai yi tunanin bata son auran da za a yi Mata ba hakan ya sa ya ce "Ba kya son shi Hafsat?." Kai Hafsat ta daga ma Mahmoud." Wa ki ke so tom?." Ni Kai nake so." Mahmoud a ba za ta ya ji maganar hakan ya sa ya bi Hafsat da kallon mamaki kafin ya ce "Da gaske Hafsat kina Sona?." Kai Hafsat ta daga ma Mahmoud tana goge hawayanta. Shiru Mahmoud ya yi kafin ya ce "Yanzu me ye matsalar?" Yayyan bana sun ki yadda sun ce dole in auri Yaya Usman, ni kuma bana sonshi." Mahmoud cikin damuwa ya ce "Amma Hafsat me ya sa tuntuni baki sanar da ni kina sona ba sai Yanzu? Me ya sa baki fadamin muna da isassan lokaci ba sai yanzu da lokaci ya kure mana?." Hafsat kanta kasa tana wasa da hannunta lokaci-lokaci Kuma tana goge hawayanta. Mahmoud kallan Hafsat ya yi ya ce "Baba ba zai yadda in aureki ba ko?." Kai Hafsat ta daga mai kafin ta ce "Babana ya ce min bacin bashi da iko dani da ya fasa auran inda bana so, amma Kuma ba zai yuwu ba saboda gwaggo uwani." Shiru Mahmoud ya yi kafin ya ce "Hafsat, kina Sona?." Kai Hafsat ta daga ma Mahmoud. "Shi kenan Hafsat indai kina Sona me zai hana ki zo mu je wani garin mu je wajan malamai su daura Mana aure." Hafsat shiru ta yi bata ce komai ba. Mahmoud jin Hafsat ta yi shiru hannun Hafsat ya kamo ya ce "Dan Allah Hafsat ki yadda mu je wajan wani malamin ya daura Mana aure, mu yi tafiyarmu wani garin mu yi zaman mu can kin ji? Kin yadda?." Shiru Hafsat ta yi tana kuka. Mahmoud bai Kuma sauraran Hafsat din ba ya ja motar shi suka tafi. Hafsat dai ta kasa cewa komai. Sun yi tafiya me nisa sosai kafin Mahmoud ya yi parking daidai wani masallaci da ya iske an gama sallar isha'i kenan mutane suna fita. Mahmoud kallan Hafsat ya yi ya ce "Ina zuwa." Mahmoud wani mutum ya samu da ya ga ya fito daga masallacin ya yi masa sallama ya gaidasa cikin girmamawa kafin ya ce "Baba dan Allah ni matafiyi ne, mun gudu ne nida wata yarinya iyayanta za su yi mata auran dole ita Kuma ba ta so ni take so, shi ne muka zo nan dan Allah a daura Mana aure." Mutumin bude baki ya yi kafin ya ce "Babbar magana, bari a yi ma liman magana tom." Mutumin liman ya samu ya yi masa bayani, shi Kuma ya bukaci ganin Hafsat da Mahmoud din. Mutumin zuwa ya yi ya sanar da Mahmoud su zo shi da yarinyar. Mahmoud motarshi ya koma ya kalli Hafsat ya ce "Hafsat, Idan har kina Sona da gaske kamar yadda kika ce ki zo a daura Mana aure yanzu a wajan nan, ni Kuma na yi miki alƙawarin kota Yaya zan yi dan ganin kin shirya da iyayanki daga baya." Hafsat ba tare da tunanin komai ba ta sauka ta bi Mahmoud har zuwa wajan limamin. Cikin girmamawa duk suka gaida limamin, limamin Kuma kallan Mahmoud ya yi ya ce "Maimaita min abinda ke tafe daku?." Mahmoud kamar yadda ya maimaita ma wannan bawan Allah haka ya maimaita ma limamin. Kai limanin ya jinjina kafin ya ce "Ku 'yan Wana gari ne?." Mahmoud karya ya yi masa ya ce daga Kaduna suke. Shiru limanin ya yi kafin ya ci gaba da yi masu nasiha akan biyayya ga iyaye, kafin ya juyo kan Hafsat ya ce "Ki macace Mata sun ce Wai mu maza ba 'yan goyo bane Kuma wani lotun maganar tasu takan so ta zama gaskiya, ba kamar ke da kika bijire ma maganar iyayanki ba, maganar tana iya hawanki nan gaba ya yi miki butulci irin na maza da matake fada. Ashawarce idan za ku ji maganata ku yi hakuri ku bi umarnin iyayanku zai fi mu alkairi, Kuma za ku ga ribar haka nan gaba. Duk abinda ka yi hakuri dashi ka bi umarnin Allah in sha Allah sai ka ci ribarsa nan gaba." Mahmoud cikin sanyi ya ce "Malam mahaifinta da mahifiyarta duk suna son zabinta fin karfinsu aka yi ne, duk abin daga yayyan babanta ne amma da dan ta iyayanta ne da sun aura min ita babanta da bakinsa ya fadi haka, suma finkarfi aka yi musu irin wanda aka yi Mana." Limamin kallan Hafsat ya yi ya ce "Wai haka ne?." Kai Hafsat ta daga Mai ta ce "Haka ne." Kai limamin ya jinjina kafin ya ce "Tom yanzu dai a fahimtata mafi a'ala a daura muku aure ya fi alkairi saboda ba a san irin zaman da zaku je ku yi ba idan an ki daura auran." Yana gama fadin haka ya tashi ya je ya Kira wasu daga cikin almajiransa da wannan mutumin da Mahmoud ya fara yi ma magana. Take aka yanka ma Mahmoud sadaki ya yi transfer dinsu ya biya, nan wannan mutum da Mahmoud ya fara yi ma magana ya zama waliyinsa inda shi Kuma limanin ya zama waliyin Hafsat nan aka daura auran Hafsat da Mahmoud. Bayan gama daurin auran ne limanin ya yi masu nasiha sosai akan zaman aure kafin ya yi masu fatan alkairi suka tafi bayan Mahmoud ya yi musu kyauta sosai. Bayan Hafsat sun koma motar Mahmoud, kallan Mahmoud ta yi ta ce "Ina so mu je gida in yi magana da Fadila kafin mu tafi."

Chapter 9 of 10