Share this page
10 / 10
Shiru Mahmoud ya yi ya ce "Kina ganin ba matsala?." Ai mutane sun yi yawa a gidan tsab zan fito ba tare da kowa ya sani ba." Kai Mahmoud ya jinjina kafin Ya ja motar suka koma unguwarsu Hafsat, nesa da kofar gidansu Hafsat ya yi parking. Mahmoud na yi parking motar mahaifinsa da ya biyosa daga baya ma yana tsayawa daidai inda ya ga motar mahmoud din bayan Mahmoud. Hafsat sauka ta yi tana kallan Mahmoud ta ce "Ina zuwa." Kai Mahmoud ya daga ma Hafsat. Hafsat na tafiya mahifin Mahmoud dake gefe ya zo ya samu Mahmoud ya ce "Mahmoud, yanzu yarinyar da gobe daurin auranta shi ne ka biyota nan, ba komai na gode da tozarcin da kake son yi min. Ba tare da iyayan yaran nan sun sani ba Ina so ka tashi mu ta bi gida." Mahmoud kallan mahaifinsa ya yi a rude zai yi magana mahaifin Mahmoud din ya ce "Ka wace mu tafi na ce Idan ba tozartani kake so ka yi ba dan ubanka." Mahmoud da mamaki ya dago yana kallan mahaifinsa jin zagin da ya yi mai saboda shi ba mai zagi bane, dan ko yana yaro zai iya cewa bai taba jin ya zagesa ba duk da shi mutum ne mai fada sai dai barshi dai da saurin kai duka. Mahaifin Mahmoud sosai Mahmoud ya bata mai rai na biyo Hafsat da ya yi hakan ya sa yana kallansa ya daga hannu ya wankesa da mari ya ce "ba zaka wuce ka shiga motarka mu tafi ba sai na ci ubanka, saboda baka da zuciya mahaifinta har dakkoshi na yi alokacin da kake Asibiti na kaishi ya ga halin da kake ciki ko zai tausaya maka amma tun da ya tafi ko ya kirani ya tambayan jikinaka har yau shi ne Kai ka taso ka biyosu." Mahmoud ganin yadda ran mahaifinsa ya bace sosai ya sa ya ce "Ka yi hakuri Abba mu tafi." Mahmoud na fad'in haka ya shiga motarsa ya tuka ya tafi, mahaifinsa ya bisa a baya-a baya a lokacin karfe 8:30PM. Mahmoud na tafiya mahaifinsa na binsa a baya a haka suka kama hanyar Katsina. Kasancewar Mahmoud cikin tsananin damuwa yake tukin hakan ya sa ya motar ta kwace masa. Mahaifin Mahmoud dake bisan a baya sosai hankalinsa ya tashi ganin yadda mota ta kwace ma Mahmoud, tafiya ya yi ya bugu wata bishiya. Mutane da dama duk da dare ya yi sun tsaya dan taimako, motar Mahmoud na bugun bishiya bishiyar ta bugu glass din motar Mahmoud. Mahaifin Mahmoud da sauran mutane da gudu aka yi kan Mahmoud wanda gaba daya jini ya wanke jikinsa, a haka suka zarosa Mahmoud cikin motar kamar gawa. Mahaifin Mahmoud ganin yadda jini ke zuba akan Mahmoud ya sa ya fasa kuka. A haka dai aka sa Mahmoud a motar mahaifin Mahmoud din, wani mutum suna tafe da dansa shima da alama Katsina suka yi shi ya shiga motar mahaifin Mahmoud din ya ja motar suka tafi. Tafiyar kusan awa daya suka yi kafin suka shiga cikin garin Katsina. Wata private Asibiti suka yi da Mahmoud suna zuwa aka kaishi emergency room. Likitocin Koda suka dubashi samu mahaifin Mahmoud suka yi suka sanar dashi sai dai akai shi asibitin kashi na nan Katsina orthopaedic. Take Mahaifin Mahmoud da wannan bawan Allah suka dauki Mahmoud suka yi orthopedic dashi. Bangaran Hafsat ko ta shiga gidansu amma ta yi ma Fadila naiman duniya bata ganta ba, hakan ya sa ba tare da kowa ya Ankara da ita ba ta shiga dakinsu ta dako wasu abubuwa masu matukar amfani a gareta ta lallaba ta fita. Sai dai babu inda ba ta dubaba babu Mahmoud babu motasa, Hafsta ta dade nan tsaye tana jira ko wani waje ya je ya dawo amma shiru. Hafsat sai da ta yi kusan awa daya tana jiran Mahmoud amma babu shi babu alamarshi, Hafsat na nan tsaye sai ga Usaini. Hafsat Kiran Usaini ta yi ta ce "Usaini Ina wannan din nan Wanda ya baka kudi dazu ya ce ka zauna nan ka jirashi idan ya dawo ka zo ka fada min wai zai sai maka waya idan ka jira Kuma baka fada ma kowa ba. Usaini da ihunsa ya ce "Aunty Hafsat da gaske wai zai ban waya? Ai Wallahi ko kwana ya ce in yi nan zan yi in dai zai sai min waya kuma Wallahi ko su habu ba Zan fadamawa b." Yauwa Usaini daga ya zo sai ka zo ka fada min." Hafsat na fad'in haka ta yi cikin gidansu da sauri. Usaini ya dade yana jiran Mahmoud amma shiru har ya daina ganin sawun mutane daga nan ya ji tsoran Kar a rufe gida hakan ya sa ya dawo gidan, kasan cewar biki ne ma mutane duk ana hira basu barci ba, Usaini ya je ya samu Hafsat dake jiran tsammani ya sanar da ita bai dawo ba. Haka barci ya kwashi Hafsat cike da tunanin ina Mahmoud din ya shiga, gashi gobe mutane sun yi yawa zai Mata wuyar fita, inma ya zo wa zai sa ya kirata, haka Hafsat ta kwana cike da tunani kala-kala. Washegari Hafsat na yin sallar asuba ta tada Usaini ta ce "Usaini ka je masallaci ka yi Sallah Amma karka dawo ka zauna a inda ka jira wannan na jiya idan ya zo ka zo ka fada min, shi Kuma ya ce daga ya zo zai baka waya irin ta baba Aminu." Usaini da babu abinda yake so kamar waya Kuma ya ji Wai za a bashi irin ta baba Aminu Usaini cikin jin dadi ya ce "Aunty Hafsat mai camera uku fa?." Eh Mana ita zai baka in dai ka jirashi har ya zo." Usaini na yin Sallah ya je ya samu waje ya zauna yana jiran Mahmoud kamar yadda Hafsat ta ce ya yi. Abu kamar wasa babu Mahmoud babu alamarshi Usaini ko tsabar son waya da yake yi ko gajiya bai yi ba. Kunu ma da sauri ya dawo ya sha ya koma wajan. Hankalin Hafsat sosai ya tashi dan gidansu anata shirye-shiryan daurin aure. Waje ta samu ta rakube tana goge hawayanta, dan sai ta ji tashin hankalinta ya fi na ko yaushe. Kanwar mahaifin Hafsat ce ta zo ta samu Hafsat na kuka, ko ta kanta bata biba, ƙarshe ma fada ta rufeta da shi ta ce "Wai har yanzu baki gaji ba?." Sai ki tashi ki je ki yi wanka ai." Haka aka taru kan Hafsat aka yi mata tsiya-tsiya kafin ta yadda ta je ta yi wankan. Tana fitowa kanwar mahaifinta ta dakko Mata daya daga cikin kayan lefan ta bata ta ce ta sa, Hafsat amsar kayan ta yi tana fashewa da kuka, kuka take sosai kamar ranta zai fita, kowa dai ya tsaya ganin ikon Allah an kasa ce mata komai, a haka Hafsat ta zira doguwar rigar lass din tana kuka sosai. Ganin ko an yi Mata kwalliya batawa za ta yi ganin yadda take kuka ya sa aka rabu da ita, amma an bata kayan masu kyau tasa. Bayan mutane sun gaji da ba Hafsat baki duk sun tafi sun barta mahaifiyar Hafsat din ta zo ta samu Hafsat cikin fada ta ce "Hafsat, babu kalar hakurin da mutane basu baki ba amma kin ki daina kukan nan ko? Ni kike so ki jama zagi ko Hafsat? So kike ace nike gugaki ko? Shi ke nan idan kina ganin kukan shine magani ai sai ki ta yi." Mahaifiyar Hafsat na fad'in haka ta tashi ta tafi ta bar Hafsat nan. Kamar yadda bahaushe ya ce rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya haka ne. Misalin karfe biyu dubun jama'a suka shaida daurin auran Hafsat Kabiru da Usman Jamilu akan sadaki naira dubu dari da hamsin✍🏻 Kara-kara-kaka ko ya auran Hafsat da Mahmoud yake? Ga Kuma wani auran iyayanta sun daura mata, koya abun zai kasan ce gurkuwa da auran nesa. Littafin So ne sila na kudi ne 500 kacal Idan kina bukata my number 08063830828 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 10 of 10