Share this page
4 / 10
shan maganin ne ta kalli Mahmoud ta ce. "Dan Allah ka ji tausaina ka mai dani gidanmu ni ko yanzu ma na ji sauk'i dan Allah" Hafsat tausayi ta ba Muhmoud kallanta ya yi ya ce. "Tom yanzu ki ci abinci anjima ki kuma shan magani in dai naga kin warke sai in mai da ke" Muhmoud restaurant d'in kusa da gidansa ya je ya siyo ma Hafsat abinci. Da ya ke Hafsat yunwa ta ke ji hakan ya sa ba ta tsaya wata-wata ba ta d'auki abincin ta ci. Muhmoud ko ya na nan zaune kiran Mahaifinsa ya shigo wayar shi ga ban shi ne ya fad'i dan sai yanzu ya tuno da kiran da ya yi mai tun d'azu cikin farga ba Muhmoud ya d'aga wayar daga ganin yadda Muhmoud ya yi shiru za ka gano fad'a Mahaifinsa ya ke mai hak'uri Muhmoud ya ba shi sanna ya sanar da shi ga shi nan zuwa. Muhmoud kallan Hafsat ya yi da ke ta cin abincinta ya ce. "Hafsat Mahaifina na kira zan je ba zan jima sosai ba zan dawo da wuri in zo in yi jinyar beautyna" Yana kai wa nan ya juya ya tafi. Muhmoud zaune a falon Mahaifinsa, Mahaifin Muhmoud kallan Muhmoud ya yi ya ce. "Muhmoud ka san dai ba zan zab'ar maka abinda zai zama illa a rayuwarka ba ko? Tom Muhmoud ba tare da izinin ka ba ama tsayina na wanda na haife ka kuma nake ganin zan iya yanke kowana irin hukuncin a kanka na tsai da ranar auranka da Nafisa saboda na gaji da ganinka babu aure" Muhmoud bai san-sanda ya tashi tsaye ba ya ce. "Abba Nafisa fa ka ce? kuma maganar aure fa kake tsakani na da ita? Dan Allah Abba idan kana ganin kamar na ki yin aure ne tom yanzu haka na samu matar aure kawai muna fahimtar juna ne kafin" Mahaifin Mahmoud kallan Mahmoud ya yi ya ce. "Koma ka zauna Mahmoud" Sai yanzu Muhmoud ya lura atsaye ya ke koma wa ya yi ya zauna. Mahaifin Muhmoud ya ci gaba da cewa ya ce. "Mahmoud ko da ace kana da yarinyar da za ka aura ban hana ka ba auran ta, tom amma ka fa sa ni sai ka auri Nafisa nan ba da dad'ewa ba ma ba zaka maidani shasha ba" Muhmoud cikin tausasa zan ce ya ce. "Abba ba wai ina k'in Nafisa ba ne, yarinyar ce bata da isassar tarbiya" Shi ya sa na ke son ka aureta in da kai kana da tarbiya sai ta sa mu awajanka" Muhmoud shiru ya yi be sa ke cewa ko mai ba. Mahaifin Mahmoud ya ce. "Shi ke nan ka tashi ka je hidimarka Allah ya yi maka albarka, hidimar aure kuma ni zan maka komai" Muhmoud tashi ya yi ya yi ma Mahaifinsa sallama ba tare da ya iya cewa ko mai ba ya tafi. Muhmoud ko da ya dawo gidan d'akin Hafsat ya shiga, kwance ya sa meta bawai bacci ta ke ba idonta biyu. Muhmoud na shigowa Hafsat ta tashi daga kwancan da ta ke, Muhmoud cikin rashin sukuni da da muwar da ya ke ci ya kalli Hafsat ya ce. "Ya jikin naki?" Nawar ke" Hafsat ta bashi amsa kai tsaye "kin sha maganinki ne?" Hafsat jin yadda Muhmoud ya ke magana kamar da kyar-da kyar d'ago kai ta yi ta na kallan shi ta ce. "Na sha"Yauwa good girl, tom yanzu ki kwanta ki huta sai da safe" washe gari Hafsat bayan tasha maganinta da kanta ta ta shi ta shiga kitchen d'in ta yi ma kanta abin break fast, bayan ta gama ci ta zo bakin k'ofar ta tsaya tana jiran fitowar Muhmoud dan ta k'ulla d'amarar fad'a da Muhmoud daga yau ba za ta k'ara kwana gidansa ba inda ta ji sauk'i kamar yadda ya yi mata alkawari inda zata ji sauki zai mai da ta gida tom dole ya maidata. Hafsat na nan zaune sai ga Mahmoud ya fita da shirinsa na fita, in da Hafsat ta ke ya k'araso cikin fara'arsa ya ce. "Beautyna ya kika tashi fatan kin warware baki daya?" Hafsat cikin d'aure fuska ta ce "Alhamdulillah na warke, ya maganar tafiyata? Dan ni gaskiya ba zan Kara kwana a gidan nan ba yau-yau d'innan nake son tafiya gidanmu" Mahmoud kallan Hafsat ya yi ya ce "Ai ba haka mu ka yi da ke ba na ce sai kin warke sosai sannan" Muhmoud na kai wa nan ya bud'e k'ofar zai fita Hafsat sauri ta yi sha gaban Muhmoud ta tsugunnan kamar mai naiman gafara ta ce. "Dan Allah ka ji tausaina mana yanzu kai baka tunanin ace arabaka da d'anka kamar yadda ka yi ma Iyayena dan Allah ka ji tausaina ka maidani wajan Iyayena da 'yan'uwana suna can cikin tsananin damuwa da tashin hankali" Muhmoud shima tsugunnawa ya yi kamar yadda Hafsat take cikin damuwa ya ce. "Hafsat dan Allah nima ki tausaya min ki fahimci halin da nake ciki, da ace zan iya barinki ki fita daga gidannan wallahi da ban kawo ki ba, saboda na yi iya ƙoƙarin fahimtar da kaina hakan bai dace ba, bari ki ji Hafsat Wallahi ban tab'a son wani abu ba aduniyar nan kamar yadda nake sonki idan ba ke ba yanzu haka Mahaifina aure ya ke son ya yi min har ma ya tsai da ranar auran ni da yarinyar da ya ke son had'awa amma Ni ke nake so ke kadai nake gani kece cika makon farin cikina Hafsat, ke ke ce farin cikina Wallahi. Dan Alllah ki tausaya min ki fahimci ba zan tab'a iya barinki ki fita daga gidan nan ba, ki yadda dan Allah Hafsat in aure sai in mai dake gida bayan mun yi aure." Hafsat jin abinda Mahmoud ya ke ce wa kuka ta sa. Mahamoud da kyar ya bude baki ya ce "Hafsat ki yi shiru dan Allah zan mai da ke gida gobe in sha Allah" Hafsat da sauri ta d'ago ta na kalan Muhmoud ta ce. "Da gaske ka ke dan Allah za ka mai da ni gidanmu?" Zan mai da ke in sha Allah ✍🏻 Fadila Sani Bakori ce ❤️💞SO NE SILA❤️ 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* Pgae 11 & 12 Washegari da wuri Hafsat ta tashi ta ta yi wanka saboda alk'awarin da Muhmoud ya yi mata na tafiya gidansu yau. Bayan Hafsat ta gama shirinta ta zauna tana jiran fitowar Muhmoud amma shiru har yanzu bai fito ba. Muhmoud ko yau sammakon fita ya yi. Hafsat jin shirun ya yi yawa ya sa ta tashi ta koma bedroom d'inta dan yau ko abinci ji take ba ta iya zama ta ci sai a gidansu, haka Hafsat ta wuni aikin jiran Mahmoud Koda ta tabbatar sammakon fita ya yi ta ci kuka kafin ta hakura ta koma dakin da yake mazaunin nata. Muhmoud ko ba shi ya dawo gidan ba tun da ya fita sai dare lokacin Hafsat ta yi Bacci. Duk da bata san-sanda Baccin ya d'auketa ba. Cikin dare Hafsat ta farka da wani irin ciwan ciki tsabar horan yunwar da tayi ma kanta dan rabonta da abinci tun jiya da baba ta tafi, jiyan ma kadan baba ta samu ta sha tea din da ta kawo mata. Gashi dama ba wani isassar lafiya gareta ba. Hafsat tsabar yanda cikinta ya kulle kuka ma kasa yi ta yi jin za ta iya mutuwa ya sa cikin dauriya ta na cije baki ta sakko daga kan lafiyayyn gadonta tana rike ciki tana hutawa in cikin ya tsaga mata a haka ta isa k'ofar bedroom d'in Mahmoud. Hafsat cikin dauriya da yadda ta ke jin 'ya'yan Cikinta na k'ullewa ta rik'a buga k'ofar dakin Mahmoud, Mahmoud ko cikin Bacci ya ji kamar ana bugun k'ofarsa saurarawa ya kuma yi. Hafsat ko cikin wata azabar da ta ji ta sa ke buga k'ofar da karfi tana cewa "Cikina" Mahmoud da sauri ya zo bakin k'ofar ya na tunanin waye haka kuma ta ina ya shigo gidan dan tunanin shi bai bashi Hafsat bace tsaye ya yi ya na sauraron ko za a kuma bugawa. Hafsat cikin azabar yanda ta ji cikin ya kuma d'aure mata ta kuma bugawa da karfi. Muhmoud da sauri ya bude kofar yana bin Hafsat dake jingine da kofar da kallo, sauri ya k'araso wajan Hafsat dake rike da ciki, tsugunnawa ya yi daidai saitinta cikin rudewa ganin ydda take rike ciki ya ce "Subhanallahi Hafsat me ke mi ki ciwo?." Hafsat cikinta ta nuna ma Mahmoud tana zubda hawaye. "Cikin ki ke ciwa?." Kai Hafsat ta d'aga ma Mahmoud. Muhmoud rasa taimakon da zai ma Hafsat ya yi ga a abu ya kama da dare tunowa ya yi da magungunnan ta na Ulcer da doctor ya ba ta, hakan ya sa ya mika ma Hafsat din hannunsa alamun ta kama ta tashi ya ce "Kama hannuna ki tashi mu je ki sha maganinki Ina jin ulcer ne inda itama tana sha ciwan ciki." Hafsat Kai ta girgiza ma Mahmoud hakan ya sa ya rabu da ita ya je bedroom dinta ya kwaso magungunanta ya kawo Mata da ruwa. Mahmoud cikin damuwar yadda ya ga Hafsat din ya bare magungunan ya mika Mata ya ce "Amsa ki sha." Hafsat Kai ta girgiza ma Mahmood. Mahmoud cikin damuwa ya ce "Dan Allah ki daure ki sha kin ji cikin zai lafa miki maganin ulcer ne fa" Kai Hafsat ta Kara girgizawa kafin ta ce "Ni abinci nake so yunwa nake ji." Ta yi maganar tana goge hawayan da ya zibo Mata. Mahmoud da sauri ya shiga kitchen dinsa jin kadan sai ga shi da tea a cup ya hado ma Hafsat ya kawo Mata ya ce "Ga tea ki sha cikin Kiki ya warware kafin, nasan kila ma duk yau ba ki ci komai ba ko?." Hafsat hannunta na rawa ta amshi cup din tea din ta kafa a baki, ko rabi bata sha ba ta fara kwara amai a wajan, tana yin aman cikin ya lafa mata gaba daya ta jima kamar ta ji sauki daga kullewar da ya yi da Kuma ciwan da yake Mata. Mahmoud cikin damuwa ya ce "In hado miki wani tea din. Kai Hafsat ta girgiza ma Mahmoud. Mahmoud tagumi ya yi Yana kallan Hafsat din ya ce "Tom me za ki ciki?." Ba zan ci komai ba." Hafsat taba Mahmoud amsa tana jingina da kofar dakinsa tana rufe ido. Mahmoud tashi ya yi ya ce "Kinga nan da sanyi kansa gashi kin bata wajan zai kara miki sanyi in bude miki dakina ke je ki kwanta ni sai in kwanta a nan falo?." Kai Hafsat ta daga ma Mahmoud ya bude mata dakinsa ta shiga ta kwanta shi Kuma ya zo ya gara wajan da Hafsat ta yi mai ta bata, kafin ya tura kofar bedroom dinsa ya shiga. Hafsat dake kwance har barci ya fara dibarta jin shigowar mutum firgigi ta tashi. Mahmoud bargonsa ya dako ya jama Hafsat kofar ya koma falo ya kwanta. Washegari Mahmood da kansa ya shiga kitchen ya hada ma Hafsat tea ya soya Mata kwai ya Kai Mata. Sai dai Koda ya shiga bata dakin hakan ya sa ya san ta koma dakinta. Mahmoud na rike da cup din tea din ta kwanda ya soya Mata ya nufi dakin Hafsat. Hafsta na kwance inda ta idar da Sallah Mahmoud ya shigo, Hafsat tashi ta yi ta zauna. Mahmoud cup din tea din ya mika ma Hafsat da plate din soyayyan kwan. Kasan cewar Hafsat dama babu abinda take bukata kamar abinci yanzu haka yunwa ce ta hanata komawa barci hakan ya sa ba musu ta ansa ta fara sha kadan-kadan, a haka har ta shanye duk Mahmoud na nan na kallanta. Ya ce "Sannu ya jikin naki?." Hafsat Maimakon taba Mahmoud amsa sai ta fashe mai da kuka tana cewa cikin kuka "Ni dai dan Allah dan annabi ka barni in tafi gidanmu kai kai min alk'awarin za ka maidani jiya dan Allah ka barni in tafi yau." Hafsat ta idasa maganar cikin kuka sosai. Mahmoud shiru ya yi yana kallan Hafsat kafin ya ce cikin lallashi "Ko jiyan ma ai ba fasawa na yi ba fita ce ta kamani ta wuri Kuma kin ga ai ban dawo ba sai dare, yau Kuma ya za ai in mai dake baki da lafiya ki bari sai jikinki ya yi sauki dan Allah, Kinga idan na maida ke haka iyayanki za su tuhumeni." Hafsat wurgi da yi ta cup din tea din hannunta tana Kuma fashewa da kuka ta ce cikin kuka "Ba wani nan kullum haka kake cewa, idan sai na ji sauki ne bana jin zanji sauki Ina a wannan gidan ni dai kawai ka maidani gidanmu dan Allah." Mahmoud shiru ya yi kafin ya ce "Ki yi hakuri Hafsat nina San na tauye rayuwarki na ajeki anan da na yi, Kuma nasan har da tafiyar baba ta Kara miki damuwa ki bari zan samo wata wadda zata debe miki kewar baba in sha Allah." Hafsat Kara fasashewa da kuka ta yi jin abinda Mahmoud ya ce ta ce "Ni ba zan zauna ba ne ai ko dama baba ce zaka dawo da ita ni gidanmu nake so." Mahmoud ganin yadda Hafsat ta haukace masa ya sa ya ce "Shi kenan zan maidake gidanku amma ki bari ki ji sauki gaba daya." Yana gama fadin haka ya tashi da sauri ya tafi ya bar Hafsat. Hafsat kullum cikin kuka take akan Mahmoud ya Mai data gidansu amma kullum magana daya yake fada mata ta bari ta ji sauki, Hafsat tun tana kuka tana kin cin Abinci ko haka zai sa Mahmoud ya mai data gida Amma yaki. Mahmoud yau sammakon fita ya yi, daga wajan aiki ya biya gida saboda kiran da Mahaifinsa ya yi mai, bayan Muhammad ya je ne Mahaifinsa ya kallai ya ce. "Muhmoud ka tab'a kiran Nafisa a waya tunda na sanar da kai saranarka da ita?" Kai Muhmoud ya girgiza ya ce. "A'a Abba" Tom me ya sa ? ko ka yi hakane dan ka tozartani ka nuna ma duniya ban isa in saka ka yi abinda baka ra'ayi ba?." "A'a Abba ba ko d'aya" Mahaifin Mahmoud kallan Muhmoud ya yi rai a b'ace ya ce. "Mahmoud idan har ba wai ka kai matsayin da ni ban isa in baka umar ni ka bi ba ne tom yau d'in nan ina so kafara zuwa zan ce wajan Nafisa, sannan na sakkko da bikinka da Nafisa sati biyu masu zuwa in sha Allah, saboda zan yi tafiya k'arshen watan nan dan haka duk wani shiri da ka ke da shi kafin auran sai ka je ka yi" Mahmoud cikin matuk'ar furgici da fad'uwar gaba ya ce. "Tom Abba zan yi in sha Allah" Me za ka yi" Muhmoud cikin in da-in da ya ce. "Duk abinda ka ce"Yauwa tom Allah ya yi maka albarka" Muhmoud cikin sanyi jiki da kasalar zuciya ya tashi ya koma wajan aiki. Muhmoud bashi ya dawo gida ba sai gaf isha ya biya restaurant d'in kusa da gidansa ya tsaya ya siyo ma Hafsat abinci. Hafsat yau gaba daya akwance ta wuni tun tafiyar Mahmoud, gaba d'aya hankalinta atashe ya ke da zaman gidan babu abinda ta ke muradin gani da ji kamar Iyayanta. Hafsat na nan kwance ta ji shigowar Mahmoud. Mahmoud da ya ke hankalinsa ga ba d'aya ya na kan Hafsat dakinta ya wuce da muwar da yake ganinta ciki sosai take damunsa, Kwance ya sa me ta cikin taushin murya Mahmoud ya ce. "Hafsat ki yi hakuri kin ji komai zai zo ƙarshe watarana." Hafsat fashewa da kuka ta yi ta ce "Babu komai na barka da Allah, da raina da lafiyata ka rabani da kowa nawa ka kawoni nan ka aje saboda ra'ayinka da Kuma son zuciya" Mahmoud kallan Hafsat ya yi ya ce "Taya zan ketare kaddarar dake kaina akanki, Hafsar ke ce kaddarata kamar yadda kike ganin na zama taki kaddarar, saidai zafin dake zuciyata yafi naki Wallahi. Amma ki yi hak'uri kin ji dan Allah nina san na zalince ki amma komai ya kusa zuwa k'arshe in sha Allah in dai kin yarda kin aminta da buk'atata?." Hafsat tashi ta yi tana kallan Mahmoud ta ce. "Wata iri ce buk'atar taka?"Ki yadda a d'aura mana aure da ke, ni kuma aranar zan mai da ke gaban Iyayanki Wallahi kin ji na rantse miki" Hafsat cikin takaici da maganar Mahmoud din ta ce. "Wato sai na yadda da auranka sanna zaka mai dani gaban Iyayena ko? Me ya sa Kai kanka kawai ka sani? Damuwarka kawai ka sani ba ruwanka da ta wani, ta ya zan yadda in aureka in da ba ni ke da kaina ba ko da ma ace ni keda kaina na fad'ama maka akwai sadakin wani akaina, Kai Wai baka san haramun bane naiman aure ciki naima?." Na sani Hafsat na sani, na sani tabbas na sani amma na rasa yadda zan yi ne ki fahince ni dan Allah, Wallahi ba zan taba iya yin gigin maida ke gidanku ba ki auri wani ba ni ba gara in aje ki anan na yadda in ta kallanki mu karasa rayuwarmu a haka inda haka kike so" Hafsat kallan Mahmoud kawai take tama kasa magana. Mahmoud tsugunna ma Hafsat ya yi kamar zai yi kuka ya ce "Allah na ne shaidata ina damuwa sosai da damuwar da nake ganinki ciki. Hafsat fada min da lilinki da ya sa ba kya son aurena?" Hafsat kallan Muhmoud ta yi ta ce "Saboda baka shigo rayuwata ba alokacin da yadace kashigo rayuwata a lokacin da an riga an amshi sadakin aurena da wani Kuma muradin zuciyata wanda ya naimi aurena ta hanyar da ta dace." Mahmoud tashi ya yi dan ya ji zafin maganar Hafsat osai ya ce. "Hmmm ni babu ruwana da wani wanda ya naimi auranki abin da na sani ana zuwa daurin auran mace ma a fasa, Kuma mutum nawa ya kawo sadaki aka maida mai saboda shigowar rayuwar wani, amma ki sa ni kamar yadda na fad'a miki za ki k'arasa rayuwarki anan, Kuma ki sani sati biyu masu zuwa aure na" Muhmoud na kaiwa nan ya fita ya bar Hafsat a wajan. Tom fa abubuwa sun cakud'e dan daga Muhmoud har Hafsat cikin damuwa su ke, shi Muhmoud da muwar da ta fi damunsa yanzu bai wuce auran da Mahaifinsa zai mai ba, tunaninsa d'aya taya zai bar Hafsat ita kad'ai bayan auransa ya koma sabon gidansa da zama, kuma ba abin ya tafi da ita ba. Hafsat ko b'angaranta sosai take cikin damuwar furucin mahmoud da yake mata indai ba zata aurai ba sai dai ta karashe rayuwarta a gidan dan ta fara ganin alamun da gaske yake ba wai wasa ba ko kurari. Hafsat na nan zaune ta na ta tunane-tunananta kala-kal wata dabara ta fad'o mata a rai, Hafsat cikin sauri ta tashi ta nufi d'akin Muhmoud tana maijin dad'in shawarar da zuciyarta ta bata tana ganin in sha Allah zata zamar mata mafita na barinta gidan✍🏻 Fadila Sani Bakori ce ❤️💞SO NE SILA❤️ 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* Page 13 & 14 Hafsat kwance ta samu Mahmoud kan lover chair din bedroom dinsa kanshi sama daga gani ya yi nisa sosai a duniyar tunani, hakan ya sa Muhmoud bai ji shigowar Hafsat ba. Hafsat tsaye ta yi akan Mahmoud dan tabbas ta lura bai ji shigowar ta ba, gyaran murya Hafsat ta yi kafin ta ce. "Yallab'e" Mahmoud kai ya d'ago ya na kallon Hafsat kafin ya tashi ya zauna yana kallanta da mamaki ganin ta shigo har dakinsa, nuni ya yi mata da ta zo ta zauna. Hafsat zama ta yi gefan Mahmoud tana wasa da yatsun hannunta, Mahmoud kallan Hafsat ya yi ya ce. "My love, ina jin ki ko kallona ki ka zo yi?" Kai Hafsat ta girgiza mai tana yin kasa da Kai daga gani dai wani abu take son cewa. Mahmoud dai yana jinta baice mata komai ba. Hafsat kallan Mahmoud ta Kuma yi kafin ta ce "Yallab'e, dama na ya tunani ne sai naga ka cancanci na aminta da soyayyarka.." Mahmoud da sauri ya kalli Hafsat dan ya tabbatar da abin da take cewa har zuciyarta ne ba iya labbanta suka tsaya ba. Hafsat da sauri ta yi k'asa da kanta ta ci gaba da cewa, "Na amince zan aureka" Muhmoud kallan Hafsat ya yi ido cikin ido ya ce. "Hafsatt, abinda kike fada da gaske ne har zuciyarki kina Sona Kuma zaki auran?." Yallabai da gaske nake Ina sonka Kuma zan aureka." Mahmoud hannu Hafsat ya kamo ya ce "Hafsat karki yaudari zuciyata kin ji na danka miki amanar zuciyata ki riketa amana babu yaudara Hafsat, Ina sonki son da ban taba yi ma wani abu a duniyar nan ba, dan Allah karki yau dare zuciyata da sunan soyayya Hafsat, kar ki zo ki kini watarana, Ina ji ajikina kamar kin yi haka ne dan ki fita a gidan nan ba Wai dan kina sona da gaske ba?" "A'a yallabai ai idan haka ne da tuni na nuna maka haka, kasan shi so a hankali-a hankali yake shiga yanzu na gama fahimtar soyayyarka a gareni shi ya sa na amince ina sonka Yallab'e da gaske kuma zan aure ka idan har Yanzu kana kan bakar aurena" Muhmoud cikin farin ciki da jin abinda Hafsat ke ce wa ya ce. "Hafsat har abada ba zan taba janyewa ba akan auranki zuciyata ta rika ta gama abinta da danni aka yiki kamar yadda aka yi danke, a shirye bake da auranki babu gudu babu ja da baya. Yau saura Kwana goma sha uku auran da Mahaifina ke son yi min dama cikin fargabar yadda zan yi da ke na ke, zan mai da ke gidanku ana gobe aurena hakan ya yi miki ko?" Hafsat maganar Muhmoud sosai ta ba ta haushi wai za mai da ta gida ana gobe auran sa ita ta zata yau ko gobe zai mai data. Hafsat cin danne bacin ranta cikin hikima ta ce. "Amma Yallab'e ana gobe bikinka ai lokaci ya k'ure in da kaga lokacin kana cikin bak'i da hidimomi" No ba wani hidimomi bare baki dan ban gayyaci kowa ba kuma ba zan gayyata ba sai a auranki zan yi gayyata dan haka ba wani hidimomi da za su yi min yawa" Hafsat ba dan ta so ba ta danne fushinta dan kar Muhmoud ya ganota ta ce. "Tom Allah ya kaimu lokacin lafiya" Ameen my love." HAFSAT cikin farin ciki ta yi baci a ranar dan rabonta da ta shiga farin ciki irin haka tun tana gida dan Mahmoud ya gama yadda da ita tasan babu abin zai hana ya mai data gida. B'angaran Muhmoud ma haka ne cikin farin ciki ya yi baccinsa dan Yanzu damuwar sa bata wuce ta auran Nafisa ba. Washegari Hafsat da wuri ta ta shi ta shiga kitchen ruwan tea ta dafa sai indomie da ta yi yi jollof da dafaffan kwai, Hafsat plate ta samu ta zuba ma Muhmoud tare da tea a cup ta aje tana gyara kitchen din. Duk abin nan da Hafsat ke yi tana yi ne dan ta nuna ma Mahmoud da gaske take tana son shi. Hafsat na kitchen ta gama had'a komai ta ga fitowar Mahmoud ya na sauri da alamu fita zai yi ita ma cikin saurin ta fita daga kitchen d'in ta ce "Yallab'e ga abin breakfast na yi maka." Mahmoud karowa kitchen din ya yi yana murmushi ya ce "Tabbas yau na yadda da abin da zuciyata take kokwanto akansa, Hafsat sai yanzu na aminta da

Chapter 4 of 10