daga hannu ya bigi Nafisa?." Wai sai maganar hannu kake Danƙo ya samu ya zaneta dashi idan baka yadda ba ka turo wani gidan yanzu ka ga yadda jikinta ya yi." Mahaifin Mahmoud shiru ya yi cike da mamaki kafin ya ce "Amma dai akwai abin da ya faru tsakaninsu Ina jin?." Nima haka na yi tunani ganin irin dukan, amma da na tambayi Nafisar ta ce min wai ya ce sai dai ta zo ta ce maka shi baya son auran da zaka hadasu shi ne ta ce mai wai ita ba zata iya ba shine fa ya kawo dukan."
Sosai ran mahaifin Mahmoud ya bace bai ce komai ba ya kashe kiran ya kira Mahmoud a waya.
Mahmoud bayan sun koma part din mahaifiyarsa kallan Hafsat ya yi da har yanzu kuka take ya ce "Haba my Hafsat me ye kuma na kuka?"
Hafsat bige hannun Mahmoud ta yi da ke k'ok'arin share mata hawaye ta ce. "Akan me za ka yi masu wannan dukan?." Mahmoud ido ya zaro ya ce "Ita kadai fa na buga dayar fa matar babana ce Kinga komai ta yi min ai babu yadda za ai in bugeta. Nafisa Kuma na ramamiki dukanki da ta yi ne" Amma ai ni ba haka ta yi min ba dukan ya yi yawa, dan Allah ni dai ka mai da ni gidanmu kafin wani abun ya sake faruwa."
Mahmoud kallan Hafsat ya yi murya k'asa-k'asa a hankali cikin muryar lallashi ya ce "Amma ai kinsan bacin Abbana da gobe ne muka yi zan kaiki, yanzu Kuma Kinga ai shi ya kawo ki nan idan na ce zan daukeki zai ga kamar mun hada baki ne amma ki yi hakuri nasan daga ya dawo komai zai wuce in sha Allah." Mahmoud ya idasa maganar cikin damuwa.
Hafsat kallan Mahmoud ta yi ta ce. "Tom ai ni tsoran kwana nan nake yi daga ka ta fi za su zo su rama dukan su akaina"
Hafsat dariya sosai ta ba Mahmoud. Kafin ya ce "Idan suka Kara bugunki in Kara ramaki."
Kai Hafsat ta girgiza ta ce
"Ni a'a, kawai ka mai dani gidanka kafin Abban ya dawo." Da yake Hafsat irin cikakkun matsoratan nan ce.
Mahmoud kallan Hafsta ya yi zai yi magana karar wayarsa ta sa ya yi shiru.
Mahmoud ko da ya duba wayar shi ya ga mai kiran shi sai da gabansa ya fad'i kafin ya daga Kiran.
Mahaifin Mahmoud ko ta inda ya shiga ba ta nan ya ke fita ba ya ce. "Ba Nafisa ya kamata ka buga ba ai ni ya kamata ka buga, inda ni na hada auran ba ita ba. Yanzu kai ba abin kunyarka ba ne ace ka bigi matar da za ka aura? Ka ga abin da ka yi ya tabbatar min nan gaba kome ya faru tsakaninka da ita kai ne baka da gaskiya, Kuma Wallahi ka yi gaggawar zuwa ka bata hakuri ita da mommynka"
Mahaifin Mahmoud na fad'in haka ya kashe wayar shi.
Mahmoud bin wayarsa ya yi da kallo bayan mahaifinsa ya katse Kiran.
Mahmoud tashi ya yi zai fita Hafsat ma ta tashi ta bi shi dan ita gani ta ke daga Mahmoud ya fita su Hajiya Jamila za su rama dukan da Mahmoud ya yi ma Nafisa akanta.
Mahmoud kallan Hafsat ya yi da mamakin ganin tabiyo shi ya ce "Ina za ki?" Hafsat cikin b'ata fuska ta ce. "Dan Allah kar ka barni ni ka d'ai Wallahi tsoransu nake ji ramawa za su yi" Babu abinda za su yi mi ki yanzu mu ka gama waya da Abbana ya ce in je in basu hak'uri ina basu hak'uri zan dawo in kuma zaki rakani tom muje" Hafsat da sauri ta girgiza ma Mahmoud kai ta ce "A'a ba zani ba"
Mahmoud juyawa ya yi ya tafi ya na murmushi dan ya lura Hafsat ta tsorata dasu sosai.
Mahmoud ko da ya shiga Falon Hajiya Jamila shiru ba kowa, sallama ya yi
Hajiya Jamila da ke kitchen jin sallama fitowa ta yi. Mahmoud kallan Hajiya Jamila ya yi ya ce. "Dama Abba ne ya ce in baku hak'urin a binda ya faru ku yi hak'uri" Hajiya Jamila "Hmmmm." Ta ce ma mahmoud dan ban hakurin na rainin hankali ya yi masu. Mahmoud ganin baiga Nafisa ba ya ce. "Ina Nafisa fa?" Hajiya Jamila banza ta yi da Mahmoud ta juya ta koma kitchen.
Mahmoud dakin da ya ke tunanin zai ga Nafisa ya shiga.
Nafisa kwance take ta na zazzab'in dukan da Mahmoud ya yi mata. Mahmoud sallama Ya yi ya shigo, kallan Nafisa ya yi da ke a lullub'e ya ce. "Ke tashi mu yi magana" Nafisa na jin muryar Mahmoud ta ta shi da sauri ta zauna.
Mahmoud kallan Nafisa ya yi ya kauda kai ya ce. "Nafisa daga yau har Yarinyar nan ta bar gidan nan na rabaki da ita, abinda na yi miki kuma ba zai sake faruwa ba sai dai in kin sake mai-mai ta abinda ki ka yi ne"
Nafisa shiru ta yi ba ta ce ko mai ba, amma Allah ne kad'ai ya san yadda ta ji zafin maganar da Mahmoud ya yi.
Mahmoud ko jin Nafisa ta yi shiru ya ce "Nafisa bi ki ji abinda na ce bane?" Nafisa cikin muryar kuka ta ce "Na ji" Mahmoud ji ya yi babu dad'i kuma dan shi mutum ne Wanda baya son shiga hakin wani hakan ya sa "Abba ya ce in ba ki hak'uri ki yi hak'uri" Yana fad'in haka ya sa kai ya yi ficewar shi.
Nafisa kuka ta fashe da shi bayan Mahmoud ya fita.
Hajiya Jamila ko daga kitchen ta ji yo kukan Nafisa da sauri ta zo wajan Nafisar.
Hajiya Jamila a rayuwata ta na bala'in son Nafisa ko dan ba ta tab'a haihuwa ba ne oho.
Hajiya Jamila rungume Nafisa ta yi ta na lalla shin ta ta ce. "Nafisa dan Allah dan annabi ki hakuri da Mahmoud ga maza nan da yawa a cikin gari kina da kyanki kina da diri ki tsaya kinace ma wani mahmoud can da ba take yake ba, in ba tsabar ya nuna min baya sonki ba yaushe zai zo ya bigeki akan wata mace." Nafisa dai bata ce komai ba kuka kawai take.
Hajiya Nafisa da kyar ta samu Nafisa ta yi shiru. Hajiya Jamila kallan Nafisa ta yi ta ce "Kin hakura da mahmoud din ko in sanar da Abbanku?." Kai Nafisa ta girgiza ta ce "Mommy Ina son Yaya mahmoud sosai, bawai Ina kuka bane dan naji zafin dukan da ya yi min bane Ina kuka ne akan bugun da ya yi min akan wata ne." Shi ya sa na ce ai ki hakura da auran nasa ni Kar in jema ya wahalar min da ke." Nafisa kallan Hajiya Jamila ta ce "mommy duk wanda kika ji ya ce baya iya jure wata wahala daga wajan masoyinsa tom akwai rauni a soyayyarsa." Kai Hajiya Jamila ta girgiza bata ce komai ba ta tashi ta fita.
Mahmoud ko fita ya yi daga gidan, bashi ya dawo ba sai dare ya tsaya ya sai ma Hafsat yoghurt ya da sweet Chocolate da biscuit ya ga masoyiyarsu ce.
Hafsat ko ga ba d'aya a tsorace take zaune dan gani ta ke kamar su Hajiya Jamila za su zo su rama dukan su akanta
Tana nan zaune Mahmoud ya shigo.
Mahmoud kusa da Hafsat ya k'ara so ya aje mata ledar hannunsa ya ce "My Hafsat yi hak'uri na barki ke kad'ai"
Hafsat banza ta yi da Mahmoud kamar ba da ita ya ke ba, Mahmoud juyo da kan Hafsat ya yi ya ce. "Tom ki yi hak'uri dan Allah idan ba so kike in yi kuka ba."
Hafsat kallan Mahmoud ta yi ce. "Abinda ka san a tsorace na ke a gidan amma ka je ka dad'e" Tom ki yi hak'uri daga munyi aure ba zan sake barinki ke kadai ba" Hafsat turo baki ta yi ta ce "Tom wa ya ce maka zan aureka?" Mahmoud had'e fuska ya yi ya ce "Ko da wasa karki k'ara ce min haka wa ya ce miki ba ni za ki aura ba, ba ki ja miji sai mahmoud." Hafsat daure fuskar ta yi ta ce. "Ni ba wasa na ke maka ba na fad'a maka gaskiya ne". Mahmoud kallan Hafsat ya yi ya yi murmushi ya ce. "Hafsat kenan ko dan kinga kamar kin kusa kub'uta daga hannuna ne ki ke fad'amin haka? Tom bari ki ji matukar kika fasa aurena Hafsat ko ranar auran ki ne wallahi sai na sato ki na kawo ki nan" Hafsat kallan Mahmoud ta yi kamar za ta yi kuka ta ce. "Dan Allah da gaske ka ke za ka iya kuma sato ni ka kawoni wajanka?" Mahmoud kallan Hafsat ya yi ganin ta tada hankalinta da kala mansa Kai ya girgiza ya ce "Zan kulleki ta waje ki kwanta ki yi bacci sai da safe" Ya na kai wa nan bai saurari abinda Hafsat za ta ce ba ya tafi.
Tun daga ranar Mahmoud ya rage yi ma Hafsat magana kamar da inda itama Hafsat din haka ya yi Mata dadi ita dai fatanta mahifinsa ya dawo ta tafi.
Akwana atashi babu wiya awajan Allah, yau ne Mahaifin Mahmoud zai dawo.
Hajiya Jamila ko da Nafisa babu abinda ya kuma shiga tsakanin su da Hafsat.
Mahmoud da kanshi ya je har airport ya taho da mahaifinsa, a mota Mahaifin Mahmoud kallan Mahmoud ya yi ya ce. "Mahmoud gobe in sha zan mai da wanna Yarinyar ga ban Iyayanta inata tunanin yadda zan bulloma wannna haukar da ka tabka. daga nan kuma Mahaifin Muhmoud ya yi ta ma Muhmoud nasiha akan abinda ya ai kata, sannan ya sake jaddada ma Mahmoud auransa da Nafisa Saturday mai zuwa .
Mahmoud rasa abinda ya ke mai dad'i yi sai dai har cikin ransa ya na mai fargabar rabuwa da Hafsat dan gani ya ke daga ta tafi ta tafi kenan.
Mahmoud da kyar ya samu ya kawo su gida.
Dayake isowar dare Mahaifin Mahmoud ya yi hakan ya sa Mahmoud na aje shi shima ya tafi makwancinsa.
Hajiya Jamila ba yan Mahaifin Mahmoud ya ci abinci ne ya d'an huta ya kula da cika da batsewar da ta ke yi.
Mahaifin Mahmoud kallan Hajiya Jamila ya yi ya ce. "Wai lafiya ne duk fushin nan na me ne ne?". Hajiya Jamila kallan Mahaifin Mahmoud ta yi ta ce. "Alhaji gaskiya ni bana son auran Mahmoud da Nafisa Ina so a fasa shi." Mahaifin Mahmoud kallan Hajiya Jamila ya yi da mamaki kafin ya ce "Amma wata kalar damuwace baki shiga ba akan atsaida ranar auran sai yanzu Kuma zaki zo ki ce min bakya so tom kima canza kalamanki aure kamar an yi an gama ne." Eh bana son auran mahmoud da Nafisa saboda na lura Mahmoud kwata-kwata ba ya son Nafisa"
Mahaifin Muhmoud ganin yadda Hajiya Jamila ta d'au zafi ya sa ya ce. "Idan aka fasa auran shi kenan hakan ya yi miki?" Eh hakan ya yi min" Tom shi kenan shakuriminki na janye maganar auran shi kenan?" Ta ce "Eh shi kenan"
Mahaifin Mahmoud ganin cika da batsewar da Hajiya Jamila ke yi ya sa ya watsar da ita shima ya ci gaba da danna wayar shi daga k'arshe ta tashi ta bar mai d'akin sh.
Hajiya Jamila
Ko da ta je ta kwanta barci gagararta ya yi dan ta san Nafisa in dai ta ji maganar fasuwar auran ta da Mahmoud to fa akwai daru.
Washegari Mahaifin Mahmoud da wuri ya kira Mahmoud awaya amma bai d'aga ba.
mahaifin Muhmoud ganin Mahmoud bai d'aga ki ranba ya sa ya tashi da kanshi ya je ya bubbuga ma Hafsat k'ofa..
Hafsat ko lokacin ta na zaune kan dadduma tama zaci Mahmoud ne dan bata san dawowar Mahaifin Mahmoud d'in ba. Hafsat bud'e k'ofar ta yi tana ganin Mahaifin Mahmoud ta yi saurin tsugunnawa har k'asa ta ce "Ina Kwana" Maihaifin Mahmoud da sakin fuska ya amsa ma Hafsat dan sai ya ji Yarinyar ta shiga ranshi bisa ga alama tana da natsuwa. Mahaifin mahmoud kallan Hafsat ya yi ya ce. "Lafiya klau ki shirya da wuri zuwa t
8:00 za mu ta fi.
Hafsat cikin girmama ta ce, "Tom in sha Allahu"
Mahaifin Mahmoud haka ya tafi ya na yaba natsuwar Hafsat.
Hafsat tsabar murnar komawa gida da za ta yi ko abin breakfast ba ta naima ba wanka ta shiga ta yi ta sa d'aya daga cikin rigunan da Mahmoud ya sai mata da ya ke ba ta da Hijab sai dai gyale tai running a kanta. Hafsat bayan ta gama shiryawa zama ta yi tana jiran kiran Mahaifin Mahmoud.
Mahaifin Mahmoud ko mamaki ya yi ganin har ya gama shirinsa Mahmoud bai kirasa ba hakan ya sa ya Kira numbert mahmoud. Mahmoud ko da ya ke Kwana ya yi be barci ba hakan ya sa ya makara Kuma ya tashi da wani irin ciwan kai.
Yanzu haka kwance ya ke ciwan kai ya da mai wayar shi kuma a silent take, yanzu haka so ya ke ya ta shi dan ya san Mahaifinsa da tafiyar wuri, hasken wayar shi ne da yaga ni ga yi sauri ya d'auka.
Mahaifin Mahmoud murya sama-sama ya ce. "Mahmoud kana ina ne?" Mahmoud cikin dauriyar da yadda kan shi ke mai ya ce "Gani nan zuwa Abba"
Mahmoud cikin dauriya da yadda ya ke ji ya samu ya watsa ruwa.
Hafsat ko lokacin har ta fito, zuciyarta ce ke da murnar za ta koma gida.
Hafsat na fitowa ta hango Mahmoud da ke tahowa zuwa inda ta ke.
Mahmoud na zuwa inda Hafsat ta ke ya ja hannunta ya maida ta Falon Mahaifiyar shi. Mahmoud ta sa Hafsat ya yi ya na kallanta ya marasa abinda zaice mata.
Ita ma Hafsat Mahmoud d'in ta ke kallo.
Suna tsaye a haka Mahaifin Mahmoud ya kira Mahmoud awaya akan ya na fa jiransu.
Hafsat na tsaye tana jira ta ji abin da Mahmoud zai ce mata ba zato sai ji ta yi mahmoud ya rungumeta. Hafsat ƙoƙarin raba jikinta dana mahmoud ta fara tana cewa "Meye haka bana son iskanci."
Mahmoud kamar zai yi kuka ya ce "Hafsat ba iskanci bane ki tausaya min Kar ki karya alƙawarin da ki kai min ki, taba kaina ki ji zafi duk da baike zuciyata zafi ba, ki duba zaman da na yi dake Hafsat da ba sonki nake ba da na musguna miki, ki tausaya min ki duba girman alwarin da kikai min..."
Wayar Mahmoud dake ta ringing ya duba ya ga number Abbansa da sauri ya saki Hafsat yana kallanta kafin ya ce "Ki je Abbana na jiranki sai watarana"
Mahmoud na fad'in haka ya fad'a kan caution d'in falon ya na rik'e kanshi.
Hafsat ja ta yi ta tsaya ta kasa tafiya, kallan Mahmoud ta yi tana so ta yi masa magana ta Kuma rasa abin da zata ce mai hakan ya sa ta tafi da sauri ba tare da tace komai ba.
Hafsat cikin sanyi jiki ta tafi har zuwa inda Mahaifin Mahmoud yake tsaye da motarsa.
Mahaifin Mahmoud batare da ya ce ma Hafsat komai ba bud'e mata back ya yi ta shiga.
Mahaifin Mahmoud da kwatancan Hafsat su ka isa har k'ofar gidan su Hafsat.
Mahaifin Mahmoud juyawa ya yi ya kalli Hafsat ya ce. "Ki shiga sai ki min sallama da Mahaifinki".
Hafsat fita ta yi daga motar ta na jin wani irin sanyi a zuciyarta...✍🏻
Fadila Sani Bakori ce✍🏻
💓💞SO NE SILA💓
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
Page 19&20
Hafsat ko da ta gidan su ja ta yi ta tsaya tana kuka ganinta a gidansu da ta yi.
Hafsat cikin danne kukan da ta ke yi ta yi sallama da d'an k'arfinta.
Alokacin ko matar wan Mahaifinta Hafsat wadda suke kira da Maman Rabi tana wanki kamar daga sama ta jiyo sallamar Hafsat.
Cikin mamaki ta waigo dan tabbatar ma kanta wa ce ce, ai ko da murnar ta ta ruga ta rungume Hafsat da ke tsaye k'ikam.
Maman Rabi cikin murna ta ke cewa "Muta nan gidan nan Ina kuke ku zo ga Hafsat ta dawo."
Kamar a mafarki haka mahaifiyar Hafsat ta tsinci maganar ai ko da saurinta ta fito nan fa duk matan gidan su ka yo waje.
Haka ga bad'ayansu su ka taru suka rungume Hafsat, masu kuka na yi masu murna na yi, Hafsat tunawa ta yi ashe fa tare da bak'o ta ke.
Hafsat kallan Mahaifiyar ta ta yi da ke can gefe tana share hawaye ta ce. "Mama ina tare da bak'o yana kofar gida" Mahaifiyar Hafsat waya ta ta d'akko ta kira Mahaifin Hafsat ta yi mai bayanin Hafsat ta dawo yanzu haka Wanda ya kawota ya na nan waje.
Mahaifin Hafsat cikin farin ciki ya yo gida, cikin k'ank'anin lokaci sai ga Mahaifin Hafsat ya dawo.
Mahaifin Hafsat ko da ya ga Mahaifin Mahmoud a k'ofar gidan ya tabbatar da shine Wanda aka ce ya kawo Hafsat.
Mahaifin Hafsat cikin murnar da ya kasa b'oyewa ya kalli Mahaifin Mahmoud ya ce, "Assalamu alaikum barka dai, na ce dan Allah ko kai ne Wanda ka kawo Hafsat?" Mahaifin Mahmoud cikin girmamawa ya amsa sallamar Mahaifin Hafsat sanna ya ce. "Eh ni ne na kawo ta" Ma sha Allah tom dan Allah mu shiga daga ciki ko?" Mahaifin Mahmoud bayan Mahaifin Hafsat ya bi suka shiga gidan su Hafsat.
Maihaifin Hafsat d'akin shi ya saukar da Mahaifin Mahmoud.
Bayan gama 'yan gaishe-gaishe ne da aka yi Mahaifin Mahmoud ya kalli Iyayan Hafsat da ke zaune duk suna jiran jin ta bakinsa.
Mahaifin Muhmoud kallan Iyayan Hafsat ya yi d'aya bayan d'aya su hud'u duk maza, Mahaifin Mahmoud ji ya yi ba zai iya ce mu su d'an shi ne ya sato masu 'ya ba, cikin hikimar ya ce. "Tom alhamdullahi ga Hafsat nan Allah ya yi ta dawo gare ku, Amma gaskiya ni ba zan iya cewa taka mai-mai ga wa inda su ka d'auki Hafsat ba, amma dai yarona shine ya tsinci Hafsat ita kuma a sa'in ba ta cikin hayya cinta, sai a hankali-ahankali da natsuwa ta fara dawomata mu ka ji ko wa cece ita, wannan shi ne abinda na sani game da yarinyarku, Hafsat ga tanan sauran bayanin sai ta k'arasa muku."
Hafsat ta yi mamakin yadda Mahaifin Mahmoud ya b'oye Mahmoud bai bayyana shine ya sace ta ba.
Mahaifin Hafsat cikin farin cikin da ya kasa boyewa
ya kalli Mahaifin Mahmoud ya ce, "Alhaji mun ji duk ba ya nan ka kuma mun gamsu Allah ya saka maka da alkairi mafifici" Ameen duk wa inna da ke gurin su ka amsa.
Mahaifin Mahmoud sallama ya yi masu tare da kyautar kud'i masu tsoka ya tafi.
Godiya sosai su kai mai ya tafi.
Bayan ta fitar Mahaifin Mahmoud ne babban wansu Mahaifin Hafsat ya kalli Hafsat ya ce. "Hafsat duk bayanin da mutumin nan ya yi game da b'atan ki haka ne?" Hafsat d'aga kai ta yi ta ce, "Eh haka ne baba" Tom ma sha Allah Allah ya kare gaba, amma ke baki san wanda suka saceki ba?." Kai Hafsat ta girgiza ta ce "Ban Sani ba sai dai na farka na ganin gidan su wannan bawan Allah da ya kawoni"
Ikon Allah daga ji dama baya wuce masu garkuwa da mutane daman ai." An dade ana tattauna zancan kafin kowa ya kama gabansa, ya rage daga Hafsat sai Mahaifinta.
Bayan kowa ya watse ne Hafsat ta kalli Iyayan nata ta ce. "Mama ina Fadila fa?." Tare su ka had'a ba ki wajan ba Hafsat amsar "Tana Islamiya" Mahaifiyar Hafsat hannun Hafsat ta gama ta ce ,"Mu je ki huta ko Hafsat" Hafsat ta shi ta yi ta bi bayan Mahaifiyar ta ta kai ta d'akin da ya ke a mazaunin nasu ita da Fadila. Hafsat na nan zaune ita ka d'ai Mahaifiyarta ta koma kitchen wajan girgi, Fadila ce ta shigo gidan da gudu Fadila ta yi shashin su Hafsat kwance ta iske Hafsat kamar mai tinanin wani abun.
Fadila k'ank'ame Hafsat ta yi ta na mai murnar da wowarta''
Hafsat na zaune suna hira ita da Fadila Mahaifiyar Hafsat ta kawo masu abincin.
Su Hafsat na tsaka da cin abincinsu ne gwaggon su yayar Mahaifinsu Mahaifiyar Usman ta yi Sallama ta shigo gidan.
Tun kafin ta k'arasa shigowa ta ke zage-zage ta ce. "Yanzu dan iskanci ace 'yar tawa ta dawo amma a rasa wanda zai kirani ya fad'amin sai dai in ji agari"
Mahaifiyar Hafsat ce ta tare ta da cewa"Yi hak'uri yaya Uwani Wallahi na yi tunanin kinji wajan Babansu Hafsat" Wadda aka kira da Uwani kallan Mahaifiyar Hafsat ta yi ta ce, "Tom wai ina Hafsat d'in ne?" Hafsat fitowa ta yi daga d'akin ta zuk'unna har k'asa ta gaida gwaggon ta kuma surikarta.
Mahaifiyar Usman kallan Hafsat ta yi ta ce. "Sannu Hafsat Allah ya kyauta gaba, Ina Iyayan naki maza suke?" Hafsat cikin girmama ta ce. "Ina jin sun fita" Mahaifiyar Usman kallan Mahaifiyar Hafsat ta yi ta ce. "Ki Fad'ama mazan gidan zan dawo da daddare" Ta na kaiwa haka ta juya ta ta fi gida.
B'angaran Mahmoud ko dama duk abinda ya ke yi k'arfin hali ya ke yi, su Hafsat na tafiya ya rike kai jin yadda yake mai ciwo sosai. yana ji aranshi shi kenan Hafsat ta tafi kenan har abada an rabasu.
Mahmoud na nan kwance a wannan halin ya rasa inda zai sa kanshi juyi kawai ya ke shi kad'ai, Mahaifinshi ya yi Sallama ya shigo dawowar shi ke nan daga rakon Hafsat da ya yi.
Mahaifin Mahmoud kallan Mahmoud ya yi da ke rik'e da kanshi ya ce "Mahmoud baka da lafiya ne?" Mahmoud kai ya d'aga ma Mahaifinsa. Mahaifin Mahmoud kallan Mahmoud ya yi ya ce. "Me ke damunka?" Mahmoud na rik'e da kanshi ya tashi zaune, hannun Mahaifin nasa ya rik'e, magana ya ke son yi ma Mahaifin nasa amma ya kasa kawai sai ya fashe da kuka.
Mahaifin Mahmoud da mamaki ya bi Mahmoud da kallo dan ba karamin abu ke sashi kuka ba ko yana yaro, cikin damuwa da kukan Mahmoud din ya dafa shi cikin kwanciyar hankali ya ce "Kai fa namiji ne? Namijin Kuma soja kuka bai dace da Namiji irinka ba, fada min meye damuwarka?." Mahmoud kasa magana ya yi ya ci gaba da kukan shi dan bai san mai zai ce ma Mahaifinsa ba ya fahimci yadda ya ke ji.
Mahaifin Mahmoud ko ganin yadda Mahmoud ya dage sai kuka ya ke sai hankalin shi ya tashi cikin nuna damuwar halin da ya ga mahmoud din ya ce "Mahmoud dan Allah ka fad'a min mana, ko wajan aikin ka ne Kasamu matsala?." Mahmoud kasa magana ya yi sai dai ya girgiza ma mahifinsa kai.
Hankalin Mahaifin Mahmoud ya tashi cikin damuwa da alamun tashin hankali ya ce. "Mahmoud so ka ke kasa min damuwa ne Ina tambayarka lafiya ka tsaya kana min kuka?." Mahmoud hannun Mahaifin shi ya kama ya ce "Abba, ka taimaka min." Mahaifin Mahmoud cikin damuwa da son sanin da muwar d'annasa ya ce, "Mahmoud fad'i min da muwarka ko mai ye ni kuma zan taimakeka ko me ye amma ban da fasa auranka da Nafisa." Mahmoud k'ara rik'e hannun Mahaifin nasa ya yi ya ce. "Abba dan Allah auran Hafsat zaka gidansu ka naima min dan Allah Abba" "Mahmoud wata Hafsat? Ba dai Yarinyar da nakai gida yau ba?." Mahmoud cikin jarumta ya ce. "Ita Abba dan Allah"
Mahaifin Mahmoud shiru ya yi ya na tunani sannan zuwa can