sharri. Ya yi nisa cikin tunanin sharrin barasa.
Sai kuma ya ji wata zuciyar tana ce mishi, babu ruwan barasa, ba ma laifinta bane, gata ne kawai ba shi da shi, rashin tsayayye a kan al’amari ne kawai ya ja mishi, da yana da tsayayye da ba a jefa shi ba ma cikin damuwa da vacin ran da zai samu kanshi cikin wannan halin ba. Inna ce ta rasu ba ta nan ne, da tana raye da ban ma samu kaina a irin wannan yanayin ba.
Kalaman da suka rinqa kai kawo a zuciyarshi kenan, bai kuma ankara ba saia ganin shi kawai ya yi yana shiga cikin unguwarsu ta Tudun Alqali dake cikin garin Bauchi.
Ya yi parkinga a qofar gidansu wanda a yanzu ya mai da shi ginin zamani saboda rushe tsohon ginin da ya yi ya yi sabo. Kawu Gixe yana zaune cikin falon shi ya yi sallama ya shiga ya tsuguna.
Da sauri Kawu Gixe ya soma tambayar shi.
“Me ya same ka Mus’abu? Me ya sameka kake wannan baqin cikin?”
Mus’ab ya matse idonshi hawayen da suka taru suka xiga, abin da ya yi dalilin miqewar Kawu Gixe tsaye saboda tashin hankali.
“Me ya sameka?”
Ya sake yi mishi tambayar bayan ya kafa idanuwanshi a kanshi.
“Maraici ne kawai ya dame ni Kawu, tunda Inna ta rasu ta barni na koma watangaririya a tsakanin mutane, bani da wani tsayayye a kan al’amarina, rashinta yasa na samu kaina cikin baqin ciki da vacin rai, da tana raye da ban samu kaina cikin qasqancin da nake ciki ba a yau. Bani da uwa bani da mai tausayina balle ta rufa min asiri, bani da kowa, bani da inda za ni in faxi damuwata.
Shi yasa na zo gabanka in yi kuka don ka qara sanin har abada ba zan daina kukan mutuwar Inna ba, inda tana raye a duniya da babu mai yi min irin tonon asirin da aka yi min a Misau, an taro an nuna min fin qarfi an hanani auren Aisha saboda wai ni xin mashayi ne, da tana nan a raye Kawu da tasa an bani auren duk da ita xin ta fi kowa sanin mugun halayena, da ba za ta hanani auren ba, saboda ta san rabani da ita zai iya haddasa min vacin rai na samu kaina a yau cikin baqin ciki da qunci da ciwon zuciya, amma wai a hakan Abu ta sani a gaba tana yiwa waxanda suka hanani auren addu’ar Ubangiji ya saka musu da alheri, don wai gaskiya da adalcin sune yasa suka hanani auren da suka yi”.
Kawu Gixe ya koma kan kujerar shi ya zauna ya zubuawa Mus’ab ido, cikin nutsuwa ya tambaye shi.
“Dama kai kana son Saddiqa ne baka yi magana ba?”
Ya ce, “Eh, Kawu hanani yin maganar aka yi ta hanyar tsoratar dani wai idan na ce ina sonta za a gaya mata halina, to ga shi ban tsira ba, abin da na guda shine ya sameni. Inna ce jagorar rabani da Aisha, su Baba da su Abu suka mara mata baya. Ni ban ma qara sanin da hannun Abu a ciki ba sai da na jita ta dage tana ta yi musu addu……”
“Kai tafi can ka rufe min baki, kai ka jawa kanka komai, yanzu ka zo kana wannan surutun da in ba sa a ba zai tashi a shirme da surutu, bayani nake so na yanda aka yi hakan”.
Mus’ab ya shiga yi mishi bayani dalla-dalla tun farkon yanda ya faro maganar a gaban Abu, har kawo lokacin da Innarshi ta yiwa Saddiqa bayanin komai, al’amuran da suka biyo bayan hakan da suka yi dalilin bikin gaggawa da suka tayar, har rotsen da ya yiwa Hamida da ya zama hujjar Abu ta fita cikin lamarinshi, da addu’ar da take yiwa iyayenshi bai voye komai ba.
Kawu Gixe ya sunkuyar da kai qasa cikin tunanin mafita. Mus’ab ya yi matuqar razana, don tunanin ko shima zai yi fushi da shi ne. nan da nan ya shiga ba shi haquri yana magiya.
“Ka taimakeni kasa baki cikin lamarin Kawu ka hana su xaurin auren da suke shirin yi jibi, ka tura shi zuwa wani lokaci dan in samu damar da zan ga Aisha in san yanda na yi-na yi mata bayanin da za ta fahimceni, zan gaya mata irin son da nake yi mata, zan yi qoqari in fahimtar da ita al’amura masu yawa da ke tsakanina da ita a baya, ban samu damar gaya mata abin da ya kamata in gaya mata ba saboda ina tsoron kar a tona min asiri a wurinta, to yanzu kuma tsoron ya qare zan nuna mata……”
“Kai rufe min baki mashirmancin banza!”
Kawu Gixe ya yi maganar a yanayi na vacin rai. Ya yi maza ya ja bakinshi ya yi shiru.
“Kira min Malam Hadi”.
Ya tashi cikin nutsuwa ya fita don cika umarnin da Kawun ya ba shi, ya nufi unguwar Railway don isar da saqon.
Malam Hadi shine amini na qut da qut a wurin Kawu Gixe. Bai yi qasa a gwiwa ba ya biyo shi suka taho tare, ya wuce cikin gida ya barsu nan suna tattaunawa.
Mus’ab yana zaune a wani xaki da ya barwa kanshi a cikin gidan, wanda yake ganin tamkar shine a gurbin na Innarshi da ta rayu a ciki, inda tana nan da ita ce za ta bani Aisha, ba tare da ta damu da cewar ni xin mashayi ne ko manemin mata ba, inda tana nan ma wataqila da ban samu kaina a wannan halin da nake ciki ba.
Ya xan yi ajiyar zuciya kafin ya sake ya sake tsunduma cikin tunanin rayuwarshi a gaban Innar tashi, yanda ya zo mata da yanda ta tafi ta barshi.
“Wayyo Inna!”
Ya yi shiru zuwa wani lokaci kafin daga bisani ya shiga gabatar mata da addu’o’i, tsawon lokaci yana cikin wannan yanayin kafin ya koma kan tunanin Aisha da kalamanta na ba ita ba shi, bayan kuma sun yiwa juna alqawarin kasancewa tare, sai da taimekon shi kan maganar neman auren shi, sai ga shi da abin ya bayyana a kana ta bijire mishi, saboda an gaya mata halayenshi.
Sannu a hankali ya sake tambayar kanshi.
“Ko meye alherin barasa? Ko ya ya zai yi ya daina shanta? Anya in har ya rasa auren Aisha zai iya daina shan barasa a rayuwarshi? Ina ma dai a ce duk mutanen duniya irin Innarshi ne masu qoqarin taimakon mutum, gyara halinshi da mugayen xabi’unshi ta hanyar janshi a ciki, taimakon shi ta hanyar qarfafawa, mutunta shi da nuna mishi munin abin da yake yin a nutse, maimakon a qyamace shi ko a guje shi”.
Kawu Gixe suna tare da amininshi Malam Hadi, kusan minti talatin suna tattaunawa kan hanyar da za su bi su fitowa lamarin. Daga qarshe suka yankewa kansu abin da ya dace suyi, wanda ya sanya Kawu Gixe cikin sauri ya shiga cikin gida ya kira babban xanshi Adamu ya aike shi cikin motar Mus’ab ya zo da ita.
Sani da Ishaq suka iso falon Kawu Gixe cikin ladabi suka gaishe shi.
“Kawu mun zo wajenka neman taimako ka sanya baki cikin maganar auren da ake shirin xaurawa Saddiqa a Misau jibi”.
Ya kalle su ya ce, “Yau ne ya kamata ku sanar dani?”
Sani ya gyara zama cikin nutsuwa ya ce, “Kawu ka yi haquri, muma yau ne da muka bi bayan Mus’ab zuwa gidan Abu muka ji cewar jibin za a xaura aure, mun kuma nemi Mus’ab a waya ya rufe, Abu kuma ta gaya mana cewar ta gaya mishi komai, bai kuma ce mata ga inda za shi ba don haka muka ce bari mu zo gabanka mu roqi wannan alfarmar, don mun san duk inda yake in ya samu labarin an xaga xin zai samu sassauci”.
Malam Hadi ya shigo tare da wasu dattawa su uku, don haka su Sani suka ja gefe suka takure suna jiran su gama abin da suke yi kafin su sake matsawa gaban Kawu Gixe su qara roqon shi ya yi wani abu kan al’amarin.
Suna zaman jiran sai ga Adamu ya shigo da manyan qunshin goro guda biyu.
“To ai ma shi kenan mun isa Allah gafarta malam ko kuwa?”
Kawu Gixe ne ya yi tambayar.
Malamin dake zaune a gefenshi cikin rawani ya ce mishi, “Eh, mun isa ai shaidu ma su kan gamsar wajen xuarin aure, balle mu a nan mu shida ne”.
Da sauri Malam Hadi ya ce, “Ai ga su Malam Isa ma sun dawo”.
Ya yi maza ya leqa ya kirasu suka shigo, su ma su uku. Nan take Kawu Gixe yasa aka xaura auren Mus’ab da Aishatu, abin da ya yi matuqar baiwa Sani da Ishaq mamaki.
An gama xaurin aure an raba goro, jama’a suna watse kowa ya nufi gidanshi, Sani da Ishaq suna durqushe gaban Kawu Gixe sun rasa kalmar da za suyi amfani da ita wajen yi mishi godiya. Sai ga Mus’ab xin ya shigo saboda kiran da Kawu Gixe yasa aka yi mishi.
“Ku gama kafin in fito”.
Kalmar da Mus’ab ya riska kenan na maganar Kawu Gixe. Ya kuma kalli Mus’ab xin bayan ya nuna su Sani da hannunshi.
“Ga masu neman ka can”.
Ya wuce ya yi tafiyarshi. Ishaq ya qanqame Mus’ab a yanayi na tsananin farin ciki.
“Na rantse yau ne na tabbatar da kalmar da Hausawa ke furtawa ta ABU NAKA…. Wai maganin a kwaveka. Kawu Gixe ya xaura auren ka Mus’ab”.
Mus’ab yasa hannu biyu ya hankaxe shi.
“Kai bana son irin zolayar da kuke yi min yau? Haka Sani ya ce min wai sun sato Aisha ashe qarya yake yi min, zuciyata a quntace take ina cikin wani al’amari da ban san shi ba……..”
Kan ya qarasa maganar tashi Ishaq ya yi mishi rantsuwa.
“Yanzun nan muka gama xaurin auren ka Mus’ab, Kawu Gixe ya baka auren, ga goro ga minti ga takardunsu kana kallo”.
Sai a lokacin ne hankalinshi ya kai garesu, gabanshi ya yanke ya faxi, cikin fargaba da tsoro kar dai shima Kawu Gixen irin auren da Abu take so ta yi ya yi mishi, auren huce fushi.
Hannu ya xora kan qirjinshi saboda harbawar da takeyi.
“Kawu Gixe ya xaura min aure?”
Da qyar ya iya buxe baki ya sake tambayar su.
“To wa ya bani?”
Sani yana murmushi ya ce, “Saddiqa”.
Mus’ab ya kalle shi haushin zolayar da suke yi mishi ya qara kama shi, me suke nufi dani waxannan? Basa tausayina ne? Ko so suke su mai dani tamkar mahaukaci? Ya juya ya fita wajen Kawu Gixen ya tafi.
“Ka taimakeni Kawu kar ka bani auren da ba shi nake so ba, Aisha kaxai nake so in ba ita ba ce gara a barni haka kar a xora min nauyin kowa a kaina, a barni kawai in yi zamana a haka”.
Kawu Gixe ya zuba mishi ido.
“Me abokan naka suka gaya maka?”
Ya buqaci sani.
“Kawu rabu dasu, su basa tausayina zolayata suke yi. Sun ce min wai da Aisha ka xaura min auren, amma na san qarya suke yi so kawai suke yi wai su ga na samu nutsuwa, bayan kuma baqin ciki ya sameni”.
Cikin nutsuwa Kawu Gixen ya ce mishi, “Ita na baka Mus’abu, da ita na xaura maka aure, ai taka ce. ABU NAKA…. Maganin a kwave ka. Gaskiya ne da ka ce inda uwarku tana raye za ta baka ita ba tare da ta xaga ido ta yi duba kan irin laifuffukanka ba, ba ta nan, to ni ina nan, nima kuma ba zan iya barinsu su rabaka da ita ba. Don haka a zaman da kake yi a yanzu Aisha matarka ce, na baka ita ta hanyar xaura auren sunna a tsakaninku, mallakinka ce tana qarqashin hukuncinka, yanda ka so haka za ka yi da ita a yau”.
Mus’ab ya sunkuyar da kai a gaban Kawu Gixe tsawon lokaci bai ita ce mishi komai ba. Sai Kawu Gixen ne yake magana mafi yawancin nasiha shan giya da neman mata.
“Manyan musibu ne Mus’abu, aiyukan savo ne masu girma, kai ka sani irin waxannan aiyukan kuma xabi’u ne na mutanen banza, mutanen da basa tsoron Ubangiji, kai ba mutumin banza bane, domin mutanen kirki ne suka haifeka, iyayenka mutanen kirki ne, ka fita cikin wannan rayuwar ko kaxan ba ta dace da kai ba, ba kuma ina yi maka wannan maganar bane a yau wai ko saboda Aisha ta zama matarka, a’a, sai dai don a zuciyata ina burin ganin ka zama cikakken mutumin kirki ba mai yawan cuxanya da zunubai ba”.
Cikin ladabi Mus’ab ya ce mishi, “Na sani Kawu, na roqeka ka yafe min rashin kawo maganar da ban yi ba tun farko na rinqa ganin kamar bani da wani tsayayye kan al’amarina, na manta da cewar duk wani wanda ya tsaya min ya taimakeni ko ya soni ya yi hakan ne a dalilin ganin tsayawarka, taimakon ka da kuma soyayyar ka a gareni.
Kai ne ka tsamoni cikin halakar da na samu kaina a ciki, ka kawoni gidan nan kuka haxu kai da Inna kuka yi min gata, kuka mai dani mutum na zama cikakken xa mai cikakken ‘yanci, kuka xorani a bisa hanya ta rayuwa.
Ga shi a yau kuma ka sake yi min wani alherin na rabani da baqin cikin da ya sameni, ka ceci rayuwata daga shiga halin butulci na ganin tamkar bani da kowa, ka bani yarinyar da nake ganin tamkar ita kaxai ke gareni, in ban same ta ba kuma ba zan mallaki kaina ba, duk da kai xin ka fi kowa sanin mugayen aiyukana, ka fi kowa sanin abin da nake yi. Na roqe ka ka taimakeni ka yi min addu’a Ubangiji ya tsare min aurena da Aisha, ya kuma zaunar damu lafiya”.
Kawu Gixe ya ce mishi, “To Mus’abu zan yi maka”.
“To Kawu ka yi min addu’ar”.
Kawu Gixe ya shirya goro da minti gami da sadakin da ya biyawa Mus’ab na kuxi naira dubu uku ya tashi amininshi Malam Hadi tare da matarshi Furera da tashi matar Raliya, suka koma a cikin motar Mus’ab suka nufi Misau Adamu yana tuqa su, don suje su isar da saqon xaurin auren da ya yi tsakanin Mus’ab da Saddiqa.
Suma su Mus’ab suna ganin tafiyarsu suka bar gidan cikin motar Ishaq, su ma Misau xin suka nufa, zukatansu cike da farin ciki da annashuwa, suna tafe suna hirar Kawu Gixe da alherinshi.
GARIN MISAU
Gidan su Inna Habiba a Misau ya cika ya tumbatsa da jama’a ‘yan saka lalle, ba qaramin cika aka yi ba a gidan kasancewar Inna Habiba ta kwana biyu ba ta yi bikin ba, tun na ‘yar autar ta Hamida.
Sai dai ita kam Inna yanzu ne take faxin bikin ‘yar auta, don haka biki sosai ta shirya, ta kuma gayyaci ‘yan’uwa nesa da na kusa, ga kuma abokan arziki.
Saddiqa tana kwance a xakinta tun bayan saka lallen da aka yi mata ta kasa fahimtar halin da take ciki, ita dai kawai ta san saka lallen ya haifar mata da matsanancin baqin ciki, damuwa gami da vacin rai mai tsanani, ga shi dai ba son Mus’ab take yi ba saboda ya fita ranta kwata-kwata a dalilin munanan halayenshi da aka gaya mata na kasancewar shi fasiqi.
To amma kuma abin takaicin shine, shima Sadisun ba ta son shi shima ya fita ranta, ba ta qaunar ko sunanshi ta ji ana ambata mata. Ta fi so a barta kawai, a barta ta yi zamanta haka babu auren, shima auren ba ta son shi, in ban da kar ta yi savo ma da ta ce ta tsane shi, don daga tasowarshin ta samu kanta cikin yanayin da take ciki a yanzu na baqin ciki da qunci da tsirarar waxanda ake ganin girmansu.
Malam Abdullahi ya fito yiwa baqin shi rakiya lokacin da Adamu ya yi parking a qofar gidan cikin motar Mus’ab, da farko ya xauka Mus’ab xin ne, sai da ya ga fitowar Adamu da sauran mutanen da suke ciki nan da nan ya yi sallama da baqin nashi ya juyo tarar Malam Hadi.
“Barka da zuwa”.
Ya isa da shi xakinshi na waje. Su Baba Furera kuma suka wuce cikin gida inda su ma suka samu tarba mai gamsarwa.
Bayan sun ci sun sha an kuma gaggaisa anyi raha yaushe gamo? Inna Habiba tana tambayar Inna Raliya.
“Yanzu nan dama za ku zo amma baku iso da wuri aka yi saka lallen nan daku ba?”
Ta yi murmushi ta ce, “To ba gashi anyi ba? Ai barinki dai na yi ki yi yanda kike so, tunda ke ce uwar ke ce uban”. Mutanen dake wurin suka taya su dariyar da suke yi.
“Sallamu alaikum! Gwaggo tana ciki?”
Muryar Malam Abdullahi ne daga waje-wajen zaure saboda cikowar mutane. Da sauri Bilkisu ta iso cikin ladabi tana tambayar shi.
“Baba Abu za a kira maka?”
Ya ce, “Eh, maza kira min ita”.
Ta yi maza ta nufi xakin da Abu ke ciki tare da ‘yan tsofaffi aminanta suna hirarsu. Tana jin kiran ta yi maza ta fita ta nufi inda Malam Abdullahi ke sauraron zuwan nata.
Sai da ta gama sauraron bayanin nashi sannan ta shigo gida tana salati.
“Iko sai Ubangiji, wani baya auren matar wani. Shi aure dama ya gaji haka, koma in ce abin da ya fi haka, dama kuma an ce matar mutum kabarinsa”.
Gaba xaya wuri ya yi tsit! Ana sauraron kalaman nata.
Ta leqa falon Inna Habiba inda jama’a ke cike ta ce, “A’a, ke Furera ashe kun baiwa xanku auren shine da kuka zo baki gaya mana ba?”
Inna Habiba ta zuba musu ido tana kallo cikin yanayi na rashin fahimta da son jin bayani.
Inna Furera ta ce, “Eh, Gwaggo gani na yi mun zo da amininshi”.
Ta ce, “Haka ne ta xaga ido ta kalli taron jama’ar dake wurin, ta ce, “Jama’a aure fa ya zama a kan Mus’abu yake, don xazu da yamma Kawunshi ya xaura mishi aure da Saddiqa, ga goro nan da minti da kuma sadakinta dubu uku ya bayar ya ce a kawowa uwarta”.
Kukan da Inna Habiba ta saka shine ya taqaita farin cikin su Bilkisu da ‘yan’uwanta, gaba xaya aka taru a kan Inna Habiban ana ta faman ba ta haquri.
Baba Furera kuwa cewa take yi, “Babu wata kunya da aka baki tunda ya ce a gaya miki ki sa a xaurawa Sadisu aure da Kubra, ba shi kenan ba magana ta qare”.
Ita kuwa Saddiqa tana kwance a xakinta ta yi kasaqe tana sauraro tare da tambayar kanta me yasa Gwaggonta kuka haka a cikin taron mutanen da ta tara?
A daidai lokacin ta ji wayarta tana qara, rabon da ta ji qaarar an daxe, don haka ta miqa hannu ta xauka don ta ga waye.
Duk da ta daina amsa wayarshi sai ta yi nufin amsawa, wai ta ji me zai ce mata. Yana jin ta xauka bai jira ta ce komai ba ya soma ce mata.
“Ina miki barka tare da albishir na zama amarya ta har abada, Aisha ina tabbatar miki da cewar daga yau kin shiga amarcin da ba zai tava qarewa ba har abada, dama can ni dake abu xaya ne Aisha, za kuma mu ci gaba da zama abu xaya”.
Saddiqa ta rasa me za ta ce mishi tunda ba ta gane me yake nufi da kalaman nashi ba balle ta gane inda ya dosa.
Abin mamakin dai shine, muryarshi ba ta cikin yanayi na tashin hankalin da ya kirata a baya, ba ta san yanda aka yi ba sai kawai ta ji ta fashe mishi da kuka. Ya yi maza ya katse layin.
Qawarta da ta fita tsakar gida don wanke hannu ita ce ta shigo tana ce mata, “Na fa ji kamar ana cewa wai yau a Bauchi an xaura aurenki da Yaya Mus’abunki, shi kuma Sadisu wai an ce a bashi ‘yar’uwarki Kubra”.
“Yaya Mus’ab?”
Da qarfi Saddiqa ta yi tambayar. Nan take kuma ta sake fashewa da wani sabon kuka mai tsanani.
Su Bilkisu da ‘yan’uwanta suka yi maza suka fice daga gidan saboda ganin an samu an shawo kan mahaifiyarsu ta daina kukan da take yi. Kasancewar dare ya riga ya fara yi bai hanasu nufar gidan Mus’ab ba dake can bayan gari don su taya juna murna.
Qwayayen fitilu sun haske ko’ina na harabar gidan, tun kafin ka qaraso kuma kana jiyo sautin jama’a, ga kuma motoci a tsaitsaye a harabar gidan alamar tuni har abokanshi dake kurkusa sun fara isowa.
A haka suka qarasa shiga gidan, daga nesa suka hangoshi riqe da sigarinshi a hannu yana kuma amsa waya.
“Yaya Mus’ab ashe kuma sai zama ango?”
Ya yi murmushi ya ce, “Eh, Bilkisu abin kamar babu wuya amma mu kam ai mun san mun ji jiki, ko kuwa?”
Gaba xaya suka yi murmushi. Nan take kuma suka shiga gaishe shi da yi mishi murna a yanayi na girmamawa.
“To ya ya Inna ta karvi labarin?”
Cikin nutsuwa ya yi musu tambayar. Suka gaya mishi komai. Ya yi ajiyar zuciya a hankali ya furta kalmar.
“Ta yi haquri, ku taimake ni ku ba ta haquri, ku ba ta haquri Aisha matata ce ta yi haquri ta karvi hakan, Kawu ya riga ya bani ita, qaddara ce hakan don haka ta yi haquri”.
Sun xan fara yin magana sai ya xaga ido ya kalli Hamida a wani yanayi da ya fi kama da kunya ko nadama tare da shan mur!
“Ba ki dai gayawa mijinki abin da ya sameki a goshin ba ko?”
Ta yi maza ta sunkuyar da kanta qasa tare da jan gyalenta ta qara rufe fuskarta dake goshin nata ta yi shiru saboda jin nauyinshi.
Suna cikin zancen da suke yi Bilkisu ta ce, “Shi kenan ‘yan ina da biki, biki ya zama nasu sai ya ya kenan?”
Ya yi murmushi ya ce, “Sai ku yi sabon shiri Balki, sabon biki sabon komai”.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 24