Share this page
Ya kalli Saddiqa ya kawar da kanshi, har lokacin idanuwanta basu wattsake daga kukan da ta yi ba, iyaka dai ta yi wanka ta kuma yi kwalliya ‘yar kaxan. Sannu da Abu tana fara’arta ta amsa, sannu da qoqari Mus’abu ka dawo ba? Ya ce mata, “Eh”. “To sannu da zuwa, Ubangiji ya yi muku albarka ya rufa muku asiri, ya kuma sa ku gama da duniya lafiya”. Ya ce mata, “Amin Abu”. Ya juya zai tafi wurinshi. Ta ce mishi, “Ga abincinka nan a kicin sai ka shiga ka xauka”. Bai kalle ta ba ya ce, “Aisha ba ta ji sauqi bane Abu? Ki bata ta kawo min mana”. Ba ta tanka mishi ba don haka ya biya ya xauka ya tafi da shi wurin nashi. Kwana biyu a jere Abu tana cikin hidimar tarirayar Saddiqa, kulawa da shagwava, har dai Mus’ab ya gundura da abin saboda ko kusa da ita ba ta barinshi yaje. Ya shiga kicin inda ya hangeta tana gashin nama, ya same ta cikin nutsuwa ya ce mata, “To wai ni Abu ni kuma ni shi kenan ne?” “Shi kenan kamar ya ya?” Ta yi tambayar tana kallon shi. Ya xan yi murmushi tare da miqa hannu wajen tayata aikin da ya tarar tana yi. “To ba kema na ji kiuna ce mata ba cutarta na yi ba, kuma ban zalunce ta ba?” Ta ce, “Eh”. Ya ce, “To tunda haka ne ba sai ki lallavata ki xan rinqa turo min ita ba, kina gani fa har yanzu ko magana na yi mata ba ta amsawa”. Abu ta yi dariya ta ce, “Naqi in lallava maka itan, ai sai daxin ya yi maka yawa, randa na tafi na barku ku biyu a gidanku ka san yanda ka yi ka lallava abinka”. Satin Abu guda a gidan ta sanar da Mus’ab shirinta na komawa Misau a kwanaki biyu masu zuwa a gaba. “Da sauri haka Abu?” Ta yi murmushi ta ce, “Ai na zauna muku Mus’ab ina laifi, in ban da gidanku kai da matarka ina za ni in yi wannan zaman?” Cikin nutsuwa da girmamawa ya ce mata, “Ai mun gode miki Abu, Ubangiji ya qarawa rayuwarki albarka”. Daga gefenta Saddiqa ta yi magana a yanayi na sanyin jiki. “Zan biki gida Abu”. Abu ta waiwaya ta kalle ta, tuni har hawaye sun fara zuba a idanuwanta. “A’a, Saddiqa dena wannan kukan ki share hawayenki ki ji abin da zan gaya miki, ki bini gida Misau kina so mujewa iyayenku da abin da zai baqanta musu rai ne? Ai ni jakadiya ce ta alheri a garesu, zan je musu ne da labari mai daxi mai faranta musu rai. Na zo na same ku lafiya, na kuma barku lafiya har ga albishir mai daxi zan je musu da shi”. Ta ci gaba da maganarta da cewa, “Aure ai girma ne, girma kuma haquri ne, don haka ki yi haquri ki zauna tare da mijinki, ki yi mishi biyayya, yi na yi bari na bari, ba ki ga irin kai kawon da yake yi a kanki ba? Yana sonki, to in kin tafi ki barshi da wa Saddiqa? Kar ki yi haka”. Mus’ab ya tashi ya tafi ya basu wuri. Tana ganin fitar Mus’ab ta qara mai da hankalinta wurin Saddiqa. “Sa hannu biyu ki rungumi al’amarin mijinki, kar ki yarda ki yi wasa da aurenki, kullum ki je ki gaishe shi, kullum ki karkaxe mishi shimfixarshi, kullum ki yi mishi abinci mai daxi. Ki sa ido sosai a kan shi, kar ki yarda hannunshi ya tava wata mace in ba ke ba ce, kar ki yarda ya mai dake qaramar mace, kina gida a zaune shi yana can wurin matan banza a waje. In tafi dake gida to ki barwa wa shi? Ki barwa matan bariki ko? Ke bakya kishi ne?” Ta tsareta da ido. “Ni kuwa ai kishi ne dani, ban tava barwa wata mace mijina ba shi yasa ma bayan rasuwarshi ban yarda na sake yin wani auren ba, sai na yi zamana kawai saboda na fi so ko a lahira a ce shine mijina na aljanna cikin yardar Ubangiji”. Yanda Abu ta yiwa Saddiqa nasiha da kalamai masu daxi, haka ta zaunar da Mus’ab ta yi mishi irin wanda za ta yi mishi, sai dai shi kam ba irin rarrashin da ta yiwa Saddiqa ta yi mishi ba. “Kar ka zalunceta ka yi haquri da ita, ka yi mata adalci, ka sani ba ta da kowa a garin nan in ba kai ba”. Ya ce, “To Abu, na gode Ubangiji ya saka miki alherinki a gareni”. Ta yi murmushi ta ce, “Amin Mus’abu ya saka mana tare”. Duk kalaman da Abu ta yiwa Saddiqa na rarrashi da kwantar da hankali, da yanda zuciyar Saddiqan ya karvi maganganun da ta yi mata bai hana zuciyarta ta karaya ba har ta yi ta zubar da hawaye tana kuka tare da faxin, “Zan bi ki Abu”. A lokacin da ta ga ana ta fitar da tsarabar da Mus’ab ya yi mata ana jibgawa cikin motar da za ta mai da ita gida Misau. GARIN MISAU A RANAR ALHAMIS DA YAMMA Gwaggo Habiba tana cikin kicin xinta tana qoqarin dama kunun tsamiyar da za suyi buxa bakin azumin nafilan da suke ita da mijinta. Tsayuwar motar da ta ji ‘jiiyim’ kusa da qofar shigowa zauren gidan yasa ta fitowa da sauri ta zo ta tsaya a tsakar gidan tana kallon hanyar shigowa gidan, cikin zuciyarta tana faxin wannan motar dai da qyar in ba Inna ta kawo ba. “Assalamu alaikum”. Muryar Abu cikin fara’a da murmushi ta shigo gidan tamkar ba ta wahala a tafiyar tata ba. “Lah! Ashe kuwa ke ce Inna, Inna sannu da zuwa, dama tunda na ji tsayuwaar motar dama na ce wataqila kece a ciki, sannu da zuwa, Inna kun shawo hanya”. Suka nufi xakinta tana shimfixa mata tabarma tana faxin “Tun shekaran jiya muke sa rai dake a gidan nan”. Abu ta yi murmushi irin wanda ta daxe ba ta yi ba. “Gidan Mus’abu fa na je a yau xin ma da ya ya na baro shi? Duka yaron nan ki gani in ya gama shigo da kayan tsarabar nan ki samu abin da kika ba shi ya ci, duk da dai ba yunwa muke ji ba”. Gwaggo Habiba ta yi murmushin jin daxin yanayin da ta ga mahaifiyarta a ciki, ta nufi wajen direban tana faxin “Wannan doguwar tafiyar da kuka yiwo Inna ki ce bakwa tare da yunwa”. “A’a, baya fa ba ta kaxan, kar dai a ce xan fitar nan da na yi ne Inna ta dawo a bayana?” Abu ta yi maza ta ce mishi, “Ai kuwa dai nice malama, hala tarin tsarabar da ka gani a tsakar gidanka ne yasa ka gane hakan?” Ya ce mata, “Eh”. Ta yi murmushi ta ce, “Aikin Mus’abu kenan”. Da daddare bayan sallar isha’i Gwaggo Habiba da Abu suna falonta, sun gaisa sun ci abinci suna hira. Ta qosa qwarai Abun ta ba ta labarin yanda ta baro Saddiqa, ita kuma sai ja mata rai take yi. Malam Abdullahi ya shigo falon ya same su a dalilin ya dawo daga sallar isha’i. “Gwaggo sai yau?” Ta yi dariya ta ce, “To yau xin ma da ya ya? Ai dagewa kawai na yi na ce in dai ba tayaku zaman auren naku zan yi ba, ai gara ku barni nima in koma wurin iyalina”. Malam Abdullahi ya yi dariya, ita kam Gwaggo Habiba sai murmushi take yi, ya yin da kanta ke sunkuye. “To ya ya kika baro su Gwaggo?” Ta yi maza ta ce, “Sai alheri, ga tsaraba can ya ce a kawo a rabawa ‘yan’uwa da maqwabta, in kuma gaya maka cewar kai da Kawunshi ku yi shirin tafiya aikin Hajji, ni kuma ni da uwarsu zamu je Umara na ce mishi a’a, ni kam Hajji zan ce don ban sauke farali ba, ga kuma girma ya riga ya kama ni, gara in je tun ban kai ga ba zan iya ba. Ya ce, to sai yanda muka shawarta”. Cikin farin ciki Malam Abdullahi ya ce, “Eh to, Gwaggo ai sai ku je Hajjin ke da Yaya Gixe mu sai mu tafi Umarar da Habiba”. Abu ta ce, “A’a, ni da kai dai mu yi Hajji, ita da xan’uwanta suyi Umarar, ai tafiyar da kai za ta fi min dai-dai”. Malam Abdullahi ya ce, “To, Ubangiji ya yi musu albarka”. Abu ta yi ta faxin “Amin-amin”. Har ya tashi ya fita saboda sallamar da aka yi da shi. Gwaggo Habiba dake zaune shiru a gefe ta xago ta sake tambayar ta, “To ya ya kuwa Saddiqa Inna?” Abu ta kalle ta cikin murmushi ta ce, “Duk wannan labari da nake bayarwa bai isheki ba sai kin ji na Saddiqa ita kaxai? To lafiyarta qalau na barota tana ta hidimar aurenta, ta ce a gaisheki, ga kuma saqo ta ce in kawo miki”. Cikin sauri Gwaggo Habiba tasa hannu ta karva tana warwarewa ta ga abin da ke jikin zanin gadon ta yi maza ta rufe tana salati, cikin sanyin jiki ta kalli Abu. “Irin wannan cin zarafin ya yi mata Inna? Wannan ai rashin tausayi ne”. Abu ta galla mata harara. “Ke kam ai ba za ki yaba mishi ba, ina can ne fa abin ya faru amma baki kalli haqurin da ya yi da ita ba, kin kuma san a kan ‘yarki ne maza suka fara yin haka. Ya dai ce in gaishe ki in kuma roqa mishi ke ki yafe mishi abubuwan da ya yi miki”. Ta miqe tana tafiya tana yafa zanin rufar ta. “Ni gidana za ni in kwana, in yara sun shigo ki xora musu kayana su biyoni da shi”. Gwaggo Habiba ta bi bayanta tana faxin, “Ki huta gajiya Inna, sai na zo miki ban gajiya”. AJAKUTA Mus’ab yana zaune a qofar gidanshi cikin shirin yin alwalar sallar magariba, ya kalli agogon hannunshi bayan ya kalli yanayin sama, zuciyarshi ta raya mishi da sauran lokaci. Nan take ta sake raya mishi yanzu kam cikin yardar Ubangiji in har komai ya tafi daidai kamar yanda ake fata, to Abu ta isa gida tana can tana bai wa su Inna labarin Aisha ta kai budurcinta, ya san babu wani labari da zai fi wannan daxin bayarwa a wurin Abu. Ya xan yi shiru kaxan cikin wani tunanin, zuciyar tashi ce dai take sake tuna mishi da irin wunin da ya yi tare da Saddiqa bayan tafiyar Abu a ranar cikin kuka da takura mai yawa, wanda ya yi dalilin da ko aiki bai samu damar zuwa ba. Son shi ne ba ta yi yasa take waxannan abubuwan ko kuwa? Ya yi maza ya kawar da wannan tunanin saboda dalilai guda biyu. Na farko mu’amalarshi da ita a farko, yanda ta bijirewa auren Sadisu ta nemi a barta kawai ta yi mata yanda ita da kanta ta gayawa Gwaggonta ita xin shi take so, da yanda ita da kanta ba tare da ya nemi ta yi mishi hakan ba ta voyewa Abu halin da suke ciki a lokacin da ta zo gidan. Waxannan dalilai guda biyu sune suka qarfafa zuciyarshi ya xan ji sanyi, ya kuma qarfafa zuciyar tashi a kan himmatuwa wajen ganin ya shawo kan lamarin nashi. Hadari ya taso tare da iska mai tsanani, wanda ya yi dalilin da liman ya bayar da umarnin haxa jam’in magariba da isha’i a masallacin. Ya shigo gida daidai ruwan saman yana saukowa, zuciyarshi ta yi mishi daxi saboda sanin da ya yi Saddiqa matsoraciya ce. Wurinta ya fara isa bayan ya gama rurrufe qofofin gidan. “Kin yi sallah kuwa?” Ta amsa mishi da eh. Ya wuce ta yana tunanin irin takurar da ya ga ta yi, ina ma dai NEPA su xauke wutar lantarkin. Yana yin wannan tunanin ya miqa hannu kan mitar gidan ya kashe wutar, duu ya bayyana a ko’ina. Ya wuce ya nufi wurinshi. Bai daxe da shiga wurin nashi ba ya ji motsin Saddiqa a cikin falon nashi. “Waye aa nan?” Ya yi tambayar don ya gane maganar ne ba ta son yi. A hankali ta ce mishi, “Nice”. “Kina son wani abu ne?” Ta xan yi shiru kafin ta daure ta ce mishi, “Wuta aka xauke ni kuma bana son duhu “. Cikin nutsuwa ya ce mata, “Eh, Aisha duhu ai ba shi da daxi”. “Ko za ka sa a kunna Jean?” Ya ce, “To, sai dai ruwan ya yi yawa bai kamata in fitar da shi a cikin ruwan ba, saboda kuna Jean ai kinga babba ne mu xan bari mu gani ko ruwan zai yi sauqi”. Ta yi shiru. “Ko kina tsoro ne?” Ta ce mishi, “Eh”. Ya yi kamar ya ce ta shigo wurinshi sai ya fasa, ya fito ya zo inda take ya kama hannunta ya ce, “Muje in rakaki wurinki”. Da hikima da lallami ta yarda suka hau gadonta tare suka kwanta, shima kuma ya yi haquri ya kawar da kai daga gareta, don ya fi son shiryawarsu maimakon kara tsoratata. Sai da aka kira sallar asuba ya miqe zai yi alwala ya mai da wutar gidan. Har wajen qarfe taran safiya ba ta sake ganin ya shigo wurinta ba, ba ta ga yana shirin tafiya aiki ba. Kalmomin Abu suka faxo mata, kullum ki gaishe shi, kullum ki yi mishi abinci mai daxi, kullum ki gyara mishi shimfixa. Don haka ta miqe ta nufi wurin nashi da nufin zuwa ta gaishe shi. A hankali ta tura qofar xakinshi tare da yin sallama, saboda ganin ba ta ganshi a falon ba. Ya amsa yana daga kwance a gadonshi, ta kai gwiwowinta qasa a yanayin girmamawa ta ce mishi, “Ina kwana Yaya?” Ya amsa “Lafiya lau Aisha, ya ya gidan ya kwana?” Ta ce mishi, “Lafiya, me kake so ayi maka na abin karyawa?” A hankali ya ce mata, “Huta kawai Aisha”. Ta xan kalle shi ta ce, “Ba ka da lafiya ne?” Ya zuba mata ido yana kallon ta tare da tambayar ta, “Me kika gani?” Cikin nutsuwa ta ce, “Na ganka a kwance bayan yau xin akwai aiki, kuma na ce me kake so in yi maka ka ce in huta”. Bai kawar da kanshi daga gare ta ba ya ce mata, “Bana cikin yanayin da zan ji daxin zuwa aikin yau, saboda na xan takura, in kuma abin da nake so za ki yi min ki zo kusa dani mana ki rage min damuwa ta”. Ta xan yi shiru kanta a sunkuye, a hankali sai ya ce mata, “Sai na ji kamar Abu ta yi ta yi miki magana a kan kar ki yi wasa da auren ki, na xauka ni da ke zamu yiwa nasihohin da ta yi mana biyayya Aisha”. Ba ta kalle shi ba balle ta yi mishi wata magana, sai dai hawayenta da suka soma zuba. Ya shure abin rufar nashi ya zo ya kama hannunta ya shigar da ita xakin. “Zo muje ki gaya min abin da ke saki yawan kuka. Nisa da gida da kika yi? Kina son ganin Gwaggonki ko?” Ta yi maza ta gyaxa kai nuna alamar, “Eh”. Yasa hannu ya share mata hawayen. “Ai na sani, na san kina ganin Gwaggonki nima kuma ba zan hanaki ko in qi kai ki wurinta ki ganta ba, illa iyaka dai kawai zan bari sai kin kwantar da hankalinki mun zauna lafiya tukunna, ko yau xin nan kika yarda muka fara zama lafiya, to ni kuma a shirye nake mu daidaita lokacin da zan kai ki ga Gwaggon naki”. Da irin waxannan kalaman na dabara ne da yawan nuna na fiki daxewa a duniya Mus’ab ya samu ya shawo kanta cikin ruwan sanyi, ta yarda ta miqa mishi al’amarinta ya samu ya yi yanda yake so da ita, ta kuma jurewa hakan. Wunin ran nan ko qofar gidanshi bai buxe ba sai da ya yi nufin tafiya sallar juma’a, ana idarwa kuma ya dawo gida. Haka washe gari asabar da kuma lahadi yana gida yana hutawarshi. “To Yaya yaushe zamu je wajen Gwaggo?” Sai ya yi maza ya soma lissafi. “To bari ko kwana talatin da tafiya Abu ta yi don kar a ganmu yanzu ayi zaton ko babu lafiya”. Ta ce mishi, “To”. Kwanaki talatin xin suna cika ya xauke ta ya nufi qasar Italy in da ya je ya yi hutun aikinshi na kusan watanni biyu, tafiyarshi ta farko tun bayan dawowarshi daga can inda yaje ya sadu da aminai, abokai da kuma tsofaffin malamanshi da aminanshi. A lokacin da suka dawo gida kuwa tunanin Saddiqa da tattalinta bai wuce na me za ta yi ko ya ya za ta yi ta kyautatawa mijinta ba. Watanni biyar sun cika bayan kawo Saddiqa da Abu ta yi har lokacin bai ce ga ranar zuwa gida ba, tamkar ya mance alqawarin da ya yiwa Abu na ba zai bari ta rinqa jin marmarinshi ba ta ganshi ba. Ita ma Saddiqa mafi yawancin lokaci ta kan tuna Gwaggon nata ne, ta ce kai Yaya yaushe ne za ka samu lokacin da zamu je gida ne? Ina fa marmarin ganin Gwaggona”. Ya yi tsaki ya ce, “Ai ayyuka ne bari dai mu gani daga nan zuwa qarshen watan nan. In ta ce to. To sai kuma wani jiqon in ta sake tunawa. Daga shi har ita sun zama tamkar basu ba, ko Liman da Mus’ab xin ya tasata a gaba ya kaita gaishe shi mamakin ganinta ya yi, ya cewa, Mus’ab xin yi qoqari ka kai wa iyayenku ita su ganta don su sanya maka albarka. Ya ce, “To malam”. Suna zaune a falonshi suna hira, sun gama karyawa Mus’ab ya kalle ta ya ce, “Ki gama aikinki da wuri ki shirya in anyi sallar magariba zamu je mu ga Dr. Usman”. To kawai ta ce saboda ya yi maganar ya fi a qirga, yau xin dai ya zartar da hukuncin tafiyar ne kawai. Da daddare Mus’ab da Saddiqa suna zaune gaban likita, Mus’ab ya gama yi mishi bayanin abin da ke tafe dasu. Gwaje-gwaje sosai ya yi musu, ya kuma umarcesu dasu kawo mishi wasu abubuwa na jikinsu. Bayan sunyi hakan ne ya xibar musu kwanaki uku ya ce su dawo don su ji sakamakon gwajin nasu. Sun dawo suna zaune gaban likitan wanda yake kallon takardun dake gabanshi cikin nazari kafin ya xan xago ya kalli Saddiqa ya ce mata, “Ko za ki xan jiramu a waje?” Mus’ab ya harzuqa da jin maganar tashi ya ce, “Matata ce fa, me za ka gaya min da ba za a faxa a gabanta ba?” Saddiqa ta miqe tsaye ta ce, “Babu komai Yay bari in je in jiraka a mota, in ka gama kawai sai ka sameni a can mu tafi”. Ya bita da kallo har sai da ta fita ta ja musu qofar kafin ya dawo da kallon shi wurin likita. “Me kake so ka gaya min likita wanda yasa ka korar min mata?” Likita ya ya kalle shi cikin nutsuwa ya ce, “Ba korarta na yi ba, bana yi maka sha’awar tashin hankali ne da ita, na san a yanda ka renita ta zama haka ba za ka so komai tsakaninka da ita ba illa zaman lafiya da kwanciyar hankali”. Gaban Mus’ab ya yi mummunan faxuwa, cikin sanyin jiki ya tambaye shi “Me ya faru likita?” Ya tsare shi da ido yana kallon shi tare da sauraron abin da zai gaya mishi. “Barasa da sigari sun riga sun yiwa kayan cikinka lahani, haka nan ka daxe kana xauke da ciwon sanyi da ake samu wurin matan da basu tsaya wuri xaya ba, saboda baka kula ka xauki matakin da ya dace a kanta ba har ta yi maka illa, ka kuma san ita wannan cutar tana cikin cututtukan dake hana maza haihuwa, don tana toshe jijiyar dake fitar da qwai zuwa mahaifar mace. To ga kuma wancan matsalar da na ce maka barasa da sigari sunyi maka, ban da wannan ita ma matarka mun same ta da ciwon, sai dai bai riga ya yi mata qarfi sosai ba, na kuma san zai yiwu a wurin ka ta samu”. Mus’ab ya ji tamkar a sama yake saboda tashin hankali, gaba xaya kunnuwanshi suka daina jin komai in ban da kalaman da likita ya furta mishi sune kawai suke ta nanata kansu. “Ka yi haquri Mus’ab kar ka xauki abin da tsanani sosai, akwai magungunan da zamu baka in ba suyi ba mu canza wasu, kai dai kar ka bari matarka ta san abin da kake ciki ba wani tabbas ne dasu ba. Kar ka kalli wannan xawainiyar da ka yi a kanta ka mai da ita matar zamani ta bijire maka ba komai bane, musamman ma da yake abin ya shafi haihuwa. Don haka in ta matsa tana so ta san abin da ake ciki ni zan iya ba da result xin da zai nuna matsalar a wurinta yake, don dai ka samu zaman lafiya a gidanka. A nan asibiti kuma ba za ta samu mai gaya mata komai ba”. Mus’ab ya miqe tsaye tare da faxin “Na gode likita”. Ya fita ba tare da ya saurari rakiyar da likitan yake yi mishi ba. Saddiqa tana zaune a qasa gaban Mus’ab, kuka take yi. Ya buxe ido a hankali cikin nutsuwa ya ce mata, “Yanzu nan baki yarda da abin da na gaya miki ba cewar ni lafiyata qalau bani da wata damuwa ba”. “Ya ya zan yi in yarda bayan ba haka na saba ganinka ba, ni idan na yi maka laifi ne baka son gaya min to ka yafe min”. Ya miqe zaune

Chapter 19 of 24