Saddiqa ke ciki, zan je in gani da kaina in bai yi min ba zan xauko ta. Saddiqa marainiya ce ba ta da kowa sai ni, nice uwarta nice kuma ubanta. Yaya Gixe ne ya cuce mu ni da ita, shine ya xauke ta ya baiwa mutumin da ya fi mu sanin ba zai riqeta ba, baqin ciki kawai zai cusa mata. To ba zan barshi ba, dama tunda na ga ina munanan mafarkai a kan ta na san…….”
Abu ta katse ta da cewa, “Babu wani mafarki kina dai son zuwa wurin xanki ne kawai, in kuma kika fito ma kika ce za ki je ganin Mus’abu wa zai hana ki”.
Gwaggo Habiba ta zuba mata ido cikin kaxuwa wasu sababbin hawaye suka zubo mata masu zafi saboda takaicin kalaman na Abu, sai dai babu yanda za ta yi.
Cikin nutsuwa ta ce, “Haba Inna, ni kuwa me zai sa ki gaya min haka? Kin sani sarai in ban da Saddiqa tana wurin nan babu abin da zai sa qafata ta taka gidan nan”.
Abu ta ce, “Oh’oh! Ni za ki kawowa wayo, in so kike a dubo miki Saddiqa ba wurinshi za ki ba, ba kya tunanin in je in gano miki in zo miki da wani sabon labarin”.
Ta miqe tana jan zanin ruhuwarta tana tafiya, fita gidan take nufin yi tana kuma qarasa zancenta, “Ba fa hanaki zuwa gidan nashi nake nufin yi ba, ai ba a raba xa da uwa”.
Takaici ya kama Gwaggo Habiba, can cikin maqogwaronta har wani xaci take ji saboda vacin rai, sai dai babu halin ta tanka.
“In kin je ki gai da Mus’abun”.
Ta faxi daidai tana fita.
Da daddare Gwaggo Habiba tana tare da mijinta Malam Abdallahi a gefen tabarmar da yake zaune yana cin abincin shi, yana kuma sauraron bayanin da take mishi na yanda suka yi da Abu.
Sai da ya ji ta yi shiru sai ya yi murmushi ya ce, “To ai sai ki haqura ki tura ta xin tunda ta ga za ta iya wannan wahalalliyar tafiyar”.
Gwaggo Habiba ta kalle shi cikin nutsuwa ta ce, “To amma Malam wane bayani Inna za ta zo da shi in dai a kan wannan yaron ne? Ka santa sarai halinshi na zahiri ma in za a faxa ranta vaci yake yi, ko yanzu ma kuma na fi zaton akwai abin da take tsoron kar a je a gani wanda yasa take faxanz uwan da na ce zan yi balle a ce ita ta zo ta faxa da kanta”.
Ya ce, “Eh, duk da hakan cikin biyu ne za ki zavi xaya, ko ita xin ta tafi ne ko kuma a haqura gaba xaya tunda ga irin kalaman da take furtawa”.
Gwaggo ta ce, “Ni kam gara in dangana in yi ta yi mata addu’a Ubangiji ya kuvutar min da ita daga dukkan sharri”.
Ya ce, “Eh, hakan ma yana da kyau”.
AJAKUTA
Mus’ab yana tsaye a falon cikin tashin hankali da fargabar rashin ganin Saddiqa a cikin gidan.
“Ke Zainab”.
Ya sake qwala mata kira da sake fitowa da gudu hawaye suna zuba a idonta
“Kin leqa nan maqwabta zuwa wajen su Abida ba ta nan?”
Ba ta iya amsawa ba saboda yanayin da ta ga Mus’ab a ciki, in ban da rawa babu abin da jikinta ke yi, ga shi kuma kusan awa xaya da rabi ne tunda suka nemi Saddiqa a gidan basu ganta ba cikin gida da cikin Ajakuta babu ita babu dalilinta.
“Kika ce kinga tana waya?”
Ta gyaxa kai nuna alamar eh, haka ne.
“Me kika ji tana faxa?”
Ya sake wata tambayar.
“Ban ji tana magana ba sauraro kawai na ji tana yi”.
Gabanshi ya sake faxuwa da ya gane wayarshi da Sarah ta saurara.
Anya Saddiqa tana garin nan ma kuwa?
Kai tsaye tambayar ta fito mishi daga cikin zuciyarshi. Kar dai gudu ta yi za ta koma Misau?
Bai jira jin amsar da zuciyar tashi za ta ba shi ba ya yi waje da gudu ya nufi cikin motarshi, sai da ya tabbatar ya xaure kanshi tamau da belt xin dake jikin motar sannan ya shiga tayar da ita, cikin zuciyarshi kuwa addu’o’I yake ta karantowa iri-iri na neman tsari da taimako wurin Ubangiji.
Mus’ab yana tafiya cikin matsanancin gudun da ba zai kwatantu ba, duk da kashedin da zuciyarshi ke yi mishi saboda yanda iska ke kaxa motar duk da mota ce mai nauyi.
Wayarshi ta yi qara a karo na uku, ya yi kamar ya sake yin buris da ita sai kuma ya yi tunanin to ko dai wani cikin masu taya shi neman ta ya ganta? Ya yi maza ya miqa hannu ya xauki wayar ya karata jikin kunnenshi.
“Hello!”
“Mutanen nan fa sun qi yarda su karvi cikiyar da muka kai musu, wai sai bayan awa ashirin da huxu da vacewar ta tukunna”.
Muryar Sani ce ta yi mishi wannan bayanin. Bai tanka ba ya mai da wayar mazauninta ya ci gaba da tuqinshi, cikin zuciyarshi kuwa mamakin hukumar ‘yan sanda yake yi wai basa karvar labarin vacewar mutumin da ya shekara goma sha takwas sai bayan awa ashirin da huxu da vacewar tashi. Ko mene ne dalilinsu na yin hakan? Oho!
Ya kwatanta yawan awa ashirin da huxu abin da za su iya yiwa Saddiqa sun isheta ta je har Misau ta zauna ta huta, ta ma kwana tana baiwa Gwaggonta labarin Mus’ab da abubuwan da ta gani a tare da shi.
In har Saddiqa ta samu nasarar isa gaban Gwaggo anya auren shi da ita zai xore? Tambayar da ta zo cikin ranshi kenan.
Tafiya mai tsanani ta awowi uku da mintoci arba’in kafin ya iso wata mararraba ta motocin da suka fito daga kudu suka nufi arewa, a nan ya yi parking cikin surquqin bishiyoyin da suka lulluve wurin, ya fito daga cikin motarshi riqe da kwalin sigarinshi a hannu da fankon ashana, cikin zuciyarshi yana tunanin a irin tafiyar da ya yi in dai Saddiqa motar haya za ta shiga kuma direban mai hankali ne, to ya wuto shi a baya, yana lissafi tare da raba awowi da mintocin tsakanin abin da ta yi kafin isarta tasha da shigar ta mota, da sallamar direba, har kawo isowarsu wannan mararrabar da ya ja ya tsaya.
To in kuma vuya ta yi a cikin garin fa?
Wata zuciyar ta aiko mishi da wata tambayar. Wurin wa? Ya sake tambayar kanshi. Nan da nan ya kori wannan tunanin.
A sanin da ya yiwa Saddiqa gida kawai za ta dosa ba za ta tsaya neman mavoya cikin mutanen da ba ta sani ba.
Da wannan tunanin ya isa wurin ‘yan sandan dake lura da wajen waxanda suka tsare hanya suna ta faman karvar naira ashirin wurin qananan motoci, hamsin ko xari wurin manya, gwargwadon dai irin lodin da ka zo da shi.
Barka da aiki Yallavai”.
Mus’ab ne yake isar da gaisuwarshi wajen xan sandan dake zaune kan wata mota a gindin wata bishiya mai yawan ganye da inuwa, wanda shi ke shugabantar wannan Road Block xin.
“Yauwa barka dai”.
Ya amsawa Mus’ab gaisuwar tashi bayan ya gamsu da kallon da ya yi mishi.
“In ce ko lafiya?”
Ya tambaye shi.
Mus’ab ya sanya hannu cikin aljihunshi ya zaro hoton Saddiqa da ya saka a ciki daidai yana cewa, “Lafiyar ba ta da yawa yallavai”.
Ya miqa mishi hoton yana cewa, “Matata ce ta baro gida ina kyautata zaton za ta biyo ta hanyar nan in har ba ta riga ta wuce ba, taimako nake so ka yi min na in tsaya tare daku”.
Ya yi mishi bayanin abin da yake so suyi mishi.
Xan sandan ya zubawa hoton ido ba tare da ya ce komai ba, tamkar dai wani nazari yake yi. Bai barshi ya kai qarshen tunanin nashi ba ya zaro bandir xin xari biyar-biyar ya jefa kan kujerar motar yana cewa, “Wannan a baiwa yara su sha kunun zaqi”.
“Ai ba sai ka yi wannan wahalar ba don za ayi maka xan wannan taimakon, su mata waxansu irin mutane ne, al’amarinsu har mamaki yake bani, ga shi dai duk wahalar da muke yi a rayuwarmu mafi yawancinta a kansu muke yi, amma basa gani balle su yaba mana, sun fi so kowane lokaci su rinqa tayar mana da hankali. Ni wani lokacin idan abin takaicinsu ya ishe ni sai in ji tamkar a raba mana wurin zama a ce ga garin mata ga na maza, su yi harkarsu muma muyi namu kowa ya yi harkar gabanshi ba ruwan wani da wani ko kuwa?”
Mus’ab ya yi murmushi daidai lokacin da ya gama fitar da hayaqin sigarinshi daga bakinshi, ya ce, “To amma yallavai da anyi hakan anya duniyar za ta yi mana daxi kuwa? Ai ina ganin da bamu yi jarumtakar da muke yin ba ma”.
Yallavai ya yi tsaki mai qarfi ya ce, “Ai kuma tsiyar kenan”.
Ya diro daga kan motar ya nufi cikin motarshi kamar zai ajiye sandar hannunshi, nan kuwa yana nufin sanin abin da Mus’ab ya ajiye mishi ne. yasa hannu ya xauka ya adanasu kafin ya fito, ya kalli Mus’ab cikin yanayin murmushi ya ce, “Amma wannan kunun zaqin ba zai yi musu yawa ba kuwa?’
“A’a, haba Yallavai wannan wuni da kuke yi a rana”.
“To an gode, bari in haura can wajan nasu don in ga irin aikin da suke yi”.
“To Yallavai”.
Mus’ab ya yi godiya, ya koma inda ya voye motarshi a surquqi ya zauna yana hangen abin da su Yallavai suke yi a inda yake voye.
“Park well!”
Tun Yallavai bai qarasa isa ba ya shiga ba da umarni, nan da nan motoci suka yi ta yin parking a gefen hanya.
Qananan ‘yan sanda suka shiga sosai leqa motoci, har duba but saboda umarnin Yallavai. Shi kuma hankalinshi yana wajen fasinjojin motocin ko zai dace da ganin yarinyar da hotonta ke sunne cikin aljihun wandonshi.
Ta kowanne vangare motoci sunyi dogon layi, ga matsanancin bincike cikin zafin rana Yallavai sai xigar gumi yake yi amma babu alamar zai gaji.
Mus’ab yana zaune cikin motarshi cikin fargaba da zaquwa daxewar lokaci ne ya dame shi, anya basu riga sun wuce ba ma kuwa? Ya tambayi kanshi.
Yawan harbawar da zuciyarshi ke yi ya hana shi ci gaba da zaman cikin motar, ya fito ya nufi bakin hanyar shima.
“Yallavai na ce anya basu riga sun wuce ba kuwa?”
Ya yi tambayar a yanayi na damuwa. Ya zubawa agogonshi ido tare da nazarin daxewar da suka yi a wurin suna cajin motocin.
Ya xago ya kalli Mus’ab ya ce, “Ina ganin har yanzu ba zamu fidda rai ba, ai ka san ba daga gida kai tsaye za ta kamo hanya ba, sai ta je tasha tukunna. Don haka ka qara haquri a wurinka don ba zamu so tsayuwarka a cikin mu ba”.
Mus’ab ya sake kunna sigarinshi ya sanya a baki, kafin ya sake gangarawa wurin zaman shi. A daidai wannan lokacin wata mota ta iso wajen peogout qirar station wagoan, ta bi bayan sauran motocin dake tsaitsaye.
Yallavai ya nufe ta da sauri zuciyarshi tana dakan uku-uku, anya ba ita ba ce wancan? Zuciyarshi ke tambayar shi.
Cikin hikima ya qara kallon hoton don ya qara tabbatarwa. Ita ce. Zuciyar tashi ta qara tabbatarwa. Yasa hannu ya buxe qofar motar.
“Fito nan”.
Ya nuna ta da sandar dake hannunshi.
Mutumin dake jikin qofar motar wanda sai ya fita kafin ta samu damar fitowa, wanda tun shigar shi motar hankalinshi yake kanta, iyaka dai bai ga fuskar yi mata magana ba, don haka ya mai da nutsuwarshi kan mujallarshi yana sauraron zuwan lokacin da zai dace da yi mata maganar.
Ya xago kanshi ya kalle shi ya ce, “Ta fito ta yi maka me?”
Gaba xaya jama’ar motar suka zubowa Yallavai ido.
“Common fito nan”.
Ya ba da umarni mai zafi don tuna musu ko shi waye?
Mutumin dake varin nashi ya fito ya tsaya gabanshi suna kallon juna.
“Wai kai waye da kake ja da hukuma? Ka kuwa san matsayin wannan abin da kake yi?”
“Ban sani ba Yallavai sai ka gaya min”.
Ya yi mishi bayani a yanayi na gatse.
Yallavai ya rabu da shi ya mai da hankali wajen baiwa Saddiqa umarnin fitowa”.
Mai mujallar ya kalle shi ya ce, “Haka kawai za ta fito ba tare da ka yi mana bayanin dalilin fitowar tata ba? Me yasa baka ce kowa ya fito ba sai ita wannan yarinyar?”
“Ita wannan da kake gani ta gudo ne daga gidan mijintaa, shi yasa zan fito da ita don in mayarwa mijinta da ita”.
Jin wannan bayani na Yallavai yasa wurin ya kaure gaba xaya fasinjojin cikin motar, waxanda mafi yawancinsu maza ne suka firfito suka kewaye Yallavai, daga masu gyaran zanzaro sai masu naxe hannun riga tare da faxin, “Wannan ai shine zance, ka tsare mu cikin jeji ka fitar da tsaleliyar budurwa a cikinmu ka ce wai za ka mayarwa mijinta da ita. To a wane matsayi, waliyi ko wakili?”
Hargowa ta jawo hankalin sauran jama’a suma suka firfito, masu isowa ma kowa ya zo sai ya yi parking ya fito don ganin abin da ke faruwa, duk wanda ya iso sai ya buqaci sanin me ke faruwa? Tun ana bayani na gaskiya har aka koma qara gishiri a kai.
Mus’ab ya iso wurin don ya kasa fahimtar abin da ke faruwa, cincirindon jama’a yasa ko motar ba a gani daga nesa, da qyar ya kutsa kai ya smau ya isa wurin da abin ke faruwa.
Yallavai wanda tuni ya gundura da lamarin ya shiga fargaba saboda cincirindon mutanen dake kewaye da shi waxanda suka zamo mishi barazana, don ya san kes suke jira su afka mishi, don sun riga sun tunzura.
Yana ganin isowar Mus’ab ya yi maza ya ce, “Yauwa ga ma mijinta nan ya zo da kanshi”.
Gaba xaya wuri ya kaure da hayaniya, “Haxin baki ne da shi suka haxa baki”. Wasu har suna cewa, “Za ma ku sani, mu nan da kuke gani ba za a kawo mana wannan iya shegen ba”.
Yallavai ya yi maza ya ciro hoton dake aljihunshi zai nuna musu don ya samu ya wanke kanshi daga zargin da jama’a ke mishi.
Wani mara kunya a ciki ya yi maza ya fige hoton ya raba shi biyu ya jefa shi a baki ya tauna ya haxiye yana cewa, “Hoto kuma har wata shaida ce”.
Mus’ab ya yi shiru yana kallo cikin nazarin al’amarin, kafin ya zaro karan sigarinshi ya sanya a baki ya kunna yana zuqa a hankali yana kallon Saddiqa dake amsa tambayoyin mai mujallar.
“Kin san wannan da ya ce wai shi mijinki ne?”
Ta girgiza kai nuna alamar ba ta san shi ba, ta kuma qara da cewa, “A’a”.
“Za ki iya tunawa kin tava ganin shi ko da sau xaya ne a rayuwarki?”
Ta tave baki ta ce, “A’a”.
Mus’ab ya gama sauraron ta zuciyarshi cike da mamaki, bai ce mata komai ba sigarinshi kawai yake sha cikin nutsuwa. Ya miqa hannu ya jawo Saddiqa daga cikin motar ba tare da wani ya lura da lokacin da ya yi hakan ba, sai kawai ganinta aka yi a tsaye yana riqe da ita ya mayar da qofar motar ya rufe.
“Ba fa za ka je ko ina da yarinyar nan ba”.
In ji mai mujallah.
“Kai waye da za ka hanani yin hakan?”
Mus’ab ya buqaci sani. Yasa hannu a cikin aljihun gaban rigarshi ya zaro kati (conplimentry card) xinshi ya miqawa Mus’ab ya karva ya gani.
Lauya ne mai zaman kanshi, ya saki katin ya faxi a qasa sannan ya yi mishi lalataccen kallo tare da tambayarshi “To sai me?”
Kallon da tambayar suka tunzura shi ya ce, “Sai ka san ba za ka ko ina da ita ba tunda ko matarka ce sai ina tana son zama da kai, don haka ni zan tafi da ita in kaita gaban iyayenta, in kana sonta sai ka bita can ka same ta ku sasanta, amma baka tsare mu a jeji ka cireta a cikin mota ba bayan mun san mugaye sun yi yawa”.
“Kana da wata shaida ne Yallavai da za ta nuna ita xin iyalinka ce?”
Wani daga cikin fasinjojin ne ya yi tambayar.
Mus’ab ya kalle shi a nutse cikin kwanciyar hankali ya ce mishi, “Babu”.
“To tunda shi da kanshi ya ce babu shiga mota mu tafi kin ji, ya tsai damu yana vata mana lokaci”.
Mai mujallah ne yake wannan bayanin.
“Wasu mutanen basu da hankali, mace ba ta son su sai suje su baiwa iyayenta kuxi su aura musu ita a kan dole”.
Saddiqa ta yunqura za ta shiga motar Mus’ab yasa hannu ya kama hannunta ya riqe.
“Da kin sallame su sun tafi kar ki yi ta vata musu lokaci”.
Ya zuba mata ido yana kallon cikin idonta.
Ita kuma ta fara kuka tana faxin “Ka sake ni, ka sakar min hannuna ban sanka ba”.
Ta shiga kici-kici da qoqarin qwatar kanta daga gare shi.
“Malam in ma matarka ce ba ta sonka”.
Mai mujallah yasa baki, ya kuma yi nufin taimakon Saddiqa ta qwaci kanta wurin Mus’ab.
Mus’ab ya yi maza ya saki hannun Saddiqa dake hannunshi, cikin zafin nama ya taqarqare ya danqarawa mutumin naushi mai qarfi a muqamuqi, abin da ya yi sanadin faxawarshi kan mutanen dake tsaitsaye bayanshi suka tare shi daga kaiwa qasa. Ya taso fuskarshi cike da mamaki.
“Ni ka buga? Za ka yi dana sani, za ka gane ku…..”
Kafin ya qarasa faxin abin da yake so ya faxan Mus’ab ya yunqura ya sake kirva mishi wani wawan naushi. Wuri ya kaure da hargowa, jama’a suka kasu kashi biyu dake qoqarin shiga tsakanin daben dake shirin aukuwa tsakanin Mus’ab da mai mujallah saboda tasowar da ya yi zai rama dukan da ya yi mishin.
Haquri suke bayarwa a sasanta al’amarin cikin ruwan sanyi ba tare da anyi tashin hankali ba.
Mus’ab yana riqe da karan sigarinshi da yake qoqarin kunnawa yana kuma sauraron maganganun da kowa yake yi, ya yin da hankalinshi da nutsuwarshi suke kan duk wani yunquri na Saddiqa.
Wani dattijo ya iso wurin yana faxin, “Haba Yallavai ya ya kuna wuri kai da yaranka amma kuma rikici yake nema ya tashi a gabanku kana kallo?”
Yallavai ya yi mishi bayani kan yanda Mus’ab ya zo wurin ya nemi taimakon shi da duk abin da ya faru, don haka shi a ganin shi yanzu tunda abin ya zama haka, to sai a xunguma ayi can gaba inda za a samu hukumar ‘yan sanda a awurin.
Mus’ab ya ce, “Shi daga inda yake tsaye ba zai qara taku xaya zuwa gaba ba tunda ya riga ya ga abin da ya fito nema, sai dai ko a xunguma a koma gari na baya tunda shima ya wuto ofishin ‘yan sandan a can”.
“Dubi nan yaro”.
In ji dattijon. Mus’ab ya mai da kallon shi gare shi da girmamawa.
“Gaya min gaskiya ka ga tsayawa nan ta yi yawa, inda muka dosa nan ba nan kusa bane arewa fa zamu. Me ke tsakaninka da wannan yarinyar?”
Mus’ab ya kalle shi cikin girmamawa ya ce, “Baba qanwata ce, kakanninmu xaya, mahaifinta wan mahaifiyata ne a wurinshi na girma, shine kuma ya bani ita matata ce”.
“Kai ku tafi ku barshi da matarshi kowa ya shiga mota ya nufi inda za shi”.
In ji dattijon. Mutanen da tsayuwar ta riga ta gundiresu suka nufi motocinsu suna tsaki tare da faxin “MATA! Hum sai a barsu kawai”.
Mai mujallah kuwa tsayawa ya yi ya ce, “To ai ita yarinyar ba ta gaskata maganar ba balle mu yarda da gaskiyarshi”.
Dattijo ya kalli Saddiqa ya ce, “Yarinya ba ki yi kama da mutuniyar banza ba, abin da ya faxa gaskiya ne ko akwai gyara a ciki?”
Ta ce, “Gaskiya ne”.
Ya kalli mai mujallah ya ce, “To kai ka ji”.
Nan da nan jama’a suka watse aka bar Saddiqa da Mus’ab suna tsaye cirko-cirko, hatta Yallavai ya koma wurin sauran ‘yan sanda sun koma kan aikinsu.
Mus’ab ya kalli Saddiqa cikin murmushi ya ce, “To ya ya kenan? Waxanda kika sani sun tafi sun barki da wanda baki sani ba, ya ya kenan? Za mu tafi gida ne ko kuwa?”
Ta yi kamar ba ta ji ba, ta soma kuka. Ya kamo hannunta ya jata zuwa inda motarshi take, ya buxe ya sanya ta a cikin wurin mai zaman banza ya rufe, sannan ya juya ya koma nashi wurin ya shiga ya zauna.
Sai da ya kunna sigarinshi ya sanya a baki kafin ya juya kan motar ta nufi inda ya fito, bayan ya yi sallama da su yallavai.
Sun fara tafiya ko wani nisa basu yi ba Saddiqa ta soma kwara amai, nan take ya tuna kalaman Innarshi.
“Saddiqa da kake gani warin sigari ma sa ta amai yake yi balle a ce ta ji warin barasa a jikin mijinta”.
Ya yi maza ya wurgar da sigarin tare da sauke gilasan motar saboda samun tsarkakakkiyar iska.
“Ki yi haquri Aisha na mance bakya son hayaqin sigari”.
Ba ta yi magana ba in ban da kukan da take yi, duk da tsayuwar da ya yi don ta gyara jikinta ta kuma xan huta.
Mus’ab ya biyo Saddiqa xakinta da shigarsu gidan.
“Ina kika samu kuxin motar da kika biyasu?”
Ta yi shiru ta qi yin magana.
“Ni dai na san tun zuwanki wurina
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 24