Share this page
xakinta jikinta sai rawa yake yi, Mus’ab ya shigo sanye da jallabiya mai ruwan shuxi, silifas xin wanka ne a qafarshi, qamshinshi na kullum yana tare da shi. Ya kama hannayenta duka biyu ya riqe a cikin nashi, ya sunkuyo da idanuwanshi cikin nata da tuni suka fara zubar da hawaye. “Ai nima zan bika, zan je ayi komai a kan idona ina gani”. A hankali ya ce mata, “A’a, Aisha yi haquri ki yi zaman ki a gida, ga ‘yan’uwanki mata nan sun zo za su tayaki zaman gidan zai fi miki sauqi da nutsuwa”. Za ta yi magana ya yi maza ya ce mata, “Shhhhhh!” Kan ta yi wani abu ya yi hanzarin sanya bakinshi a nata, kusan minti guda kafin ya saketa. “Kar ki yi min musu, addu’a kawai za ki yi min”. “To Yaya”. Cikin rawar murya ta faxi hakan. Bai jira ya ji sauran maganar ba ya yi maza ya fita daga xakin, ya samu su Idris da Sani a waje da suka zo don suyi mishi rakiya. Saddiqa ta nemi wuri ta zauna a qasa tana ta faman kuka Abida tana rarrashinta. “Ki yi haquri Aisha, ki yi ta addu’a kawai Ubangiji dai yasa ayi a sa’a”. Ta xago ta kalleta cikin hawaye ta ce, “Iyayenmu fa basu san da aikin ba, na yi na yi mu gaya musu ya qi, wai yana tsoron kar su hanashi gara in an yi kawai su ji”. Abida ta jinjina lamarin, nan take kuma sai ta ba ta shawara. “To yanzu tunda ya riga ya tafi ai sai ki gaya musu su sani, don kuwa ai yana buqatar addu’arsu”. Ta yi maza ta miqe ta xauko wayarta, lambobin Gwaggonta ta danna, tana jin muryarta ta soma kuka. “A’a, me ya sameki Saddiqa ba dai wani abin ne ya faru tsakaninki da mijin naki ba ko?” Saddiqa ta ce, “Eh, Gwaggo”. Gwaggo ta yi maza ta ce, “Yau to ai yanzu muka gama magana da shi ya kirani muka gaisa, mun kuma xan jima muna magana ban ji alamar damuwa a tare da shi ba”. Cikin nutsuwa Saddiqa ta tambayeta ya gaya miki daga ina ya kira ki Gwaggo? Da sauri ta ce mata, “A’a, bai gaya min ba, wani abu ya faru ne?” Ta yi tambayar a yanayi na nuna damuwa. “A’a, Gwaggo babu abin da ya faru, amma shi yana asibiti wai za a yi mishi tiyata”. Da sauri ta tambaya, “Tiyata? Ba shi da lafiya ne?” Tana share majina tana maganar, “Lafiyarshi qalau a kan dai maganar nan ne, na yi na yi ya qi ya bari, na kuma ce ya gaya muku wai ba zai faxar muku da gaba ba, bayan haka kuma yana tsoron kar ku hana”. Shiru Gwaggo ta yi na wani lokaci alamar jikinta ya yi sanyi, a hankali cikin nutsuwa Saddiqa ta jita tana cewa, “To Ubangiji yasa ayi mishi aikin a sa’a”. Ta ce, “Amin”. Tana ajiye wayar kiran Mus’ab ya shigo. “Albishirinki Aisha”. Ta yi maza ta ce mishi, “Goro”. Yana murna ya ce mata, “Yau hira sosai muka yi ni da Inna da na kira ta”. Ta ce, “Kai Yaya Mus’ab, wannan ne abin albishir xin, ni ina ce ma za ka ce min an fasa yin tiyatar ne”. A hankali ya ce, “A’a, Aisha ai likitocin da za suyi aikin ma sun riga sun iso tun xazu, Dr. Usman ya gaya min cewar shi da wasu likitoci uku ne za suyi aikin. Kin san wani abu?” Ta yi maza ta ce mishi, “A’a, sai ka faxa”. Ya ce, “To zan shiga tiyatar ne hankalina a kwance bana tsoro ba kuma na fargaba, na kuma yarda cewar duk wani abin da ya faru ko zai faru, to daga Ubangiji ne, na roqe shi ya yafe min zunuban da na yi ta aikatawa waxanda suka zama sanadin da na cutar da lafiyata. Ke kuma na gode miki Aisha, na zauna dake zama mai daxi, kowane lokaci a cikin tattalina da kyautata min kike, kin yi komai don ki faranta min. Mafi alherin al’amarinki kuma shine, kin zama sanadi na daidaituwar tsakanina da mahaifiyata, in ban fito daga wannan tiya…..” Ta yi maza ta saki wayar a qasa saboda firgitar da ta yi tare da faxin “Na shiga uku!” Nan take kuma ta soma kuka. Da qyar ta iya yin shiru saboda rarrashi da kalaman qarfafa gwiwa da su Abida suka yi ta yi mata. “Gaskiya ba zan iya zaman nan ba gara min kawai muje asibitin”. Abida ta ba ta haquri. Jimawa can ta sake cewa, “Nifa gara min kawai in tafi don ban ga amfanin zaman da nake yi a nan ba”. Tasa hannu ta kira layin Mus’ab don ta gaya mishi ya barta kawai ta zo asibitin don ta ganshi. Sani ne ya amsa. “Hello! Aisha akwai wani abu ne?’ A hankali ta tambaye shi “Yaya fa?” Ya ce, “Ai tun qarfe takwas da rabi suka shiga dashi, dama shine mutum na biyu a tiyatar da za suyi yau”. Cikin Saddiqa ya ba da sautin qulululuuu! A lokacin da idanuwanta suka kai kan agogon dake wurin, qarfe goma sha xaya har da kwata, kusan awowi uku kenan da shigarwar da aka yi mishi. Ko a wane hali yake ciki yanzu? Oho! Ta yi maza ta ajiye wayar ta nufi banxaki saboda kaxawar da cikinta ya yi. Wunin ranar zirga-zirgar da ta yi ta yi kenan. Wajen azahar ta isa asibitin bayan ta riga ta yi sallarta a gida. A hankali ta tura qofa ta shiga xakin da aka nuna mata cewear shine nashin inda aka bashi, jallabiyar da ya baro gida da ita ne a ajiye a kan gadon. Ta miqa hannu ta xauka ta ninke ta sanya cikin jakar dake hannunta, ta ajiye jakar a kan gadon ta nufi inda ta hango Sani da Idris a tsaye. Tana isa wurin ta gane a kusa da xakin tiyata suke tsaye. Su dukansu biyun babu wani annuri a tare dasu, gaba xayansu idanuwansu sunyi zuru-zuru, bakunansu sun bushe. “Sannu Aisha”. Idris ne ya yi mata gaisuwar a yanayi na qarfin hali. Ta yi nufin wucewa zuwa inda ta hango qofar da aka rubuta Theater room a jiki, da sauri suka ce mata, “Ai ba a zuwa nan, iyakar wurin tsayuwar kenan inda muke xin nan, ki dawo kawai ki yi haquri ko kuma ki koma can xakin ki samu su Abida in an fito da shi ai nan xin ne dai za a kawo shi”. Ba ta yi magana ba kuka kawai take ta yi. Dr. Usman ya zo wucewa tana kallon shi yana magana da su Idris ba ta iya qarawa ta ji abin da suke faxa ba, tana dai kallon fuskokinsu zuciyarta kuma tana raya mata, ta gaji da kallon nasu ta yi qoqarin matsawa kusa dasu don ta ji me yake gaya musu haka wanda bayanin ya qi qarewa. “Yanzu dai sai mu qara haquri mu haxa da addu’a”. Qarshen maganar likita da ta ji kenan. “Me ya faru? Me ake ciki na ji yana cewa ayi haquri?” Ta yi musu tambayar a firgice saboda ba ta same shi ba ya riga ya wuce. Tun kafin su san me za su ce mata ta fara kuka. Da sauri Idris ya soma yi mata bayanin “Ba fa wani abu bane mai tsanani al’amari ne da yake faruwa da mutane da yawa, kin san kowa da yanda qarfin jininshi yake, an gama aikin sai dai bai dawo sosai ba ta yanda za su iya fito da shi”. Yana nan kenan tsakanin akwai da babu. Zuciyarta ta raya mata. Nan take jiri ya xebeta ta tafi za ta faxi, da sauri wata mace dake wucewa ta bayanta tasa hannu ta tare ta, su Abida suka yi maza suka kama ta aka kaita xakin aka kwantar da ita. “Ki fa kwantar da hankalinki kar kuma shi a fito da shi ke kuma kin samu matsala”. Kukanta kawai take yi ba ta ko kallon su balle ta amsa. Awa xaya baya aka fito da Mus’ab. “Gareka nake ya Ubangiji, gareka nake neman taimako”. Abin da yake ta nanatawa kenan. Gaba xaya ana tsaitsaye a kanshi cikin sauraro. An fito daga sallar magariba kenan sai ga Kawu Gixe da Abu sun iso asibitin, nan da nan Saddiqa ta xan samu nutsuwa a tare da ita. “Iko sai mai shi, haka al’amarin yake? To Ubangiji ya ta da kafaxarshi”. Gaba xaya aka amsa “Amin”. Kalaman Abu ne wannan bayan ta amsa sannu da zuwa da gaisuwar da aka yi ta yi mata. “To a nuna min inda zan yi sallah”. Saddiqa ta wuce za ta nuna mata, ta tarar tuni har Kawu Gixe ya idar. Ta tsuguna a gefe tana gaishe shi. “Ya ya aka yi aka yi irin wannan aiki haka baku sanar da gida ba?” Ba ta iya ce mishi komai ba in ban da kukan da take yi, saboda ta riga ta gama tsorata da yanayin da aka fito da shi a ciki. Har suka bar asibitin ran nan bai wani dawo cikin hayyacinshi ba, ita kam ta so a ce an barta ta kwana a wurinshi Abu ce ta ce gara su tafi wai in sun zauna me za suyi mishi bayan ga likitoci suna ta kaiwa da kawowa, ga kuma Kawu Gixe da Sani suma a nan za su kwana? Sun dawo gida Saddiqa sai bin Abu da kallo take yi, zuciyarta tana raya mata duk halin da Mus’ab ke ciki hankalinta a kwance yake, da kanta ta xebo abinci ta zauna ta ci ta xora da ‘ya’yan itace, ta yi wanka ta hau gado ta yi kwanciyar ta tana tambayar Saddiqa,. To don kin qi ci kin qi sha sai me? Ina ce duk iya shegenku ne ya jawo hakan? Da kin hanashi ai da bai yi ba. Saddiqa ta zuba mata ido tana kallon ta cikin matsanancin takaici, ta ma rasa me za ta ce mata. Dare ya yi nisa sanda ta farka ta duba agogon wayarta uku da rabi ne na dare, ta shafa inda Abu ke kwance ba ta nan, ta tashi ta tura qofar banxaki a hankali don ta gani, nan ma ba ta nan. Ta fito falo ba ta ganta ba. Har ta zuwa za ta koma xaki sai ta tura qofar xaya xakin, Abu tana ciki a zaune kan sallaryarta hannayenta duka biyu a xage zuwa sama, kuka take yi hawaye sai gudu suke yi a fuskarta. “Ya Ubangiji, wannan yaro Mus’abu….” Abin da kawai Saddiqa ta iya ji kenan. A hankali ta mai da qofar ta rufe ta nufi xaki ta je ta kama tata harkar. Suna idar da sallar asuba suka isa asibitin, har lokacin Mus’ab yana kwance a rigingine kamar yanda suka barshi, bambancin kawai shine a yanzu yana furta kalmomi da wanda ke kusa da shi yake iya ji. “Cikina, cikina, a san min ruwa in sha”. Saddiqa ta kalli mahaifinta ta ce, “Baba wai zai sha ruwa”. Kawu Gixe bai kulata ba sai Sani ne ya yi mata bayani, “Sun ce kar a ba shi komai”. Tausayin halin da yake ciki yasa Saddiqa ta soma zubar da hawaye. Da sauri Kawu Gixen ya ce mata, “Ke, kar fa ki kawo mana iya shege a nan? Kuka? Ba ki san za a yi hakan bane da kika ingizashi yaje ya yi? Wannan fitina da me ta yi kama? Dole ne sai kowa ya haihu? Waxanda basu haihu ba basa rayuwa ne? Yanzu babu bayin Allah mutanen kirki da su basu haihun ba?” Abu ta tave baki ta ce, “Uhm! Nima dai abin da na ce mata kenan”. Sani ya yi maza ya ce, “A’a, Kawu Aisha kuwa babu yanda ba ta yi da shi ba shi ya qi”. Da sauri Kawu Gixe ya ce, “To me yasa ba ta faxa ba ta ja bakinta ta yi shiru?” Cikin nutsuwa Sani ya ce, “Kawu ina ganin tuna an riga anyi sai ayi addu’a kawai ayi dace, ita Aisha kam Kawu kowa ya ganta ai ya san ta shiga wani al’amari, tunda ai ko shekaran jiya gidansu ba haka na ganta ba, daga jiya zuwa yau ne fa ta yi wannan zabgewar”. Kwanan Mus’ab uku kafin ya dawo cikin hayyacinshi sosai ya san abin da yake ciki da waxanda suke tare da shi. Kowa sai murna yake, yana fara samun sauqi Abu ta yi xib! Ba ta ko kallon inda yake kwance, ko ya yi qarfin hali ya yi mata magana ba ta wani kulawa balle ta amsa. Saddiqa ta kalle shi ta ce, “To kai ka yi haquri mana ka yi shiru dole ne sai ka kula Abu?” Abu ta galla musu harara dukansu biyun, ta ce, “To ni don ba a kulani ba sai me? Ni ai bake ba ce ya dena kulani mana. Fitinannun mutane masu neman fitinar tsiya, ana zaune lafiya ku tada mutane a tsaye”. A hankali ya buxa baki ya ce, “Ki yi haquri Abu, Aisha ba ta da wani laifi nine na hanata gaya muku, in ta bi umarnina kuma ai ba laifi ta yi ba”. “To amma kai me yasa za ka yiwa kanka irin wannan abin, kai baka san haquri ba?” Ya xan yi murmushi ya ce, “Zuciyata ce Abu ta qi ta yi min daxi, babu abin da take so irin ta ga Aisha da ciki, ko ganin mace mai juna biyu na yi sai in ji inda a jikin Aisha yake da ya ya zan ganta ta yi?” Ta kawar da kai tare da tsaki ta wuce ta yi tafiyarta ta barsu su biyu. Ya miqa hannu ya yafito Saddiqa ta matso kusa da shi, a hankali ya buxa baki ya ce mata. “Ki yi haquri Aisha, mun sha wuya amma kwanan nan in muna raye da yardar Ubangiji buqatarmu za ta biya, zan ganki kema kina tura cikinki kamar yanda nake ganinshi wurin matan mutane”. Saddiqa ta yi murmushi ta ce, “Amma dai kuwa kafin ayi hakan Yaya ai kuwa dai kam an sha wuya”. Ya ce, “Eh, amma ai babu komai Aisha, in dai har buqata ta biya to ai kuma duk wata wahala tarihi ce”. Ta ce, “Haka ne Yaya”. An sallamo Mus’ab ya dawo gida a dal8ilin sauqin da ya smau. Kawu Gixe da Abu kuma sun koma gida Misau. SHEKARU BIYAR BAYAN YIWA MUS’AB TIYATA Saddiqa da mijinta suna zaune lafiya cikin kwanciyar hankali da nunawa juna qauna mai yawa, sai dai har yanzu matsalar gidan ba ta kau ba, buqata kuma ba ta biya ba, haihuwa da ake neman ba ta samu ba. Bayan tiyatar farko da aka yi mishi, Mus’ab ya sake komawa wata tiyatar nan ma ya tsira da qyar, ita ma dai anyita ne a dalilin jijiya ta toshe, wato dai lalurar farkon ce ta sake dawowa. Har yanzu kuwa babu wata alama da ta nuna an samu nasara, domin cikin shekaru bakwai xin aurensu ba a tava ko da vari ne a gidan nashi ba, sai dai al’ada ta xuake, in anyi bincike a ce wani ciwo ne yake neman tava mahaifa. Suna cikin rumfa a harabar gidan bayan Mus’ab xin ya dawo daga gudun motsa jiki suna tattaunawa. Ya miqa hannu ya xauki inibin da ya tarar tana ci a tiren silba yana taunawa a hankali. Saddiqa ta zuba mishi ido cikin nutsuwa saboda ta gane akwai abin da yake son gaya mata. “Na ga kamar magana za ka yi?” Ya xan yi murmushin qarfin hali tare da faxin, “Hankalinki nake so ki bani”. Ta yi maza ta ce, “Dama a wurinka yake”. Ya ce, “To, kin gane ko?” Ta ce, “Uhm! Ina jinka”. Ya yi ajiyar zuciya mai qarfi ya ce, “Yanzu ke Aisha kina ganin zamanmu haka a gidan babu qaruwa ya yi dai-dai?” Ta ce, “Kamar ya ya?” Ya ce, “Babu haihuwa mana, ke kin ce ba ki yarda a ce za a sake yi min wani aikin ba, a gabanki ne kuma likita ya tabbatar mana da cewar ciwon nan ya sake dawowa, amma in anyi saurin cire shi ba zai zamo mai tsanani sosai ba. To ina ce gara kawai in je ayi aikin tun bai qara yin qarfi ba?” Ta zuba mishi ido tana kallon shi a wani yanayi na rashin sanin abin yi, da qyar ta iya buxa baki ta ce mishi, “Ashe maganar sake yin aikin nan bai qare ba?” Ya gyara zama cikin sakin fuska ya ce, “Ba wai bai qare bane, so nake mu fahimci juna ni dake Aisha, nima ba son aikin nan nake yi ba, to amma ya ya zan yi?” Ta zuba mishi ido kamar ta yi magana, sai kuma ta fasa. Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Ina zuwa”. Da sauri ta miqe ta shiga gida tamkar mai xauko wani abu ta dawo. Ya zauna nan wajen minti sha biyar bai ga ta dawo ba, ya miqe ya bi ta cikin gida su qarasa maganar. Yana shiga falonta ya tarar da ‘yar guntuwar takarda ajiye a kan kujera. Ga abin da ya gani a rubuce. YAYA MUS’AB Na dai lura babu abin da kake so irin ka ganni cikin tashin hankali da damuwa, ka ganni cikin matsanancin hali. To na gaji ba kuma zan sake yarda ka sake jefani cikin wata fitinar ba, don haka na tafi, daga yau na bar maka gidanka, zan koma gaban masu tausayina”. Sai wata rana. Mai qaunarka Aisha. Mus’ab ya zubawa wasiqar ido cikin kixima, ya rasa me ya faru? Me ya yi da zafi haka har da za a xauki irin wannan matakin? Tsawon lokaci yana tunani ya kasa ganowa. To ko dai ta gaji da zama dani ne babu haihuwa? Tunda ta san matsalar tawa ce. Ya xauko wayarshi ya danna lambobinta, ta xauka ya jita tana kuka, jikinshi ya yi sanyi maimakon vacin rai zalla. “Aisha me ya faru? Ki dawo mu yi magana”. “Ka qyale ni kawai, ka barni kawai in huta na gaji, na gaji da ganin fitina gara in yi nesa da ita”. “Kina ina ne yanzu?” Ta ce, “Ina kan hanyar tafiya gida, zn tafi Misau zan koma gaban iyayenmu”. Ba ta jira wata magana daga gareshi ba ta yi maza ta kashe wayar tata. Ya zubawa wayar ido yana kallonta tare da nanata faxin Misau. Cikin kixima. Saddiqa tana zaune gaban Gwaggonta cikin gajiya da vacin rai, tunda ta isa take zaune gabanta tana kuka, hankalin Gwaggo ya kai matuqa wajen tashi saboda kukan da take yi da kuma halin da ta ga Saddiqan a ciki. Abu ta iso saboda aiken da Gwaggo Habiban ta yi mata, ganin Saddiqa ya sata mummunar faxuwar gaba, ta nemi wuri ta zauna cikin sanyin jiki tana tambayar ta. “Lafiya? Me ya faru? Me ya kawo ki gida ke kaxai? In ma rikici kuka yi ai bai kamata ki biyo doguwar hanyar nan ke kaxai ba, in kika yi haquri zai wuce kina xakinki. In abin ya yi tsanani da za ta faxa ma sai a tashi babba ya je” “Inna ai tunda aka kai mishi ita ba ta tava shiga wannan yanayin ba, in dai kuma ba matsalarsu bane”. Gwaggo Habiba tana faxin hakan ta kama kuka, duk da a gaban Abu take ta kasa haquri yau kam ta voye damuwarta kan lalurar rashin haihuwar Mus’ab, xa guda xaya namiji da take da shi. A baya ba ta tava tsammanin hankalinta zai koma gare shi har damuwarshi ta zama tata ba irin yanda ta zama a yanzu, ta rasa dalili, xinbin jikokin dake gareta sun kasa sanyaya zuciyarta ta yi sanyi kan rasa xa a gidanshi da aka yi. “Me ya faru Saddiqa? Yi magana mana, ki gayawa uwarki damuwarki kinga kin sata tana kuka. Yi mata bayani dan ta samu sauqin damuwarta”. Cikin zuciyarta ita ma ta yi tunanin yarinyar nan wataqila ta gaji ne da lalurar Mus’abu tunda ta riga ta san matsalar tashi ne. tausayin Mus’ab ya yi matuqar kama ta. Cikin kukan ta ce, “Na gaji, fitinarshi ta isheni, don haka na bar mishi gidanshi yaje ya yi ta yin abin da ya ga dama”. Ta miqe taje ta hau gadon Gwaggonta ta yi kwanciyarta saboda kasancewar hutun sallah take yi. Gari ya waye sanda ta tashi ta je ta yi wanka da ruwan xumin da Gwaggonta ta kai mata, ta fito ta zauna tana shafa. Gwaggo ta kalleta cikin nutsuwa da kulawa ta ce mata, “Kin rame Saddiqa, tunda kika je gidan mijinki ban tava ganin ki na kasa jin daxin ganin naki ba irin wannan karon, ku rinqa yiwa rayuwa haquri, duk abin da kuka gani zai wuce wata rana har ayi ta bayar da labari”. Ta ce mata, “To Gwaggo”. Ta miqe ta xauko doguwar riga ta sanya ta rufe kanta da gyale, ba ta tsaya yin kwalliya ba tasa kai za ta fita. “To ina za ki ba ki karya ba?” Ta ce, “Da na je na gai da Baba ya ce in na kintsa in je yana son magana dani, kuma na ga shigar Abu ma wurin shi kar in tsare su”. Ta ce mata, “To”. An haxu a xakin Malam Abdullahi shi da Abu da Saddiqa, ta sake gai da shi cikin ladabi da nuna girmamawa. A hankali cikin nutsuwa ya tambaye ta. “Me ya faru kika baro mijinki kika dawo gida ke kaxai Saddiqa?” Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Baba na gaji da zama da shi ne kawai”. Gaban Malam

Chapter 22 of 24