Share this page
A tsakar gida ya samu Abu tana ‘yan kintse-kintse. “Wa ya zuba min ruwa a randa ne?” Ya ce, “Nine na kuma sa aka share miki tsakar gida”. “Ubangiji ya yi maka albarka”. Ya ce, “Ameen”. Ya bi bayanta zuwa cikin xaki. “Ya ya kuka yi dasu Baban Abu?” Ta ce, “Dukkansu sun qi, ko da yake da na je gidanka ai a cikin maye na same ka, sai yaushe za ka kama kanka ka zama mutum na sosai ba riga ba Mus’ab? Sai yaushe. In na yi nufin taimakon ka kan auren yarinyar sai kuma tausayinta ya kama ni, ba za ta iyaka ba ka fi qarfinta, ba za ta iya da kai ba Mus’abu”. Ya matsa kusa da ita yana kallon ta ya ce, “Haba Abu, dambe zamu rinqa yi da ita ne da za ayi ta cewa ba za ta iya dani ba? Nine fa nake sonta, kin tava sanin so kuwa? Baki san mutum bawan abin da yake so ne ba”. Harara ta galla mishi kafin ta ja tsaki. “To gaskiya zan gaya miki Abu, in na rasa Aisha kema za ki rasani, don tafiyata Italy zan yi in yi zamana ba zan sake dawowa ba”. Ta sake jan wani tsakin ta ce, “Uhm! Sai me in ka yi hakan?” Ya yi murmushi ya sake matsawa kusa da ita ya ce, “Taimake ni Abu ki rufa min asiri kar ki bari su rabani da yarinyar nan, taimake ni ki gaya min abin da kike ganin ya dace in yi”. Ta ce, “Ka tafi ka koma wurin aikinka ka ga yau kwananka uku, zan yi nazarin abin yi ai ba bikin suka sanya ba”. Ya ce, “To Abu”. Ya ciro kuxi masu yawa ya ajiye mata ya ce, “In kin yi min addu’a ki rinqa haxawa da sadaka”. Ta ce mishi, “To”. A waje ya yi bankwana da baqinshi bayan su ma ya yi musu alheri, sannan ya nufi gidan iyayenshi. A waje ya samu Saddiqa tana sharar qofar gida, ya ce, “Yauwa Aisha, ai gara ki shareni kinga shi kenan sai a bar mikini”. Ta xago ta kalle shi fara’ar dake fuskarshi ta kau, cikin sanyin jiki ya isa gareta. “Kuka kika yi haka? Me ya same ki?” Ta soma wani kukan. “Anyi miki wani abu ne?” Ta yi shiru. Ya ce, “Gaya min mana, ko kuwa nine na ja Inna ta yi miki faxa?” Ta ce, “A’a”. “To mene ne?” Tana kuka take gaya mishi “Bana jin daxi, ban san abin da ya same ni ba, qirjina yana yi min nauyi”. Ya qara matsawa kusa da ita ya ce, “Yi haquri Aisha, don wannan kar ki rinqa kuka, yawanci haka mutum ke yi in zai girma. Yanzu na zo ne mu yi sallama zan koma Ajakuta”. Da sauri ta kalle shi ta ce, “Yanzu?” Ya ce, “Eh, ki yi min addu’a kawai bari in shiga gida in yi musu sallama, ki jira ni a nan”. Ta ce mishi, “To”. Da sauri ya shiga ya fito ya sameta a inda ya barta, ya xauko zoben da yake sanye da shi ya matsa kusa da ita ya ce, “Kin gani Aisha zobe ne ya yi min kyau, sai na yiwa yatsanki sha’awarshi, yngo saka mu gani”. Ba ta yi musu ba. Ya yi mata dai-dai, ya kuma dace da yatsun nata. Ta xago yatsun tana nuna mishi, “Ka gani”. Ya yi murmushi ya ce, “Dama yatsun masu kyau ne Aisha, taimakeni ki yi min alqawari ba za ki cire zoben a jikinsu ba”. A hankali ta buxe baki ta tambaye shi, “Babu wani abin da yake faruwa kuwa?” Da sauri ya ce mata, “Akwai, sai dai tunda su Innan basu gaya miki ba to ki yi haquri lokaci zai yi da za ki ji komai, kin gane?” Ta ce mishi, “To”. “In gaya miki wata magana?” Ta yi maza ta ce mishi, “Eh”. A hankali ya ce mata, “Kina da kyau Aisha, kul kika yarda wani abu ya dameki, ni zan tafi na roqeki ki rinqa yawan tunawa dani kina tausayina saboda bani da kowa babu wani wanda yake sona, Inna ce kawai dama to na riga kuma na rasata, kin gane?” Ta ce mishi, “To”. Kwana uku da isar Mus’ab Ajakuta yana kwance tamkar mara lafiya, wurin aikinshi ma ranar Mondy bai iya zuwa ba, yana gida abin da ya yi matuqar tayarwa Jennifer hankali duk da ba kula juna suke yi ba. Mus’ab yana kwance Sani yana zaune a gefenshi ya ce, “Wai ni ciwon gaske kake yi ne ko damuwa ce ta yi maka yawa?” “Gani nan ne kawai Sani, ka duba ka gani wai ‘yar wayar da nake samu muna ‘yar hirar ma ina tahowa sai Inna ta karve”. Sani ya ce, “Nifa inda nine kai da tuni na tafi wurin Kawu Gixe na gaya mishi komai”. “To ai Kawu Gixin ne ya ce ita ce wuqa da nama a kan maganar yarinyar”. Sani ya ce, “Duk da haka tsananin ai ya yi yawa, ita yarinyar da alama ai in ta samu an ci za ta ce ba ta son wancan mutumin, sai kawai ka yi qoqari ta amsa da bakinta tana sonka”. Da daddare suna hirarsu a falo bayan sallar isha’I sai ga Jennifer ta shigo, ganin Mus’ab a zaune riqe da karan sigari ya sata tambayar abin da ta fara gamuwa da shi. “Wannan kuma wace ce na gamu da ita yanzu?” Ya yi murmushi ya ce, “Gaisheni ta zo yi mene ne?” Ta tave baki ta harare shi ta ce, “Ka dai ji kunya, yarinyar cikinka ka koma nema, wanan ai ba ta fi sha takwas ba, in ta yi qoqari ashirin”. Ya ce, “Jennifer kenan, to ni xin dame na fi haka, ai nima yaro ne ba shi yasa kema kike biye dani ba”. Jennifer ta zo har wuya ganin Sani yana dariya. Ta ce, “Ba laifinka bane ni na zo gidanka. Uhm! Tun farkon mu’amalata da kai da ka nuna kana sona sai da Felicia ta yi min kashedi a kanka ta ce kar in yarda za ka yi amfani dani ne kawai ka awurgar a lokacin da ka ga dama, bayan ka rabani da samarina na gaskiya”. Mus’ab ya yi dariya bayan ya fitar da hayaqin sigarin, a hankali ya miqa hannu ya kaxe tokar kafin ya kalle ta cikin murmushi ya ce, “Sai dai baki ji kashedin da qawar taki ta yi miki ba, saboda kin mato a kaina, kinga santalelen yaro. Haka nan ita ma qawar taki da take yi miki kashedi, kashedin nata bai hanata amsa kiran da na yi mata ba sai da na gaji da ita na watsar don kaina”. Ta yi magana cikin yanayin xaci, “Babu laifi, wata rana ba za ka yi ba, don wata matar ma dole ka ganta ka qyaleta”. Ya ce, “Ehm, babu matsala tunda dai na samu na bi ta kanki ke da qawar taki ai ni shi kenan buqatata ta biya”. Sani yana danne dariyar shi yana faxin, “Kai ku kam kuna da abin mamaki, in baku ga juna ba babu zaman lafiya, in kun haxu kuma sai kunyi faxa. Wace irin soyayya ce wannan? Kai Mus’ab ko gaishe ka aka zo yi wai sai anyi faxa da kai a baka da lafiyar ma?” “A’a, to in an zo gaishe ni sai a zageni in qyale? Ta zo gaishe ni ta coge a nan?” Sani yana murmushi ya ce, “Kema Jennifer har dake, mara lafiya ai kusa da shi ake zuwa. Dawo ta nan ki ji damuwar shi”. Ya miqe ya fita ya basu wuri yana faxin “Dawo ta nan Jennifer in dai dubiyar kika zo yi da gaske ba qarasa shi kike son yi da baqaqen maganganunki ba”. Mus’ab ya fara nishi “Wash! Ya kalle ta cikin murmushi, kafin ta ce za ta yi wata magana tuni yasa hannu ya cafkota ya shiga sumbatarta. Sani ya shigo ya gansu ya yi kamar bai ga abin da suke yi ba, ya wuce ya yi tafiyarshi. Saddiqa tana Misau ta rasa inda za ta sa ranta ta ji daxi, an sanya bikinsu da Sadisu sati biyu kawai aka xiba. Qunci da takaici ne suka gallabeta, sai dai in an tambayeta ba za ta ce ga taqamaiman abin da ya haddasa mata hakan ba. Tana kwance cikin kasala da rashin sanin abin yi, wayarta ta yi motsi alamar saqo ya shigo a cikinta. Duk da ta daxe ba ta samu wayar Mus’ab ba saboda daxewar da ta yi ba ta riqe wayar ba, miqa hannu ta yi ta xauko wayar, ga abin da ya ce mata. Aisha! Mutane suna rayuwa, mutane suna mutuwa, wasu su ce sai anjima, wasu za su iya mantowa amma ni kam har abada kina cikin zuciyata. Mus’ab Abdullahi! Ta sake kallon kalmomin cikin tunani, ba ta gane komai game da kalamanshi ba. Ya ji labarin bikin ne? Ta tambayi kanta. Ta yi kamar ta kira ta tambaye shi sai kuma ta fasa. Mus’ab yana kwance a xakinshi wasanni suke yi da Jennifer lokacin da wayarshi ta yi qara, a haka ya miqa hannu ya xauki wayar cikin sauri ya kaita kunnen shi. “Hello Ishaq”. Qoqarin faxin hakan ya yi saboda yanda Jennifer ke sarrafa shi. “Yaushe rabonka da Misau?’ Cikin hanzari ya bar komai ya miqe zaune. “Me ya faru?’ Ishaq ya ce, “Na fa ji kamar sun sanya bikin yarinyar nan, don shekaranjiya na je gai da Abu ita take bani labari”. Mus’ab ya zama tamkar mutum-mutumi a zaune a kan gadon, ya rasa me zai ce in ban da gumi babu abin da ke keto mishi a jikinshi. Jennifer ta kixime tana faxin “Me ya faru? Anyi mutuwa ne?” Tana qoqarin qanqame shi take faxin “Maman ka ce ta mutu”. “Shut up Jennifer!” Ya faxi da qarfi tare da yin jifa da ita ta faxa can gefe. Banxaki ya shiga ya yi wanka ya fito ya kama shirin tafiya ba tare da ya jira wayewar gari ba. Sani ya shigo xakin saboda kiran da Jennifer ta je ta yi mishi saboda tsoratar da ta yi da yanayin Mus’ab da ta gani. Cikin harshen Hausa yake yiwa Sanin bayani za su kasheni ne Sani, za su aurar da yarinyar nan Aisha suna son ganin na yi mutuwar tsaye. Ita kuwa Jennifer sai faman sorry take cewa tana qoqarin rarrashi da kwantar da hankali. “Bari in fito mu tafi tare kawai don bai kamata ka yi wannan doguwar tafiyar a wannan tsohon daren kai kaxai ba kana kuma tuqi”. Tare suka fito da ‘yammatansu su biyu da dama suka kawo don su taya su kwana, suka sauke su a hanya suka wuce suka kama hanyar Misau. Qarfe shida da rabi na safe Mus’ab da Sani suna zaune a falon Mus’ab xin a gidanshi na Misau, yana yiwa Saddiqa waya lokacin ta idar da sallar asuba. “Me yasa za ki yi min haka Aisha? Me yasa?” A kixime ta tambaye shi cewa, “Me na yi maka kuma daga ina kake maganar?” A hankali ya ce mata, “Gani nan a gidana Aisha na zo Misau yau kuma maganar aurenki ya kawo ni, ina son ganin ki yanzu, ina so mu tattauna al’amuran dake tsakaninmu, mu gamu yanzu a gidan Abua ina son sanin abin da ake ciki”. Mus’ab yana zaune gaban Abu yana kallon agogon hannunshi yana kuma kallon hanyar da Saddiqa za ta vullo. Ita kam Abu haquri take ba shi tana kuma gaya mishi wai har ta samar mishi wata yarinyar da take shirin sawa ayi xaurin auren rana xaya da na Saddiqan sai gata ta shigo. Ramar da ya gani a tare da ita, ita ce ta fara sanyaya mishi jiki. Mus’ab ya kalle ta cikin nutsuwa. “Kin yi ciwo ne Aisha?” Ta sunkuyar da kanta qasa hawaye suka soma zuba daga idanunta. “Daina kuka ki gaya min Aisha kina sona?” Da sauri ta xago ta kalle shi idanuwansu suka haxu, ta yi maza ta sake sunkuyawa. “Gaya min kawai Aisha, ai ni na daxe ina sonki, na daxe ina burin mallakar ki a matsayin matata, na daxe ina buri da fatan in samu damar da na sanyaki a gabana na gaya miki wannan kalmar ina sonki Aisha, ai bani da wata budurwa a Misau in bake ba, kece yarinyar da nake so ban samu damar da muka zauna muka tattauna matsalolin da masoya ke fuskanta ba saboda tsoro”. “Tsoro kuma?” Ta yi tambayar cikin wani yanayi. “Yanzu tsoro ne ya hanaka gaya min abin da ya kamata a ce tuntuni ka gaya min?” Ya yi maza ya ce, “Eh, Aisha tsoro ne, in ban da haka ai da tuni na gaya miki cewar duk duniya bani da abin da nake so kamar ki”. Ta miqe da niyyar tafiya ta barshi. Ya yi maza ya kama hannunta ya riqe. “Kar ki tafi ki barni Aisha, kar ki yi fushi dani taimakeni ki rufa min asiri, ki taimakeni kamar yanda Innata ta taimake ni a farko, ai ita ta haifeki Aisha, taimakeni ki yi min kwatankwacin gatan da ta yi min a farko”. “In ma ban yi ba, ba laifina bane kai ne tsoro ya hanaka yin abin da ya dace ka yi”. “Ai tsoron ni kar a rabani dake ne Aisha, Inna ta ce in na ce ina sonki za ta baki labarin mugun halina, tana qina dake ne wai a dalilin tana tsoron kar in cutar dake. Na rantsre miki ba zan iya cutar da ke ba Aisha, don haka ki toshe kunnuwan ki a kan abin da za ki ji an gaya miki a kaina”. Ta kalle shi cikin nutsuwa ta ce, “Kana nufin ba gaskiya bane?” Da sauri ya ce mata, “Gaskiya ne Aisha, gaskiya za ta gaya miki, ni ban tava jin wata magana ta fito bakin Inna ba sai gaskiya, don haka gaskiya kawai za ta faxa, ni xin ne ita ta haifaeni ta fi kowa sanina, tana qina dake saboda wasu halaye nawa da take ganin basu yi mata ba. To amma kar ki manta na zauna gaban Innata ta tausaya min ta taimakeni ta rabani da duk wani abin da nake yi a wancan lokacin, don haka na roqe ki duk abin da za ki yi a kaina ki tausaya min kar ki juya min baya”. Saddiqa ta miqe da nufin tafiya gida Mus’ab ya biyota. “In kin je gidan za ki yiwa Inna maganar ne?” Ta ce, “Ai nima tsoro nake ji”. “Haba Aisha, ki taimakeni mana kar ki bari su aurar dake ga wannan mutumin na fishi dacewa dake, na fishi sanin darajarki, zan fishi girmamaki in kika daure kika toshe kunnuwanki kan abin da za ki ji a kaina kika amince kika aureni. To ni kuwa ba zan tava baki kunya ba”. Suna isowa qofar gidan ta shige ciki ta barshi nan a tsaye. Innarta tana ta aikin qunshe goron da take aikewa da shi na gaiyatar mutane biki, ta kalli Saddiqa yanda fuskarta ta canza. “Hala daga wurin yayanki kike?” Ta koma gefe xaya ta tsuguna alamar tana son yin magana, sai dai ta kasa, ta rasa ta inda za ta faro zancen. Ta kalli Inna cikin rawar jiki da rawar murya ta ce mata, “Inna mene ne?” Ta yi shiru saboda yanda jikinta da muryarta suke rawa. Inna Habiba ta zubawa Saddiqa ido cikin tausayi, zuciyarta ta tabbatar mata da cewar son Mus’ab take yi, sai dai ba za ta barshi ya yi nasara a kan yarinyar ba. “Me ya faru Saddiqa? Me kike son gaya min? Tambayi duk abin da kike son sani zan gaya miki ba tare da raina ya vaci ba, ba zan yi fushi dake ba balle in je ina yi miki faxa, ai baki da wata uwar da ta wuceni, nice uwarki. Yayanki ya gaya miki wata magana ne?” Saddiqa ta soma kuka, ta ce, “Yana sona, Inna ya ce kece kika hanashi ya gaya min yana sona bayan kuma shine xan’uwana”. Gwaggo ta yi murmushi ta ce, “Ke yarinya ce Saddiqa shi yasa baki gane dalili ba, ke da yayanki ‘yan’uwa ne da zumunci ya haxaku, sai dai halayenku da xabi’unku ba xaya bane, shi ba abokin haxinki bane, hanyar jirgi daban ta mota daban, ba zamu iya dashi ba halayensa sun fi qarfinmu”. Ta ce, “A’a, Gwaggo ni zan iya da shi, ni shi nake so ba Sadisu ba, dama na yi shiru ne kawai don bai riga ya furta min ba, amma yanzu tunda ya gaya min ya yi min rantsuwar bai da wata budurwa a Misau in ba ni ba. To ki taimakeni ki yafe min kar ki baiwa Sadisu ni, Yaya Mus’ab nake so”. Ta kai gwiwpyinta qasa ta durqusa a kansu alamar roqo cikin kuma kuka mai tsanani. Inna Habiba ta zuba mata ido tana kallon ta, ta ce, “To Saddiqa ni dama ai ba wai bana sonki da shi bane, savanin dake tsakaninku ne na ga ya yi yawa na ce gara miki inda za ki samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Amma tunda haka ne ai shi kenan, ni na gane ke ko warin sigari baki so a kusa dake, to shi kuwa na ji labari an ce lokacin da kamfanin sigarin da yake sha na Rothmans suka yi bikinsu har kyautar girmamawa suka yi mishi saboda cinikin da yake yi musu. To wannan ma da xan sauqi a awurina da ya tsaya a haka nan, inda kike ganinshi mashayin barasa ne na qarshe”. Saddiqa ta qwalla qara da iyakacin qarfinta tare da kama kanta da hannayenta duka biyu. “Wayyo Inna! Wayyo Allah!!” Inna ta samu damar xora bayaninta da cewa, “To shi nake jiye miki, kin san halin mashayi bai da wata amana, ga shi manemin mata. A nan garin ne kawai baya yi, amma an tabbatar min da cewar duk inda yake in ba a nan bane bai rabo da matan banza suna biye da shi, shi yasa nake tausayin quruciyarki. Kina da sha takwas ne yana da talatin da biyar, ina tausayin ki zama matar mashayi ko manemin mata, shi yasa na zava miki Sadisu yaro qarami, bai girmeki da wasu shekaru masu tsanani ba, za ku yi quruciyarku tare ne ku girma tare, a kan idonmu aka haife shi har ya girma, bai da wani halin assha, shi yasa na zava miki shi ku biyun dukanku yaran kirki ne masu biyayya masu ganin girman na gaba. Ko kuwa har yanzu kin fi son auren yayanki a kan Sadisu?” Cikin kuka ta ce, “Na haqura Gwaggo, na yarda da zavin da kika yi min na auren Sadisu”. Daxi ya kama Inna Habiba, ta shiga sanyawa Saddiqa albarka, cikin zuciyarta kuwa faxi take yi ja’irin yaro kawai, ba zan barka ka yi galaba a kanta ba balle ka sanyani in ji kunya, bayan na riga na yi alqawarin baiwa xan aminiyata ita za ka zo ka bijirar min da ita. Mus’ab kuwa yana can gidanshi tare da Sani suna tattaunawa kan yanda za ayi, sai dai maganar kawai yake yi amma hankalinshi yana can wajen sauraron wayar Saddiqa, don ta gaya mishi yanda suka yi da Gwaggonta shiru babu wayar. Hankalin Mus’ab ya kai matuqa wajen tashi. Sani ya kalle shi cikin raxa ya ce, “Ina ganin tunda ni a gida ba a san na zo ba, tunda da sauran duhu muka iso muka kuma taho nan kai tsaye, ko in ka ga da matsala abin zai mana gardama in xauke maka yarinyar mana in tafi da ita sai kai ka yi zaman ka, ka yi ta taimakawa wajen neman ta, ka ga babu mai gane kana da hannu cikin vacewar tata, in yaso daga baya in hankula suka kwanta sai a dawo da ita sai a xaura muku aurenku”. Mus’ab ya zuba mishi ido cikin nazari ya ce, “Da zan yi jarumtakar yin hakan to da na ji daxin shawarar taka, to ba zan iya ba saboda dalilai guda biyu. Na farko bana so wani savani ya sake shiga tsakanina da iyayena, a yanzu mun shirya ni da babana, ni da shi muna da fahimtar juna, zamu zauna tare mu yi hira, zai bani shawara zai yi min nasiha har muna zuwa unguwa tare. Inna ce bani da wannan fahimtar da ita, ina kuma qoqarin ganin mun samu daidaituwa sai kuma in zo in tafka musu irin wannan laifin? Bana zaton in ya bayyana zamu sake samun wata fahimta dasu. Na biyu duk matsanancin son da nake yiwa Aisha ina son mallakarta ne ta hanyar aure, in babu auren to bani da wata buqata irin wannan a tare da ita, don ba zan iya keta haddinta ba, don haka na fi so iyayenmu su yarda su bani ita in mallaketa ta zama matata da izininsu don mu samu albarka, in kuma yi qoqarin gyara abin da na riga na vata a baya. Yanzu fatana bai wuce komai za a gayawa Aisha ta yarda ta daure ta bani haxin kai ba, in har ta yi min haka, to komai zai zo min da sauqi. Don in har ta dage ta ce ni take so, ina ganin kamar Innar za ta yi sassauci”. Gajiya ya yi ya xauki wayarshi ya danna lambobin Saddiqa, kwance take a xakinta har lokacin kuka take yi ba ta daina ba. Kamar kar ta xauki wayar sai kuma wata zuciyar ta ce ta xauka. “Na ji shiru ne Aisha shine na ce bari in bugo in ji me kike ciki? Sai dai na ji kamar kina kuka, me ya same ki?” Ta ce, “Kukan baqin

Chapter 8 of 24