Share this page
dasu ina cikin manema ‘yarsu don su sani a wurina girmamawa ne”. Abu tana cin kilishinta tana korawa da ruwan lemon kwali ta ce, “Kai kam kafaffen mutum ne, in da rabon za a lissafaka cikin waxanda aka kayar ai babu makawa sai anyi hakan”. Ya yi murmushi ya ce, “Eh, babu komai tunda ba zan zama nine na farko ba a jerin mazan da aka tava kayarwa wajen neman aure ba, ba kuma zai yiwu a ce nine zan zama na qarshe ba, a ce daga kaina an daina, ko shi gwanin da kike so xin ai an gaya min aure ya nema aka ka da shi, shine aka yi fushi aka yi nufin share mishi hawaye da Aishan”. Abu ta qyalqyale da dariya ta ce, “Kai kuwa a ina ka samo wannan labarin?” Ya yi shiru yana kallon ‘yan yatsun hannunshi. “Ka kuwa san shima ya tsargu da kai?” Mus’ab ya xago ido ya kalle ta cikin sauraro, a zuciyarshi kuwa daxi ya ji, sai dai ya voye. Tana murmushi ta xan rage murya wai za ta yi mishi tsegumi. “Ai na je gidan su Saddiqa na samu rigima tsakaninta da Gwaggonta wai ta qi fita hira wajen Sadisu, shine na tambaye ta dalili ta ce, wai kullum ya zo sai ya yi maganar Yaya Mus’ab, ta ce mishi ya daina ya daina tunda ba alheri yake faxi a kanshi ba ya qi dainawa, don haka ta daina zuwa hirar tashi. Na ce to ta yi haquri ta je in sake yi mata maganar ka ta gaya min ni zan ce mishi ya daina don a zauna lafiya”. Sallamar Saddiqa ta hana Mus’ab faxin komai, ta shigo cikin kwalliya sosai, wani haxaxxen leshi ne a jikinta mai ruwan bula, ga duwatsunshi sun haxu sai xaukar ido suke yi, tana tafe a yanayin takun ta mai cike da rausaya ta qaraso tana kallon Mus’ab ta saki wani lallausan murmushi. Ya ce, “In kika sake yi min irin dariyar da kika yi min a gidan Inna ba yarda zan yi ba”. Ta rufe baki da hannu xaya wai tana qoqarin danne dariyar, ta wuce can gefen Abu ta zauna tana gaisheta. “Abu ke baki yiwa Yaya magana a kan askin qasumbarshi ba?” Abu ta xago kai ta kalli Mus’ab ta kawar tana sha’aninta. “To ni ina gamina da shi da zan tsura mishi ido sai na gane abin da qasumbar shi ke ciki, da ta fi haka kenan?” “To ai kuwa dai da ta yi yawa”. Saddiqa ta ce, “Ka ji Abu”. Ita ma ta kawar da zancen. “To wai ni ba an hana mata fita da irin wannan qamshin bane?” Ta ce, “A’a, Abu na aure ba? Ai ni ba matar aure ba ce”. Abu ta tave baki ta ce, “Ai sai ki yi”. Har kusan awa guda da zuwanta hira ake yi. Ta kalli Mus’ab. “Yaya ba zamu bane?” Ya ce, “Zamu”. Yasa hannu ya xauki xan makullinshi ya ce, “Abu zamu unguwa Aisha za ta rakani wajen budurwata ta ganta”. Abu ta ce, “Sai kun dawo”. Ya yi parking xin motarshi a harabar gidanshi. Ta ce, “A’a, gidanka kuma muka zo?” Ya ce, “Eh, nima zan yi wanka in yi kwalliya don kar ki fini cinyewa a wurinta, don haka fito mu shiga”. Ta yi murmushi ta ce, “Amma sai dai ka yi sauri don kar dare ya yi”. Da sauri ya ce, “Af! Hakaa ne fa, yau ranar taxi ne ga shi kuma da so nake ki yi min girki kafin mu tafi don yunwa nake ji, ko za ki vata kwalliyarki”. Ta ce mishi, “A’a”. Ya miqa hannu yana tayata zare gyalen dake jikinta tare da faxin “Kawo mayafin in ajiye miki don saurayin ki zai zo hira ai ba za ki bar yayanki da yunwa ba ko kuwa? Ban yarda na ci wani abu tunda na taso, na xauka zan zo in samu kin yi min wani tanadi”. Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Ai ban san da zuwan naka bane”. Ta xan kalle shi ta ce, “To yanzu me za ka ci?” “Oho! Duk abin da kika yi kika bani zan ci, ni dai kawai in ji na qoshi buqatata ta biya kenan”. Ta ce, “To shi kenan”. Ta shiga kicin ta soma shirye-shiryen yin girki. Mus’ab ya biyo ta ganin yanda ta sake a ciki ya ba shi sha’awa, ina ma dai bayan aurensu ne take wannan aikin. Ta kalle shi da gefen ido saboda ganin tsayuwar da ya yi. “Ai na xauka wankan za ka yi akfin in gama”. Ya xan qara matsowa ya ce, “In ina jin yunwa ai bana iya komai, har gara ma in zo nan ina taya ki wasu abubuwan don ki fi saurin gamawa”. Ta ce, “To bari in yi maka jelof”. Ya ce, “Babu matsala, sai dai zan sha farfesu”. Ta ce, “To”. Yana taya ta aikin yana yi mata hira. “Za ki yi kyau da karatu Aisha”. Ta ce, “A’a, bai dame ni ba Gwaggo ba ta so”. Ya ce, “Eh, ai daxina dake kenan biyayya, in Inna ba ta son abu shi kenan sai kema ki qishi, ina fata dai kin cika alqawarin da kika yi min na hotuna”. Ta yi murmushi ta ce, “To me za ka yi da hotunana bayan ga sabuwar budurwarka ka samu kuma ban ganka da hotonta ba”. A hankali ya tambaye ta ya ce, “Kina kishi ne?” Da sauri ta juyo ta kalle shi, ya yi kamar ba daga bakinshi maganar ta fito ba, don haka ta ci gaba da aikinta, shima yana nashi na yankan albasa da tafarnuwa. “Kishi!” Ta faxi kalmar cikin zuciyarta. “To a kan me za ta yi hakan?” Nan da nan ta ji wani bayanin na daban yana zuwa mata. “Ai kuwa Abu ta tava gaya mata cewar akwai aure tsakaninta da yayan nata, ban da haka jangwarzo ne da iya gaskiyarta kuma ta faxa kowace budurwa za ta yiwa kanta sha’awarshi”. Ta yi maza ta tsayar da wannan tunanin ta hanyar tunawa kanta Sadisu Gwaggo take so ta aura, don haka maganar ta qare. “Ga albasar Aisha”. Ta juya ta karva, maimakon ya bar wurin sai ya qara matsowa ya ce, “Na ce ba Aisha”. Ta ce, “Na’am”. A hankali ya tambaye ta, “Kina son wannan mutumin ko son baki ne, ko kuwa dai kin yarda ne don ki farantawa Gwaggonki rai?” Ta dakatar da abin da take yi kafin ta xago da nufin kallon shi, kallon da yake yi mata ya sata sunkuyar da kanta qasa, amma hakan bai sa ta fasa gaya mishi abin da take nufin gaya mishin ba. “Bana son irin wannan tambayar na rufe wannan hirar a tsakaninmu, in kuma ba haka ba yanzu zan gudu in bar maka girkin…. In bar maka gidanka”. “To a kan me za ayi hakan Aisha? Ai faxin bakya so xin ya wadatar da komai, ba zan sake ba, wannan da na yin ma na tuba”. Nan take kuma ya canza hirar da faxin “Abu ta yi min maganar idonta, shine na ce ko za ki taimaka ne gobe mu kaita Kano ta ga likitan ido, kin san za ki yi mata amfani sosai ko a wajen layi ne”. Ba ta ce mishi komai ba, shima bai sake maganar ba. Ya ci abincin sosai, Saddiqa ta zuba mishi ruwan lemo a kofi, maimakon ya karva sai ya ce mata. “Aisha sau nawa kike jin mutane suna cewa kina da kyau?” Ta ce, “Zan gudu in barka in ka sake, don ni na tsani a sani a gaba ana cewa ina da kyau”. Ya ce, “To ki yi haquri amma taimakeni ki yi min adalcin barina in faxi magana guda xaya”. Ta ce, “Faxi”. Ya ce, “Kin iya kwalliya, wani lokaci sai in ga tamkar ba a garin nan kika koyi kwalliyar ba, gaki da murya mai daxi, ga shi duk abin da kika sawa jikinki sai ya karveki, gaki da nutsuwa, gaki da girmama iyaye, ga shi kin iya girki, gaki da kamun kai. Ni gaskiya….” Ya yi maza ya yi shiru saboda ganin hawaye sun fara cika idanuwanta, cikin hanzari ya miqe. “Bari in watsa ruwa in fito mu tafi”. Wani lafiyayyen Kaftani ne a jikinshi da ta yi matuqar dacewa da hular dake kanshi, ya yi matuqar yin kyau, ga qamshinshi dake iya nutsar da zuciya. Kallo xaya ta yi mishi ta kawar da kai zuwa ga kallon agogo. “Da alama dai ka fasa zuwa hirar nan yau tunda kalli lokaci”. A zuciyarshi ya samu nutsuwa don ya san ita ma tata hirar babu. Ya ce, “Eh to, sai in fasa zuwa tunda na ga kina yiwa askina dariya sai na mai da qasumbata kar in je ita ma ta ce na ragewa kaina kwarjini”. Ta yi murmushi ta ce, “Ta a kaini gida”. Ya ce, “Yanzu kuwa”. Sun fito harabar tsakar gida take tambayar shi cewa, “Yaya ni su waye suke sha maka sigari ne a gida?’ Ya taya ta kallon guntayen sigarin da take magana a kai ya ce, “To ya ya zan yi Aisha gida na jama’a? Wani abin ai dole sai ka yi haquri, kema bakya son shi ko?” Ta yamutsa fuska ta ce, “Ai ni warin taba amai yake sani”. Bai yi mamakin yanayinta da ya gani ba, saboda ya san sanda yake yaro ya san Innarshi kan ware abin amfani na daban saboda baqin da ta san mashaya sigari ne. Wani hamshaqin kanti suka je ya tsaya yana kallon ta ya ce, “Muje ki zavi abin da kike so”. Ta xaure fuska ta ce, “Bayan tsarabar da ka zo min da ita?” Ya yi shiru ya tsareta da idanuwanshi ya ce, “Kin dai koyi yin jayayya dani”. Ta yi maza ta ce, “Ba haka bane”. Ya ce, “To ya ya ne? Sai kuma ki zo gidana ki tafi haka ko ‘yar tsarabar ‘yan oyoyo babu. Shiga ki duba wani abu”. Suna cikin kantin wanda babu komai a ciki in ban da kayayyakin mata, yana cikin tayata zaven takalma sai ga Sadisu ya shigo cikin kantin. Mus’ab ya yi kamar bai ganshi ba ya ci gaba da abin da yake yi. Ya iso wurin da suke ya ce, “Barka dai”. Ya cewa Mus’ab. Ya yi kamar bai ji shi ba sai da Saddiqa ta ce mishi, “Yaya ana magana”. Ya xaga ya ce mishi, “Barka”. Vacin ran Sadisu ya qara bayyana, ya ce, “Saddiqa me kike yi a nan yanzu?” Ta kalle shi cikin sakin fuska ta ce mishi, “Sayayya”. Ya ce, “To ina son ganinki a waje”. Ya yi maza ya juya. Ta xaga ido ta kalli Mus’ab a hankali. Ya ce mata “Jeki mana”. Ta bi bayan Sadisu. Shi kuwa ya ci gaba da tsintsintar abubuwan da yake ganin za su yi mata kyau, har minti goma sha biyar ba ta shigo ba. Ya fara tunanin me suke faxa haka? Ko dai sun wuce ne suka tafi suka barshi a nan? To ko dai ya leqa ne ya ganewa kanshi? Kai a’a, gara dai ya qara haquri kar yaje leqawa Sadisu ya ganshi. Ya koma wajen zaven agigona sai ga Saddiqa ta shigo. Da sauri ya yi kamar bai samu wata matsala ba, haka nan bai gane yanayin da ta shigo a ciki ba. Ya ce mata, “Mu ga xan hannun ki ko wannan zai yi miki?” Ta ce, “A’a, ni ka kaini gida kawai”. Ya ce, “To”. Ya mayar ya ajiye. Ya rungumo ledojin ya zo ya biya kuxin suka shiga mota, ko tsayawa wurin sayen kaji bai yi ba ya kaita gida ba tare da ya ce mata komai ba. Washe gari da safe tun tara Saddiqa ta isa gidan Abu cikin kwalliyar wani lallausan voil mai ruwan madara, ta yi kyau sai qamshi take yi. Tana sallama a qofar xakin Abu Mus’ab ta fara gani yana zaune kan tabarma yana cin ximamen da Abun ta yi mishi. Ya kalle ta cikin nutsuwa ya ce, “Ni dai sai dai duk yanda za ki yi dani ki yi, amma ba zan daina cewa kina da kyau ba”. Abu ta ja tsaki ta ce “Matsa ni ka gani in wuce, in dai Saddiqa ce mai kyau a wurinka ai baka more ba, tunda baka san kyan ba kenan”. Ta fice ta barsu. Ya xaga ido yana kallon ta cikin nutsuwa, ya ce mata, “Zolayar ki fa take yi don kuwa ta fini sanin kina da kyau, sbaoda ta fini sanin da su wa kike kama”. Ta xaure fuska tare da juyar da idanuwa nuna maganar ba ta dame ta ba. Hakan da ta yi yasa shi bin idanuwan nata da kallo, zuciyarshi ta raya mishi kuka ta yi. Kamar ya tambaye ta abin da yasa ta yin kukan, sai kuma ya ga to a na me? Alama ne dai na wata qila saqon shi ya fara tafiya. “Za ki ci xumame?” Ya yi tambayar don ya kawar da shirun da ta yi. Ta ce, “A’a, na qoshi, kuma ma ni bana cin abu mai nauyi da safe”. Ya yi murmushi ya ce, “Ai kina da kyau ne”. Ta yi maza ta vata fuska. Abu ta shigo daga wurin alwala take, sallar walaha ta soma gabatarwa. “Siraran mutane basu cika cin abu mai nauyi ba, musamman ke gaki ‘yar gata, yanzu ni yanda nake qaton nan in ban ci abu mai nauyi ba in yi me?” Maganar tashi ta sata murmushi, ta ce, “Kai ba wani qato bane fa Yaya, ai kai dogo ne jikinka ya dace da kai kwarjini kawai ya qara maka, in ban da haka da ka yi tsayi mai yawa”. Ya yi murmushi ya ce, “Dame na fiki tsayin Aisha? Qafa shida ne fa dani”. Ta ce, “Lah!” Ya katse ta da cewa, “To bari Abu ta idar mu gwada tsayin ni dake ta gani”. Ya kalle ta ya ce, “Bani ruwan sha”. Da Sauri Abu ta shafa fatiha ta ce, “A’a, kar ki je min bakin randa barni in kawo mishi, haka kawai kin yi dalilin da aka sare min bishiyoyina na shekara da shekaru”. Mus’ab ya ce, “Aka rage musu ganye dai Abu, kuma ai kema hakan ya fi miki dan za su fi ba da iska mai kyau”. Qarfe goma da rabi suka bar Abu suka kama hanyar Kano. Mus’ab da Saddiqa suna gaban mota, ita kuwa Abu tana baya, Saddiqa tana karanta mujallun da ta samu zube a cikin motar, shi kuwa Mus’ab yana hira da Abu. Ta xauko goron ta za ta gutsira ta ce, “Nifa wannan goron ba isana zai yi ba, in an gani a tsaya a saya min”. Mus’ab ya ce, “Ki rinqa shan Ice-cream Abu bana sonki da cin goron nan bai da wani amfani a jiki in ban da cutar da lafiya”. Ta harare shi ta ce, “Au haba? Na ce to da goro da taba fa?” Ya yi shiru bai amsa mata ba. Ta sake faxin “Na ce shi da sigari fa?” Mus’ab ya yi kamar ba da shi take yi ba. Ta ce, “Hhm! Mai sigari kuma har ya cewa mai goro wani abu? Abin da masu yinta ma kashedi suke yi muku suna faxin tana cutar da lafiya, mashayanta kuma za su iya mutuwa tun cikin quruciyarsu saboda cutar da take yiwa lafiyarsu”. Da sauri Saddiqa ta rufe mujallar dake hannunta ta juyo ga kallon Abu ta ce, “Ya ya kike danganta shi da shan sigari?” Gaban Abu ya faxi, ashe ba su biyu bane a motar. “Ke tafi can shashasha”. Ta ci gaba da cin goronta. Ta sake juyawa wajen Mus’ab ta ce, “Yaya kai kana shan sigari ne?” Bai juyo ya kalleta ba balle ta ga yanayin fuskarshi, ya ce, “To ina na san wannan bayani Aisha, ai Abun kawai za ki tambaya ta gaya miki”. Jin da ta yi Abu ce za ta yi mata bayani yasa ta haqura. Tamkar Mus’ab jira yake yi a ambatar mishi sigari, nan da nan kwaxayinta ya taso mishi, sai hamma yake yi yana qarawa. Ya gaji ya ce, “Sammin goron naki Abu in xan tauna”. Ta ce, “Haka kuma?” Ya ce, “A’a, bani kawai in gutsira”. Ta ce, “To”. Ta miqa mishi yana duba goron kafin ya jefashi a baki, ya juya ya kalli Saddiqa ya ce, “Ke kam na san bakya cin goro”. Ta ce, “A’a”. Ya ce, “Nima yau ne saboda na ji kamar zan yi gyangyaxi”. Abu tana daga baya ta ce, “A’a, ai haka tsiyar goro da taba yake”. Saddiqa ta valla mata harara ta ce, “Ni bana son ana ambaton sunan taba a kusa dani”. Abu dai suvutar baki take yi tana yin maganar, ta yi nufin kame bakinta daga hirar shima Mus’ab ya yi nufin daina jan Abu da hira don gudun kar ta yi mishi tonon asiri. Asibitin ido na Niger Optical Service suka je, sun ga kan lokaci da aka yi alqawari, an kuma sallame su da magunguna bayan an tabbatar musu da cewar idon bai da wata matsalar da ta wuce shekaru ke haddasawa. Daga can Mus’ab ya zarce dasu Cort Road gidan abokinshi na makaranta Ishak, suna yin parking maigidan ya fito, yana ganin baqin ya buxe baki yana faxin, “Amma yau ka burgeni, ai ban san ka da irin wannan kirkin ba, ko da yake ga waxanda suka kawo ka, uwargida ne da amarya ko?” Ya shiga yiwa Abu da Saddiqa sannu da zuwa. Ya matsa kusa da Abu saboda ganin fitowar matarshi Atika don tarar Saddiqa. “Ai ni yau shar dani tunda ga amaryata ta zo”. Abu ta yi murmushi tare da faxin “Yi dai a hankali kar matar gidan ta ji ta qi yi min malmala mai auki”. Gaba xaya suka yi dariya. Atika ta wuce gaba tana yiwa Saddiqa jagora zuwa saman gidan, ita kam Abu wurinsu Mus’ab ta yi zamanta. Nan da nan Atika ta zagayesu da kayayyakin lashe-lashe da tanxe-tanxe. Ta kalli Abu ta ce, “A’a, ke kuma a nan za ki hakimce wurin maigidan?” Ta ce, “A’a, ni bana zama xakin kishiya”. Suka yi dariya. Atika ta zauna suka gaisa, sannan ta xebowa Abu nata plate xin ta kawo mata kusa da ita, sannan ta juya da sauri ta haura sama inda ta bar Saddiqa tana jiran dawowarta. Mus’ab ya kunna sigarinshi ya sanya a baki bai cewa kowa komai ba, sai da ya zuqe kara biyu. Ishak ya kalle shi ya ce, “Yallavai wannan shirun duk a daxin yake?” Mus’ab ya kalle shi ya ce, “Yau ai ba qaramin wahala na sha ba”. Ya kwashe bayanin duka ya yi mishi na yanda suka yi a mota. Ishak ya yi murmushi ya ce, “Ai in har ka saba shan sigari bayan ka ci abinci, to bari cin abincin ka zauna da yunwarka ya fi sauqi, ko kuma in ka ci ka san yanda ka yi ka yi dabarar da ka xan xorata, amma kai a ina ake yin haka?” Yana tambayar yana dariya ya ce, “Har sigarin ba ta san kana sha ba? Tafxijam! Ai za ka wahala, ka voye wuta ka voye hayaqinta? Ai in aka voye wasu abubuwan shi sigarin sai kawai a nuna mata ana sha, in yaso sai a roqeta ta ba da lokaci za a daina kafin nan ta shiga gida shi kenan”. Abu ta qyalqyale da dariya tana kallon su, ya sake wani murmushin ya zubawa Mus’ab ido ya ce, “Ai haka ake yi, amma ka tattara komai ka voye, ni da ban voye duka ba ma ai da aka gano abin da ake ciki ba qaramin bori aka yi ba”. Mus’ab ya gyara zama ya ce, “Ni neman auren nawa ne babu gata a ciki, nan inda kake ganin Abu ma ba ta tare dani, shi yasa ta yi ta qoqarin tona min asiri a gabanta”. Abu ta yi dariya ta ce, “Ubangiji ya shiryeku yaran nan”. Suka ce, “Amin”. Ita kam Saddiqa tana can suna shan hira da Atika tamkar sun daxe da sanin juna, rayuwar da Atika ke ciki ta ba ta sha’awa, saboda ganin da ta yi tamkar komai nata ya yi dai-dai. “Ya ya ban ga yara ba a gidan?” Ta yi murmushi ta ce, “Yanzu ne fa nake da cikin bai ma fi wata uku ba, Mus’ab bai baki labarin wahalar da muka yi wurin neman haihuwa ba?” Saddiqa ta yi murmushi ta ce, “Kun daxe da auren?” Ta yi maza ta ce, “Shekara uku fa, abokan aurenmu wasu ma sunyi biyu”. Saddiqa ta yi dariya ta ce, “Yanzu nan in an shekara uku ba a haihu ba sai hankali ya tashi? Ai bai wuce amarci ba”. Atika ta zaro ido tare da faxin, “Tafxijan! To bari mu ga ku yanda za ku yi naku amarcin, in baki sani ba in gaya miki, Mus’ab yana ganin kin wuce wata uku za ki ga ya fara…..” Ta katseta da cewa, “Lah, Yaya Mus’ab fa Yayana ne ba saurayina bane”. Atika ta zaro ido haxe da cewa, “Kina nufin ba kece nake jin suna labarinki da Ishak ba?”

Chapter 5 of 24