Share this page
Su Ishaq suka shigo, Sani ya wuce kicin Ishaq ya tsaya wurinsu yana faxin “Qannen ango ne a daren nan?” Suna gamawa gaisawa Sani ya sake shigowa cikin falon da abubuwan ci da na sha yana ajiye musu, yana yiwa Mus’ab bayani. Ishaq ya katse shi ya ce, “Bilkisu ku fita a mai daku gida mu zamu koma Bauchi yancu zamu je musa ango a lalle, a can zamu yi hidimar bikinmu, zamu xora muku nauyin haxa mana kayan aure duk da mun san kuma hidimar taku tana da yawa, don haka mota za ta zo ta xauke ku gobe, sai ku samu Atika a Kano ku haxu ku yi sayayyar ko kuwa?” Suka amsa “To”. Mus’ab ya miqe ya shiga xakinshi ya fito rungume da wasu lesuna ya zube, ya sake komawa ya fito riqe da akwatin matafiya ya zo ya miqa musu suka buxe suna dubawa. Sarqoqi ne masu asalin kyau haar kala uku, kowanne kuma yana haxe da wara-waran da suka dace da shi. Mus’ab da Ishaq suka yi singing xin cek guda biyu suka miqa musu. “Ga shi nan in kun je yin sayayyar kar ku mance da kawunanku”. Suka sa hannu biyu suka karva tare da godiya gami da fatan alheri. Biki sosai su Mus’ab suka yi a Bauchi, don can suka yi hidimar tasu a gidan Kawu Gixe. Ko ita ma kuwa Inna Habiba duk da vacin ran dake cikin ranta voyewa ta yi, hidima sosai irin wacce ba ta tava yi ba, ga kuma su Bilki da suka qara qayatar da bikin ta hanyar sakar mishi kuxi sosai. Anyi xaurin auren Kubrah da Sadisu, an kuma kaita gidan mijinta duk wani shiri da Inna Habiba ta yiwa Saddiqa ta kwashe ta bayar an kai wa Kubrah gidan Sadisu. ‘Yan biki sun watse an bar Saddiqa da Innarta a gida kamar yanda dama suke. Suna zaune a falon Innar suna hira, akwatinan auren Mus’ab ne a gabansu suna qara dubawa. “Ai zan yi maganinshi, wai shi ya iya shege ko? Ya za ga yaje ya kaiwa Yaya maganar shi kuma Yaya da yake bai ganin laifinshi duk da ya fi kowa sanin shi, ya xauki auren ya ba shi. To ai zan ga mai kai mishi ke, kar ki yarda zuciyarki ta karyo a kan qiyayyar da kike yi mishi, don wannan aure da Yaya ya xaura ba komai bane illa fitina, ba zamu iya shi ba don haka bake ba shi, kar ma ki yarda ki saurare shi, don ba za ki tare a gidanshi ba ma, kuma nan ina jiran randa zai shigo gidan nan titsiye shi zan yi sai ya rubuta takardar sakin auren ya bani sannan ya fita”. Saddiqa ta kalleta cikin nutsuwa ta ce, “To amma Gwaggo kin san da haka kike ta bani kayanshi ina xaurawa? Ko jiya fa tirmi goma kika bayar a xinko min?” “Ai ba zan mayar mishi da kayana ba har zinaran sun zo kenan ladan kukan da ya sani na yi a cikin mutanen da na tara ana kallona ina sharvar majinar baqin ciki”. Saddiqa ta vata ido ta ce, “Dama an bar mishi kayanshi kawai Gwaggo, da wanne zai ji?” Ta yi maza ta ce, “Kul! Na sake jin wannan maganar a bakinki, kwalliyarki za ki yi ta yi dasu”. Da daddare misalin sha biyu da rabi Mus’ab yana kwance a xakinshi dake gidanshi na Misau, ya yi sha’awar a ce shima an kawo mishi Aishanshi kamar yanda aka yiwa Sadisu tashi matar, ina ma dai a ce a gefenshi take yana a kwance, ga shi kuma daren mai cike da iska ne mai xauke da saqon sanyi a cikin shi. Ko sai yaushe ne haqqina da damuwa ta za su zamo abin dubawa wajen Inna? Shima Baba ya yi shiru ya zuba ido yana kallon abin da ake yi min xin bai tanka ba. Ya xan yi tsaki mara sauti, a dai-dai lokacin da ya miqa hannu ya xauko wayarshi dake gefenshi a ajiye ya soma dannaa lambobinta. Ko ba ta amsa maganar da nake yi mata ai tana jina, bari in gaya mata abin da zan gaya mata. Tunanin dake zuciyar shi kenan. Saddiqa wacce Gwaggonta ta dawo da ita kwana a xakinta, a nan gadonta suke kwana tare tun bayan watsewar ‘yan baki, saboda tsoron da take yi na kar Mus’ab ya shigo cikin gidan ba ta sani ba. “Xauki mana ki ji abin da zai ce miki”. Don haka ta miqa hannu ta xauka. “Aisha!” Ya kira sunan a hankali cikin jan hankali da nutsuwa. “Wai ni me yasa haqqi in nawa ne taka shi bai da wuya wurin Inna? An fi sati guda yau tunda Kawuna ya bani aurenki amma har yanzu ba a ce min ga lokacin da za a kawo ki ba, an xaura auren Kubrah da Sadisu ne bayan nawa xaurin auren, amma tuni da yake shi xan gata ne an kai mishi tashi matar. Ki taimaka ki yiwa Inna magana mana tunda ke ‘yar lelenta ce ki gaya mata kema kina buqatar mijinki, na rantse miki zama dani zai fiye miki na zaman gidan daxi, ba zan rinqa barinki kina kwanciya a kan kafita ba kan qirjina zan rinqa shimfixe ki, kin san kuwa xuminshi ba zai tava yin daidai da na katifa ba. Zan jiyar dake daxin da baki tava xanxana ba, zan yi miki tausa da sumba….” Ya yi maza ya katse layin saboda kukan da ta soma yi mishi. “Uh-uhm! Abin da ya iya kenan”. Mus’ab yana zaune gaban Abu, hira suke yi mai daxi, sai qamshi yake yi yana kuma cin dambun zogalen da Abun ta yi musu. “Ai na zo ranar talata bakya nan Abu, za ki ce wai angwanci ya voye ni. Kuma ni wane angwanci zan yi tunda an qi a bani matata”. Abu ta qyalqyale da dariya ta ce, “To ba dai zamanka take yi ba? Ko ba daxe ko ba jima ai za ta baka ita”. “A’a, Abu ni kawai a bani matata babu maganar ko ba daxe ko ba jima, ni na xauka ma za ki je wajen ta maganar a bani itan”. Ta ce, “A’a, ranar talata gidan Kubra na je saboda ‘yan’uwan mijinta sun zo nan sun kawo kaya na abin arzikin da taje musu da shi, suka ce a shaidawa iyayenta cewar ‘yarsu ta kai ‘yancinta, don haka na je don ba ta daga can kuma na je na gayawa Innarku na kuma kai mata abin da suka zo da shi”. Mus’ab ya ce, “Kai wannan al’ada taku Abu sai yaushe za ku barta?” “Mu barta a kan me?” A hankali ya yi tsaki, ya ce, “Haba, abin da ya kamata ya zamo sirri tsakanin miji da mata wai sai ayi ta bi ana yayatawa, ai ni ba zan yarda ayi min irin wannan bankaxar ba”. Ta galla mishi harara ta ce, “Eh, ai ku dama ‘ya’yan zamani ko in ce yanzu duk wani abu na al’ada dake taimakawa wajen kame mutunci da gudun abin kunya bakwa son shi, faxin budurwa ta kai budurci bankaxa ne amma neman matan banza ayi ta lalacewa dasu wannan ba bankaxa bane?” Ya yi murmushi don ya san inda ta dosa. “Abu kenan, mai da wuqar ni yanzu zuwa na yi in roqeki ki taimakeni ki sa baki a bani tawa matar nima”. Ta ce, “To zuwa yamma zan je gidan in ji abin da suke ciki”. Abu tana zaune a falon Inna Habiba suna gaisawa, Saddiqa ta fito daga can cikin xakin ta sha kwalliya cikin sabbin kayan aurenta, ga zinare ya kama jijkinta, duk da ba a kaita gidan miji ba sheqe take yi saboda qarin kulawar da ta samu. Abu ta harareta ta ce, “Uu-uhm! Ita kuma wannan amaryar a gidansu take kwalliyar amarcin? To wai me ya hana a kai Saddiqa gidan mijinta ne?” Ta zubawa Inna Habiba ido tana kallon ta tare da sauraron amsar tambayar tata. “Kin san dai baki da ikon riqe mishi mata a wannan lokacin, matarshi ce in dai ba so kike ki shiga alhakinsu ba”. “Alhakinsu Inna?” Ta yi tambayar cikin wani yanayi. Abu ta ce, “Eh mana, alhakinsu su duka, an ce miki ita ba ta son mijinta ne? Ko yaushe rabon da ki ganta tana kuka? Wannan kyau da sheqin da take yi an ce miki na zannuwa da zinaran da kike ba ta tana xaurawa ne? Basu bane kwanciyar hankali ta samu a dalilin an ba ta mijin da take so, da kin ba ta shima da yanzu ta fi haka, don da ta fi haka samun nutsuwa a wurinshi. In kuma kina jira ne sai ta sulale ta je ta same shi kin yi abin kunyar da gaske to”. Saddiqa ta sawa Abu kuka cikin yanayin shagwava ta ce, “Ni bana so, bana so Abu, bana so”. Ta soma kuka har tana shure-shure. Abu ta gallla mata harara tare da faxin, Tafi can munafuka”. Ta kalli Inna Habiba ta ba ta umarnin cewa, “Ki hanzarta xaukar yarinyar nan ki kaita gidan mijinta tun bamu kai ga vacin rai ba”. A nutse cikin ladabi ta ce mata, “To Inna, to ko za ki turo min shine ya zo mu san abin da muke ciki, kin san fa duk xan tanadin nawa na kwashe na kai wa Kubrah, kuma tunda aka yi xaurin auren fa bai leqo gidan nan ba, ina ce ya dace ya zo?” Ta ce, To bari zan turo shi tunda kuna son ganin shi”. Ta tashi ta fita ta nufi gidanta. Mus’ab ya yi murmushin jin bayanin da Abu ta yi mishi, ai bai kamata in fiki saninta ba Abu, so take in ji gabanta ta tilastani sakin aurena, tana shawara dani ne balle aa kan wannan auren da ta riga ta qi? Bana son shirin a bani matata kawai, ai ko wani za ta aura ni mai yi mata komai ne balle kuma ta zama tawa”. Abu ta yi kasaqe cikin yanayi na gaskata kalaman nashi, a hankali ta ce, “To kan wannan kam ai ka fini sanin nata, ina na yi wannan tunanin. Wato iya shege nima za ta yi min? To tashi ka tafi ka bar mata ita mu gani ko za ta yi ta riqe ta da auren naka a kanta”. Mus’ab yana kwance a falonshi, sigarinshi yake zuqa yana kuma tunanin rabonshi da wurin aikinshi. Lokacin da ya ji wayarshi ta yi qara yasa hannu ya xauka, lambobin Saddiqa ne. Ya xauka ya kai kunnen shi. “Ran amarya ya daxe, yau kin yi sha’awar jin muryata ne kika bugo min waya?” Shiru ta yi ta kasa amsawa. Ya ce, “In ce ko dai lafiya?” Ta sake yin shiru. Ya ce, “Ko ina son ganina ne?” Da qyar ta iya buxa baki ta ce mishi, “Eh, ka zo”. “In zo?” Ya tambaye ta. Ta ce, “Eh”. “Kina son ganina?” Ya sake tambayar. Ta ce mishi, “Eh”. Ya saki lallausan murmushi saboda abin da zuciyarshi ta raya mishi. “To ki gayawa Inna zan turo direba ya xauke ki”. Da sauri ta ce mishi, “A’a, kai ka zo”. “To shi kenan ki fito mu haxu a gidan Abu”. Ta yi maza ta ce, “A’a, sai dai ka zo nan gidan”. Ya ce, “A’a, Aisha in zo wurinki kina cikin gidanku ai ba zan iya ba, wai ba ki san ko ban yi surukuta da kowa ba dole in yi da Inna, ai in ba ita ce ta ce ki kira mata ni ba a yanzu babu abin da zai sa in shigo muku gidanku saboda kunya da girmamawa irin ta surukuta”. Da sauri Saddiqa ta ce, “Ai ita xin ce ta ce in yi kiranka”. Ya ce, “A’a, ban yarda ba wayo kawai kike son yi min”. Ta kama rantsuwa ta ce, “Ita ce ta ce na kira ka amma kar in ce in jita ne in ce in jini wai za ka fi saurin zuwa”. Ya ce, “Naqi yarda da wannan maganar taki, saboda a bakinki na saba jin kina cewa, wai maganar fari ita sarki yake karva, don haka sai anjima”. Ya ajiye wayar cikin nazarin abin yi tunda ya gane Innarshi ta matsu tana son ganinshi. Nan take ya qara sanin akwai abin da take shiryawa a kanshi. Yana zaune cikin ladabi a gaban Kawu Gixe bayan ya gama mayar mishi da bayanin halin da ake ciki. “To kai me ya hanaka zuwa ka ji kiran da take yi makan?” “Tsoro nake Kawu kar in je ta bani umarnin da zan kasa cika mata, har yanzu auren bai kwanta mata ba, sai nake ganin kamar so take in je ta titsiyeni ta tilastani yin abin da ba zai yi min daxi ba a kan auren”. Kawu Gixe ya xan yi shiru zuwa wani lokaci kaxan kafin ya dawo da nutsuwarshi gare shi. “To wai kai me ma ya zaunar da kai ne? Ka baro wurin aikinka kusan sati uku tuni abokanka sun koma kai kana zaune kana zirga-zirga a hanya, ka kama hanya ka yi tafiyarka ka koma wurin aikinka”. Mus’ab ya sake kallon shi cikin ladabi ya ce, “To Kawu Aishan fa?” “Ka yi tafiyarka ka barta mana ba taka ba ce? Ko za ta sake xaura mata wani auren ne a kan naka? Tunda zamanta da ita bai isheta ba ta je ta yi ta yi, kana can wurin aikinka ma in ka yi haquri za ka ga ta turo maka ita, ai matarka ce”. Mus’ab ya yi kamar ya ce ba za ta turo ba Kawu. Sai kuma ya haqura ya amsa umarnin da yake ba shi na kar ya yarda ko aike ya ji shi yana yi musu. Ya ce, “To”. Ya yi mishi sallama ya fita, maimakon ya nufi Ajakuta sai ya koma Misau don yin shirin tafiya Ajakuta. Mus’ab yana zaune gaban Abu suna magana kan tafiyar da zai yin, ya fiddo kuxin da ya sunne cikin babbar rigar shi ya ajiye a gefen Abun. “Ki kaiwa Inna”. Ta kalli tudun kuxin kafin ta mai da kallon nata gare shi ta ce, “Ba ka ce Kawun ka ya hanaka yi musu aike ba?” Bai amsa ba. Ta buxe ledar da kuxin ke ciki ta ce, “To na mene ne, me za ta yi da shi? Ko kuwa na sayayyar ne?” “Bana son sayayya Abu, ki kai mata ki kuma ba ta haquri kan rashin zuwana, na roqeta ta yafe min”. Tausayinshi ya kamata. Ta kalle shi cikin nutsuwa ta ce mishi, “Ubangiji ya yi maka albarka, ya rufa maka asiri ya kuma azurtaku kai da ita da samun zuriya xayyaba”. Daxi ya kama Mus’ab, sai dai bai ya cewa komai ba, sai a zuciyarshi ne ya amsa amin xin. Ya sake miqa mata wasu. “Na waye su kuma?” Ya ce, “Naki ne Abu, ki sha fura”. Ta yi murmushi ta ce, “Har da zuma da kaji. To ina na baban ka?” “Sai da na je wajen shi a kasuwa kafin na zo nan”. Ta ce, “To madalla”. Ta shiga qara yi mishi addu’o’in da ta saba yana cewa “Amin”. Ta biyo shi don rakiya tana cewa, “To baka faxi yaushe zamu sa rai da kai ba”. Ya ce, “Abu kenan, mata fa zan tafi in bari ai kema kin san ba wani daxewa zan yi ba”. “To ba Kawunka ya ce ka tafi ka mance dasu ba?” Ya yi murmushi ya ce, “To zan iya ne?’ MUS’AB YA ISA AJAKUTA Mus’ab ya koma Ajakuta, bayan komawar Sani da daxewa, don haka tuni labarin yin auren nashi ya bazu a ko’ina. Tarba mai yawa da girmamawa ya samu a wurin abokan harkoki daban-daban, abokan arziki na wurin aiki, da na sha’anin gari sun shirya mishi liyafar taya shi murnar auren nashi. Su ma abokan bariki ba a barsu a baya ba, sunyi mishi irin nasu shirin. Kwananshi uku da komawa Jennifer ta isa gidan nashi a dalilin labarin dawowar shi da ta ji. “Oh Darling!” Ya faxi hakan dai-dai lokacin da suka haxa ido. Ta qara xaure fuska sosai nuna alamar ba wasa ya kaita ba. “Kar ka sake Darling ya fita daga bakinka, kar kaa nemi ka mai dani qaramar yarinya, maciyin amana kawai”. Ta ja tsaki ta sake galla mishi harara kafin ta ce, “Wai ka yi aure? Imgine. Uh-uhm! Ko wace ‘yar iskar ka samu ka aura?” Mus’ab ya kalleta cikin murmushi da nutsuwa ya ce mata, “Ba ‘yar iska ba ce, Jennifer da za iya auren ‘yar iska ai da ke na aura. Yarinya ce mai asali da tarbiya wacce mutunci, zumunci da kawaici irin na iyayenmu yasa na sameta, in ban da haka da iya shegen da kuka koya min a bariki yasa na rasata. To sai na yi sa’a iyayenmu mutanen kirki ne, zumuncinsu ya kan fiye musu komai, shi yasa na sameta. Yarinya ce ‘yar qarama, don ba ta fi sha bakwai ba”. Ta ja tsaki ta ce, “Mai abin kunya, kai kuma irin lalacewar da ta same ka kenan bin yara ‘yan qanana sa’o’in ‘ya’yan cikinka? Ina tausayin wannan yarinyar da ka je ka baiwa ubanta kuxi ya baka ita”. Ya yi kamar maganar tata ba ta soke shi ba, ya daure ya haxiye sai ya ce mata, “To, quruciya ai ba qarya bane Jennifer, in ka bi mai ita kuma baka yi laifi ba, ba ga shi nima kin manne min ba, ni ina bin wasu ne ai kema kina bina kina dangwala tunda ni dai na san ni ba sa’anki bane kin girmeni”. A fusace qwarai ta ce mishi, “Haihuwar ka na yi ba girma ba”. Sani dake gefe yana jinsu ya yi qoqarin danne dariyarshi, ya yin da Mus’ab ya ci gaba da magana. “Ai ya riga ya bayyana kin san in ya riga ya zo shaf-shaf bai voye shi”. Ta ce, “Eh, ai na ce kai na haifa”. “A’a, ni kam ai kin yi kaxan ko in ce baki isa ba, ni ai masu mutunci ne suka haifan, gamuwa daku ne ya yi sanadin da na zama haka. Amma mai shekaru irin nawa dai kam talatin da biyar na san ba za ki rasa shi ba a qauye an barwa iyaye”. “Kai Mus’ab wai meye haka ne? Ina laifin Jennifer da ta zo gidan nan ta nuna kishinta kan auren da ka yi, ai qauna ce ta kawo hakan. Maimakon kawai ka ba ta haquri ka yi mata alqawarin auren naka ba zai kawo qarshen mu’amalar dake tsakaninku ba?” Ta yi maza ta ce, “Qyale shi kawai Sani, laifina ne da na zo gidanshi, ba ya yi aure ba? Ai gara ya wulaqantani, ni dai na san auren shirme ya yi don babu inda zai je, biki ne kawai don ba za ka tava daina neman mata ba ya riga ya zama jinin jikinka haka za ka mutu”. “A’a-a’a!” Sani ya tsoma baki. “Ke Jennifer…..” Kafin ya yi magana sai Mus’ab ya ce mata, “Eh, na ji ba zan daina neman mata ba, to amma ai zan iya daina neman tsofaffi ko in koma neman yara sa’o’in matata, ai na samu ci gaba idan na yi hakan”. Mus’ab ya ci gaba da harkokinshi na sharholiya kamar yanda dama ya saba. ‘Yammata sai wacce ya zava, ita kanta Jennifer da suka yiwa juna cin mutunci sun sake shiryawa, suka mannewa juna har ta dawo gidaan shi da kwana. Sai dai hakan bai hana shi yin wasu ‘yammatan baa, sai dai baya kawo su gida ya kan yi harkokinshi ne in ya fita yawon shi na qa’ida. A garin Misau kuwa, fiye da wata guda ne da tafiyar Mus’ab ko waya baya yiwa Saddiqa balle wani aike. Inna Habiba ta rasa inda za ta vullowa al’amarin. “An xauki auren yarinya an ba shi ya tafi ya yi banza da ita, rabon da ya xauke qafa zuwa gida haka ai an daxe. To ya samu yanda yake so an damqa mishi auren da bai san darajarshi ba, shi yasaa na yi ta fatan ya zo gabana in titsiyeshi ya saki auren don kar ya tafi ya barta da auren shi a kanta hakan bai yiwo ba, ba kuma wani ne yaja min wannan vacin ran ba illa Yaya Gixe, ya kuma zuba ido yana kallo ba zai neme shi don a sana bin da ake ciki ba, babu kuma wanda ya san ranar dawowar shi”. “Assalamu alaikum”. Muryar da ta yi sallama daga cikin zauren ita ce ta yi dalilin katsewar tunanin zucin nata tare da haifar mata da faxuwar gaba. Cikin nutsuwa ta kalli Saddiqa da suke zaune tare tana zanen lallenta, ta ce, “Kamar muryar Yaaya Gixe?” Da sauri Saddiqa ta miqe ta fita, ta dawo ta ce, “Ai kuwa dai shine Gwaggo”. Ta yi maza ta shuri tabarma ta nufi zauren don yi mishi shimfixa tana faxin “Yaya sannu da zuwa”. Sai ga Abu ta shigo da xan qunshinta a hannu. Inna Habiba tana gaisheta tana kallon qunshin nata. Ta wuce ta barsu tare da xan’waunta. “Yanzu nan Habiba har yanzu zaman yarinyar nan a gabanki bai isheki ba, kwana wajen arba’in da tafiyar yaron nan amma baki yi tunanin bari ki tura mishi matarshi ba?” “Bai fa damu da auren ba Yaya, don bai san darajarshi ba, dama duk kai kawon da yake yi na a bashin ne kawai, amma tunda aka ba shi ya sake nuna damuwarshi a kanta ne? Sau nawa ina cewa ya zo ya qi?” “Ai ya san halinki ne, ya san in ya zo gabanki ba za ki yi mishi adalci ba. Yanzu zuwa na yi ki gaya min me kike ciki?” “To yanzu dai ina wani adashi ne nake

Chapter 11 of 24