Share this page
“Ke tashi sakarya mara zuciya, kin kwanta kin saki jiki kin hangame baki kina ta yin bacci sai ka ce ba da vacin rai kika kwanta ba”. Saddiqa ta ce, “Kai Avbu kenan, sai ka ce ba tare muka yi baccin ba”. “Tashi ni mu shirya mu tafi”. Saddiqa ta yi maza ta miqe. “Fita ki tambayi matar gidan ko an kawo mana motar?” Ta fita tana magana da Abida, ita kuwa sai kallon Saddiqa take yi cikin sha’awa. Gasu nan dai a falo yanzu suka dawo bari in tambayesu. Ta ce, “To”. Ta koma xaki tana yiwa Abu bayani, ita kuma Abida ta nufi falon mijinta ta gaya musu tambayar da Abu ke yi. A hankali Mus’ab ya buxaa baki ya ce, “Xan kira mana ita Abun”. Ta ce, “To”. Ta tafi. Idris da Sani suka gaisheta ta amsa, ta qi amsa ta Mus’ab. “Haba Abu, ai tamu dake ba ta vaci, muna ‘yar haka dake ne? Ai Aisha ce ya kamata ta yi fushi dani, ke kuma sai ki haxamu ki yi mana faxa ki sasantamu ki ce mu zauna lafiya, tunda na saba jinki kina cewa shi aure sasanta shi ake yi ba lalatawa ba”. Da sauri ta ce, “Ba irin naka auren ba, ai kaimaa baka nufin yinshi, mai nufin yin aure ba zai yi wannan abin da kake yi ba, tunda dai duniya ka tasa a gaba ai sai ka je ka yi ta yi, amma Saddiqa kam zan mayarwa uwarta da ita, don suna kuka aka raba su ta kuma roqeni in har na ga ba daidai ba kar in bar Saddiqa don ba za ta iya da kai ba”. Sani ya yi murmushi ya ce, “Haba Abu…..” Kan ya yi maganar da zai yi ta yi maza ta kwave shi, ta ce, “Kul! Kar ka ce za ka ce min komai, ina ce ku dukanku iya shegen kuka tasa a gaba, ai ina ganin lokacin da ka dawo. To ko varawo ne ya dawo gidanshi a wannan lokacin ai yaa isa lalaataccen varawo”. Idris ya ce, “Gaskiyaa ne Abu, ita wannan rayuwar ai ba rayuwa ba ce, yaushe za a haxa matan bariki da matan da kuka bamu?” Abu ta ji daxin zancen shi, ta saki jiki suka yi ta hira. Ta kwashe bayani duk ta yi mishi, tun daga ranar da Mus’ab ya zo gidanta da zancen neman auren Saddiqa, har kawo barowarsu gida jiya da abin da ta zo ta tarar a nashi gidan, wanda idonsu ya ganar musu ba ta rage komai ba sai da ta gaya mishi. Cikin nutsuwaa ya ce mata, “Ya gayaa min Abu, saboda shima ya san bai kyauta a. to amma kuma abin da ya yin bai kai na ki tafi mishi da maatarshi ba, ki yi haquri”. Ta yi maza ta ce, “A’a, abin da ya kamaceni kenan in yi adalci a tsakaninsu, ba za ta iya da shi ba ya fi qarfinta, baqin ciki kawai zai yi ta qunsa mata, yarinya ce ‘yar qarama”. Idris ya ce, “Na ganta ai”. Ta yi maza ta ce, “Yauwa, to wannan randa ya ce zai yi mata irin dukan da na ga ya yiwa wata jiya ai falle-falle za a xauke ta. Amma da yake ita wancan xin mai qoqari ce sai na ga ta fito da qafarta tinqis-tinqis har tana iya magana”. “To amma Abu”……. Abun ta yi maza ta kalli Mus’ab ta ce, “Kai kar fa ka ce za ka rinqa tsoma min baki”. Ya yi maza ya yi shiru. Idris ya ce, “To ki yi min wata alfarmaa mana”. Abu ta ce, “Ta mene ne in ji in zan iya”. A hankali ya ce, “Za ki iya, so nake ki bar maganar tafiya a yau ki haqura har zuwa jibi, ke da kanki kin ce yarinyar nan a jigace take, ke kanki ba ta fiki jigata ba. To ku xan hutaa mana kafin ku tafi”. Ta ce, “To sai dai gobe, amma jibi kam ya yi yawa”. Ya ce, “To na gode, Ubangiji ya saka da alheri”. Ta ce, “Amin”. Da yamma Abida tana aikin abincin dare, ta bari ta leqa xakin da su Abu suke ta kira Saddiqa. “Aisha ko za ki fito ki xan taimaka min ne?” Cikin sauri ta tashi ta fito suka shiga kicin xin tare suna aikin tare da hirar da Abida ce mai kawo zancen, ita amsa ne kawai nata shima a taqaice. Zirga-zirgar Umar ta dame su, Saddiqa tasa hannu ta xauke shi ta goya shi suka ci gaba da aikinsu. Idris ya shigo kicin xin riqe da ledar yankakkun kaji, Abida ta karva tana yi mishi sannu. Ya yi murmushi ya ce, “Amaryar kike sawa aiki? To bari in kira angonta ya ganta”. Saddiqa tana jin haka ta yi maza ta bar kicin xin ta xauka da gaske kiran nashi zai yi. Abida ta ce, “To ai sai ka shigo ka tayani tunda ka korar min ita”. “Haba Abida, ai sai Abu ta ce yanda kika ga damaa kike juyani”. Abu dake kusa bai sani ba ta yi maza ta ce, “Ai gara maka haka, a juya kan da wannan tanbaxa da su Mus’ab suke yi”. Da daddare bayan cin abinci Mus’ab da Idris suna tare da Abu, saqarta take yi tare da sauraron bayanin nasu. “Haba Abu, ki taimaakeni mana irin taimakon da na saba ganin kina yi min, kar ki tafi min da Aisha ki yi haquri ki samu kwanaki biyar zuwa bakwai don ki rarrasar min ita. Shi Kawuna da ya ce zai kawo min ita ai bai ce miki in kinga ba daidai baa ki mai da ita, ke kin san ba zan cuceta ba, don kin fi kowa sanin ina sonta, don haka ki taimakeni ki rufa min asiri”. Ta harare shi ta ce, “In yi qarya kenan?” Idris ya karve da cewa, “Ba qarya bane Abu gyara ne, ai kinga ni bana goyon bayan abin da yake yi, zan sa miki ido a kan zaman ina ganin ba daidai ba ko somi-somin wulaqanci zan sata a mota in kawo miki ita har gida Misau, don ba ta cancanci ganin irin wannan baqin cikin ba”. Abu ta yi shiru cikin nazari, zuwa can ta ce mishi, “Kai a’a, ba zan iya barinta ba, na kuma roqeka kaima kamar yanda ka ce min in yi maka alfarma in qara kwana, to nima ka yi min alfarma ka kawo min motar da za ta mai damu gida gobe”. Da sauri ya ce mata, “Cikin yardar Ubangiji zan kawo muku”. Ta ce, “To, na gode”. Ta miqe ta shiga ciki ta barsu a nan. Ya kalli Mus’ab cikin nutsuwa ya ce mishi, “In har baka samu wata hanya ta hanasu tafiya ba zan ba da motar da za ta mai dasu, saboda ba zan yarda in vata mata ba, saboda tsohuwa ce mai mutunci da addini”. Mus’ab ya yi shiru sai dai hakan bai hanasu ci gaba da tattaunawa ba. Washe gari da asuba daga fitowarsu daga masallaci ya bar unguwar a cikin motarshi, daga Idris har matarshi dama Abun sunyi zaton bai son ganin tafiyarsu ne yasa ya yi hakan. Suna ciki suna shirye-shiryensu na lodin tsarabar da Idris ya yi musu, ga kuma Abida da take ta yi musu girke-girken da wai za su riqe su ci a hanya. Qarfe bakwai da rabi daidai motar da za ta xauke su ta iso aka shiga fitar musu da kaya saboda ba qaramar tsaraba Idris ya yi musu ba. Suna cikin haka sai ga Mus’ab ya iso gidan xauke da limamin babban masallacin garin cikin motarshi, wanda kuma shine kakan Idris. Dattijo mai kimanin shekaru tamanin a duniya, yana riqe da sanda a hannunshi saboda matsalar qafa da yake da ita. Gaba xaya su Idris suka iso wurinshi suna yi mishi sannu da zuwa. “Har baqin namu sunyi harama ne?” Idris ya amsa “Eh, malam ai har sun kammala shiri”. Ya ce, “To ai sai mu xan shiga daga ciki don mu gaisa”. Ya ce, “To”. Ya gayawa Abu ta amince da hakan cikin yanayi na girmamawa. Liman ne kaxai zaune a kan kujera, sauran duka a qasa suke har da Abu suna sauraron shi bayan an gama gaisawar. “Ki yi haquri, ki yi haquri da duk abin da ya yi, mu yi ta addu’a muna roqon Ubangiji ya shirya mana su. Ai abin da ya saura tsakaninmu dasu kenan a yanzu, don haka kar ki tafi mishi da matarshi na roqi wannan alfarmar ina fata za ki yi min ita”. Abu ta gyaxa kai nuna alamar za ta yi tare da faxin “To Allah gafarta malam Ubangiji ya yiwa zuriyarta albarka, ya kuma sa ta gama da duniya lafiya”. Aka ce “Amin”. Sai ya yi tambayar cewa, “Ina yarinyar take?” Abida ta yi maza ta miqe ta shiga ciki ta fito tare da Saddiqa, ta zo ta durqusa ta gaishe shi ya amsa tare da sa mata albarka. Da aka sake nutsuwa sai ya kalli Abu cikin fara’a ya ce, “Kin kawo mishi alheri irin wannan kuma ki ce za ki tafi da shi? Bar mishi ita ai tashi ce, Ubangiji zai daidaita tsakaninsu, mu dai mu yi ta addu’a. in kinga ka dage a kan roqon abu, to kuwa Ubangiji ya yi nufin biya maka buqatarka ne, in ba haka ba, ba ma zai baka ikon ka roqa ba”. Ta sake cewa, “Haka ne”. “Mu yi sallati ga manzon rahama” Liman ya ba da umarni. Nan da nan aka shiga yi, liman ya yi addu’o’i ga ma’auratan dama sauran jama’ar musulmi baki xaya aka shafa. Ya miqe nuna alamar tafiya, Mus’ab ya yi maza ya bishi suka tafi ya mai da shi gida. Abu ta bi bayan Saddiqa zuwa xakin da aka sauke su. “To haka kuma abu ya kasance, wannan dattijo bawan Allah ya zo ya xaure ni da jijiyoyin jikina babu yanda zan yi in yi musu da shi, da dai na san wani yaje xaukowa ai da sammako muka yi muka tafi”. Saddiqa tasa hannu ta share hawayen kukan da take yi. Ta kalli Abu cikin nutsuwa ta ce mata, “Dama shi kike jira, ai tunda kike cewa ya gudu don bai son ganin tafiyarmu na ce miki ba zai gudu ba wani abin yaje yi mu hanzarta tafiya kawai kika qi, kika ce mu tsaya jiran girke-girken da ba ci kike ba. Dama ni Gwaggona ta gaya min cewa babu wanda kike so a cikin jikokinki sai shi”. Ta kama kuka sosai. Abu ta kama salati tana faxin “Ka ji ja’irar yarinya, kamun bakin da za ki yi min kenan? Yanzu a wannan zuwan da na yi me na yi na son Mus’abu? To ban fi son shi ba, gaya min yanda kike so in yi yau na ji”. Ta juya ta fita ta je ta yi alwala ta soma gabatar da sallar walaha saboda sallamar da Idris ya ce mata ya yiwa mai motar a qara natsuwa kafin ta tafi. Ta daxe a zaune tana addu’o’o ya yin da Saddiqa ke kwance lamo a kan shimfixarsu, sai aka leqo aka cewa Abu Idris yana son ganin ta a falo. Ta shafa fatiha ta shiga falon, maimakon Idris Mus’ab ta gani a zaune. Yana ganinta ya yi murmushi alamar samun nutsuwa, ita kuma ta yi maza ta tsuke tata fuskar. “Wane ne mai kiran?” A hankali ya ce mata, “Nini Abu”. Kan ta yi magana ya yi maza ya kai gwiwoyinshi qasa ya durqusa a kansu. “Ki yafe min abin da na yi na laifi kike fushi dani, Abu ban saba irin wannan mu’amalar dake ba. Na yi baqin ciki tare da nadamar al’amurana da na sameki a wurin nan, da kuma na gane fushin da kika yi dani mai yawa ne sai na ji tamkar na tozarta kaina ne, na wulaqanta saboda na gane na qure haqurinki a kaina. Sanina dake tun ina yaro duk wanda ya faxi laifina a gabanki korarshi kike yi, ki ce sharri ake yi min aniyar kowa kuma za ta bishi, in kuma iyayena ne suka faxi laifin nawa tunda su kin san ba masu yin sharri bane a gare ni, sai ki shiga yi musu faxa kina faxin wai komai qanqantar abin da na yi ba za su zauna suyi ta yi min addu’a ba, sai su rinqa taya masu neman vatani su yayata qarya a kaina. To amma wai a irin wannan haqurin naki da qaunarki a gareni na qureki, ni wane irin mutum ne Abu?” Abu ta nemi wuri ta zauna saboda hawayen da suka soma zubo mata tana sharewa da bakin zanin dake yafe a jikinta. “Ban sani ba Mus’abu, ni dai na san kullum ina addu’ar Ubangiji ya shiryeka”. Ta soma kuka sosai. Ya qara matsawa kusa da ita yana rarrashinta, har ya samu ya shawo kanta suka fita waje suna xan takawa. “Ga gidana can Abu mu shiga ki ga irin gyaran da ake yiwa Aisha”. Ta yi maza ta ja ta tsaya, “Kai, a’a, wannan gida naka ai ba zan sake shigarshi ba”. “Babu komai a ciki da za ki gani ya vata miki rai, wurin da Sani ya bari nake gyara mata, shi ya koma cikin garin, dama a can yake ni na kira shi ya dawo nan saboda bana son zaman kaxaici”. Ta ce, “A’a, hali dai da ya zo xaya, amma kai ma ai kai kaxai kake zaune ba”. Ya yi shiru ya qi tanka maganar tata. Da yamma suna zaune a falon da ya ce mata shine na Saddiqan, komai na wurin a kammale yake an gyara shi, an sauya duk wani abin da ya kamata a sanya, wuri ya yi matuqar yin kyau, sai mai shi ake jira ta shiga. Mus’ab xin ne yaje ya lallavo Abun ta zo nan suke hira. “Kar ki damu da maganganunta Abu, ba ki yi komai na fifitani a kanta ba, wurin Inna kawai ta ji wannan maganar cewar kin fi sona a kan kowa. Amma in ba haka ba me kika yi mata? Ita da kike ta rarrashinta ma kina ta tarairayarta, ni kuma kina ta fushi dani kina ta zare min ido, ki kawo ta xakinta kawai Abu sai ki yi tafiyarki gida ki gayawa su Inna kin barmu lafiya, in ina tare da ita ba zan barta ta yi ta wahala ba, balle ta je tana zama da yunwa ko xurarta sai in rinqa yi”. Abu ta yi kamar za ta yi murmushi ta kasa saboda halin da Saddiqa ke ciki na yawan kuka da qin cin abinci yasa ba ta jin daxin zuciyarta, ga kalaman da take ta furtawa na wai son da take yiwa Mus’ab ya hanata yi mata adalci, bayan su dukansu biyun jikokinta ne. “Abu!’ Abu ta yi maza ta katse maganar ta shi ta hanyar faxin, “Ni dai abin da nake so in roqeka shine, duk abin da za ta yi maka na vata rai kar ka ce za ka buge ta”. Ya yi maza ya ce, “Haba Abu, Abu ki daina yi min irin wannan maganar, sai in ga kamar kin xaukeni mara hankali”. Da daddare ranar Abida ta yiwa Abu rakiya aka kai Saddiqa gidan mijinta, babu abin da bai tsaru ba, komai ya yi daxi gwanin sha’awa, ta ko’ina sai qamshi kake ji, ga kuma ni’ima. Abida ta yi musu hira har zuwa goman dare, da za ta tafi kuma Mus’ab ya yi mata kyautar leda mai shaqe da turaruka masu tsadar gaske. Tunda aka shigo da Saddiqa gidan ta nemi wuri ta zauna ba ta sake xaga ido ta kalli wani ba, balle ta ji wani abin gidan ya burgeta, balle ta buxe baki ta amsa wata magana da suke yi mata, balle a samu ta yarda ta ci wani abun da ya kewaye su da shi, sun yi rarrashi har sun gaji. Mus’ab yana zaune kan kujerar roba a qofar gidan, duk da daren ya yi nisa sigarinshi yake sha lokacin da Abu ta fito ta same shi. “Na ce ba”. Ya xaga ido ya kalle ta bayan ya wurgar da sigarin dake hannunshi. “Ko za ka haqura ne kawai in tafi da yarinyar nan in yaso daga baya……..” Bai jira jin daga bayan yanda za ayi ba ya ce mata, “A’a, abu ai don kina nan ne yasa hakan, in mu biyu ne daga ni sai ita na san yanda zan yi da ita, don haka zan shirya miki jibi ki tafi gida”. Ta yi maza ta ce, “Gobe dai, me zan zauna in yi kuma har jibi?” Ya ce, “To shi kenan”. Washegari sun idar da sallar asuba Mus’ab yana kicin yana qoqarin shirya musu abin karyawa, Abu ta leqo ta ganshi a hankali ta ce mishi. “Ban fa san yanda aka yi ba sai na ga yarinyar nan ta gaji ta kwanta har bacci ya xauke ta”. A hankali ya ce mata, “Ta wahala da yawa”. Ta tave baki ta ce, “To ni dai zan tafi duk da zuciyata ta qi yarda ta ji daxin barin yarinyar da zan yi, na kuma kasa yin jarumtakar xaukanta in tafi da ita ba tare da yardarka ba, ko kuma zargin da ta yi min xin ne yake nema ya zama gaskiya a kaina na fifitakan oho!” “Ba ni kika fifita ba Abu, aure kika girmama. In ban da darajar tashin ai ba za a baki ita a ce ki kawo min ba. Amma da yardar Ubangiji ba za ki yi nadamar bar min ita da za ki yi ba, saboda ba zan barta ta shaidi komai daga gareni ba sai alheri”. Ta ce, “To, Ubangiji ya shiryaku”. Ya ce, “Amin”. Saddiqa tana ta sharar barcinta lokacin da Mus’ab ya gama shiryawa Abu tafiyarta zuwa gida, tsaraba mai ximbin yawa ya yi mata, ga maqudan kuxaxe da ya ba ta gami da wasiqu zuwa wurin Kawu Gixe da kuma Baban shi. Qarfe bakwai da minti arba’in dai-dai direban ma’aikatarsu ya iso qofr gidan kamar yanda Mus’abu ya yi mishi umarni, su Abida da Idris suka zowa Abu sallama, suna nan ma motar ta tashi ta tafi. Mus’ab ya koma cikin gida ya yi shirye-shiryen da zai yi na kintsi, ya yi wanka ya shirya cikin qananan kaya coporet wears. Ya shiga wurin Saddiqa daidai lokacin da ta buxe ido. “Kin tashi Aisha?” Ba ta yi mishi magana ba. Ya zauna a bakin gadon yana kallon ta, kanta a sunkuye ba ta xaga ta kalle shi ba, sai dai ta shaqi daddaxan kamshin shi. “Kin rame da yawa Aisha, ga wahalar tafiya, ga shi kin zo kin ga abin da bai kamata ki gani ba, ga kuma zama da yunwa da kike ta yi. Na roqeki ki yi haquri ki mai da komai ba komai ba mu fuskanci abin da ke gabanmu na zaman aure mai daxi. Mu biyu ne dake yanzu a gidan nan, in ban da abubuwa marasa daxi da suka faru da wannan lokacin shine lokaci mafi soyuwa da zaquwar zuwanshi a gareni na ganina tare dake mu biyu kina matsayin matata”. Ta xaga ido ta kalle shi saboda nanata kalmar mu biyun da yake ta yi, idanuwansu suka haxu daidai lokacin da ya furta mata kalmar “Abu ta tafi”. Kurma mishi ihu ta yi, nan take ta mimmiqe ta soma shessheqa tana qoqarin sandarewa tamkar wacce take shirin suma. Dr. Usman ya iso gidan saboda kiran da Mus’ab ya yi mishi, yana tsaye a kanshi ya gama yi mata komai. “Za ta daxe tana baccin, ina kyautata zaton ruwan zai qare kafin ta tashi, za ta xan samu kuzari saboda akwai duk wani abin da take buqata a ciki mun saka”. “To Doctor na gode”. Sai cikin dare ta farka, yana kwance a gefenta. Yana ganin ta tashi zaune shima ya miqe ya zauna yana kallon ta, ya yin da ita kuma ta sunkuyr da kanta qasa hawaye suka soma zuba. Ya yi maza ya ce mata, “Look Aisha, ba fa irin zaman da zamu yi dake ba kenan, don kuwa ba auren qiyayya aka yi mana ba, ina sonki ne kina sona kafin Inna ta gaya miki halina kyakkyawar mu’amala ce a tsakaninmu, zuwan da kika yi kika ga wata a gidana kuma ba yana nufin kin kamani da wani mugun abu bane. Zaman da zamu yi dake ne nan gaba zai zama in kin kama ni da laifi kin kama ni, amma abin da aka gaya miki a kaina na hali ko kika ga na aikata wannan abin da ya shafeni ne ni kaxai, yanzu ne kike da haqqi a kaina, kamar yanda nima nake da shi a kanki, don haka ki yi haquri abin da ya faru a baya ya wuce mu fuskanci wanda yake gabanmu kawai”. Ba ta tanka ba shima bai sake mata magana ba, ya miqe ya nufi banxaki ya haxa ruwan wanka ya gaurayashi da turare mai qamshi, ya fito ya ce mata “Kina da haqqi a kaina, na yarda zan tsare miki shi ko wane iri ne, na yi miki alqawari zan kiyaye. Amma nima zan tsaya in ga kin kiyaye nawa haqqin ko da ba duka ba. Ga ruwan zafi can na zuba miki ki je ki yi wanka”. Shiru ta yi ba ta tanka ba, ba ta kuma nuna alamar za ta yi abin da ya ce ba. Don haka ya naxe hannun riga sai kwai ta ji ya sureta yaje ya tsomata cikin ruwan har da rigar dake jikinta. Ya kama zai tuveta ta qanqame jikinta wuri xaya. Ta ga dai hakan ba zi mata ba, ta yi maza ta qwallara mishi ihu. “Zan yi”. Ya sake ta tare da faxin ya fi sauqi hakan. Ya fita ya barta. Ta gama sanya kayan da ta samu ya ajiye mata ba tare

Chapter 13 of 24