Share this page
yayi unlocking car ɗin ya fita. Sake kallon kanta dan ganin ko dai dagaske akwai abinda tayi da yasa yace bazata shiga wajen ba sedai har lokacin bata ga komai ba, shrugging kafaɗarta tayi koma menene tunda dai ze siyo mata ai shikenan. Kamar yadda tace haka ya siyo, two wrap ɗin kilishi se four cups of strawberry ice cream, buɗe bayan motar yayi ya saka kafin ya shiga mazaunin sa yana miƙa mata wayar ta, karɓar tayi tana faɗin "Thanks Ya Saraki". Smile ya sake mata da yasa ta zaro idanun ta tana juyowa gaba ɗaya ta zubawa fuskar sa ido "Did you just smile Ya? Oh my God kaga kuwa yadda kayi kyau, Lord of universe ni Kisnah". Sosai ta bashi dariya yadda tai maganar wholeheartedly, yanzu ya kuma fahimtar wani abu a tare da ita, she's Frank and open, tana yin abu da iya gaskiyar ta ne ko me za'a yi mata kuwa, kalli dai yanzu abinda tayi kamar wata yarinya ƴar 12-13 years. "Dan Allah smile again Ya Saraki, ina son sake ganin your cute dimple pls". "Shut up, I don't smile you're dreaming". Kwaɓe fuska tayi "Dreaming without sleeping, Allah nidai I see you smile". "See, mafarki kawai kika yi, so nawa mutum be yi bacci ba yake mafarki ma, i too experience that sometimes". "Ban taɓa ji ba amma, kenan nima yanzu nayi mafarkin kana murmushi, amma gaskiya fa kayi kyau a mafarkin". Girgiza kai kawai yayi ya cigaba da tuƙin sa yana tunanin shekarun ta nawa da take da rashin wayo haka, kalla yadda yanzu yayi fooling ɗin ta kuma ta yarda. 'she's just a little spoiled girl'. Ya ayyana a ransa. Cikin haka suka ƙarasa gida ta fito daga motar tareda buɗe baya ta ɗau leda ɗaya wanda ke ɗauke da kilishin da two cups na icecream ɗin ta bar ɗayar a ciki "Ga naka nan Ya, thanks and Good night". Ya Masa rasa me zece se kawai ya tsaya yana kallon ta,  da gaskiyar mutane da ke cewa baka sanin halayyan mutum seka mu'amalan ce shi, kamar dai yarinyar nan, a kallon farko mutum ze concluding zata yi girman kai da ɗagawa, rashin mutunci da dis respect, wanda shima a haka ya kalle ta da farko, sedai yanzu sam ba haka yake gani tattare da ita ba. Maganganun Inusa ne suka dawo masa kansa ranar da ya kawo shi gidan, gyaɗa kai yayi cikin yarda da abinda Inusan ya faɗa kafin ya sa hannu ya ciro ledar ya ɗauka ya wuce ɗakin sa. Ajiye ledar yayi ya ciro icecream ɗin ya saka a fridge haka kilishin dan baya jin wata yunwa yanzu, komawa kan sofa yayi ya zauna tare da jawo wayar da aka bashi yai mata texting "thank you"....................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 17 (8/8/2022 6:50 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________                           Page 1️⃣7️⃣ _______________________📖 Daga wanka ya fito ɗaure da towel a ƙugun sa se ƙarami a kansa da yake tsane gashin sa har ya tabbatar ya gogu kafin ya cire ya ajiye, kan mattress ɗin sa ya zauna tare da janyo jakar da ya zuba kayan mayukan sa ciki ya fito da wanda za shafa ya shafe jikin sa da shi kafin ya ciro mayukan gashin sa kana ya miƙe ya ɗauko madaidaicin mirror ɗin da ya siya tun yana zaune a shago ya ajiye kan sofa ta yadda ze iya ganin komai sannan ya shiga mulke gashin kan sa da su ɗaya bayan ɗaya kafin ya ɗau comb ya shiga taje shi kana yayi styling ɗin shi, sosai gashin yayi kyau ya kwanta kamar wani Balarabe. Wardrobe ya ƙarasa ya ciro wata Black shadda da ya ɗinka tun yana kasuwa tare da Alh Musa, ba wata me tsada bace amma ba ƙaramin kyau tayi masa ba kamar ka sace shi ka gudu, links ɗin sa ya saka a hannun rigar tare da na wuya, farar hular da ya siya yake haɗa shaddar da ita ya ɗauko yasa tare da takalmin da shi kuma Alh Musa ne ya siya masa ranar da ya fara saka shaddar yace ga takalmin ya haɗa dashi se ya fi kyau. Fatabarakallah Ahsanul khaliqeen, kyan da Saraki yayi cikin shaddar ba me faɗuwa da baki bane just imagine it yourself, turarukan da ya siyo jiya ya jawo yana feffesawa dan jin ƙamshin kowanne har ya sami wanda yayi masa ya feshe jikin sa gaba ɗaya kafin ya ajiye ya ɗau daddumar da ya ɗora kan sofa tun kafin ya shiga wanka ya feshe ta da turare itama dan yau juma'a, wayoyin sa ya kwasa ya fita tare da ɗiban canjin 2k ɗin sa na jiya ya fita bayan ya saka wayoyin sa a aljihu. Sosai ma'aikatan gidan suka dinga yaba kyan da yayi shifa'u sedai yayi musu murmushi tare da faɗin ya gode har ya fice daga gidan pray mat ɗin sa rataye kan kafaɗar sa. ****************** "Wannan gayun se ina kuma auta". Murmushi Laylah ta saki jin auta da ummah ta kira ta dashi wanda se tana san tsokanar ta take faɗa, juyawa tayi ta dubi umman da ke zaune kan stool ɗin mirrorn ɗakin Laylahn "Allah umma yau tsokana kike ji kawai, bayan kin san zance gaida Mami ne". "Oh na manta, ashe za'a je gaisuwar surukai ne, to ai ba kya tafi haka ba dama ina da saƙo wajen gimbiyar bari in baki ki tafi mata dashi". Umma ta faɗa tana fita daga ɗakin yayinda ita kuma ta cigaba da gyara ɗaurin ɗankwalin shaddar da take yi, sosai ta ɗaura shi ya zauna kai kace kafa mata shi akai, kallon kanta take yi tun daga sama har ƙasa tare da yabawa da adon nata, turare ta ɗauka me sanyin ƙamshi ta fesa dan bata manta ba Ya Yarima ya taɓa mata faɗan saka turare me ƙarfi. Mayafi ta ɗauka da ya hau da kayan jikin ta ta yafa tare da fita daga ɗakin nata daidai lokacin umma ta fito daga nata ɗakin hannun ta riƙe da leda me dan girma ta miƙa mata "Gashi ki kai mata ki kuma ce ina gaishe ta sosai da sosai". "Insha Allah umma nah, se na dawo". "Allah ya dawo dake lafiya autar umma kuma surukar gimbiya". Da sauri Laylah ta fice daga gidan cikin jin kunyar umman fuskar ta ɗauke da murmushin jin daɗin surukar gimbiya da umma ta kira ta dashi, driver ta saka ya kaita sashen gimbiya Haleematu dan da tazara sosai tsakanin sashen matan sarki dana waziri wanda ita ɗin ɗiya ce wajen wazirin sarki Muhammadu Hasheem II. Da sallama ta shiga turakar gimbiya Haleematu dan tuntuni ta zama ƴar gida da bata neman iso kafin shiga, kan kilisar ta ta sake ta zaune cikin kyakkyawan adon ta dake ɓoye ainahin shekarun ta ya sa ayi mata kallon batakai haka ba alhalin tana cikin shekarun dattijan taka ne yanzu. Da farin ciki gimbiya Haleematu ke amsa gaisuwar Laylah da ta zube gaban ta, ba ƙaramin farin ciki take yi ba a duk lokacin da tayi tozali da yarinyar dan tana ganin ta ne kamar Sarakin ta wanda ba dan wannan ƙaddarar ta sharrin maƙiya ba da tuni yanzu ana batun bikin su ne, Allah ya sani tana son yarinyar saboda irin soyayyar da take gwada wa Sarakin ta wanda ita in har zaka so Saraki to fa ka gama mata komai a duniya. Baya ga haka ita ɗin ɗiyar aminiyar ta ce da bata da kamar ta a duk faɗin garin Giwa da kewayen ta, ga kuma babanta da ya kasance ɗan uwan me martaba kuma wazirin sa me dattako da sanin ya kamata. Karɓar ledar hannun Laylah tayi kana ta sallama kuyangin ta suka shiga hira da Laylahn irin hirar uwa da ɗiyar ta har lokacin Sallah yayi, ko da gimbiya ta shiga yin Sallah ɗakin ta itama Laylah ɗakin kusa da na gimbiyar ta shiga ta gabatar da Tata sallar kana ta fito ta wuce personal kitchen ɗin gimbiyar dake nan falon ta. Abinci ta dafa mata me rai da lafiya tare da lemukan gargajiya da ta san gimbiya tafi son irin su dan ƙarin lafiya da ƙarfin jiki kana ta kwaso ta jera su kan ledar cin abinci da ta shimfiɗa gefen kilisar gimbiyar. Ko da Mami ta fito taga aikin da Laylah tayi ba ƙaramin daɗi taji ba ta dinga saka mata albarka a ranta tana fatan Allah ya dawo mata da Sarakin ta lafiya ayi bikin su dan fa tabbas ɗan nata be fa mata bayan Laylah. Cikin so da ƙauna da kuma shaƙuwar dake tsakanin su suka ci abincin tare suna ɗan taɓa hira jefi jefi har suka gama Laylahn ta kwashe kwanikan zuwa kitchen ta kuma wanke su tare da gyara kitchen ɗin tas. A ranar kam ma'aikatan sashen gimbiya hutu suka yi dan Laylah ce ta sake gyara sashen tare da haɗe shi da sassanyan turaren wuta me shiga rai kana ta shiga ɗakin gimbiyar ta gyara mata wardrobe kafin ta gyara ɗakin gaba ɗaya. Waɗannan halayen na Laylah ke kuma ƙara wa gimbiya son ta Dan duk sanda tazo gidan tofa bata da zama ta dinga hidima da gimbiyar kenan har se ta koma nasu kafin ta huta wanda yanzu ma haka ne. Ko da ta tashi tafiya kaya sosai mami ta haɗa mata har ledoji biyu tare da godiya da sa albarka har suka rabu. Cikin farin ciki ranar Laylah tayi bacci wanda duk take gidan Mamin hakan ke faruwa dan sosai hankalin ta yake kwanciya da ƙaunar da Mamin ke mata har take ji a ranta bata da sauran matsala sets jiran dawowar Saraki dan ta san tabbas fa bashi da wata mata se ita Laylahn gimbiya. *********** Zaune take cikin kyakkyawan garden din ta ta barbaza takardu a gefe gabanta kuwa laptop ɗin tace haka kuma hannun ta riƙe da wayar ta, wannan zaman duk na yin assignment ɗin CON005 ne sedai har fiye da mintina Talatin da zaman nata ba abinda ta fahimta haka ko kan pen bata saka a paper da sunan rubutu ba, dafe kanta tayi tana sauke ajiyar zuciya cikin tsananin damuwa dan zuwa yanzu kam bata san ya zata yi ba wallahi, tayi tayi amma ta kasa gashi ita bata san wani senior ɗin su ba a department ɗin law balle taje ko ɗora ta a hanya ayi, hasalima ko ƴan level ɗin su ba kowa ta sani ba balle ayi maganan saman su. Cikin karaya ta miƙa hannu ɗan sake duba question ɗin a karo na ƙarshe taga ko zata fahimci me za'a yi dan Allah ya sani daga wannan karon in har bata gane ba to ta haƙura ta bar wa Allah kawai, ta tafi da carryover ɗin ta gyara next year. Zaro takardar tayi se taga wasu takardu sun faɗo tare da ita, ɗan tsira wa takardun ido tayi ganin su ɗauke da rubutu alhalin ita tasan bata ajiye paper me rubutu ba se kuma ta kauda kanta ta ɗau wadda take buƙata a lokacin sedai ganin ta itama cike da rubutu yasa ta ɗan yi turus gaban ta na faduwa kafin kuma ta shiga warware ta da sauri har hannun ta na rawa. Cikin sauri ta shiga bin paper da ido wadda ta tabbatar tata ce dan ga sunan ta da ragowar information ɗin ta da ta rubuta nan jikin paper, kamar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi jikin ta ya ɗau rawa kafin ta shiga karanta jerarren rubutun da akayi shi cikin ƙware wa layi bayan layi duk da kuwa takardar bame layika bace Dan plain sheet ce, tsaf ta karanci rubutun gaba da baya sedai ganin be ƙare ba yasa da sauri ta ɗauko papers ɗin da suka faɗi ɗazu ta hau neman continuation ɗin ta ɗora karatun, wasa wasa nan da nan ta gama karantawa kuma se lokacin ta fahimci me malamin ke nufi amma saboda tsabagen mugun ta yadda yayi twisting question ɗin ba za ka taɓa kawo abinda yake nufi ba kenan. Tsananin murna ne ya kamata har da hawayen ta sosai ta ninke takardun ta maida cikin textbook ɗin ta se kuma ta shiga tunanin waye ya amsa mata question ɗin, ita dai in bata manta ba har jiya da ta shiga test bata rubuta ko A ba bayan question, kuma tun da ta fita da littafin ba wanda ta bawa haka kuma tun da ta dawo dasu ta kai ɗaki bata kuma ɗauko su ba se yanzu haka kuma ba wanda ke shigar mata ɗaki balle tace. "Yaa Saraki". Sunan yai ringing a mind ɗin ta, ɗan shiru tayi kafin kuma ta shiga gyaɗa kanta cikin yadda da shi ɗin ne yayi mata dan tun a motar ta bar littafin da zata shiga test se jotter kaɗai ta shiga dashi ta koya wa su Meenah abin da tayo research haka kuma da ta shiga Company a mota ta bar su gaba ɗaya wanda tun da ta ɗebe su daga motar da suka dawo daga Company bata kuma fito dasu ba se yanzu, to in bashi bane waye yayi mata, aljanu ko wa? Kai shine ma, wallahi shine. Da sauri ta kwashi takardun ta fita daga garden ɗin ta shigo ta main falo kafin ta sake fita da gudu gudu ta ƙarara compound ɗin tana ƙwala masa kira, sosai ta ke kiran shi not minding yadda ragowar workers suke binta da kallo, Isa me bawa flowers ruwa ne ya shaida mata ai yaje masallaci, bata ji daɗi ba dan ta so ta sake shi yayi mata confirming shine ta kuma gode masa sedai zata jira ya dawo. Juya wa tayi zata koma ya turo ƙaramar ƙofar gate ɗin ya shigo da sallama a bakin sa, da sauri ta juya dan da ɗan karfi yayi sallamar hakan yasa itama ta ji, da gudu ta nufe shi wanda shi dan be lura da tahowar ta ba se ji yayi an faɗa kan sa da ƙarfi, ƙamshin turaren ta ne yasa ya gane ita ce ya kuwa yi saurin janye jikinsu a yana istigfar a ransa yan kuma haɗe fuska a fili. Sakin baki tsirarun ma'aikatan dake kaikawo a compound ɗin suka yi suna bin su da kallo kasancewar da yawa sun tafi sallar juma'a, bata ko bi ta kan su ba ta ɗago tana kallon Saraki da ya haɗe rai cif sedai ita ko a kwalbar rigar ta dan bata ma san abinda tayi ya haɗe rai ba kuma dama ya saba kusan ko da yaushe haka yake haɗe rai in Yana tare da ita so shiyasa ma bata wani damu ba. "Yaa kai kayi min assignment ko, daama wallahi na kasa yi kaga tun da safe nake zaune amma ko fahimtar question ɗin ban yi ba, Nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi ya ja da ran iyayen ka, Nagode sosai, kai ban ma san ta ya zance maka Nagode ba wallahi". Ta faɗa sounding very very happy, addu'ar da tayiwa iyayen sa a ƙarshe ya sa ya ɗan sassauta haɗe ran da yayi yana kuma tausar kan sa da ita hakan a wajen ta bakomai ba ne and he promised to transform her so be kamata ya dinga haɗe rai haka ba dole ta nasiha ce yi mata musamman irin wannan lokutan da take cikin farin ciki. "Kalli, ƙafar ki ko takalmi babu kika fito". "Yaa bazaka gane farin cikin da nake ji ba, I feel like in yi ta rawa har se na gaji". "So in kikayi rawa se a san kina farin ciki kenan? Wat of kiyi alwala kiyi sallah raka'a biyu ki gode wa Allah da yakawo miki ɗauki lokacin da kika yi giving up? A tunani na hakan se fi ko?". "Sure hakan zan yi riƙe takardun nan bari kaga in ma je inyi yanzu da sauri". Ta faɗa tana sama sa takardun a hannun sa kafin tayi cikin gida da gudu, girgiza kai yayi ya wuce ɗakin sa bayan ya sake haɗe rai ganin yadda gana ɗaya ma'aikatan compound ɗin suka saki aikin su suka maida hankalinsu kan su. Zama yayi kan sofa bayan ya shigo ɗakin ya cire hular kansa ya ajiye tare da pray mat ɗin kana ya wuce wajen fridge dan ciro ruwa se kuma ya ci karo da ledar kilishin jiya da cups ɗin icecream, fasa ciro ruwan yayi ya ɗauki cup ɗaya na icecream ɗin ya koma kan sofar ya shiga sha a hankali har ya ƙarar kafin ya jefa cup ɗin cikin ƙaramin waste bin dake gefen ƙofar ɗakin. Bum yaji an faɗo Masa ɗaki without taking excuse hakan yasa ya ɗago da sauri dan ganin waye se kuma ya ci karo da fuskar ta tana sake masa kyakkyawan smile, ɗan yamutsa fuska yayi dan Allah ya sani ya fara takura "Me kika zo yi nan". "Ya kai fa nazo nema, kaga tun da kayi min assignment ɗin dama akwai test ɗin da Zamuyi gobe kuma kaga akwai abubuwan da ban iya ba acikin shine na ɗauko ka koya min, laah na manta ban faɗa maka ba nayi sallar na godewa Allah kamar yadda kace". Ɗan dafe kansa yayi saboda tsabar surutunta da har ta fara samasa ciwon kai "Ki kwashi litattafan ki gobe na koya miki". "Yaa ai gobe ne test ɗin fa". "To kai na ciwo yake, ya zan miki ne, a'ah". Jikin ta ne yayi sanyi jin yace kan sa na ciwo, kwashe takardun ta da ya ajiye kan sofa a gefen sa tayi tare da juyawa zata fita "Sorry yaa, ban sani bane Allah ya baka lafiya". Dan tsaki yayi kafin ya dakatar da ita "A ina zamu yi karatun dan ba dai a ɗakin nan ba". Da sauri ta juyo cikin farin ciki se kuma ta ɗan rage fara'a "Baka ce kanka na ciwo ba". "Out in bakya buƙata". "To muyi a garden ɗina ko main garden gashi can ta gefen gate". "Meet me there a main garden ɗin by 3pm". Da sauri ta amsa da toh kafin ta fita cikin jin daɗi....................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 18 (8/9/2022 8:06 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________                           Page 1️⃣8️⃣ ______________________📖 Kamar yadda yace haka ta sake shi a main garden ɗin gidan by 3pm suka soma karatun, ba ƙaramin yabawa ƙoƙarin ta yayi ba a zuciyar sa ganin duk abinda ya koya mata take ta ke kwashe shi dama akace kabar abinda zuciya ke so. Itama a nata ɓangaren haka tai ta yaba yadda yake mata bayani dalla dalla cike da ƙwarewa da sanin malamar karatu, sosai ta kasa daurewa har ta kai ga furta masa abinda yake yawo a ranta "Yaa wai ya akayi ka iya karatun mu haka sosai, ko dai kaima law ka karanta?". Shiru yayi mata a lokacin dan be san amsar da ze bata ba, be shirya sanar da wani asalin sa ba haka ne shirya tattauna personal life ɗin sa da outsider ba Kai koma insider ɗin ne he's not interested balle kuma ita da yanzu ne yake kan sanin wacece ita. "Amma kuma me yasa baka nemi aiki ba tun da nasan ka gama karatun ka da alama". Ta sake faɗa dan ta ɗau shirun sa as yes eh law ya karanta "I was withdrawn from the school". Ya  sami bakin sa da faɗa dan alamu sun nuna Yes cikakkiyar lawyer ɗin za'a yi a wajen, shikuma ba ya san duk abinda ze kawo ta zarge shi kan abinda ba haka bane. "Eyya, so sad amma akan me?". Ta sake tambaya further Dan dai tasan baze yiwu ace akan bashi da ƙoƙari bane se dai something different da take son sani dan daga yadda yake mata bayani ta tabbatar a lokacin da yana makaranta ba za'a rasa sashi cikin gifted and talented students ba. "Don't wanna talk about it now". Gyaɗa kanta tayi cikin nuna fahimta kafin tace "I understand, maybe later ko?". Ɗaya mata gira kawai yayi dan ya fahimci in ba haka yayi mata ba ba ƙyaleshi zata yi ba alhalin taɓo maganar makaranta da karatu da tayi yasa yaji incident ɗin da ya faru ya dawo masa sabo Dan if not because of it da tuni i yanzu yana zaune in his own office handling office stuffs. Ba su tashi daga karatun ba se da aka kira Asr prayer hakan ma dan ya tashi ne ba yadda zata yi dashi dan in ta ita ne  bata ƙi sukai har magrib ba yana koya mata tana kuma ƙiriniyar tambaye tambaye abinda babu ruwan ta be kuma shafe ta ba. Kashegari har bakin ƙofar lecture hall ɗin su ya kai ta tare da mata addu'ar fatan nasara abinda ya saka Kisnah dakatawa ta ƙura masa ido for a while kafin ta gyaɗa masa kai idon ta na kawo ƙwalla, abu ne tunda ta taso zata ce ba wanda ya taɓa damuwa da yi mata wato fatan alkhairi da nasara in zata yi assignment, test ko exam. To wa ma take dashi bayan kawu da family ɗin sa? Se ko abokan Abbu da ta manta rabon da ta taka ƙafarsa gidan su haka suma tuni suka dena damuwa da neman ta tun bayan wani cin mutunci da kawu ya yi musu lokacin da ya kaita England karatun primary ita kaɗai shikenan duk suka zare hannayen su a kanta. Kawu da matar sa Mommy kuwa.. hmmm.....bata masan ya zata kwatan ta su ba, ta wani ɓangaren the two are perfectly synonyms of each other, in other views Kuma su ɗin antagonist wa juna. Suna da matuƙar close similarities ta ɓangaren tsananin son kuɗi da kwaɗayi sedai suna da bambanci wajen tsananin son ƴaƴa da Mommy ke dashi da kuma hassadar da bata ma iya ɓoye ta, munafunci da baƙin ciki kuwa wajen Mommy har na siyarwa akwai, to taya ma zata yi wani tunanin samun fatan nasara ga matar da a kullum so take taga bayan ta ko kuwa ga kawu da kullum hankalin sa na kan yadda za sami kuɗi ta kowace hanya. Bayan su waye a cikin rayuwar ta? Ƙawayen ta, yes ƙawayen ta, taya zata fassara su? Da wa zata fara a ciki? Meenah da ba inda ta dosa a rayuwar ta ban da son holewa, ita dai tayi ta watsa ƙwayar da indai da ita to fa bata da matsala, ko kuwa da Leekha da tsabar shan giya har ya taɓa mata hanta seda akai mata aiki ko kuwa Hameedar da ƙiri ƙiri take iya fahimtar ƙyashi da hassadar ta cikin ido da Muryar ta har ma da ayyukan ta, dama dama Surayya, duk da mugun son mazan ta tana son karatu haka ta kan yi magana ta cikakkun masu hankali in taso bayan ita gaba ɗaya ragowar ukun ita ce ta sauya rayuwar su kan son karatu, a dole suke yin shi ba dan sun so ba shiyasa basa taɓa damuwa da wata matsala a karatun nasu wanda duk aka samu akasi ita ke yin tsayin daka har se ta tabbatar komai ya koma daidai kuma yana tafiya yadda ya kamata. Ajiyar zuciya tayi kafin ta saka yarda ta ɗauke ɗigon hawayen da ya sauka daga idon ta tana ƙarasa shigewa hall ɗin, sama sama ta gaida da ƙawayen nata kafin ta maida hankali kan littafin da ta shigo dashi wanda ta fara rage karatun exams ɗin da zasu fara ne next week insha Allah, tana jin su suna hira sedai bata ma maida hankali ba balle ta fahimci akan mene suke hirar. Cikin haka halitta ɗaya da zata iya kalla tace ta tsana a duniyar ta ya shigo cikin hall ɗin,

Chapter 11 of 27