a wajen da yayi yaki biyu sedai be juyo ba hakan yasa ta sha gaban sa da sauri tana ƙwalƙwal da ido tare da langaɓar da kai
"Am sorry Ya, Dan Allah kayi haƙuri".
Shiru yayi yana kallon fuskar ta kamar me son gano wani abu a cikin ta kafin ya magantu
"Sorry? For what? Me kika min na haƙuri kuma?".
"Ni dai am sorry please".
Jijiga kansa yayi
"A sani na ana bada haƙuri ne in anyi laifi, nikuma ban san kinyi wani laifi ba". Ya faɗa yana shirin ratse ta ya wuce, da sauri ta maza ta ruƙo hannun sa
"Amma Ya fushi fa kake sani shiyasa na baka haƙuri".
"Fushi akan me, kawai se in kama fushi ba Amin komai ba kamar mahaukaci, Ni bana fushi da ke".
"Allah ya fushi kake yi".
Wannan a ɗan kausashe ya fisge hannun sa
"Na faɗa miki ni bana fushi dake so Please leave me alone, I wanna sleep".
Ya faɗa yana yin gaba da sauri, itama da saurin ta biyo shi tana share hawayen da ya zubo mata
"Am sorry for that night yaa, am sorry for the dress, am sorry for everything please".
Ta faɗa Muryar ta na breaking saboda kukan da ya taho mata, tsaya wa yayi jin abinda take faɗa, sosai yaji daɗi a ransa ganin ta san abinda tai kenan tunda gashi ta faɗa da bakin ta sedai not so easy like this, baze haƙura da sauri ba ko dan gaba dan haka se ya ɗan yi ƙaramin tsaki ya juyo a masifance
"See I have nothing to do with your night partying or whatever and also your dressings, this life's so simple, so easy and you have the right to live your life as you wish, as you want and as you plan, am not your father nor your brother, we have no any blood ties or something, am only driver, a mere driver whom you paid to serve you, and am doing that, you also payed me, so I have nothing to do with your life, please am sleepy, make you go live me rest".
Ya ƙarashe cikin pidgin Yana wuce wa gaba ya bar ta a wajen sororo tana bin bayan sa da kallo har ya ƙure mata kafin ta sulale ƙasa, ba kuka take ba dan kafin abu yasa ta kuka ana daɗe wa, tasowar ta batare da kowa a tare da ita ba da sunan family yasa ta zama strong, very strong da ba ƙaramin abu ke sa hawaye forming a idon ta ba, hakan yasa yanzu ma bata yi kuka ba se dai tana jin zafi, zafin yadda ya faɗa mata magana, yadda ya tafiyar sa ya barta jama'a na kallon ta duk da tasan kowa a wajen sabgar sa yake ba wanda ya damu da wani amma ta ji haushi ta kuma ji zafi.
A hankali ta tashi tana kakkaɓe yashin jikin ta kafin tayi making up mind ɗin ta, he said she should leave him and she'll, he said she should live her life as she want Kuma zata yi amd she'll show no concern to him or everything related to him, zata nuna masa she had a heart a ƙirjin ta, a very strong heart.
Da wannan tunanin ta koma ɗakin su inda ta same su zaune anata raha da dariya.
Zama tayi cikin su itama dan ba zata ɓata ranta saboda shi ba ehe, nan sukai ta kallo ana hira har se to one kafin Deeq ya musu sallama ya tafi nasa ɗakin suma kowa ya shige bedroom ɗin sa.
Kashegari da safe ko da suka shirya motar Deeq suka shige suka fita gaba ɗaya, yawo sosai suka sha dan ya zazzagaya da su wurare sosai, they had a lot of fun together, sun yi hotuna sosai haka basu suka dawo ba se after twelve hakan yasa ranar basu haɗu ba gaba ɗaya.
Washegari basu fita da wuri ba se two da su Hameedah suka matsa mata shiga cinemar dake cikin resort ɗin wai kallon wani American Film, sam ita bata ra'ayin anything Hollywood Amma haka dole suka takura mata shiyasa kawai ta haƙura ta bisu se gashi to her surprise film ɗin ya burge ta over.
Two hours film ɗin yayi lasting kafin suka fito duk ta gaji ga yunwa da take ji se dariya suke mata wai Madam food amma ko kallon su bata yi ba ta faɗa restaurant ɗin gurin ta nemi table ta zauna tare da kiran waiter ta ticking abinda take so kafin ta koma cikin kujerar ta lafe tana jiran a kawo.
Sosai ta maida hankalin ta kan abincin har ta cinye French rice ɗin kafin ta koma kan grilled chicken ɗin ta hau ci, hannu ta sa ta kuma ɗauki wani part ɗin zata kai baki kamr an ce ta ɗago suka haɗa ido, sosai ta haɗe rai ta ɗauke nata idon daga kan sa ta cigaba da cin abincin ta, shima ganin haka se kawai yayi smiling Yana ƙara sa plate ɗin gaban sa.
Tissue ta saka ta goge hannun ta kafin ta dau wayar ta tana niyyar miƙewa taji zaman shi kan kujerar gefen ta
"Good evening beautiful".
Ko kallon sa bata yi ba ta ƙarara tura wayar ta cikin aljihu ta juya zata tafi yai azamar ruƙo hannun ta wanda yasa dole ta tsaya kafin kuma tai masa kallon da yasa ya sakar mata hannun ta ba shiri.
Ita tarasa wannan wane irin mayen mutumi ne, tun jiya da suka haɗu dashi a park ya nace mata, ko kallon shi ta ƙiyi akan hakan be sa ya fasa Binta duk inda tayi ba, zata iya rantse wa har a cinema da ta kula da kyau se ta ganshi.
"Am sorry pretty, ba binki nake yi ba nima nazo hutu resort ɗin nan ne, You know aikin banki da takura shiyasa tun da nasamu na gudu shine na ɓuya a nan dan kasan ba wanda ze san ina nan".
"Ni zan sanar kana nan ko dan ka Dena takura min ai".
Dariya yayi ya biya suka jera suna fita daga restaurant ɗin tare
"Am sorry kar ki faɗa Please, kinga Daddy yasan ina nan se yayi kilishi da namana yasin, oh Rabb mu Dad is fire wallahi".
Dariya ya bata sosai ganin yadda yake wani malƙawaya hannu yana kwatanta wa da yadda ya haɗe rai wai kamar yadda Dad ɗin sa ke yi.
Shima dariyar yayi suna tafe yana mata hira har yake faɗa mata yana room 52 ne, jijjiga kai tayi jin ɗaki biyu ne kawai ya raba su, ASAD as he said his name was, is a handsome guy me cike da barkwanci da fara'a hakan ke daɗa ƙara masa kyau, cikin some minutes se gashi yasa Kisnah ta saki jiki dashi though dama bata da wuyar sabo sedai in ba'a iya zama da ita ba.
Seda ya rakata har ƙofar ɗakin su ta shige kafin ya wuce nasa cike da tuna mata da alƙawarin haɗuwar su a playground za suyi basket ball...........✍️.
©️ Ouummey 📚✍️.
☑️ Ote, comment and share fisabilillah.
Ouummey 22 (8/13/2022 8:50 PM )
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 2️⃣2️⃣
________________________📖 ƙarfe bakwai yau ma suka shirya suka fice sedai tun a hanya suka raba hanya dan su football za suyi ita kuma za suyi basketball da Asad.
Sport wears ne a jikin su, Hameedah da Surayya suna team ɗaya #team_red yayin da Meenah da Leekha suke team ɗaya #team_blue haka suka raba kan su based on color ɗin sport wears ɗin nasu.
Ita kam Kisnah Black sport wears ta saka wandan daidai gwiwa rigar me ɗan tsayin hannu shima iya gwiwar hannun se scarf da ta saka ta ɗaure kan ta da be iya rufe gashin ba gaba ɗaya, takalmin ƙafar ta kuma fari ne tas kamar dai na jiya.
Tun da ta doso filin Asad ya sake ball ɗin hannun sa ya kafe ta da ido, ya Salam this girl is really pretty, her eyes, her lips, her eyelids, her skin, her curves, her hair........her her her Kai! She's just perfect, really perfect in all ways.
Dafa kafaɗar sa da tayi yasa yayi firgigit ya dawo hayyacin sa, kallon fuskar ta yayi kafin ya sake mata smile itama ta maida masa hakan ya kuma saka shi yarda she's just perfect, dan the way she looks when she smiled is so muah.
Ɗauko ball ɗin tayi dan taga alamar shi yana can cikin tunanin abin da bata san meye ba, gaban sa ta dawo riƙe da ball ɗin kafin ta kalle shi
"Ready?". Ɗan murmushi ya saki da ya sashi looking so handsome Dan shima kyakkyawa ne,
"Very ready".
Kallon sa take yi kamar ba zata jefa ball ɗin ba kafin ta mamaye shi ta jefa ball ɗin ta kuma bita da sauri, da sauri shima bita yana son ƙwatar ball ɗin sedai ta ƙi bashi dama daga ƙarshe ma ta buga uban tsalle ta jefa a basket ɗin shi kafin ta dire tana ƙyalƙyala masa dariya har da rawar ta.
Haɗe rai yayi irin yaji haushin nan yayinda cikin ransa farin ciki yake yi ganin yadda take walwala, godiya yake wa Allah da ya haɗa su dan daga cikin dalilan guduwar nasa daga gida har da batun matar aure da ake takura masa dashi.
Cikin wannan tunanin da yake yaga ta jefo mishi ball ɗin ya kuwa cafe kafin shima ya shamma ce ta ya fara buga ball ɗin towards ɓangaren ta, da sauri ta bishi suka shiga bugawa har tayi nasarar ƙwace wa ta koma garin sa da wasan ya biyo ta da sauri tana ta kubce masa har ta daka tsalle zata jefa ya ruƙo ta ta kuwa faɗo ball ɗin tayi gefe ya matsa gurin da sauri ya riƙe, cikin ɗan ɗaga murya Kisnah ke faɗin
"Allah You cheat, wannan cheating ne, ai dai ba a haka kawai se a ruƙo mutum".
Dariya yayi mata haɗe da gwalo ya tafi ragan ta da ball ɗin sedai yana zuwa jefawa itama ta tafi da sauri ta jawo shi ya kuwa yi baya har suna yin gware kafin ya faɗi, da sauri ta ɗauke ball ɗin ta jefa net ɗin shi, kwaɓe fuska yayi ita kuma ta hau yar fa hannaye
"Kaga maganin me yin cuta a wasa, Gashi nan na cinye ka wobul (tayi masa gwalo), kuma na tashi wasan tafiya zanyi football".
"Allah baki isa ki tashi ba, se da kika ga kin cinye ni zaki tashi Allah a'a sedai mu cigaba".
Da sauri ta ruga da gudu tana barin basketball field ɗin heading to football field, da ɗan gudu gudu shima Asad ya bita trying to catch her sedai tuni ta shige cikin masu yin football ɗin da ta ga suna da yawa ba iya su Meenah bane, dole ya haƙura ya koma ya samu seat ya zauna Yana maida nunfashin wasa da kuma gudun da yayi.
Da sauri ta shige field ɗin ta ɗauke madaidaiciyar ball ɗin da suke bugawa, tsayawa duk sukai suna kallon ta kafin Surayya ta nufe ta
"Meye haka Kissy, please give us our ball ki tafi kema ki cigaba da basketball ɗin ki".
"Mun gama ai, nazo yin football ne da ku".
"Then Zaki shiga team ɗin mu ne dan mune seven in number su kuma eight, guys queen Kisnah is joining us, she'll be in our club, so the game will be restarted".
Aikuwa haka kowa ya koma club ɗin shi aka fara afresh, sosai suka maida hankali kan game ɗin kowa yana trying to score for his team, game ɗin ba ƙaramin daɗi tayi musu ba da at last aka tashi 3-1, su Kisnah 3 su Meenah 1 dan fa Surayya ba ƙaramar ƙwalluwa bace a football game.
Kan tables ɗin da ke gaban field ɗin suka zazzauna kowa na maida numfashi kafin su fito da ruwa suka hau sha, ko da suka sha ruwan haka suka cigaba da tsokanar juna, ana tsokanar su Meenah su kuma suna depending if not because, if not of, har goma kafin su tashi suka tafi ɗaki.
Tare da Asad Kisnah ta jera suka wuce floor ɗin yana ta bata labari, his school life, family drama and more tana ta dariya.
Ko da suka je ƙofar ɗakin haka suka taya bakin entrance ɗin suka cigaba da hira har suka shiga firar Indian films tana ta lissafa masa fina finan da ta kalla shima haka
"Kin kalli mother India?".
"No, Amma naji ana yayi kyau so after na bar nan zan neme shi in kalla".
"Yayi kyau over wallahi, ai ina dashi, go and freshen up Nima kafin nan nayi wanka na huta se kizo mu kalla".
"Okay, yanzu kuwa dan har na fara zumuɗi, yauwa room nawa ma?".
"Wai har kin manta?, Jiya fa na gama faɗa miki".
"Kai dai tuna min ina sauri in wanka".
"Room 52 girl".
"Ok, see yha soon Mr Man".
Ta faɗa tana shigewa ɗakin nasu shima ya wuce nasa, a falon ta tadda su Surayya duka suna zaune da alama har sun yi wanka dan sun cire sport wears ɗin, bedroom ɗin ta ta nufa zata shige Meenah ta dakatar da ita da sentence ɗin ta
"Wai Kisnah a ina kika samo mutumin nan da yau gaba ɗaya ya ɗauke hankalin ki daga kan mu da ma Deeq, dan gwara ma Deeq ya je unguwa ze dawo amma daga jiya da muka zo wajen nan zuwa yau a falo kaɗai muke samun zama dake daga mun fita shikenan se kuma mun ganki".
"He's a friend, don't mind".
Haka ta faɗa kafin ta wucewar ta ciki, da ido suka rakata har ta ƙarasa shigewa kafin Surayya tayi saurin canja topic ɗin Leekha na karɓa mata dan kar ma akawo wani batu kan Kisnahn.
Wanka tayi kamar yadda tace masa ta canja kayan ta zuwa guntun wando iya gwiwa da ƴar ƙaramar rigar sa da bata ƙara sa sauka kan cikin ta sosai ba ta kitse jelar kanta tare da kame ƙarshen da ɗan ƙaramin band yadda ba zata since ba dan sosai kan ke da santsi.
Gaba ɗaya nan ta baro wayoyin ta dan bata san tana kallo ana damun ta da kira shiyasa ma ba zata tafi da ko ɗaya ba, adai falon ta kuma tadda su har yanzu suna zaune se dariya suke yi alamun hirar tana kai musu yadda suke so gaban su cike da kayan ciye ciyen da drinks kala kala.
"Se na dawo".
"Ina kuma zaki yanzu?". Wannan karon Leekha ta tambaya, ɗan kallon Leekhan tayi cike da jin haushin yadda suke wani titsiye ta kamar wata ƙaramar yarinya sedai sanin ba halin Leekhan bane hakan se ta mata uzuri yau ɗaya dai
"Ɗakin Asad, akwai Film ɗin da zamu kalla tare a system ɗin shi".
"Why not shi yazo ku kalla a nan?". Hameedah tayi interrupting sedai ko kallon ta Kisnah bata yi ba ta dubi Surayya
"Mind joining us?".
"No, am feeling somehow sleepy, kya bani labari".
Gyaɗa kanta tayi tana ɗagawa Meenah yatsu biyu
"Se na dawo babe".
"Hope you enjoy the movie". Meenah ta amsa mata sannan ta fice, tana fita Surayya ta miƙe ta musu good night ta shige bedroom ɗin ta haka ma Leekha ya saura Hameedah da Meenah, juyowa Hameedah tayi tana kallon Meenah da wani expression on her face yayinda Meenahn ta kau da kai kamar bata gani ba ta mata sallama ta wuce, dole ba dan ta so ba itama ta wuce nata bedroom ɗin dan ba yadda zata yi bayan ta kashe ƙwan ɗakin.
Knocking biyu Kisnah tayi Asad ya buɗe mata ƙofar ɗauke da murmushi a saman fuskar sa yana sanye da three quarter da farar t-shirt da ta kama jikin sa sosai, itama smile ta Masa tare da shiga ɗakin ya maida ƙofar ya rufe.
Kan doguwar sofar dake ɗakin ta zauna tana ɗan miƙe legs ɗin ta, be zauna ba ya wuce wajen fridge ɗin ɗakin ya zubo musu dambun naman dake cikin wani rufaffen madaidaicin container ya Kuma ɗauko drinks ya kawo ya ajiye kan Centre table ɗin da ke falon ya koma ya ɗauko glass cups masu kyau guda biyu ya ajiye sannan ya koma ya ɗauko system ɗin sa dake kan bed kana ya dawo ya janyo table ɗin gaban sofar a hankali kafin ya zauna kusa da Kisnah yana danne danne cikin system ɗin kafin ya ɗago ya dube ta
"Ready?".
Yesssss". Ta faɗa prolonging the 'S' sound.
"Here we go". Ya faɗa yana starting film ɗin sannan ya ɗora kan table ɗin suka shiga kalla.
Tun kafin ayi wani nisa sosai Kisnah ta fara kuka dan sosai Film ɗin yake da abun tausayi, lallashi ne Asad ya sha shi dan kamar wata ƙaramar yarinya haka ta koma, wasa wasa ba Film ɗin ya ƙare ba se after 2 dan it's a 3 hour film, ko da aka gama bata tafi ba wani Indian comedy na Rani Mukherjee me suna Aiya ya saka mata dan lightening mood ɗin ta, cikin ƙanƙanin lokaci kuwa se gashi tana sheƙa dariya kamar ba ita ce ta sha kuka ba, a hankali a hankali bacci yake fisgar ta dan yau ta gaji sosai har ma dai yayi nasarar sace ta gaba ɗaya, gyara mata kwanciya Asad yayi ya cigaba da kallon sa har se da Film ɗin ya ƙare wanda lokacin it's to five am sannan ya fara tashin ta a hankali.
A hankali ta fara buɗe idanun ta ta sauke kan sa, murmushi me sanyi ya yi mata kafin cikin cool and low tune ya Fara mata magana
"Hey sleeping beauty, it's subhi, kije kiyi sallah a ɗakin ki, okay?".
Out of sleep ta gyaɗa masa kai kafin ta fara ƙoƙarin miƙewa sedai dake ba sakin ta baccin yayi ba se ta kasa har se da ya riƙe ta helping her to stand ya kaita har bakin ƙofa sannan ta zare jikin ta tana lumshe masa ido alamun zata iya tafiya, waving ɗin ta yayi ta fita kafin ya maida ƙofar ya tafi toilet dan yin alwala.
Tafiya take a hankali har tana ɗan layi na bacci har ta wuce ɗakin su bata sani ba , daidai lokacin Saraki ya fito dan tafiya masallaci kamar yadda ya saba dan a can yake karatun Alkur'ani tare da nafilolin sa kafin exact lokacin sallah yayi, sosai yayi mamakin ganin ta a wannan lokaci and to his utmost surprise kamar ma layi take alaman bata cikin hayyacin ta sosai.
Kamar ya wuce ta sedai ya kalli ƙofar ɗakin su da ta wuce a baya sosai dan shi yana room 45 ne su suna 50 amms har ta wuce ɗakin nasu tama gota nashi, da sauri ya ƙara sa inda take tare da ruƙo ta dan dakatar da ita, a hankali ta juyo dan fa baccin ne sosai a kanta, ganin shi yasa ta ɗan ware sleepy eyes ɗin ta da suka canja kala zuwa golden brown saboda bacci
"Yaaaaaaa". Ta ja sunan sosai abinda ya sa Saraki kuma shaida ba'a hankalin ta take ba
"Yaaaaaaa ɗakiiii zaaani".
Cikin takaici ya juya ta zuwa hanyar da ta baro hakan yasa ta buɗe idon sosai ta gan a bakin room 43 ma take
"Kaga ban ma san na wuce ɗakin bama, am toooo sleeeepyyy".
Bece mata komai ba har lokacin sedai cikin ransa cewa yake taya zata san ta wuce tunda bata cikin hankalin ta?
Har bakin ƙofar ɗakin nasu ya rakata kuma be tafi ba seda yaga ta shiga cikin parlon kafin ya juya ya koma hanyar da ya baro heading to the elevator.
A falo ranar Kisnah ta kwana dan baya iya kai kanta ɗaki ba saboda nauyin baccin dake kanta, se after seven ta tashi ta koma bedroom ɗin ta ɗora baccin ta daga inda ta tsaya.
Ƙarfe goma ta farka ta shiga wanka sannan ta shirya bayan ta fito, yau kam ba laifi Canadian gown ta saka da yakai mata ƙasa dan har yana jan ƙasa ta baya ta sake gashin ta bayan ta taje shi tare da shafe shi da mayukan kai masu ƙamshi ta feshe shi da turaren gashi ta ɗora masa sun hat me kyau sosai kalar brown Wanda gown ɗin jikin ta milk and brown ce haka takalman ƙafar ta milk heels ne.
Ƙarar wayar ta yasa ta ƙara sa inda ta watsar dasu jiya da dare ta ɗaya wadda take ƙarar ta kai kunnen ta ganin sunan Surry
"Mun fita kina bacci Queen, in Zaki biyo mu muna highway mountain".
"Okay, I'll see in zan zo ɗin".
"Okay". Surry tace tare da kashe wayar.
Zama ta ɗan yi tana tunanin ta bisu ne ko kuwa tayi zaman ta?
"Garden". Kamar daga sama haka sunan ya faɗo cikin ranta, da sauri kuwa ta miƙe dan a rayuwar ta tana matuƙar son guri me korayen ciyayi da bishiyoyi shiyasa tun tana yarinya Abbi yayi mata ƙaton garden a gidan su.
A hankali a hankali take takawa kan corridor ɗin ɗakunan dan sosai marbles ɗin ke da santsin da in batayi taka tsantsan ba ze iya tiƙa ta da ƙasa saboda tsinin takalmin ta, gyaran muryar da taji a bayan ta yasa ta ɗan waiga hakan yasa suka yi four eyes da Saraki da ya fito dan zagaya wa saboda jiya gaba ɗaya a ɗaki ya wuni shiyasa yanzu yake buƙatar fresh air
"Good morning yaaa".
Gyaɗa mata kai yayi alamar amsawa dan yanzu kam ya sauko daga fushin da yake yi dan ganin abinda ya faru jiya yasan da beyi fushi ba da ko yaya ba zai bata space ɗin kwana wani waje ba dan zata kasance ƙarƙashin idon sa ne.
"To where?".
"Garden, won't mind joining me please, am lone".
"Okay". Ya ce mata dan haka suka jera suka cigaba da tafiya, daɗi sosai Kisnah ta ji ganin ya dena fushi da ita haka itama se ta ajiye alwashin ta a gefe.
A tare suka shiga elevator ɗin ɗan yana da faɗi sosai, a third floor suka sauka dan akwai garden me kyau a floor ɗin kafin ta masa jagora zuwa garden ɗin da tun 2 years back ta haddace hanyar shiga cikin sa though an samu sauye sauye a resort ɗin.................✍️.
©️ Ouummey 📚✍️.
☑️Ote, comment and share fisabilillah.
Ouummey 23 (8/17/2022 8:10 PM )
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Assalamualaikum warahmatullah ɗauka cin masoya littafin *SARAKI* daga kowane group most especially*SARAKI FANS CLUB* ina godiya sosai da addu'o'in ku ga ƴar uwa ta , Allah ya saka da alkhairi ya bar ƙauna, Allah kuma ya jiƙan dukkan musulman da suka riga mu gidan gaskiya, marasa lafiya Allah ya basu lafiya, mu da muke da ita Allah ya kara mana ya bamu ikon gode, masa Ameen summa Ameen.
Once again, nagode Allah ya bar zumunci da ƙauna 🥰.
Page 2️⃣3️⃣
_______________________📖 sunkuyar da kanta tayi ƙasa ganin irin kallon da yake watsa mata na rashin yarda kafin ta sake ɗagowa sedai wannan karon idon ta ya ɗan sauya launi
"I swear to God ban Sha komai ba, so nawa zan faɗa maka bana shaye shaye ne yaaa"?".
Ta ƙarashe maganar ranta na suya, a rayuwar ta taƙi jinin shaye shaye shiyasa kullum cikin yiwa su Hameedah faɗa take yi, ita magani ko na rashin lafiya in har ba kwantar da ita tayi ba bata taɓa shan sa, duk kuwa irin ciwon kan da zata yi ko ciki sedai ayi mata allura dan magani is her perfect enemy.
Ɗan furzar da iska yayi daga bakin sa kafin a hankali yayi magana batare da ya kalle ta ba
"What about haɗa hanyar da kika ringa yi jiya da na ganki, me ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 27