Share this page
ya rungume cikin son kare ta ko yaya ne. Wani irin ƙara ce ta tashi lokacin da motar su ta daki wannan tankar haka kuma tayi baya kamar wadda aka tura da mugun gudu kafin ta shiga hantsilawa tayi gefen dajin dake Wajen, seda ta jujjuya sosai kafin ta tsaya, mintuna ƙalilan Saraki ya fara ƙoƙarin ganin ya fito daga motar cikin  dauriya da son ganin mutanen cikin waccan motar basu iske su a wajen ba dan yasan yin hakan tamkar ƙarshen rayuwar su ne yazo. Da ƙyar ya iya fita daga cikin motar kafin ya samu yin dabarar da murfin ɓangaren sa ya buɗe ya zaro Kisnah da take a sume jini na bin fuskar ta, kallon ta ya tsaya yi cikin tunanin yadda de yi da ita dan tabbas baya tantama hannun sa na dama a karye yake dan yana iya jin yadda yake masa lilo haka kuma yayi masa nauyi sosai, ƙarar dosowar babbar motar wajen su yasa da sauri ya saka hannun hagun sa ya ciciɓata da ƙyar ya saɓa ta a kafaɗar sa kafin ya shiga gudu da ita ta cikin duhun ciyayi da bishiyun gonar da suka faɗa, be ko yi wani nisa ba motar su ta kama da wuta hakan yasa ya dakata gami da juyowa ya kalle ta. Yadda take ci da wuta ya saka shi furta alhamdulillah dan yasan ba dan rahamar Allah ba da tuni suna cikin motar yayinda wutar zata tashi ta cinye dukkan wata tsoka da ƙashi na jikin su. Jin kamar sautin Muryar mutane yasa ya juya da sauri ya cigaba da tafiya da ita cikin tsananin dauriya dan ba ƙaramin jin jiki yayi ba, wani irin jiri jiri yake ji sanadin dokuwa da kan sa yayi lokacin da motar ke tumble sedai aka ce wai shi gudun ceton rai da ban ne wanda hakan ne yasa har yake iya daurewa dan ganin sun tserewa magautan su. ***** Can ɓangaren ƴan hirer killers ɗin da kawu ya turo kuwa suna ƙarasowa gab da wannan tanka suka tsaya tare da firfitowa dan sun hango ta tunda nesa, wajen da motar su Kisnah ke ci da wuta suka ƙarasa don tabbatar da su ne ɗin ko wasu ne sedai number motar su dake kan ci da wuta ta tabbatar musu da sune dan ga tambarin KS nan dake bayan duk wata mota tata, duk da ganin motar na ci da wuta basu fasa bincika gonakin dake gefe gefen hanyar ba dan tabbatar da sun mutu basu sami kuɓuta ba. Ganin basu ga wani alama dake nuna sun kuɓuta ba yasa suka koma motar su suka zauna har se da gaba ɗaya motar ta ƙone ƙurmus kafin suka juya bayan sun ɗauki hotunan motar lokacin da take kan ci, number motar da kuma lokacin da ta gama ƙonewa gaba ɗaya. ******* Gudu sosai yayi kafin ya fara tafiya a hankali kan sa na juya masa saboda tsabar jirin da yake ɗiban sa, tun yana iya tafiya har ya kasa ya nemi ƙarƙashin wata bishiya da yake ganin ta dishi dishi ya kwantar da Kisnah tare da zama kusa da ita yana maida numfashi ɗai ɗai cikin tsananin azaba da jigata. Da hannun sa me lafiya ya dafe kan sa da yake jin kamar ana masa ihu a ciki, tun yana gani dishi dishi har ganin sa ya ɗauke gaba ɗaya ya daina gani da fahimtar komai. ********* A hankali ta fara buɗe idanun ta tana yi tana rufewa tare da buɗe wa saboda yadda take gani uku uku har ganin ta ya daidai ta. Cikin mamaki take bin wajen da take kwance da kallo, jar ƙasa ce sosai akayi ginin da ita dan gata nan a fili ana iya ganin ta, haba ɗaya ginin da akayi da ita be fi kamu biyar ba se kuma wasu karare ko yayi zata ce ne da aka haɗa aka tashi ɗaki dashi, a ɗan tsorace ta nemi miƙewa sedai da sauri ta dafe kanta tana faɗin "Wash". Saboda zafin da ya ziyarci kan nata a daidai lokacin ne kuma komaɗaɗɗiya kuma yamutsattsiyar mata ta shigo ɗakin hannun ta ɗauke da wani ƙoƙo, wata irin zabura Kisnah tayi da har yasa taji kamar kanta ze faɗo saboda nauyi ga kuma zafin da ya ziyarce ta sedai bata ko kula hakan ba ganin wannan aljanar tana nufo ta. Da sauri matar ta ƙara sa matsowa wajen Kisnah tana ajiye ƙoƙon hannun ta kan wani ɗan tudu dake gefen su, da hanzari ta saka hannun ta da ƙashi ne kawai da fata ba ko ɗigon tsoka (a ganin Kisnah ) ta ruƙo ta ganin tana neman fita daga ɗakin, wani irin ihu Kisnah ta saki jin matar ta riƙe ta haka kafin ta sami zarafin magana matar ta shiga yi mata magana cikin wata gurɓatacciyar Hausa da ba wani ganewa take ba "Kayi haƙuli yalo, baka da lashiya magani nak kawo maka kashi". Ai ina Kisnah bata ma tsaya ta saurare ta ba balle ta fahimci me take son cewa se ƙoƙarin ƙwace hannun ta kawai take tana zarar idon tashin hankali, cikin zuciyar ta kuwa bata bar tunani ya akayi ta zo hannun wannan aljanar ba, ganin fa bazata tsaya ba gashi maganin na neman bushewa yasa matar ta ɗan ɗaga murya ta ƙwala kiran "Bingel". "Na'am". Wata ƴar matashiya ta amsa tana shigowa cikin ɗakin, kallon ta mayar tayi kafin tayi mata maganin cikin wani irin yare aikuwa da sauri yarinyar ta ƙaraso ta kai nata hannuwan da bambancin su dana tsohuwa zance ko dattijuwa ce kaɗan ne, aikuwa se gashi sun danne Kisnah ta kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi, sosai mamakin yanda waɗan nan matan masu matuƙar siran ta kamar me suka iya danne ta haka har takasa motsi. Ƙwaryar da matar ta shigo da ita ta janyo ta dangwalo wani koren abu cikin wata leda kamar mai kamar kuma ruwa me ɗan kauri ta shiga shafawa Kisnah kan goshin ta zuwa cikin kan ta kaɗan, runtse ido kawai Kisnah ta ke yi cikin tsananin zafi dan yarinyar da aka kira da Bingel ta danne mata baki da tafin hannun ta ɗaya saboda tsabar ihun da ta ke kurma musu. Seda suka gama shafa mata maganin kafin Bingel ta cire hannun ta a bakin Kisnah, da sauri kuwa ta tofar da miyan da ta tara jikin rigar Bingel ɗin sedai ko kallon ta bata yi ba balle ta nuna ta ji haushi se ma wata ƙwarya da bata san yaushe aka shigo da ita ba da Bingel ɗin ta miƙawa matar nan suka kuma matse mata baki suka ɗura mata kafin suka sake ta, a tamanin ta duro daga kan abinda suka kwantar da ita da bata ma tantance mene ne ba ta shiga kakarin amai sedai ko ɗigo hasalima wahalar da kanta kawai tayi dole haka ta haƙura ta koma ta zauna tana hararar Bingel dan ita dattijuwar suna gama ɗura mata maganin ta fice. Murmushi Bingel ta sake ma Kisnah da yasa tayi kamar wata zombie a idanun Kisnah duk da kuwa Bingel kyakkyawar bafulatanar daji ce sedai a idanun Kisnah ita bata ga wani kyau ba se ma tsorata ta da take yi. A can wajen ɗakin kuwa dattijuwar na fita ta tadda wani yamutsattsen farin bafulatanin daji sedai yafi matar nan kyan gani sosai, murmushi ta sake masa da dole wanda be saba ganin su ba ya tsorata sedai a wajen su su murmushi ne hakan, da ɗan sauri dattijon ya matso kusan matar "Nene Ina fatan kin shafa mata kuma tasha maganin". Ya faɗa cikin cikakkiyar Hausar sa da tafi ta su matar da ya kira Nene nesa ba kusa ba, gyaɗa masa kai Nene tayi tana nuna masa ƙwaryar hannun sa "Ƙin sha yalon can yayi sheda muka masa danna ni da Bingel, na shafa ma mun sha masa, aradu yalon kwai ƙarfin kai arɗo". Ɗan murmushi arɗo yayi cikin fahimtar matar tasa, taurin kai shine ƙarfin kai a wajen su, kallon ta yayi yana faɗin "Tun da ta sha ai da sauƙi, yanzu ki haɗo min wani na bawa yaron can dan shi har yanzu be farko ba kuma da alama ya fita shan wahala". "Tau arɗo". Ta faɗa tana shiga wata bukka nan gefen inda suke tsaye, tsawon lokaci tana ciki kafin ta fito da ƙwaryar da ta shiga a hannun ta ta miƙa wa arɗo, karɓa yayi ya juya ya shige wata bukka da ke ɗan nesa da wadda Kisnah ke ciki seda ya duƙa sannan ya iya shiga ciki, itama kamar waccan an yi mata ginin jar ƙasa kamu biyar kafin aka ƙara sa da asabari da kuma ya yume ya yumen su. Kwance kan wani gadon kara da aka shimfiɗawa wani tsumma na hango Saraki, gaba ɗaya kamannin sa sun canja dan ƙafar sa ɗaure take da wani tsumma bayan an zagaye ta da karare haka ma hannun sa na hagu, da sallama dattijon ya shiga ɗakin yana ƙara sa gaban Saraki ya tsaya tare da bin sa da kallo na wasu daƙiƙu sannan ya ajiye ƙwaryar hannun sa ya ƙara sa wajen Saraki, hannu yasa ya ɗago ƙafar ya shiga kallon tafin ƙafar da yayi jajir dashi ga kuma alamun cuwuka sosai a jiki, hannu yasa ya lakato wani mai cikin wata ƴar jakar fata dake jikin sa ya shiga shafawa a tafin ƙafar, seda ya shafe ko ina kafin ya saki ya matsa yana taɓa ƙaurin sa da yake ɗaure da kararen, se aya taɓa sosai sannan ya gyaɗa kansa tare da yayyafa wani farin Ruwa kan gurin sannan ya tashi. Wajen hannun ya matsa ya kama hannun ya jinjina shi cikin nasa kafin ya ajiye a hankali bayan ya ɗan jijjiga shi, a hankali ya sunkuya ya kai bakin sa ya shiga tofa abinda ban sanu ba kan hannun, koren magani irin wanda aka shafawa Kisnah ya lakata ya shafa masa shima a kansa kafin ya tashi ya fita bayan ya sake bin sa da kallo. ****** A can wajen su kawu kuwa duniya sabuwa bayan sun ga hujjojin da yaran su suka basu na shedar mutuwar su Kisnah, wani ɗan ƙwarya ƙwaryar liyafa ranar suka yi a tsakanin su shida Alh Haladu. Seda aka kwana aka wuni da faruwar lamarin kafin ya shigar da ƙorafi kan ɓatan Kisnahn yana me nuna tsantsar damuwa da tashin hankali Wada da ƙyar ƴan sandan suka sami lallaɓashi ya bar police station ɗin bayan an barbaza jami'ai cikin garin manya dan nemo inda take. Ranar farin ciki wajen su Mommy kamar sallah ko ma fiye duk da so tayi su wulaƙanta rayuwar ta sedai ko a hakan ma duk ɗaya dan haka ta shiga addu'ar kar Allah yasa Kisnahn ta bayyana, haka ƴan sanda suka ɗin ga shiga lungu lungu neman ta amma ko alamar ta, ba wani club, hotels ko cinema dake garin manya da jami'ai basu shiga neman ta ba amma duk ba wani labari, cikin ƙanƙanin lokaci gari ya ɗauka da batun ɓacewar Kisnah, kiran wayoyin da ake wa su Meenah da su Surayya na wai jaje yasa suka san meke faruwa a ranar kuma suka haɗu gaba ɗaya suka tafi gidan su Kisnahn sedai ba ƙaramin rashin mutunci Mommy ta shuka musu ba dan ko barin su su zauna bata yi ba ta shiga jifan su da munanan kalamai har tana neman ɗora musu alhakin ɓatan Kisnahn, al'amarin be musu daɗi ba haka dole suka tarkata ƙafafun su suka fice daga gidan sedai basu koma gida ba neman ta da suka shiga yi a wuraren da suka san suna zuwa. A kwana na uku da ɓatan ne kawu ya shigar da batun wai yana zargin driver ɗin ta ne ya sace ta, nan fa lamari ya canja aka shiga neman Saraki ruwa a jallo sedai rashin sanin inda za'a iya samun sa ya sa dole aka taƙaita binciken bayan an saka jami'ai a ko wani titi dan bincike duk motar da tazo wucewa. Ranar da suka kwana biyar da ɓata ne aka samu rahoton samun ƙonanniyar motar su da suka fita a cikin ta, jami'an bincike aka ɗauko suka shiga aikin su a daidai wajen da aka ga motar kafin daga baya suka sanar da cewa motar ta kama da wuta ne sanadin dukan tankar mai da ta tare hanya wanda ya dukan yasa murfin gidan man ɓalle wa abinda ya haddasa tashin wuta a motar kenan bayan ta hantsila har so biyar. Al'amarin ya girgiza da yawa cikin jama'a dan zuwa wannan lokacin babu wani mazaunin garin manya da maƙoftaka da bai san da ɓatan the CEO na K &S companies ba, ranar kawu kam a asibiti ya kwana saboda yadda ya dinga sumewa ana yayyafi masa ruwa daga ƙarshe kuma ya dinga sambatu kamar wani zararre dole aka dangana dashi asibiti. Duk yadda Mommy ke ƙin Kisnah seda ta ɗan yi sanyi sanadin mutuwar kafin kuma daga baya ta watsar ta shiga fantamawa cikin nera, su Maigado kuwa duniya sabuwa babanta ya zama me kuɗi. Seda kawu yayi kwana uku a asibiti kafin aka sallamo shi lokacin ya dawo daidai sedai ba uhm balle uhm uhm sedai yayi ta kallon mutane, dole a ka rufe Companies ɗin K&S har zuwa lokacin da kawu ze dawo hayyacin sa ga kuma jimamin mutuwar mamallakiyar wajen da ma'aikatan ke ciki. ******* Seda Saraki ya kwana shida be san wa ke kan sa ba kafin ya farfaɗo, zuwa lokacin kuwa tuni ciwukan ƙafar sa da yaji sanadin gudu cikin daji yana taka ƙayoyi sun fara warkewa, zuwa lokacin kuwa har Kisnah ta saba ganin su Bingel dan ta daina tsoron su sedai kuma bata kula su haka kuma bata iya cin abincin su sedai a bata fura da nono kullum........................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, Comment and share fisabilillah. Ouummey 32 (8/24/2022 10:07 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________                            Page 3️⃣2️⃣ _______________________📖 Zaune take a bakin bukkar ta kan wata tabarmar kaba tana bin Bingel da ke kwanto shanu da garken su ke can gefen bukkokin su da kallo, yadda take iya kwance su ta na shafa jikin su ba tare da tsoro ba ba kuma tare da su shanun sun wa Bingel ɗin komai ba ya matuƙar ƙayatar da ita, ba tun yau ba in taga Fulani na kora shanu abin ke burge ta da cika ta mamakin yadda suke iya controlling ɗin su, yanzu kuwa da take ganin hakan a gaban ta sosai se take jin kamar itama ta gwada sedai kuma tana tsoro. Sanye take da kayan saƙi irin na Fulani, ƙaramar riga da bata sauka kan cikin su ba se zanin saƙi ɗaure a jikin ta shima be ko kai ƙaurin ta ba, gashin kanta ya wani barbaje kamar be taɓa ganin gyara ba, ƙafafun sanye da wani tsohon silifas da arɗo ya samo mata da ƙyar cikin garin su dan ta ƙi yadda ta saka irin takalman su. Da sauri ta miƙe ganin Bingel na shirin ficewa da shanun bayan ta gama yi wa Nene magana cikin bahagon yaren su da ya kasance fulatanci sedai na su fulatancin ba irin na gamagarin Fulani bane, nasu na Fulani daji ya sha banban da ragowa. "Ki tsaya ni, nima zanje". Tsayawa Bingel tayi tana kallon Kisnah kafin ta juya ta kalli babar ta, gyaɗa mata kai Nene tayi alamun su je tare tun d tana so. Ba yau ne ta fara fita kan ta ba ɗan kwali ko hula ba haka ba yau ta fara fita da kayan da basu rufe mata jiki ba shakka yasa ko kaɗan abin be dame ta ba ta fice a yadda take, ita matsalar ta ɗaya da kayan nauyi ga kuma zani da bata saba sawa ba da yake bata matsala wajen tafiya shiyasa ma in ta tashi take ɗaure shi can sama dan da ƙyar yake kai wa gwiwar ta, ɗaurin zanin kuwa dole ya bawa wanda yaga yadda ake yin sa dariya dan kawai cukurkuɗa kayan ta take ta cusa tayi gaba abinda, to ta ina zata fara wahalar da kanta, dole dai su ɗin zata saka tun da nata gaba ɗaya sun ɓaci da jini haka wasu guraren duk sun yayyage. A hankali suke tafiya da Bingel yayinda shanun suke gaban su, kalle kalle take hannun ta riƙe da sandar da ta saka dole Bingel ta ɗauko mata itama wai zata taya ta kula da shanun, sosai garin ya burge ta ganin ko ina cike yake da korayen ciyayi, daga inda take ta hango kogin dake gaba da su sosai wanda da alama nan zasu tsaya da shanun, aikuwa suna kaiwa wajen taga duk shanun sun tsaya haka kuma sun fara ƴan ciye ciyen su, seda ta juya bayan ta sannan tasan ashe sun shiga daji sosai dan bata ma iya gane ta wace hanya suka kawo nan ɗin ba. Ɗan kallon Bingel tayi kafin ta juya ta shiga bin wata hanya da taga wasu kyawawan tsuntsaye na tafiya a jere a jere a sama, sannu a sannu take bin tsuntsayen tana irga adadin su har tayi nisa bata ankara ba, seda ta gaji kafin kuma ta juyo dan komawa wajen Bingel sedai sam ta rasa ta hanyar da ta shiga wajen, hanyoyi ne da yawa gasu nan haka yasa ta daburce ta rasa ina zata bi, tsayawa tayi cikin tunanin wace hanya zata bi daga ƙarshe dai ta zaɓi bin hanyar dake right hand ɗin ta, without any second thought ta shiga tafiya tana me fatan Allah yasa hanyar daidai ta ɗauka, seda ta ɗan yi nisa kafin tafara jiyo muryoyin mutane da kuma ɗan kukan shanaye ƙasa ƙasa aikuwa cikin azama ta ƙara sauri wa tafiyar ta dan ta isko wajen dan tun da ta jiyo kukan shanu ta san ta dawo wajen Bingel. Wasu Fulani samari ta gani kowanne riƙe da sanda a hannun sa suna tsaye suna magana da ƴar dariyar su suna nuna wani ɗan uwan su da ke duƙe ƙarƙashin wata sanuwa yana shan nonon ta, zaro ido Kisnah tayi ganin abinda yake yi kafin ta fara yamutsa fuska cikin ƙyanƙyami, wani irin amai ne ya tuƙo ta ganin yadda ruwan nonon ke biyo wa ta gefen bakin sa aikuwa nan ta duƙa ta shiga amaye ƴar guntuwar fura da nonon da yayi saura a cikin ta, kakarin aman ne yasa hankalin samarin ya dawo kanta gaba ɗaya har wanda ke ƙasan saniyar, sakin shanuwar yayi ya fito daga ƙarƙashin ta ya tsaya yana ƙarewa Kisnah ta kallo a lokaci ɗaya yana lashe ragowar nonon dake gefen bakin sa da harshen sa, da sauri ragowar samarin suka yi kan Kisnah sedai kafin su ƙarasa Bingel da ta biyo bayan ta neman ta ta riga su, ɗan duƙar da kai tayi ta gaida su kafin kuma ta zuba gwiwoyin ta a ƙasa ta gaida ɗaya saurayin dake tsaye yana kallon Kisnah. Jinjina mata kan da yayi yasa da sauri ta koma wajen Kisnah ta bata ruwa ta wanke bakin ta ta miƙe ita kuma Bingel ta rufe aman da ƙasa kana ta ja hannun Kisnah dake tsaye tana hararar saurayin dan su tafi "Wacece wannan?". Tambayar da saurayin yayi mata kenan cikin Yaren su, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa ta shiga bashi amsa "Baƙuwa ce da Arɗo ya tsinto cikin gona kwanakin baya". "Shi arɗo ya manta da al'adar mu ne da kuma sharaɗin da wassai ya kafa mana a wannan garin da har ze karɓi baƙuncin budurwa, ko kuwa yana son jamana bala'i da masifa ne?". Da sauri Bingel ta tare shi dan jin abinda yake faɗa "Ai ba budurwa bace lamiɗo, matar aure ce da mijin ta aka tsince su, ya sami rauni ne sosai shiyasa baya iya fitowa". Wani kallo saurayin da aka kira lamiɗo ya bi Kisnah dake tsaye tana kallon su cikin rashin fahimtar abinda suke cewa dan da Yaren su suke magana (kuyi hqr fa, banjin fillanci balle in yi muku😝). "Ki cewa arɗo ya shigo fada ƙarfe biyar na yamma". Da toh kawai Bingel ta amsa musu kafin ta ja hannun Kisnah suka wuce yayinda lamiɗo ya raka su da mayatatttun idanun sa. Tafiya suke cikin dajin shiru ba me magana, to ita Kisnah ba gane Hausar su take ba haka kuma bata fahimtar Yaren su, har gwara su in tayu magana suna ganewa, tunani kawai Bingel ke yi na dalilin da ze sa lamiɗo yace arɗo yaje faɗa yau bayan yau ɗin ba ranar fadanci bace, to ko dai be yadda baƙuwa matar aure bace ba ko kuma meye, da wannan tunanin a ran Bingel suka ƙarasa wajen da tabar shanun ta ranar bata bari ta kai lokacin da take tashi kiwo ba ta kora shanun ta suka kama hanyar gida. Suna zuwa gida bata kula Nenne dake mata barka da dawowa ba dan bata gane me tace ba duk inda cewa da Hausa ta faɗa se kawai ta ɗaga mata hannu tare da gyaɗa kai alamun amsawa ta wuce bukkar da aka ajiye Saraki a ciki. Zaune ta sake shi kan gadon shi na kara da aka shimfaɗa wa wani tsumma, da sauri ta ƙara sa ta zauna gefen sa tare da kai hannu zata taɓa nashi me ciwo ya kautar da sauri yana hararar ta "Ina kika shiga da se yanzu zaki shigo, wato a garin da baki san kowa ba ma bazaki daina yawo ba ko?". Karyar da kai tayi cikin son Kare kanta "Yaa ba fa yawo naje ba, I was so bored staying alone, su ba iya yarena sukai ba duk da suna ganewa amma ni ko fahimtar su bana yi sedai fa in ta zama ina bin su da kallo shiyasa yau na bi waccan yarinyar kiwo, kuma baka ga garin ba wallahi me kyau and their atmosphere is so wow banda Kuma beautiful look na garin". Girgiza kan sa yayi kawai, ya sani dole da ma zata gaji tunda ko abokin fira bata da, haka kuma bata saba da zama waje ɗaya ba haka ma wani ƙalubalen ne shiyasa ma be yi mata wani faɗa sosai ba. "And a haka kika fita ba". Kallon kanta tayi kafin ta ɗan taɓe baki "To su irin kayan su kenan, suma haka suke yawo kaga kuwa ba laifi na bane, ni bacci na zo yi dan bana iya bacci a wancan ɗakin ina jin tsoro, can't wait ka samu sauƙi mu bar dajin nan if not Allah mutuwa zan yi, bana iya cin komai se fura da nono fa yaa, kuma basa sa sugar se zuma ni kuma bana so" Ta ƙarashe tana kaiwa kwance gefen sa, kallon ta kawai yayi bece komai ba, to me zece mata, kar tayi bacci? Bayan yasan a halin da take tana buƙatar baccin sosai dan gudun abinda ka iya faruwa da ita. Ya ji daɗi da bata kasance mutum me saka abu a rai ba dan da wata ce ya tabbatar har yanzu ba zata saki ranta ba saboda abinda su kawu suka aikata kuma hakan ze iya sawa ta kamu da ciwon depression Wanda ita ma Kisnahn ya San tana fama dashi ko da ba yawa sedai dole ta damu, her only family turns out to be her worst enemy, abin is not easy at all. Kamar yadda tace kuwa bacci ta shiga yi abin sa yayinda yake zaune Yana tasbihi a ransa, a rana ɗaya fa Allah ya canja musu yanayin rayuwa, yanzu dai dubi da rich, beautiful, sexy and fashionable Kisnah kwance akan gadon kara rabin jikin ta kwance kan tabarmar kaba, wa ce taɓa yadda 8 days back in aka ce masa zata yi rayuwa a irin wannan wajen, waze yarda in akace masa zata saka irin wannan kayan, waze yarda in akace masa her long black silky hair ze yi wannan busu busun ba gyara? Sure life is unpredictable and Allah is the all doer. Rufe nasa idon yayi lokacin da tunanin rayuwar sa ta baya ta faɗo masa, ba iya Kisnah ba shikansa be taɓa kawo rayuwa a irin wannan wajen ba balle

Chapter 20 of 27