Share this page
dukiyar ta bace muke cin arziƙi, na miki alƙawarin sena wulaƙanta rayuwar ta kuma kin tabbatar da zanyi ko? Gyaɗa kai maigado tayi kana ta karɓi dubu biyun da mahaifiyar tata ke bata ta saka a jaka, buɗe baki tayi zatai magana sai dai ƙamshin da ya gauraye falon tareda takun takalmi ne ya katse ta. "Ƙwas ƙwas ƙwas" haka sautin takalmin ke bayarwa wanda ya shaida na mace ne, a hankali suka ɗaga kansu zuwa staircase ɗin dake parlon duk kuwa da sun tabbatar ita ɗin ce ke saukowa. Matashiyar budurwa ce da bazata wuce shekaru 18-19 ba, fara ce sosai domin skin ɗin ta har wani yellow yellow yake yi saboda tsabar hutu da jin daɗi, sanye take da wata guntuwar red gown da bata gama ƙarasa sauka a gwiwar ta ba, sosai rigar ta kamata ta kuma haskata, ƙafar ta na sanye da red high hill takalmi se gashin kanta da ya sha gyara ya lafe a gadon bayan ta se ko red hat da ta ɗora masa, hannunta ɗaya riƙe da car key da take karkaɗawa se ɗayan riƙe da mini red purse da ta sha adon stones se walwali da ɗaukar ido take yi. Ƙarasawa tsakiyar falon tayi cikin takunta na cat walk, hannu ta saka ta ture hat ɗin baya hakan yasa fuskar ta bayyana kana ta ɗago ta dubi Mommy dake zaune ta sakar mata wani makirin murmushi. Se yanzu na tabbatar da kyanta domin iya fuskar ta abar kallo ce, wasu irin idanuwa gare ta masu matuƙar maiƙo da ɗaukar hankali wato oily eyes, Haka Kuma ƙwayar idanunta ba baƙa bace golden brown ce wadda kalar take sake dulmiyar da duk me kallon ta, idanunta matsakaita ne masu ɗauke da zara zaran thick black eyelashes Wanda suke kwanciya sosai in ta rufe idanun, haka girarta cikakkiya ce dan har tana neman haɗewa sai dai ba ta ƙarasa haɗewar ba, siririn hanci gare ta mai matsakaicin tsayi se ƙaramin bakin ta mai ɗauke da kyawawan luscious pink lips Wanda kallo ɗaya za'a yi musu asan zasuyi matuƙar daɗi da laushi a baki, a taƙaice dai ita ɗin na tsananin kama da jarumar nan sridevi ta ƙasar India. Karkaɗa mukullin hannunta tayi daidai fuskar Mommy kafin ta ce mata "Hi". Takaici da baƙin ciki ne suka cika zuciyar Mommy da ɗiyar ta mai gado sedai ita gogar ko a jikinta, juyawa tayi ta nufi entrance ɗin falon ta fita, sai da ta buɗe ƙofar sannan ta juyo ta kalli Mommy cikin yamutsa fuska tace "oops, kinga na manta, ki faɗa wa mijinki account balance ɗina yayi low, Ina buƙatar transfer ɗin 2 millions urgently in ya fito".  Tana gama faɗar haka ta fice daga falon zuwa farfajiyar gidan. Girman farfajiyar gidan kawai ya isa sanar da ainahin girman gidan, domin kuwa kuwa manya manyan flats uku ne a cikin gidan wanda duk flat ɗaya ya yi girman gidan masu rufi asiri uku ko huɗu. Ba tareda ta tsaya amsa gaisuwar da ma'aikatan gidan ke ma ta ba ta ɗaɗɗaga musu hannu dan sauri take yi, wata jar mota ta buɗe wadda ke cikin motoci sama da goma dake harabar gidan, motar se ƙyalli da ɗaukar ido take yi, shiga ciki tayi tai mata key kana ta fice daga gidan cikin matuƙar gudu kamar yadda ta saba. Gudu take yi sosai yayin da ta ƙure volume ɗin motar cikin waƙar Dil to pagal hai dan ita ɗin die hard fan ɗin Indian films and music ce, yanzu haka cinema zata je kallon sabon Film ɗin jaruma Rani me suna Black, gashi ta kusa makara duk datasan bata da matsalar ticket nata a ajiye yake. Wayar ta ce ta fara ringing hakan yasa ta rage volume ɗin waƙar tai picking tareda sa wayar a speaker ta ajiye ta. "Hey Kisnah beauty, kina Ina ne, gamu har mun shiga cinema baki ƙaraso ba? "On my way babe" "Okay, se kin ƙaraso". Kashe wayar tayi ta ƙure volume ɗin waƙar ta, tana tuƙi tana bin waƙar tareda girgiza kanta cikin zallar nishaɗi. Gudun da take yi sam ba na hankali bane amma ba yadda mutane suka iya da ita dan har sun fara sabawa, shiyasa da yawa masu ababen hawa ke kaucewa suna bata hanya, wasu na zagi wasu na tsine mata yayin da ita bata masan sunayi ba. Haka salan tuƙin ta yake shiyasa Bata driving da kanta se dai ta ɗau driver, to driver ɗin nata ne babansa ba lafiya dole ya ajiye aikin dan kula dashi, yanzu hakan tana kan neman wani ne shine fa kwana biyu take tuƙa kanta dan bazata iya zama gida ba dole se ta fita. A gurguje tayi parking motar ta dan lokacin har an fara Film ɗin, hakan yasa tayi wrong parking tayi blocking wasu manyan motoci uku. Zama tayi a gurin zamanta na musamman inda ta sami ƙawayenta huɗu duk sun iso, ba tareda ta kula kowacce ba ta zauna tareda fito da park ɗin creamy crackers ɗin ta ta fara jefawa a baki tana maida hankalin ta kan Film ɗin.................📝              Ouummey ✍️ ☑️ote Comment Share. Ouummey 03 ( 7/29/2022 7:56 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________                          Page 3️⃣ __________________📖 jefa crackers ɗin take bakin ta yayinda hankalin ta gaba ɗaya ke kan moves ɗin jaruman. Kwaɓe fuska tayi lokacin da aka haska scene ɗin da jarumi Amitabh bachan yake saka jaruma Rani Mukherjee a cikin ruwan sama, kan kace me se ga hawaye na zuba a fuskar ta, meenah da ta san haka ze faru ce ta riƙo ta jikin ta tana lallashin ta, juyowa ragowar sukayi, Hameedah, Surayya, da Maleeka sukayi suna sake comforting ɗin ta har tayi shiru, tagumi ta saka tana cigaba da kallon, ita ɗin me tausayi ce most especially ga masu nakasa da kuma talakawa, most of the times in tazo cinema se tayi kuka saboda tausayi, either na yadda wasu ke fama da talauci, yadda ake ciki zalin wasu ko rabuwar masoya kuma ba hakan ne ze Hana ta dawowa gobe ba. "Yeeeeeeehhhhhh".  Ta buga tsalle tana ihu lokacin da jarumar ta kammala degree ɗin ta tana speech ranar convocation , gaba ɗaya ta ruɗa wajen da ihun ta da tsalle wai murna take, majority na occupants ɗin ji suke kamar su shaƙe ta dan takaici yayinda minority basu ko kalle ta ba dan sun saba da ihunta tun bare in tana kallon wrestling, yanzu zaka ji tana ihun "yauwa, dake shi, ɗaga shi ka buga shi, karka bari ya yarda kai, wayyo, tashi, yauwa kauce, ehen kai masa duka........" and many more of this. Ɗaukar ledar crackers ɗin ta tayi ta nufi hanyar fita tana waƙe waƙen ta da suka zauna a bakin ta kai kace ita ce ta raira su, bin bayanta su Hameedah suka yi yayinda meenah ta ƙara sa suka jera suna tafiya har suka fita daga cikin ainahin cinema ɗin zuwa parking lot ɗin da ta ajiye motar ta. Maza huɗu suka tarar tsaye jikin motoci ukun da tayi blocking saboda saurin da take yi, nufar motar ta tayi zata buɗe ɗayan ya sha gaban ta yana jifanta da wani ɗan iskan kallo, ɗagowa tayi itama tana masa kallon mamaki dan bata ma lura da cewa tai blocking ɗin su ba. "Wace iriyar kidahum ce ke da Zaki blocking ɗin mu da wata gwanganin motar ki, ko baki da idanu ne da baki ga motocin mu ba lokacin da zaki yi parking? Sakin baki tayi tana kallon shi jin wai ita yau wani useless being ya Sami bakin zagi, bata gama dawowa daga duniyar mamakin ba ta ga wani ya zo ya tsaya gefen wancan yana hararar ta kafin ya fara magana "Kayi mamaki ne Haroon, kalle ta fa, da ganin su kaga ƴaƴan talakawa masu shegen buri da fafa, anje an aro kaya da mota an shigo cinema dan a sami wani me ɗan maiƙo a liƙe masa, bana tantama ta ga shigar mu shine bari tayi blocking ɗin mu dan tayi driving attention ɗin mu towards her, sedai bata san tayi a banza ba, mara hankali kawai". Wani irin tafarfasa zuciyar ta ta fara a ƙirjin ta, inda sun mata magana cikin mutuntaka ita me basu haƙuri ce dan bata da wannan girman kan, sedai yanzu da suka biyo mata ta wannan hanyar zata gwada musu ainahin wacece Kisnah. Sam be lura da intention ɗin ta ba se ƙarar marin da ya karaɗe gurin se ko raɗaɗin da ya ratsa kwanyar sa, kafin a ankara ta saukewa ɗayan ma nasa a kuncin sa, zaro idanu Hameedah tayi yayinda Meenah tayi hanzarin riƙe ta ganin tana aniyar ƙara marin wanda aka kira da Haroon, fincikewa tayi ta ƙarasa gaban ɗayan tana nuna shi da yatsa tace "inga uban da ya tsaya maka yau a garin nan in Kai ɗan halak ne". Juyawa tayi da nufin wucewa ragowar biyun suka sha gabanta fuska a haɗe duk da cikin ransu fargaba ce cike dan basu san wane ɗiban albarkar zata yi musu ba su kuma. Kamar wanda ya fita daga shock haka yayi firgigit yana kallon ta cikin tsantsar takaici da baƙin ciki "Lallai yau se na yi maganin ki, se n ga uban da ya tsaya miki a garin nan". Ya faɗa yana zaro dalleliyar wayar sa yayi danne danne na ƴan sakanni kana ya sa a kunnen sa. "Ina buƙatar motar ƴan sanda biyu yanzun nan ciki har da mata, ina parking lot ɗin clear screen cinema". Gyara tsayuwa Kisnah tayi tana sakin murmushi yayinda ragowar matasan biyu suke kwarzanta wanda yayi kiran "Gaskiya Abeed ka nuna wa yarinyar nan ko waye kai in ba Haka ba ai ƙimar mu ta zube, ace har mace ta samu guts ɗin ɗaga hannu ta mareka, gaskiya this is so disgusting". Hura hanci kawai Abeed yake Yana aiyana abinda ze sa ayi mata a police station ɗin dan se ya sa an wulaƙan ta ta, jinginewa tayi jikin wata mota dake bayan tata ta maƙala airpeace a kunnen ta tana maming waƙar guzarish tana gyaɗa kai, su Surayya da suka san ba abinda aka isa ai mata su ma hankali kwance suka jijjingina da motocin su suna pressing phones ɗin su. Jiniyar motar ƴan sanda ce ta cika wajen yayinda suka ƙaraso har inda Abeed ya faɗa musu, kashe motar suka yi sannan ragowar suka fiffito. Da hannu Abeed ya nuna inda take tsaya yana haɗe fuska irin ba wasa ɗin nan "Arrest her know". Ya faɗa cikin sigar bada umarni. Da hanzari ƴan sanda biyu mata suka ƙara sa inda take har lokacin idanun ta a lumshe, buɗe idon ta tayi jin an riƙe mata hannu ana ƙoƙarin ɗaura mata abu, cikin zafin rai ta janye hannun tareda wanke ta da zazzafan marin da seda tayi baya kamar zata faɗi, gani take tunda tazo duniya ba'a taɓa yi mata tozarci irin na yau ba. Da sauri ɗayar ta tare ƴar uwar ta tana wurgawa Kisnah wani mugun kallo, bata ko kalle ta ba ta janyo wayar ta daga purse a fusace ta Fara dannawa, cikin tsiwa da rashin kunya ta ke magana tana wawwatsa hannaye "Har ni jami'an ku zasu zo suce zasu kama, waye su, eye nace waye su, waya tsaya musu, to wallahi se sun san sun taɓa ni, kuma ina buƙatar ganin ka yazun nan in ba Haka ba kasan sauran". Kashe wayar tayi tana huci yayinda jami'an suka sha jinin jikin su, kallon kallo suka tsaya yi a tsakanin su da alama communicating suke ta hakan, tsayuwa suka gyara dan babban su yace su tsaya su gani, maybe ma duk kurari ne kawai. "Shigowar motar ASP ne ya sa gaba ɗaya ƴan sandan zaro ido, basu kaɗai ba har su Abeed sun sha jinin jikin su da ita dan su kansu sun zata irin pretending ɗin nan ne se ga ASP a gaban su. Tura hular kanta tayi baya shedar zata yi rashin mutunci, kallon uku saura kwata tayiwa ASP kana ta nuna matan nan biyu "A basu suspension ɗin wata ɗaya, su kuma waɗannan a tafi da su har se na neme su, mind you wallahi aka sake a ka bada belin su without my consent se rai ya ɓaci". Ta ƙarashe tana nuna su Abeed, ba tare da ɓata lokaci ba ASP yasa ragowar ƴan sandan suka riƙo su Abeed aka danna su a mota su ma matan ƴan sandan suka shiga da kansu. Dogon tsaki taja ta buɗe motar ta ta shiga ta tayar, batare da ta kula ko ɗaya daga cikin ƙawayen nata ba tayi wa motar key ta fice a 360, girgiza kai kawai Meenah tayi tana fatan Allah ya kai ta gida lafiya dan a yadda ranta ya ɓacin nan ta san yau gudun da zata sheƙa ba na hankali bane, sallama sukayi kowacce ta shiga motar ta ta ɗau hanyar gidan su, dama tafiyar ta suke jira dan ba wadda ta isa ta tafi ta barta sedai ita ta tafi ta barsu. Zagi ne tashi shi har ba adadi dan da yana fitowa a jiki to fa yau da ba zata sake ganuwa ba, wani shegen parking ɗin ganganci tayi ta fice daga motar ko samun arziƙin rufewa batayi ba, daidai ƙofar da zata shiga parlor taji an bangaje ta, ɗagowar da zata yi sukai ido huɗu da Maigado, bata jira komai ba ta sauke mata nata marin a kuncin ta kafin ta ja tsaki ta wuce tana tsartar da yawu, sakarere Maigado tayi da hannu a kunci kafin ta bi ta ciki a fusace, fizgota tayi tana daidai zata fara hawa matattakala, riƙe hannun Maigado tayi wanda ta ɗaga da  sunan marin ta ta murɗe shi har se da ta fara ihu kuma taƙi saki, ihun Maigado ɗin ne ya fito da Mommy dake nata parlon da baƙi, kallon kallo suka yi kafin Mommyn ta ƙaraso ta ƙwace hannun Maigado wanda ta saki ne kawai ba dan Mommyn ta ƙwata ta ƙarfi ba. Nuna Mommy take da yatsa cikin nuna gargɗi tana faɗin "Ki jawa ƴar ki kunne kiyi mata gargaɗi, hawainiyar ta ta kiyayi rama ta wallahi, in ba haka ba wataran se na karya ta a gidan nan, in ta ƙaryata kuma kar ta fasa in har ta haifu cikin uwar ta wato ke". Tana gama faɗa abin da ke ranta ta hayewar ta sama cikin tafiyar gudu gudu sauri sauri, key ta sa ta buɗe ƙofar ta shiga parlon tare da maida ƙofa ta rufe. Haɗaɗden falo ne da yaji kayan ado na zamani masu matuƙar tsada da kyau wanda samun irin su se gidan wane da wane, tun a nan ta fara cire kayan jikin ta tana watsar wa, kafin ta shiga bedroom saura pant da bra kawa a jikin ta, toilet ta wuce ta shige cikin jacuzzi tana kunna tap ɗin ruwan sanyi. Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ruwan ya fara sauka a jikin ta, haka ta kasance cikin cold water for at least 30 minutes kafin taji ga dawo daidai ta buɗe rariya ya fita, fita tayi daga jacuzzin kana tai diluting hot water with cold one daidai yadda take so ta shiga ta fara wankan ta. Towel ta ɗaura ɗan guntu da beko gama sauka ƙasan kwankwason ta ba ta fita daga toilet ɗin, wardrobe ɗin ta ta buɗe dan duba kayan da zata saka, cike damƙan wardrobe ɗin take da kaya kamar za'a buɗe shago, sutturu ne gasu nan kamar zasuyi magana kama da ga kan atamfa, lace, shadda, abayas se ƙananan kaya wanda sune sukai dominating. Tsaki taja dan ta rasa wane ma kayan zata saka, kan gado ta faɗa ta ja bargo rabin jikin ta ta rufe ido, bacci take ji kamar me, sauƙin ta ma yau bata da lectures shiyasa zata yi abin ta ta more. Kamar wadda akayi wa magana ta tashi da sauri zuwa jikin wasu drowers dake jikin bango, ɗaya dag ciki ta jawo slowly, hannu ta ɗora kan photo album ɗin dake ciki kafin ta jawo shi a hankali cike da takatsantsan dan bata buƙatar abinda ze taɓa mata shi balle har ya yage. Zama tayi bakin gadon ta buɗe shi a hankali tana yi tana shafawa, photo ne ya bayyana a shafin Farko na album ɗin, hoton wasu kyawawan couple da kallo ɗaya za'a yi musu a tabbatar da tsananin ƙauna da soyayyar dake tsakanin su, ƙurawa hoton ido tayi tana kallo cikin wani irin maɗaukakin shauƙi da ya kasa ɓoyuwa kan fuskar ta, hannu ta ɗora daidai saitin fuskar macen ta shafa haɗi da lumshe kyawawan idanun ta, tsawon mintuna kafin ta buɗe idanun ta janye hannun ta ta maida fuskar namijin yayinda idanun ta suka cika da hawaye, shafa fuskar take cikin kewa da son kusan ci sedai hakan ba me samuwa bane. Next page ta buɗe wanda ke ɗauke da hoton same couple sedai wannan karon hannun su riƙe yake da jaririya nannaɗe cikin showel me tsananin kyau da ɗaukar hankali dan an masa ado ne irin na yara a jiki, ko daga idanu kasan ze yi tsananin taushi, fuskokin ma'auratan ɗauke da kyakkyawan murmushi da ya ƙara musu kyau duk da duk cikin su ba baya wajen kyan. Hawayen da ya zubo daga idon ta yasa ta maza ta rufe album ɗin tareda janye shi dan bata so ya ɗiga akai balle ya ɓata shi, maida shi tayi wajen ajiyar sa kana ta dawo kan gadon ta kwanta, ɗaga pillown ta tayi ta janyo wani photo guda ɗaya wanda shima dai photon wannan couple ɗin ne ta rungume a ƙirjin ta kana ta kashe wutar ɗakin haɗi da lumshe idanun ta..........................✍️ ©️ Ouummey 📚✍️ ☑️ote,Comment andShare fisabilillah. Ouummey 04 (7/30/2022 6:00 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________                       Page 4️⃣ __________________📖 ƙarfe huɗu da rabi sannan ta tashi daga baccin, miƙa tayi ta ɗan zauna for some minutes har ta ji tayi daidai sannan ta miƙe ta shiga toilet. Wanka tayi sannan ta ɗauro alwala ta fito, zama tayi kan madubi ta lailaye jikin ta da mayukan shafawan ta masu matuƙar tsada da suke tashin ƙamshi kamar wani turare, busar da gashinta tayi tayi oiling ɗin sa ta parking ɗin shi in a crazy style. Kwalliya ta zauna ta tsara a fuskar ta kamar me shirin zuwa zaɓen sarauniyar kyau na duniya, though nude make up ne amma ba ƙaramin haɗuwa tayi ba, gajeran wando ta saka wanda ya tsaya iya cinyar ta se ƴar shimi me siraran hannuwa biyu a each kafaɗa, band kalar wandon ta saka a kanta tareda sake yiwa jikin ta ɓarin turarurruka masu ƙamshi sosai. Jikin wardrobe ɗin ta koma ta buɗe wani side ta Ciro dogon hijab Wanda take sallah da shi ta zura kana ta koma inda praymat ɗin ta yake ta tada sallah. Shaf shaf tayi sallar ta idar da Azahar, without any azkar ta Kuma miƙewa ta tada sallan la'asar shima nan da nan ta idar, gaba ɗaya raka'a takwas ɗin a mintunan da basu fi huɗu ba tayi ta idar. Cire hijab ɗin tayi ta saka wani flat shoe me matuƙar taushi ta buɗe ɗakin ta fita, ta ƙofar bayan dake jikin stairs ɗin nata ta fice zuwa garden, Zama tayi cikin ɗaya daga cikin kujerun da suka ƙawata kyakkyawan gurin da yake da matuƙar kyau da ɗaukar hankali duba da yadda korayen flowers da ciyayi suka lulluɓe shi, gefe ɗaya kuma swimming pool ne me ɗan girma ruwan cikin sa tsaftatacce dan ana iya hango ƙasan pool ɗin. Gefen hagu kuma bishiyu ne da sukai girma na ban sha'awa, bishiyar guava, bishiyar ayaba, bishiyar mango and some other kinds of fruits. Airpeace ta saka a kunnen ta ta lumshe idanunta tayi tana sauraren waƙar ta cike da jin daɗi da nishaɗi, a duk lokacin da take buƙatar kaɗaici nan ne wajen zaman ta, ta ji waƙar ta in ta Kai Mata ta taka rawar ta. Se kusan ƙarfe bakwai ta bar wajen dan har an ɗan jima da idar da sallar magrib, wannan karon ta cikin main parlor ta ratso ta wuce su Mommy zaune suna hira ita da ƴaƴan ta, wani banzan kallo Maigado tabi ta dashi haka ma Mommy banda Awwaf da ya bita da kallon ƙurilla kamar ya cinye ta ɗaya. Bata dubi ko ɗaya daga cikin su ba ta haye stairs ɗin ta tana yi tana moving jikinta towards each sound na waƙar. Sauke ajiyar zuciya Awwaf yayi ya dubi mahaifiyarsa, haɗa ido suka yi tana jefa masa kallon gargaɗi, shafa kansa yayi ya ɗan zame zuwa kishingiɗa, hannun Mommyn ya riƙo yana marairaice murya "Mommy I can't take my eyes off this beautiful creature, pls ki bar ni na aure ta mana". Wani irin fisge hannun ta Mommy tayi tana watsa masa wulaƙantaccen kallo sedai kafin ma ta buɗe baki tuni Maigado ta riga ta "Over my dead body, yanzu kai yaya da bakin ka kake faɗar zaka auri wannan karuwar? Are You in your right sense or yau ɗin ma kaje kasha kayi tatul ne, duk wulaƙanci da rashin mutuncin da take mana baka gani ba kake batun aurar ta? what came over you ne? Ko da yake ba abin mamaki bane zaka iya fiye da haka ma zakayi tunda ba uban mu ɗaya ba ai dole se ka nuna mana wannan bambancin". Zaburowa yayi ze dake ta Mommy ta riƙe shi tana hararar shi kamar idanun ta zasu faɗo "You stupid boy, har ni zaka kalli fuskata kace zaka auri maƙiyar da bani da sama da ita? Eye, ko da yake gaba ɗaya zantukan Maigado akan daidai suke , zaka iya fiye da haka tunda ka zama son of that worthless bitch, lemme tell you something, wallahi ko da wasa na kuma Jin that bitter sentence from your mouth se na saɓa maka ta yadda baka taɓa tunanin zan iya ba, stupid being kawai". Komawa yayi ya zauna yana me dafe kansa kafin kuma ya buɗe su yana kallon ta "Naji na bar maganar auren ta, but sincerely speaking I can't take my eyes off her, dan haka I'll follow ko ma wace irin hanya ce in same ta dan I have passion in her". Washe baki Mommy da Maigado sukayi, Mommy ta dafa shoulder ɗin sa "That's my son, se yanzu naji daɗi, nima ban ce ka ƙyale ta ba, ka bi kowace hanya ka biya buƙatar ka akan ta zan tsaya maka, in fact ma Sena fi kowa farin ciki da murna saboda rayuwar ta ta lalace". Murmushi ya sake jin yadda Mommy ke goyon bayansa tareda ƙara masa ƙarin gwiwa, sosai yaji yana zumuɗin samun damar aiwatar da ƙudurin sa dan yasan ko ta wace hanya Mommy bazata taɓa bari a gano shine ba, haka suka cigaba da tsare tsaren su na abubuwan da zasu yi wa Kisnah su huce takaici da baƙin cikin da take ƙunsa musu. Baiwar Allah ita tana can ɗakin ta kwance a gado bayan ta idar da sallar magrib, chatting suke yi da su Hameedah suna bata haƙuri kan abinda ya faru ɗazu ta bada umarnin a sake su Abeed ita kuwa ta kafe tace bata san zance ba, dole a wulaƙanta mata su dan bazata yarda su tafi Scot free ba. Kashe datan tayi ganin tara yayi, a ƙa'ida tara take bacci in har bata da party ko club ɗin zuwa, wanda tuni ta ware ranakun juma'a, asabar da Lahadi as clubbing days ɗin ta. Miƙewa tayi cikin shigar kayan baccin da tai wadda ƴar guntuwar riga

Chapter 2 of 27