Share this page
gida fiye da so uku sannan ya wuce a hanzar ce zuwa masallaci. Ko da ta shiga wanka ta fara yi tare da canja kayan jikin ta da suka takure ta,  gajeran wando ta saka da ya wuce cinyoyin ta se ƙaramar riga me kamar shimi tana yi tana tunanin yanda zata dena saka irin wannan kayan ta koma saka wasu, tuno da yace tayi Sallah yasa ta miƙe tana ɓaɓɓata fuska kamar yana gaban ta ya zurma hijabin tayi ƴar fakin ta kamar yadda ta saba. Kan bed ta faɗa dan kam yau bacci zata yi da wuri dan ta huce gajiya ta kuma tashi da wuri gobe, da kayan jikin ta ta kwanta bayan tayi offing light tare da locking ƙofar ta, within minutes tayi bacci abin ta. A can ɓangaren Saraki kuwa be dawo gida ba seda akayi sallar Isha, wanka yayi ya canja kaya zuwa jallabiya mara nauyi ya zauna kan sofar ɗakin ya buɗe pack ɗin abincin sa na tun office dan shikam kasa ci yayi a can, gani yake kallon sa zata dinga yi. Seda ya cika cikin sa ya kwashe ragowar ya saka a fridge sannan ya zauna zuwa lokacin da abincin ze faɗa masa, tunanin ta ne ya faɗo masa a lokacin "Allah yasa tayi Sallar". Ya faɗa a fili dan yasan kaɗan daga ayyukan ta taƙi yi ɗin, wanda tayi ma takura mata yayi to wanna da baya nan kuwa ai se abinda Allah yayi kawai. Murmushi yayi tuno dramar su a office ɗin yau, ya sani she's so simple compared to girls of her age Kuma masu kyau da dukiya irin nata, ya sani da wata ce baya jin de iya tanƙwara ta cikin sauƙi haka bayan shi ɗin ba komai ne gare ta ba se mere driver Wanda yake mata aiki take biyan shi haka kuma yasan Allah ne yaso ta da shiriya shiyasa ya sa ta zama mara girman kai balle wulaƙanci though yakan ga tayi wa wasu sedai yawanci ba talakawa bane masu kuɗi ne wanda ya fahimci kodai sun shiga gonar ta ko kuwa sun wulaƙanta kan su. Kwanciya yayi tare da karanto addu'ar bacci ya shafe jikin sa kana ya lulluɓa yana rufe idanun sa a hankali hopping bacci ya ɗauke shi kar ya kuma shiga wata duniyar tunanin da yake ta hana kan shi faɗawa a kullum. ******* "Wai Awwaf me kake nufi da zaman da kayi a wajen ƴan iskan abokan ka bayan kasan ina jiran ka mu fara namu takun kan waccan ƴar iskar, in Kuma ka fasa ba zaka iya bane ka faɗa min in yi introducing wanda ze iya cikin tafiya ta". Da sauri ya miƙe zaune yana hankaɗe matashiyar dake kwance kan sa, Muryar sa har tana rawa ya fara magana "Haba Mommy wane irin bazan iya ba, kin kuwa san yadda nake burin mallakar yarinyar nan da har kike batun kawo wani, to wallahi bari kiji in kika yi hakan se na tona asirin kowa ya sani, gwara ma ki jira ni dan nan da kwana uku zamu dawo, ina dawowa kuwa ba ɗaga ƙafa zan yi ba dan nasan tun yanzu kun riga kun shirya yadda komai ze kasance". "Are You threaten me?, Lallai har yanzu baka san wace uwar ka ba, ka wuce kwana ukun da kace ka gani in komai be faru ba, sedai kaji ana yi shashasha kawai". Mommy ta katse wayar tana huci dan kalaman Awwaf ɗin na wai ze Tona asirin ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba, zaman tayi a kan kujera tana jefar da wayar, da sauri ƙawar ta Jamila dake zaune ta cafe tana matsowa kusa da Mommyn "Haba sadiya, meye abin fushi haka a maganar yaron nan, kin fa san su samarin nan in suka ga sun girma se haƙuri, kawai lallaɓa shi za muyi ya dawo dan plan ɗin se ya fi tafiya dashi dan nikam yanzu bana yadda da saka bare cikin aiki na kin san mutanen yanzu ba amana, kalli fa yadda yaron can Nuhu ya ci amanar Hajiya Talatu, yanzu gashi ta sanadin sa tayi biyu babu, shiyasa duk abin naka gwara shi ɗin dai, so ki kwantar da hankalin ki dan Ni nasa zamu yi Nasara, tabbas zamu lalata rayuwar Kisnah ni na faɗa miki". Ajiyar zuciya Mommy ta sauke tare da wani zazzafan huci "Duk yadda zan kwatanta miki yadda na tsani yarinyar nan Jamila ba lallai ki game ba, kin san dai yadda muka sha fama da rayuwa cikin talauci har Allah ya kashe iyayen ta muka dawo zama tare da ita cikin daula, ina faɗa miki yarinyar nan bata taɓa bari na na samu kwanciyar hankali ba tun ma tana yarinya har se da baban Maigado ya kai ta England karatu sannan na sami sauƙi muka sami damar rayuwa cikin jin daɗi da walwala muka huce duk wani haushin abubuwan da talauci ya sa mana a da, zan iya ce miki ban taɓa shiga cikin damuwar da na shiga ba shekaru huɗu baya zuwa yau wato dawowar yarinyar kenan, ban san wane irin banzan tunani ne ke damun baban Maigado ba amma saboda tsabar baƙin ciki yaƙi kai Maigado ƙasar waje karatu, ki ga dai yadda ita wannan ta yi kyau ta ƙaro aji ga wayewa shiyasa samari kamar ana mata wahayi dan ma ita bata saurarar su ita kuwa Maigado fa, duk da ta samu waye wa da aji amma ai ba kamar waccan ba haka kafin kiga saurayi ɗaya ya biyo Maigado da sunan aure wallahi se a fi watanni zuwa shekara, sedai an ayi rayuwa a ji daɗi sauƙi na ɗaya ita sam ba hakan a gaban ta amma da ya kike zaton tashin hankalin da zan shiga, yanzu fa ki kalla wai ta koma zuwa Companies ɗin ta zata dinga kula dasu manufar ta a hankali a hankali ta ƙwace komai nata dake hannun baban Maigado, ta yaya hankali na ze kwanta in har ban ga na Kai ta ƙasa ba fisabilillahi". Sauke numfashi Jamila tayi tana gyara zama sosai tare da fuskantar Mommy "Shiyasa nace miki da ki yarda Awwaf ya aure ta, a ganina ta haka ne kawai zamu sami nasara a kanta, kinga maganar Companies ko d ta ƙwace wa take dashi da zai kula mata dasu dole dai mijin t zata ɗora a kan komai  so kinga sun dawo hannun mu dai haka kuma ta nan ne kaɗai zaki sami damar musguna mata ki fanshe duk tarin tashin hankali da damuwar da ta jefa ki a ciki ko ba haka ba?". Shiru Mommy tayi dan ita kam Allah ya sani bata jin zata taɓa yarda ta bar ɗan ta auren yarinyar da ta san karuwa ce, ita da take fatan samun tsarkakkun jikoki da sirika me mutunci se ta yadda a kwaso mata kaska, to amma kuma duk batun Jamila na akan hanya, bari dai zata yi tunani taga wanne ne fi mata in ya kama auren se ta haƙura amma fa se ta tabbatar ta hana ga haihuwa dan bata buƙatar zuri'a daga gare ta. Juyowa tayi ta kalli ƙawar ta kuma ƴar uwar ta da ta zuba mata ido dan jin me ta yanke "Kin kawo shawara me kyau dan haka zan yi tunani Jamila, kafin dawowar Awwaf zamu tsayar da batu ɗaya". Jinjina mata kai jamilar tayi ta reda sauke murya tayi mata raɗar da ta sa suka saki dariya tare da tafawa....................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 27 (8/20/2022 8:40 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________                            Page 2️⃣7️⃣ ________________________📖 yau kam tun shida ta tashi, wanka tayi ta canja kayan ta zuwa fararen sport wears ta fice training, jogging taje tayi ta dawo sannan ta wuce gym ɗin da ta saka a ka haɗa mata a wani ɗaki dake gefen personal garden ɗin ta, bata fito ba se after 8, a gurguje ta koma ɗaki tayi wanka ta zauna ta gyara jikin ta tare da shafa mayukan ta na jiki da na ka. Tsaye tayi gaban wardrobe ɗin tana bin kayan ta da kallo cikin tunani kayan da zata saka, Muryar sa ce ta shiga maimaita kanta cikin ƙwaƙwalwar ta kamar lokacin yake faɗa ".......and the last shine you'll be dressing decently and abandoned clubbing, shikenan...........". Ɓata fuska tayi kamar a lokacin yake gaban ta yana faɗa mata, sake kallon wardrobe ɗin tayi tana maimaita 'decent dress' a ranta sedai a idanun ta duk kayan ta a decent dan ita bata ga illar su ko aibun su ba. Sauke idanun ta tayi kan wani Pakistan me matuƙar kyau, pusha Pink, ciro shi tayi ta warware tana bin shi da kallo, sosai ya burge ta da adon da akayi masa most especially na rashin nauyin sa, nan da nan ta zura shi a jikin ta kafin ta ƙarasa gaban mirror ta sha ga bin kan ta da kallo tun daga sama har ƙasa. A hankali tayi sighing ganin yadda yau mata kyau sedai she's feeling uncomfortable sosai dan bata taɓa saka irin su ba, ita kam kayan ga kullum different designers English wears ne, da su ta buɗe ido kuma da su ta saba shiyasa duk lalacewar su ita bata gani. Sake kallon kayan jikin ta tayi, rigar ta sauka har kan cinyar ta, wandon kuma ya buɗe sosai har yana fitowa ta tsayar gefe da gefen rigar yayin da ta tsuke da ƙafa se mayafin kayan dake hannun ta da bata san ya zata yi dashi ba dan bata jin zata yada shi ko a mafarki kuwa. Turare ta fesa tare da kama gashin ta in chignon style ta ɗora masa sombrero ta fice bayan ta watsa phones ɗin ta cikin clutch kalar platform ɗin ƙafar ta wato blue. Mommy dake zaune kan sofa tana kallon movies ta bi ta da kallo baki sake ganin kayan jikin ta, ba tare da ta kalli Mommy ba ta nufi ƙofar fita se kuma ta dakata tana dafe kan ta haɗu da faɗin "Ouch, Allah yasa ban manta ba yau". Da sauri ta koma falon tana ƙwalawa Rayya kira wanda yasa Rayyan fitowa daga kitchen da sauri tana amsa mata "Please follow me akwai kayan da zaki taya ni sakko dasu, tun jiya ya kamata na fito dasu but na mance". Saman suka koma tana gaba Rayya na bin ta a baya ta buɗe ɗakin suka shiga, kallon ɗakin kawai Rayya take tana sake ware idanu dan zata iya rantse wa tun da take bata taɓa ganin haɗaɗɗen ɗaki irin na Aunty Kisnah ba, ɗakin is just so wow masha Allah, tana can admiring ɗaki har bata ji maganar da Kisnah take mata ba se da ta taɓa ta "Am sorry Aunty, na shagala wajen admiring ɗakin ki har ban san kina magana ba". "Ke kam kullum ai a haka kike, Allah ya shirya ki kawai, ni ɗaukar mun wannan bag ɗin ki kai min ƙasa ki dawo yanzu Please". Da sauri ta ɗauka tayi ƙasa duk da jakar da nauyi amma bata fi karfin ta ba, seda ta sauke bags shida kafin suka ƙare Kisnah ta rufe ɗakin suka sauka gaba ɗaya, zaune suka sami Mommy a inda take sedai yanzu gaba ɗaya hankalin ta baya kan kallon da take yana kan haɗaɗɗun bags ɗin ne, ficewa Kisnah tayi batare da tayi mata wani bayani ba kan kayan se can suka dawo falon tare da wasu ma'aikatan gidan uku. Bags biyar ta nuna wa ma'aikatan suka ɗauka suka fitar dasu waje yayinda ta kalli Mommy "Wannan bag ɗin ta Maigado ce, tsarabar resort ce kuma na manta ban bata ba tun jiya yanzu kuma am in hurry ba zan iya jira har ta fito ba se ki bata, am off". Ta faɗa tana ficewa abin ta zuwa compound ɗin gidan inda aka ajiye ragowar bags ɗin kusa da blue ɗin motar da zasu fita da ita "Yaa wannan Black bag ɗin taka ce tsarabar resort ne". Ɗagowa yayi ya kalle ta ita kuma tana wa ma'aikatan da suka fito da bags ɗin magana akan su saka ragowar cikin Booth. Kallon ta kawai yake yana admiring shigar jikin ta, yadda tayi kyau cikin kayan abu ne da ba za'a iya yiwa kallo ɗaya a kau da kai ba musamman ga irin shi da basu taɓa ganin ta da wau kayan ba apart from English wears da take sawa. Sosai tayi masa kyau a ido kamar ya ɗauke ya ɓoye, se ta koma sak kamar Indians ɗin in ka cire sombrero ɗin da ta saka sedai hakan se ya bada wani style na daban. Juyowa da tayi bayan ta gama magana da ma'aikatan yasa ya ɗauke idanun sa da sauri daga kan ta yana istigfar a ransa dan yasan ya saɓa ƙa'idar kallon da Musulunci ya sharɗan ta, kallon bag ɗin gaban sa tayi taga har lokacin tana nan ko matsara da ita bata yi ba "Mudi ɗauki jakar nan ka kaiwa yaa ɗakin sa, yaa bashi key ɗin Please". Be san me ya faru ba se samun kan shi yayi da miƙa key ɗin wanda ita kanta seda hakan ya bata mamaki dan bata yi tunanin ze bayar ɗin ba ta dai faɗa ne. Ɗaukar jakar Mudi yayi yakai ɗakin kamar yadda tace ɗin sannan ya dawo masu da key ɗin, karɓa tayi ganin Sarakin kamar hankalin sa baya kan su dan se miƙa masa key ɗin ake amma kamar be san ana yi ba. Bubbuga jikin motar tayi hakan yasa shi buɗe idon sa da ya rufe ya zuba su kan ta, da sauri ta kautar da nata idon dan jin yadda gaban ta ya faɗi da kallon nasa "Muje yaa kaga ba Company muka nufa direct ba, kar muyi latti". Buɗe murfin motar kawai yayi ya shiga batare da yace komai ba dan ko ya buɗe bakin be san me zai ce ba dan duk wasu kalaman bakin sa sun gudu tuni. Shiga itama tayi ta zauna a seat ɗin ta ya tada motar suka fita daga gidan, har suka hau titi ba wanda ya kuma magana a cikin su se shine ya kai hannu ya kunna tafsir ɗin Suratul mu'umin daga bakin Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam (rabimahul lah). "Yaa ba Company muka nufa direct ba, zamu fara zuwa Al~araby orphanage and home of the disabled". (ƘASAR MU A YAU). Ta faɗa da sauri ganin ya ɗauki hanyar Company "Okay". Yace bayan ya samo Muryar sa da ƙyar kafin ya yi amfani da Google map na motar ya nemo location ɗin orphanage ɗin sannan ya ɗau hanya. Orphanage ɗin da ɗan tazara da inda suke dan a ƙalla 30 mins ne ya kai su, tun daga gare security ɗin wajen ke ta gaida su dan sun san Kisnah farin sani, wajen na daya daga wajejen da take matuƙar son zuwa watannin baya dan tana driving pleasure being with the kids. Office ɗin Dr Imam khaleed suka nufa bayan sun fito daga motar wanda shine ainahin me orphanage ɗin haka kuma dama ta saba se ta fara zuwa sun gaisa kafin ta wuce wajen yaran duk da ba ko yaushe yake zama a orphanage ɗin be se ya samu dama amma yana ƙoƙarin shigowa kullum dan duba buƙatun yaran though akwai manager a gidan dake handling komai in baya nan sedai yau da take sauri ba zata iya tsayawa gaisawa dasu ba dan they have a lot dake jiran su a Company. Cikin fara'a da mutunta juna suka gaisa da Imam khaleed dake ta Jan Saraki da hira wanda sedai yayi ta masa murmushi se ko amsar da bata gagara ba har suka yi sallama suka fito bayan sun sanar dashi security za su shigo da tsarabar yaran wadda Auntyn su tayi musu kamar yadda suke kiran Kisnahn. Fuska cike da farin ciki yake ta yi musu godiya ba wai dan sun kawo abin da babu a gidan ba a'a se dan kulawa da ƙaunar da take nuna wa yaran a ko yaushe, bags ɗin da ke Booth securities ɗin suka fitar kamar yadda aka umarce su kana suka nufi office ɗin shugaban su dashi su kuma suka ja motar suka fita. Duk da bata samu ganin yaran ba dan rashin zaman da bata yi ba haka suna lokacin sun shiga school amma fara'ar dake fuskar ta bata tafi ba ko kaɗan, a kullum in ta shiga gidan ji take kamar tana tare da family ɗin ta ne kuma family ɗin Nanar ta, ba ta fatan lokacin da zata daina ziyartar yaran a rayuwar ta dan wannan shine babban burin Nana har ta yi mata nisa dan haka ita kuma ta ɗauka wa kanta alƙawarin cigaba da kula da farin cikin Nana har ƙarshen rayuwar ta. Har suka ƙara sa masana'antar fuskar ta na ɗauke da wannan fara'ar, da walwala da komai ta gaida da duk ma'aikatan wajen kafin suka haura office ɗin ta, yau ma aiki suka sha kamar ba zasu tafi gida ba har se da aka kira magrib kafin suka bar building ɗin, yau ɗin ma haka ya tsaya a kanta tayi dukkan sallolin akan lokacin su tun daga Azahar har zuwa magrib da suka yi a nan kafin suka wuce gida. Cikin kwanakin haka suke kan ayyuka da kuma tsare tsare da suke ganin ze daƙile duk kan wata ta'asa dake faruwa a Company ɗin ta kuma kawo cigaba, alhamdulillah kuma an yi nasara sosai dan a kwanakin da suka biyo baya ba'a sake jin wasu ƙorafi akan ɓatan kuɗi ko kaya ba, haka ma ma'aikata dolen su suka mai da hankali kan aikin su dan ba wanda yake son a kore shi ko a rage masa matsayi kamar yadda Saraki ya tsara mata tayi threaten ɗin su. Izuwa yanzu komai Masha Allah inda a ƙarshe Kisnah ta bawa Saraki post ɗin personal assistant ɗin ta haka kuma next kin ɗin ta wanda ze iya shiga office ɗin ta ya gabatar da ayyuka ko da bata nan. Sannu a hankali suke ƙara shaƙuwa batare da ɗayan su ya ankara ba dan kusan ko da yaushe suna tare da juna, a office suna tare, a mota ma haka Kai hatta da gida dan da yawan ayyukan da basu ƙarasa a office ba haka zasu tattaro shi su kawo gida su zauna kan sa har se sun ga komai yayi dadai. Zuwa yanzu kam alhamdulillah dan little by little kisnha ta bar yin shigar da take na rashin tsari, duk da ba wai tana saka atamfa ko shadda ko lace bane sedai tana saka decent dresses, so da yawa takan saka jeans da t-shirt Amma se ta ɗora mata kimono dake kai mata har ƙasa kuma ta ɗaura yafa scarf, hatta da straight skirts in ta saka se ta nemi jackets, after dresses ko overcoats ta ɗora musu hakan yasa ya fitar da kusan rabin wardrobe ɗin ta ta bawa Rayya wasu ragowar kuwa duka ta bawa Maigado dan native wears ne ita kuma ta sake sabon zubi da ta zauna tayi online shopping daga England sune take amfani dasu yanzu. Duk da Maigado taji daɗin kayan amma hakan bashi ya hana ta yin baƙin ciki da takaici ba dan ita a gare ta ƙasƙanta ta Kisnah tayi da har zata bata kaya, alhalin kayan ko ɗan kwali bata taɓa ɗaura wa na daga cikin su, ranar haka suka zauna suka kashe lokaci wajen shirya plan ɗin tarwatsa Kisnah wanda dawowar Awwaf kaɗai suke jira komai ya fara tafiya kamar yadda suka tsara dan tuni Mommy ta amince da shawarar Aminiya kuma ƴar uwar ta da Jamila na auren Awwaf ɗin da Kisnah (ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta😏). ***** Sati na uku kenan da fara aikin su tare kamar yadda a office ɗaya suke zama sedai an fitar masa da nasa table ɗin a side ɗaya na cikin offices ɗin ta dake kowanne Company, a yadda suka tsara duk tana zama a kowane Company ne tayi kwana biyu, ma'ana tana komawa kowane Company ne duk bayan kwana takwas, in taje K&S drinks yau da gobe to jibi da gata kuma se taje K&S construction, next is K&S couture......haka haka har ta zagaya duka sannan ta kuma dawo wa farko wanda suka fara da K&S constructions. Yau ma zaune suke a K&S drinks, kowa na fama da keyboard na system ɗin shi, a cikin drinks ɗin da aka fitar last week ne aka samu wasu gurɓatattu wanda kusan an rasa rayuka kimanin goma sha uku sanadin shan lemon hakan yasa mutane yin bore har suna batun maka kamfanin a kotu, wannan yasa hankalin su ya tashi da son ganin sun daƙile wannnan ɓarakar da ta ɓullo ta hanyar gano wace iriyar ƙwaya ce ko poison aka saka haka kuma taya ya ƙwayar ta shiga cikin wasu daga drinks ɗin yayin da wasu kuma babu tunda ko da case ɗin ya ɓullo aka dawo musu da goods ɗin daga wholesellers ɗin su an yi tasting majority dan har su sun sha kuma babu komai a ciki, sosai abin ya ɗaure wa jami'an binciken dake kan al'amarin kai wanda hakan ne yasa aka dakatar da batun shiga kotu har se an kammala bincike. A hankali ya miƙa hannun sa ya ɗau hankerchief ɗin sa dake kan table ya goge gumin kan goshin sa kafin ya tura kujerar sa baya cikin sauke numfashi. "A cikin ma'aikatan gurin nan aka haɗa baki akayi wannan abun, waye Emeka maji?". Tsayar da abun da take yi cikin computer ɗin tare da maida hankalin ta kan sa "Yana ɗaya daga cikin in charge masu kula da quantityn ingredients ɗin da ake zubawa yayin haɗa drinks ɗin". Ta faɗa tana ƙure shi da idanu cikin son ƙarin bayani "Come closer". Da saurin ta kuwa ta bar seat ɗin ta zuwa table ɗin sa tare da jawo kujera ta zauna next to him, juyo mata screen ɗin system ɗin sa yayi yana mata playing vedio ɗin da yai pausing, shiru tayi ta zuba wa screen ɗin ido tana kallo cikin tsananin mamaki da rashin yarda da abinda take ganin har short video ɗin ya ƙare...........................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 28 (8/20/2022 8:41 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Ouummey 26 (8/20/2022 8:39 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________                            Page 2️⃣6️⃣ _________________________📖 Tare suka zauna a office ɗin suna ayyuka sedai ana kiran sallah ya dakata daga aikin da yake yi na bin record ɗin spendings na watan da ya wuce da ta nemi a kawo nata shine fa yake bin lissafin dan ganin ko daidai yake. Da kallo ta bishi kafin ta kautar da kanta ta cigaba da shigar da bayanan da take cikin laptop ganin ya shiga toilet, be daɗe ba ya fito fuskar sa jiƙe da ruwa haka hannun rigar sa a nannaɗe yana ƙoƙarin saukar dashi da alama dai alwala yayi. Ɗagowa tayi ta bishi da kallo jin fitowar sa sedai unfortunately idanuj ta ya sauka kan tsintsiyar hannun sa da yake ƙoƙarin sauke hannun

Chapter 17 of 27