Share this page
shara sosai da be hana a hango albarkatun ƙirjin ta ba, net ɗin ya kai har saman ƙirjin sosai, ƙafar ta kuwa wani shegen takalmi ne me tsini kamar tsinke, tsananin mamakin yadda za'a iya taka wannan takalmin shi ya daskarar dani waje ɗaya, barima ta gwal ta ciro cikin kayan fashions ɗin ta ta saka a kunnen ta yatsun hannunta kuwa ta wadata su da gold rings uku uku a kowane hannu, sarƙar ƙafa me kyau ta ciro ta zauna kan madubi ta maƙalawa ƙafarta ta dama kana ta zaro wata kyakkyawar jigidi me wani irin sihirtaccen sound ta ɗaura a dirarren ƙugun ta, turarurruka masu matuƙar kaifin ƙamari ta ɗauka ta feffesa a ko ina na jikin ta, kallo ɗaya me kallon ta ze to mata ya kirata cikakkiyar karuwa me licence, sheɗaniya number ɗaya haka kuma wadda shiryuwar ta se Allah..................✍️. *☑️Ote, Comment and Share fisabilillah*. Ouummey 08 (8/2/2022 3:41 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________                            Page 8️⃣ __________________📖 Box ɗin da take ajiyar keys ɗin motocin ta ta buɗe ta ɗauka ɗaya ba tare da ta tsaya duba wacce bace dan duk motocin ta latest ne, cikin ƙwarewa da iya taka takalmin ƙafar ta take taku ɗaiɗaya har ta fito daga bedroom ɗin ta, fresh kunun aya da ke fridge ɗin ta ta ɗauka gora ɗaya ta fita dashi a hannu, yanzu ma rufe ƙofar tayi bayan tayi resetting password ɗin buɗewa wanda haka take yi indai zata yi amfani dashi wajen kulle ɗakin da password. Sskin baki maigado dake kan dining tayi cikin ƙarewa shigar Kisnah kallo, bawai shigar tata ce ta bata mamaki ba dan ta saba yin wadda ma ta fita, yadda kowane kaya ke mata kyau shine yake sa take kasa riƙe kanta kullum Kisnahn ta fito se ta bita da ido. Yatsu biyu ta ɗagawa maigado cikin salon sheɗanci kafin ta wuce ta gaban ta tana kaɗa mata dirarren ƙugun ta da ya fito fes cikin wando jikin ta though ƴar jacket ɗin da ta ɗora kan kayan ta rufe har zuwa saman gwiwar ta, wata farar dunƙulalliyar mota ce me matuƙar kyau da ɗaukar ido ta buɗe ta saka drink ɗin ta a cikin kafin itama ta shiga ta zauna, warming up motar tayi kafin ta saki horn wa maigadi, da saurin sa ya fito daga ɗakin sa ya ƙarasa gefen gate ɗin, password ɗin gate ɗin ya daddanna gate ɗin ya fara zuge kansa shikuma ya matsa gefe, da mahaukacin gudun da ya zama tsarin ta ta fice daga gidan yayin da megadin ya koma ya sake pressing password ɗin rufe wa, kawu dake tsaye ta can saman benen sa yana kallon komai ya saki wani makirin murmushi kafin ta juya zuwa cikin parlon sa. Wayar sa ya ɗauka dake gefen sofar da yake zaune yai daddanna wasu numbers kana ya kara a kunnen sa, shiru yayi zuwa lokacin da aka ɗaga wayar sannan ya fara magana "Ta fito yanzu wanda am sure ba zata dawo da wuri ba se zuwa 2am dan haka ku bi bayan ta kuga inda tayi, kusan yadda zaku tare ta in ta fito lokacin dare yayi tsakiya kowa na gida, tun yanzu ku ɗau matsaya dan bana son aikin wasa, ban ce kuyi mata komai ba se barazana dan ina so ta tsorata ta bar batun dukiyar ta dake hannuna". Amsar da aka bashi daga can ya sa ya jinjina kai cikin gamsuwa kafin ya katse wayar yana jin sa cikin farin ciki dan ba shida tashin hankalin da ya wuce yaji Kisnah na maganar karɓar dukiyar ta wadda da ita yake ci yake taƙama yake wadaƙa da bushasha shiyasa yanzu ba shi da burin da ya wuce ya mallake ta takowace hanya kuwa. *******              *HIDEAWAY CLUB (The young Anacondas)*. Tun kafin ta ƙaraso bakin gate ɗin club ɗin take sakin mahaukatan horn, da sauri masu gadin wajen suka wangale makeken gate ɗin, ƙaton building ne da tun kafin ka shiga zaka san babban waje ne da ya ƙawatu da kayan alatun rayuwa, ginin tsakiya ne da ya wadatu da gilasai ta ko ina ba abinda yake se ɗaukar ido da reflecting abubuwa, kyawawan fulayoyi da furanni ne shushhuke a compound ɗin club ɗin da ya zagaye ginin club ɗin dake tsakiya. Parking tayi a parking lot ɗin wajen ta kashe motar, da gudu masu gadi da suka rufe gate suka ƙaraso wajen da take suna washe haƙora dan sun san tabbas yau kakar su ta yanke saƙa dan kyauta ne Kisnah take musu ta manya, kamar yanzu buɗe mata ƙofar tayi ta zuro ƙafafun ta kafin a hankali ta fito da gangar jikin, rusunawa sukai da sauri kowanne na gaisuwa da kirari, murmushi ta hau sake musu dan ita kam bata da wulaƙanci haka macece me fara'a da in kaga ta ɗaure fuska to fa an kai ta ƙarshe, gaishe su tayi daga tsaye sukuma suna durƙushe wanda biyu daga cikin su za su haife ta a haife dayan kuwa ya girme mata nesa ba kusa ba, check ta yi signing ta miƙa musu dan bata fito da cash ba, da sauri babban cikin su ya karɓa suna zuba godiya, bata kuma kula wanzuwar su ba ta ɗau wayar ta da goran kunun ayar ta ta rufe motar ta wuce cikin main building ɗin club ɗin. Babban hall ne dake shaƙe da jama'a maza da mata, mostly samari da ƴan mata ne a ciki se kuwa tsirarun manyan mata da maza da tsufa yai wa gardama sukai faɗuwar baƙar tasa. Ihu da sowa club ɗin ya ɗauka baka jin komai se kiran sunan Queen Kissy it's kuwa se murmushi take yi yalwatacce tana ɗaga hannun ta dake riƙe da key ɗin mota, ɗaya bayan ɗaya manyan yaran wajen suka ƙarasa suna rungume ta ba maza ba mata, da ƙyar suka ƙyale ta ta ƙarasa wajen su Meenah dake zaune a permanent VIP seat ɗin su, kujera Meenah ta ja mata ta zauna wanda itace permanent wajen zaman ta se Meenah a gefen daman ta, Hameedah a gefen hagun ta se Surayya da Maleeka a ragowar kujerun wajen da suka kasance biyar se wani haɗaɗɗen madaidaicin table a tsakiyar su. Daga inda suke take kallon ƴan wajen kowa ke sabgar gaban sa gefe ɗaya kuwa ƙaton filin rawa ne da ƴan rawa kowanne na ƙoƙarin son ganin ya nuna tasa bajintar, a nan kan table ɗin su kuwa manyan kwalaben wine ne da Maleeka tayi ordering dan iya kam cikakkiyar mashayiyar giya ce, a rana se ta shanye kusan kwalba uku ko huɗu, a irin wannan ranakun kuwa da suka zo club kafin su tashi tana iya shan biyu, ita kuwa Meenah gaba ɗaya hankalin ta yana kan lemon coke da take jijjigawa dan ƙwayoyin da ta zuba su narke, ita bata shan giya amma tana shan ƙwaya, Hameedah kuwa shisha ce take zuƙa tana fesarwa cike da ƙwarewa se Surayya da ita kuma hankalin ta ke kan mazan wajen, ita bata shaye shaye ko kaɗan se dai akwai ta da son maza, gajeren tsaki Kisnah ta saki tana fincike robar coke ɗin dake hannun Meenah dan a ɗan zaman ta na mintina talatin wannan ce roba ta biyu da Meenahn zata shanye wadda ta shigo ta tarar da wata a hannun ta. Cikin ɗan maye kaɗan da ƙwayar kan saka ta Meenah ta ɗago ta kalle ta, wata shegiyar harara Kisnahn ta wurga mata da ta saka ta komawa ta lafe cikin kujerar ta tana kumshe idanun ta dan tasan ma'anar hararar shine ta shanye iya kason ta na yau. Miƙewa Kisnah tayi ta zare ƴar jacket ɗin jikin ta ta ajiye kan seat ɗin ta tare da wayoyin ta, gorar sassanyan kunun ayar ta ta buɗe ta ɗaɗɗaka har yai rabi kafin ta rufe ta ajiye ta fice daga VIP ɗin ta nufi wajen masu rawar. A take duk masu rawar suka tsaya can kafin suka fara fita ya rage saura wasu uku, nan da nan aka canja kiɗan dake tashi wajen daga American songs zuwa Indian songs, wani irin kumshe idanun tayi tana jin kiɗan na ratsa ta kafin a hankali ta fara takawa ta kai tsakiyar mutum ukun, cikin wani irin salo ta fara kakkarya gaɓɓan jikin ta cikin salon waƙar tana malkwaɗe wa, banda ihu da sowa da tafi babu abinda ke tashi a wajen dan ko shakka babu tafi asalin jarumar da ta hau waƙar iyawa, haka ta dinga yin rawar waƙoƙi da dama kafin ta dakata tace a maida mata American songs ɗin, nan ma haka ta hau yi kai kace ba musulma nace balle ɗiyar hausawa kuma. A nan ta ɓata lokaci har kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare kafin ta fita a wajen, liƙi kam ta sha shi, manyan yaran wajen sun yi ruwan kuɗi kamar a ƙasa ake samo su, daloli da saifa sunyi kuka se ko ƴan dubu dubu dan babu ƙasa da dubun, ko da ta fito kowa ba ta kalla ba duk da ɗumbin mazan dake ƙoƙarin son yi mata magana, maida jacket ɗin tayi jikin ta kana ta zauna kan kujerar ta bayan ta kwashe wayoyin ta da gorar kunun ta ta maida kan table cikin mamakin ina Surayya ta je, takaici ne ya kamata ganin yadda gaba ɗaya daga Meenah har Maleeka suka fita hayyacin su yayinda Hameedah ke ta sambatu cikin maye. Kawar da kai tayi daga duban su ta buɗe goran kunun ayar ta ta kafa kai ta shanye dan sosai take buƙatar jiƙa maƙoshin ta, cillar da robar tayi sannan ta ja wayar ta ta hau latse latsen ta, tsawon lokaci kafin ta fara jin kan ta yana mata nauyi, jijjiga kan tayi cikin son dena jin komai ta cigaba da danna wayar ta, wani irin jiri jiri ta fara ji kafin ta fara ganin bibiyu uku uku, da sauri ta ajiye wayar tana dafa kanta da hannu ɗaya yayinda take mutstsika idon ta da ɗaya hannun. Sedai maimakon ta dawo daidai se ma ƙaruwa da abin yake yi dan har gani take kamar gurin na tafiya, sama ta dawo ƙass, kamar dai tana yawo a cikin gajimare, tashi hankalin ta yayi dan duk iskancin ta bata shaye shaye, ba abun da ta tsana ma a rayuwar ta kamar giya, ƙwayar kuwa ko a asibiti aka bata bata sha duk tsananin da rashin lafiyar da take yi kuwa. Kafin kace me ta rasa hankalin ta gaba ɗaya da har ta faɗa kan table ɗin gaban ta tana wasu irin surutai marasa kan gado gaba ɗaya jikin ta ya saki idanun ta sun juye. Daga can gefen wajen zaman su wasu samari ne da kallo ɗaya zaka musu kasan manyan yara ne saboda irin shigar dake jikin su, cike table ɗin gaban su yake da kayan shaye shaye, tukunyar shisha, ƙwayoyi, kwalaben maganin tari, cocain har ma da wasu da ban ko san su ba, su huɗu ne kowanne kuma da kalar kayan mayen da yake bankawa cikin sa banda ɗaya daga cikin su da yake danna waya yanayi yana duban Kisnah a kaikaice. Wani irin shu'umin murmushi ya saki kafin ya dubi na gefen hagun sa yana miƙewa "Ni na wuce, yau dai tarkon da na ɗana ya kama ɗawisu". Dariya duk suka sake na gefen damar da na faɗin "Kai baaba yau zaka kwashi Gara yacin, ko dai nima nazo na ɗana ne in ka gama". Wata shegiyar harara wanda aka kira da baaba ya sakar masa "Ka jimin ɗan iska, yau ina suhan ɗin taka da har kake kiran in rage maka, to bari kaji till Dawn zan yi dan haka ma kar ku jira ni ku wuce kawai zamu haɗe gobe". Sowa suka sa suna tafawa kafin ya musu sallama ya wuce, wajen su Kisnah ya ƙarasa lokacin tayi nisan da har bata gane waye a kanta, hannu yasa ya shafi fuskar ta yana kunshe ido saboda tsananin taushi da santsin fatar ta, wani irin lashe leɓe yayi da harshen sa cikin salon su na gogaggun ƴan guguwa kafin ya sa hannunsa biyu ya ɗauke ta kamar wata baby doll ya fice da ita daga wajen gaba ɗaya. A tazame Surry dake wani ɗaki ita da saurayin ta suna romance ta fincike jikin ta ganin yadda yau wani namiji ya samu damar taɓa Kisnah har ma ya ɗauke ta a hannun sa, da azama ta fita daga ɗakin wadda dama basu rufe ƙofa ba, to rufewar me zasu yi bayan kowa iskancin sa yake a fili, ko kafin taje har ya saka Kisnah a mota yayi mata key, da gudu Surayya ta koma table ɗin su ta ɗau key ɗin motar ta ta fita itama, tana fitowa compound shikuma Yana fita da motar daga building ɗin, a gigice ta figi motar ta fice kafin masu gadi su gama rufe gate ɗin da ya fita. Hannu ta kai zata yi accelerating motar se kuma ta fasa dan in yasan an biyo shi ze iya gudun da ze tsere mata dan ƙarfin hali ne kawai take yi amma jikin ta a mace yake da abinda saurayin ta ya gama yi mata. Sannu a hankali take bin bayan motar har suka ƙarasa bakin kasuwar durumi in da ta tabbatar ko ihu tayi za'a iya jin ta saboda shagunan masu kwana dake kan titin, ƙara gudun motar tayi taje ta sha gaban shi har ƙiris ya rage bata daki gaban motar shi ba, ajiyar zuciya ya sauke jikin sa na ɓari dan da be yi saurin tsaida motar Ba da se sun daki wanda Allah kaɗai yasan me ze faru in da hakan ya kasance. Ƙurewa motar gaban sa ido yayi cikin son gano waye ya sha gaban sa sedai be yi nasara ba kasancewar motar me baƙin gilashi, cikin motar kuwa hannu na rawa Surayya ta danna kiran jami'an tsaron da ke police station nan gaba dasu kaɗan dan ƙa'ida ne akwai police station gaban duk kasuwannin garin. Cikin Sa'a bugu biyu wani ɗan sanda yai picking call ɗin ta sanar dashi me ke faruwa, take ya shaida mata hadu nan tafe, cikin ɓacin rai baaba wanda asalin sunan sa Sageer ne ya fito daga motar dan ganin wane ɗan rainin hankalin ne ya tare masa hanya, a fusace ya kaiwa glass ɗin motar Surry wani mahaukacin bugu, ganin fa in aka cigaba da haka se iya fasa glass ɗin kuma ya damƙe ta yasa hankalin Surry tashi dan kallo ɗaya zaka yi wa baaba Kasan gawurtaccen ɗan Air ne, tunanin da ya zo kan Surayya yasa da hanzarin tai unlocking motar kana ta buɗe murfin da dukkan ƙarfin ta, take kuwa ya tafi ya daki kan baaba dake jiran a buɗe ya ciwa koma waye mutunci. Faɗuwa yayi gefe kan sa na zubar jini dan ba ƙaramin dukan sa murfin yayi ba Gashi kuma ƙarfen motar me ƙwari ne sosai, a fusace yake neman miƙewa dan cin uban Surry da tana buɗe motar yaga macece, da sauri ta finciko kwalbar lemo da tasha tana hanyar zuwa club ɗin ta jefe shi da ita, take ta same shi a ka ya kuwa fasa ƙara dan sosai kwalbar ta shige shi, jiri ne ya fara ɗibar sa saboda jinin dake zuba wanda har se da ita kanta ta razana, da sauri ta ƙarasa motar da ta fara ƙoƙarin fito da Kisnah daga motar sedai ta kasa dan duk jikin ta ya saki hakan yasa ta ƙara nauyi sosai, da ƙyar Surayya ta tallafo ta jikin ta suka nufi motar ta suna yi suna layi kamar zasu faɗi dan Kisnah tafi Surry nauyi nesa ba kusa ba. Ihu Surry ta saki jin shigar kwalba a gefen cikin ta wanda baaba ya daɓa mata dan baze bari taci bulus ba, sakin Kisnah tayi cikin jan numfashi a wahalce hakan yasa duk suka zube a wajen, tsabar taurin kai haka baaba ya miƙe jiri na ɗibar sa na komai ya ja su su biyun da hannu ɗaya ɗayan na dafe da kan sa, jiniyar motar ƴan sanda da yaji yasa ya sake su ya nufi faɗa wa motar da dan ya tsira saboda be manta kashedin baban da ba na in aka sake kama shi baze sake bailing ɗin shi ba, sedai ko kafin yakai mota tuni wani ɗan sanda ya sakar masa harbi a kafa da ya tilasta masa faɗuwa, da gudu wasu daga cikin ƴan sandan sukayi kan su Kisnah dake sheme a ƙasa bata hayyacin ta ga kuma Surayya dake zubar da jini a sume wasu kuma suka yi kan baaba aka sa masa ankwa a hannu sannan aka sashi a mota.......................✍️. 😭Wayyo Allah Kisnah ta😭 amma gaskiya baaba Allah ya isan mu😭 Surry mun gode miki Allah kuma ya baki lafiya😔. Duk wanda be min jajen abinda ya faru da Kisnah ba aradu bani ba shi eh😏 ©️ Ouummey📚✍️ *Vote, comment and share fidabilillah.*                             Ouummey 09 (8/3/2022 3:51 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________                            Page 9️⃣ _______________________📖 Asibiti aka wuce dasu su duka dan ceto ran su musamman Surayya da tafi su jigata. Kula sosai ake basu ganin ƴan sanda ne suka kawo su, dressing akayi wa baaba a kan sa tare da ƙafar sa dan bullet ɗin be shiga ƙafar ba yadai shafe ta ne. Allurai kawai aka yiwa Kisnah da zasu taimaka mata dawowa hayyacin ta da wuri ban da wannan ita kam bata cikin kowane haɗari, Surayya ce dama dai ke cikin matsala kasancewar kwalbar ta shige ta sosai dan se da akayi mata aiki aka cire guntuwar kwalbar da ta karye mata a jiki sannan aka ɗinke wajen, aluran kariya aka yi mata kafin a maida ita ɗakin hutu. Ta can ɓangaren kawu kuwa yana can yana baccin sa hankali kwance da tunanin koma ina Kisnah take zuwa yanzu an kirea mata warning ɗin da ze tsoratar da ita a kansa. Tun farar asuba da ya farka ya dannawa gang ɗin nasa kira batare da ya ko duba lokaci ko gabatar da sallah ba da ake ta kira a manyan masallatan kusa da su, seda tayi ringing ta gama har so biyu basu ɗauka kafin ana uku su ɗauka, be ko amsa sallamar da suka yi masa ba ya fara tambayar su batun aikin sa. "Acan muka kwana oga amma har zuwa ɗazu karfe huɗu bata fito ba kuma kasan ƙarfe uku ake rufe club ɗin, da alamu dai ta lura da muna binta to ta bi wani, hakan yasa dole muka haƙura muka koma maɓoyar mu dan ƴan sanda suna fitowa patrol, sedai a tara gaba". Cikin wani tuƙuƙin takaici da ɓacin rai kawu ya kashe wayar, tsantsan disappointment na wanzuwa kan fuskar sa dan ba abin da ya tsammaci ji ba kenan daga gare su. ************* A hankali a hankali ta fara buɗe idanun ta da take jin sun mata nauyi sosai, dishi dishi take gani dole ta sake maida idaun ta rufe kan ta sake buɗewa, a sannu a sannu har ganin ta ya daidaita ta fara ganin komai normal, ƙarewa ɗakin kallo take cikin tunanin me kuma ya kawo ta asibiti dan a cikakken kallo ɗaya da tayi wa  ɗakin ta tabbatar asibiti ne saboda gadajen dake jere a ɗakin, ƙarafan ƙarin ruwa da arin magani da ɗakin ke yi. Da ƙyar ta iya miƙewa tsaye dan nauyi da ko ina na jikin ta yayi mata, canular ƙarin ruwan dake hannun ta ta fisge har jini na rushing daga inda aka saka allurar amma bata damu ba,  band ɗin kanta ta cisge ta ɗaure hannun dashi wanda hakan yasa doughnut ɗin da tayi wa gashin ta bajewa ya kwanta lamɓan a bayan ta. Ƙafafunta ta zuro ƙasa da niyyar miƙewa sedai da sauri ta ɗauke cike da ƙyanƙyamin floor ɗin asibitin da yai jurwayen ƙura, hannu ta zura ta janyo takalman ta da bata san waye ya cire mata ba ta maida abin ta ƙafar ta sannan ta sauka, batare da tsayawa neman inda wani likita yake ko wanda ya kawo ta asibiti ba ta fice daga ɗakin, cikin Sa'a ba wanda ta haɗu dashi cikin ƴan sandan da suka kawo su ko likitan da ya karɓe su dan haka ta fice har bakin titin da ke gaban asibitin, napep ta tsayar ta shiga bayan ta faɗa masa inda ze Kaita, this is the first time of her being a motar haya kowace iri ce kuwa, kalle kalle take a titin har ta gane unguwar da take kafin ta sauke ajiyar zuciya. Tun da ta shigo motar mayen ƙamshin ta da ya kama jikin ta ko da bata saka ba balle ta ƙara wani yake tashi yana cika masa hanci, lumshe idanun sa yayi dan Allah yayi shi mutum me matuƙar so da ƙaunar ƙamshi sedai nata yayi ƙarfi da yawa shiyasa yake tashi sosai dan ko daga nesa mutum ze iya jin sa. Kamar kullum yau ma t-shirt and jeans ne a jikin sa sedai masu ɗan tsada ne dan duk kuɗin da yake samu a sallamar sa tarawa yake yana ƙara sutura dan mutum ne shi me son ƙyale ƙyale a jikin sa, kansa na ƙasa bakin sa na ɗan motsi hannun sa sanye da counter yana pressing alamar dai tasbih yake yi. Tun zaman ta bata san akwai wani a cikin napep ɗin ba se da traffic ya tsaida su daidai gaban wani me ɗan kiosk a gefen titi, ƙishirwar da ta addabe ta yasa ta neman ruwan da zata sha hakan yasa cikin muryar ta da bata gama dawowa daidai ba tai wa me napep ɗin magana dan ba ko sisi a hannun ta "Excuse me drive, bani ɗari biyar mana se in haɗa maka da kuɗin ka in ka kaini". "Ok". Kawai me napep yace tare da miƙo mata ɗari biyar ɗin da ta buƙata, karɓa tayi sannan ta juya side ɗin da ta hango me kiosk sedai wani ne a gefen side ɗin, batare da wata damuwa ba ta miƙawa na gefen nata kuɗin "Help me collect some water please brother". A hankali saraki da idanun sa ke kan counter ɗin hannun sa ya ɗago yana me sauke idanun sa kan hannun ta dake miƙo masa kuɗin, kamar baze karɓa ba se kuma ya saka nasa hannun ya zare kuɗin dake cikin yatsun ta cikin takatsantsan, ta ƙofar wajen sa ya miƙa kuɗin ya karɓo mata ruwan haɗe da canjin kana ya juyo ya miƙa mata, a side ɗin fuskar ta idanun sa suka sauka daidai lokacin da take gyara gashin ta da ya zubo ya rufe mata fuska, wani irin yamutsa fuska yayi ya ajiye mata ruwan nan gefe tare da kuɗin kana ya kau da kansa gefe yana kallon waje. A zuciyar sa kuwa wani irin ƙyanƙyamin ta ne ya cika zuciyar shi ganin gashin kanta da duk a tunaninsa attach ne ta saka ga kuma yatsun hannun ta da tayi wa fixing long nails da suka sha pink jan farce, ko kaɗan be lura da kayan jikin ta ba dan kallo ɗaya yayi mata be sake marmarin kallon ta ba dan ko ba ya ƙyanƙyamin ta shi mutum ne me kiyaye doka da ƙa'idojin da Muslunci ya gindaya, ba wanda ya sake ko tari tun bayan thank you

Chapter 5 of 27