Share this page
zauna da tarin gajiyar da yake ciki ba bayan all he's going through is because of her, Kai abubuwan hannun ta tayi ta ajiye gefen toilet ɗin kaɗan sannan ta koma corridor ɗin da drums ɗin su ke ajiye ta ɗau empty bucket ta zuba ruwa sosai ta fara ƙoƙarin ɗauka sedai nauyin da ta ji yasa ta ajiye tana yarfe hannun ta, kwaɓe fuska tayi dan all these are new to her, bata Saba da irin wannan rayuwar ba sedai bata jin zata fasa wanke toilet ɗin, da ƙyar ta iya kai bucket ɗin bakin door na toilet tana sauke numfashi tare da kallon palms ɗin ta da suka ɗan yi ja, numfashi ta sauke cikin faɗa wa kanta zata iya ta juya zuwa ɗakin su ta ɗauko daya daga cikin brooms ɗin da ya siyo ta ɗauko me ƙwari ta jujjuya a hannun ta (tsintsiyar kwakwa), banɗakin ta koma ta tura ƙofar, yamutsa fuska tayi itama dan itama ta ga rashin clear ɗin da ya faɗa, tunani take ta ina zata fara wanke wa se kuma tunanin kar ta ɗebi germs a kayan ta yasa ta ajiye broom ɗin ta tsugunna ta tattare ƙasa wandon fakistan ɗin jikin ta har zuwa kusa da gwiwar ta sannan ta ɗaure rigar a ƙugun ta se kuma ta tsaya kallon broom ɗin kamar zata fashe da kuka dan siri sirin saman ta san baze iya wanke toilet ɗin nan ya fita ba. Saudah dake tsaye ta window ɗin ta tana kallon ta ce ta fito kamar zata yi wani abu, motsin ta yasa Kisnah kallon wajen suka haɗa ido se ta ɗan sake mata ƙaramin murmushi, maida mata saudah tayi tana ƙarasowa kusan ta "Lafiya kike tsaye bakin banɗaki haka". "Ehm ina son wanke toilet ɗin ne but nasan wannan broom ɗin won't clean anything, ya zan mata pls". Ƴar dariya saudah tayi kafin ta shiga ɗakin ta ta fito da wata wuƙa kana ta karɓi tsintsiyar hannun Kisnah ta shiga datse ta a ranta tana mamakin yadda zata ce zata wanke toilet ɗin da bata ko daɗe da gama wanke shi ba, tana rage ta tana tambayar Kisnah yayi amma se tace a'a a sake datsewa har seda aka kai tsintsiyar kusan rabi kafin tace yayi mata ta karɓa tare da yiwa saudah godiya ta wuce toilet ɗin ita kuma saudan ta shiga gyara wajen . Ajiye komai tayi a gefe na tunanin bata saba ba bata kuma taɓa yi ba ta zuba toilet wash a floor ɗin tare da detergent tare da disinfectant ta zuba ruwa ta shiga wanke shi da iya ƙarfin ta, kusan saɓi uku tayi wa floor ɗin kafin ta ga yayi mata daidai a idanun ta ta saka ruwa ta ɗauraye sannan ta sake feffesa disinfectant da kuma toilet freshener, take kuwa scent ɗin toilet ɗin ya canja ba kamar ɗazu da yake fitar da wari kaɗan kaɗan ba. Bucket da broom ɗin ta maida corridor ɗin su sannan ta koma ta kwashi ragowar disinfectant, toilet wash da toilet freshener dan detergent kam se da ta ƙarar dashi tas, ajiye kayan tayi inda ta ɗebe su cikin wani ƙaramin basket sannan ta matsa wajen da yake kwance, hannu ta kai da niyyar tashin sa se kuma ta maida ta zuba wa fuskar sa ido cikin yi masa kallon ƙurilla a karo na farko tun da suke tare. Kallon sa take tana admiring duk wani abu na fuskar sa da idon ta ya kai kan sa har ta sauke duban ta kan ɗan siririn baƙin gashin da ke saman bakin sa da be haɗe da madaidaicin gashin dake haɓar sa ba, jajayen laɓɓan sa ta ƙurawa ido kafin kuma ta kawar da kai da sauri tana ɗan matsawa baya jin hannun ta ya fara mata ƙaiƙayin son shafa gaba ɗaya fuskar sa tun bare ma gashin haɓar sa, ɗan gyaran murya tayi cikin kunyar kanta da ya kamata sannan ta shiga bubbuga pillown da kan sa ke kai tana kiran sunan sa. A hankali ya buɗe idanun sa dake cike da bacci ya zuba a kanta yana kallon ta, kallon da ya haifar da wani electrification a cikin jikin ta gaba ɗaya sedai ta kasa kawar da kanta duk da abinda take ji dan kyan da idanun sa suka masa a lokacin baze bar ta ta janye ɗin ba, rufe idon da yayi yasa tayi firgigit cikin tuna abinda ya kawo ta dan haka ta sake kiran sunan sa, wannan karon bata kalli fuskar sa bata shiga masa magana Muryar ta a sanyaye dan tun kallon farko da yayi mata komai na jikin ta ya saki. "Ka daure ka tashi kaje kayi wanka, na kai maka ruwan toilet". Maida idanun yayi ya rufe dan baya jin ze iya tashi a lokacin saboda daɗin da baccin yayi masa "Lokacin Sallah fa yayi ma, gashi can naji kamar ana kira a masallaci". Ta faɗa da sauri dan tasan abinda zata ce kenan ya tashi ba musu, aikuwa dai tar ya buɗe idon sa yana kallon ɗakin su da yake da ɗan duhu kafin ya miƙe ya zauna na wasu sakanni Sannan ya tashi ya ɗau buta ya fita, ruwa ya zuba na alwala sedai yana buƙatar amfani da banɗaki dan fitsari yake ji, takaici ne ya kama shi na tuno yanayin banɗakin na ɗazu, be san me yasa masu gidajen hayar garin nan basa yin toilet a ɗaki dan duk gidan da suka je kafin nan suma toilet a waje yake kuma guda ɗaya, be yi shiru ba lokacin ya tambayi dillalin ko ze iya samun ɗaki me haɗe da toilet sedai amsa ya bashi da su basa toilet a ɗaki sedai in gidan kai ne. Ɗaki ya koma ya fara fitar da kayan wankin toilet dan gwara ya wanke ta shiga a tsaftace duk kuwa da gajiyar da yake tare da ita har lokacin, bata ce masa komai ba ya fita daga ɗakin hannun sa ɗauke da robobin sedai yana dosar wajen ya hango floor ɗin very clean and neat ga Kuma ƙamshi da yake yi, tsaye yayi yana bin toilet ɗin da kallo kafin ya juya zuwa ɗaki da sauri. Ajiye robobin yayi cikin baskets ɗin su ya shiga bin Kisnah dake zaune da kallo, a ƙafar wandon ta da hannun rigar ta ya tsayar da kallon sa ganin yadda suka jiƙe, basket ɗin kayan wankin toilet ya ɗauka ya shiga bubbuɗe su yana dubawa, alamun an yi amfani dasu da ya gani yasa ya tabbatar itace ta wanke. "Wa ya saki fita wanke toilet bayan kin San da ciwo a ƙafar ki kuma ba iya wanke irin wannan kikai ba, what in kika faɗi fa". Yaso ya bata dariya sedai kuma ta ji daɗin kulawar sa "Taya bazan je wankewa ba bayan ka kwanta a gajiye baka yi wanka ba saboda rashin kyan toilet ɗin, nikam ba zan iya barin ka kwanta haka ba". Sosai kalaman ta suka yi tasiri a ran shi haka kuma yaji daɗin concern ɗin da ta yi showing Masa sedai be nuna ba ya bar abin a ransa "Rashin yin wanka na is none of your business, ƙafar ki ya kama ta ki maida hankali ta warke ba yin abinda ba'a saki ba". "Ciwo na is none of your business, wankan ka ya kamata ka maida hankali kayi ba damuwa akan ciwon da ke jiki na ba". Ta bashi amsa cikin jin haushin rashin appreciating effort ɗin ta. Murmushi ne yayi escaping a lips ɗin sa jin ta maida masa da amsa daidai abinda ta faɗa masa, be kuma cewa komai ba ya fita daga ɗakin ya wuce toilet ɗin bayan ya ɗau mini basket ɗin wankan su dake ɗauke da sponge, soao, shower gel, da turaren wanka. Ba kaɗan ba yaji daɗin wankan duk da ruwan ya Salamce ba kamar lokacin da ya sirka shi ba da zafi sosai, ko da ya gama se yaji kamar ya sauke wasu nannauyan kaya a jikin sa, fitowa yayi hannun sa riƙe da bucket ɗin ruwan basket ɗin wankan a cikin sa jikin sa sanye da baƙar jallabiyar da ya shiga da ita a hannun sa. Gaba ɗaya se yaji shi so uneased feeling kamar kowa na kallon shi dan be saba hakan ba, be ji sauƙin abin ba se da ya shiga ɗakin su sannan ya sauke ajiyar zuciyar relief. Tashi tayi ta fita daga ɗakin ganin ya ciro kaya ze saka amma ya ƙi sawari ya tsaya kallon ta riƙe da kayan a hannunsa, lokaci ta bashi sosai sannan ta koma ɗakin dan tasan ya isa ace ya gama shiryawa, jallabiya ya ɗora kan three quarter ɗin da ke jikin sa ya ratse ta ya nufi fita "Ina kuma zaka je yaa". Ta tambaya da sauri, ɗan tsayawa yayi tare da kallon ta "Ita kuma sallar wa ze yi min?, ko bake kika faɗa min an kira ba?". "To wasa nake ai, na faɗa ne dan ka tashi kayi wanka, shugaban an iya baƙar magana". Ta ƙarashe can ƙasa kamar me gunguni. Bece mata komai b aya koma cikin ɗakin ya zare jallabiyar jikin sa ya ajiye kan jakar kayan sa kana ya nemi waje yayi zaune kan carpet ɗin dake tsakiyar ɗakin ya rage daga shi se three quarter da t-shirt mara nauyi da ta kama shi a jikin sa. Tana ganin ya koma ɗakin ta fita ta shiga neman abinda zata ɗora musu girkin dare, jallof sphagetti take son yi sedai basu da kayan miya da vegetables ɗin da zata haɗa dasu, komawa ɗakin tayi ta dube shi yana zaune "Zan ɗora girki yaa amma babu kayan miya da sauran abin buƙata". Shiru yayi yana tunanin wane girki ta iya da har zata ce masa ba kayan haɗi, shifa ko da ya siyo kayan abinci ba wai nufin sa ta dinga girki ba dan yasan ba abinda ta iya, ya siyo ne dan ya dinga dafawa da kansa, yayi musu breakfast, lauch da dinner, in Kuma ya fara fita sana'a se ya dinga musu breakfast da dinner launch Kuma se ta dinga siya. "Ki bar girkin se gobe yau zan siyo abinda za'a ci gobe kuma se ki min listing duk abinda babu se a siyo". Ya faɗa yana kaiwa jingina, bata ƙi ba ta koma ta zauna bayan ta mayar da abubuwan da ta fito dasu da wanda zata yi aikin girkin dasu. Haka suka cigaba da zama shiru kowa da tunanin da yake a ransa har aka kira magrib ya fita, kamar yadda yace haka ya shigo da ledar da yayi musu takeaway da zasu ci da dare bayan yayi sallar isha a masallaci................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, Comment and share fisabilillah. Ouummey 41 (8/28/2022 8:55 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________                            Page 4️⃣1️⃣ _________________________📖 kan katifar su ka kwanta su biyun sedai kowa yana edge ɗaya na each side, dukkan su sun daɗe bacci be ɗauke su kowa da irin kalar tunanin da yake a ransa kafin Sarkin iya sata ya ƙwamushe su. Yau ma seda ya tada ta da asuba sedai be fita ba se da ya tasa ta gaba tayi alwala tare da saka hijab ta zauna kan dadduma sannan ne ya fita, zama tayi jiran ayi kiran sallah na biyu ta gabatar da sallah kamar yadda yace mata sedai ta ƙi yin nafilar da yace ta yi maimakon zaman jira dan kar bacci ya ɗauke ta. Tana idar da sallah ta cire hijab ɗin ta ninke ta maida jakar kayan ta ta koma katifa ta kwanta cikin sake sabon bacci, ko da ya dawo ya same ta kwance be yi yunƙurin tashin ta ba dan jikin sa ya bashi tayi Sallah, kan daddumar da ta bari ya zauna ya shiga yin azkhar ɗin sa ya gama ya ɗora da tasibihan da ya saba sannan ya tashi ya zare doguwar rigar jikin sa ya ajiye tare da mayar musu da ƙofar ya rufe ya wuce kan mattress ɗin ya kwanta a wajen sa tare da lulluɓa, mintuna kaɗan kuwa bacci ya ɗauke shi dan har yanzu yana ɗan jin gajiyar aikin jiya a jikin sa. Hayaniyar yara dake tashi a tsakar gidan ya hanata bacci yadda take so dole ta haƙura ta tashi ta zauna tare da duban wall clock ɗin da ya taho dashi jiya bayan Isha da ya je siyo musu abinda zasu ci, ƙarfe tara da mintuna uku na safe amma shi ne har yara sun tashi a baccin su gashi itama sun hanata nata da iface ifacen su da duk bata saba dashi ba, ita a gida in ta kwanta bacci ba wanda ke tashin ta har se ta gaji ta tashi dan kanta, to ina ma suke da yaran da zasu dinga irin wannan hayaniyar. Tsaki taja tana ayya na sam gidan haya be yi ba a ranta, kallon gefen da Saraki yake tayi taga shi baccin sa yake hankali kwance da alama ma be san ana wata hayaniya ba balle har ta dame shi, buta ta ɗauka ta buɗe ɗakin ta fita tana hamma a hankali, drum ɗin su ta buɗe ta ɗebi ruwa cikin butar dan zuwa toilet sedai tana zuwa bakin toilet ɗin ta ja ta tsaya ganin yadda aka yi masa kai baka ce shine wanda ta wanke jiyan nan ba, wani irin ɓaci ranta yayi da bata san sanda ta doka uban tsaki ba ta juya zuwa ɗakin su bayan ta dangwarar da butar a ƙofar shiga ɗakin. Fitsari take ji sosai ga kuma wanka tana son yi amma a yadda toilet ɗin yake ta gwammace tayi fitsarin a jikin ta da ta shiga, takaici yasa kawai ta fashe da kuka dan fitsarin ya matse ta. Kukan ta ne ya tashe sa daga baccin da yake yi, be miƙe ba seda ya saurara sosai yaji kukan a ɗakin su ne, zaune tsakiyar carpet ya ganta ta haɗa kai da gwiwa tana gurzar kuka kamar ƙaramar yarinya, dafe goshin sa yayi cikin tambayar kansa yanzu kuma me aka yi mata da take wanann kukan da sassafe, kallon ƙofar su yayi da haske ya ratso ta jikin labulen lu, shi dai yasan seda ya rufe ƙofar daze kwanta dan haka kenan ita ta buɗe ta fita, kenan a wajen akayi mata abinda yasa take kukan hala, ganin tunani baze kaishi ba yasa ya tambaye ta da Muryar sa irin ta wanda ya tashi da bacci "Ada dai nasan kina da jarumtar rashin yawan kuka sedai naga alama a kwanakin nan kin koma raguwar ƙarfi da yaji, yanzu kuma me akai miki kike kuka haka kamar wata ƴar baby?". Seda ta ja hanci kafin ta buɗe baki tayi magana cikin sautin kukan da har lokacin bata dena ba "Ba toilet zan shiga ba, kuma duk an ɓata shi kamar ban yi wahalar wanke shi ba jiya kuma ni fitsari nake ji sosai". "Kawai ki ce kina son yin kashi kuma sun ɓata meye na sako kin wanke shi jiya in ba salon dama kiyi min gori ba kin wanke min toilet nayi wanka, Allah ma yasa ni ban sa mutum ba". Ta sani so yake ta bar kukan shi yasa ya tsokane ta sedai bata jin zata saki ranta in ba fitsarin nan tayi ba dan ji take marar ta ta wani ɗaure kamar zata fashe. Fita yayi daga ɗakin ya ɗau bucket ɗin wankan su ya cika da ruwa kana ya dawo ɗaki ya ɗauki basket ɗin wanke toilet ya fita, da sauri ta tashi ta bishi daidai lokacin da ya zare jallabiyar jikin sa da ya saka lokacin da ze fito ta karɓa da sauri shi kuma ya shiga wanke toilet ɗin tana tsaye bakin ƙofar riƙe da rigar sa, seda ya wanke toilet ɗin fes kafin ya ɗauraye sannan ya karɓi rigar sa ya zura ya fito ta maida ƙofar ta rufe da sauri dan kamar ma fitsarin ya fara zubowa taji, ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta gama fitsarin tayi tsarki sannan ta buɗe ƙofar zata fito sedai taci karo da ruwa a bucket ɗin su tare da kwandon wanka bakin ƙofar, zagaye wa tayi ta wuce zuwa ƙofar ɗakin ta ɗaya labulen tana tambayar sa ruwan wankan sa ne wancan sedai amsar da ya bata yasa taji wani abu na ratsa zuciyar ta game dashi "No naki ne, ki maza kije kiyi wankan kafin nan nawa yayi zafi se in yi in kika fito, in Kuma kika bari suka sake ɓatawa ba wanke miki zan yi ba tam". Murmushi ta saki na farin ciki kafin ta juya ta koma toilet ɗin ta shigar da ruwan da kwandon ta rufe ƙofar ta shiga wanka tana lumshe ido saboda zafin ruwan da ke ratsa ta, duk da ta fi son wanka da ruwan sanyi amma wanan ta san zai taimaka wajen tafiyar mata da gajiyar gyara ɗakin da suka yi dan gwara shi yayi wanka tun jiyan ita kuwa se yanzu ne za tayi . Dogon hijab ɗin da ta saka ta ɗora kan towel ɗin da ta ɗaura a jikin ta ta buɗe ƙofar ta fito hannun ta riƙe da bucket da basket ɗin su a ciki, a ƙofar su ta ajiye ta shige ɗakin da ƴar guntuwar sallama a bakin ta, miƙewa yayi ya bi ta gefen ta ya fita zuwa juye nasa ruwan yayinda ita kuma take kiciniyar cire hijab ɗin jikin ta dan ta shirya. A nutse ta kammala shafar ta sannan ta ciri wasu riga da skirt da ta gani cikin jakar kayan da yace mata ta ta ce ta sanya, skirt ɗin baƙi ne daya sauka har kan ƙaurin ta se rigar sa ja da tayi mata cif cif a jiki, gyara gashin ta tayi ta sa masa ribbon ta zazzage jakar cikin neman abinda zata rufe gashin ta dan so take ta fita ta nema musu abin da zasu karya, se da ta birkice kayan duka kafin ta samo ƙaramin baƙin veil ɗin wata Arabian gown me sauƙin kuɗi da ya haɗa mata a kayan, mai da ragowar tayi ta rufe jakar sannan ta yafa veil ɗin da ya tsaya iya kafaɗun ta ta fita bayan ta ciri kayan tea a gurin da suka adana kayan abincin su, gas ta kunna ta ɗora ƙaramar tukunya ta zuba madaidaicin ruwa tare da jefa Lipton ɗin a ciki ta rufe ta zauna kan ƙaramar kujerar robar da ya haɗo cikin kayan robobin da ya siyo musu tana jiran shayin ya tafasa. Tana zaune ya fito daga wanka ya nufo ɗakin, gaban ta ya tsaya yana ƙarewa shigar ta kallo kafin ya juya bayan su dan ganin ko akwai me ganin su, ba kowa se yaran da ke ta wasan su a tsakar gidan da suka yi wa kaca kaca kasancewar weekend ba boko se islamiyya ita kuma se da rana, fisgo hannun ta yayi daga zaunen da seda ta miƙe haka kuma ba ɓata lokaci ta faɗa kan ƙirjin sa dan fisgar ba ta wasa ya mata ba, cikin ɗakin ya jata suka shiga kafin ya saki hannun ta ya shiga bin ta da kallo, ran sa ya matuƙar ɓaci ganin ta zaune a tsakar gida da wannan shigar a jikin ta bayan ta san basu kaɗai bane a gidan sedai yanzu da ya gama ƙare mata kallo se ya nemi faɗan da ya shigo da ita ze mata ya rasa dan ba ƙarya kayan sun matuƙar amsar ta haka sun fito da hasken ta sosai, ba ƙaramin kyau tayi masa ba shiyasa ya manta da faɗan da ya shirya yi "Lafiya yaa, tea fa nake dafawa Dan mu karya, am hungry sosai". Ta tambaya ganin bece mata komai ba se kallon ta da yake yi hakan yasa ya tuno da faɗan da yayi niyya dan haka ya watsa mata harara "Wai me yasa bakya jin magana ne, so nawa zan faɗa miki babu kyau fita da irin shigar jikin ki amma dan taurin kunne kin ƙi denawa, yanzu dan Allah dubi fa yadda kika fita bayan kin san akwai wasu mazan da basu dace su ganki a haka ba". Kallon kanta ta sake yi tun daga ƙasa har sama kafin ta dube shi "Yaa kalla fa kayan jiki na ba inda yake buɗe a jikina se fa hannu na kawai, and se fa da nasa veil a kaina fa, kuma iya ƙofar ɗaki na fita ba waje ba". "Ba inda yake buɗe amma ba curve ɗin da be bayyana ba a jikin naki zaki tsaya yi min musu, meye amfanin veil ɗin naki, da baki saka ba gaba ɗaya ze fi, tunda da baki fita ba ai seki sa himma yanzu ki fitan na manta ne ba yau kika fara tallan jikin ki ba kin saba, You go ahead ki nuna halin ki anan ɗin ma kinji". Ya ƙarashe a zafafe jin tana neman raina masa hankalin wai ba waje ta fita ba, to me ya hana ta fita wajen se taji daɗin da take so kowane low class ya kalle ta ai dama ta saba. Ita ba me damuwa da abinda mutane suke faɗa a kanta bace shiyasa bata taɓa ɓata ranta dan an kira ta karuwa sedai bata san me yasa ba a duk lokacin da shi ya faɗa mata magana se taji rayuwar ta ya ɓaci kamar dai yau, gaba ɗaya walwalar da ta tashi da ita se ta neme ta ta rasa, bata kuma ce masa komai ba kamar yadda be kuma kallon ta ba ya juya ya zauna kan katifa yana shafa mai a jikin sa, dogon hijab ɗin da ta shiga wanka dashi ta zura jikin ta ta fita wajen gas ɗin, tea ɗin ya tafasa ba so ɗaya ba dan gashi nan yayi kala sosai, madaidaicin tea flask ɗin su ta janyo ta saka cup ta dinga ɗiba tana zubawa a ciki har ya kusa cika sannan ya ƙare ta sauke tukunyar ta ajiye a ƙasa dan dama ta kashe gas ɗin. Ɗauraye pot ɗin tayi ta maida ɗaki sannan ta koma ta shigar da flask ɗin ciki ta ajiye tsakiyar carpet ɗin su, cups ta ɗauka ta fita ta ɗauraye suma ta kai kusa da flask ɗin sannan ta ɗauko gwangwanayen kayan madara da ya siyo jiya da dare tare da bread ta ajiye, cup ɗin da ya fi girma ta ɗauka ta tsiyaya masa tea ɗin ta saka cubes ɗin sugar huɗu ta zuba masa madara da bournvita sannan ta kai masa gaban sa da yake zaune kan carpet kusa da katifar su ya shirya cikin jeans dogo da t-shirt. Duk abinda take yi yana kallon ta haka kuma mamaki ne ya hana shi magana na yanda ta haɗa tea daidai, tambayar kan sa ya ringa yi a ina ta koya kafin kuma ya bawa kansa amsa da ai ba wani wahala zata iya haɗawa dan alamu sun nuna ita ke haɗawa kanta. Nata ta haɗa ta koma gefe ta shiga sipping a hankali zafin shi na ɗan ƙona ta sedai ko kaɗan ba wannan zafin ne a gaban ta ba dan zafin maganganun da ya faɗa mata ɗazu sun ninka wannan so ba iya ka, ko rabi bata yi ba taji shayin ya fita a kanta ta ajiye dan dama haka take, indai ranta a ɓace yake bata iya cin abinci shiyasa ba ta ko kalli gefen da bread ɗin yake saboda tasan ba zata iya ci ba. Tunanin rayuwar ta ta shiga yi da yadda ta taso ba wani me kwaɓa, komai tayi kawai daidai ne a wajen kowa, bane ce mata yi, bari, gyara  ko makamancin haka shiyasa take duk abinda taga yayi mata daidai a ranta, yanayin shigar ta kuwa abu ne da yabi jinin ta, tun da tayi hankali da masu irin shigar ta buɗi ido ta kuma rayu a tsakiyar su under supervision ɗin Mrs Andrew Smith Wanda itace matar shugabar makarantar da kawu ya danƙata a hannun sa, bata san meye al'adar ta ba,

Chapter 26 of 27