kaɗai zaisa yaƙi mutuwa, ko kuma ke kice kin janye"
Ni dai sai godiya kawai nake yi nama rasa godiyar wacce iri zanyi musu dukkansu.
Ɗakinmu ɗaya da Mariya kuma shekarunta ko ya haura nawa zai zama da kaɗanne.
Gidansu gidan karamci ko shara sun hanani, duk abinda na tashi zanyi da zummar taya aiki sai Umma da Mariya su hanani fur.
Ana gobe zan koma gida ina kwance shiru, Mariya da Umma sun sun tafi umara, asalin tafiyar ta Mariya ce ta kaita ne domin ta roƙi Allah ya cire mata son tsohon mijinta a zuchiyarta. Sun yi mun alƙawarin da sun dawo zasu sa Kamilu Ya kawo su har inda nake. ina tunanin yadda zan koma mu kwashe da su Maigogul.
Ga sammaci har an yanka goben magatakarda zai kaima Babangida sabon sammacinshi. Ni da lauyana kuma duk abinda ya kamata ya sani dole na sanar dashi kuma ya ajjiyeni akan magana ɗaya babu gargada.
Idanuna na lumshe
Ko yaya su Mardiyya suke, kuma yaya suka ji lokacin da labarin ɓatan dabo na ya bayyana musu oho.
Ƴar Shuwa na tuno nayi wani murmushi wanda ni kaina bansan ma'anarshi ba, girgiza kaina kawai nayi ta yi.
Washegari da wuri na shirya Baba Haule mai aiki ta kawo mun abincin karin kumallo.
"Mai sunan Malam yace in kin gama ki fito yana jiranki"
Gabana ya tattake ya kuma yankewa. Tunda dai na tashi nake cikin faduwar gaba.
To Haule nagode sosai.
Sannan na gode da kulawarki gareni. In sha Allah zan dinga kawo muku ziyara lokaci zuwa lokaci."
A sanyaye nayi karinnan na sha magungunana.
Ƙarfe goma dot muka tsaya a daidai gidan da su Adama suke haya.
Tun kafin mu tsaya na hango Adama a tsaye a dokin ƙofar da tsohon mijinta ga ƙatuwar leda a hannunshi yana miƙa mata.
"To ki sauka ki soma shiga sai ai mun iso ko? Sai mu tafi gidan naku"
Ajjiyar zuchiya na sauke dan tun muna hanya na sanar dashi wajen yayyena zamu soma zuwa. Tukunnan
Toh bari inje gama ya ta can a tsaye da mijinta"
Idanu ya ƙura ma Adama har yana sauke tangaran ɗin jikin tagar motar tashi.
Daidai Adama ta dumo wani ashariya ta lailayama mijinta kenan.
Idanuna na runtse shi kanshi na fahimci zagin ya kiɗimashi. Abinda nake gudu ƙila fa saiya faru, shi yasa tun farko nake ta neman hanyar zillewa amman dana lura bani da wata hanya dole sai Dr Kamilu ya haɗu da su Rakiya yasa dole muka tawo. Tunda ko basu hadu a gida ba zasu haɗu a kotu ai.
A hankali na sakko sai kawai Adama ta ganni.
A guje ta shige cikin gidan
Sai gasu tare da su Labbai harda Uzairu Zuchiyata.
Gam muka rungume juna ni da Adama da Uzairu zuchiyata dukkanmu muka saki kuka ni ko da gaske nake rerashi kamar wata ƙaramar yarinyar goye.
"Iko sai Allah Lolo kece kika dawo ashe zaki dawo garemu mu har mun cire ƙauna da sake sanyaki a idanunmu. Duk rintsi kada ki sake tunanin guduwa mu tsaya ma kanmu da kanmu"
Cewar Uzairu zuchiyata dake tsaye kusa daf da mijin Adama.
"Ya isa haka Adama ido ya soma yawa."
Labbai tayi maganar tare da ɓanɓareni a jikin Adama
Tare muke da baƙo Adama. Yana so yaga su Rakiya"
Kafin ma in rufe baki har ya ƙaraso inda muke da sallamarshi.
"Allah sarki bawan Allah kaine ka tsinceta kenan? Tawo mu shiga daga ciki. Su Maigogul basa nan Hauwa ce kaɗai a gidan."
Kallonshi nayi nace.
Yaya mu shiga kaji basa nan. In ka sake dawowa ka gansu"
Muna gaba yana biye damu har cikin ɗakin su Adama wanda naga sun samu arzikin gyarawa har da gas ƙarami, ga ɗan kayan abincinsu a gefe.
Waje muka bashi akan kujerar ya zauna shi da Uzairu zuchiyata wanda hankalinshi yana kan wayarshi ma.
Mu kuma muna kan katifa.
Gaggaisawa akayi Dr Kamilu ya kwashe kab halin daya same ni ya basu kabari da dai irin jinyar dana sha duka komai dai.
Ajjiyar zuchiya Adama ta sauke.
"Tabb ashe daman akwai bayin Allah irinka? Bawan Allah mun gode maka da iyayenka baki daya Allah ya saka da alkhairi.
Ni na tashi daga bacci na tarar bata gidan cikin dare ta fice. Kuma ta fita ne a cikin wani irin mawuyacin hali mai muni. Alhamdulillah data faɗa hannu nagari. Jiya jiyannan naje na dubo su Mardiyya inata dai basu haƙuri kan rashin uwarsu da irin zaman da suke yi a hannun matan uba.
To iyayenmu har yanzu suna kan bakarsu akan ba'a isa an kashe wannan auren ba. Ita kuma Lolo dama tauri gareta inta botsare kamar gandar kai haka take.
Amman dai zamu kuma tuntuɓarsu Allah bashi in suka ji irin halin data shiga fitar data yi ko zasu sassauto"
Dr Kamilu ya gyara zama yana kallon agogonshi.
"To a dai fahimtar dasu ba'a zaman aure da zalunci. Haka zalika ba'a aure dole balle irin nata auren mai cike da zalunci. A irin kondishon ɗin da take ciki ba'a buƙatar ko tunani ta yawaita balle shiga wata damuwa.
Inaga Sabuwa ni zan tafi ko zuwa dare sai in dawo inaso shi Baba mu gana dashi ko zai fahimceni"
Da sauri na ɗago Labbai tayi carab tace.
"Ai shi tafiya yayi Allah kaɗai yasan yaushe zai dawo ma. Sai dai in ya dawo ko a waya ne saita sanar maka"
Muka haɗu muka rakashi har bakin motarshi muna mishi godiya marar iyaka.
Kayana ya sauke mun
Muna shiga ɗakin sai ga Maigogul ya faɗo ɗakin afujajan babu ko sallama.
Tsaye yayi hannunshi riƙe da ƙugu yana kallona tar.
"Lolo kece ashe da gaske ashe zaki dawo garemu?"
Nice Maigogul "
Sai kuma naga ya zauna yana ƙare ma ɗakinsu Adama kallo
Labbai na gaban tukunya tana zuba abinci, Uzairu zuchiyata ko hankalinshi na kan waya sai murmushi yake yi.
"Lolo sabida mun hana mijinki ya sakeki sabida ke ƴar abu ta kazan ubace shine kika tafi wajen shi Khalid mai hure miki kunnen gabaki ɗaya ayi duk abinda za'ayi ko?
Ai kin bamu mamaki kuma baki cika ƴar duniya ba da kika dawo. Sannan da kika tawo wajensu Adama kin kaso auren ne hankalinki ya kwanta ko?"
"Haba Maigogul wai me yasa baku damu da rayuwarmu bane, ku dai kan ku kawai kuka sani?"
Faɗin Adama kenan. Daƙuwa yayo mata.
"Ohh sabida kuna zawarci shi Dakacin da yake zuwa wajenki yana baza ƙaryar kaya ya kasa turo iyayenshi. Mijinki yanzu haka yana gida amman kin ƙi bashi haɗin kai shine ita kike so ta kaso auren nata. In ta kaso kika san waye zai zo ta aureta? Sannan in hakane baga can mijinki yana ta godonki ki koma kin ƙi ba sabida kina neman maiƙo ba. Shine ita kike son rabata da nata maiƙon da yake hannunta ko? Kuma ai ko dan Mardiyya ai ta daure tayi haƙuri. Lolo mufa dukka wannan akan sonki muke yi wallahi Allah"
Adama tace
"Shikenan tunda haka kace a mayar da auren shi Alhaji in yazo zan faɗa mishi na koma gidan mijina shikenan ai. Inata faɗa muku saki ukune aure ya ƙare a tsakaninmu ƙaryace kawai yake yi muku"
"Ni dai bance miki haka ba Adama. Ba haka nake nufi ba ehe"
Sai naji yayi ƙasa da muryarshi. Harma da bagarar da zancan ta hanyar cewa.
"Labbai miƙo mun inci in tafi. Hiye harda kifin gongoni kuke girki ni ubanku kun barni cikin wahala"
Kai kawai na girgiza ina jin baƙin ciki tamkar yayi ajalina.
Saida ya zuba loma a bakinshi kafin yace.
"Kici yanzu in mayar dake ɗakin ki tun kafin kayi nayi ta dawo."
A_a Maigogul wallahi Allah na gama auren Babangida bazan sake zaman aure dashi ba. Na gwammaci in kashe kaina kowa ya huta tunda ba ƙaunata kuke yi ba"
Na ƙarashe maganar cikin tartsatsin kukan baƙin ciki.
Adama ta shiga labarta mishi halin da na shiga da duk labarin da Dr Kamilu ya basu. Uzairu zuchiyata ya ɗaura da cewa.
"Yarinyarnan tana fa da ƴancinta a wannan karon mu ƴan uwanta wallahi sai inda ƙarfinmu ya ƙare daga nan har kotun Allah ya'isa. Wannan karon har ku in bakui wasa ba wallahi a kotu zamu maka ku a cire mana hakkunmu. Yanzu fa da a ƙasar wajene hukuncin ma kisa za'ayi muku"
Labbai tace.
"Tabbas kuwa a wannan karon dole sai Lolo ta rabu da mijinta tunda dai tace bata yi. Bari ma in kira su Rahama in sanar musu da dawowarta. Mardiyya ma akwai waya a hannunta bari in kira su roƙi Babansu suzo"
Nan da nan ta kira su Rahama. Tana kashewa ta kira Lambar Mardiyya ihun yaran naji suna karanto adda,ar godiya ga Ubangiji
Ai sai kukana ya tsananta."
"To ai shikenan. Na tsame hannuna a kan sha'anin Lolo. Ai kowa rai yaima daɗi ba kamar maishi ba. Kuma duk daɗin inuwar gemu taba kai ga maƙoro ba. Allah ya baku sa'a mu ƴan kallo ne. Nauyin ki ba a kaina zai ƙare ba inma kin fito yawon tazubas kike sha'awar komawa gaki ga duniya. Har ku koma ga Allah ba ku isa kunyi abinda ni ko uwarku tayi ba. Kai kuma da kake cewa a yanke mana hukuncin kisa Bismillah. Lolo kiyi haƙuri ki dena kukan haka kukanki na dafani kinsan sonki"
Kwanon daya ci abincin ya jefo ma Adama a fuska ya fice.
Hmm kaɗai na iya cewa.
Idona kawai na runtse na kwanta na juya bayana kawai.
Ina jinsu sunata hirarsu har Rahama ta ƙaraso, su Sadiya ma duk suka shigo da suka dawo. Harda Hauwa saida ta rarrafo tazo ganin ƙwab. Rakiya ma tun kafin ta dawo gida labarin dawowata ya isheta.
Itama ansha tababa da'ita su Adama ke Magana ni ko bana ko buɗe idona ma.
Maƙota sukaita shigowa munafurcinsu ni dai sai dai ace musu bacci nake yi.
Idanuna biyu ras.
Mardiyya:.
Suna zaune tana ba Malama maganin da Babansu ya kawo mata na mura tana sha. Ƴar Shuwa tayo sallama ta shigo tare da tsayawa a kansu.."
"Ba wanki kike mun ba ubanme yasa kika barmun wanki kika dawo wajen wannan makirar yarinyar. Ke ga mai ƙanne ko?"
Aɗɗa'u yace.
"Ita ba makira bace wallahi. Kuma in ummin mu ta dawo saina faɗa mata duk dukanmu da kike yi"
Ai kafin Mardiyya tayi magana tuni Yar Shuwa ta makanta ganin Aɗɗa,u da wani zazzafan gigitaccen marin da sai da ya shiɗe.
"Kaji mun ƙaramin marars kunya. Ko da yake barewa ba zata yi gudu ɗanta yayi rarrafe ba. Tunda ka Tsotsi nonon Sabuwa kuma jinin Maigogul da kayi nayi yana yawo a jikinku dole kayi.
Ke kuma dan abu ta kazanki zaki wuce ne ko saina ɓallaki?".
Da sauri Mardiyya ta dure Malama ta fita ta koma kan tulin wankin da Ƴar Shuwa ta tula mata dana Fati dana Babangida ma.
Zuwa tayi ta dasa kujera tana kallon Mardiyya tana zage_zage.
Wayar da Babangida ya mallakama Mardiyya dan ya dinga jin ya suke in baya nan. Da kum su riƙa magana da Sauban itace ta shiga ruri. Ganin number Labbai yasa ta ɗaga da sauri. Ai tana jin abinda Labbai tace sai ta miƙe.
"Kika ce Umminmu ta dawo? Alhamdulillah"
Iyakar abinda tace kenan ta kwashi gudu sai ɗaki.
Su Aminu suna kan Malama da take ta faman kukan ciwo. Mardiyya ta shigo sa gudu ta ɗauki hijabinta ta saka.
"Ku taso muje wajen Babanmu ya bamu kuɗin mota Umminmu ta dawo.
Ai nan suka shiga murna a gaggauce suka fito Ƴar Shuwa sai kwaɗama Mardiyya kira take yi amman ko waige.
Da wani bawan Allah suka ci karo yana neman ɗan aike. Ganinsu yasa ya tsaidasu.
"Ku shiga cikin gidannan kuce ana sallama da Babangida kacigari "
"Ai Babanmu ne. Baya nan yana makaranta"
Aɗɗa'u ne yayo maganar.
"A ina makarantar take dan Allah?"
Mardiyya tace.
"Babu nisa can ƙasan layinnan ne yanzu ma wajenshi zamu je"
Ai kuwa wannan ma'aikacin kotu yabi su Mardiyya har makaranta wajen Babangida.
Mai gadin makarantar ne ya shiga ya kirawo musu shi.
Tun daga nesa daya hango su Mardiyya tsaye da wani mutum sai yaji faɗuwar gaba.
Hakan yasa ya ɗago ƙafa ya ƙaraso.
"Baba Ummi ta dawo zamu je wajenta"
Ƙuruci dangin hauka. Malama ce ta tari Babanta da wannan maganar.
Sai kan shi ya ɗaure ya shiga rarraba idanu tsakanin yaran da wannan mutumin.
"Assalamu alaikum bawan Allah kaine Babangida kacigari ko?"
Hannun daya miƙo mishi dan suyi musabaha shima ya miƙa mishi tare da amsa sallamar.
"Nine Babangida Allah yasa lafiya?"
"Sai alkhairi dama naje gidanka nemanka ne to sai yaranka suka ce dama wajenka zasu zo suma shine na biyo su. In babu damuwa mu ɗan keɓe mana"
Yaranshi ya kalla yayi jim daga bisani yace.
"Mardiyya ku shiga ku zauna a waccan barandar ku jirani"
"To Baba"
Ta ja yaran zuwa ciki. Wannan mutumi ya miƙo ma Babangida sammaci.
"Wannan sammacine daga kotun musulunci matarka Sabuwa ce ta shigar da ƙaran
Akan abinda take ƙaran, da kuma ranar halartar kotun yana jikin takaddar zaka gani.
Dama Abinda ya kawo ni kenan na barka lafiya "
Musabaha suka kuma yi har wannan mutumin ya wuce Babangida na tsaye kanshi na jujjuyawa ya shiga zurfin tunani. Duk da ta ƙasan ranshi yayi matuƙar farin ciki da jin kalmar Sabuwa ta dawo, sai dai wannan sammacin ya danne mishi murnar tashi.
"Sabuwa uwar rigima da taurin kai. Mu zuba muga waye zaiyi nasara a tsakaninmu. Babangida shine mijinki tilo a duniya, babu ɗan abu ta kazan daya isa yasa in sake ki"
Muryar su Aminu ce tasa ya juyo da sauri ya kallesu.
"Mardiyya Ummanku wai ta dawo da gaske tana gida yanzu haka?"
"E Baba ta dawo Labbai ce ta kirani take sanar mun. Acan ta sauka shine muka zo ka bamu kuɗin mota muje wajenta"
Tashin hankalin da yake ciki ai sai ya kuma nunkuwa duk da yana da yaƙinin su Rakiya zasu iya dawo da'ita ko Baba Malam ya kirata yace ta koma ɗakinta. Da wannan dalilin ya sauke ajjiyar zuchiya. Ya shafi kan Malama zafi rau.
"Mamana jikin har yanzu da zafi. Inaga zansa zuwa yamma a kai ki asibiti"
Kuɗi ya zaro a aljihunshi dubu ɗaya ya basu suka kama hanya suka tafi.
Shi kuma ya koma class amman ina ya kasa koyarwar sam dole ya nemi izinin cewar baya jin daɗi zai koma gida.
Yana tafe yana juwa.
Su Ramatu ana tsakar gida an barbaje magungunan mata matan unguwar sun cika tsakar gidan anata batsa Babangida ya shigo.
Karab a kunnenshi yana jin sanda Ramatu take ba da labarin jiya data yi amfani da wani magani waishi kurman namiji wai saida Babangida yaita ihu tana rufe mishi baki."Kai kawai ya girgiza dan ƙarya take yi shi salab ma ya jita musamman jiyan.
Kanshi a ƙasa yazo ya wuce su ya shiga ɗakin Ramatu kwananta ne.
Zubewa yayi a kujera baƙin ciki goma da ashirin ya haɗe mishi.
Sai da Ramatu ta ƙaraci surutunta kafin ta shigo ɗakin.
"Lafiya ka dawo alhalin lokacin dawowarka cin abincin rana bai yi ba? Kaga ni ko cefanen banyi ba ma wanda zan aika ya siyo mun kayan miya na rasa kuma yaran waccan matar naga basa gidan.
"Wacce matar kike magana akai Ramatu?"
Yayi tambayar cikin tuhuma jin kamar muryarshi a ɓace yasa ta haɗiye maganarta.
Ɓurum Ƴar Shuwa ta shigo ɗakin da shirinta tsab na fita uunguwa.
Zama tayi a kujera.
"Sannu da dawowa?"
"Hmm yauwa sannu"
Sai ta ɗanyi murmushin dole kafin tace.
"Dama yanzu na fito zan leƙa makaranta in sanar maka Mama ce ta kirani wai tana son ganina da gaggawa shine dama"
Ƙur yayi mata da idanunshi kamar yana karantar wani abu daga motsinta.
"Amman bana hana a dinga biyo ni makaranta ba. Shin wayar hannunki meye amfaninta da ba zaki kirani ba?"
"Allah ya huci zuchiyar mijina da girman kujerarka. Wayarce babu kati shi yasa wallahi. Aimun afuwa"
Sassautowa yayi kaɗan. Hannu yasa a aljihu ya ciro dubu guda ya miƙa mata.
"Kar kiyi dare kinsan ke zaki karɓi girkin dai yau ko?"
Murmushi tayi harda wani kallon gefen da Ramatu take tako tsume. Sai ta saki murmushin kissa.
"Ni ko nasan ni zan karɓi girki Jannati. Ai kamar yadda kake zumuɗin zagayowar kwanana nima inayi. Ko zaka bani kuɗin cefanen nayo a gida dana dawo girki kawai zan ɗaura"?
Hannu yasa a ajjihu ya ciro dubu biyu ya bata.
"Me kake so to a girka?"
Saida ya ɗan yatutse fuska kafin yace.
"Tuwo zaki yi miyar kuɓewa ɗanya kisa nama kona ɗarri biyar ne na gaji da cin shinkafa shinkafa "
Miƙewa tayi tana dariya.
"An gama harda kifi ma zan haɗa in saka maka. Ni saina dawo. Ramatu na fita"
Ciki ciki Ramatu tayi mata saita dawo.
Ledarta data ajjiye a ƙofar ɗakin ta ɗauka yara na biye da'ita taima matan gida sallama.
Gidan dillaliya ta shiga. Tako yi katari babu kowa a gidan dillaliya kamar ma fita zata yi.
"Ƴar Shuwa kece da hantsi haka ta samu kenan?"
"Uhm dillaliya duk wanda kika gani a gidanki ai siya ko siyarwa yazo yi. Tukunna ma dan Allah an samu kulolin kuwa?"
Dillaliya tace.
"Bana kuloli sunyi wuyar samu waɗanda na samu gaskiya masu tsada ne irin na ƙarfennan dubu har ɗari da goma. Jiyannan kishiyarki ta siye su wallahi.
Idanu Ƴar Shuwa ta zare harda dafe ƙirji ta furta.
"Na shiga uku. Kikace fa dubu ɗari da goma kuma Ramatu ta siye dama Ramatu na da kuɗi haka?"
Dillaliya ta fashe da dariya tace.
"Ki dai zauna ta fiki fada. Kinga tun lokacin da kika haɗo kan kulolinki duk kika siyar ɗayar mai shegen tsadan saida nace miki kada ki siyar amman kika ƙi ji. To ga kishiyarki tasai waɗanda suka fi naki tsada kuma babu mamaki dan tasan kina da sune. Waɗannan fa in sababbine zasu iya yin ɗari huɗu ma"
Ƴar Shuwa duk saita ruɗe abubbuwa suka caɓe mata goma da ashirin.
Atampopi biyu ta zaro ta miƙa ma dillaliya tana haɗiyar yawu.
Bayan dillaliya ta gama jujjuyasu saita buɗe jakarta ta zaro dubu sha uku ta ba Ƴar Shuwa.
"Haba dillaliya bafa kayan sata bane. Ya atampopina masu tsada zaki mun haka?"
Kuɗin ta miƙa ma Dillaliya ita kuma ganin haka yasa tace.
"Kai daɗina dake gajen haƙuri yanzu iyakar abinda ke wajena kenan. In kika dawo ki biyo
Allah bashi na sama miki wasu kulolin kinga sai mu wanye.
Dariya Ƴar Shuwa tayi tace.
"Dillaliya kin yarda dai ina binki bashi ko?"
Dariya suka saka duka.
A tare suka fito har titi daga wajenne kowacce ta kama gabanta.
Rai babu daɗi Ƴar Shuwa ta shiga gidansu da sallama an je munafurci.
MRS BUKHARI
Gobe bazan samu zarafin turowa ba haka jibi ma sai zuwa talata in Allah ya kaimu cikin masu rai
Aimun afuwa bani da lafiya ne yanzu haka ma daga asibiti muka dawo.
Nagode sosai son so💪🏼
[8/18, 7:50 AM] BADA'AT IBRAHIM: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA GOMA SHA BIYU
*KUYI HAƘURI BA KULLUM ZAKU DINGA SAMU BA HAR SAINA SAMU LAFIYA NAGODE SOSAI*
SABUWA:.
Idanuna ban buɗesu ba har saida na jiyo amon muryarsu Mardiyya. Malama ta faɗo jikina tana kiran sunana. Naji jikinta kau da zafi.
Da sauri na miƙe zaune kaina ya wani mugun sara mun har saida na dafe.
Mardiyya bata da lafiya ne Malama?"
Dawowa suka yi kusa dani dukkansu sai tattaɓani suke yi.
"E Ummi bata da lafiya mura da zazzaɓi take yi amman Baba ya siyo mata magani. Yace ma da yamma zai kaita asibiti. Ummi ina kikaje dan ALLAH kada ki sake tafiya ki barmu"
Murmushi kawai nayi musu. Aɗɗa'u yace.
"Maman Fatima kullum saita dake mu kuma taita tsine miki Ummi."
Adama tace.
"Zata rina. Ƴar abu ta kazan... Zan rakaku gidan in zaku koma wallahi sai munyi kare jini biri jini da'ita dan Yar Shuwa zuma ce sai da wuta."
Nan wannan yace wannan wannan yace wancan. Ni dai ina maƙale da yarana.
"Ummi baki da lafiya ne kin rame sosai?"
Mardiyya bani da lafiya tun ranar dana barku ina kwance ne a asibiti ko gane wanda yake kaina bana yi."
Nan yaran suka shiga aikin yi mun sannu da jikina.
Rakiya ce ta aiko ai kiranmu dukkanmu.
Miƙewa mu ka yi muka ɗiba yuu zuwa gida.
Gaza na tsakar gida ya gwafe sai wanke kaya yake yi. Ga wasu lesuka ya dauraye harya shanya. Naga ga wata mata mai kama da ƴan daba taci riga da wando ta ɗame a zaune a gefenshi tana ta shafa kan Rahine.
Ga magina a cikin gidan sun tayar da ginin ɗaki harma an gama zance dan baifi bulo ɗaya za'a ɗaura ba a kashe ginin.
"Allahu Akbar kaga Lolo Sabuwa mai sabon aiki ba ehh ashe kin samu kanki yarinya kin waiwayo gida? Bafa zan ɓoye miki ba gara da kika dawo duk tsiya ku mata ne kar ku sake ku shiga bariki gara ku zauna ehh a gabansu Rakiya kuyi duk wacce zaku yi. Duk da ehh na sani da gabansu da Bariki duk ɗaya amman ko yayane zasu yi muku garkuwa dai"
Maigogul dake zaune akan turmi yana yanka nama yace.
"Loko kizo ki shirya su Adama sui miki rakiya gidanki dalilin kiran da Rakiya tayi miki kenan tun kafin uban mijinki yazo kinsan zaice miki ki koma ɗakinki dai kafin a gama shari'ar da kika nace"
Na buɗe baki zanyi magana Gaza ya daga mun hannu tare da tsame hannunshi a wankin. Wuƙa ya zaro a kugunshi ya shiga kartawa a wani ƙaton dutse da muke zama.
"Inaaa wallahi Allah daya ne Lolo ba zata koma gidan wancan ɗan akuyar ba. Ko abinda ya faru a kotu wallahi Ni Gaza dan bana gidannane da bazai faru ba.
Nifa zan kashe Babangida uban kowa ma ya huta wallahi. Ehh jibi yarinya yadda ta fita hayyacinta har ta gudu ta bar gida yanzu ta dawo ace zata koma. Ai ko shine autan maza ehh gara ta zo ta zauna tunda ba dole bane sai tayi auren ba. Dattijo a wannan karon fa Babangida zai iya rasa ranshi in baiyi sakinnan ba, wai anya kuwa ba'a caca aka ciyomu ba kuwa? Ƙiyayyar da kuke ehh mana tun muna yara ai ta isa. Ke Lolo ki shiga ki zauna ki bararraje."
Maigogul yace.
"Inta bararraje kai zaka ɗauki nauyinta ashe ko?"
"To saime tunda kai ba iyawa zaka yi ba saita rataya ai a wuyana. Su kuma waɗannan yaran su bar gidannan tun kafin in yankasu Wallahi kar su sake zuwan mana gida. Ku kuzo ku fice kafin in yanke ku ehh"
Da sauri ya nufo kanmu.
Matar dana gani a gefen Gaza da bansan wacece ba itace tayo carab ta riƙe wuƙar tana magana da muryan dabanci.
"Ahh huce Gaza ai su yarane kuma basu da lefi a kan komai. Zasu koma shima ubansu bazai bari su dawo nan ba. Eh su Maigogul a dinga sassauta musu iyayene koma yayane eh ba zaka so mu haifi Maigogul ƙarami yazo yana sa'insa damu ba"
Kaina a ɗaure cikin rashin kuzari nace.
Gaza wacece wannan ɗin?"
Ihu yayi da wuƙa a hannunshi yana jujjuyawa kafin yace.
"Wallahi aure nayi fa Lolo da aurena na baro gidan yari ma kinji rabo. Kin ganta nan ƴar amana ake faɗa miki mace mai haƙuri da kulawa. Kayanta nake wankewa ma kuka shigo. Wallahi baki ga kulawa ba lokacin ina kotu harda nama take kawo mun. Allah kin ganta da aikinta gandiroba ce mai tsaron ƴan balaja'u.
Idanu na zare kawai ina mamaki.
Rakiya tace.
"Ai sai ku koma tunda Gaza ya ɗaure miki baya zaki bijire mana."
"A_a kada ki ja magana Rakiya a bijire take fa dama. Wai yau aka saba wannan rikicinne. Ku dan abu ta kazan... Kuzo ku bar gidannan nan ai ba gidan ubanku bane"
A gigice Mardiyya ta riƙe hannun ƙannenta suka fita. Juyawa nayi na bisu a baya na jasu zuwa gidansu Adama. Ina jiyo ihun Gaza yadda kuka san mahaukaci wallahi. Yaushe ma dan Allah ƙwaƙwalwata zata huta a gidanma. Maigogul sai donna zagi yake yi shi kuma, girki ma yake yi yau a gidan.
Ku zauna anan nima yanzu zan dawo"
Nan na barsu na koma ciki na tadda matar Gaza a cikin su Adama a ɗakin Rakiya harda Gazan sai labari suke ana dariya.
"Lolo kinga gini inayi ko? Madamsy nake ma gini kinsan bata tare ba har yanzu tana kwana dasu Rakiya ne."
Allah sarki Allah ya baku zaman lafiya"
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ameen ai Lolo tun a gidan yari Gaza yaita bani labarinku
Sai bayan da mukai aure ya fito sai muka zo muka tarar ba'asanma inda kike ba. Amman yanzu me ake ciki dangane da makomar auren naki?"
Adama ce ta basu labarin na sake shigar da wata ƙarar harma an kaima Babangida sammaci. Gaza yace.
"Bana wallahi in dai Babangida bai bini a hankali ba saiya rasa rayuwarshi. Nifa Lolo da zaku yarda sawa zanyi a kamosho in saka mishi wuƙa a wiyanshi wallahi sai ya sake ki. Ko in kasheshi kya yi idda ne ko takaba oho dai. Uban kowa ya huta.
Su su Maigogul babu abinda suka saka a gabansu sai son kudi.
Ku duba yadda duk muka zama ƴaƴa duk babu na gari"
Rahama ce tayi carab tace
"Gara ka bari abi matakin Shari'a tukunna. Yaci albarkacin ubanshi da ƴaƴanshi Gaza.
Na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 19