Share this page
Maigogul. Maigogul har tasha ya raka mu bai baro tashar ba ƙarewarta har saida motarmu ta tashi. Ƙarfe taran safiya a Kano tayi mana. Uzairu zuchiyata ya kira wani abokinshi ko ina suka san juna oho sai gashi anzo har tasha an ɗaukemu a ƙatuwar mota, ni dai ina bayan mota nayi zuru." Mrs BUKHARI ce taku Babangida :. [8/24, 10:16 AM] BADA'AT IBRAHIM: https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=ems_copy_c IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI BABANGIDA:. Tuƙin cikin rashin nutsuwa yake yi. Babu nutsuwa tattare dashi ƙwaƙwalwarshi sai hasko mishi fuskar Sabuwa da Khalid take yi. "Yanzu kana ji kana gani zai rabaka da matarka ya kuma aureta kai kana kallo?" Zuchiyarshi ce ta shiga tunzurashi. Tsaki ya saki kawai ya girgiza kai. "Ina wallahi bazan taɓa bari haka ta faru ba. Sai dai ni dashi mu rungumi juna mu mutu amman ba dai ya auri Sabuwa ba." Wawan burki yaja a daidai bakin layinsu. "Ku sauka kuje akwai inda zanje" Yayi musu maganar a kausashe. Babu shiri suka sakko yaja motarshi fuu sai majalisa dama acan suka yi da Mustapha zasu haɗu ya karɓi motarshi mashin ɗinshi ma yana majalisar. Ko daya ajjiye motar bai zauna ba cewa yayi dasu yana zuwa. Kai tsaye ya nufi gida Baba Malam yana zaune a kujera cikin almajirai yana karɓan karatu Babangida ya shiga da sallama. Ita data zame mishi wajibi ita ya amsa amman durƙuso da gaisubar Babangida basa gaban Baba Malam. "Baba Malam dan Allah kaimun aikin gafara kaimun izini in dawo da Sabuwa ɗakina tunda har yanzu iddarta bata cika ba. Wallahi tunda muka rabu ban sake samun kwanciyar hankali bane. Kuma a yanzu wallahi na tuba na dena duk abinda nake yi. Nayi maka alƙawarin bazan sake sakin ko wacce mace ba ba kuma zan sake jajiɓo Aure ba" Ƙur Baba Malam yayi yana kallonshi yama rasa me zaice dashi. Domin dashi da shi ai sun san saki ne da babu kome a tsakaninsu. Haƙiƙa yaga ɗimuwa da gushewar tunani tattare da Babangidan. Yau ga ranar da yake yawan tunatar da Sabuwa zuwanta tazo. Murmushi yayi yace. "Bakin alƙalami ya riga daya bushe. Hala baka san ƙarfi da zafin shari'a bane ko? To ka sani in ma sabida uwarka kake yi Babba ta bar gidana kenan har abada. Kasan har saida na rabu da'ita na samu nutsuwa kuwa? Kai yaro tashi ka kama gabanka kada ka sake zuwanmun da irin waɗannan yashasshun zantukan. Inma turoka akayi ga amsa ka samar in kayi wasa ƴar gaisuwar taka da nake amsawa sai in dena nan ba wajen wasa ko wajen gwaji bane" Da sauri Babangida ya miƙe har yana tuntuɓe ya fice a makarantar ya nufi gidan Malama Babba. Acan ya tadda Kawu Manga a tsakar gida sunata tattaunawa duk akanshi ne. Waje ya samu kusa da Kawu Manga ya zauna jiki a mace ya gaishesu dukkansu kana ya ɗauki tagumi. "Toh kin dai ji abunda ake ciki. Nayi nayi ya amince yaronnan yaci gaba da koyarwa a makarantar Wallahi yaƙi fur. Dana matsa ma sai ya dena magana. Nifa Babba bana ganin lefin Yaya sabida a tsari na tafiyar rayuwar Yaya shi yadda da amincewa ɗaya ne tak. Daga ranar daka ci amanarshi ko ka aikata abinda zatonshi bai zata ba shikenan kai dashi yadda har abada" Malama Babba tace. "Toh shikenan babu komai tunda haka Malam ya zaɓa ai. Babangida nayi nayi dashi ya ɗebi kadarorina yayi amfani dasu tunda yana da ido a harkar baban bola amman yaƙi. Filina sukutum na mallaka mishi ya samu ya gina ya zuba matanshi a ciki yaƙi amsa, nice zanyi mishi ginin yaronnan wallahi yaƙi. Ni ba daɗin wannan faɗi tashin da yake yi nake ji ba. Nace to ya sai da filin ya samu mota ya ɗan dinga hawa yana sana'a da'ita duk dai abinda aka kawo Babana yaƙi yadda." Babangida yace.. "Baƙin amsa nayi ba. Ke Malama ce kina da saninki kada sona ya rufe miki idanunki. Ba daidai bane ki ɗauki wani shashe na dukiyarki ki bani ni ni kaɗai ba tare da kinba sauran yaran naki ba. Inma lallai akwai buƙatar hakan dole saida amincewarsu ɗari bisa ɗari da saka hannu kan takaddar yarjejeniyar cewar an bani abu kaza da amincewarsu bakuma ya cikin gado, ko hakan akayi an tauyesu. Malama in kowa ya yarda Kudidi da Sa'a ba zasu taɓa yadda ba. Ayi haƙuri kawai ina kan nema da izinin Allah komai zai wuce. Ni da magana nazo Kawu inason in mayar da Sabuwa ɗakinta gaskiya " Idanu Malama Babba ta zare kawai sai ta saki kuka kawai. Kan Babangida ya sake cajuwa shi kaɗai yasan irin azabtuwar da zuchiyarshi take yi. Ga wani irin masifaffen kishin Sabuwa da yake ta danne mishi numfashinshi. "Kul ka kuma zuwa mana da wannan maganar. Ni dai ko bayan raina kada ka sake gayyato mana Sabuwa cikin haularmu, sannan ai kasan aurenku ya ƙare har sai in Sabuwa ta yi wani auren ta fito ko? Ya kake son sake saka mahaifiyarka a cikin mawuyacin hali alhalin kasan a cikin halin jinya take." Miƙewa yayi har wani jiri na dibarshi. "Kuyi haƙuri bazan sake wannan zancan ba in sha ALLAH wannan shine jarabawata son Sabuwa shine ƙaddarata." Fita yayi a gidan yana haɗa hanya. Sai da akayi magriba ya shiga majalisarsu daidai ana cin abinci. Lokali ya zara ya dinfa cunkusa abincin bama tare da yasan me yake yi ba. "Maza wai lafiya ko kuwa Sumy ce ta zaburar dakai ne haka? Hmmm kasan Allah da ace nasan haka matan yaren ibra suke da irin wannan masifar babu abinda zaisa in taimaki yarinyarnan Allah nake faɗa maka. Yarinya tabi duk ta fitini kowa ni kaina bata ƙyale ni ba kai Adeiza masifa ce" Murmushi Babangida yayi kawai tare da girgiza kanshi. Amman ya kasa cewa uffan, yayi hankali bazai taɓa sake fitar da maganar iyalinshi ba. Lokalin ya ajjiye ya zuba zoɓo ya sha ya idasa cika cikinshi. Kafin ya miƙe. "Kunga bari in samu in rarrafa anayin isha ina da ɗalibai yau sai mun haɗu gobe." A hanya ya tsaya ya siya kayan tea leda biyu ɗaya nasu ɗaya nasu Mardiyya. A gurguje ya shiga gidan ya ajjiye mashin ɗinshi da ledojin biredin ya fice. Ƴar Shuwa:. Babangida yana fita ta ɗaga waya ta kira Mama a waya. "Mama a saka mun idanu akan Babangida ya tawo dashi da tsinannun yarannan zai kawo su wajen Sabuwa. Naga kanshi yana rawa kamar so yake ya dawo da'ita ma fa. Dan cemun yayi har maganar ta faɗa ma." Mama daga cikin wayar tace. "Ah haba dai wane mutum ai wallahi bai isa ya mayar da Sabuwa ba ta fita kenan. Yaran basa nan da kaina zan saka miki idanu akan komai." Da wannan sukai sallama Ƴar Shuwa ta datse wayarta tayi jigum akan kujera tana ta aikin tunani. Ai kuwa sai can Mama ta yo mata filashin da sauri ta kira. Mama ta labarta mata ai Babangida ya haura layin harma ya kori Sabuwa gida daya taddata tana taɗi. "Da gaske in muka yi sake kina ji kina gani Sabuwa zata dawo gidanki. Abunyi shine gobe ki ƙoƙarta kizo nan gida sai mu je wajen wani boka zai faɗa mana duk abunda ake ciki. In muka ji nasan matakin da zamu ɗauka akai. Ga Adama ma gobe za'a ɗaura aurenta ai na faɗa miki ko?" Tsaki Ƴar Shuwa tayi tace. "Shikenan goben zanyi ƙoƙari inzo muje Allah yasa ya barni kinsan shi da shegen kafiya. Bari in je cefane Mama sai mun yi waya" Wayar ta datse ta wancakalar a kan kujera. Ta jima tana aikin tubkar mugunta a zuchiyarta sai da ƙyar ta samu ta miƙe ta sake gyara ɗakinta, ta sake zanin gado ta wanke banɗakinta tas. Kana ta rufe ɗakinta suka tafi cefane ita da maƙociyarta Jamila ƙawarta. Suna tafe suna tattauna matsaloli sabida itama Maman Abdul ɗin saura sati biyu mijinta ya ƙaro aure. Duk ta ƙarar da rabin kayan ɗakinta bokaye nata faman cin kuɗinta suna ta mata ƙaryar auren bazai yiwu ba tana zaune zaice ya fasa amman har saura sati biyu bata ji yace uffan ba. Sai shirye shiryen biki da yake ta ƙarfi. Yau danginshi ma suka kawo mata akwatin dannar kirji. Daga haka tayi saranda. Har suka je suka yi cefanen hira ɗaya ce suke yi har suka shigo cikin gidan. Matan gidan ko wacce tana kitchen anata girki, wasu kuma sunata shirye_shiryen ɗaurawa. Ramatu tana ƙofar ɗakinta anata mata lalle ja. Sumy kuma tana ɗaki ta ƙure waƙar yarensu tana ta bi. Ita bata fitowa cikin matan gidan zaman hira sam. Asalima bata kallon kowa kota fito abinda ke gabanta take yi. Hatta su Ƴar Shuwa basa gabanta asalima kallon raini da gazawa ta ko wanne ɓangare take yi musu. Jiki a mace zuchiya cunkushe da tunanuka Ƴar Shuwa ta dinga aiyukanta. Ta sha wuyar dakan saƙwararnan sosai da sosai. Saida ta gama ta aika yara suka karɓo mata kular Ramatu da Sumy. Ramatu dai ta bayar da tata kular. Amman Sumy sai cewa tayi da ƴan aiken ace ta ƙoshi. Saida Yar Shuwa ta gama komanta ta sha wankan yamma ta nufi ɗakin Sumy domin da sanar mata dalilin da yasa bata karɓan abinci duk ranar girkinta. Dake yau zuchiyar tata a kusa take. Ai kuwa tana shiga kitchen ɗin Sumy ta sameta a tsaye tana kaɗa ƙwai ga taliyar Ƴan yara a kula taji kifi da kayan lambu. "Wajenki nazo malama" A rainace Sumy ta juyo tace. "Ay to shiga gani nan" Hararar juna suka yi Ƴar Shuwa ta ja ƙaramin tsaki ta shiga. Tana shiga taga atampopi da shaddaji sunfi kala talatin a ƙasan kafet gasu sababbi dal dal kuma bana akwatunanta bane dan fes ta haddace kayan akwatunanta tsab. Zama tayi taci gaba da ƙare ma falon kallo komai yana zaune a muhallinshi. Cikin yauƙi irinna matan da suka jima a bariki bariki ta sansu suka santa. "Gani Allah ya sa lafiya. Kuma Allah yasa inji alkhairi" "Kusan ba lafiyar bace ta kawo ni ba gaskiya. Na zone cikin lumana in tambayeki dalilin da yasa duk ranar girkina bakya cin abincina sai dai kiyi naki kici ke da agolan ɗan da kika tawo mana dashi. Naga in Ramatu ce take girki ai kina ci. Shin abincin nawa ne babu daɗi, ko kuma tsabtatace baki yadda da'ita ba da bakya cin nawa abincin yau dai inaso in sani. Dan kwanaki nayi ma Jannaty magana yace in bar zancan." "Au ashe ma yace ki bar zancan shine baki ji maganarshi ba kenan? To ni dai bani da lokacin amsa wannan tambayoyin wanda ya zaunar dani in yana da abun faɗa shi zaice. Kinga anata kiran sallah kinsan mu akan lokacinta muke yi. Ku dama Shuwa Sallah bata damesu ba" Tana faɗin haka ta shige ƙofar da zata sadata da ciki ta bar Ƴar Shuwa bakinta a hangame. Ƙwafa tayi ta taso ta koma ɗakinta tana jiran Babangida ya dawo ayi wacce za'ayi. Tana sallar magriba ya shigo ya ajjiye mata ledar biredin karyawa ya fice tasan kuma sai goman dare zai shigo. Tana zaune har ya dawo yaran duk sunyi bacci. Waje ya samu ya zauna da sauri ta tarbeshi harda murmushin dole. Duk da kishinshi ne fal zuchiyarta Allah ya gani tana mutuwar son Babangida gashi ta ɗauki kishin Duniya ta ɗaura akan Babangida. "Wanka zaka soma yi ko abincin zan kawo maka"? Ɗan gajeren tsaki yayi yace. "Wankan dai. Abincin ki saka a firji da safe zanci a ƙoshe nake tam" Kanta basai ya ɗaure ba. To ranar data fita a girki ma baici abincinta na safe ba, baici na dare ba. Gashi yauma yanaso yace mata bazaici ba. Ita kanta Ramatu da take karɓan abincin sau da dama tana ganinta zata kira almajirai ta basu, duk da dai tana ci ba kamar Sumy da bata ci ba. A sanyaye taje ta haɗa mishi ruwan wankan. Yana wankan ita kuma ta saka abinci a firji ta sake ɗaɗɗakan tsumi banda wandda ta dinga ɗirka da yamma har danshi take yi dab magriba. Kayan baccinta ta saka mai ɗaukar hankali kayan da in dai ta saka ranar kam ba'a cewa komai ne. Amman yau kam ko kallo bata ishi wanda akai dominshi ba. Asalima zazzaɓi taji a jiknshi kau dole ta ɓallo fanado ta bashi ya watsa ya bi da ruwa. Haka ya kusan kwana, ko ace ya kwana akan sallaya ko da yayi sallar ya gaji a wajen yayi bacci. Duk rashin bacci ishasshen dake idanunshi kiran sallar farko ya miƙe ya shiga banɗaki ya goge bakinshi ya ɗauro walwala da zai fita ya tashi Ƴar Shuwa ya fice. Saida yabi ɗakuna biyun ya tashesu. Har zai fice a ɗakin Sumy yana jaye da hannun Amir tace dashi. "Ji mana wallahi ka takama matarka wannan yar Shuwa ɗin kunne na fita buɗewar idanu da zallan iskanci ai kai ka sani. Wallahi Allah ka ja mata kunne kada in kamata in zauneta." Kai ya girgiza yace. "Ke kenan faɗa bakya ko gajiya Sumy bakya ko jin kunyata da nauyina ji yadda kike ɗaga mun murya a gaban yaro" "Wa wai namijin duniya shi zanji kunya? Ka yaudari kanka kasan babu wata kunyarka da zanji. Yadda baka ragamun ba, yanzu babu ragama ɗin da zanyi ina dalili ma to" Tana faɗin haka ta shigewarta ciki. Shi kuma ya ja hannun Ameer zuwa ɓarayin su Mardiyya. Su Aminu ya kira suka tafi masallaci. Basu suka shigo ba saida rana ta fito sukai nafila kana suka shigo. Ɗakin su Mardiyyan ya sake komawa ya saki Ameer ya tafi wajen uwarshi. Shayi da biredi da ƙwai Mardiyya ta ajjiye ma Babansu a gabanshi. Murmushi yayi daya tuno irin tsugunan sak da Sabuwa take yi in zata bashi abinci irinshi sak Mardiyyan tayi. "Allah yayi muku albarka. Yau babu islamiyya anyi hutu ko?" "E Baba amman muna so zamu je gidan Anty Alawiyya yau suna" Sai da ya cinye biredin bakinshi yace. "Af ashe yau suna kinga na mance shaf. To shikenan ai sai ku shirya kuje. Iyayen naku ma dukka zasu je." Malama ce tayo carab tace. "Baba Adda ita take koyama su Aɗɗa'u karatu. Ko Aɗɗa'u?" Ta ƙarashe zancan tana kallon Aɗɗa'u. Mardiyya ta harareta dan bata so ta faɗa mishi ba" "Mardiyya da gaske ne ke kike shiga ajinsu Aɗɗa'u. Riƙon ƙwarya aka baki ko ajin Baba Malam ya baki ne? Kai amman nayi farin ciki gayaa" "A_a ba riƙon ƙwarya bane yace in dinga koyarwa a islamiyya ne kafin a dawo hutu sai in shiga sahun koyar da matan Aure tunda dai na kammala karatuna, kuma yace zai dinga biyana albashi duk wata. Amman Baba inason zuwa jami'ar in yi digiri a fannin Islamic sitadis." Murmushi farin ciki yayi lokaci guda kuma ya gintse ranshi jin ta ambaci jami'a" "Kima cire batun jami'a Mardiyya. Duk ilimin addinin da kike buƙata Mardiyya ba sai kin shiga jami'a ba zaki iya. Yanzu littattafai nawa kika haddace, hadisai ɗari nawa ne a kanki? Iyakar wannan ma Mardiyya ai sai dai ki gode ma Allah. A mata_ mata jikokin Baba Malam babu wacce ta taɓa jan ragamar karɓan aji an dai samu a mazan. Amman kinga ke cancanta tasa Baba Malam ya ɗaukeki kin zama Malama. Ni dai nasihata daku a kullum shine ku riƙe kanku ku shafe duk abinda ya faru a baya. Nayi muku alƙawarin dawo muku da mahaifiyarku muzo mu rayu har ƙarshen rayuwarmu cikin aminci" In yana hira dasu wallahi ji yake yi kamar kada ya motsa ko nan da can. Wato yaran har mamakin nutsuwarsu da biyayyarsu yake yi. Allah al hakim kenan baƙar tukunya mai fidda farin tuwo. Bayan ya gama karyawa ya basu kuɗin mota kana ya fita. A zaune a gaban kulolin abinci yaje ya samu Ƴar Shuwa taci kwalliya sai baza ƙamshi take yi da ita da ɗakin dukka. Yara kuma suna cin abinci. Zama yayi yana ɗan zolayarta kaɗan dan ya sata farin ciki. Ai kuwa duk turɓunewar da tayi sai da ta saki ranta. "To ayagi zuba mun abincin ko?" Kular ta buɗe ta zuba mishi sakwarar ta tura mishi gabanshi tana haɗa shayi tace. "Amman yanzu ka sake ninka lokacin da kake zama a masallacine? Naga daɗewar tana yawa" Ta sani sarai wajensu Mardiyya yake zuwa ya shantake. Itama ta ganshi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. "A_a kinsan dake bani da lokacin da nake ganawa da su Mardiyya shine na zaɓi bayan sallar asuba a matsayin lokacin da zanje in gansu inci abincinsu suji daɗi kamar yadda ko wacce cikinku nake cin abincinta tare da yaranta." Wani kishine ya turniƙeta har tana ƙwarewa so take tabi duk hanyar data dace dan ganin ta takura yaran so take ya rarraba ma matanshi su ta yadda ba zasu samu lokacin kansu ba sai dai a makaranta. Amman ta rasa yadda zata kawo lamarin gabanshi ne. Yau dai tana fatan zata faɗa ma boka sai ya bata sa'a akan hakan. Dalilin ta kenan da yasa bata yi wata banzar magana ba. Yana cin abincin yake tambayata abinda ya haɗata da Sumy. Nan ta kwashe labarin komai ta faɗa mishi. "Hmm zan yima tubkar hanci. Zan taraku inji ta bakin kowa yau inna dawo in sha ALLAH. " Ajjiye mata kuɗin cefane yayi da kuɗin motar zuwa suna, harda kuɗin barka ya bata. Ya shirya tsab abunshi Haka suma ragowar matan ya bibbisu da kuɗin mota kana ya saka kai ya tafi nema. Ƴar Shuwa na kammala abinda take yi ta shirya ta saka doguwar rigar lace mai ɗan karen tsada ga takalmi ga jaka masu tsada. Yaranta ma kayansu masu tsada. A gurguje tayi ma kowa sallama ta nufi gida. Ko data shiga yaran kawai ta ajjiye suka tafi ita da mama sune har Ringim garin su Babangida. Sunje sun samu wajen mai maganin cike dam da dandazon mata zasu yi ashirun. A zuwansu har mutum biyar ne a bayansu suma. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI TAKU CE [8/25, 8:18 AM] BADA'AT IBRAHIM: Na dade ina fama da bushewar ,kaikai da warin gaba , Na gwada magungunan asibiti da na gargajiya amma babu wani sauki. Sai wata kawata ta gabatar min da Oriflame Feminelle Wash mai dauke da lactic acid, prebiotics, hyaluronic acid, da peach extract… rayuwata ta canza. Yanzu Alhamdullillah no more itching ,odour and dryness Dm to get yours 💖 Yana da laushi a fata, pH-balanced, kuma cike da sinadarai masu kare ki. Ki huta daga wahala, ki rungumi kwarin gwiwa. Contact me Tru:08022059556 IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI Sabuwa:. Sai gamu a zawaciki gida dubu. A cikin jerin gwanon kyawawan gidajen gidan Abokin Uzairu zuchiyata suke. Maigadine ya buɗe mana get muka shiga. Masha Allah tsarin gidan yayi yau ga fulawowi tako ta ina. "Maza Allah yayi yau mun haɗu ido da ido. Gaskiya ashe kafi kyau a fili. Am wannan ba wannan sister ɗinka bace da kake yawan saka hotonta ba?" Abokin Uzairu zuchiyata ke magana da baturiyar hausa ina nufin Hausar ƴar zamani anayi ana lankwasawa gayu a dole. Ai nan shima naji Uzairu zuchiyata ashe shima ya iya. Ni dai ina biye dasu da ƴar ƙaramar jakar kayanmu har zuwa babban falon gidan. Wata dattijuwa muka tarar a falon tana zaune tana cin abincin safe dankali da ƙwai. "Sagagi baƙon naka ne ya iso kamar a Kano ya kwana?" Sasagi yayi dariya. "Wallahi Mum nima shi ya tasheni a bacci da asuba suka tawo. Ƙarasawa nayi muka gaisa da Dattijuwar. Cikin fara'a ta tarbemu tana tambayar ya iyayenmu. "Ah suna lafiya sunce ma a gaisheki Hajiya" Cewar Uzairu zuchiyata daya koma kamar bashi ba musamman in naji yana magana hausa_ hausa turanci_turanci. Miƙewa tayi tace. "Ku hau teburi kuci abinci. Ni kam zan fita ne ma. In kin gama Sasagi zai kai ki ɗakin ƙannenshi mata ki zauna tare dasu." Toh Hajiya mungode sosai." Bayan mun gama karyawa Sagagi ya shiga dani ɗakin ƴan matan gidan su kuma suka shiga gari sai wajajen azahar Sasagi ya shigo kirana zamu je yin paspo. A lokacin muna hira da Sakina ƙanwarshi. Macece mai fara'a da son hira. Tare muka je da Sakina aka yi mana paspo suka ce gobe mu dawo a bamu kayanmu. Muna komawa gidansu Sakina aka tarbemu da abincin rana shinkafa da miya da salak inji kanawa. Ina banɗaki ina alwala wayata ta shiga ruri. Har na fito wayar sai kira akeyi. Nasan dai bazai wuce ƴan biki ba. Ilai kuwa su ɗinne Amarya da kanta ke kirana Ina dariya na ɗauki wayar tare da zama a bakin gado" "Lolo ku dai taya ni murna gamu a Malam madori Allah ya ƙaddara nima na shigo babban family. Gamu dukka amman babu ke babu su mardiyya sai banji daɗi ba" Nima ina jiyo hayaniyar ƴan biki duk sai hankalina ya koma can wallahi. Sukaita karɓan wayar suna sake rikitani. Kashe wayata nayi na miƙe da hijabin Sakina a hannuna zanyi sallah. "Sai kinyi sallah zamu ci abincin wai nifa ke nake ta jira kuma wallahi yinwa nake ji sosai" Dariya nayi mata. Na lura Sakina wayaiyace sosai gata da mugun saurin sabo. Zama nayi na saka lokaci muka soma cin abincin. "Amman bazawarace ke kamar ni ko? Dan naga ba yarinya bace da ganinki" Kallonta nayi saida na cinye abincin bakina tukunna nace. Bazawarace mai yara huɗu harda ƴar budurwa" idanu ta zare tace. "Yanzu a hakan da wannan jikin naki me kyau har budurwa gareki? Masha Allah gaskiya kin more jiki. Nima bazawarace mai yara uku amman ƙananune. Butulci da tozarcin ɗa namiji ne ya fito dani daga gidan aurena na tsallake na bar yarana. Duk da iyayena sun tsaya mun amman al'ummar gari ban tsira daga maganganunsu ba. Cewa suke yi wai aikina na zaɓa akan auren kuma wallahi ba haka bane Sabuwa. Toh duk da dai hakan gashi wani dai auren dole zan sake yi. Inata adda'ar Allah yasa a karo na biyu a dace." Hmm to ameen Sakina ai mu dai mata muna ganin rayuwa. Ni kin ganni sai jibi zan gama iddar ma. Saina nutsu kafin na soma tunanin wani auren duk da ni mazan duk sun fice mun a kaina. Kuma sai in dinga ganinsu a cikin riga iri ɗaya" Dariya tayi tace. "Wallahi nima hakan nake gani. Amman fa hakan na da nasaba ne da wahalar da muka sha. Ni dai nayi istikara zuchiyata kuma ta samu nutsuwa wallahi Sabuwa ko bacci bana yi sosai ina kai kukana wajen Allah akan wannan auren da zanyi na biyu in babu alkhairi duk yadda nakai da son inyi Allah kar ya bani damar yi" Mun jima muna ta surutu kafin dai na gabatar da Sallah itama tayi tata sallar. Da yamma list Uzairu zuchiyata da Sagagi suka ɗaukemu suka zagaya garin Kano damu sosai gaskiya kano tana da kyau sosai gasu da wuraren buɗe idanu da shaƙatawa sosai har siyayya muka yi naga Uzairu zuchiyata sai facaka da kuɗi yake yi. Har kantin ƴan gayun maza muka rakashi ya sassai suturu masu kyau da tsada sosai abun yaita bani mamaki dai. Nima ya sai mun dogayen riguna biyu masu kyau da takalmi. Washegari bayan mun karɓi paspo ɗinmu Sasagi da Sakina suka kaimu tasha har saida motarmu ta cika kafin suka tafi. Mun tsayar da alƙawarin in sha ALLAH zan zo bikin Sakina dani za'ayi komai daya dace munyi musayar lamba ma. Hajiyarsu ta bayar da danƙareriyar atampa tace a kaima Rakiya turare kuma a bawa Maigogul. Wai ni Uzairu zuchiyata a ina kasan su Sasagi haka ni naga ba zuwa Kano kake yi ba?" Hararata yayi yace. "Kaji mun yarinya fa. Au in zan zo Kano. Zaunar dake zanyi in baki labari kenan. Tunda ni gantalinku in zaku je kuna bani labarine. Ina da abokai a kab garuwan arewa a kudu ne kawai bani da aboki. Adam a zango ma abokinane" Dariya kawai nayi mishi. Wai Uzairu zuchiyata kaima kirista kenan zaka aura kamar yadda Sama ya auri matarshi? Kuma da gaske ita wannan Felisha ɗin take sonka bata da wata manufa a kanka?" "Wallahi bata da wata manufa yo Lolo inma tana da wata manufar zadai muyi aure. Ta riƙe manufarta nima in riƙe nawa. Da kike ganina ni kaina ina da manufar auren nata. In kin lura ai ba budurwa bace ta taɓa yin aure a baya suka rabu da mijin a shekaru zata yi Rahama kinga kuwa ai ba sa'ar aurena bace. Wallahi lolo rayuwar cikin gidanmu abun dubawace shin mu haka zamu ƙare ne? Kinsan Allah shi yasa kawai nayi amfani da damata kawai. Kuma Felisha tace zata mayar dani makaranta ko da iya karatun na tsira ai na gode. Balle inna tafi na tafi kenan" Haka dai mukaita tattaunawa har muka iso Dutse. A bakin tasha ina tsaye zan sai lemo da Ayaba sai muka ga Sama yana tuƙa wulbaro. Uzairu zuchiyata kaga can Sama" Ai kafinma in rufe baki Uzairu zuchiyata ya shiga kiran sunanshi. Ƙarasowa yayi. "Ku kuma me

Chapter 16 of 19