tsara rayuwar gidan aurenta a haka ba"
SABUWA:.
Washegari
Sassafe Mardiyya tayi kiran wayar Adama take sanar mana Malama a asibiti ta kwana ba lafiya. Abunka da sha'anin ƴa da uwa sai hankalina ya tashi ba shiri su Labbai suka soma girkin asibiti. Taliya da kifin gongoni suka dafa sai shayi mai kayan ƙamshi ko basket bamu dashi a leda muka zuba komai.
Jikina babu ƙarfi nayo wanka tas na zura doguwar rigar kanti daga cikin rigunan da Dr Kamilu ya sai munne. Labbai sai ta saka ɗaya doguwar rigar tawa, Adama kuma ta saka lace muka fito sai ga motar Dr Kamilu a ƙofar gidan isowarshi kenan.
Gilashin motar ya zuge yana mun murmushi nima murmushin nayi mishi. Ya ƙurama Adama idanu yana ɗan murmushi.
Yaya kaine sassafe haka?'
Na tambayeshi"
"Kin ganni dai dake na kwana cikin raina. Yaya Adama ina kwananku yaya Lolo da jiki?"
Nan dai suka gaggaisa.
"Dama nazo in duba jikin nata ne sannan in gaishe da su Mama'"
Gabana ya yanke ya faɗi Adama tace.
"To sakko mu ƙarasa gidan. Dama asibiti zamu je dubiyar ƴar gidan Lolo karamar jiya a asibiti ta kwana.
Ai kuwa ya ajjiye motarshi muka ɗunguma zuwa cikin gidanmu
Shigarmu da sallama wallahi sai ji mukai an jefo bokitin roba tabb ya sauka aƙirjin Dr Kamilu.
Gaza ne suke damben Allah tsine a tsakar gida shi da madamcy. Ga su Rakiya a tsakar gidan kowanne harkan gabanshi yake yi. Babu wanda ya damu da abinda su Gaza suke yi.
Hauwa na gaban murhu tana dumame, gasu Qamriyya a tsakar gidan duka. Rakiya kuma wasu jemammun kayan gado aka kawo mata tana siye. Ga Maigogul a kan turmi yana brosh. Uzairu zuchiyata yana zaune akan kujerar tsugunno yana ta aikin goge ƙafarshi. Su Sadiya kowa na zazzaune babu wanda ya shiga faɗan su Gaza.
Illahirin kunya ta kamani da mugun gudu Gaza ya biyo madamsy ita kuma ta nufo kanmu ai kuwa ta bangajeni sai gani a ƙasa jiki dama duk ciwo ya cinyeshi. Gaza sai ɗuma zagi yake tayi.
"Ke Rakiya ga baƙo munyi fa"
Cewar Maigogul daya nufo mu da sauri. Ni kuma a sanyaye Sadiya ta ɗaga ni na miƙe ina kaɗe jikina.
"Bawan Allah kayi haƙuri ka shigo gidan ka tarar anata hatsaniya. Shaye shaye kasan babu abinda baya sawa shi yasa. Wannan rikicin tun dare ake yi da sassafe suka ci gaba da faɗansu duk kamar a bige suke sun ci kai shi yasa. Yanzu da zaka goyi bayan ɗaya sai cibi ya zama ƙari, ƙari ya zama ƙababa shi yasa kaji munyi kurum. Labbai surikinne aka kawo shi Allah yayi kenan?
To madallah"
Da sauri ya koma da kanshi ya ɗauko tabarma ya shinfiɗa ya riƙo hannun Dr Kamilu suka zauna. Gaza kuwa ya kama madamcy sai dukanta yake yi sai da ya daketa son ranshi kana ya rabu da'ita yayi ficewarshi ma a gidan.
A sanyaye Dr Kamilu ya gaishe da su Rakiya da Maigogul kafin Adama ta gabatar musu dashi.
Baki Maigogul ya washe.
"Allah sarki munfa gode da ɗawainiya wallahi Allah ya saka maka. Itama muna ta lallaɓata ta daure ta koma ɗakinta wallahi kaga taƙi shi wannan mahaukacin wan nasu daya fita ya ɗaure mata baya akan ba zata koma ba. Ƴan uwanta mata duk sun goyi da bayanta.
Kafa gansu cike da gidan duk zawarawane zaman auren ya gagaresu dama itace ta samu...
Carab Adama tace.
"Sauri muke yi Maigogul ƴar wajen Lolo ce babu lafiya zamu je asibiti mu dubota dama gaisheku yazo yayi.
"Assha to ai sai mu tafi tare. Kai Uzairu zuchiyata maza sako kaya muje asibiti. Malam Kamilu da mota kake ne?"
"E Baba da mota ai sai in sauke ku"
"To to shikenan Allahu Akbar bari in shirya ai sai mu tafi baki ɗaya."
Ya ƙarashe yana wannan dariyar da in yayi sai inji kamar in haɗiyi zuchiya in mutu.
Da sauri ya shiga ɗaki ya bugo kwalliya ya fito yana ta baza ƙamshi yayi kyau tabbas tamkar wani minista ko ɗan majalisar jaha fa haka yake ado komai nashi mai daraja ga kyau Allah ya huwace mishi idanunshi farare tar_tar gashi da suma mai laushi da furfura jefi_jefi.
Uzairu zuchiyata shima ya bugo nashi wankan dama dai jirgi ɗaya ne ya kwaso su yasa wani ƙaton takalmi sai sheƙi yake yi hmmm.
"Dama nace akwai kayan abinci Yaya Adama a mota ko yara zasu shigo dashi?"
Dr Kamilu ya yi maganar yana kallon Adama.
Maigogul yayi carab yace.
"Muje kaji in kwaso in dire musu sai mu tafi"
"A_a Maigogul su Sadiya kuzo muje ku shigo da kayan. Anfa gode sosai"
Nan su Rakiya da Hauwa suka shiga godiya. Dubu goma_ goma yaba Rakiya da Hauwa. Ga ƙaton buhun shinkafa da katan na taliya da mangyaɗa an dire a kofar Rakiya. Mu kuma muka shige mota Maigogul yana gaba sai labarai yake ba Dr Kamilu marasa ma'ana, daga yace ƙawarshi ta gari kaza, sai labarin sunje bikin Ƴar gwamnan gari kaza haka dai dama salon hirarshi suke. idanuna na lumshe wasu siraran hawaye suka gangaro mun. Gashi Maigogul sai ƙoƙarin saka su Labbai a hirar tasu yake yi. Suma suka biye mishi sukaita hira har muka karasa asibiti.
Muna sakkowa a motar muka haɗa idanu da Babangida. Dr Kamilu kuwa dama bai fito ba yace bazai shiga ba dan gudun fitinar Babangida.
Gaba muka yi ni kunya tasa na kasa tsaiwa muyi sallama ma. A guje Maigogul ya biyo bayanmu yana cusa kuɗi a ajjihu bakinshi kuwa har kunne.
A cikin ɗakin da Malama take muka tadda Babangida fuskarshi a mugun murtuke gashi ya shigo ya tadda Malama sai kuka take tana kiran umminta. Muna shigowa nayi saurin isa bakin gadon na zauna na rungumi diyata ina shafa bayanta. Sai tayi tsit tana ta sauke ajjiyar zuchiya ta ƙanƙameni sosai yarinyar tamkar tana tsoron kada in gudu.
Ana kan gaggaisawa muka jiyo sallamar Baba Malam da Malama Ƙarama da Wawo sun shigo suma da abincinsu niƙi _niƙi.
Har ga Allah banso muka haɗu da Dattijon ba domin bana so ya bani wani umarni in saɓa mishi.
Yako nuna farin cikinshi da ganina duk da yayi mun faɗa sosai akan kada in kuma tafiya ko'ina duk abinda ya dameni in garzayo in faɗa mishi.
"Babangida kaida waccan ku fice ku bamu waje"
Babangida dama a takure yake da sauri ya fice. Ramatu tabi bayanshi sum_ sum_ sum.
"Maigogul gaka ga Sabuwa dama nayi niyyar zuwa gidan daga asibitinnan sai gashi mun haɗu. A gaskiya roƙo dama zanyi Sabuwa ta dawo ɗakinta tunda labarin ƙarar data kuma shigarwa ya iso mun. Tayi haƙuri in Allah ya cika mata burinta sai ta tafi gabaki ɗaya. Amman yanzu ai ba daidai bane ace tana zaune a gida ba ko ba gaskiya ba?"
Maigogul yace.
"Wannan gaskiya ne ni da Rakiya munyi munyi da'ita amman taƙi komawa. Kuma tun ranar data bar gidan nata tana asibiti babu Lafiya"
Nan ya kwashe labari ya ba Malam Baba harda ɗorawa da cewa.
"Yaronne ma ya kawo mu asibiti yanzu yaje gida dan mu gaisa sai dai fa Babangida yazo har ƙofar gidan anyi ɗauki babu daɗi daga zuwa ya runtuma a wuyan wannan bawan Allah ya kamashi da kokawa akaita turzawa. Yaita rantsuwar dai bazai yadda ya saketa ba. In sha ALLAH daga nan in aka sallami yarinyar zata koma gidanta kai tsaye in yaso sai a tafi da Adama da ita Labbai ɗin zuwa yadda shari'ar ta kaya. Har cikin raina bana goyon bayan mutuwar auren Lolo wallahi "
Ni dai bance komai ba kuma bana jin a wannan karon zanyi ma Malam Baba biyayya nifa na baro gidan kenan.
Kuɗi ya ɗakko masu yawa yace in riƙe a hannuna ya ba Maigogul ma harda su Adama.
A taƙaice dai kwanan malama biyar a asibiti muna jinya. Kullum Babangida yana zuwa amman ko ga miciji bama yi ma juna yayi yinƙurin samun damar magana dani nice ban bashi damar ba nace mu haɗu a kotu kawai. Tunda matarshi ta fice a asibitin ranar da muka je babu wacce ta sake tako ƙafarta. Daga dangin Babangida matan babu wanda yazo mazan dai sun zo Sauban ma yanata hidimar kawo abinci dasu lemo da ayaba. Dr Kamilu kuma kullum sai munyi waya ya tambayi jikina.
Rana na shida aka sallamemu kuma a ranar ne zamu yi zaman kotu na farko.
Ni dai kai tsaye gida muka wuto da Malama dasu Adama duka. Sunyi juyin duniya akan in koma ɗakina naƙi fur. Su Sadiya ma nasa suka je suka tattaromun suturuna da duk wani abu muhimmi suka kawo mun ai kuwa ɗakin dama ba girma ba duk saiya cike.
Sha ɗayan rana a kotu tayi mana ni da su Adama da Rakiya Maigogul yace ba zashi wani kotu ba.
Sai gani gasu Malama Babba da Sa'a a harabar kotu sun zo suma.
Kafin mu shiga cikin kotun Dr Kamilu shi da lauyana suka ƙaraso. Sha ɗaya dot muka shiga ɗakin shari'a.
Nan aka gabatar da dalilin ƙarana lauyana ya zayyano hujjojinmu,
Alƙali ya buƙaci shaiduna uku.
Baba Malam yayi mun shaida, Adama ma haka, sai Ramadan da ake yawan aikowa. Aƙali yayi musu tambayoyi dangane da abbuwan da suka sani, suka amsa gwargwadon saninsu. Akaita turzawa. Lauyan Babangida ya kakkkareshi da hujjojinsu na ƙarya. Alƙalinnan yayi shiru bayan ya gama sauraren dukkan bayani daga ɓangare biyun. Sai ya buƙaci in fito cikin ɗan akwaku. Na fito na tsaya zuchiyata a bushe.
Tambayoyi ya dinga jero mun ina amsawa cikin rashin tsoro ko na misƙala zarratin. Alƙali sai rubutu kawai yake yi.
Lauyan Babangida ya tashi a zabure ya dinga mun sharri irin wanda sukaita mun a kotun baya dai.
Haka aka ɗage sauraren ƙara akan nan da wata ɗaya mu dawo domin yanke hukunci zuwa lokacin an gama bincike domin tabbatar da adalci. Alƙali ya nemi Babangida ya sake ni ya nuna shi a sake bashi dama. Ni kuma na nuna wallahi bazan sake zaman aure dashi ba abadan.
Da haka zaman kotun ya ƙare muka fito zuchiyata fes har wani murmushi nake yi dan daɗi.
Babangida da su Malama Babba kuwa hankalinsu a matuƙar tashe yake.
Baba malam ne ya tare mu.
"Sabuwa kizo gobe ki same ni a gida da safe zamu yi Magana dake."
A kunyace na amsa mishi
Washegari sassafe kuwa na isa. Kuɗi dubu ɗari shida ya ƙirgo a baƙar leda ya damƙa mini.
"Ga kuɗi ko alƙali zai ce ki fanshi kanki da kuɗi, duk da shima da kanshi yana da damar da zai iya sakin ki kuma kin saku bisa ga dalilai masu yawa da kika gabatar. Na fahimci shi wannan alƙalin yana alƙalanci da gaskiya da amana zai raba auren naku ne kuma alƙali yana da damar da zai saki mace na sanshi tare muka yi karatu dashi.
Amman dai Sabuwa kin yadda har cikin zuchiyarki zaki rabu da Babangida dai ko?"
Cikin ƙarfin guiwa na amsa mishi ba wasa yaita mun nasiha akan kada in sake in koma kan rayuwata ta baya yaita mun nasihu har saida naji haka kurum tsohon ya bani tausayi.
Haka kwanaki sukaita shuɗewa a kwana a tashi har lokacin shiga kotu ya zagayo.
Muka je amman Babangida da lauyanshi basu zo ba.
Aka sake saka lokacin sati guda. Muka sake zuwa amman Babangida bai zo ba, kuma anata aika mishi ɗan aike daga kotu. Sai a zama na uku da aka aika mishi da takaddar gargaɗin ƙarshe dan kotu ba sa'arshi bace shine suka tawo dashi da lauyan nashi.
Babangida yaƙi amincewa ya sake ni aka kaɗa aka raya.
Ni dai duk zaman da akayi ina kan bakata.
Har sai da akayi zaman kotu na ƙarshe.
Bayan alƙali ya gama tattare bayanai ya jima yana nazarin can sai yace.
( الطَّلَاقُ مَرَّتَانِ ۖ فَإِمْسَاكٌ بِمَعْرُوفٍ أَوْ تَسْرِيحٌ بِإِحْسَانٍ ۗ وَلَا يَحِلُّ لَكُمْ أَن تَأْخُذُوا مِمَّا آتَيْتُمُوهُنَّ شَيْئًا إِلَّا أَن يَخَافَا أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ اللَّهِ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ اللَّهِ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا فِيمَا افْتَدَتْ بِهِ ۗ تِلْكَ حُدُودُ اللَّهِ فَلَا تَعْتَدُوهَا ۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ اللَّهِ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ )
البقرة (229) Al-Baqara
Saki sau biyu yake, sai a riƙa da alheri, ko kuwa a sallama bisa kyautatawa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da kuka ba su, face fa idan su (ma'auran) na tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba, Idan kun(danginsu) ji tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba, to, babu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyakokin Allah ne saboda haka kada ku ketare su. Kuma wanda ya ƙetare iyakokin Allah, to waɗannan su ne azzalumai.
Fasali ya ja kafin ya ɗaura da cewa
" A bisa hujjoji kamar haka
*Imam al-Dasuqi ya rubuta cewa:*
للزوجة التطليق على الزوج بالضرر وهو ما لا يجوز شرعا كهجرها بلا موجب شرعي وضربها كذلك وسبها وسب أبيها
*Matar tana da damar samun saki daga mijinta saboda cutarwa (wadda ba ta halatta ba a shari'a), kamar barin ta ba tare da hujja ta shari'a ba, ko duka ta haka, ko yi mata zagi, ko zagin mahaifinta.*
*Asali:* al-Sharḥ al-Kabīr wa Ḥāshiyat al-Dasūqal-Dasūq
Saboda haka, mace Musulma na da cikakken iko ta nemi saki daga alƙali idan mijinta yana cutar da ita (*at-tatliq bil-darar*) – ko cutarwar tana da nasaba da duka ne, maganganu, ko ciwon zuciya (emotional abuse) – ba tare da wajabcin ta mayar masa da sadakinta ba ko wani diyya.
Ko da ba a samu shaidu ko hujjar gani ba, *shekarar da mace ta bayar cewa tana cikin cutuwa* na iya wadatarwa ga alƙali ya yi la’akari da sakin — musamman idan akwai wasu alamu ko yanayi da ke goyon bayan hakan.
*Imam Khalil ya rubuta cewa:*
*ولَهَا التَّطْلِيقُ بِالضَّرَرِ ولَوْ لَمْ تَشْهَدِ الْبَيِّنَةُ بِتَكَرُّرِهِ وعَلَيْهِمَا الإِصْلاحُ وإِنْ تَعَذَّرَ وإِنْ أَسَاءَ الزَّوْجُ طَلَّقَا بِلا خُلْعٍ*
Ma’ana: *Mace na da damar samun saki saboda cutuwa, ko da kuwa babu bayyanannen shaidu na cewa abin na faruwa sau da dama. Dole a fara yunƙurin sulhu, amma idan hakan ya ci tura, kuma mijin yana da laifi, za a iya sakinsu ba tare da neman yardar miji ko mayar da sadaki (khul’i) ba.*
*Majiya: Mukhtaṣar Khalīl 1/111*
Idan aka zo ga magana, halayen rashin da’a daga miji—irin su duka, barin mata, ko zina—suna daga cikin hujjoji masu ƙarfi da za su iya ba wa mace damar neman saki daga alƙalin shari’ar Musulunci. Manzon Allah ﷺ da kansa ya taɓa shiga tsakanin wani miji da matarsa da ake bugunta da ƙarfi, inda ya kafa misali na doka cewa shugabanni su gyara irin wannan hali.
Aliyu ɗan Abi Ṭalib ya ruwaito:
*Matar Al-Walid ibn ‘Uqbah* ta je wurin Annabi ﷺ tana kuka tana cewa, “Ya Manzon Allah! Al-Walid yana buguna ni!”
Sai Annabi yace:
*قُولِي لَهُ قَدْ أَجَارَنِي*
*"Ki ce masa: 'Ya ba ni kariya.'"*
Bata daɗe ba sai ta dawo tace: “Bai yi min komai ba sai ƙarin duka!”
Sai Annabi ﷺ ya yayyanka wani yanki na rigarsa ya ce:
*قُولِي لَهُ إِنَّ رَسُولَ اللَّهِ قَدْ أَجَارَنِي*
*"Ki ce masa: Lalle Manzon Allah ya ba ni kariya!"*
Bata daɗe ba ta dawo tace: “Bai yi min komai ba sai ƙarin duka!”
Sai Annabi ﷺ ya ɗaga hannuwansa yana cewa:
*اللَّهُمَّ عَلَيْكَ الْوَلِيدَ أَثِمَ بِي مَرَّتَيْنِ*
*"Ya Allah! Ka hukunta Al-Walid, domin ya yi mini laifi sau biyu!"*
*Majiya:* *Musnad Ahmad 1257 – Ingantacce (Sahih)*
Dangane da yadda mijin Sabuwa ke zuwa kan shinfiɗarta kuma
*Shaykhul-Islam Ibn Taymiyyah ya ce:*
*يَجِبُ عَلَى الرَّجُلِ أَنْ يَطَأَ زَوْجَتَهُ بِالْمَعْرُوفِ...
*Ya wajaba ga namiji ya kusanci matarsa ta hanyar da ta dace da al’ada. Wannan yana daga cikin manyan hakkinta a kansa, ma fi girma fiye da ciyar da ita. An ce wajibi ne akalla sau ɗaya a cikin kowane watanni huɗu. Wasu kuma sun ce ya danganta da buƙatarta da ƙarfin mijin, kamar yadda ciyarwa ke zama bisa buƙata da iyawarsa. Wannan ra’ayi na biyu shi ne mafi inganci.*
*Majiya:* *Majmu’ al-Fatawa 32/271*
*— Ya kamata mijin ya kusanci matarsa ta hanya da za ta gamsar da sha’awarta, ba wai kawai ya tsaya kan jin daɗin kansa ba, kuma ba da tsauri ko tashin hankali da zai cutar da ita ba.*
*— Shari’ar Musulunci ta gane cewa watsi da buƙatar jima’i ba matsalar jiki kawai ba ce, sai dai tana shafar nutsuwar zuciya da lafiyar kwakwalwa, waɗanda su ne ginshikan zaman lafiya a aure.*
*Imam Ibn Qudamah:*
*ويُسْتَحَبُّ أَنْ يُلَاعِبَ امرأتَه قبلَ الجِمَاعِ لتَنْهَضَ شهوتُها فتنالَ مِن لذَّةِ الجماعِ مثلَ ما نالَ*
*— An so (miji) ya rika wasa da matarsa kafin jima’i, domin sha’awarta ta motsa, ta ji daɗin jima’i kamar yadda shi ma yake ji.*
*al-Mughnī 10/232*
A bisa waɗannan hujjojin da waɗanda lokaci ba zai bani damar zaiyanosu ba
Sabuwa na sake ki, in kin gama idda kin samu miji kiyi aurenki na rufe wannan shari'ar ta ƙare.
Sakin yana nufin babu damar kome har sai kin yi wani auren kin fito.
Kina da damar riƙe ƴaƴanki in kina so. Kuma ratayayyen hakkine a kan ubansu ya ɗauki ɗawainiyarsu bisa daidai samunshi da kotu zata duba ta ayyana mishi kuɗin da zai dinga baku duk wata.
Bugu da ƙari su saurara kuji abinda Allah yace.
( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نَكَحْتُمُ الْمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ طَلَّقْتُمُوهُنَّ مِن قَبْلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمْ عَلَيْهِنَّ مِنْ عِدَّةٍ تَعْتَدُّونَهَا ۖ فَمَتِّعُوهُنَّ وَسَرِّحُوهُنَّ سَرَاحًا جَمِيلًا )
الأحزاب (49) Al-Ahzaab
Ya ku waɗanda suka yi imani! idan kun auri muminai mata, sa'an nan kuka sake su a gabanin ku shafe su, to, ba ku da wata idda da za ku lissafa a kansu, kuma ku yi musu kyautar jin daɗi kuma ku sake su saki mai kyau.
( لَّا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ إِن طَلَّقْتُمُ النِّسَاءَ مَا لَمْ تَمَسُّوهُنَّ أَوْ تَفْرِضُوا لَهُنَّ فَرِيضَةً ۚ وَمَتِّعُوهُنَّ عَلَى الْمُوسِعِ قَدَرُهُ وَعَلَى الْمُقْتِرِ قَدَرُهُ مَتَاعًا بِالْمَعْرُوفِ ۖ حَقًّا عَلَى الْمُحْسِنِينَ )
البقرة (236) Al-Baqara
Kuma babu laifi a kanku idan kun saki mata matuƙar ba ku shafe su ba, kuma ba ku yanka musu sadaki ba. Kuma ku ba su kyautar daɗaɗawa, a kan mawadaci gwargwadonsa, kuma a kan maƙuntaci gwargwadonsa; domin daɗaɗawa, da alhari, wajibi ne a kan masu kyautatawa.
( وَإِن طَلَّقْتُمُوهُنَّ مِن قَبْلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ وَقَدْ فَرَضْتُمْ لَهُنَّ فَرِيضَةً فَنِصْفُ مَا فَرَضْتُمْ إِلَّا أَن يَعْفُونَ أَوْ يَعْفُوَ الَّذِي بِيَدِهِ عُقْدَةُ النِّكَاحِ ۚ وَأَن تَعْفُوا أَقْرَبُ لِلتَّقْوَىٰ ۚ وَلَا تَنسَوُا الْفَضْلَ بَيْنَكُمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ )
البقرة (237) Al-Baqara
Kuma idan kuka sake su daga gabãnin ku shãfe su, alhãli kuwa kun yanka musu sadãki, to, rabin abin da kuka yanka fãce idan sun yãfe, kõ wanda ɗaurin auren yake ga hannunsa ya yãfe. Kuma ku yãfe ɗin ne mafi kusa da taƙawa. Kuma kada ku manta da falala a tsakãninku. Lalle ne Allah ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.
Alƙali ya tambayeni na yafe ko ya bani kuɗin.
Darajar Baba Malam yasa nace nayafe mishi.
Alƙali ya ɗaura da cewa
"Shi kuma Babangida kotu zata ci tararshi na ƙin amsa kiran da kotu tayi mishi dan kotu ba sa'arshi bace"
Na sanar ma alƙali bani da buƙatar riƙe yaran yaje ya riƙesu.
Ina gama faɗin haka.
Alƙali ya rubuta takadda tare da buga hatimi a jiki yasa magatakarda ya miƙo mun.
Guduma ya buga duk muka miƙe.
Da gudu na fita waje nayi sujjada a ƙasa ina godema Allah har da kuka dan murna.
Su Labbai ne suka ɗaga ni.
"Cau cau wallahi kunsan Allah dama yau nayi niyyar saka kan Babangida gabas in mishi kisan mummuƙe dan naga shari'ar taƙi ƙarewa ashe zata ƙare, na Allah basa ƙarewa."
Cewar Gaza da yake taya ni murna. Duk ƴan uwana suna bayana abinda yake sake ƙarfafa mun guiwata kenan. Maza muka shige motar Dr Kamilu muka fice a kotun.
Mahaifiyarshi kuma tata motar ta shige ta tafi wata kotun dan tsaya ma wata matar itama, aikin fa kenan zamani ya lalace da gaskiyarka in baka da hanya ba lallai ka samu adalci ba. Inajin wani irin daɗi marar misaltuwa na ratsani jina nake tamkar an sauke mun dala da gwauron dutse a kaina. Team Babangida kuma ya jikin naku?
BABANGIDA:.
Babangida kuma da ƙyar aka jawoshi daga kotun ya fito dan ji yake duniya na juyawa dashi ga ba guiwa😆. Take yaji wani irin matsanancin son Sabuwa ya shigeshi so mai girman da bai taɓa yima mace makamancinshi ba.
Gashi gobe asussubar fari zasu wuce garinsu Sumy ɗaurin aure tare da su Sa'a da zasu tafi da akwati. Ya ƙuƙuta yayi ma matan nashi kaya kala bibbiyu da ƙyar da kuɗin ɗinki.
Kawu manga ne ya iso kusa da Babangida ya dafa shi suka haɗa idanu.
"Mustapha kayi ƙoƙari ka tawo da Babangida can gidana akwai zama da zamu gudanar na family. Babangida ita fa rayuwa da kake gani haka take juyawa da duk wanda yayi wasa da'ita duk wanda yayi guga da zummar ɗiban duniya ƙarshe inya jawo bazai tadda komai ba.
Ba kai bane baka ɗauki saki a bakin komai ba?
Sai gashi yau kaine alƙali ta sakar maka mata kuma ta saku har a wajen Allah gashi harma ka shiga mawuyacin hali akan haka. Nifa na ɗauka farin ciki zaka yi naga gobe_gobennan zaku wuce wajen ɗaurin aure. Danni ba zuwa zanyi ba tunda dai munje an ganmu mun gabatar da kanmu da sadaki ai magana ta ƙare"
Su Sa'a dasu Wawo ne suka zo suka wuce su Kawu manga ko wanne zuchiyarshi babu daɗi.
Babangida na bayan motar Mustapha yayi shiru kana ya takure waje guda ya shiga wani irin zurfin tunani. Irin diramomin da sukaita yi da Sabuwa, da Cus da yake kiranta, da irin yadda ya hanata saƙat yake ta tunowa.
"Babangida yafa kamata ka sararama kanka akan batun Sabuwa. Ni dai wallahi tun daga farkon haɗuwarku kawo yau da Allah ya ƙaddara ƙarshen zamanku bansan wata riba da zance kunci a aurenku ba. Tunda dai yarinyar ta shigo rayuwarka kake ta karo da matsaloli manya.
Shin Babangida ko dai kana son Sabuwa ne mu bamu sani ba ka barmu a duhu?"
"Wallahi Mustapha nima ban san sonta nake yi ba ashe mugun sonta nake yi. Amman ina jin wani irin yanayi a jikina akan Sabuwa sosai. Nafi yawan tunaninta fiye da duk matan dana aura a rayuwata. Mustapha ina ga fa soyayya da kishin Sabuwa ne ya lulluɓemun zuchiyata ya haifar mun da muguwar tsanarta. A yau dai naji duk duniya babu macen da zan iya rayuwa da'ita sama da Sabuwa. Mustapha wallahi badan kada a saki Malama Babba bane yasa na dage naƙi sakin Sabuwa ba. Sonta nake yi naga Ƴan taskar Badiat suna ta bina da bita da ƙulli tuban nawa ma sun kasa yadda dashi"
Dariya Mustapha yayi yace
"Kaga wannan Ummin Maman hum yarinyar akwai daɗin murya ko ita zata maye gurbin Sabuwa ne? "
Da harara Babangida ya bishi kawai daidai isowarsu ƙofar gidan Kawu manga can suka baro Kawu Manga tare da Baba Malam.
"Ni shawarar da zan baka kawai ka mance da Sabuwa a cikin rayuwarka kayi tsayuwar daka wajen ganin Baba Malam ya yafe maka.
Ga mata nan birjik a bariki waɗanda suka fi Sabuwa kyau yara masu asalima. Naga gobe ɗaurin aurenka ma zamu tafi. Sumy kam ai tayi kuma duk wani taro zaka iya shiga da'ita ba tare da anji kunya ba yarinya ga turanci."
Buɗe murfin motar Babangida yayi ba tare da yace dashi ci kanka ba ya wuce cikin gidan.
Ga takalman ƴa uwanshi nan a ƙofar falon yana jiyo hargagi da maganganu marasa daɗi da Sa'a da Kudidi suke fesarwa.
Idanu ya lumshe shikenan shi kullum a kanshi ake zama a falimi? To shikenan ta faru ta ƙare zama ya ƙare tunda dai har Sabuwa ta fice a rayuwarshi ai. Sai hankalin kowa ya kwanta Allah ya isan da mahaifinsu yayi mishi ta hau kanshi. Babban abu mafi ciwo sakin Malama Babba da Baba Malam zaiyi a matsayinshi na ɗa ace shi yai sanadiyyar tsinka igiyar auren data riƙa ta haure shekaru sama da sittin kaico.
A hankali ya zame takalminshi ya shiga da sallama. Uwa kenan itace kaɗai ta iya amsa sallamar Babangida har tana nuna mishi wajen zama kusa da ƙafarta.
Sai yaji tamkar yayi wayyo. Jikinshi har rawa yake yi ya tsallake su Wawo ya zauna adaidai inda ta nuna mishi. Kannan nashi a ƙasa duniya tayi mishi atishawar tsaki, sai tamaule zuchiyarshi take yi a ƙirjinshi son Sabuwa na neman rayuwarshi."
MALAM BABA:.
"To Yaya mu fa roƙonmu a madadin ni da ƴaƴanta shine ka daure ita Babba ta dawo ɗakinta dan ALLAH. Wannan al'amarin ya faru mu barshi a ƙddarar da bawa bai isa kauce mata ko nuna wayonshi ba."
Hannu Baba Malam ya saka a aljihu ya ciro takaddar saki ya miƙa ma Kawu manga.
"Wannan takaddar sakin Babba ne. Tuni na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 19