roƙeka kada ka aikata abinda zaka sake komawa gidan yari ga madamsy nan ka barta da wa?"
"Ahh in barta da Allah mana. Wai ke Rahama an faɗa miki tsoron gidan yari nake yi? Naci dubu wallahi sai ceto. Wallahi ke wuya a Lagos wuya a kwatano, wuya a tafa wuya a mararraba, wuya a shagamu fa."
Madamsy ce ta shiga yi mishi kirari yana ƙara botsarewa da ƙyar suka harhaɗu aka bashi haƙuri daya tsaya abi matakin kotu tukunna in hagu ta ƙiya a wannan karon dole ayi dama.
Ni dai da ba daɗin jikina nake ji ba na miƙe na fito ni dasu Labbai zamu koma can ɗakinsu.
"Lolo zan samu dubu uku a hannunki zanyi kuɗin motane wallahi kun ganni baƙi zanje tasha in taro zan kaisu ges house ƴan kuɗaɗen jikina dasu nayi girki."
Maigogul ke magana yana gaban murhu yau dai shi yake girki a gidan duk da ba wani sabon abu bane. Yayi gwafe_gwafe a gaban wuta jallof sai ƙamshi take zubawa wallahi saida yawuna ya tsinke"
To zan aiko maka dashi"
"Allahu Akbar kaga ƴar albarka wacce aka haifa tsiya na bacci. Lolo ta Maigogul Allah yayi miki albarka. Ba zaku tsaya kuci abincin nawa bane? Duk da baƙi na dafama. Bari in zubo miki ke kaɗai zaki samu arzikin cin abincinnan Lolona uhm bana so kina damuwa Lolo kin ganni nan Hamshaƙin garnaƙaƙin mai kuɗi nake miki fatan ki aura. Lolo kika auri mai kuɗi dani zaki tafi ai bazan iya zama ba"
Ya tashi harda ɗan gudunshi ya zari kwano a kwando ya zuba mun da dama kuwa ga nama an yayyanka ƙanana abinci sai ƙamshin kori yake yi.
Hawayene masu zafi suka zubo mun daya tawo da sauri ya bani kwanon.
Madadin in amsa sai na faɗa kafaɗarshi na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuchiya.
Shiru Maigogul yayi yana riƙe dani da hannu ɗaya ga abinci a ɗayan hannun nashi.
"Aikin banza da wofi yanzu nan har Maigogul ya kai irin wannan uban a wajenki Lolo? "
Cewar Rakiya.
Ɗagoni yayi yana share mun hawaye da gefen malum malum ɗinshi yana wani irin murmushi.
"Lolo kiyi haƙuri ki dena yawan kuka ni Maigogul ina tare dake har abada. Zaki yi albarka zaki samu rayuwa mai kyau a gaba. Amshi abincinki kije kici ki ƙoshi"
Amsa nayi na kalleshi muka yi murmushi.
Sai kawai ya amshi kwanon ya sake zuba mun abincin na karɓa na fita Rakiya sai shewa take yi.
Da muka isa ɗakin su Labbai saina buɗe kayana na zaro dubu shida naba Sadiya ta kaima Maigogul dubu huɗu Rakiya dubu biyu.
Abincin daya bani kuma nasa su Mardiyya a gaba suka ci. Saida suka gama na aiketa ta siyo biredi suka kara da shayi. Ganin lokacin shan maganina yayi ne yasa nima na sha shayin na warwatsa magungunana na jingina da bango ana ɗan hira ina saka baki sabida in ƙwarara kaina.
Hmmm wajajen huɗun yamma muka jiyo sallamar yaro wai ana sallama da Sabuwa inji wani mutum a ƙofar gida.
Ina kyautata zaton Yaya Kamilu ne. Wanka na fito da sauri na soma saka kayana.
"Mardiyya kije ki ce ma mai kirana ganinan fitowa likitane shi ya taimakeni a asibiti kuma shi yaita biyan komai na maganina"
Na faɗa mata ne tun kafin su zargi wani abun su soma tuhumata ko in bar ƙwaƙwalensu da hasashen da bansan wanne iri bane.
Fita tayi a nutse nima na samu zarafin shiryawa na zura hijabina na ja hannun Malama muka fito.
Ai kuwa shi ɗinne yana jingine a bakin motarshi Mardiyya na gabanshi yana mata tambayoyi tana amsawa na isa da sallama.
"A_a Sabuwa har kin warware an shiga cikin ƴan uwa ko?"
Dariya nayi mishi kawai.
Ya yafito Malama halamun taje. Sakinta nayi taje suka gaisa yake tambayarta ita izufinta nawa tunda yaji Mardiyya tayi sauka"
"Sabuwa ashe yaran namu malamai ne dan ko ni babu sittin a kaina akwai dai arba'in."
Murmushi kawai nayi Mardiyya ta kama hannun Malama zasu koma ciki yaa kirayi sunanta.
"Mardiyya tsaya ku shigarma da Ummi kaya"
Both ya buɗe ya zaro manyan fararen ledoji ya miƙa mata. Tana kan karɓa na hango Babangida yana daidai ƙofar gidanmu yana tawowa idanunshi a kaina ƙem.
Har su Mardiyya suka shige bai ƙarasoba.
Isowarshi ke da wuya sai cewa yayi
"Sabon farka kika samu shine kika yi ƙaryar kurumcewa kika gudu kika bar gidan aurenki da yaranki, kika tafi kika barni da kewarki da tunaninki ashe?
Malam dan abu ta kazan ubanka... Bata faɗa maka tana da aure bane? Ko da yake son zuchiya bazai barka ka tuno wannan ba.
Nine mijinta wanda zamu ƙare rayuwarmu tare"
Kawai saiya cukume Kamilu.
"Ki shige gida Sabuwa wallahi ko in miki dukan tsiya na rantse tunda baki da mutunci matar ƙaddara maras kamun kai ko ki koma ciki ko ni dashi muyi mutuwar kasko wallahi"
Kamilu yace.
"Sabuwa shige gida abunki zanyi mishi bayani"
Ina Babangida da dambe ya kama Kamilu Ni Ko nasa hannu aka na kwarmata ihu dan na fahimci Babangida ranshi yayi mugun ɓaci sosai yafi ƙarfin Kamilu.
Ai kuwa jama' a kamar jira suke yi suka fiffito ciki harda su Adama.
"Tabb Lallai Babangida abun naka yakai
Labbai maza kirawo Gaza yazo ya raba wannan faɗan.
Ina gefe ina kallo kukanma yaƙi zuwa mun dan nasan bama a soma komai ba.
Ina buɗe idanuna na hango Ƴar Shuwa na tawowa wajenmu. Gaza kuwa a guje ya tawo matarshi na biye dashi. Su Rakiya ma sai gasu afujajan babu ko mayafi.
Yana isowa yasa hannu ya ɓanɓare Babangida a jikin Kamilu faɗa ya koma a tsakaninsu.
Babangida ya naushi Gaza 'Gaza ya rama.
"E lallau yau sau nayi ajalinka wallahi wai ni ka fasama baki Tabb yau zaka gane waye Gaza"
Wuƙa ya zaro kamar ƙibtawar idanu ya yanki Babangida, Babangida idanunshi sun rufe da kishi sai tijara yake yi. Madamsy ce tayi saurin shiga tsakaninsu.
Ƴar Shuwa ganin jini na fita a jikin Babangida yasa ta dinga danna ihu kowa da kowa ya fito. Da ƙyar faɗan ya lafa da taimakon mutane, da taimakon su Rakiya da suke ta cakume Gaza. Maigogul dai baya nan. Sun sha naushi in nausa da Babangida sosai shi kuma Gaza ya yayyankeshi a waje kusan huɗu ga jininshi nan kaca kaca. Kamilu yana riƙe da hannun Gaza ga dattijai anata bashi haƙuri.
"To naji amman ya bar unguwarnan kuma kada ya sake zuwa layinnan da sunan zuwa wajen ƙanwata wallahi ko yaranshi na gani sun zo gidanmu saina illatasu. Ai kai ƙaramin dan abu ta kazan ubane mu iyayenka ne yaro a iskanci."
Babangida na ɗaure hannunshi da ɗan kwalina daya faɗi yace.
"A fito mun da yarana to. Kuma wallahi ko mutuwa kuke yi kuna dawowa Sabuwa tawace ina son matata sonta a jinin jikina da jijiyoyina suke yawo bazan saki Sabuwa ba sai dai duk abinda za'ayi ayi
Kai kuma wallahi bazan taɓa yafe maka hakkina a kanka ba."
Gaza sai ihu yake yi ganin matarshi shi ya hana ya kai Babangida ƙasa.
Labbai ce ta tarkato yaran ta turasu gabanshi. Shine ya ja hannayensu suka bar layin. Gaza ya ja hannun matarshi suka tafi. Su Rakiya suka bishi Rakiya sai ɗebo zagi take tana dura ma Gaza. Shi kuma yana faɗa yana sake rantsuwar faɗanma yanzu aka soma.
"Kinga ƙanwata kiyi haƙuri zuwanane duk yaja wannan abun. Ki shiga gida ki tabbatar baki ɗauki damuwa kin ɗaura ma kan ki ba. Kinsan ba lafiya gareki ba.
Ashe Babangidan naki mahaukacin zaki ne. Duk da naga halamun makauniyar soyayyar da shi kanshi bai gane soyayya bace a tattare da amonshi ba, amman tabbas yana mutuwar sonki. Ki je zamu yi waya kinji ko?"
Kai kawai na ɗaga Adama ta ja hannuna muka shige ciki.
Naci kuka kamar raina zai fita har saida ciwo ya bigeni sai Dr Kamilu Adama ta kira bai jima ba ya dawo yaita rarrashina yana bani kalma har dai raina ya ɗanyi sanyi amma fa ba sosai ba gaskiya.
Babangida:.
Yana tafe su Mardiyya na binshi a baya ya riƙe hannunshi da ɗankwalin Sabuwa wanda ya jiƙe da jini sharkab.
A guje ƴar Shuwa ta biyosu lokacin har sun hau abun hawa.
"Baban faty ashe dama zaka iya zuwa wajen Sabuwa matar da tabi tsohon saurayinta. Bayan data dawo kuma ta wuto gida kai tsaye. Inaga dai bokancin Sabuwa da mahaifinta yayi tasiri a kanka dan bokace ita da ubanta nasan baka san wannan ba"
Kallonta a matsayin mahaukaciya Babangida yake yi. Idanunshi a mugun rine ga yaranshi jikinsu duk yayi sanyi .
"Malam ja abun hawannan mu tafi kaji ba hankali bane da'ita"
Ƴar Shuwa tace.
"Tafiya zaka yi ka barni wai?"
"Ke in kinga dama kema kiyi zamanki a gidanku. Ba Sabuwa ba ko wacce macen ma ta fice mun a raina gayyar tsiya"
Da faɗa yake maganar dan a mugun hasale yake.
Fuu abun hawan ya wuce ya bar Ƴar Shuwa tana sheƙa dariya a titi.
"Ai wallahi Babangida ko tsirara zanyi yawo dolen dole saika rabu da Sabuwa har shegiyar ƴarta sai ta bar gidanka domun ba Yarka bace.
Ai tunda Sabuwa ta kwace mun Khalid to dole ta rabu da Babangida. Kuma saina saka mata baƙin jinin da ko kallonta wani ɗa namiji bazai kuma yi ba wallahi sai dai ta dawwama a gaban shegun iyayenta Khalid kuma saina rabasu ya dawo hannuna domin tun kallon farko ni Khalid naso ba abokinshi ba."
A titi Babangida yasa aka sauke su Mardiyya shi kuma ya wuce kemis aka wanke mishi wajen yankan a can layinsu. Kai tsaye gidam Kawu Manga ya nufa.
Yana shawo kwana ya hango Kawu Manga tare da Baba Malam a ƙofar gida harda Sa'a tana gurfane a gabansu.
Baiso Baba Malam ya ganshi a wannan halin da yake ciki ba amman babu yadda ya'iya haka ya nufesu.
",ina wuni Baba Malam yaya kufan jikin naka?"
Baba Malam sai ya yinƙura da ƙyar ya miƙe.
"Manga zan shiga daga ciki in kwanta. Ke kuma Sa'a duk bijirewar da zaki yi daidai ne. Sauban ai ɗanki ne kina da ikon zaɓa mish mace ta gari kam ai naki da sauƙi akan abinda ƙaninki ya aikata ai duk wata ɓaraka daga wajen mahaifiyarku ne"
Yana kaiwa nan ya shige. Ai kuwa yana shigewa Sa'a tace.
"Duk Babangida ne ya ja mana bala'innan. Ni kuma taya ina kallo ɗana zai auri yarinyar da aka sameta bata hanyar aure ba. Da uwar ƴar da uban ƴar duk gasu ga kamarsu. Inace ita uwar wajen saurayinta ma ta gudu da aurenta..."
"Yafa isheki Sa'a. Ki sani nima daga yau na soke maganar auren Sauban da Mardiyya. Ƴata ko zata rasa miji ni ni kaɗai ubanta na isa in sanyata a farin ciki. Kawu zan koma dama nazo in sanar muku Sabuwa ta dawo, amman gidansu ta wuce kuma ta sake mayar dani kotu"
Yana gama faɗin haka ya wuce yana jin tsabar jiri tamkar ya faɗi. Da ƙyar ya iya kai kanshi gida. Ɗakin Sabuwa kai tsaye ya shiga bai zarce ko inaba sai kan gado ya kwanta yana shaƙar ƙamshinta wani al'amari na bijiro mishi a zuchiyarshi game da sabuwa shi ba ƙiyayya ba kuma ba jin haushi ba.
Kiran wayar Sumy ce ta dawo dashi hayyacinshi wanda yayi daidai da kiran sallah azahar da aka soma a masallacin unguwar.
Ɗaga wayar yayi a sanyaye. Yana ɗauka yace.
"Sumayya bari inje masallaci inna fito zan kiraki"
"To shikenan ina fa jiran kiranka ato dan ina da magana fa ato."
Kai kawai ya gyaɗa ya kashe wayar ya mayar aljihunshi ya fito falo.
"Aminu kuyi alwala bari in sake kaya sai mu je masallaci ko?"
Sai da ya sake taɓa jikin Malama kafin ya fita har zuwa lokacin da zazzaɓi kau a jikinta. Shi sai yake jinma kamar zazzaɓin ƙaruwa yayi.
Dole ma ya ƙaru ai irin wannan jafa'in daya faru a gabansu ai dole ya sake assasa hauhawar zazzaɓi.
Ɗakin Ramatu ya shiga ya ko tadda ɗakin maƙil da mata.
Sabida haushi kawai sai ya fita ya nufi ɗakin Ƴar Shuwa ya saka ki ya buɗe ya shiga.
Yana tsaye a cikin uwar ɗakinta zai cire kaya Ramatu ta shigo.
"Haba ranka ya daɗe ya zaka shigo nan kuma alhalin kasan nice nake dakai har sai anyi la'asar girkina zai fita.?"
Ƙur yayi kawai yana kallonta yama rasa mai zaice mata. Sai a lokacin ne taga yankan dake tafin hannunshi dana wuyanshi mammanne da filasta.
"Subhanallahi wannan ciwon kuma fa daga ina haka?"
Wucewarshi banɗaki yayi ya sakar ma kanshi ruwan sanyi kawai idanuwanshi a lumshe yana hango Sabuwa a gaban Dr Kamilu harma da yaranshi.
Kanshi a mugun ɗaure yake ga tambayoyi cike a bakinshi ko ya fesar babu mai bashi amsarsu.
"Wato Sabuwa dai na lura ajalina take so tayi ta huta. Ko wanne ɗan iskan ta kuma samowa oho. Kuma iyayenta da ƴan uwanta suka mara mata baya. Ni Sabuwa zata ci ma amanar Aure?"
Lafiyayyen hannun ya doka a bango yana jin wani irin ƙaikayi a zuchiyarshi.
A gaggauce ya dauro alwala ya fito.
A zaune fa a bakin gadon ƴar Shuwa ya fito ya tadda Ramatu.
"Ki tashi ki fice mata a ɗaki. Ai da tana nan ko labulen ɗakin baki isa kin riƙe ba balle har kima kanki masauki a kan gadonta ko?
Bana son neman jarfa ki barni da damuwar dake damuna dan ALLAH"
Jikinshi ya goge harya sauya kaya Ramatu bata fita ba tana kallonshi baki a taɓe.
"Wai shin har sai zuwa yaushe zuchiyarka zata dena wahalaka akan Sabuwa ne. Oho wato wannan ciwon ma ƴan gidansu ne suka sake ji maka amman ka saketa kaƙi sakinta. To ma dame tafi ragowar matan daka dinga saki in banda farar fata.
Tsinka mata mari yayi mai zafi
A ɗakin ya barta a tsaye yayi ficewarshi. Shine dai ta biyoshi ta fito tana riƙe da kunci
Masallaci suka wuce da yaran ana idar da Sallah ya dauki Mardiyya da Malama a mashin sai asibiti. Ai kuwa suna zuwa akace ciwonta ne ya tashi babu shiri aka basu gado da gaggawa.
Daga shi sai Mardiyya a asibitin har zuwa bayan la'asar kuma ya kira Malama Babba ya sanar mata a tunaninshi zata turo a zo a zauna dasu a asibitin shi kuma ya tafi neman kuɗi sai yaji shiru.
"Mardiyya ki zauna da Malama ina zuwa yanzu ɗaya daga cikin Ummanku zata zo ta zauna da Malama su kwana ke kuma inna dawo sai in mayar dake gida"
"Toh Baba sai ka dawo Allah ya tsare"
Har wani tashi kan Babangida yayi sabida tsantsar daɗi.
Yana tafe yana lissafi har ya karasa gida. Bai shiga gidan ba sai da akayi magriba tukunna.
Ɗakin Ƴar Shuwa ya nufa kai tsaye ya taddata a kitchen tana tuƙa tuwo.
Bai kulata ba ya shige ciki, itama babu abinda tace mishi har saida ta gama tuƙa tuwonta kana ta shiga ta sameshi yana waya da Mustapha yana labarta mishi an ba Malama gado. Sai da ya gama wayar tas ya sauke kana ya dubi Yar Shuwa da tayi ƙuri tana kallonshi.
"Ki haɗa abinci a kula zan kaima su Mardiyya a asibiti Malama aka ba gado. Sannan inason ki zuba ruwa a filas"
"Kash gashi abincin daidai cikinmu da yarana na girka sai kuma naka. Ruwan zafin dai tunda da wuta bari in ɗaura a hita yanzu."
Ficewa tayi ta jona ruwan a ƙaramar robar fenti tana tsaye tana jiran ruwan tana magana a zuchiyarta ko kuma ince saƙa mugun saƙa.
Biyota yayi ya dubeta suka haɗa idanu tayi kwalliya da ƙananun kaya tayi kyau sai ƙamshin humra take yi.
"Ki haɗa nawa abincin a kula bari in samu Ramatu dan ita zata kwana dasu."
Nanma bai jira abinda zata ce ba ya shiga ɗakin Ramatu ya taddata suna cin abinci ga TV suna kallo ko ina kaca_kaca ga kayan ɗaki har kaya amman Ramatu irin matannanne da ba ko yaushe suke gyaran daki ba. Duk randa taso gyara wa dai zata gyara komai ta ajjiye komai a muhallinshi.
Jallof ɗin shinkafar manja da alaiyawo suke ci da ruwansu ɗan kamface a gabanta.
"Lafiya naga ka shigo ɓangarena kaga kar kasa jarababbiyar matarka ta biyoka"
Murmushin takaici kawai yayi.
"Ki gama cin abincin zan kai ki asibiti zaki zauna da Malama bata da lafiya an bata gado."
Idanu ta ware amman da suka haɗa idanu taga ya murtuke fuskarshi tamau bata ga fuska ba dole ta hadiye maganarta ta kora da ruwan sanyi "
Sallar isha da aka soma kirane yasa ya tashi tsaye.
"Ki tsimtsa kafin in dawo sallah sai mu wuce. Su kuma yaran ki miƙa su wajen Aisha ko ki miƙa su ɗakinsu Mardiyya"
Yana faɗin haka ya saka kai ya fita.
Tare suka je masallaci da su Aminu.
A cikin masallacinne yake sanar musu Mardiyya na asibiti tare da Malama.
"Amman kunci abinci.?"
Aminu yace.
"E na dafa mana farar shinkafa dama muna da miya"
"To akwai ragowar abincinne ka zuba sai a kaima ita Mardiyyan?
Kafin Aminu yayi magana ma yace ya barshi kawai tunda a gida Mardiyyan zata kwana.
Suna shigowa ya karɓi abinci da filas ɗin ruwan zafin a cikin basket ƙarami.
Tun daga tsakar gidan Ramatu ta hau mashin ɗin tana riƙe da basket ɗin abincin aminu ya buɗe musu get suka fita.
Mardiyya na zaune ƙwalam ta hango Babansu da yadikkonsu ajjiyar zuchiya ta sauke.
"Mardiyya yaya jikin na Malama ta farka kuwa?"
"Ta farka Baba tana ta kuka tana kiran Ummi ni kuma wayata babu kati ban kira mata Ummin ba. Likita ma yace in ka dawo yana son ganinka."
"To shikenan bari naje. Ramatu bata abincin taci sai in zo mu tafi."
Ficewa yayi. Mardiyya kuma ta tusa wannan tuwo a gaba malmala ɗaya ƙarami da nama tsoka ɗaya ta cinye. Ramatu kuma ta hakimce a bakin gadon jinyar sai hararar Mardiyya take yi. Sauban ne ya shigo da kaya kici_kici harda su lemu da ayaba da abinci kula guda, da ruwa katon guda.
"Baba Ramatu ina wuni ya mai jiki?"
Sauban cikin girmamawa yake gaishe da Ramatu. A gatsine ta amsa tana ƙarema ledojin daya jibge a gaban Mardiyya ido. Ledar da kular take ciki ya buɗe mata.
"Kici abincin kince mun yinwa kike ji ko?
Kai ta ɗaga mishi kafin daga bisani tace.
"Baba ma ya kawo mun tuwo naci. Sai dai tunda wannan kai ka kawo bari inci kafin mu tafi"
Abincin ta zuba a plate lafiyayyar jalof ce wacce taji ɗanyen kifi. Ramatu kanta saida ta haɗiye yawunta. Mardiyya na cikin ci Babangida ya shigo da sallamarshi. Sauban ya kalla ya dubi ledojin daya kawo ya kalli abincin da Mardiyya take ci. Idanunshi ya lumshe yaji wani abu na tafasa mishi ranshi.
"Baba ina wuni yaya jikin Malama?"
"Lafiya Sauban. Jikinta da sauƙi za'ace. Kaine da wannan hidimar?"
Kai Sauban ya sosa tare da cewa.
"Ah ai wannan ba komai bane"
Zama Babangida yayi a farar kujera.
"Mardiyya zubo mun in ɗanci kafin mu tafi"
Mrs Bukhari
#Team Babangida
#Team Sabuwa
#Team Gaza
#Team Maigogul
[8/19, 7:41 PM] BADA'AT IBRAHIM: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA GOMA SHA UKU
Harta ciro kwano zata zuba mishi sai yace ta zuba mishi a cikin kwano da taci.
Ko data zuba mishi bai wani ci sosai ba. Ta miƙa mishi ruwa yasha sai yace.
"To Sauban mu fa tafiya zamu yi Ummansu ce zata zauna a wajenta. In kaje gidan ka gaishe da Sa'a"
Tare suka fita dashi Mardiyya ta hau mashin ɗin Babangida Sauban ya shiga motarshi kowanne ya nufi gida.
Saida Babangida ya jima tare da su Mardiyya a ɗakinsu kafin yayi musu sai da safe ya nufi ɗakin Ƴar Shuwa yana murɗawa yaji ta kulle ɗakinta saida yaita bugu kafin tazo ta buɗe mishi ya shiga.
Yana zaune a bakin gado tunani yayi mugun yi mishi yawa sai ya jiyo muryar Ƴar Shuwa a kanshi.
"Aina ɗauka acan dukka zaku kwana a wajen ita yarinyar shi yasa ma na kulle dakina.
"Zauna muyi magana ɗake"
Fuskarshi a mugun murtuke take babu ko wasa dis a fuskarshi, sai jikinta ya mutu. Zama tayi a kusa dashi tana saurarenshi.
"Da farko inaso in tambayeki ki tabbatar kin faɗa mun gaskiya in kikai mun ƙarya ranki zai ɓaci kuma zan saɓa miki"
A sanyaye tace.
"Ina saurarenka"
"Kulolinki ina suke danna lura kin dena saka mun abinci a kula. Sai yau naga wata koɗaɗdiyar kula a ciki kenan kika zuba mun abinci, sannan ina kika samota dan ni ban sanki da wannan kular ba naga kuma ba sabuwa bace."
Gabanta ya faɗi ras da jin abinda yake tuhumarta akai. Dama tasan za'a rina shi yasa tun kafin azo hakan taso ta samu kula ta siya ko sakan ko sabuwa mai ɗan rangwamen kuɗi.
Ita kanta jin Ramatu ta sai kula mai tsada ya matuƙar ɗaga mata hankali. Gashi shima ya tare ta da maganar.
"Kulolin suna gidanmu ne da ragowar kayan wutana sabida kaga kitchen ɗina babu kanta ga ƙanƙanta kulolina manyane ba zasu zauna a kitchen ɗin bane."
Ƙur yake kallonta.
"Sai kuma kika kasa cire mun kular da zaki dinga zuba mun abinci a ciki? Sannan har sai kin kai kuloli gidanki ga ƙarƙashin gado ga store naga tarkace ne a ciki me yasa baki ajjiye a ciki ba"
Tsuru_tsuru tayi mishi. Shi kuma bai yadda da abinda ta faɗa mishi ba. Shi zarginshi siyarwa tayi tayi hidimar bikin ƙanwarta dasu dan yaga ta dinka kayayyaki manya harda su takalmi da jaka. Kuma hakanne a dalilin bikinne ta harhaɗa ta kaɗar dasu sabida ta fita kunya dangi suna ganin tana auren mai kuɗi ace an tashi bikin ƙanwarta ba'aga tayi bajinta ba har ƙaramin zobenta na gold saida ta siyar duk a bikin dan kawai tayi bajinta.
"Hmmm ki kira waya gobe a dawo miki da wasu kulolin na faɗa miki kenan. In kin fahimta ni namijine mai son kula ɗebi da kanka wannan tsarinane kuma kin sani ba tun yau ba.
Magana ta biyu itace me yasa inna bada kuɗin gawayi sai in dawo in same ki kina girki da risho."
"Ai Ramatu ma a rishon naga take yi"
A tsawace yace.
"Yanzu dake nake yi ba Ramatu ba. Ko so kike mu kafa teburinta a ɗakinki?
Wato na fahimci rayuwar ƙarya daga ke har ita kuke son yi. Bazai yiwu kuje ku jawo mun jarfa ba. Ni na rungumi ƙaddarata ace ku matana kun kasa ɗaukar ƙaddararku kullum ƙorafinku kifi nama, ko ban bada kudin kifi ko nama ba sai in dawo in gani a girkinku alhalin nasan ba sana'a kuke yi ba. To wallahi in kuna son zamanku lafiya ya zame muku dole ku dawo cikin taitayinku.
Duk da a cikinku duk sabida kuɗi kuka aureni Sabuwa ce kaɗai a lokacin dana aureta ƙarma ƙarma kawai nake yi.
Kuma daga yau dole a haɗe girki duk wacce take da miji zata yi girki na dukka gidan har da su Mardiyya"
Baki zata buɗe tayi magana a zafafe ya nuna mata yatsa.
"Kimun shiru maras kunya fitsararriya kawai sai in fasa bakin ki Allah. Bar ganin nayi sanyi ki zaci zan ɗauki take_ taken iskanci wallahi ƙaryane. wallahi baku isa ku juya ni yadda kuke so ba wannan doka ce na kafa daga gobe ki ɗaura girkinki da kowa."
Yana gama wannan maganar ya haye gado yayi kwanciyarshi.
Shinfiɗa ta fita falo tayi ma yara ta dawo ta juya mishi baya a gado. Cikinsu babu wanda yayi bacci sai tubkewa da warwarewa suke yi. Ita ta ƙuduri niyyar gobe sassafe zata je ta kai ƙaranshi wajen Malama Babba dan tayi rantsuwar ba zata taɓa haɗa girki da kishiya ba har taci abincin kishiya ba
Shi kuma Babangida da tunani biyu ya kwana tunani na farko na sabuwane da wannan namiji daya gansu tare. Sai kuma Malama dake gadon asibiti.
Har mafarki yayi Sabuwa ta dawo cikin rayuwarshi suna ta zuba soyayya harma sun sake samun karuwar ɗiya mace mai kama da Mardiyya sak.
Farkawa yayi da asuba sai yaji zuchiyarshi ta sake yin nauyi sosai.
Yana dawowa sallar asuba sai yayi wanka ya kintsa Ƴar Shuwa tana gado tana baccin asara.
"Aisha ki tashi ki dafa shayi zan siyo kayan tea"
Cikin magagi ta amsa mishi amman harya dawo bata tashi ba. Ga yara a falo sai kawai ya juna ruwa a hita ya tafasa ruwan tea ya soya musu ƙwai. Ya zuba nasu Mardiyya ya cika musu jug da tea ƙwansu ya zuba a kwano ya kira Aminu yazo. Daidai futowar Ƴar shuwa daga ɗaki tana muƙa.
Da kallo tabi Babangida da Aminu da aka miƙa mishi jug. Yawu ta haɗiye muƙut bata ce uffan ba ta koma ciki. Da kanshi ya sallami yara tsab, ƴan asibiti kuma ya ware musu nasu harya zuba a basket. Yana gama karyawa ya miƙe ya ajjiye mata kuɗi nera dubu biyar.
"Ga kuɗin cefanen rana dana dare dukka ayi da ƴan asibiti"
Ficewarshi yayi baibi ta kanta ba. Itama ko a dawo lafiya bata ce mishi ba. Ta zauna tana ta tunanin ƙila lokacin rabuwarta da Babangida ne yazo dan ita bata
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 19