jikin kujera kunnenshi babu abinda yake tariyo mishi face muryar Sabuwa.
"Wanka zaka soma yi ko abinci zaka ci?"
Yajiyo muryar Ƴar Shuwa. A hankali ya buɗe idanunshi ya ƙura mata idanu cikin tuhumar da saida ta tsargu a karan kankin kanta.
"Uhm kina farin cikin Sabuwa ta fita fit a cikin rayuwata ko Aisha? To baki sani ba rabuwata da Sabuwa tamkar an kashe macijibe ba tare da an sare mishi kaiba. Nasan duk wannan kwalliyar, da sababbin kula da wata sabuwar tarairaya duk sabida kinji labarin da kike mafarkin jine tunma baki zama mallakina ba. Lokacin kina ƴar kwalta kina yawon bina hotel_hotel muna aikata ɓarna."
Sai yayi wani murmushi wanda shi kaɗai ya barma kanshi sanin fassararshi. Miƙewa yayi ya shige banɗaki.
"Baka yi ƙaryaba Babangida burina shine Sabuwa tayi rayuwar wulaƙanci, ƙaskanci kuma ta hau layi. Duk da ko sanda take gidan naka sharar gidanka ta fita kima da daraja.
Sabuwa naci nasarar rabaki da yaranki da Babangida. Saura nasara ta gaba ɓalɓanta yaranki da kuma damejin ƙwaƙwalwar Mardiyya da sannu zata san cewar wannan gidan bana ubanta bane, ƙannenta ba nata bane, uban da take taƙamar itace babba a wajenshi ba nata bane."
Ƙaran wayar Babangida daya ajjiye a kujerane ya katse ma Ƴar Shuwa saƙarta da mugun zare wanda take ta saƙawa a zuchiyarta.
Ganin sunan Sumy yasa ranta ya ƙara yin matuƙar zafi. Agogo ta kalla ta girgiza kai.
"Lallai wannan yarinyar sai na saisaita mata hankalinta. Sha ɗaya da rabi na dare zata kira magidanci sabida iskanci bayan jibi za'a ɗaura auren ma"
Tana cikin surutanta Babangida ya shigo falon ɗaure da tawul a ƙugunshi. Shagala kawai tayo wajen kallonshi Allah ya jarabceta da wata iriyar soyayyar Babangida tun a haɗuwar farko da suka yi. Amman shima sai ya nufo wajen sabuwa kamar dai yadda Khalid yayi mata.
Kuma fa duk abinda shi babangidam zaiyi mata soyayyarshi rufe mata idanu take yi wannan itace ƙaddararta ta yadda. Domin daga lokacin da Babangida ya talauce ta gane Babangida ne ƙaddararta. Gashi shi yana da wasu matan bayan ita, dama karuwan da bata sansu ba na waje masu juya ƙwaƙwalen mazajen wasu abar matan gida da cizon yatsa. Ko tayi yinƙurin son barin gidan sai taji inta bar Babangida kamar rayuwarta tazo ƙarshe ne.
Har ya ƙaraso inda take bata sani ba ta yi zurfi a tunani.
Gira ya ɗaga mata.
"Bani wayata nasan Amaryace tayi kira."
"Amarya ko karuwarka ba. Ƴar iska ya za'ayi ta kiraka a irin wannan daren in ba ka nuna mata mu matan gidan bamu da wata daraja ba tama isa?"
Wayarshi ya fisge ya wuce daining ya zauna yana daddannawa.
Daidai Ƴar Shuwa ta karaso zata zuba mishi abinci ita kuma Sunmy ta dauki wayar.
"Hello Amaryar Babangida har yanzu baki yi bacci ba ko dai ɗokin gobe zanzo ne ya hanaki bacci?"
Wannan maganar a iyakar fatan bakinshi kawai ta tsaya ita kanta Sumy tayi mamakin furucinshi ballantana yar Shuwa da take tsaye tana ji tamkar ta danneshi ta karɓe wayar ta dankarata da ƙasa. Sai dai shi yaƙi ai ɗan zamba ne. Tananan tana jiran shigowar Sumy tayi alƙawarin saita raina kanta kuma bata isa ta wuceta a zuchiyar Babangida ba.
Murmushin takaici kawai tayi ta zuba mishi abincin ta ja kujera ta zauna tana fuskantarshi sonshi na cin ƙasan zuchiyarta kamar son Babangida zai halakata haka take ji. Gashi talaucinshi ya gama isarta Mamansu ma sai lokaci take bata na kaso auren, in ta yinƙura sai taji ina ba zata iya ba.
Mrs Bukhari
Tabb ko yaya zata kasance dasu Gaza masu zuwa ɗebo kaya oho
[8/22, 11:42 AM] BADA'AT IBRAHIM: https://chat.whatsapp.com/EEK9H2V5iSOFXz0Xud5Eox?mode=ac_t
Yar uwa ta, kin dade kina neman in da zaki samu nighties da lounge wears masu musulmin kyau, saukin farashi da kuma kyan gani? 😍 To ki daina nema! A thrift bae closet, mun bude exclusive group inda za a dinga kawo thrift nighties, lounge wears da sauran su masu kyau, kamar Sabbi kuma farashinsu abin mamaki ne, very affordable 🤩.
A nan ne za ki kasance cikin na farko da za su ga sababbin kaya kafin su kare. Idan kina son kada ki rasa mafi kyawun kaya kafin a sayar da su gaba ɗaya, to shiga cikin group ɗin yanzu kafin ya cika 👇
https://chat.whatsapp.com/EEK9H2V5iSOFXz0Xud5Eox?mode=ac_t
IDAN KAYA YA GAJI..
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA GOMA SHA BIYAR
Babangida har ya shige ciki, sai kuma ya fito ya zauna a falon.
Ta ɓangaren Sumy kuma cewa tayi.
"Goben yana nan dai a matsayin ranar da zaku tawo ɗin ko, sannan jibi nanan a matayin ranar ɗaurin auren ko? Ga gidanmu cike da ƴan uwa na nesa dana kusa. Babangida kada ka bani kunya kasan da sanin kai ka lalatamun rayuwa kuma kai ka ajjiyeni sai yadda kake so kake yi dani a hakanma ai ka karya ka'idar wata ukun da muka tsayar amman dai nayi maka uziri kaima ka sani."
Idanunshi ya lumshe ita ƴar Shuwa tana ganin tamkar lumshewar daɗine. A ɓangarenshi lumshe idanun da yayi na baƙin cikin rayuwarshi ta bayane da irin yadda sukaita gudanar da rayuwar wa jo ko shi da Sumy ya maisheta tamkar matarshi. A tunaninshi biredi zaici ya yaga leda irin tunanin da yayi akan Sabuwa sai gashi ledojin sunƙi su yagu miki.
Kusan matanshi saida ya sansu a waje ya gama ɗebe duk wata albarka ta jikinsu kafin ya aurosu. In aka ware ɗaiɗaiku wanda bashi ya sansu a farko ba suka yaudareshi da kamewarsu ashe suma tantiranne irinsu Hamida kenan. Ai lallai dama ance mazinaci baya auren kintsattsiyar mata sai mazinaciya irinshi. Face waɗanda ƙaddarace ta ja rayuwarsu zuwa ga mazinatan alhalin su basu san hanyar zina ba.
Yana tsoron a wayi gari ayi zina da yaranshi mata kamar yadda yaita zinace zinace da ƴaƴan mutane. Yana kuma tsoron yaranshi su auri miji irinshi a baya. Shi yasa yanzu yake hana kanshi bacci sosai yake tsayuwar dare, yawan sadaka, da yawaita azumin litinin da alhamis ko Allah zai yafe mishi kusakuranshi na baya.
"In sha ALLAH Sumy. Da mun taso zan kiraki in sanar miki mun kamo hanya. Sauran maganar in na iso ma karasheta ki kwanta kiyi baccinki Amaryar Babangida kaci gari daga ke ba ƙari an rufe ƙofa"
Ya ƙarashe maganar yana jin tamkar zuchiyarshi zata bulluƙo ta fito sabida ciwon da take yi mishi Lokaci guda idanunshi suka sauya daga farar zuwa jajaye.
Ƴar Shuwa ta shaƙa iyakar shaƙa ita a tunaninta iskancin nashi ne ya motsa jin muryar Sumy.
Miƙewa yayi yana shirin shigewa ciki
"Abincin fa?"
Juyowa yayi ya kalleta yama mance tana zaune a wajen.
"Bana jin cin komai Sabuwa In akwai madara ki bani tea kawai ya wadatar dani bakina babu daɗi. " Taji sarai da sunan Sabuwa ya kirata. Taji zafi mai yawa amman saita kanne.
Duk dai yadda Ƴar Shuwa taso hilatar Babangida su raya wannan daren ta mantar dashi damuwar da sabuwa ta saka shi a ciki abun yaci tura dan kusan a kan sallaya Babangida yayi bacci a lokacin tayi jiran har bacci ya ɗebeta.
Da asuba da zai tafi masallacine ya tasheta shi kuma ya fice.
Su Aminu ya shiga ya kira suka wuce masallaci.
Suna fitowa daga masallaci ɗakin Sabuwa ya shiga kai tsaye ga hotonta a kafe a bango. Gani yake yi kamar zata ɓullo ga ƙamshinta daram a ɗakin yanata shaƙa.
Bayan sun gaisa da yaran sai yace yau baza su je makaranta ba su shirya akwai biki a gidan ƴan Ringim ma zasu zo.
Mardiyya saita tashi tsam ta shige uwar ɗaki.
Kawai sai Babangida yaji ta bashi tausayi sai yabi bayanta. A kan gadon Sabuwa ya taddata tayi ruf da ciki tana kuka.
"Mardiyya" Ya ambaci sunan yarinyar. Amman abun mamaki sai taƙi kulashi dole ya tattaka ya shiga ya sameta.
"Kiyi haƙuri kina gani ba a san raina na rabu da umminku ba. Asalima alƙaline ya raba auren da kanshi. Amman ki sani inda rabo sai kiga Allah ya sake ƙaddara na zama mijin Sabuwa a karo na biyu. Ki dena kuka ki rungumi ƙannenki nima ina tare daku.
Abu na gaba da zance miki umarni na baki kada ki sake ɗaga wayar Sauban in da hali ki kulle layinshi ta yadda bazai iya samunki ba kinji ko?"
Kai ta ɗaga mishi tana shessheƙar kuka. Yaita rarrashinta dai
Tashi yayi ya fice danji yake kamar ya rungumeta su haɗu suyi kukan rashin Sabuwa.
Yana shiga banɗaki ya faɗa yayo wanka
Shida da rabi har ya gama shirinshi tsab sai ƙamshi yake yi. Kuɗin cefanen abincin ƴan biki ya ƙirgo ya ba Ƴar Shuwa da kuɗin girkin dangin Amarya. Sai ta nuna ita ba zata karɓi na dangin Amarya ba sai dai ya ba Ramatu.
"Hmm duk rashin kunyar Sabuwa inna sakata abu tana yi. Allah sarki Sabuwa mai bakin tsiwa alkhairin Allah ya isar miki a duk inda kike, haƙiƙa nayi rashi
Ni kam mun tafi sai mun dawo"
Har zai fita ta karɓi kuɗin cefanen girkin dangin Amaryar sabida yabon da yayi ma Sabuwa ya daketa ainun.
A gurguje yayi sallama da Ramatu sai fuskewa take yi dai. Su Aminu ma yayi musu sallama kai tsaye gidan Kawu manga ya wuce acan suka haɗu da abokanshi kusan mota huɗu suka yi. Biyu ta maza, biyu ta mata masu kai kayan akwati da ɗakko Amarya cikinsu harda Yar Malama Babba Yaya Hanne.
Ƙarfe takwas na safe suka ɗauki titi fetal zuwa jihar kogi. Basu suka isa garin ba sai ƙarfe shidan yamma, da taimakon waya da Babangida yaje ta faman yi da Sumy har suka ƙarasa gidan wan mahaifinta inda anan akai musu masauki.
A lokacin ne Babangida yasan Sumy yaren Ebura ce yasan dai tana da yare amman basu taɓa maganar yarenta ba tunda barikin zallah suka saka a gaba.
Da halama dai danginta talakawane sosai dan gidan wan mahaifin nata ma abun tausayi a shagon maza aka saukesu su Sa'a kuma akayi cikin gida dasu.
Duk sun gaji motocinsu dasu kansu sun wahala sosai, ba'a binsu ko wacce Sallah dan haka sai aka gabatar musu da abinci a matsayinsu na baƙi
Sakwara da miyar ɗanyen kifi wanda akafi sani da tarwaɗa masu harshen nasara kuma su kirashi ( cat fish) dashi aka tarbesu da kunun zaƙi na jar dawa mai sanyin gaske.
Ta ɓangaren tarban baƙi da karamci iyayen Sumy ba daga nan ba.
A cikin gidan ma su Sa'a sun samu tarba da girmamawa mai kyau kuma sun karɓi akwatunan da aka kawo cikin yabawa da adda'ar Allah yasa gidan zamanta ne. Sai yara yare akeyi hausa ma bata ishi da yawan dangin Sumy ba.
Sai da daddare Sumy ta samu keɓewa da Babangida da wata ƙawarta data rakota.
"Sumy naga kin sake yin kyau ko dai ƙyallin Aure ne?"
Cewar Babangida da yake da zuba lallausan murmushi na dolen doliya.
"To haka dai kace, ni fa saida aka tabbatar mun da isowarka kafin hankalina ya kwanta. Tunda nazo ban samu nutsuwa ba ga gulmammaki da aketa faman yi a kaina ta dalilin Amir. Wasu sun yadda ta hanyar Aure na same shi, wasu basu yadda ba har saida suka ji labarin zan koma gidan Babanshi sannan suka yadda"
Shiru yayi kawai yana tunanin yadda son zuchiyarsu yasa suka haifo yara bata hanyar Aure ba. Shin da wanne idanu yaran zasu kallesu a gaba in abun ya bayyana?
"Lafiya kake kuwa sai naga kayi rama kamar ma ba kaiba"
Muryar Sumy ta daki dodon kunnenshi.
Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba.
Mustapha ya ƙaraso inda suke da sallamarshi kamar gaske.
""Sumy babu ɗan wani Club ne haka a garinnan naku muje mu huce gajiyarmu. Ko ya kace tubabbe?"
Ya doki kafaɗar Babangida da sigar zolaya yayi tambayar.
Harara Babangida ya doka mishi.
"Wallahi kayi ma kanka karatun tanutsu Mustapha kaji tsoron Allah"
Dariya suka saka harda tafawa tamkar mata.
Yana dariyar yace.
"Zancan gaskiya mu kam a rakamu wani hotel mu kwana acan na fuskanci kamar bakwa samun wuta, ni kuma wallahi bazan iya kwana ba'a ƙarƙashin fanka ko Ac ba."
Sassauto muryarshi yayi yace.
"Sumy waccan ƙawar taki ta sha ce ko ta kaiwa kasuwa?"
Babangida ya haɗe rai yace.
"Wai meye haka Mustapha?"
"Ha'a to me nayi. Kasani ko a ɗaura auren tare da zata amince dan wallahi na samu wannan kayan zuwa koton ƙarfe yayi mun rana."
Da kallo Babangida ya bishi dan ya gasgata abinda yake faɗan da gaske ne. Ya tabbatar da gaske Mustapha yake yi dan ya sanshi ba sanin yanzu ba. Sumy tace.
"Ai kuwa da ace gaske kake zaka aureta sai mahaifinta yafi kowa farin ciki. Diyar wan Babanmu ce a gidansu aka sauke ku.
Ta girmeni gaskiya Allah dai bai fito mata da mijin bane kuma har digiri tayi. Ana dai zargin kishiyar Mamansu ce tayi musu asiri. Dan har yayyenta guda biyu mata ba su yi aure ba. Ba'a ma zuwa zance wajensu"
Mustapha yayi dariya yace.
"Kunsan Allah? To ni naga waje asirinnan fa ya karye. Sumy in mahaifin yarinyarnan ya yarda gobe a ɗaura aurenmu tare da naku, Kawu manga duk zai karɓa mana auren tuwona maina"
Ƙaramar magana wasa wasa sai ta zama gaske.
Da su Babangida suka tari Kawu Manga da zancan salati ya dinga yi kafin can yace.
"To shikenan kuje zamu tattauna da mahaifinta duk yadda ake ciki kwa ji koma menene. Sha'aninku ni tsoro yake bani Mustapha. Zan kuma yi waya da Baba na shago tukunna in ya amince Hajiyarka ta amince shikenan."
Mustapha ya samu damar keɓewa da Adeiza. Inda abun yazo mata kamar almara a guje ta amshi Mustapha hannu bibbiyu cike da mamaki ma.
Haka mahaifinta da labarin yazo mishi kamar bazata yaita murna yana gode ma Allah.
Hakanne kuwa ya faru washegari da misalin ƙarfe sha ɗayan rana aka ɗaura auren Sumy da Babangida, dana Mustapha da Adeiza a bisa sadaki dubu ɗari_ɗari.
Mahaifin Adeiza yayi ma Mustapha bayanin dama su a yarensu miji shi ke yin kayan ɗaki basa kai mace da komai. Ko Sumy ita dai ta haɗa kuɗaɗe tayi ma kanta kayan ɗaki tayi ƙaryar Babangida ya tura mata kuɗin yace ta siya. A cikin garin lokoja ta sai kayan ɗakinta na gani a kuma gani.
Mustapha yayi na'am da bayanin mahaifin sabuwar matar tashi.
Cikin minti talatin aka fito da Amare da ƴan tsakiyarsu da mota guda na kayan hatsi na gara suka ɗauki hanyar komawa Jigawa cikin ayarin motocin Amare.
SU ADAMA:.
Sassakkowa suka yi tare da karnukansu da sanduna a hannunsu sai muzurai suke yi.
Cikin ƙanƙanin lokaci yara yara da mata dake kan layi zasu unguwa wasu zasu makaranta babu shiri layin ya zama shiru duk sunyi tsit a cikin gida sai dai leƙe ta katangu.
"Ke Adama wuce gaba muje wallahi na samu Babangida saina daddatsashi ɗan abu ta kazan uba.. na daɗe da cikinshi ai kowa yasan ya azabtar da Lolo."
Maigogul yace.
"Gaza tunda dai an rabu na faɗa maka ka rabu da Babangida yafa yi ƙoƙari fiye da sauran surukai da akayi a baya kai harda wanda ma za'ayi a gaba"
Gaza ya buɗe baki yace.
"Au haka kake ma kanka fata? Duk irin Akuyancin da yayi maka kana fatan samun wanda ma ya fishi kenan? Gaka ga duniya Dattijo. Maza mujenku ciki duk wanda sukai muku ku saka musu sara wallahi ba wani shege "
Ɗu suka nufi ƙofar gidan bankaɗa get ɗin gidan sukai da mugun ƙarfi karnukansu ne suka soma shiga gidan.
Take matan gidan da ƴan biki da suka soma taruwa suka dare tsakar gidan ya zama sai fili da kwanukan wanke_wanke da kayan wanki, harda su kayan cefanen biki.
"Adama ku ku shiga, mazaje ku bisu kuje ni da Dattijo zamu tsaya anan kuje a ciro komai da komai. In ga uban da zai hana ku, har ƙwayayen wutar lantarki ku ciro kar kubar komai. Kayan abinci ma a kwashe kai komai a kwaso hatta shara muna son abunmu. Ko ba haka ba Maigogul?"
Gaza ya tambaya yana zaro wata shinfiɗediyar wuƙa mai zarto.
"Hakane a kwaso komai tunda uban Babangida ne yayo mata. Kuma yace ta kwashe abunta ai kaga bama bar musu ba"
Dariya kawai Gaza yayi ma Maigogul.
Haka su Adama sukaita fito da kaya Mardiyya kuma ta haɗe ƙannenta suka takure a waje ɗaya tana ta hawaye tana sauke ajjiyar zuchiya. Malama ce kawai bata kuka itama yarinta ke damunta amman dai ganin ƴan uwanta suna kuka ga kayan Umminsu anata fitarwa sai jikinta yayi sanyi ta rirriƙe ƴan uwanta gam.
Har aka gama loda komai da komai a mota babu wanda ya leƙo ga Gaza yasa karnuka sai haushi suke yi bisa umarninshi.
Ƴar Shuwa tana ciki da ƙannenta duk ta tsure bata samu kwanciyar hankali ba har saida taji shiru babu haushin karnukan halamun su Gaza sun bar unguwar kenan. Tsoronta Gaza tasan zai iya cewa a fito da'ita yayi mata abinda yaga dama tasan babu abinda zai faru.
Ajjiyar zuchiya ta sauke. Kawai taji an ɓallo ƙofarta Rahine na gaba Gaza na baya suka haɗa idanu da Ƴar Shuwa.
Wallahi sai ga fitsari sharshar yana bin ƙafarta.
"Ke Adama da Labbai ku shiga kui mata dukan shan gishiri. Ni eh in nace zan taɓata mutuwa zata yi wallahi."
Yana tsaye bakin ƙofar su Adama suka shiga suka rufe Ƴar Shuwa da dukan mutuwa Labbai kuwa fuskarta ta samu taita duka ta tara mata jini a idanunta bakinta kuwa leɓen ƙasa tsagewa yayi tsabar azaba.
Gaza yasa Rahine tayi fitsari a tsakar ɗakin suka kama hanya suka fice
Sai lokacin mutane suka samu sukuni. Fuska a kumbure aka wuce da Ƴar Shuwa asibiti. Saida akayi mata ɗinki a leɓenta, idanta ya tara jini ta ciki sosai. Cikin ƙanƙanin lokaci halittarta ta canja fuska da baki suka aune.
SABUWA:.
Ina tsakar gida muna magana da Rakiya muka jiyo tsayuwar motar su Gaza.
Rakiya inaga a siyar da ragowar kayan kawai. Katifa da sib kawai zan bari inaso mu sake ɗaki wancan dasu Adama suka kama yayi kaɗan gaskiya kinga wataran har su Sadiya suna zuwa mu kwana."
"To amman Lolo in kika sake samun wani mijin ayi yaya? Ke kinsan dai bamu yi miki a auren farko ba ba zamu yi miki a aure na biyu ba ko?
Duk da bamu da wajen ajjiye kayannan a dai zube su a tsakar gida muga yadda zata kaya. In kuma kince a siyar to"
A siyar kawai ko ɗan kunne na siya in maƙala a kunnena in auren yazo sai in siyar zaifi mun tunda dama ina da wasu"
Miƙewa Rakiya tayi ta zare mayafinta a igiyar shanya.
"Bari inje Lolo banci ta zama ba. Dillali zan kira yaima kayan kuɗin goro kawai a siyar. In yaso kayan kitchen ɗin mata sa zo su sissiya inaga hakan zaifi."
Ai kuwa hakan akayi dubu ɗari da saba'in aka sai kayan dukka banda katifa da sib amman har firizata babba na siyar da'ita. Ragowar kayan kitchen ɗina kusan Layuza ce ta sai rabi da kwatan kayan sai wani feleƙe take yi mun gashi kusan kullum tana gidan.
Mun bazama neman ɗaki ciki da falo cikin sa'a muka samu a farkon layinmu gidan Baban Anya. Sai lokacin muka samu sakewa mu huɗu ne da ɗakin zamu dinga haɗa kuɗi mu biya. Ko wacce dubu goma goma.
Haka lamura sukaita tafiya rayuwa tayi ta juyawa. In aka ɗauke tunanin Yaƴana da da matsalolin gidanmu da sai ince bani da damuwar komai jina nake tamkar sabuwar mutum.
Sai dai kash matsalolin gidanmu na yau daban na gobe daban. Gaza da matarshi sun sake lalata mana gidan da hayaniya sosai. Bamu muka samu sukuni ba har saida Gaza yaje ya rikito wani jarfan aka sake wucewa dashi gidan yari. Ita kuma Madamsy tace ba zata zauna yinwa da rashin gata ya kasheta a gidanmu ba zata tafi can garinsu ga ƙaramin ciki a jikinta. Maigogul yayi juyin duniya akan kada ta tafi ta zauna ta haife abinda ke cikinta amman sai wayar gari akayi babu madamsy babu dalilinta.
Gaga_gaga rayuwa ta tafi sosai.
Wata ranar asabar ina zaune akan katifa ina chart da Dr Kamilu. Su Adama kuma sunata zancan bikinta gobe da yardar Allah za'a ɗaura aurenta zamu je mu kaita can Malam madori. Har munje mun yi jere babu laifi komai sabo Adama ta siya sabida Alhajinta ya sake mata aljihu babu laifi. Itace ta huɗu ga tarin yara a gidan maza da mata gidan dai gaskiya gidan yawane har surukan Adaman suna cikin gidan.
Da ganin irin tarbar da akayi mana ya nuna mana suna adawa sosai da auren babu wanda yake maraba da zuwan Adama, gashi garin ƙauye ne duk da dai babu laifi suna da wayewa akwai makarantu kuma akwai ruwa da wuta. Kuma in aka duba baya sai dai muce ya fima Adama sau dubu ɗari.
Sai dai fa abincin gidan na gandu ne miyar gidan babu komai a cikinta face daddawa da gishiri. Muma masu jere dashi dai aka taremu da farau_farau. Babu suturun arziki a jikin matan Alhaji da ma su yaran gidan. Amman gaskiya gidan yana da kyau, kuma ɗakunan matan tubarkallah, a haka dai gobe za'a rurrufa akai Adama ta zauna a haka ta dage da adda'a shi ɗinma da yaya akayi har bikin yazo. Sai da Maigogul yaita yawo da'ita wajajen masu magani ana mishi kiranye kafin yazo dan abun yafi ƙarfin Maigogul, sai da aka rufe bakin mahaifiyarshi ma kafin itama ta amince.
Wayata ce tayi ruri Khalid ke kirana ikon Allah ko dai yasan aurena ya mutu ne? Na ayyana hakan a raina tare da ɗaga wayar tashi.
Ajjiyar zuchiya ya sauke wanda saida duk wata tsiga ta jikina ta tashi.
"Sabuwa gani a ƙofar gidanku ki fito in saka ki a idanuna dan ALLAH ko zuchiyata zata samu nutsuwa"
Idanuna na lumshe da muryar jan hankali yake maganar irin ta mayunwacin zakin daya ga akuya"
Wanne gidan namu kake kofar shi Khalid?"
Murmushinsa yayi mun kafin yace.
"Ki gafarceni ƙofar gidan aurenki. Wallahi Sabuwa mafarkinki ne ya dameni dan ALLAH ki fito ni ko hannunki in riƙe"
Hmm Khalid ka karya alƙawari amman.."
"E naji amman a soyayya ai akwai afuwa ko Babyn Khalid shi kaɗai har abada?"
Ɗan murmushi nayi kawai.
To ai shikenan kazo gidanmu can ka sameni"
Ajjiyar zuchiya ya sauke.
"An gama ranki shi daɗe gani nan zuwa. Saima na biya na siyo miki nono mai sanyi nasan kina so. Ko in bari in nazo sai muje mu siyo tare Baby, kinga daga nan ma ehh..."
Ɗan saurayin dariya muka yi dukkanmu ni dai kashe wayata kawai nayi. Ina girgiza kaina. Khalid duk bala'inshi a wannan karon bazai taɓa ribatata ba, ko dan in kiyaye martabar yarana.
"Lolo mai lallen har yanzu bata fa zo ba inaga ke da Labbai ku leƙota dan ALLAH "
Cewar Adama da take jin ta matsu kamar ta jawo gobe haka take ji.
Ga dahuwar tattabara ta tusa gaba sai haƙa take yi tana haɗawa da wasu irin tsumi da ƙawarta ta dafo mata.
To Labbai muje mu dubo ta."
Kafin mu yinƙura ma sai gata ta shigo da sallamarta.
Yauwa kinga yanzu dama zamu je mu ɗakkoki kamar Amarya. Amman dan ALLAH Adama a soma yi mun kinga nawa babu yawa ke ko Amaryace sai afi awa nawa ana yarfa miki"
Hararata Adama tayi tace.
"Lallai yama za'ayi kice a soma yi miki. Ku bari ta gama dani ga kitso za'ayi mun kuma zanje gidan Ladidi zamu je karɓo ɗinkinmu a shagon tela, ga ƴan ragowar siyayyan ƙananun abubbuwa da ban ƙarashe ba."
Baki na taɓe nayi kwanciyata.
Uzairu zuchiyata muka jiyo muryarshi kusan tun daga waje yanata rakaɗo mun shegen kira.
Da sauri na fito tsakar gidan daidai shigowar Matar Sama da cikinta a gaba.
Ahh Rita kin ƙaraso kenan, ina shi Sama ɗin?"
Murmushi tayi da kwaɓaɓɓiyar hausarta tace.
"Baya nan yana Lagos ya tafi neman kuɗi. Ko waya ma Bama yi"
Nii tausayi ta bani Allah yasa ba gidoga yayi mata ba. Kai gidogarce ma indai Sama ne.
Ban kai ga bata amsa ba Uzairu Zuchiyata ya shigo ya finciki hannuna muka fice a guje.
Bai saki hannuna ba sai a filin ɗakin Rakiya.
Rakiya na tsintar shinkafa Maigogul yana gaban madubi yanata shafa hoda.
"Lafiya zaku shigo da gudu kamar wasu ƙawayen Amarya menene hakan, ko wani sabon salon iskancinne zaku faɗo mun kai"
Maigogul dake gyara zaman gogul ɗinshi yace
"Kash Rakiya kin fiye faɗa wallahi. Daga shigowarsu kin taresu da balbalin masifa. Kai Zuchiyata menene, Lolo yaya akayi ko dai sabon bazawari kika samu ne?"
Salati Rakiya ta rabka tace.
"Da iddar a kanta kake mata maganar sabon bazawari?'
Baki ya taɓe kawai. " Iddar ba saura kwana uku ta ƙare ba to kuma menene?
"Maigogul ƙwallonane ya shiga raga. Shekara da shekaru sai yanzu Allah ya cika mun burina. Mata na samu a ƙasar Canada. Mahaifinta ne ya buƙaci ganina domin su sanni sai a tsayar da maganar aurenmu."
Miƙewa Rakiya tayi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 19