Share this page
tana murna. "Ƙasar waje fa kace Uzairu Zuchiyata ko dai ƙaryar daka saba ma Ƴan mata a waya muma ita zaka mana?" "A_a wallahi Rakiya kinga Felisha ma ta buƙaci in tawo da ƙanwata Lolo dake ita kaɗai na taɓa haɗata suka gaisa. Yanzu bazama zanyi nemo masu dola account za'a turo mun kuɗin paspo nawa dana Lolo. Zasu nema mana takaddar yardar shiga ƙasan. In suka turo mana zasu biya mana kuɗin jirgi sai Canada. Lolo gobe sassafe zamu je Kano ayi mana paspo na fita ƙasar waje da zaran bizarmu ta fito zamu wuce. In muka je ma Kanon ma san yadda za'ayi kuɗin a turo. Muna cikin alkhairi dumu dumu" Nan Maigogul ya shiga murna har yana cewa. "Kash Uzairu Zuchiyata ni dai da ka bar Lolo mun tafi tare ayi duk wacce za'ayi gemu da gemu inta kama ma sai a ɗaura auren kawai. Canada fa kabar Lolo kawai gobe muje Kano ayi mana paspo. Su gobe a Malam madori ma zasu kwana." Rakiya tace ina wuta ta saka Maigogul. "Maigogul kwantar da hankalinka zaka Canada acan za'a ɗaura auren dole da kai za'aje. Yanzu shirye_shryen bikin kawai za'ayi kuma ita Felisha ta ganni ido da ido. Sauran batun zai biyo baya." "To shikenan Amman dole ko kwalli ko turare in sama maka ka shafa sabida soyayyar tayi ƙarko Canada ba wasa ba Uzairu Zuchiyata. Lallai kai ka gajeni a fagen farin jinin mata masu kuɗi ƙaddarace tasa na auri mata faƙarahu alal lalurati ka gansu dai. Dama_ dama ma ita Uwar taku. Kiran da Khalid yaimun ne yasa na fita a ɗakin. Hauwa nagani a laɓe a bakin ƙofarmu ta kasa kunne tana sauraren abinda muke cewa. Kai kawai na kaɗa ina hasaso irin tashin hankalin da zai afku da ace Rakiya ce ta fito ta samu Hauwa a tsaye tana mata laɓe. Baki na taɓe nayi ficewata ina fita muka haɗa idanu da Khalid wanda ya ƙurama cikin gidanmu idanu ko ƙibtawa bayayi. Shiga gaban motar nayi sanyi da ƙamshinshi na asali suka bigeni. BABANGIDA:. Basu suka iso jigawa ba sai da daddare sosai sau biyu mota na lalace musu a hanya abinda yasa sukai dare sosai kenan. Ƴan Rakiyan rabuwa biyu suka yi rabi suka bi Amaryar Mustapha, rabi suka biyo su Sumy gidanta. Duk da cewar darene bai hana danginta sakin guɗa ba. Ƴar Shuwa dake manne a jikin taga ta leƙo tana ƙwafa ga baki da fuska a aune. Ƙur tabi takun amarya da idanunta tana share hawayen baƙin kishi dake zubo mata gashi ko ina ciwo yake yi mata a jikinta tafa daku iyaka. A kujerar falonta ta dawo ta kwanta. Yau Babangida zai shigo gobe ne taji shiru bai shigo ba, tasan ba kwananta bane a tunaninta zai leƙo ya sanar mata dawowar tashi. "Lallai dole saina miƙe zan iya kwasan ƴancina a gidannan. Babangida bansan wanne irin mayen mata bane a rashin kuɗinma saida ya ƙaro aure kuma fa in yaga dama sai yace zai cike gurbin Sabuwa ko?" Murmushi tayi tace. "Duk yadda zanji zafi ba kamar in Sabuwa bace akace yau ta dawo sunci gaba da aure da Babangida ba. Amman wannan ɗin nasan da wacce tazo tunda naga ko a waya kulawa ta musamman yake bata. Kuma tana iya kiranshi a duk sanda taso ta kirashi. MRS BUKHARI Ina ƴan rakiya zuwa Canada suke a soma rubuta sunayen masu zuwa biki Su Lolo za'aje Canada [8/23, 2:29 PM] BADA'AT IBRAHIM: https://chat.whatsapp.com/EEK9H2V5iSOFXz0Xud5Eox?mode=ac_t Yar uwa ta, kin dade kina neman in da zaki samu nighties da lounge wears masu musulmin kyau, saukin farashi da kuma kyan gani? 😍 To ki daina nema! A thrift bae closet, mun bude exclusive group inda za a dinga kawo thrift nighties, lounge wears da sauran su masu kyau, kamar Sabbi kuma farashinsu abin mamaki ne, very affordable 🤩. A nan ne za ki kasance cikin na farko da za su ga sababbin kaya kafin su kare. Idan kina son kada ki rasa mafi kyawun kaya kafin a sayar da su gaba ɗaya, to shiga cikin group ɗin yanzu kafin ya cika 👇 https://chat.whatsapp.com/EEK9H2V5iSOFXz0Xud5Eox?mode=ac_t IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA GOMA SHA SHIDA BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI Haka Ƴar Shuwa taci gaba da tubkewa tana warwarewa zuchiyarta sam babu daɗi. Tasan kamun Allah ne yasa soyayya Babangida tayi mata matuƙar yawa a zuchiyarta har take jin in ya rabu da'ita tamkar bama zata iya rayuwa ba. Da ba dan hakan ba wallahi da ko yaƙi Allah saiya bata takaddarta tuni. Babangida:. Tunda dai ya sallami abokanshi, ya sallami Amarya da danginta da su tsire da lemukan kwalba. Sai ya nufi ɗakin Sabuwa.yana tura ƙofar ya shiga kanshi ya juya mishi sosai ganin babu ko tsinke a ɗakin sai bargo da yaran suke kwance dukkansu kawai. Duk sunyi bacci yaran banda Mardiyya da idanunta biyu idanuwanta sunyi jawut halamun taci kuka irin na fitar hayyaciinnan. Tsugunnawa yayi a kusa dasu ya rasa abinda zaice yayi shiru na tsawon lokaci masu yawan gaske. Ga wayarta Sauban yanata kira biyayya irin nata taƙi ɗaga wayar, da idanu Babangida ya kalli wayar kawai. Sai can yace da Mardiyya. "Sabuwa da kanta tazo ta ɗebe kayanta shine ta kasa bar muku katifa?" Ajjiyar zuchiya na tashin hankali ya sauke ya sake ja ya sauke. "Ba ita tazo ta kwashe kaya ba su Maigogul ne suka zo dasu Gaza" Ƙur yabi Mardiyya da idanunshi tausayinta ya kamashi sabida itace babba yanzu hankalinshi ya dawo kanta ne baki ɗaya burinshi ya kawar da'ita a gabanshi kawai amman rayuwa mai kyau da inganci yake nema mata ba Auren Sauban da Sa'a zata ta cusguna mata ba. "Shikenan kuyi haƙuri ku kwana a hakan gobe in Allah ya kaimu zan siyo muku gado da katifa. Mardiyya kece babba ki kula da ƙannenki kinji? Sannan kada ki ɗaga wayar Sauban na riga dana rabaku, akwai abinda nake so in zaunar dake mu tattauna ɗiyata. Akwai abinda kuke so ne?" Miƙewa zaune tayi ta gyara zamanta da kyau. "E Baba mu dai so muke zan dinga mana girkinmu daban ba sai mun jira kowa ba dan Allah Baba" Wallahi Babangida sai yaji hawaye na zubo mishi tsabaragen rauni. "Bayan wannan kuma me kike so Mardiyya dan Allah kiyi gaggawar sanar dani zan sama muku shi" Ya ambata a ƙagauce cikin zabarin son jin me take so kuma. "Shikenan Baba, kuma muna so duk juma'a tunda babu islamiyya mu dinga zuwa wajen Ummi muna dubata. Baba ba daɗewa zamu yi ba. Inma kaine zaka dinga kaimu ka jiramu duk babu damuwa" "To shikenan zan duba in gani. Bawai bana son kuje inda Umminku take bane, gidanne kawai bana son kuna yawan zuwa. Amman zan ƙoƙarta ko sau ɗaya a watane zan dinga kaiku." Da wannan matsayar suka tsaya. A ɗakin Ramatu yaje ya kwanta, amman tunanin Cus da baƙin rashin kunyarta wanda a yanzu yake jin dama zata dawo tazo tai ta yi mishi fitsarar idanu zai zuba yaita kallonta tana ƙara burgeshi ya hanashi bacci Washegari gida ya kaure da yinin biki, shi kuma ya tsallake gidan ya siyo ma su Mardiyya gado da katifa, sai katifa tasu Adda'u. A wajen Mustapha ya amshi kuɗin bashi, duk da Mustapha ya sanar mishi babu bashi tsakaninsu amman shi ya kafe kan saiya dawo mishi dashi. Yana isowa yaga Sauban da Mardiyya a ƙofar gida Sa'a tana dukan Sauban tana zaginshi daidai isowar Babangida. Ranshi ya kai iyakar sosuwa murmushi mai ciwo yayi kawai ya sakko a gaban motar kaya. Sa'a na ganinshi ta shige gida Babangida ya ƙaraso ya dafa kafaɗar Sauban. Mardiyya dake kuka ya kalla. "Ki shiga gida Mardiyya kada ki sake kuka" "To Baba" Juyawa tayi ta shige, Babangida yabi takun yarinyar da kallo har saida ta kule ya dubi Sauban. "Sauban kayi haƙuri Mardiyya Ɗiyata ce, kai kuma Sa'a ce mahaifiyarka. Tunda dai ta nace bata sonka da Mardiyya kayi haƙuri Allah zai ɓullo mata da wanda zai sota a yadda taken wani bare can. Yarinya bai kamata a hukuntata da laifin iyayenta ba. Shin Sa'a ta taɓa faɗa maka wani abunne dangane da dalilin da yasa za'a haɗa Auren naku?" "A_a Kawu na sha tambayarta ma dalili amman bata faɗa mun. Amman Kawu ni koma menene inason in auri Mardiyya kuma mahaifina ma ya amince. Kawu dan girman Allah kada ka rabamu. Jiya yadda naga rana haka naga dare, yanzu haka zazzaɓine a jikina, a duba lamarinnan kawu" Murmushin gefen baki Babangida yayi. "Sauban kenan. Kayi haƙuri dai wannan auren bazai yiwu ba. Ina mai baka umarnin kada ka sake zuwa wajen Mardiyya kuma kada ka sake nemanta a waya ka barta zuchiyarta ta warke, ka yarda ta manta dakai, kaima ka daure ka mance da'ita kada akan ku ku biyu zumunci ya ruguje" Hannunshi ya sauke a kafaɗar Sauban ɗin. Da haka Sauban ya ɗauke ƙafa a rayuwar Mardiyya sai dai fa ya ƙudurce a ranshi shi da aure har abada bazai yi ba in dai ba Mardiyya aka aura mishi ba. Haka yaita jinya a tsaitsaye yaro duk ya zauce ya fita kamanninshi fa. Ango Babangida dai haka ya kwana a ɗakin amarya ga ɗansu a falo Amir abun dai babu armashi amman ya riga daya rungumi ƙaddararshi kawai. Kuma yaji canji akan da sosai. Ko da su Sa'a suka ga Amir tabbas sunce kamarshi sak da mardiyya kamar kwabo da kwabo. Amman tunaninsu bai basu cewar Ɗan na Babangida bane. Sabida sun san wannan kamar ana iya samunta ko da ba'a ma taɓa ganin juna ba. Magungunan mata da Sumy tai ta dibga sunyu aiki sosai a jikinta. Washegari ya haɗa kan matanshi a ɗakin Ƴar Shuwa tunda itace babba. Tayi farin cikin girman data samu amman tana kishi da Sumy sosai musamman yadda taga Babangida na wani kallonta. Gata Ƴar duma duma da'ita fatarta akwai kyau da gani zata yi laushi sosai. Baki ta taɓe daya faɗa musu ɗanta zai zauna a hannunta. Haka dai ya tsara yadda za'a dinga girki da karɓa_karɓan kwana a tsakaninsu. Rayuwar dai taita shurawa aiyuka sukaima Babangida yawa sosai dan yana koyarwa a makarantu fin uku. Kuɗi yake tarawa yana so in Allah ya dafa mishi zai koma sana'ar Baban bola irin na unguwa da ake kawo musu suke siya, in sun tara kamfani tazo ta kwashe. Tsakanin Ƴar Shuwa da Sumy kuma ana buga kishi da kirsa na ƙin ƙarawa sosai Sumy suke zaman gugar jigida da Yar Shuwa abin duniya yabi ya damu Ƴar Shuwa sosai. Ramatu kuwa tana gefe dan wannan faɗa yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba, basa ma ta tata sam. Duk juma'ar ƙarshen wata yana kwasar yara ya kai gidansu Sabuwa. Amman gudun fitina sai dai ya jira su Mardiyya a bakin layin su Sabuwa ya basu awa ɗaya suje a gaggaisa sai su fito ya maidasu gida Allah baisa ya taɓa ganin Sabuwa ba tunda dai ta bar gidanshi. Adama ko Labbai dai su suke rako yaran wajenshi. Gaga_gaga haka rayuwa taita garawa har zuwa tsawon wani lokaci. Yana tsaye a bakin mudubi yana gyara tsayuwar hularshi Ƴar Shuwa ta shigo ta sameshi ya buga shadda mai ruwan toka. Wani ƙududun baƙin kishine ya turniƙeta ta tsani juma'ar ƙarshen wata kamar yadda ta tsanii mutuwarta sabida tasan Babangida sabida Sabuwa yake son zuwan. Amman in ba haka ba ai yaran sun san hanyar zuwa gidan ya barsu su tafi da kansu mana. A duk lokacin da zaije kaisu kwalkiya ta musamman yake yi. Duk da ta baza ƙannenta suna mata c i d kuma sun tabbatar mata Babangida baya haurowa layin shine ma ta ɗan samu sassauci amman fa ba sosai ba tunda tasan gurbin Sabuwa yananan. Kuma wani faɗa da suka yi duk kishinta sai da ta roƙeshi ya cikace mata huɗu ya kulle ƙofa ita zata fi samun nutsuwa. A wannan faɗanne yace da'ita har gaba da abada gurbin Sabuwa zaici gaba da kasancewa dan bai cire ranshi da dawowarta ɗakinta ba. "Lafiya wannan irin kallo kamar zaki hadiyeni. Tunanin me kike yi haka inata magana shiru?" Cewar Babangida dake magana da yar Shuwa yana fesa turare. "Hmm naga sai sake gyara zaman hula kake ta faman yi tun tuni sabida zaka je gidansu tsohuwar matarka. Ai na riga dana bugo jirginka duk wannan kwalliyar sabida ita kake yi. Wai ni Babangida zawarcin Sabuwa kake yi ne ko?" Murmushin cusa haushin daya saba shi ɗin dai ya kuma yi kafin tace. "Me kika gani?" Yayi tambayarne sabida yaji abinda zata ce. Yana mamakin yadda tafi kishin Sabuwa fiye da sauran kishiyoyinta. "Sabida naga yadda kake ɗaukar wanka da aro motar abokai in zaka je wajenta abun yayi yawa. Sannan tunda dai Sabuwa taso rabuwa dakai ta makaka a kotu ka dena baccin kirki kullum kana Sallah. Da alƙali ya saketa sai ka sake ƙaimi wajen sallarka ta dare ni shine na kasa gane maka. Wai dama Sabuwa kana sonta duk abinda kaita mata a rayuwa har saida ka kaita maƙura?" Murmushi yayi kafin yace. "Ina mamakin yadda kika tsani aminiyarki sabida ni. Da gaske na ɗauka ni'imar da ƙawarki take ciki kaɗai kika biyo. Sai daga baya na fahimci da wata manufar taki ta daban kika shigo ni tsanine kawai. Kina bani mamaki in kina kishi da Sabuwa. Sabuwa da kike gani mun rabu ne bamu rabuba wallahi. Zauna kina nan zaki ji ana guɗar shigo da'ita cikin gidannan a karo na biyu. Dan tuni ciniki ya faɗa" Yayi hakanbe danya haɗa zuchiyarta da aiki na wuni guda, tunda yasan shi sakine mara kome itace jahila bata sani ba. Ficewa yayi daga uwarɗakin zuwa falo. A guje ta sha gabanshi a kiɗime. "Wai dan Allah Sabuwa zaka sake kwaso mana duk rashin tarbiyyar dake tattare a gidansu?" Ranshi ya sosu da abinda tace akan Sabuwa har fara'ar da yake yi saida ta ɗauke. "Da gidansu Sabuwa da gidanki duk ɗaya nake kallonsu. Ki ƙaddara gidanku yafi nasu tarbiyya amman ai kema tarbiyya Maigogul ne tunda a cikin gidan kikai rayuwarki. Ashe ke butulu ce Yar Shuwa har haka. Waime Sabuwa ta tsare miki ne haka? Wallahi Sabuwa ko yanzu tayi miki fintinkau, ta tafi data tashi tafiya saita warce zuchiyata tayi tafiyarta dashi. Aisha babu komai a ƙirjina Sabuwa ta tafi da komai, kuma bazan iya karɓowa ba. " Yana isada maganarshi ya ajjiye kuɗin cefane akan kujera. "Sakwara da miyar kifi za'aci yau a gidan. Sannan kada ki cika ma doyar ruwa sakwara in ba Sabuwa ce tayi ba bana gane kanta duk saita sake. Ko ita zaki kira a waya ta taimaka ta faɗa miki yadda take yi ne?" Ya ƙarashe zancan yana dariya ya barta a wajen zuchiyarta kamar zata toye dan ƙuna. Su Mardiyya kuma Babansu na fitowa suma suka fito ko wanne cikinsu zuchiyarshi cike da murna. Mota suka shiga Babangida ya ja motarshi fu. Wayarshi ce tayi ruri Sumy ke kiranshi amman bai ɗaga ba dan tun da dai ta fahimci Babangida ta ƙare mishi bashi da komai saita buɗe faifayin rashin mutuncinta gashi tazo a lokacin da rashin Sabuwa ya ladabtar dashi da kuma alƙawarin daya ɗaukarma kanshi in ba dai da wani ya kama matarshi ba, ko kuma tayi yinƙurin kasheshi ba. To babu batun saki haka su ukunnan zasu ci gaba da zama har mai rabawa ta raba su. Suna isowa bakin layin ya hango motar Khalid a ƙofar gidan. Tabbas ya shaida motar sarai. A madadin ya tsaya saiya kunna kan motarshi zuwa cikin layin. Kafin ya ƙaraso ya hango Sabuwa ta shige motar Khalid. Wani yawu mai ɗaci ya haɗiye take jijiyoyin kanshi sukai raɗa_raɗa. A bayan motar yayi parking. Yana ta ambaton Allah dan har wani duhu_ duhu idanunshi suke yi. "Mardiyya ku shiga gidan ku gaisa da kowa ku fito mu wuce" Yadda yayi maganar kaɗai yasa kowa ya shiga taitayinshi kawai. "To Baba" Kaɗai Mardiyya ta iya cewa ta tusa ƙannenta a gaba. Yana yinƙurin fitowane ya hango mahaifiyar Ƴar Shuwa ta leƙo tana waige_waige ga waya a manne a kunnenta. Jikinshi ne ya bashi Ƴar Shuwa ce duk yadda akayi tasa a leƙoshi a gani..zuchiyarshi na tafasa Allah _Allah yake yi ya fito yaje ya samu Khalid ya fesar musu da maganganun da suka daɗe a zuchiyarshi. Bai jira komawar Maman Ƴar Shuwa ba ya fito ya tunkari motar tasu. SABUWA:. Ƙur mukaima juna ni da Khalid. Wallahi har ga Allah har kuma a cikin raina inason Khalid. Sai dai matsala guda biyu. Na farko rayuwar da muka gudanar a baya. Na biyu rayuwar da muke gudanarwa a yanzu tun da aurena a kaina. Inna Auri Khalid banyi ma kaina adalci ba. Kuma duk bala'in sona da yake yi bazai hanashi zargina ba. Kuma zai iya fin Babangida rashin ganin darajata da kimata. Zan iya komawa gidan da yafi na jiya. Ai ina ganin zai fi mun sauƙi in Auri mutumin da wani abun bai taɓa shiga tsakaninmu ba. Duk da wannan shine abu mai wuya duk wani ɗan mutunci bazai zo neman aurenmu yazo ɗaya biyu ƴan unguwarnan su barshi yazo na uku ba. Ina tunanin irin su Khalid sune daidai da irin rayuwarmu. Ya Allah ka kawo mun ɗauki amman dai irin rayuwar da nayi a baya har abada bazan koma ba, ya Allah kayi riƙo da hannayena. Hannuna da Khalid ya riƙe gam ne yasa na buɗe idanuna muka ƙurama juna idanu. "Sabuwa naga kinyi ƙiba kin sake yin haske. Da ganin yanayinki kamar kin samu ƴar nutsuwa. Na buɗe baki zan yi magana tare da yinƙurin fisge hannuna kenan saina ga Babangida ya zuro kanshi cikin motar ta ɓangaren da Khalid yake. Da sauri Khalid ya waiga jin hucin mutum a gefenshi. Idanu suka haɗa da Babangida idanunshi sunyi jawur jijiyoyi duk sun tattaso a fuskarshi. Da sauri Khalid ya saki hannuna ya haɗe ranshi shima. "Kai a tunaninka kaci nasara ka rabani da Sabuwa ko? Hmmm ka sani duk wanda yayi guga da nufin zai ɗebi duniya ko ya jawo bazai ga komai ba. Ka neme ta da aurena a kanta ma balle yanzu da saura kwana uku ta gama idda. Ke kuma kin kyauta dama halinki ne. Abu ɗaya nake son sanar muku wallahi _wallahi wannan mitsiyacin bai isa ya aureki ba. Yadda na rasa shima sai dai ya rasa. Sannan in dai irin hannun wannan ƙazamin kike son komawa ai kinyi gwari kuma kinci baya. Mutumin daya nemeki yake kwanciya dake, ya kai ki hotel_hotel shine harda yo miki tsarabar rigar mama da ɗan kamfai, da sigari da aure a kanki shine kike tunanin gidanshi zaki koma kuma ki samu nutsuwa, shi kike tunanin ki aura Sabuwa?" Murmushi yayi mun idanunshi tamkar zasu zubo da ruwan hawayen da suka taru yace. "Kinyi gwari Cus kinyi gwari Cus. Ajjiyeki zaiyi a gida yaita zarginki, kuma ba zaki taɓa burgeshiba neman matanshi zaici gaba dayi ya lalata miki rayuwarki a banza daga ƙarshe hawan jinin dana ɗaura miki ya kasheki a banza. Dake ke jahila ce ai lissafinki bazai kawo mik..." Ya isheka nace Babangida ka sani kai ba ubana bane. Kuma na yarda na gamsu zam auri Khalid ko dan in ƙunsa maka baƙin cikin da zai yi ajalinka ko yayo maka sanadin kamuwa da cuta marar warkewa kamar dai yadda ka haddasa mun hawan jini. Yaya kuke so in saka kainane" "Rufa mun baki ko in bubbuge bakin naki wallahi " Ya ɗaga hannu Khalid ya cabke. "Sanda take gidanka ma..." Fisge hannunshi Babangida yayi ya shaƙe wuyan Khalid da mugun ƙarfin da Khalid ya kasa ƙwatar kanshi. Fitowar yaran da Maigogul ne yasa ya sake wuyan Khalid. Da sauri na fito a motar yaran suka nufo ni. Maigogul kuma ya nufo wajen Khalid har jikinshi na rawa. Sororo Babangida yayi yana kallon yadda Maigogul yake ɓare_ɓaren son karasawa wajen Khalid har yatsu Maigogul ya take mishi. "Ummi ashe kina waje. Ina wuni?" Cewar Mardiyya da take kallona cike da fara'a. Ina nan ai banga shigowarku bane shi yasa. To ya karatun? Aminu, Yaya Aɗɗa'u yaya rashin ji? Malama yaya rashin son magani." Babangida yace. "Ku dallah ku tawo muje ni na gaji" Jin yadda yayi maganar da zafine yasa yaran sukai saurin juyawa. Da harara ya bini kawai ya tusasu a gaba suka wuce. Maigogul yana wajen Khalid yana zubar da mutunci. "Ke Lolo tawo mana me kike yi a tsaye da yara ki barsu su tafiyarsu" Yana juyowa yaga ni kaɗaice a tsaye. "Au ashe sunma tafi ai dai yafi. Kinyi baƙo maimakon kiyi ciki dashi a_a sale_salin ƴan unguwa su ganku aje a tareshi ai mishi munafurci. Ki kaishi can gidanku " Wani ƙududun baƙin cikine yasa nace. Ai mun gama Maigogul." Ina faɗin haka nayi shigewata ciki na barshi da Khalid ɗin. Ya suka ƙare oho ya dai shigo ya nemi gefen gado ya zauna yana dandalan yawu yana ƙirga kuɗi. Rakiya sai harara take zabga mishi. "Wai Sabuwa shi wannan ɗin da dai batun aure yazi dai ko? Naga akwai gari a hannunshi ni dai na shaida mishi nanda kwana huɗu ma ya turo magabatanshi" A_a Maigogul wallahi ni ba aurenshi zanyi ba. Gaskiya karma ka karbi kuɗinsu Rakiya ki saka baki fa a wannan karon ba yadda zanyi ba wallahi. Yaushe ma na gama warkewa akan ciwon baƙin cikin Babangida " Takalmi ya jefo mun nayi maza na rufe fuskata. "Mara kunyar kawai ni zaki ma baƙin ciki dan abu ta kazan...." Miƙewa nayi da sauri zan gudu yako yi nasara ya tare ƙofa. "Yau ga tsiya da wasali ƙasa. Wai meye haka ne Maigogul karyata zaka yi ne ko me?" Yana huci ga takalmi a hannunshi yace. "Kinga wata shirgegiyar mota ce fa tazo wajenta Rakiya baki ga wanda yake cikin motar ba yaro matashi mai tsabta. Ga kuɗi yanzu wannan kuɗin da kika ga ina kirgawa duk shi ya dunƙulo ya bani har jikinshi fa yana rawa. Dama meye dalilin da yasa muka nace ta zauna a gidan wancan fitsararren tambaɗaɗɗen yaron ba sabida arzikin da take ciki bane? To kuma yanzu Allah ya aiko mata da wani shine zata ce bataso. Ga yayyenta da ƙannenta babu ma mai shinshinarsu in banda Adama da gobe za'a ɗaura aurenta. Tana gani nine kwana a buzu ina buga ƙasa hakan baiyi ba har saida muka bi ƴan tsubbu kafin auren ya kusan tabbata zamu ce. Shine wannan yarinyar zata mun haka? Rakiya ƙyaleni da'ita nace" Tare suka haɗu sukaita zagina Rakiya ta rufeni da duka Hauwa ce tazo ta fincikeni. "Ke Hauwa babu ruwanki ki bari Rakiya ta ladabtar mana da'ita kaga ƴar baƙin ciki"? Ficewa nayi a gidan ina haki na koma can gidanmu. Ina shiga Khalid ya kira wayata a zaure na tsaya na amsa wayarshi. "Sabuwa ashe aurenki ya mutu shine kika kasa sanar dani, ko dai kina sha'awar komawa gidan mijinki ne ni ina can ina haukana a kanki?" Ajjiyar zuchiya na sauke. Na samu damar saisaita kaina dan na fahimci in banyi ma Khalid dabara ba wallahi sai dai inji labarin an ɗaura mana aure. Harga Allah bana fatan sake faɗawa matsala. Maganganun Babangida sun sake farkar dani ainun. Ba haka bane. Dama ni niyyata shine inna kammala iddata sai in neme ka." Murmushi yayi mun yace. "Burinmu ashe ya kusan ciki Sabuwa. Ɓarayinki yananan a rufe madam ɗina ma tuni na faɗa mata aure zanyi in saka matar a wannan wajen". Murmushi nima nayi mishi tare da cewa. Amman ai ina buƙatar lokaci. Maigogul ya shigo yake sanar mana cewar ya faɗa maka nan da kwana huɗu ka turo. To a zahirin gaskiya ina buƙatar kamar wata biyu masu kyau ko babu komai ai ya kamata in gyara jikina. Kuma yanzu haka gobe za'ayi bikin Yayata, ni kuma goben ma tafiya zamu yi da Uzairu Zuchiyata." "Uzairu zuchiyarki fa kika ce?" Dariya nayi nace. Au kishi ya motsa kenan? Yayanane uwa ɗaya uba ɗaya. Kano zamu je gobe dashi akwai abinda zamu yi ne" Bamu gama wayar ba saida na tabbatar Khalid ya janye da batun turo magabatanshi nan da kwana huɗu an ɗage sai zuwa wata biyu masu zuwa. Har a cikin raina bana jin zan iya aurenshi ko da maza sun ƙare. Amman ina tsoron yin saki na dafe. Naso batun bikin Adama ayi komai dani ko cikin abokan ango zamu dace duk da ko wacce cikinmu roƙonta shine ta dace wani abokin ango ya ƙillota yace yana so. Da tunanuka ratata na wuni. Dik da dai muna ta hira ana yima Adama tsiya sunje sun siyo kayayyakin bacci harda wanduna shine su Aisha da yaranta da suka zo zamu kwana tare suke ta mata dariya. Sai naji ina kewar nawa yaran da yanzu suna gefena. Amman inna tuno Babangida ya tafi da tulin buhunhunan ɓacin rai da kishi sai inji wani sanyi a zuchiyata. Tabb yau babu zaman lafiya duk wacce take da girki yau zata gane kurenta in tayi wani wargi." Washegari sassafe dan masifa muka wuce tasha ni da Uzairu Zuchiyata yaci uban gaye ya ƙwama gogul yayi kyau sai kamanninshi ya sake fitowa sak da

Chapter 15 of 19