Share this page
sameki a gidansu Felisha sai mu tattauna dukkan abinda ya dace ayi a gama kawai uhm?. Felisha can i have your number? ( Felisha zan iya samun lambarki)" Ya tambayeta tare da ƙare maganar da murmushi. "Yeah of course " ( E sosai ma) Nan ta bashi lambarta ni dai ina tsaye Uzairu zuchiyata sai kashe mun idanu yake yi. Dala ya ciro a ajjihunshi ya zura mun a cikin jakata yana murmushi yana kallon cikin idanuna ya suri akwatinshi ya wuce mu. Takunshi na bi da kallo har sai da Uzairu Zuchiyata yace. "Lolo muje kin kafe bawan Allah da idanu. Nifa dama tun a gidan cin abinci naga hakan wallahi. Tabbb wannan ba dai maiƙo ba, naga dala ya dunbuzo ya cunkusa miki ke mu dai watanmu ne ya tsaya ƙyam ya maman maza. " Dariya muka yi harda Felisha da bata sam me muke cewa ba sai dai muna tafe inaji tana tambayar Uzairu zuchiyata waye wannan Alhajin. Uhm wai kunji Uzairu zuchiyata yadda yake karya harshe irin na turawa kuwa? Sai ku rantse da Allah yayi digiri da digirgir lallai karanta ƙamus yayi rana. A madadin mu fita a Airport sai muka zagaya ɗakin jira ashe jirgi zamu sake shiga daga nan Canada zuwa Alberta. Ƙarfe goma dot jirginmu ya tashi. Awanmu huɗu a zaune a jirgi dan masifa Felisha sai nan nan take yi damu gata kyakkyawa duk da dai ba yarinya bace, amman dai shekarunta sunyi daidai a matsayin matar Uzairu zuchiyata tunda dai ba na yau bane shi ɗinma. Mun sauka a jirgi a cikin Airport ɗin YYC CALGARY INTANATIONAL AIRPORT. da misalin ƙarfe biyun dare kai tsaye muka wuce gidan cin abinci dake cikin Airport ɗin. Dan Uzairu zuchiyata yace yana jin yinwa sosai dan ta faɗa mishi daga nan Alberta kai tsaye birnin CALGARY zamu wuce a mota sai mun yi tafiyar awa huɗu da rabi. Dole muka ci abinci muka rama sallolin da ake binmu ni dai duk na gaji ma wallahi. Anan Airport ɗin muka samu masu tasi suka ɗaukemu. Ananne muka sha kallo muka kashe ƙwarƙwatar idanunmu. Kai an tafi anyi mana nisa najeriya sosai. Gari tsab komai akan tsari ga shukoki masu ban ƙawa a hanya takota ina simintinnan a lailaye wasu titinan ma da muka wuce su intalock ne ba kwalta ba. Ga lantarki tako ta ina gari kamar rana Ba dai mu muka shiga cikin gidan iyayen Felisha ba sai da safe. Danƙari ai tun daga bakin ƙofar shiga muke taka jajayen fulawowi da muka shiga cikin babban falon gidan kuwa balambalone sunfi ɗari kala kala duk an watsar dasu. Uzairu zuchiyata yana tallafe da Felisha har gaban iyayenta da mutanen gidan nasu. Mun sha runguma da sumba a kumatu tako ta ina anata waƙoƙin tarbanmu abinda yafi komai bani mamaki shine wato Uzairu zuchiyata ba karamin taƙadarin baduniye bane hannu ta saka a ajjihu ya ciro wani ɗan akwati mai ɗauke da zoben daimon ya durƙusa a ƙasa yana nuna ma Felisha zobennen tare da kakkafeta da idanunshi. Bakinta ta rufe tana kuka iyayenta da ƴan uwanta suka shiga tafi. "Will you marry me ( zaki Aure ni?) Ya furta. Nan ɗakin yahau sowa anata ambaton " Yes_yes ( E_E) "Yes ( E) ta furta tare da miƙo yatsunta ya zura mata wannan zoben ya miƙe ya rungume kayanshi. Hmm ni naga fitsara a wajen turawa saida komai ya lafa aka nuna mana ɗakinmu na saukar baƙi ɗakin da aka bani yana kallon na Uzairu zuchiyata. Banɗaki na faɗa da sauri gudawa nake ji sosai, ina zama akan sita na soma yi ina sauke numfashi sai lokacin na samu zarafin ƙarema banɗakin kallo komai na ciki kalan sararin samaniya ne, ga tsari harda kafet a shimfiɗe a bayan gidan, wajen wanka kuma ƙatoton bawone na wanka a lokacin shi ake yayi mu a Najeriya ma sai gidan wane da wane ko gidan masu kuɗin da ɗinnan. Saita ruwan wanka nayi daidai yadda zan iya na gargasa jikina sannan naji daɗi alwala na ɗauro na fito na zauna akan kujerar doguwa. Kai turawa sun iya tsara waje marar hayaniya. Ɗakin ƙaramin gadone sai kujera sai madubin bango da tebur a ƙasan mudubin inda anan mai da su turare suke, ga kafet mai laushi malale a ɗakin, sai wani ƙaton taga kusan bango guda babu labule a jiki daga ciki kuna hango waje wasu fulawowine koraye shar masu sanya mai kallo nutsuwa a bayan tagar. Man dana gani a gaban mudubin shina shafa na ɗauki doguwar rigata na zura ni dai bana ce ga gabas ba ƙofa kawai na kalla na gabatar da sallolin da ake bina ina sallama ta ƙarshe Felisha ta buɗe kofar bata shigo ba tace dai in fiti muci abinci. Uzairu zuchiyata mutuminku yana kan tebur daga shi sai gajeren wando da riga amles da wata hula yana ta hira da mahaifin Felisha suna dariya. Waje na samu a gefen wata ƴar budurwa na zauna muka sake sabuwar gaisuwa turancin nawa da suka lura babu ƙarfi sai suka fi mayar da hankalinsu a kan Uzairu zuchiyata. Soyayyen dankalin turawa da soyayyar kaza mai zuma aka zuzzuba ma kowa da wata iriyar miya ita bata siga ba ita bata mazar ƙwalla ba dai Ni dai dankalinne na ɗanci babu laifi amman kazar da ƙyar na cinye yanka ɗaya zaƙi ne cau a jikinta na kora da wani lafiyayyen jus ɗin kwakwa dake cikin wani kwali mai daɗi. Uzairu zuchiyata kuwa ranshi fes Felisha take bashi abinci a baki yana amshewa harma da tambayarta wanda yayi girkin. An ɗan jima ana hira daga bisani iyayen Felisha da ƙannenta suka tafi suka basu waje. Nima wajen na basu nayi komawata ciki. Rigar baccin da Uzairu Zuchiyata ya sai mun itace a jikina ina kwance na rufa a lallausan bargo Felisha ta turo ƙofa ta bani wayarta wai ana son magana dani. Karɓa nayi tare da kara wayar a kunnena sai naji muryarshi mai sanyinnan yace. "Shalele da fatan kun sauka cikin ƙoshin lafiya ko?" Idanuna na lumshe nace. Lafiya lau gani ma a kwance inaso in ɗan yi bacci duk na gaji" Murmushi yayi mun tare da cewa. "To babu damuwa ki kwanta kiyi bacci. Gobe zan kira ki ki saka mun ranar da zanzo in ganki domin mu tattauna wata muhimmiyar magana" Idanuna na buɗe tare da cewa. "To shikenan nagode ƙwarai sai munyi magana a huce gajiya" Da haka muka yi sallama na mayar ma da Felisha wayarta na dawo ɗaki. Murmusawa kawai nayi mrs Buhari Tofa mutanen Canada dai an sauka lafiya. Ga kuma wani Alhaji ya ɓullo Ga Alhajin da Maigogul yayi ma Sabuwa tayi shima. Ga Ƴar shuwa dai ta faɗa harkar maɗigo. Anan littafi na uku yazo ƙarshe. Littafi na huɗu dana biyar zai soma zuwa muku bayan mun gama dogon hutun da zanje. Akwai sauran labari sosai a gaba. Akwai cakwakiya masu yawa fa a gaba Dan Allah na roƙeku a wannan karon aimun uziri zan tafi hutu mai tsayi kafin in dawo sabida idanuna sun tasanma ciwo sosai To dole sai nabi a hankali da fatan za ku daure kuyi mun uzuri dan Allah? An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 19 of 19