tarbiyyar gidansu Sabuwa yasa suke tunanin ba za'ayi auren ba"
Iska ya busar yana jin wani zazzaɓi_zazzaɓi na buso mishi.
"Saratu ku kwantar da hankalinku. Gobe ki tambayi Malam zuwa ƙauyensu in ya barki zamu je a motata. Inma hagu taƙi yi zamu koma dama. Kinsan Allah Babangida bazai Auri wannan yarinyar ba. Kuma dena damun kanku"
"To Yaya Hanne ai bazai taɓa barina zuwa ƙauyansu ba sabida yasan abinda zai kaini. Kuma kinsan kafiyar Malam kuwa? Balle wannan abun yadda ya ɗaukeshi da zafi. Kuma duk ya fimu tsanar Sabuwa da danginta ma."
Yaya Hanne ta dafa Malama Babba tace
."zanzo gobe zaki ji zuwa da dawowan Saratu. Kai kuma saika kiyaye gaba kana ganin halin da kasa mahaifiyarka a ciki. Gata da kishiya sun samu abun goranta mana marar goguwa."
Shi dai Babangida yama kasa cewa komai, zuchiyarshi sai tuƙa mishi take yi. Duk duniya babu wanda yake so sama da sabuwar budurwarshi wadda a lokacin ita ce a gaba. Duk da baya jin aurenta, amman tana da dukkan abinda yake buƙata a jikin mace.
"Ka fasa bankinka ka ciro dubu talatin zan kaima Malam kuɗin sayen rago kamar yadda ya buƙata"
Cewar Malama Babba.
Haka dole Babangida yayi abinda Malam yace musu. Malama Babba taje ta sameshi ta bashi kuɗin.
Ta ɓangaren Babangida yamma nayi ya isa majalisarsu nan akaita kacancana zancan masu zugashi ya aureta ya koya mata darasi sunfi masu cewa kada ya aureta yawa.
Ya gamsu da ya aureta yai mata wulaƙanci na fitar hayyaci yai mata sakin wulaƙanci.
Murmushi mugunta yayi da ya hango irin rashin mutuncin da zaiyi mata.
Sai yaji hankalinshi ya kwanta a sauwaƙe zai koyar da'ita darasin rayuwa.
Washegari."
Malama Babba tai ta jiran Yaya Hanne ba ita tazo ba sai wajajen sha biyun rana.
Abunda tazo mata dashhi yafi ƙarfin tunaninta bata taɓa zatin haka ba.
"Kinga wannan maganin ? Kina zuba ma Malam a abincinshi wallahi zancan wani aure ya ƙare. A taƙaice duk taurin kanshi sai yadda kika yi dashi Allah"
Jikinta da hannunta har rawa suke yi ta amshi maganin. A ranta ta gamsu kota wanne irin haline da dai a auro Sabuwa gara ta kauce hanya.
"Amman Yaya Hanne babu abinda zai sameshi ko?"
"Babu abinda zai sameshi. Ke dai ki saka mishi maganarnan a kasheta kowa ya huta"
Haka ta amsa akan nan da kwana biyu in girkinta ta zago zata zuba mishi."
SABUWA:.
Sassafe Malama ƙarama tamun wankan jego, tayi ma jinjira wanka, Rahama kuma ta wanke kayan da muka cire har da nata.
Ina daga gado ina cin tuwo Rahama kuma tana waya dasu Rakiya tana sanar dasu halin da ake ciki biki saura kwana talatin da bakwai kenan.
"Rakiya inaso kije ki samu Zahira ta gidansu Malam Bala ta haɗo mana magunguna zamu biyata daga baya sabida a tari abun da wuri kunga bamu da lokaci"
"To ba zuwan bane matsalar ba. Kuma nasan Zahira zata baku bashi. Waye zai kawo muku gida babu kowa sai Uzairu zuchiyata kuma kun dai san halin wannan kafaffen tsohon."
Rahama tace.
"Aba Uzairu zuchiyata ya kawo in yazo ƙofar gidan ya ba almajiran gidan zasu kawo nana."
"Rakiya tace.
"To shikenan zanje yanzu, dan dama gyalena na hannuna inaso zanje dubo Adama ne jikin dai yaƙi ance kishiyoyinta sun rarrafa sun kaita ƙaramin asibiti kuma ga ba kuɗi. Da ƙyar na haɗa dubu biyu su Sadiya suka harhaɗa mun shine zanje. Zan soma zuwa wajen Zahiran tukunna"
Da haka sukai sallama.
"Lolo kinji jikin Adama yayi tsanani kishiyoyinta nema suka kaita asibiti.
Ni dama gida Rakiya ta dawo da'ita duk da gidanma babu daɗi. Inma ta dakkota abinda zata ci shine aiki. Amman wallahi da kashe auren akayi da sai yafi.
Kwananta nawa dama a gida tayo yaji da kanta yinwar gidan da rigimar gidan yasa ta kwashi jiki Aisha ta rakata ta koma ɗakinta."
Ai da tana jin magana da tuni ta kashe wannan ƙaddararren auren. Allah dai ya bata lafiya. Amman Rahama ni da an bar wani maganin matan. Ni ba auren soyayya ba ba komai ba ina ni ina wani shan magunguna azo a barni da biyan bashi."
Rahama tace.
"Ai ko ba aure zaki yi ba yadda kika haihunnan yana da kyau kiyi gyara sosai. Ki bar ganin irin auren da zaku yi kenan. Sanda zai lallaɓo ya biyo dare mu muna ina? Su Labbai su Adama da Layuza duk ba irin auren da suka yi ba kenan?"
Haka dai mukaita hirarmu muna daga ɗaki.
Da yamma sai ga kunun kanwa da naman gashi shaƙe da kwano naci naci har saida na ture.
Ina samun kulawa a gaskiya fiye da tunani. Kullum sai naci naman gashi, ga magunguna Rahama sai durkamun take yi harda nasu tsugunno a gaushi duk inayi.
Ranar suna aka yanka mun katuwar tinkiyata a soye marau aka kawo mun halamu sun nuna ko tsoka ɗaya basu ɗauka ba. Ni dai nasa Rahama ta raba nama gida biyu aka kira Uzairu zuchiyata yazo ƙofar gida Rahama ta bashi ya kaima Rakiya harda dubu biyar na bashi dan Adama tana gida auren nata ya mutu ga jinya har yanzu bata warke ba."
Malama Babba:.
Ta ɓangaren Malama Babba tayi iyakar yinta Malam yaci wannan maganin a ranar da yaci sai batai mishi maganar ba sai washegari ta tareshi da maganar suna kwance.
"Malam yanzu wai da gaske kake yi yaronnan Babangida shi zai auri wannan yarinyar ƴar marasa tarbiyya? Ka duba watan yarinyarnan ta shiga na gomaa kenan a gabanmu mahaifinta kawaline kuma maras mutunci yanzu duk girma da darajar wannan gidan namu mai daraja da surukan da yaranmu suka auro daga gidan malumta a rasa wacce za'a gaiyato cikin haular sai Sabuwa?"
Tsam yayi yana kallonta. Tunda ta iya tunkararshi da wannan maganar tabbas yasan akwai abinda take saƙawa abinda yaji suna faɗa ta aikata kenan. Sai yayi ƙoƙarin gwadata ta hanyar cewa.
"To yaya za'ayi ɗanki ne ai ya jajiɓo mana ita. Sai nake ganin kamar dashi da ita ƙwaryar sama ke dukan ta ƙasa. Ko wacce ƙwarya da abokin burminta, in banda abinki mugu ai shi yasan makwancin mugu, ba'a abota sai hali yazo ɗaya"
Yayi shiru tare da kafeta da idanu yana karantarta
"Malam bambamcinsu a fili yake. Kai mai mutuncine, malami mai koyar da al'umma. Ka duba makarantarka ɗalibai nawa garemu muna ba mutane karatu harda tarbiiya. Nima Malama ce da taimakonka na zama hakan. Ƙarama ƴar gidan malamai ce. Kaf surukanka daga gidan malumta suka fito. Taya zamu haɗa iri da Sabuwa"
Dariya yayo sosai wanda ya daɗe bai yi irinta ba.
A baɗini kuma zuchiyarshi ji yake tamkar zata faɗo dan raɗaɗi. Yafi kowa ƙin Sabuwa yafi kowa ƙunsan baƙin ciki da takaici in yaganta, ko yaji muryarta da duk danginta da abinda ma ya shafeta baki ɗaya. Shi ta ɓangarenshi zai aurama Babangida Sabuwa ne sabida ita yarinyar da aka haifa, an riga da an haɗu ko ba'a soba. Dalili na biyu zai aura mishi itane a matsayin horarwa dan yayi imanin Babangida zaifi son ya auro ƴar mutunci, ƴar manyan mutane, ƙila ma ƴar malamai kamar yadda sauran ƴan uwanshi suka yi hakan. Na uku, zaiyi hakanne a matsayin hannunka mai sanda ga sauran yaran gidan. Duk da baya fatan a sake samun Babangida kashi na biyu, amman kashi na farkon ma ai baisan za'a samu ba. Hausawa suka ce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.
Dalilinshi na huɗu shine ita kanta Sabuwan ai mata adalci a taimaki rayuwarta a tsamota daga cikin duhun da take. Ƙila ta sanadinta ƴan uwanta su shiryu. Domin har ga Allah duk yadda yake ƙin Sabuwa yafi ƙin Babangida fiye da'ita. Ita gaskiya gaskiya ce baya bayan kowa sai bayan adalci. Waɗannan sune manyan dalilinshi.
"Yanzu dai mu kwanta da safe ma ƙarashe maganar na gaji, gashi ina da raɗin suna da asuba"
Yana faɗin haka ya juya mata baya.
Zuchiyarta fes ta kwana amman da asuba kafin ta bar turaka Malam ya kankare mata hadda ta hanyar wasu kalmomi marasa yawa sai firgitarwa da sare guiwa.
"Babba ki sake sanar da Babangida batun kuɗaɗennan lokaci nata gabatowa, sannan ya tabbatar a satinnan ya nemi inda zai zauna sabida ayi fenti da komai. Za'aje ayi mata jere ranar talata mai zuwa rana ita yau kenan."
Yana gama faɗin haka ya nufi hanyar waje saida ya fita ya girgiza kai yace.
"Mata kenan mai ilimi ma kenan ina ga jahila kuma?"
Haka dole ƙanwar naƙi Malama Babba ta saduda, ita ta sai da sarƙarta ta danƙama Malam Baba dubu ɗari biyu daya buƙata a wajen Babangida. Shi kuma Babangida ta barshi da neman haya.
Harma an samu ciki da falo da bayan gida da kitchen sai dai gidan gidan yawane sosai. A haka aka kama akayi duk gyare_gyaren daya dace kamar yadda Baba malam ya buƙata dai.
Ta nashi ɓangaren kuma Malama Ƙarama ya kira ya bata dubu ɗari biyu da hamsin. Da wasu dubu ɗari uku daban.
"Ɗari biyu da hamsin ɗin kayan lefe zaki haɗo mun ke da Larai. Wannan ɗari ukun kuma kayan gado da kayan kitchen nake son a sai ma yarinyarnan kina ganin zasu isa ?"
Sai da Malama ƙarama tayi murmushi kafin tace.
"Na lefen dai ya isa zata samu kaya da yawa. Ammman kaga na kayan ɗakin a gaskiya ba zasu isaba in dai kaya masu kyau za'ayi mata. Sai dai in irin kayannan na bakin kasuwa za'a sai mata"
Kai ya girgiza yace.
"A_a ayi mata komai mai kyau. Kamar yadda kuke ma yaranku. Yanzu to kawo ɗari ukun ki gani. In yaso duk abinda ake buƙata a rubuta komai da kudinshi da jumulla. Yanzu ku gama na lefen tukunna"
Ai kuwa haka akayi a cikin kwana biyu da Malam Baba ya basu suka haɗa akwatuna guda biyu da kit shaƙe da kaya masha Allah.
Malama Babba tana zaune tana lissafin yadda ta zama bora a gidan mijinta sai ganin Larai da akwati kici_kici tayi.
"Waɗannan akwatunan kuma daga ina Larai"?
"Kayan auren Babangida ne Baba malam ne ya bamu kudin muka haɗa"
Da mamaki ta kalli Larai ta dubi Wawo dake zaune yana dama ma Baba malam fura.
"Kuma sai baki kai ɗakin uwarki ba tunda itace uwar bikin ba?"
" Baba malam ne yace a kawo miki"
Kafin ta kuma cewa wani abun sai ga Malama Ƙarama ta shigo da sallamarta. Sai da ta nemi waje ta zauna kafin tace.
"Babba ga akwatin Babangida nan na haɗo. Toh Malam yace da magriba Wawo da Bashiru su kaimu gidansu Ita Sabuwa mu kai musu akwatin. Sai ki ma Yaya Hanne Magana. Goggo ma tana kan hanya tare zamu je akai."
Sai da Malama Babba ta hadiye yawu muƙut kafinnan tace.
"Toh shikenan. Allah ya kaimu da rai da lafiya."
"Ameen Babba Allah ya albarkaci auren kawai zamu ce"
Tana gama faɗin haka ta fice.
Malama Babba tace.
"Har fishin da Malam yake yi dani yayi irin wannan ƙamarin?
Taya zan ƙaunaci wannan yarinyar ai har gaba da abada"
MRS BUKHARI
"
[8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA UKU.
SHAFI NA BAKWAI 7
"Ai muma Malam Baba ya tutsiyemu na harhaɗo kan mazan gidan dubu ɗari uku muka haɗa mishi. Babangida ma saida ya bayar. Bai faɗa miki bane?"
Kai ta girgiza tace.
"Bai sanar dani ba. Damuwar dake damunshi yaushe zai bashi damar sanar mun da wani abun. Yau bamma saka shi a idanuna ba. To me Malam zaiyi da kudi?"
"Sai Allah bazai wuce duk akan bikin bane"
Haka dai sukaita tattaunawa ta ɗaga waya ta sanarma Yaya Hanne duk abinda ake ciki.
Kafin magriba sai ga Goggo ta iso dama dai ƴar ɗakin Malama Babba ce anan take sauka.
Ta sauka ko samun damar tattaunawa basui ba. Suna yin sallar isha suka wuce kai kayan lefe.
GIDANSU SABUWA:.
Tun yamma Maigogul ya kafa ya tsare a ƙofar gida domin tarbar masu kawo akwati.
A cikin gidan kuma Rakiya jallof ɗin shinkafa da kifi tayi ma ƴan kawo akwati sai lemun kwalba da aka siyo guda biyu rak sai ruwa guda biyu shima. Da ƙyar Maigogul ya bayar da dubu uku wai kuɗin salala. Rakiya ta bi kan yaran ɗakinta kafin su fita gantalinsu da ƙyar ta haɗa kudi suka kama dubu biyar.
Suna zaune a tsakar gida takwas daidai suka jiyo sallamar mata daga zaure.
Maigogul ne ya soma shigowa riƙi _riƙi da akwati a ka su Malama ƙarama na biye dasu.
Dama tun magriba Rakiya ta shiga gidansu Ƴar Shuwa ta sanar ma da mahaifiyarta to ta shigo tananan sai matar ƙanin Maigogul itama tananan tazo.
"Ku shiga ga ɗakin uwar Lolon nan, kunga ma uwar tata nan.'
Ya faɗa yana dariya tare da shigewa da akwatin a kanshi.
"Marabanku ku shiga"
Rakiya ta faɗa tare da miƙewa tabi bayansu. Goggo sai taɓe bakinta take yi.
Bayan an gama gaggaisawa a zatonsu Maigogul kuma zai basu waje ne amman sai Goggo taga zama dam. Ita to bata san waye ba kuma irin matannanne ita masu faɗa da yawa. Sai cewa tai
"Hala kaine Babban wan Amaryar dai ko?"
Maigogul ya gyara zaman gogul dinshi yace.
"Ni ubanta ne nina haifeta. Baiwar Allah kuyi abinda ya kawo ku ina da wajen zuwa dama isowarku nake jira"
Baki Goggo ta rike tana mamakin wannan abu.
."Toh kayane ai gasu na Sabuwa. Sai a bubbuɗa a gargani bisa al'ada ko? Duk da banga jama'a masu tarbar masu kawo kaya ba kamar yadda al'ada ta tanadar."
Babu dai wanda ya kulata Mama ta miƙe ta bubbuɗe akwatin ta shiga ɗaɗɗaga kayayyakin ana gani harda Maigogul a ɗadɗaga kayayyakin bacci da aka zuba haɗe da kayan kwalliya."
"Tabarakallah kaya sunyi an gode. Maigogul sai ka fita ko zasu ci abinci"
Mikewa yayi tare da bibbige malum_malum dinshi a kansu, su dai mamaki ya ishesu.
"To ni kam na tafi. Rakiya bikine damu ni kam sai jibi ma zaku ganni. Baƙi munga kaya Sabuwa tayi goshi ba'a taɓa wata yarinya rabin abinda akaima lolo ba, lallai da sa'armu muke tafe kafaɗa da kafaɗa"
Ya saka kai ya fice yana dariya.
Goggo tace.
"To Malama ƙarama inaga ai sai mu tafi ko?"
Umma tace
"Abincin fa?"
"Zamu tafi dashi kar muyi dare"
Cewar Goggo tayi hakanne danta kuresu domin a kallo ɗaya da taina gidan ta gane suna cikin talauci"
Ai kuwa kwanon da suka gani na abincin ya tabbatar da zarginta.
Har gaban mota Mama da Tani suka rakasu suka danƙa dubu Biyar ɗinnan a hannun Malama Ƙarama dan sunga tafi Goggo sauƙi."
Gidan Malam:.
Ai fa suna dawowa aka buɗe sabon faifayin surutu abinka da mata. Wannan kuɗin salala da wannan abinci akaita maganar a tsakar gida har dai yaje kunnen Baba malam sai da ya tsawatar.
Washegari Malama Ƙarama da Larai suka wuce kasuwa cikin kwana biyu suka gama siyan komai aka jibge a gidan Kawu Manga .
Baba malam da kanshi yasa aka je aka sanarma da su Rakiya ranar da zasu zo a debi kaya aje jere.
SABUWA:.
Gaga gaga abubbuwa sukaita faruwa, ni dai hankalina kwance daga ni har Rahama mun yi ƙiba sabida cin daɗi, haka ma jajiriyata tayi kiba duk wanda ya ganta sai ta bashi sha'awa.
Saura kwana ɗaya in yi alba'in wanda yayi daidai da gobe ɗaurin aurena.
Ni da kaina da safe naje na samu Malam a waje cikin almajirai.
Yana ganina ya girgiza kanshi ya taso ya same ni a zaure.
"Lafiya Sabuwa me kuke da bukata?"
Babu kunya dan a lokacin bamma santa ba nace.
"Kitso da ƙunshi nake son ayi mun. To ina da me kitso kar tazo a hanata shigowa"
Hannu yasa ya rufe baki da dukkan halamu maganar ta matuƙar bashi kunya. Da ƙyar yace.
"Jeki zan turo Ƙarama"
Na wucewata ina mamakin dalilin da yasa ya buɗe baki.
Na koma ciki Rahama tace.
"Ya ake ciki me yace miki?"
Uhm wai in dawo zai aiko kishiyar babar su Babangida "
Bamma rufe baki ba sai gata ta shigo.
"Ke Sabuwa ƙunshi da kitsonne ba zaki iya faɗa mana ba sai Malam kika tsallake mata a tsakar gida kika sameshi shi. Dake ku a gidanku babu manya. Uban naki ma bai kama kanshi ba bare ku. To kul a gidannan mu ba'a haka.
Duk abinda kike buƙata ki sanar mun ni zan isar miki wajen Malam ɗin dan ba sa'anki bane. Ƙunshi da lallai kuma zan turo Yahanasu tayi miki maras kunya"
Ahh to naga ai zamanshi nake yi"
Na faɗa ina ƙunkunni.
"Au zaman Malam ɗin kike yi?"
"E mana to da zamanki take yi? Ku dai gidannan akwaiku da tsurfa kaiii kuna da zuzuta ƙaramar magana ta zama babba. Wai dama haka malaman suke ne?"
Rahama ta faɗa tare da juya kai tamkar ba ita tayi maganar ba.
Haka dai Malama ƙarama ta fice. Ba'afi awa biyu ba mai kotso tazo.
Mune har bayan isha muna abu ɗaya. Kitso dai sai da akayi guda ɗari da hamsin. Ƙunshi kuma salateb aka jeramun suffa. Sai takwas na dare aka gama.
Washegari na fito fes dani.
Tun asuba muke ta harhaɗa kaya ni da Rahama, muna kan tattare kayan Malama ƙarama tayo sallama ta shigo hannunta riƙe da baƙar leda cike dam da alawa da goro na ɗaurin aure.
"Gashi ke goron ɗaurin auren ne. Malam kuma yace ku shirya bayan la'asar za'a kai ki."
Wani sanyi naji a raina jin wannan aure ya ɗauru. Murmushi nayi dana tuno rantse_rantsen da Babangida ya dinga mun akan bazai aureni ba. Rashin sani yafi dare duhu ashe daga ranar da zan tare a matsayin mata a gidan Babangida da ranar matsalata ta buɗe sabon shafi mai wuyar biyawa.
Yamma nayi akace mu futo ba ai taro ko ɗis ba asalima ko yaran gidan basu zo ba. Mardiyya na bayan Rahama ta goyata muka fito tsakar gida da kayayyakinmu.
Malama ƙarama, da Goggo, sai Larai sai kuma ni da Rahama aka ɗauke mu a mota zuwa gaba can da unguwarmu. Gidan gidane mai cike da jama'a. Da sallama muka shiga sunata hada _hada a tsakar gida, yaran gidan sunata tsalle tsallensu akwai yalwar tsakar gida sosai a gidan.
"Sannunku fa da aiki matan gida. Ga abokiyar zama kun sake samu"
Cewar Larai kenan.
"Ayya sannunku da zuwa. Ai mu da muka ga irin dukiyar da aka zuba da gyaran da akayi mun zaci amaryace munga idanta a bude tangararan"
Cewar wata zabiya uwar rawar kai ta ci wani pink din janbaki baki sai kace babanin akuya. Goggo tayi dariya tace
"Ba Amarya bace ga ƴarta a baya ma. Allah dai ya baku zaman lafiya"
Suka amsa da ameen . Ni dai ina tsaye a gefe. Malama ƙarama ce tai mana jagora zuwa ɗakina.
Lallai Baba Malam ya zuba mun dukiya ko diyarshi ce ni iyakar gatan da zai yi mun kenan.
Goggo dai saida ta lalleƙa ko'ina tana girgiza kai.
"Ƙarama tashi mu tafi kinji."
Tashi suka yi suka fita babu wanda suka kula, muma bamu ce dasu uffan ba.
"Ke Lolo yanzu duka wannan aljannar duniyar wai naki ne? Uhm cikin shege yayi miki rana, mu ne dai muka hadu da jar masifa Adama dai Allah ya yanke mata wahala."
Tashi nayi na cire mayafina harda ɗankwalina muka shiga kitchen ga kayayyakinan a jejjere, wasu ma suna kwalinsu, ga gara tubarkallah Baba Malam yayi mun. Muka tafi ɗakin gado shima yayi kyau, ko ina kefet ne mai laushi. Zama nayi a bakin gadon nayi shiru haka suddan kuma sai nake jin faɗuwar gaba mai tsanani. Har Rahama ta gama jera kayana dana Mardiyya ban ko motsa daga inda nake ba"
"Lolo kinji magriba ake kira bari kiga in yi Sallah sai in kama hanyar gida kuma"
Kallonta nayi tana shimfide Mardiyya a kan gado..
Gidanki zaki koma?"
"Wa? Can gida zanje gobe zamu zo muyi namu bikin ai, kuma a gyara miki wajen da kyau"
Tana bayan gida aka aiko yara biyu ko wanne da kwano a hannunshi na abinci.
Toh kuce musu an gode ko?"
Na amshi kwanukan da fara'a na ajjiye akan teburin tsakiyar falon. Na koma ciki ina ƙara ƙarema ɗakin kallo. Rahama ta shigo daga banɗaki ta sameni a tsaye ina riƙe da labule ina duba kyansu.
"Uhm Lolo anyi ɗakin kai. Kinsan Allah ke kam haɗuwarki da Babangida alkhairi ne. Jibi waje Lolo komai mai tsada.. kab cikinmu babu ma wacce ta taɓa samun arzikin irin gidan hayarnan da aka kama miki. Dan wallahi da gani tsada zaiyi in kika duba yanayin tsarin ginin. Kitchen ɗinki jibi shaƙe da kayan arziki ga su kayan kallo a falo."
Dariya kawai nayi mata na shiga banɗakin ita kuma ta tada Sallah.
Na fito na sameta a tsaye ta gama shiryawa tsab.
Rahama nace ko zaki farke katan din taliyar dake kitchen ki tafi muku da ko uku ce kwa karya dashi?"
"Sosai ma muje to in buɗe kinga har su maggi da mai na ɗiba.
Ai kuwa hakan akayidan mangyaɗa ma da muka rasa a ina za'a zuba Rahama ta buɗe ruwan gora na swan ta kwankwaɗeshi tas muka cika da mangyaɗa. Abincin da matan gidan suka kawo ma a leda na juye mata nace ta kaima Rakiya.
Mardiyya na goya na ɗauki jakata na kalle ɗakin na rakata har bakin titi saida ta samu abun hawa kana na dawo.
A hanyata ta dawowa na tsaya na sai biredi da ƙwai a shago da taliyar ƴan yara dan ba ƙaramar yinwa nake ji ba."
Babu kowa a tsakar gidan sanda na shigo ko wacce tana ɗakinta da iyalanta. Nima ina shiga na rufo ƙofata na kwantar da Mardiyya a kujera na shiga kitchen ɗin na kunna gas na ɗaura ruwan zafi. Sannan na fito na yi Sallah a falo.
Taliyar ƴan yars na dafa da kwai sai tea mai kauri dana haɗa dama muna da kayan tea da mika tawo dashi a kaya.
Nayi ƙat na shiga da kwanukan kitchen na wankesu na mayar dasu inda na ɗauka
Ƴata na ɗauka muka shiga ciki muka hau shirin bacci. Kaya masu sauƙi obarol na saka ma Mardiyya ni kuma wata doguwar riga mai sauƙi na saka wacce nake bacci da'ita tunda na koma gidansu Babangida.
Na kashe hasken ɗakin nayi baccina raina ɗaya
Wani irin bacci nayi wanda ban taɓa yin irinshi ba. Bani na farka ba sai bakwai na safe shima sabida bugun da aketa ma ƙofatane yasa na bude idona a hankali gari tangararan.
"Lolo kizo ki buɗe mana ƙofa"
Na jiyo muryar Maigogul ta windon uwarɗakin nawa.
Da sauri na duro na zo na buɗe musu.
Dukka ƴan gidanmu ne suka zo harda ƴan ɗakin Hauwa. A mazan dai daga Uzairu zuchiyata sai Ma'aru ne suka zo. Daman sune basu fiye yawo ba a gidanmu bar Uzairu zuchiyata dai da yaudarar mata, shi kuma Ma'aru ɗan yankan ajjihune ranar cin kasuwannin ƙauye yafi fita.
"Kai kai kai Lolo haka Allah ya kashe ya baki, irin wannan kaɓakin arziki haka? Masha ALLAH "
Cewar Maigogul dake tsaye yana karema ko'ina kallo su Adama kuma duk sun zazzauna wasu a kujera wasu a kasan kafet.
"Ai kasan itafa Lolo tun tasowarta ta zama daban komanta ya bambamta dana ƴan uwanta"
Cewar Rakiya tana yi tana kallon Hauwa. Dariya Hauwa tayi tace.
"Gaskiya mana ta haifi ƴar shege, kuma taje ta haihu a gidansu Baban shegen kinga ai ita kaɗaice hakan ya faru a kanta"
Nan cacar baki da habaice_habaice ya soma.
Ni kam suna cikin mayar da zance nayi komawata ciki su Adama suka biyoni dukkansu.
Zuwanku ne ya tasheni ma a bacci. Bari in yi Sallah sai mu shiga kitchen. Adama ashe haka abu ya faru?"
"Ke dai je kiyi Sallar tukunna dai akwai labarai ai"
Cewar ƴar Shuwa kenan wacce ta ɗauki Mardiyya tana taɓa mata kumatu.
Ina cikin Sallah, su Adama sunyi baje _baje wasu a gado wasu a ƙasa Adama babu ko riga a jikinta daga ita sai bireziya da dogon wando hijabi ta ziro kawai. Ina cikin sallah Sai kawai Babangida ya ɗaga labulen uwar ɗakin. Daidai nayi sallama muka haɗa idanu dashi.
Wani irin wulaƙantaccen kallo ya watso mana na raini. Yayi tsaye riƙe da labule shi bai shigo ba, shi bai koma ba.
Su Adama duk suka miƙe tsaye suna neman hanya.
Ina jiyo Maigogul yana gaishe da Babangida amman bai ko yi gezau ba.
Ai saika basu waje su wuce ko?"
Na faɗa cike da tsiwa.
Shigowa yayi yana muzurai su kuma suka fice ɗaya bayan ɗaya. Mardiyya na kafaɗar Sadiya.
Zama yayi yana ƙarema ɗakin dani kallo.
Miƙewa nayi na ninke sallayata na cire hijabina ina shirin ficewa a ɗakin naji yace.
"Ke Sabuwa"
Juyowa nayi ina kallonshi.
"Me mutanen gidanku suke yi a gidana haka cikin falo? Ohhh nagane"
Sai naga ya miƙe ya iso har inda nake yana wani zazzare idanu.
Daf dani ya tsaya har ina shaƙon kamshin jikinshi wanda yake cakuɗe da warin hayaƙin sigari.
"Sun zo ne a cinye garar da ubana ya hadoki dashi ba. Ai kab ƴan uwanki babu wacce ta samu gida irin wannan. Shine akazo za'aci banza harda tsohon najadun ubanki"
Maganar ta dira a zuchiyata sosai
Wallahi duk lalacewar iyayena da ƴan uwana ina son kayana, kuma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 19