Share this page
kukeyi anan na ganku da jaka tafiya zaku yi ne?" Hmmm Sama kenan. Baka ko leƙowa gida kama mance damu sai dai matarka da'ita aketa komai. Gaza shima matarshi ta gudu ga ciki a jikinta. Matarka shekaran jiyannan da tazo bikin Adama take faɗa mana kana kudu wai neman kuɗi ashe a wannan kudun kake" Uzairu zuchiyata yace.. "Dama duk guje_gujennan ka dena kayi dakonka ka koma gida kayi kwanciyarka a gado ai yafi maka kwanan tashar. Duk da dai a tashar kai kam ka girma dole kafi gane hakan. Bijeka wallahi baka da wata maraba da majinuni. Lolo muje kinji" Sama ya dubemu yace. "Kada ku sake ku faɗa mata kun ganni. Inna tara abinda zan tara kafin haihuwarta zan koma. Duk da wallahi ban tara ko sisi ba kuɗin ana abinci da hayaƙi kawai yake ƙarewa" Nan mu dai muka barshi yanata surutai harda ashariya fa kamar haukacewa ma yayi wallahi ni ko saina ɗauki damuwar duniya na ɗaurama kaina Uzairu zuchiyata kuwa ko a gyalenshi sai harkokin gabanshi yake yi. Niko muna shiga gida da zancan naso in tari Rakiya sai muka ga Gaza a zaune a tsakar gida yana cin abinci a roba ya rame duk ta tara suma. "Kaga Sabuwa da Uzairu Zuchiyata. Eh ai naji kuna cikin alkhairi dumu_dumu kai Uzairu zuchiyata ka samu mata eh a Canada. To in Allah yayi tafiyar taku muma ƙila eh silar mu auri turawan canne yasa. Kema Lolo ina miki fatan eh wani baturen yace zai aureki Allah kuwa. Gashi na dawo na tarar eh Adama anyi aure. Allah ni mamakina ma eh ya akayi su Sadiya wai basu shiga ba eh sai Adama guzuma. Gashi wai Madamcy ta tafi nazo na tarar tabar ɗakin sunnah. Zata eh dawo Amman munyi waya da maɗaurin auren eh namu" Wallahi tun muna gane me yake cewa mu dai har muka dena fahimtarshi a fahimtata shima kamar matsala ya samu fa. Ya shiga mana labarin firsina. Ni dai zama nayi ina wuce gajiyata. Uzairu zuchiyata yana zaune a turmi yana cin ayaba yace. "Ai gara ta dawo tunda kaima ka dawo tazo ta haihu. Nima dai na kusa shiga daga cikinnan ɗan Babannan da muke ji ana cema abokanmu muma ace mana" Uzairu zuchiyata Wayarka fa aketa kira" Dariya yayi yace. "Ke rabu da ƴan wahala. Ni wallahi Felisha tana aurena sim zan sake. Kinsan turawa da kishi yanzu saita yanki jiki ta faɗi ta mutu. Ko tayi kukan kura ta kasheni. Ko ta rataye kanta Dama itace zata mutum da sauƙi kinga na gaji dukiyarta" Dariya muka yi harda Gaza shima. "Bari in eh yi wanka inje inyi aski kafin Madamcy ta dawo. Rakiya ta tafi kayi nayi Hauwa kuma wai Layuza ta haihu jiya ma a gidanta ta kwana." Baki na taɓe kawai mukai zamanmu a tsakar gida. Da faɗa Rakiya ta shigo da tarkace cikin ƙaton Buhu a kanta. Tanata zage zage har ta dire. "Au kun dawo ne?" Mun dawo Rakiya. Ƴan biki basu dawo bane?" Zama tayi a kusa dani tace. "Hmmm basu dawo ba Lolo sai anjima nake ga ko yamma. Ke Lolo jiya dai da daddare Adama sai da ta lakaɗama uwargidanta duka" Salati muka saka ni da Uzairu Zuchiyata Rakiya kuma ta zuba tagumi tana girgiza kai kawai. "Dama an shirya hakanne dan a gano wace irice Adaman ita kuma maimakon ta kwantar da kanta ta tura musu aniyarsu saita kasa daurewa ta biyema su Labbai har abinda zai faru ya faru. Allah dai ya taƙaita kowa laifin uwargidan yake gani" Kai kawai na girgiza na shura mata tsarabar kayan marmari dana yo musu na miƙe. Ni kam zanje in watsa ruwa in kwanta in huta. Ashe Layuza ta haihu kuma?" Na faɗa ina taɓe bakina. "Ta haihu ranar da kuka tafi ɗanta namiji. Hauwa ma tana can ta tare. Sai kuka ga Gaza shima ranar da kuka tafi kwatsam su Adama sun kama hanya sai gashi uwa an jefoshi. Masu ɗaure musu ƙunƙuru sunsa an sakoshi ba ana shirin doka gangar siyasa ba. Hmm itama matar tashi tana hanya yau zata dawo" Tana cikin wannan labarin Gaza ya fito daga ɗakinshi ya nufo Rakiya. "Ga ɗan madubi in Madamcy tazo ki bata. Wannan dubu biyun ki bata na cefane dan ba dawowa zan yi da wuri ba ki faɗa mata zanyi dare" Rakiya tasa hannu ta karba yana fita nabi bayanshi nayi shigewata gidanmu. Buɗe ƙofar nayi na jefa jakata na zari bokiti na ja ruwa a rijiya nayi wanka fes kafin na shiga ɗaki. Ai banci ta bacci ba, ko ina kaca kaca saida na share awa guda ina gyare gyare kafin na samu dama na kwanta bacci yayi awon gaba dani. Cikin baccin wayar Khalid ta tasheni. Idanuna a lumshe na ɗaga wayar Hello ranka shi daɗe. "Mitsiyaciyya la'ananniya tambaɗaɗɗiya kawai. Ai babu shiri na wattsake nice harda miƙewa zaune zumbur. Matar Khalid ta zageni ta zageni yadda take so. "Kece Sabuwa wacce ta hana mijina sukuni kika hana ya dinga kwanciyar aure dani ko? Mitsiyaciya la'aninniya ai an bani labarin har gidana ya taɓa kawoki. Sabuwa duk ranar da mukai ido huɗu dake to wallahi ki kuka da kanki dan sai nayi miki abinda baki zata ba. Shegiya karuwa mai bin mazan mutane" Shiru nayi naita tunanuka masu yawa. Jikina yayi wani irin sanyi. Ajjiyar zuchiya kawai na sauke ina shirin zan sakko akan gadon in yi alwala akaci gaba da kiran wayata da lambar Khalid ni dai ban ɗauka ba alwala nayi nayi sallar la'asar na kulle ɗakin na nufi gidansu Rakiya. Ina shiga na tarar da madamcy ta dawo tana girki a gaban ɗakinta. Dariya tayi data ganni, nima nayi mata dariya. Wato kinji masoyin naki na hannun ƙarfen ya dawo shine har kin dawo. Wannan soyayya dame tayi kama" Dariya muka saka duka harda Rakiya da take shanya. Su Labbai ne suka yo sallama suka shigo kwararam kwararam. "Ya na ganku haka babu komai a hannun kowa?" "Ai Rakiya ke dai bamu waje kawai. Madamcy kin dawo kenan?" Cewar Labbai data zube a tabarma. Nan duk muka baje akaita hira ana mayar da zance. Suna bamu labarin faɗan da akayi. Muma muka basu labarin abinda ya faru da basanan. Mune har magriba muna gidan. Matar sama ta miƙe tace. "Ni kam zan tafi gida Rakiya sai wani lokacin kuma" Binta muka yi ni da Labbai zamu rakata anan na labarta mata inda zata je taga mijinta yana gari babu inda yaje." Washegari saiga Khalid yazo mun a kiɗime fur naƙi saurarenshi na faɗa mishi ya fita a rayuwata bazan taɓa aurenshi ba. Tun yana magiyar harya hakura tun yana kiran wayata yana samu harma na kulle layin nashi ta yadda koya kirani baya samuna, tun yana zuwa ƙofar gidanmu ya turo yaro, wallahi har ya soma shigowa kai tsaye. Sau biyu yana durƙusawa akan guiwowinshi akan yin yi mishi rai, na biyun har hawaye yayi mun yaita mun rantsuwar zai zauna dani duk rintsi ni kuma naƙi fur Allah. Gaga_gaga haka lamura sukaita tafiya kwanaki nata tafiya har kamar wasa yau saura kwana biyu tafiyarmu canada mun gama shirya komai tsab akwatunanmu sababbi mun zuba duk abinda muke buƙata lokaci kawai muke jira gobe zamu wuce Kano. Daga kano zamu shiga jirgi zuwa Lagos ta can jirginnu zai tashi da izinin Allah ƳAR SHUWA:. "Mama wannan mutane haka danƙam anya kuwa zamu tsaya? Suna fa nace zanje kinsan halin dangin miji yanzu sai su iya faɗama Babangida banzo da wuri ba" Hararata Mama tayi tace. "To saime su faɗa mishin mana. Ke da kike neman yadda zaki kafu da kyau a gidan kuma. Ai ba'a bori da sanyin jiki ni naso ma in kaiki Maiduguri ne ɗungurungum ayi a gama. To mijinki baya barin tafiya ke kuma kina tsoron kada ya sakoki. Ina mamakin irin son da kike yima mijinnan naki shi ba kuɗine dashi irin na da ba balle kice Saifa kin tashi tsaye zaki iya karɓan ƴancinki" Ƴar Shuwa tace. "Wallahi hakane Mama kinsan amaryar da ya kawo itama tazo da nata salon iskancin duk tabi ta tsaneni kofa abincina bata ci shi kuma ya ɗaure mata ƙunƙuru baya cewa uffan sai dai duk ranar girkina tayi nata" Mama tayi tsaki tace. "Ai saiki samu hujjar da zaki saka borin cewar tunda abun hakane a raba girki ko wacce ta dinga yin nata. Dama yanzu wa yake wani yayin girki da kishiya ai kowa yaci nashi gudun kada a barbaɗa maka abinda zai zo ya halaka rayuwarka" Zaman wata matashiya da ba zata haure shekarun Ƴar Shuwan bane yasa suka tsayar da hirar tasu. "Akwai mai waje fa baiwar Allah " Ƴar Shuwa ta faɗa ma wannan matar. Sai tayi murmushi tace. "Nice mai wajen Yar aikinace nasa tazo ta kama mun layi saida na tashi daga bacci shine nazo" Kallonta dukka suka shiga yi. Da gani matar mai kuɗin gaske ne dan komai na jikinta na kuɗine gata da fara'a. Haka kurum ƴar Shuwa taji wannan matar tayi mata wani bala'in kwarjinan da bata ko son dena kallonta. Ita kuma idan suka haɗa idanu sai tayi mata murmushi. Tunda dai suka zauna har azahar basu samu shiga ba saura mutum biyu a gabansu damma sauƙinta bibbiyu ake shiga. Wannan matar ce ta dafa kafaɗar Ƴar Shuwa tace. "Ko zamu je mota muci abinci kafin layi yazo kanmu Mama ta jire mana layin?" Tayi maganar tamkar tana magana da saurayinta. Mama tace. "Kuje mana in layi yazo na kiraku" Ƴar Shuwa ta miƙe tana murmushi tabi bayanta sukaita ratsa taron mata har suka zo wajen da manyan matan da suke zuwa wajen bokan suke ajjiye motocinsu. Wannan mata ta buɗe bayan ƙatuwar motarta fara. "Bismillah ki shiga ta waccan ƙofar ko?" Ƴar Shuwa ta zagaya ta shiga suka zauna tare a gidan baya. Basket ɗin abincin yana kujerar tsakiya. Wannan mata ta buɗe lafiyayyar miyar ganyen da ƙamshinta ya mamaye cikin motar. Da tuwon shinkafan daya tuƙu. "Guda nawa zaki ci?" Ta faɗa tana rausaya idanu" "Biyu zaki saka mun ya isheni" Murmushi kawai tayi ta saka mata ta sa mata colali itama ta saka nata. Motar tayi tsit baka jin komai sai ƙaran cokali kawai, gashi ta kunna musu motar ac sai ratsasu take yi. Irin rayuwar da ƴar Shuwa ta daɗe tana burin kasancewa kenan. Kamar tana karantar zuchiyarta sai ji tayi tace. "Macce tana iya zama duk abinda take son ta zama sai dai in taso ta damkwafe a waje ɗaya. Kin saba zuwa nanne dama?" Ta ƙarashe maganar da tambaya ga idanunta masu kwarjini ta zuba ma Ƴar Shuwa. "Yaune zuwana nan wajen na farko. Mijina nake son mallaka sai kishiyoyina da nake son a saisaitama zama, da kuma tsohuwar matar mijina da yake son dawo da'ita. Kefa kishiyar ko mijin kika kawo?" Dariya suka yi duka. "Ni abinda ya kawo ni ma duk ba wannan bane. Kinsan duniya cike take da abubbuwan ban mamaki. Aini namiji bana mishi kallon ishasshe balle har in kawo shi wajen malami balle kuma kishiya" Ƴar Shuwa tace. "To hala akan kasuwanci ne ko?" "Ashe kin gane in banda abunki ana ta kuɗi wa yake ta ɗa namijin da yanzu zaka iya sakinshi ka auro duk wanda kake so in kana ganin da takura" Ƴar Shuwa sai taji matar ta kuma burgeta. Ƙwanƙwasa ƙofar motar da aka shiga yine yasa suka juya. "Kinga Mama ta biyo mu ƙila layinne yazo kanmu" Ƴar Shuwa ta ɓalle murfin motar ta fita dama ta gama cin abincin. Wannan baiwar Allah kuma ta fito da kula ƙarama a hannunta ta miƙa ma Mama. "Ga naki Mama dama nace in muka gama kema sai a kawo miki naki" Mama ta ƙarba tana godiya. "Ga Ƴata ko zaku yi ƙawance tunda naga kamar kin fita wayewa. Kin ganta mijine yake yadda yaso da'ita kishiyoyinma ba ƙyaleta suka yi ba. Ni auren ma naso in kashe to mijin nata irin almajirannanne ya kafeta a gidan bata ko son ayi batun rabuwa. Kyau iya kyau kin ganta dai tubarkallah mijin nata karayar arzikice ta sameshi yanzu ticha ne fa." Baki ta taɓe. "Ticha fa Mama. Yanzu kamarki mijinki ticha ne? No nasan yadda zanyi Mama. Mu dai jenku" Nan suka rankaya suka koma waɗanda suke gabansu su biyunnan suna ciki sai sun fito zasu shiga Suna fitowa suka shiga dama bibbiyu ake shiga. Ita wannan matar godiya kawai taje yima bokan ta ƙara bashi kuɗi masu yawa duk na godiya. "Ku kuma meke tafe daku. Ke ki dena wannan kalle kallen kar kije ki makance. Mijinki kuma ba zaki iya mallakarshi ba. Sai dai kishiyoyin naki. Sabuwa kuma babu kome a tsakaninta da mijinki. Yaran mijin dai zaki samu nasara a kansu amman sai kin zuba musu magani a abinci sunci da kansu zasu roƙi uban nasu suce zasu dawo wajenku sai yadda kika yi dasu" Ƴar Shuwa tayi mamaki Amman ba sosai ba kasancewar ba wai yau ta saba zuwa wajen bokaye ba." "To amman boka" "Ke iyakar abinda zai yiwu na faɗa miki yarinya duk ma inda kika je sai dai suci kuɗinki Babangida ba zaki iya mallakarshi ba. Kuma bazai taɓa dena son uwar Yaƴanshi ba. Sai dai fa ba zasu sake zaman aure ba." Ƙullin maganine ya faɗo daga sama guda biyu ɗaya a ƙunshe a jar fata ɗaya a ƙunshe a baƙar fata. "Wannan jan maganin shi zaki barbaɗama kishiyoyinki a ƙofar ɗakinsu su taka Muddin suka taka zasu biki zasu miki biyayya tamkar ke kika haliccesu. Wannan kuma yaran mijin naki zaki sama a abinci suma in suka ci zaki samu duk abinda kike so daga garesu. Sai dai akwai wani haske mai gauraye da duhu da yake tunkaroki sai kinyi a hankali. Na hangi tashin hankali, da ruɗani, na hangi nadama, da dana sani. Amman akwai dukiya, ɗaukaka, farin jini duk a cikin lamarin" Kan su Ƴar Shuwa ya ɗaure sosai. Mama taso jin ƙarin bayani amman ya ɗaga mata hannu dole taja bakinta tayi shiru. Kuɗinshi ya faɗa Mama ta kunce bakin zaninta zata ƙirgo. "A_a Mama bari in bayar ai mun zama ɗaya" Kuɗin ta ƙirgo ha da ƙari ta bashi suka fito tare. Ta nemi ta rage musu hanya ai kuwa babu musu suka shiga. Ai suna kama hanya aka ɓalle da wani irin ruwa mai cike da iska, ga garin yayi shegen duhu sosai. Sai samun gefen titi suka yi suka tsayar da motar dan ko gabansu basa iya gani tsabar yadda ruwan yayi ƙarfi. "Baiwar Allah kinga wata ƙudurar Ubangiji ko. Da ba dan ke ba da ruwannan haka zai taremu a hanya. Nace wai me sunanki ne kuma a wacce unguwar kike ne a Dutse?" Mama ta ƙarashe maganar tana mai dariya. Itama dariyar tayi. "Sunana Samirah amman Mama ba'a Dutse nake ba ina cikin jigawa ne cikin garin Bamaina anan nake" Ƴar Shuwa kuwa hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba tana dai zaunene tana tunanin wacce ƙaryar zata yi in taje gidan sunan da tun safe ta fita zata je. Ga kishiyoyinta suna can dole ma su sanar ma Babangida lokacin da taje gidan sunan ko dan gulma. Sanda suke bin layi ma tana ganin kiran Sa'a ƙin ɗauka tayi sabida bata san me zata ce mata ba. "Ƴar Shuwa wannan tunanin na meye haka zaki kashe kanki a banza akan wani talakan mijinki. Muna hira hankalinki baya ma wajenmu yau ga tsiya" Sai lokacin Ƴar Shuwa ta ɗan yi murmushi suka ci gaba da hirarsu. Sai wajajen biyar ruwannan ya tsagaita Samira taja motarta suka wuce. Har ƙofar gida ta sauke Mama ta wuce da Ƴar Shuwa gidan Alawaiyya. A ƙofar gidan suka tsaya har zuwa wannan lokacin ruwan ana yayyafi" "To inaga abinda za'ayi saka number ki anan. Na zama direbanki in kun gama ki kirani a waya zan zi in ɗaukeki in kaiki har gidanki. Ni dama zaki bani wajen kwana ai sai in kwana a wajenki gobe in kama hanyata ban fuye son zaman hotel ba sabida mijina babban mutum ne kuma yana siyasa kinsan hakan ka iya haifar mishi da yarfe irin nasu ƴan siyasa." "Ai babu damuwa duk da nice da miji akanki zan iya sadaukar da kwanan nawa ga abokan zaman nawa ma." Baki ta taɓe tace. "Amman har sai kin sadaukar da kwananki shin baki da ɗakinki daban kike nufi tare kuke kwana a ɗaki ɗaya wai?" Murmushi ƴar Shuwa tayi tace. "A da dai yana da turakarshi ɗakunanmu kuma a yalwace suke suma. Amman tunda karayar arziki ta sameshi shikenan muka daqo gidan haya da zama haka dai aketa haƙuri" Da haka dai ganin su Sa'a dasu Sumy sun fito suna dariya yasa Ƴar Shuwa tayi sallama da sameerah ta fito daga motar. Kallonta Sa'a tayi da mamaki tace. "Wai sai yanzu kika iso ke da akace tun safe kinma riga kowa fitowa shine saida taron sunan ya ƙare tas zaki zo? Kin ganmu fa ko wacce guduwa zata yi ruwane yaƙi ya tsagaita. Da bama zaki zo ki tadda mu ba" MRS BUKHARI [8/26, 8:42 AM] BADA'AT IBRAHIM: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GV5vhgDl7ul6aRQ08xqvVy?mode=ems_share_t Barka da zuwa wannan group me albarka,kina business amma kullin kina yawan ayimiki ,logo, sticker da sauransu Kiyi joining wannan linki din insha Allah zan koya miki yanda zaki yi da wayan hanninki batare da ko sisin kiba Ina nufin 🆓🆓🆓🆓! Yes 🆓! Harma kidinga yima wasu kina samun kudin ki Daga gida Kawai waya kike nema da datan ki Kawai kishiga group din for more update Thank you IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA GOMA SHA TARA. Tsallakawa tayi inda suke. Sumy ta kawar da kanta gefe. Ita kuma ƴar Shuwa tayi mata dariyar muguntar da yake ɗauke da fassarar zaki shigo hannune yarinya. "Wallahi tun safe na fito sabida ayi aikin komai dani. To kana naka Allah na nashi ina hanyar zuwa sai ga kira daga gida Mamanmu babu lafiya. Duk wuninnan a asibiti muka yi shi amman da sauƙi na mayar da'ita gida ma. Ga kuma yanayi na ruwa" Murmushi Sa'a tayi ta saki fuskarta tace. "Allah sarki to Allah ya bata lafiya. Ramatu ma bata daɗe da tafiya ba Anty Sumayya ma tafiya zata yi nima gida zanyi ki shiga gidan dai babu kowa gaskiya duk kowa ya tafi sunan baiyi armashi ba sabida ruwa" Sallama tayi ma Sa'a ta shige a tunaninta ruwa ai ta sha. Taje taba maijego abinda zata bata tayi mata irin bayanin da tayi ma su Sa'a. Mintinta arba'in ta kira Samirah akan tazo su tafi. Bata haura minti goma ba sai gata ta iso ƙofar gidan. Sallama tayi da Alawiyya ta fice Samirah taja motarta suka nufi gidan Ƴar Shuwa zuchiyarta cike da tunanin yadda zata yi da B house. Ga yara ta barsu a gidan Mama dan ta kasa tsayawa a fito dasu ta tawo dasu sabida sauri ta dai ce ma Mama gobe a kawo su. Ɗakinta a gurguje ta buɗe hannunsu niƙi_ niƙi da ledoji da fantimoti mai taya suka shiga Samirah ta zauna a kujera tana ƙarema ɗakin kallo. "To bari in yi sallah in zo in ɗaura abinci ko azahar banyi ba gashi har magriba ake kira" "Nima banyi ba bari inyi nima" Ƴar Shuwa ce ta soma shiga banɗaki ta ɗauro alwala a gurguje so take kafin Babangida ya shigo ya zamana ruwan tuwonta na wuta tunda dai tana da miyar kuɓewa ɗanya Ai kuwa ina suna kan Sallah Babangida ya leƙa uwar ɗakin da sallama ganin mata biyu ne yasa ya dawo falo ya zauna ranshi ya ɓaci sosai. Ya rasa sai yaushe zaiyi magana ɗaya a kan abu ne a dena. Idanunshi ya lumshe tunanin chus na ragargazar ruhinshi dama gangar jikinshi. Wayarshi ya zaro ya shiga cikin ma'adanar hotunan dake cikin wayar folda ta musamman shaƙe da hotunan Sabuwa ya shiga yayi ma hotonta ƙur shi kaɗai yana murmushi yana kallon bakinta. Fitowar Yar Shuwa ne yasa ya kashe hasken wayar ya zuba mata idanu. "Sannu da dawowa ka ganni sai yanzu ko? Kasan yanayin ruwa yanzu ma zan ɗaura girki amman kafin isha ma na Kammala in sha ALLAH" tana faɗin haka ta fice ta je ta kunna risho ta ɗaura ruwan tuwo kafin ta dawo taja ta zauna tana son sanar dashi batun yaje ɗakin Ramatu ya kwana. "Amm dama baƙuwa nayi Ƴar uwarmu ce daga Maiduguri tazo shine nace ko zaka je ɗakin Ramatu ka kwana ne tunda ni ina da baƙuwa gobe zata tafi ma" Kallonta yayi kawai yayi murmushin da shi kaɗai yasan fassararshi. Tashi kawai yayi ya fice zuwa can ɗakin su Mardiyya. Yayi zamanshi cikin yaran yaje ya samesu suna cin shinkafa da miya harda latas. Hannu ya saka shima ya shiga ci yana tambayarsu yaya sunan ya kasance da suka je Malama baki abun magana itace ta shiga bashi labari. A haka har suka gama ci ya ja hannun su Aɗɗa'u zuwa Masallaci. A masallacin bayan sun idar da sallah naƙocinsu ya tareshi yake sanar dashi Aɗɗa'u ya tare yarinyarshi a hanya an aiketa ya ƙwace kuɗin dake hannunta. Bayan haka kuma yaran anguwa suna kiranshi da ɓarawo dan har kaji yake sacewa. Hankalin Babangida ba ɗan ƙaramin tashi yayi ba take ya shiga ba wannan bawan haƙuri da godiyar dole kan faɗa mishi halin da ɗanshi yake ciki.. Hmm ranar a ɗakinsu Mardiyya ya kwana a falo a tsakiyar su Aɗɗa'u. Ƴar Shuwa ta kawo mishi abinci yace baya ci. Tayi juyin duniya akan sai ya bar dakin ya koma ɗakin Ramatu sabida tafi kishin yaran Sabuwa fiye da yadda take jin kishin Ramatu da Sumy. "Kije bana son damuwa dan ALLAH. Gobe da safe in baƙuwar taki ta tafi kya bani labarin abinda ya kai ki Ringim ko?" Gabanta ya tattake ya faɗi babu guiwa a jikinta da ƙyar ƙafafuwanta suka iya janta zuwa ciki. Murmushin takaici da baƙin ciki kawai yayi. Ya dubi Aɗɗa'u wanda yake bacci kamar shi sak da Yan gidansu Sabuwa gashi har dabi'unsu ya ɗakko dan dai shi tunda yake bai taɓa sata ba." Yar Shuwa babu guiwa ta shiga ɗakinta ta tadda Samira tsirara haihuwar uwarta da ubanta da sunan tana shafa mai. Zama tayi a kan gadon ba tare data ce uffan ba. Matsowa Samira tayi ta rungumeta ta baya ta shiga mata raɗa a kunnenta. "Tun sanda na haɗa idanuna dake naji a raina kin kwanta kinyi lub. Shuwa ina son zan baki duniya ki juya duniya da mutanen cikin duniya yadda ranki yake so. Ki mallaki gidaje, motoci, duk shekara kije umara dan aikin Hajj akwai wahala sau ɗaya ma ya isheki. Amman in kin bani haɗin kan abinda nake da buƙata a wajenki. Sai dai ina da tarin tulin sharuɗɗan da nake gindayama duk macen da zanyi mu'amala da'ita. Wannan kuma in kin shirya zaki sameni ne a Bamaina." Iska ta hura mata a kunnenta mai sanyi. Tuni ta lumshe idanunta. Abunda yafi komai bata mamaki shine yadda taji ta kwaɗaitu da Samira. Sakkowa tayi daga gadon ta zura rigar baccinta kana ta jawo musu leda mai cike da kaza da gurasa. "Baby sakko muci kinji duk da dai na ganki a damuwa wani abunne?" Ajjiyar zuchiya ƴar Shuwa ta sauke ta sakko suna cin kazar tana faɗa mata halin da take ciki a gidan tsakaninta da kishiyoyinta musamman ma Sabuwa da yaranta. Duk da a tunaninta ta gama da yaran Sabuwa. "Hmm ki dena damun kanki da Ɗa namiji kina tare dani. Duk taurin kanshi nan gaba kaɗan da kanshi zai dinga roƙonki yana so kuyi mu'amalar aure kina ƙi. Daga lokacin babu wata kishiya da zata sha gabanki. Su kam ki dena ma ta tasu baga magani kin karɓo ba? Ai maganin bokannan yankan wuƙa ne Mijinki kuma ai ya baki wata damane da zaki yi nazarin abinda zaki ce mishi ya kaiki Ringim. Ga dabara kice magani kuka je karɓowa da Mama na rashin lafiyarta. Ba lallai bane ya tsananta bincikenshi ba. Ke kofa ya tsananta an gano inda kuka je wajen boka ne. Tuburewa zaki yi akan cewar ku baku sani ba kwatance akayi muku zuwanku na farko kenan" Ajjiyar zuchiya Ƴar Shuwa ta sauke haka ta kwana cike da tunane _tunanen tayin Samira. Ta riga ta jarabtu da soyayyar Babangida tsoronta Allah tsoronta kada ya kamata da wani abun da za'ace har aure ya ƙare a tsakaninsu ji take yi zata iya mutuwa. Gashi tana son kuɗi tana da burin ganinta a cikin sahun manyan matan da akeji dasu. Washegari asussubar fari Ƴar Shuwa duk taje ta zuzzuba magungunan da boka ya bata a ƙofofin ɗakunan waɗanda akeso su taka. Har a ƙofar ɗakinsu mardiyya saida ta barbaɗa Sumy tana kitchen ɗinta zata dafa ruwan zafi taga sanda Ƴar Shuwa take mata barbaɗe a kofar ɗaki. Sai da ta shige ɗakinta tayi dariya kawai. tana shiga ciki tayi fitsari a kofi ta fito ta watsa a ƙofar ɗakinta ta cillar da kofin cikin kwandon shara. Su mardiyya

Chapter 17 of 19