ina jin zafin a zagesu.
Murmushi nayi nace.
Ai ko sunci bakai ka siya ba. Da kake kiran ubana tsohon najadu, naka uban ko bai zama tsohon najaduba ya haifi ɗan duniya hayaƙin..."
Marin bakina yayi bub yana zare idanu.
"Ke ni zaki zaga dan iyayenki? Ko da yake babu tarbiyyar bin miji a tattare da sha'anin gidanku. Uwar da uban sa'insa suke yi ko shigowata. Amman ki sani zan koya miki hankali kuma wallahi sai na gigita duniyarki. Na tsanake ke da yarinyar da kuka haifa kike ikirarin tawace. Kuma na lashi takobin sai da kanki kun yi nadamar aurena kin kuma nemi hanyar rabuwa danni kije ki sallamesu kizo ki sauke nauyin da Allah ya ɗaura miki"
Narantse da Allah sai dai mu gigita duniyar juna. Babangida bari kaji in faɗa maka nima fa ba sonka nake yi ba kaddararmu ce kawai a haɗe. Kaga ai ko babu komai ka samu ribar bariki kuma ko na fita a rayuwarka har gaba da abada ba zaka manta ni ba"
Tsaki naja nayi ficewata na barshi yana ta kwaɗa mun kira da ƙarfinshi na gaske.
"Ke Lolo ba kina ji mijinki na kiranki ba?"
Cewar Maigogul daya biyo mu kitchen.
Ƙyaleshi Maigogul rigima yake ji ina daidai dashi ni kuma."
"A_a Lolo yanzu dai duk tsiyar Babangida mijinki ne kije kiji menene"
"Rabu da'ita ai dama ƴar balaja'u ce yaushe zata iya biyayyar Aure ko da yake bata da laifi kai ka koyar da'ita"
Babangida ne fa ya rike labule ya dubu tsabar idan Maigogul yake faɗa mishi hakan.
Shi ko wallahi ko gezau sai ma wannan dariyar mai sani baƙin ciki ita yayi. Uzairu zuchiyata ne yace.
"Ai ko mutuwa tana jin kunyar mahaifa ka duba taronmu nan duk ƴaƴanshi ne amman ji irin furucin da kake furtawa"
Harara Babangida ya zabgama Uzairu zuchiyata yace.
"Kai kuma mai zubin ƴan daudu ba dakai nake yi ba. Cin abinci ne dai ya kawo ku da sassafennan sabida dama tun asali maiƙon gidanmu da darajar gidan namu kuke bi. In ba haka ba meye naku na zuwa da safe haka kusan ku ashirun wannan rashin kaine fa"
Tsaki yaja ya koma ciki a hakanma bai isheshi ba yaci gaba da maganganu yana ta yaɓo musu.
Su dai kowa yayi shiru Hauwa kuwa sai cewa tayi.
"Uhm ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta. Dama shi bariki iyakar ribarta kenan"
Rakiya ta dubeta tare da ƙanƙance idanu.
"Me kike nufi da iyakar ribar bariki kenan?"
Maigogul dake ƙofar kitchen yace.
"Toh zaku ci gaba da raba hali a gidan yarinya salan mijinta ya sake fitowa yayi mana tijara ko?"
Yana gama faɗa haka yace.
"Adama ku ƙara sanwar naga taliya huɗu kuka ciro yaushe zata ishemu fisabilillahi?"
"Zamu ƙara da makaroni leda ɗaya Maigogul. Kaga kaje ka zauna bai kamata fa kana cikin kitchen ɗinnan ba gaskiya. Kana jin wancan maras mutuncin abinda yake cewa."
Labbai bata gama Magana ba muka jiyo Hauwa na cewa.
"Abinda nake nufi ai kin sanshi. Ke da kikai aure a barikin baga mijin naki ba har gobe kuna cukume_cukume ba? To ga kuma ƴarki mijinta ya leko yana gargasa mana Magana."
Kafin Adama ta fito Maigogul ya tsallako kitchen ɗin ya kama taliya yana bude mana.
"Hauwa dan ALLAH bama son neman fitina ku daure in kuka koma gida sai ku ɗaura daga inda kuka tsaya."
"A_a fa ya za'ai ta faɗa mata magana irin haka?"
Cewar Labiban Hauwa. Adama tace.
"Na ci ubanki wallahi in haɗaki da bango in shaƙeki. Ji yarinya figigiya da'ita wai ni zataina rashin mutunci."
Da ƙyar dai fitina a falon ta lafa sakamakon kallo da na fito na saka musu. Uwar ɗaki na koma inaso zan dakko kuɗi in ba su labbai a samo kayan miya ko da da kifin gongonine muyi girkin dashi
Babangida yana banɗaki dan ina jin saukar ruwa daga cikin banɗakin. Jakata na dauka na fita.
Dubu biyu na ba Labbai da Sadiya. Basu daɗe ba sai gasu da kayan miya harda kifi ɗanye.
"Lolo ai a gidannan naku ana saida kifi ashe kala kala kin gansu manya. Kayan miyanma gida biyu ne tsakaninku mai kifin ce ta kwatanta mana muka siyo.
Maigogul yasa hannu ya karɓi ledar kifin yana dubawa.
"Babu laifi yayi kyau. Kinga kin huta gya dinga siye. Uhm Aisha matsa kiga in yanka muku kifin sai in soya muku."
Matsa mishi Aisha tayi ya karasa inda wajen wanke_wanken yake ya soma yanka mana kifin. Mu kuma muna ta hira. Duk da zuchiyata a cunkushe da maganganun da Babangida ya zubo ma su Rakiya take. Hakan bai hana mu wasa da dariya ba.
Babangida ne ya leƙo kitchen ɗin ko me zaiyi oho.
Ganun Maigogul a bakin famfo yana wanke kifi yasa ya buɗe bakinshi galala yana kallonshi
Shi kuwa Maigogul sai ya hau dariya.
"Uhm kifine nake yanka musu ba iyawa zasu yi ba baka jiba da ƙanƙara sosai wai nace inna soya musu ai na taimaka musu. Kasan lokacin suna yara wallahi ni nake yin girkin gidana safe rana dare, sai dai ranar da bananan sai iyayensu suyi. Kasan nayi girki a hotel gashi na iya haka siddan akaimun maƙarƙashiya aka koreni ina kan ganiyata"
Tsaki Babangida yayi yace.
"Ni Babangida na shiga ukuna wannan wacce iriyar ƙaddarace ke bibiyata haka?"
Aikin banza aikin wofi"
Na faɗa da tsiwa tare da hararar Babangida na ja dogon tsaki.
Ta gefenshi Maigogul yake so ya raɓe ya fita. Ni ko dan in ƙara baƙanta ma Babangida sai cewa nayi.
Dama kayi mana miyar kifin Maigogul yaushe rabon muci girkin da kayi mai daɗinnan"
Yana jin haka ya washe bakinshi yana farin ciki. Sai naji tausayinshi ya kamani.
Babangida na tsaye na kunna ma Maigogul ɗayan gas ɗin.
"Miƙo abun tuya da mangyaɗa. Lallai yau zaku ci miya ƴar kwatano takumbo kenan"
Babu shiri Babangida ya koma ciki fu.
Da harara na bishi, su Adama kuwa sai ƙunshe dariyarsu suke yi.
Haka muka gama dafa farar taliya da makanoni sai miyar jajjage wacce ta wadatu da kifi.
Maigogul da kanshi ya rarraba mana shima ya zuba nashi, Uzairu zuchiyata ya dinga rarraba musu.
"Lolo wannan ki kaima mijinki"
Ya miƙo mun abincin a plate.
A_a yadda yake ciki da rashin mutuncinnan nasan ko na bashi ba ci zai ba. Ku dai kuci ku ƙoshi kawai"
"A_a Lolo ke dai kai mishi koma baici ba kin bashi. Kinga irin wannan daular da Allah ya huwace miki samunta? Kada ki sake Babangida ya sake ki duk wuya duk rintsi. Kai mishi dai ki zo kuci abinci da ƴan uwanki"
Karɓa nayi na shiga uwar ɗakin.
Yana kwance yana waya da mace dan naji ya ambaci baby.
Baki na taɓe tare da ajjiye mai abincin a durowar gefen gado ina ƙoƙarin wucewa ya riƙo hannuna.
Da sauri na juyo ya wani kashe mun idanu.
"A_a Baby zamu haɗu da yamma. Yanzu ina gidane inaso nayi bacci. Amman baccin ma ya gagara jama'a ce cike da gidan nawa ma"
Tsaki nayi tare da fusge hannuna ina shirin fita yayi saurin kashe wayar ya cabkeni ya jefa a gado yana nunani.
"Wai dame kike taƙama ne. Ni kike ma tsaki dan uwarki?"
Ba dai uwata ba kasan uwar da kake zagi dai"
Ina faɗan haka ya duro a kaina. Muka shiga dambe da gaske. Da ƙyar na kwace kaina na fito.
Muna gama cin abinci ba'a daɗe ba su Maigogul da su Rakiya, da su Ma'aru sukai mana sallama. Kafin su tafi saida maigogul yayi mun miyar sutu mai daɗin gaske taji soyayyen kifi.
su Adama kuma muna gama hutawa. Adama taima Mardiyya wanka na shiga na ɗakko mata kaya lokacin Babangida yana bacci. Wankan nima nayi na saka atampata daga cikin kayana da suka kawo mun daga gida. Duk da ƴar Shuwa ta kwashe rabi da kwatan kayanma.
wanke_wanke da gyaran kitchen da bubbuɗe wasu kayayyakin da ba'a buɗe ba muka soma. Muna ajjiye komai a muhallinshi bamu muka kammal ba sai azahar.
Lokacin Sallah nayi Babangida ya fice.
Allah ya taimakeni bai dawo gidan ba.
Abincin dana kai mishi kuwa ko taɓawa bai yi ba.
Ƙwafa nayi na ɗauki plate ɗin nakai na rufe abincin a kitchen.
Labbai na kitchen ɗin tana mana jallof mai kifi ƙamshi duk ya kaure ko'ina kunsan kifi da ƙamshi.
A taƙaice dai sai magriba su Labbai suka bar gidana.
Na ɗibar musu abinci mai yawa musamman ma Rahama.
Babangida bai tashi dawowa ba sai wajen biyun dare yazo yana buga mun ƙofa.
Cikin bacci na jiyoshi haka nazo na buɗe mishi. Nayi komawata gado na kwanta.
Shi kuma yana tsaye yana jera kayan sawarshi daya tawo dasu cikin jaka.
Gaga_gaga haka rayuwar taci gaba da garawa.
Babu daɗi sam zaman gidan Babangida. Dan bamu da aiki sai faɗa, har dukana yake yi duk da nima bawai barinshi nake yi ba.
Matan gida bamu daɗe ba suka gane Babangida maras kirki ne ta ɓangaren iyalinshi.
Mu'amalarshi mai kyau da mutanene da kuma sakin fuskarshi, ga yawan larabci da kawo hujjoji da hadisai yasa ake ganin kamar nice marar kirki ba shi ɗin bane.
MRS BUKHARI
[8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA UKU
SHAFI NA TAKWAS 8
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI.
To kunsan sha'anin gidan haya musamman gidan yawa. Sai ya zamana ko a hira sai kuji suna faɗa mun magana.
Ni kuma a lokacin ba kanwar lasa bace ya zamana bana shiri da kowa a cikin gidan sai mace ɗaya Maman Hidaya itama tsohuwar ƙauriyace shi yasa tamu ma tazo guda.
Haka dai al'amura suka ci gaba da tafiya. Watana huɗu a gidan Babangida babu abinda ya taɓa shiga tsakaninmu na mu'amular aure.
Kuma ya dena kwana a waje sai dai fa sai dare ya raba yake shigowa cikin gidan yaita buga mun ƙofa matan gida na jinmu kullum.
Wani sa'inma daya shigo zamu kaure da rikicin da zai iya kaimu har asuba muna abu ɗaya.
Dan wallahi in rikicina ya tashi da kaina nake rarumarshi da damben, ko in fasa mishi wayarshi da zaran wata ƴar bajala'u ta kirashi.
Daya ga haka washe garin dana fasa wayar da mace ya kwanta a gadona ya jefoni falo a ƙasa na kwana ina kukan baƙin ciki.
Mardiyya kuwa bai taɓa ɗaukar yarinyarnan ba kwata_kwata ko kuka take yi a kusa dashi baya ɗaukarta baya kuma rarrashinta sai dai yaita kallonta kawai.
A wata biyar ɗinnan sau biyu naje gida, shima da ƙyar Babangida ya barni. Saida na sauka a ƙofar layinmu na gane ashe Babangida na biye dani a machine. Bai gushe ba har saida yaga na shige gidanmu tukunna.
Yau dai tun sassafe nake ta aikace_aikace sabida gobe akwai biki a gida na Adama da Ƴar Shuwa kuma duk a gida za'ayi anko ma iri ɗaya muka yi .Ankon da sai da Baba malam ya saka baki kafin Babangida ya yarda yayi mun. Kuma ya saka shi ya bani kudin gudunmawa.
Ina zaune Malama Babba ta korani a waya ta zage ni tas ta inda ta tsikara ba tanan take jawowa ba duk akan kuɗin ankon da akasa Babangida ya bani ne kuma.
Tana tsaka da maganarta ma na kashe wayata a hakanma nayi mata da ƙauna tunda dai ban faɗa mata magana ba.
Da daddare ina kwance a kan kujera ina kallo. Mardiyya kuma tana ɗan wasanta a ƙasa ta rarrafa can in kamota ta sake komawa.
Tunda dai ta soma rarrafe da mikewa tsaye kullum bata da aiki sai rigima da fasa mun abubuwa.
Na tashi zan kamota a gaban tv Babangida yayo sallama ya shigo.
Juyowar da zanyi naga ni yaketa kallo idanunshi cike da ruwan sha'awa.
Dogon baƙin wandone a jikina sai farar top da na saka matsattsiya kaina babu ɗankwali sai sabon kitson da wata mai kitso tazo ta yarfamun shuku da na gaba.
Ga ƙunshi nayi dai haka.
Haɗe rai nayi na dawo na zauna.
Kujera ya samu ya zauna
"Sabuwa babu ko sannu da zuwa""
Rijalu kenan in suna son abu sun iya kwantar da kansu.
Ai Rakiya bata koya mun ba ka tuna?"
Nayi maganar idona na kan tv.
Murmushi yayi wanda in ba dan yana buƙata ba sai dai mu hau sama mu duro.
"Toh a kawo mun abincina ko shima Rakiyan bata koyar dake yadda ake ba miji abinci ba?"
Banza nayi mishi na nuna mai abincin akan tebur na ajjiye mishi komai da komai.
Hatta akan abinci saida Baba Malam ya kirani yayi mun faɗa kafin na soma yin girki dashi.
Ko da gara ta ƙare babu laifi ya siyo abinci ya jibge har nama da kifi da kayan miya masu yawa ya siyo na adanasu a gidan ƙanƙara.
Sai dai fa baya bani ko asi komai dai ya siyo ya ajjiye, ko kitso nake son na sabumta dole saina tambayeshi. A nanne yake yin yadda yaso kafin ya bani. Ko zai bani kai da kai yake bani, koma ya bani bai isa ba.
Ɗaukar Ƴata nayi a ƙasa harta soma bacci muka shiga ciki. Dan saƙon da Babangida yake miƙo mun ya soma tasiri a jikina. Nima dauriya kawai nake yi.
Ina shiga ciki na shinfiɗe Mardiyya da baccinta yayi nisa a gefe. Ina da burin siyan gadon yara amman ina bani da kuɗin haka dole na haƙura.
Shirin bacci nayi na yi kwanciyata na ba ƙofa baya.
Can Babangida ya shigo shima ya gama abinda zaiyi ya kwanta.
Sai da dare ya kusan rabawa naji yana lalubena.
Hannunshi na ture tare da juyowa cikin tsiwa nace.
Meye wannan kuma kake yi.?"
"Halalina nake nema wasu ƴan iska ma aka basu balle ni da aka ƙaƙabamun ke ƙaddara mai munin gaske"
Ai ku ake rabama ƴaƴan iska sai ƴan iska irinku"
Ina faɗan haka ya ruƙunkumeni dambe sosai ya kaure a tsakaninmu duk na yakusheshi, shi kuma yai mun wulakancin da wallahi da safe da ƙyar na shiga cikin ruwan zafi. Kafin na samu salama. Ina zargin maganin ƙarfin maza ya afa duk da dai dama a wannan fagen bashi da tamka a cikin mazajen da nayi mu'amala dasu.
Haka raina a jagule na isa gidanmu aka shiga hidimar biki.
Kwanana hudu a jere ina sunturin zuwa gida dan Babangida yaƙi fur in je gida in an gama bikin in dawo. Ƴar Shuwa dai Allah yasa nan Dutse suka soma zama mijin nata ya samu aiki a jigawa sai ya tattago matarshi ya siya musu ƙaramin gida can muka kaita dai.
Muna gama bikinsu ƴar Shuwa kuma aka shiga bikin gidansu Babangida za'ayi bikin mutum biyar Alawiyya da Sauwama sai maza uku biyu ƴan dakin Malama ƙarama ɗaya ɗan ɗakin su Babangida.
Daga lokacin na soma sanin ashe ma gidan babu wani haɗin kai na azo a gani. Dan dai suna da ilimine shi yasa suke yin abun na hankali.
Biki dai rana ɗaya akeyi amman ko wanne ɓangare da ankonsu, abinci ma bambamcewa akayi.
Surukan gidan kuwa sai lokacinne nasan adadinsu da kalarsu.
Sai dai fa ko wacce wani irin kallon gani_ gani take yi mun. Duk inda na gilma ni da Sadiya dake riƙe da Mardiyya sai inga ana zunɗena.
Ƙanne da yayyen Malama Babba kuwa sai da suka ci mun mutuncin da duk taurin raina saida na zubar da hawaye. Nima na farfaɗi maganganun da ya jawo rikicin da Malam Baba yace in koma gidana washegari buɗar kai bama sai nazo ba.
Gaga gaga
Wata na takwas da aure Babangida yayo aure wata ranar juma'a.
Ina kwance naga ya shigo da magriba abunda bai taɓa yi ba kenan. Saye ya shigo da farar malum_malum sai ƙamshi yake zubawa.
Ban isheshi kallo ba naga ya ɗebi kayanshi a jaka ya jejjera ya kwashe turarukanshi daya jera a gaban mudubi.
"Kizo ki kulle ɗakinki ni yau aka ɗaura mun aure da budurwa tiya leda ba irinki tokumbo ba. Gangariya ba irinki oshele ba.
Yarinya ƴar gidan malamai ba irinki ƴar gidan kawalai ba. Dan haka ni na tafi saina gama dandalar romo tas."
Ficewa yayi.
Sabida tsabar zafin kalmominshi, da kishin da banyi tunanin zanyi akanshi ba yasa idanuna suka rufe.
Ganin zai fita ya barni da cizon yatsan ban mayar mishi da martaniba yasa na duro a guje naje na sha gabanshi.
Ai wallahi baka isa ka faɗa bam mayar maka ba"
Dariya yayi tare da buɗe baki zai yi magana nayi wuf na rigashi.
"Da kake kirana tokumbo. Ai ire irenku suna numfashi a doron ƙasa ba za'a taɓa dena samun mata tokumbo ba.
In kuma juninka neman matan banza ne da sannu zaka tadda wacce zata zama ajalinka.
Aure da kayi ko a jikina.
In sha ALLAH ba zaka taɓa samunta yadda kake tsammani ba. Murhu sai tukunya ɗan banza sai ƴar banza.
Ina gama faɗin haka na koma ciki da sauri na kulle ƙofar uwarɗakin na shiga aikin zurga zurga.
Wallahi kishi masifa ne mata. Kar kuyi mamaki dan nayi kishin Babangida.
Har ga Allah ai ina sonshi sosai kuma dai kun sani
Kuma ko auren dole aka ma mace da mijinta ranar da zai kawo mata batun ƙarin aure dole sai taji babu daɗi a ranta. Nasan masu kishiyane zasu biya wannan karatun. Marasa kishiya sai dai suce Sabuwa tayi asara ko menene na kishin Babangida oho.
A wannan daren sabida tsabaragen masifa ji nayi kamar in ƙona kaina in huta. A ranar na gane dare da tsawo yake.
Washegari sassafe ina gama aiyukana na wuce gidan ƴar Shuwa takwas a ƙofar gidanta tayi mun. Dama munyi waya da'ita a daren jiya ta sanar dani miji ba'a ɗakinta yake ba. Kuma itama tana cikin matsala babba.
Ina ƙwanƙwasa ƙofarta kishiyarta ta wani leƙo tana cewa.
"Waye haka sassafe dan rashin hankali. Mai gidanma ba za'a barshi yayi bacci ba"
Tana leƙowa muka haɗa idanu irin kallon dana watso mata ya tsoratata sosai.
Tana dai tsaye har Ƴar Shuwa ta buɗe mun ƙofa.
"Aisha baƙuwa da sassafe haka kika yi. Kamar Sabuwa ƙawarki ko?"
Kuji gulma wato dai kishiyoyi akwai gulma wallahi ɗaiɗaikune masu iya ɗauke kansu ga sha'anin kishiya.
"E wallahi ai Sabuwa zata iya kawo mun ziyara a duk sanda naga dama sabida ƴar uwatace"
Hannuna ta figa muka shige ciki.
A kujerarta na zauna.
Ita kuma ta shiga ɗan kitchen dinta da kamar karin kumallo take haɗawa.
Jinta shiru yasa na shiga kitchen ɗin na sameta a gaban doyar da take soyawa a zaune ta gasa tagumi tayi shiru.
Bata san na shigo ba har saida na dafata tukunna ta juyo da sauri. Ƙurama juna idanu muka yi dukkanmu muna cike da damuwa.
Doyar zata ƙone ki kwashe tukunna sai mu nutsu muma juna bayanin matsalalolinmu.
Doyar tayi maza ta kwashe ta toya mana ƙwai guda biyu da ruwan tea.
Muna kan karyawa take zayyyanu mun irin matsalolin da ta soma fuskanta daga kishiyarta na makirci da haɗata faɗa da miji duk ran kwananta.
"Kinga jiya a ɗakina yake wallahi har tsirara nayi a gabanshi amman ko gezau da kika sani. Duk wata hanyar maɗe da hilatar ɗa namiji kinsan na iya Sabuwa ni gangarance a wannan babin. Amman ace kayi aure miji kuma ya ɗaukeka da kai da banza baku da maraba. Shikenan duk soyayyar dana iya a bariki zata ƙare kenan. Duk yadda nake tafiya da imanin maza ace nawa mijin na kasa tafiyar dashi. Shikenan tarairaya da nuna kulawa an barma mazan bariki kenan?
Kai na jinjina ina taɓe bakina.
Ni duk wani iskancin Babangida wallahi baima taɓa damuna ba wallahi. Nifa jiyane kaɗai Babangida ma ɓirɓishin sonshi da kishinshi suka tashi mun da yace yayi aurennan.
Tunda haka yake miki ki share shi kawai kiyi harkokin gabanki. Tunda naga matar tashi in jeraku za'ayi ko sisi babu mai siyanta."
Dafa mun cinya tayi tace.
"Sassauta murya dan kamar tana laɓe wallahi. To ai inna barta ta samu galaba a kaina kenan. Ni haihuwa nake son nayi tunda ita kanta albarkacin yaran take ci. Kuma dasu take yi mun gadara.
Akan ƴarta ta goye fa sai ya sauka a kaina muna mu'amalar aure ya tafi sabida kawai yaji kukanta mafiya yawan lokuta shiryawa kawai take ta saka yarinyar kuka dan ya baro ɗakin nawa.
Wani sa'inma baya dawowa sai in yayo sallar asuba.
Sabuwa babbar matsalata fa shine matar tashi wallahi duk bala'ina kamar tsoronta nake ji. Kinsan Allah ko haɗuwa muka yi gabana yata faɗuwa kenan. In naji muryarta a tsakar gida bana fitowa sai dai in ta kama dole. Gashi yana cewa zai mayar damu maiduguri kawai can kuma a gidan gandu suke kinga in muka koma yaya zanyi? "
Mun jima sosai muna tattaunawa da Yar Shuwa nice har la'asar kafin na baro gidanta.
Sai naji na ɗan samu sauƙi babu laifi dai
Haka naita zuba ido yau Babangida zai dawo a_a gobe ne shiru har saida ya kwana ashirin cib da magriba sai gashi lokacin ina kaɗa miyata ta yauƙi nayi tuwona na alkama.
Ƙurama juna idanu muka yii kowanne cikinmu da abinda dai yake saƙawa a zuchiyarshi.
Nice na soma kawar da kaina.
Dana gama girkina bayan ya dawo sallahr isha na zuba mishi yaci.
Haka zaman yaci gaba da tafiya babu daɗi cin mutuncin iyayena da cin zarafina babu wanda Babangida ya fasa saima abinda ya ƙaru.
Ya tsani yaga su Adama a gidana, ya kuma tsani ince zanje gida ganin gida.
So da yawan lokuta yana korar su Adama haka dole suke fita zukatansu a jagule kuma suna ƙyaleshine dan gudun kada su turguɗe mun auren nawa. Har Maigogul Babangida ya taɓa kora wallahi a nanne Maigogul ya zazzare mishi idanu ya nuna baifa isaba. Inaji sun daɗe suna faɗi in faɗa. Cin fa mutunci da cin kashi babu wanda Babangida bai mun ba, babu wanda danginshi basu yi mun ba.
Wata haihuwa da Sa'a tayi ne da naje suna ananne farkon haɗuwata da matar Babangida mai suna Zahiya fara kyakkyawar gaske mai hijabi da niƙabi.
Abinka da dangin miji an gama faɗama kishiya sirrinka ko gaisawa yarinyarnan taƙi muyi sai feleƙe take ta faman yi tayi nan tayi can.
Ni da Adama data rakani sai ido muka ɗauka muka zuba mata har habaici take zubarwa. To ananne da naji ta ambaci sana'ar kawalci na dira a bakin mitsiyaciya nai mata kafirin duka na tarwatsa taronnan tsab.
Aurenma bai daɗe ba suka rabu da ciki a jikinta daga baya cikin ya zube.
Kwatsam Babangida yace in shirya gobe gobe zamu tashi a wannan unguwar zuwa wata unguwar.
Cikin dare yasa naita haɗa kaya ina ɗaurewa a buhu. Sassafe su Labbai suka zo suka taya ni harhaɗa kaya mota na waje anata loda kaya.
Muna gamawa naima matan gida sallama babu wacce tace zata rakani face maman Zahira kawata. To Babangida ya gama shafeni da baƙin fenti.
Hmm muna zuwa ƙofar gidan da aka tsaya sai muka ga motar kayan Amaryar a ƙofar gidan akata aikin saukewa gasu Sa'a da su Gudidi da sauran maza ƙannen Babangida.
Ga ɗaki ga ɗaki ni da sabuwar Amaryar Babangida wacce za'a ɗaura auren a ranar.
Mu da su muka cakuɗa akaita jera kayan ɗaki matan gida kuma suna ta kallon ikon Allah dai.
Su Adama sai rarrashina suke yi sabida yadda suka ga na damu ainun.
Da daddare muna zaune ni da Rahama da naita roƙonta ta tayani kwana sai ga Babangida ya leƙi.
Ganin Rahama ne yasa ya koma. Ni dai a wannan dare da ƙyar nayi bacci.
Masu karatu na barku da hasashe ku hasaso duk wani wulaƙanci da za'aima mace ta muzanta wallahi babu irin wanda Babangida bai mun ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci na lalace na fige na fice a hayyacina. Abinci fa akwai a gidana babu wannan yinwar hakama sutura.
Amman baƙin cikin ba Babangida suke cusa mun yana da yawa sosai.
Gaga gaga haka rayuwa taita garawa matsaloli ta ko wanne ɓangare gana Babangida gana matarshi, gana danginshi, ga mai dungurungum na ƴan gidanmu.
Ko da yaushe a cikin zuwa beli muke. Wannan ya yi sara, a_a wancan yayi sata, wancan yayi ma mace ciki muke nan a haka zamu ƙare.
Ga ƴar Shuwa sabida tsabar damuwar da take ciki ko gidanta bana zuwa daga baya ma suka koma maiduguri can dangin mijin duk da danginsu ɗaya.
Gaga_gaga
Ina zaune da tsohon cikin Aminu a kan gadon Rakiya anata taɗin bikin Sadiya ni dai bana cewa uffan sabida tun jiya nake jina wani iri dai.
Toh ni kam Rakiya zan tafi gida. Jikinne nake jinshi babu daɗi inaga haihuwarnan tana hanya dab take da isowa"
Adama ta miƙe tace.
"Ni kaina tafiya zanyi Lolo. Allah ya kaimu asabar ɗin duk abinda ake ciki kafin masu kawo kayan su zo zamu haɗa abinda ya dace.
Ina mota a zaune zani gidane na tuno mai zai hana in dinga duba tunda babu wahala Maigogul a gabana yake yin abubbuwa da yawa.
Murmushi nayi dana tuno ba ƙaramin kuɗi zan samu ba kuwa.
Ina isa gida naƙuda ta kamani matan gidanmu ne suka tsaya mun hardai na haifo ɗana namiji naci azaba har sau biyu na suma bayan yaron ya duro duniya.
Ko da aka kira aka sanar ma Baba Malam batun haihuwar shiru har washegari babu wanda yazo barka.
Babangida ma yana ɗakin sabuwar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 19