Share this page
kuwa data basu abinci basu ci ba Mardiyya haka siddan taji jikinta bai bata ba ta ko juye abincin a baƙar leda suka zubar. Su Babangida asubar fari suka fito zuwa Masallaci bayan dashi da yaran duk saida suka yi adda'ar fitowa daga ɗaki kafin suka taka maganin suka yi wucewarsu cikin kariyar Ubangiji. Kafin su fita daga gidanma saida suka yi adda'ar fita daga gida suka nufi masallaci. Ramatu kuwa tana fitowa ta taka wannan maganin taji wani zumm zumm a ƙafafunta yana haurawa a hankali har izuwa kanta. Ta ɗan jima a tsaye saida taji kamar ta dawo daidai saita wuce ɗakin aminiyarta da asussuban dan gulma na cinta na kwanan Babangida a ɗakin su Mardiyya Sai da safen Babangida ya zaunar da Aɗɗa'u ya dinga mishi nasiha yana karanto mishi illar sata da matsayin ɓarawo a musulunci. Daga ƙarshe ya ƙarashe nasihar a kansu baki ɗaya kana ya fita zuwa ɗakin Ƴar Shuwa yana tafe yana ambaton Allah ya tattake asirin baiji ko gezau ba. A falo ya samu Ƴar Shuwa da Samira suna cin ragowar ɗunamen kazar jiya. Samira da shirinta tsab harma ta fito da akwatinta falo. Zama yayi a kujera suka gaisa da Samira yake tambayarta yaya Maiduguri. "Maiduguri alhamdulillah yanzu ma nake shirin inna karya in kama hanya garinmu da nisa. "Allah sarki hakane kam. To Allah ya tsare a gaida mutanen gidan" Miƙewa yayi ya shiga ciki. Samira tace. "Bishi kiyi mishi bayani Baby. Ki tafi mishi da kaza in zaici." Miƙewa tayi ta haɗa mishi kayan kari ta shiga. Ta wuce shi yana wanka bata daɗe da zama ba ya fito da jallabiya a jikinshi zama yayi a gadon yana goge ruwan jikinshi. "Ina kwana?" Ƙur ya ƙura mata idanunshi yayi murmushi tare da cewa. "Me kika je yi a Ringim a iyakar sanina baku da ƴan uwa a ko'ina sai a Maiduguri. Sannan meye ya hanaki zuwa sunan Alawiyya da wuri har saida taro ya watse alhalin da safe kika fita da zummar tafiya gidan sunan?" "Mamace babu lafiya harma asibity na kaita to shine wata ƙawarta ta mana tayin mai maganin gargajiya. Kaji abinda ya kaimu Ringim kuma ko kafin mu isa nayi kiran wayarka bata shiga har a Ringim ɗin na kiraka wayar taƙi tafiya. Ga ruwa ya taremu a hanya kaji dalilin daɗewar da dalilin zuwa Ringim " Ƙur yayi mata yana mata kallon tuhuma sai yaji bai gamsu sosai ba da abinda tace. "Zargina kake yi da wani abun?" Ajjiyar zuchiya ya sauke illar bariki kenan kab matan zarginsu yake yi da zaran sun tambayi zuwa anguwa baya taɓa samun nutsuwa har sai yaga sun dawo. Wannan matsalar ma yanata kaita gaban Allah akan ya nutsar da zuchiyarshi waje guda "Tuwon da kika yi jiya shi zaki kawo mun ɗumamen inci maza in fita kada inyi latti. Da sauri ta fita kafin ta dawo ya gama shiryawa tsab. Yana cin tuwonne ta soko mishi zancan dawowar su Mardiyya wajenta. Ai sai ya ajjiye cokali ya kurɓi ruwan shayi ya miƙe yana gyara zaman hularshi. "Wannan maganar nace dake a barta kada a sake yinta ma. Ai su Mardiyya basu da inda zai ishesu anan a ina kikeso su zauna sabida Allah in ba dai kin shirya son takurama yaran bane amman yaushe uhm dan ALLAH ya ma za'ayi haka?" A ajjihu ya saka hannu ya ciro dubu uku ( bafa ta yanzu bace dubu ukun, ta da ce) "Ga kuɗin cefane nan kiyi shinkafa da miya da latas" Ya fito yayi ma Samira sallama ya fita daidai yaran sun fito zasu tafi makaranta Mardiyya kuma zata tafi koyarwa. Hijabinta har ƙasa kamarshi sak da yarinyar kamar an tsagakara. Samira ma bata daɗe ba ta tafi dubu arba'in ta ƙirga taba Yar Shuwa data rakata mota tana zaune ac na dukanta ta damƙa mata kuɗin. "Baby sai yaushe zan jira zuwan naki?" "To zanyi ƙoƙarin sanin yadda zan ninkeshi baibai. Shi mutumne mai zargi da kulle wallahi gashi baya barin ayi tafiya amman zan san yadda duk zanyi zan zo" Shafa ƙirjinta tayi murya ƙasa ƙasa tace. "Kiyi ƙoƙari kisan duk ƙaryar da zaki yi mishi ya barki ki tawo sabida mu samu mu tattauna kuma in gabatar dake ga manyan mata a matsayin sabuwar Baby na." Da wannan suka rabu Ƴar Shuwa ta dawo Cikin gida. Suna haɗa idanu da Ramatu sai taga tayi saurin sauke kanta ƙasa. Murmushi tayi a ranta ta ayyana magani ya cisu kenan. Anjima in tayi abincin rana zata ma Sumy gargaɗi akan kada ta sake yin girkinta daban duk ranar girkin ita ƴar Shuwan kamar yadda aka saba. Hakan kuwa akayi bayan Ƴar Shuwa ta kammala girkinta na rana ta kira Ramatu ta kawo kularta ta zuba mata sai muzurai take yi mata. Tsulum ta miƙe ta nufi ɗakin Sumy ta sameta a zaune tana shan ƙanzon masara na kwali da madara (cornflakes) "Yayi kyau wato ke an ɗaure miki ƙunƙuru ko duk ran girkina sai ki nemi abun ci sabida baki da mutunci ko?' Da ƙarfi take maganar wai ita ga shugaba. Ai kuwa ranar an kwashi ƴan kallo dan Sumy data miƙe saita watsa mata ƙanzon masarannan a fuskarta ta jawota suka soma dambacewa. Ko da Babangida yazo lefin Ƴar Shuwa ya gani cikin ƙosawa ya raba girki baki ɗaya sabida ya gaji. Kuma kuɗinshi na wajen Alhaji Abubakar Baban bola ya fito miliyan goma sai kawai ya raba girkin abun dai baima Ƴar shuwa daɗi ba sam ga kuɗi da aka narka a wajen boka amman ace Ramatu ce kaɗai ta mallaka. Ai dama Sumy ta mallaka da abun yafi mata sanyi. Haka abubbuwa suka jagwalgwale ma ƴar Shuwa. Gashi duk dabararta Babangida yaƙi barinta tayi tafiya bare ta je ta samu Samira a Bamaina. Suna dai waya, kalaman soyayyar da Samira take yi mata ko namiji albarka Saida biki ya taso a Maiduguri sai tayi amfani da wannan damar. Mama da kanta tazo ta roƙi Babangida akan zasu je biki da Yar Shuwa Maiduguri ba jimawa zasu yi ba kwana biyar kawai zasu yi. Shine Babangida ya amiince ba dan ranshi ya so ba, ba kuma dan ya yadda dasu ba gabaki ɗayansu ba. Idanunshi ya lumshe yana jin zafin rashin Sabuwa a rayuwarshi. Komai nashi ya sukurkuce sabida Sabuwa har koyarwar ma baya wani maida hankalinshi. Gashi yanzu ya kama waje yana siyan kayan baban bola in ya tara sai masu kamfani su zo su siye a kwashe a mota. Kuɗaɗen shiga sai suka ɗan ƙaru mishi,iyali kuma ya ƙara musu kuɗin cefane kuma kullum ko wacce ita da yaranta da shayi da ƙoyi da mummuƙi suke karyawa kunsan dama ta ɓangaren ciyarwa babu wasa mutumin naku Amman kullum zuchiyarshi babu daɗi hoton Sabuwa da tunaninta shine abincin cin shi da shanshi. Wani jirin jarabar sonta da kishinta yake ji. Matanshi kab sun san halin da yake ciki cikinsu babu wacce bata ƙorafin rashin samun lokacinshi da suke yi musamman ma Ƴar Shuwa data damu kanta ta hana kanta sukuni sai bokaye mayaudara ke cin kuɗinta a ƙoƙarinta na ganin ta mantar da Babangida Sabuwa abun ya ci tura. Ita kuma ta lashi takobin ko tsirara zata yi yawo saita cire Sabuwa a zuchiyar Babangida hatta su Mardiyya sai ya koresu a gidan. Ta saka su a gaba da zagi da hantara yarannan. Kullum a cikin azabtar dasu take amman a bayan idanun Babangida. Sai dai labarin na dawowa kunnenshi ta bakin Sumy. Suna ɗauki babu daɗi da yar Shuwa sosai kullum suna cikin faɗa kuma yana faɗa mata ta cuceshi data shigo rayuwarshi dan shigowarta ne ya tunzura Sabuwa har ta dage saida suka rabu. Ya mai nadamar saninta a rayuwa baki ɗaya. MRS BUKHARI. [8/26, 8:43 AM] BADA'AT IBRAHIM: https://chat.whatsapp.com/EEK9H2V5iSOFXz0Xud5Eox?mode=ac_t Yar uwa ta, kin dade kina neman in da zaki samu nighties da lounge wears masu musulmin kyau, saukin farashi da kuma kyan gani? 😍 To ki daina nema! A thrift bae closet, mun bude exclusive group inda za a dinga kawo thrift nighties, lounge wears da sauran su masu kyau, kamar Sabbi kuma farashinsu abin mamaki ne, very affordable 🤩. A nan ne za ki kasance cikin na farko da za su ga sababbin kaya kafin su kare. Idan kina son kada ki rasa mafi kyawun kaya kafin a sayar da su gaba ɗaya, to shiga cikin group ɗin yanzu kafin ya cika 👇 https://chat.whatsapp.com/EEK9H2V5iSOFXz0Xud5Eox?mode=ac_t IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA ASHIRIN CIB😆 SABUWA:. Yau dai sassafe muka fito da akwatunanmu zamu wuce garin kano. Dani sa Uzairu zuchiyata da Maigogul daya tubure shi sai yayi mana Rakiya har izuwa Lagos kafin ya dawo. An yi juyin duniya yaƙi yarda haka Uzairu zuchiyata ya haƙura. "To Rakiya Hauwa mufa arziki ya kiramu dama dai ance kashine to ni dai na tako nawa. Kuma ko babu komai ta sanadiyyata Sabuwa zata keta hazo." Baki Hauwa ta taɓe ba tare da tace uffan ba. Maigogul bai ce uffan ba sai gyara zaman hularshi yake yi ya caɓa adon burgewa. Gaza da madamcy suka fito muka yi sallama muka kama hanyar zuwa kano bayan mun yi sallama da ƴan uwa, dan Adama ma a gida ta kwana sun samu saɓani da mijinta. Layuza ma dai auren ya ƙare dama igiya ɗaya ce jol take yawo a kanta to ya tsinke igiyar da yaga ya soma samun faraga. Gata da goyo amman a hakan ya korota Maigogul dai yace yana dawowa daga Lagos zai tusa Layuza a gaba a mayar da goyon ɗan nata. Da misalin ƙarfe sha ɗayan rana muka shiga Kano. Kai tsaye daga tasha muka yi shatar tasi ta kaimu har Airport na kano dan jirginmu na zuwa Lagos ƙarfe biyu cib zai tashi. A Airport muka yi sallah muka ci abinci. Maigogul sai waye_waye yake yi da jama'arshi ta Lagos dan baya rasa mutane a ko wanne jaha yanda kuka san wani mai babban muƙami a hannu." "To Shikenan mun samu an kama mana babban Hotel a Lagos ɗin ɗaki biyu Lolo naki ɗaya, sai ni da Uzairu Zuchiyata mu riƙe ɗaya. Amman lolo akwai wani Alhaji da matarshi ta mutu yana ta son ya sake aure shine nake son in tambayeki in Khalid bai shirya ba me zai hana in haɗaki dashi?" Wani irin kallo nayi ma Maigogul wanda shi kanshi saida ya dibibice mamakine ƙarara a fuskata da abinda naji yace. "To Shikenan na fahimci bakya so. Amman ni sonki da arziki nake yi babban hamshaƙine Lolo shi kanshi ma ba lallai fa ya amince da tayin nawa ba dan babbane a muƙami abokin hulɗata ne" Idanuna na lumshe kaina ya wani sara mun. Uzairu zuchiyata ne yace. "Maigogul ai daka bar Lolo ta nutsu ta fitar da wanda ya dace ya kuma yi daidai da rayuwarta. Sannan shi mutumin da kake so ka hadasu ya yanayin ƙarfin kuɗinshi yake?" Dariyar da Maigogul da Uzairu Zuchiyata suka saka abun mamaki sai kawai naga sun tafa. Nan Maigogul ya dinga ɓarin zance yana ba Uzairu zuchiyata shi kuma tuni yai na'am da wannan mutumi har hotonshi ya nuna ma Uzairu zuchiyata a waya. "Wallahi ke Lolo da sa'arki ma dai aka haifoki wallahi irin wannan mai arziki haka a rayuwarnan wa yake son wahala? Jibi Adama fa yadda a lokaci ƙanƙani tabi duk ta lalace har ta yo yaji. Ni dama Maigogul ne ya dage saita auri ɗan ƙauyannan amman wallahi ni nasan dama ba za'ayi abun arziki ba. Shifa ɗan ƙauye baifa san cima mai daɗi ba fa kuɗinshi ba bana ci bane na cizo ne" "Ai in faɗa maka wallahi a lokacin da aka haifi Sabuwa mun samu alkhairai da yawa fa. Ai a lokacin ne Alhaji tsalha ya biya mun kujerar umara fa naje, shi yasai ragon sunanta. Wani maigidana Marigayi Alhaji muttaƙa shima ya sai rago tiƙeƙe ya bani. Ya ɗakko dubu ashirin ta zamanin baya ya bani. Uzairu zuchiyata a sunan Lolo shinkafa da miya aka ci saida kowa yaci ya ƙoshi shi yasa take da sa'a" Uzairu zuchiyata yace. "Amman ni lokacin da aka haifeni fa? Gara inji insan wacce iriyace sa'ata ya ƙarfin taurarina suke na zahiri?" Harara na zabgama Uzairu zuchiyata na baƙin ciki da takaicinsu su duka biyun. A jirgi ya ƙarashe mishi labarin yadda sunanshi ya gudana, ya dinga soki buritsun zance Uzairu zuchiyata yana ƙara turashi dama shi haka halinshi yake. Karfe uku cib muka sauka a Airport dake garin Lagos. Ni dai dana shiga jirgi na sake gane Allah da girma yake. Ashe jirgi haka yake da girma amman a sama a hangoshi ƙarami? Isarmu titi ke da wuya muka tare abun hawa zuwa hotel ɗin da aka turama Maigogul adireshin a waya da lambar ɗaki kamar haka uku sifili da uku ɗaya (30 da 31) Eco Hotel Banana Island. Wannan hotel ɗin a tsada in akwai wanda ya fishi tsada a Lagos to tsadar da kaɗanne amman abinda na sani hotel ne wanda yawanci turawa da hamshaƙan ƴan kasuwane suka fi iya kamawa sabida bala'in tsadarshi. "Yauwa Sabuwa ke shiga mai uku sifilin kiyi odar duk abinda kike so akwai abinci kyauta ko sau nawa zaki ci. Kuci ku ƙoshi banza ta faɗi. Ni dana huta zan shiga garine" Ni dai ɗakin na buɗe na shiga na shiga ƙarema haɗuwar ɗakin kallo. Zamana nayi akan gado ina ajjiyar zuchiya. Ni bana ma jin yinwa tunda munci abinci a Airport. Mayafina na zare kawai na haye gado inaso inyi bacci. Sai nayi shiru kawai ina kallon yadda ac yake buso hayaƙin sanyi, sanyin na ratsa jikina. Fuskar Alhajin da Maigogul ya nuna ma Uzairu zuchiyata ce ta faɗo mun na lumshe idanuna. Ina tunanin da ba dan bansan wanne iri bane shi dana amshi tayin Maigogul. Abu ɗayane yake sani tunani da tsoron komawa gidan jiya. Nasan abune mai wuya in ba mazinaci bane tunda har Maigogul ya sanshi. Ƙila mata yake kai musu tunda yace abokin cinikaiyarshi ne. To inma nace ba shi ɗin ba waye zai aureni wai? Bana tunanin akwai nutsattse kamammen da zai iya neman aurena in dai gaskiya zamu faɗama kanmu tunda ubanmu ma kawaline. Sannan maza da yawa suna cikin harkar zinace_zinacennan in dai zai riƙeni da mutunci ba gara in aureshi ba me ku kuke gani amma? In kuma na tuno da kuɗurar Allah sai in ji a raina nagartaccen miji kintsattse yananan zuwa lokacine bai ba. Tunda Allah ya sani na tuba nayi nadamar gabaki ɗaya ma rayuwata ta baya wallahi Allah kenan. Dan na gaji da irin rayuwar gidanmu Allah ya sani so nake in nesanta dasu sosai ko zam samu nutsuwa a rayuwata. Kuma nafi ƙaunar auren gudun sake tsundumawa rayuwar dana tsinci kaina a baya. Lumshe idanuna nayi a hankali banfi minti goma da rufewa ba bacci ya kwasheni. Maigogul Suna shiga ya cire babbar rigarshi ya faɗa banɗaki yayo wankanshi ya fito daga shi sai wandon shaddarshi da tawul a wuyanshi. "Uzairu zuchiyata kirasu a waya su kawo mun farfesu mai zafi in sha ni fita zanyi." Uzairu zuchiyata daya ƙyafe a gado yana waya da Felisha ya gyaɗa mishi kai tare da ɗaura yatsanshi a saman labɓanshi ma'ana yayi shiru. Shiru Maigogul yayi harda kama bakinshi. Zama yayi a kujera ya ciro manshi ya shafa ga shadda ya zarota ya kintsa tsab wanka iyakar wanka ya feshe jininshi da turaruka masu ƙamshin daɗi ya ƙarama yatsanshi zobe guda ɗaya mai baƙin dutse kasancewar agogon hannunshi cikinshi baƙine yana son kwalliyar ta fita da kyau. Uzairu zuchiyata saida ya sallami Felisha kana ya kira Hotel ya faɗa musu saƙon Maigogul cikin minti sha biyar suka kawo farfesun naman akuya lafiyayyen gaske suka dire mishi yana ci yace. "Uzairu zuchiyata ka shawo kan Lolo ta amince da batun dana kawo mata sabida naga tafi su A'isha wayewa ne kuma turancinma babu laifi tana kwaciɓawa shi yasa nayi mata wannan tayin fa. Ƙarshe in nace su Labbai zan bashi kaga harkar ta lalace kuma Lolo ce zata samu samunta ya zama namu babu kokonto. Wallahi ta aureshi munfa yi bankwana da talauci fa, gaka zaka auri baturiya kaima kaga fa harkar kawalcinma sai in dena Alhaji ya bani jari ko na motocine in dinga zuwa kwatano ina shigo dasu tunda a baya mun ɗan taɓa harkar" Uzairu zuchiyata yace. "Wai Maigogul kai ko wacce sana'a kayi ta ne?" Dariya yayi mishi kamar bazaai magana ba saida yasha romo sosai kafin yace. "Hmm har kwasar kashi nayi. Uzairu zuchiyata har angola munje munyi kasuwanci abunne yaƙi karɓarmu shi yasa muka koma harkar kawalci kuma muka shigeta da ƙafar dama shi yasa bana wasa da aikina. Har a cikin kwata mun kwana. Ni dai dan Allah tunda Lolo ƙawarka ce kama zaɓeta sama dani ubanka to ka shawo mun kanta ko Allah yasa makkannan mu sake komawarta." Da haka Maigogul ya gama shan farfesunshi ya saka kanshi ya fice. Uzairu zuchiyata kuma ya koma dakin Lolo. SABUWA:. Ina baccina Uzairu zuchiyata yazo ya tasheni da bugun ƙofa jiki a mace na tashi naje na buɗe mishi. Saida muka yi Sallah yayo mana odar lafiyayyen abinci muna ci ne yace dani. "Lolo in kikayi la'akari da gidanmu da irin mazajen da ƴan uwanmu suke aure ni sai inga kamar riba zaki ƙirga. Ga shawara kyauta wannan Alhajin ta ɓangarenki ki amince dashi ki barma Maigogul sauran. Ni dai shawarar da zan baki kenan a taƙaice. Kinga nima abinda zai fissheni nayi kina ganin shekarun dana kwashe ina neman irin abinda raina yake so da sannu ba gashi kusan nakai ga cimma abinda nake so ba?" To zanyi nazari akai kafin mu dawo zan yanke hukuncin amincewar ko akasin hakan" Mardiyya na kira a waya ta haɗani da su Malama a waya duk muka gaggaisa suna makarantar islamiyya lokacin suna jiran Babansu ya gama ya ɗaukesu su koma gida. Nan na faɗa musu zamu yi tafiya ni da Uzairu Zuchiyata zuwa ƙasar canada su taya mu adda'a. Uzairu zuchiyata yayi carab ya fisge wayar. "Mardiyya da bakinku na karatu mai albarka ki roƙa mana Allah yasa in samu nasarar abinda zai kaimu. Ita kanta uwar taku ku sakata a adda'a" Mun ɗan jima muna waya tana faɗa mun matsalolinsu ni dai a kullum abinda nake cewa dasu suyi haƙuri duk runtsi su dinga tsayama junansu suna gani duk lalacewar gidanmu muna iya tsayama kanmu a kan duk wani abu duk girmanshi. Gaga_gaga washegari tun ƙarfe goma muka fito zuwa Airport sai ƙarfe uku jirginmu zai tashi amman ana jiye mana turmutsutsun dake titin Lagos shi yasa aka bamu shawarar mu tafi da wuri mu jira lokacin a Airport. Mun fita tun goman amman sai karfe ɗaya muka isa Airport sabida turmutsutsun titin Lagos ( go slow) kai tsaye muka wuce inda ake duba kaya a na'ura domin tantanewa. Sannan muka wuce wajen jira ga kujeru nan shaƙe da mutane. A wata kujera muka zauna da wasu mata da miji. Maigogul kuma na kusa da wani Alhaji ya zauna shima ya tsaɓa kwalliya. Hannu Maigogul ya miƙa mishi suka gaisa daga haka ya soma yi mishi surutu kai kawai na girgiza. Muna zaune aka kira fasinjar Dubai duk suka. Miƙe suka hau kan layi in suka miƙa takaddar hannunsu aka duba sai su bi wata ƙofa su fita a haka har suka ƙare. Sallahr azahar muka yi muka dawo Uzairu zuchiyata nifa yinwa nake ji. Ya kamata mu nemi abinda zamu ci gaskiya. Kai kaga Maigogul ya samu mutum sai surutu kawai yake ta zuba mishi babu kamun kai babu komai" Baki Uzairu zuchiyata ya taɓe kawai. "Kinga ga wani windo can muje muga me suke dashi ko zamu iya siya kinsan Airport kayansu tsada ko ruwane" Kafinma mu miƙe Maigogul ya iso inda muke. "Lolo muje sama akwai gidan cin abinci wannan bawan Allahn da muke tare dashi yayi mun tayi zuwa cin abinci shine nake faɗa mishi tare da yarana nake." Kallonshi nayi na bi bayan Alhajin da kallo da yake kan ƙafar bene yana haurawa. Jikina a sanyaye nabi bayansu har zuwa saman ni da Uzairu Zuchiyata teburinmu daban, Maigogul da Alhajin teburinsu suma daban ga jama'a anan ɗaiɗaiku suna zaune suna cin abinci. Dafadukan soyayyar shinkafa mai ɗauke da kayan lambu wadatacce aka kawo mana da kaza akai muka ci muka ƙoshi muka kora da lemun limka na kwalba. Godiya muka je muka ma wannan Alhajin. "Wannan sunanta Sabuwa ƴar gaban goshina kenan yarinya ƴar albarka mai tausayi. Ta rabu da mijinta tana da yara huɗu. Wannan kuma wanta ne Uzairu zuchiyata" Da sauri muka katse Maigogul ta hanyar sake yima wannan Alhajin godiya gudun kada Maigogul ya sakar mana ɓera a yayi. Ai kuwa sai muka ji an soma sanarwa a amsa kuwa cewar fasinjan Canada su hau layi jirginmu yana jiranmu. Sakkowa muka yi cikin hanzari zuwa ƙasa muka shiga layi. "Sabuwa Uzairu zuchiyata ni zan koma zamu haɗu a Lagos ranar da zaku dawo zan tawo in tarbeku. Duk abinda na baka ka tabbatar kayi amfani dasu kada kayi mana asara" Alhajinnan yana bayan Uzairu zuchiyata sai ya dube ni yayi mun murmushi ni ina layin mata. Na lura tun muna wajen cin abinci yake ta mun murmushi. Kaina na sauke kawai. "Alhaji ni zan nufi jigawa kuma in babu damuwa ka bani lambarka mana" Cewar Maigogul yana dariya. Katinshi ya zaro a ajjihu tare da littafin rubuta kuɗi ( check) ya rubuta ma Maigogul kuɗin da mu bamu san nawa bane Maigogul yaita runtuma godiya ya nufi hanyar fita. Da ido kawai na bishi yadda yake tafe bagajan_bagajan ina juyowa muka haɗa ido da Alhajinnan fuskarshi dai ɗauke da murmushi da wani irin kallon tsan da yake yi mun. A haka dai har muka fito aka duramu a bus zuwa bakin jirgi duk muka shiga kowanne ya zauna a inda lambarshi ta fito. Idanuna a runtse har saida jirgi ya saisaita a sararin samaniya kana na buɗe idanuna na sauke ajjiyar zuchiya wai yau mune a jirgi zamu tafi wata ƙasar Allah mai yin yadda yaso. Tafiyar ashe ba tafiya bace mai sauƙi ba. Wasane_gaskene saida muka yi tsawon awanni goma sha bakwai a zaune. Muyi bacci mu farka, muci abinci, muje muyi fitsari haka dai haka dai bamu muka iso Canada ba sai wajajen ƙarfe takwas na dare. Tafiya yankin azaba wai damma jirgi akwai daɗi babu gajiya babu galabaita sam. Hannun Uzairu zuchiyata na riƙe gam dan wallahi Allah ina sauke ƙafata a ƙasa bayan mun sakko daga ƙafar benen jirgin sai naji tsoro ya kamani. Jakata Uzairu zuchiyata ya riƙe mun sai dariya yake yi mun. "Lafiya Uzairu zuchiyata wani abunne ya samu shalelen Baba? Naga ka riƙeta ga jakarta ka riƙe?" Cewar wannan Alhaji da muka shiga jirgi tare. Kaina kawai na sauke Uzairu zuchiyata yace dashi. "Babu komai rigimace kawai Alhaji" Sai ya ɗanyi dariya irinta dattijai. Mu dai muna ta bin mutane a baya a baya har muka shiga wata ƙofa. Ananne akwatunanmu suke suna yawo akan wani ƙarfe mai sulu, in jakarka tazo gabanka Sai ka zare, in kayi sanya ta wuce saita sake dawowa zaka ɗauka. Uzairu zuchiyata ne ya ɗakko mana akwatunanmu wannan Alhaji yana biye damu ƙafa da ƙafa. Uzairu zuchiyata ya zuge jakata ya ciro tabarau ya saka, ya feshe jikinshi da turare ya saka namijin goro a baki sabida ya ɗauke mishi bashin da bakinshi yake yi. Muna shiga wata ƙofar tangaran sai muka jiyo ihu daga can nesa na wata baturiya da fararen fulawowi shaƙe a hannunta har tana kuka. Watsarmun da jakata Uzairu zuchiyata yayi ya kwasa a guje yana ambaton "My Heart ( zuchiyata_ zuchiyata) Ni kuma na tsugunna zan kwashe kayana da suka zubo a jaka wannan Alhajinma ya tsugunna zai kwashe mun. Ganin ya rigani tsugunnawa sai ni na miƙe inata kallonshi hardai ya gama kashewa. A tsanake cikin nutsuwa ta jini ya ke komanshi hatta murmushi ɗan gayu yake yi. "Ga jakar taki shalele. Amman dai tunda hakane ki saka mun lambarki ta najeriya Allah bashi in muka koma gida sai in kiraki in kawo miki ziyara ma har gida. Alhaji Baba ma nasan zaiyi farin ciki da wannan haɗin ko? Allah dai yasa ban yi miki tsufa ba kinganni da furfura" Murmushi kawai nayi mishi gabana na tsananta faɗuwa na karɓi jakata. Wayarshi ya miƙo mun na amsa na rubuta mishi lambata na miƙa mishi. Sai ga Uzairu zuchiyata da Felisha sun ƙaraso hannunsu sarƙe dana juna abinka da turawa. Rungumeni Felisha tayi tana farin ciki tare da yi mun sannu da zuwa ƙasarsu mai albarka. Aka sumbaci gefe da gefen kuncina dai Ni dai sai murmushi kawai nake yi. Alhaji ya tambayi Felisha ina zamu je ta faɗa mishi har adireshin gidansu naga ta bashi sai ya dubeni yace. "To shalele abinda zaifi zan zo in

Chapter 18 of 19