Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ο»Ώ[11/3, 10:43 AM] πŸ˜˜πŸ’•: πŸ’– _*MATA KO BAIWA??*_ πŸ’– ( _*SHORT STORY*_) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) _*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI*_ _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ _*1&2*_ _Wani Kauye ciki k'auyaki dake k'aramar hukumar mani dake jahar katsina_ "Dije Dije.!!" "N'aam inna. Ganinan fitowa ina duba Hijabi ne dazan sa duk sunyi datti ne." ''Kiyi Azama to kifito kafin Baffanki ya dawo na idar da girki kizo kiyo man cefanen." "To Inna." Fitowa tayi tana sak'a k'ok'arin saka Hijabin a kanta cikin wata atamfa duk ta kod'e sai hijabin farar ce Amma duk ta kod'e." "Inna kawo kud'in to." "Yauwa Dije. Amshi nan ki wuce kitafi duk nasan baki da shiriri ta a hanya kiyi sauri kidawo Kafin Baffanki yadawo." "To Inna." Fitowa tayi cikin natsuwa tana tafiya tad'anyi nisa da gidan su taji Magana a bayanta "Manya mata su dije." d'ago Fuskar ta tayi cike da murmushi domin tagane ko wanene mai magana... "Habu kenan kajika da wata irin magana wai manya mata fa." "Ai don kin cancanci sunan shiyasa ake kiranki dashi ne Dije." Murmushi kawai tayi tare da cewa "Habu kenan.'' "Ina zaki ne dije?" "Inna zanyo ma cefane ne." "Muje na taka miki to." "Aaa Habu kabar shi Allah." A'aaa keda kawai baki san rakiyar ko .?" "A'aaa bahaka bane?'' "Shikenan kawai muje." Haka ya rakata har wajen Lado mai cefane tayo cefene suka rankayo suka dawo suna tafiya yana mata fira har suka kusa isowa kusada da gidan su sannan yayi mata bankwana tana waiwaye har ta shige gida fuskar ta ta d'auke da fara'a Inna ganin yadda ta shigo yasa ta cewa "Lafiyanki Dije zaki shigo fuskar ki da murmushi tare waiwaye gashi ko sallama baki yi Haba dije.."? "Inna kiyi Hak'uri ne na manta.".... "ni jeki gyaraman cefane ki d'oraman bisa wuta." "To Inna." Cire Hijabin tayi tare da mik'a Inna Kud'i. Inna cikin mamaki ta bita da kallo "Kud'in menene kika bani bacin kud'in cefane kad'ai na baki ni." "Inna Dama dama.." "Kintsaya yiman inda inda dama me?" "Habu ya bayar da kud'in cefane." "Da walaki shiyasa kika manta da sallama sanna kuma kika shigo kina waiwayon k'ofa ko?" Dije sunna k'anta k'asa tayi kawai batayi magana ba... "Ina kuka had'u da Habun? ko wajen shi kikaje?" Dije dasauri ta d'ago idonta ta kalli inna. "Inna yaya zance gunshi Had'uwa nayi dashi fa a hanya yace sai ya rakani fa nace A'a yace sai ya rakani shine muka tafi" inna kallon ta tayi "nayarda dake dije Amma kik'ara rik'e mutunchi kinji ko kinsan abu kad'an ake jira kayi a wannan k'auyen a shiga yayata abu k'alilan Kuma kinsan Baffanki Baisan akwai wani abu tsakaninku da Habu ba saboda ke shaida ce Baffanki bai son ya ganki tsaye da wani da sunan tad'in wadda ni kaina ban san Hujjar ta hakan domin sa'aninki tuni Anfara samu su Lallle. Amma tuni na fahimci Abinda ke tsakaninku keda Habun. "Inna ta karki damu Dijenki bazata tab'a sakaki cikin wata damuwa." Murmushi tayi "Allah yayi miki Albarka to." "Ameen Inna bari na cigaba kafin Baffah ya dawo." "Shikenan bari naje na dama Furar tashi kinsan da yadawo ita zai fara tambaya." "Inna nima zansha furar." "Ai nasani keda Baffanki naki ba'a gane gwani gurin shan fura."..... *LAGOS* Zaune yake laptop ce gabanshi sai wasu takaddu dake gabanshi baki d'aya hankalinshi yana gun lap top d'in dafe kanshi yayi da hannu guda tare da jinginar da kanshi a bisa k'ujera idon shi yana rintse. Taku take a hankali kamar tana tausayin k'asa cikin wasu dumamen English wears tasaka riga da wando riga ta lab'e jikinta Duk rabin nonuwan ta waje suke Nufar inda yake tayi tare da d'ora Hannun ta bisa Kafad'arshi "My Ammar!" Bud'a idon su yayi ya d'ora gare ta Amma baiyi mata magana sai kallon ta da yake domin k'amshi tureren ta tare da dressing d'in datayi har yafara jin wani feeling. "My Ammar wai baka da hutu kullum kana kan lap top kana aiki ya kamata ka dinga hutawa in kadawo daga office aiki ya k'are kaga kingin time nawa ne dana babyn mu." Shafa cikin dake jikinta tayi tare yi masa wani kallo " inason shigar da wasu takaddu ne yau sun kai 3days wajena yau nasake son shigar dasu gashi gobe muna da meeting" K'ara shigar da k'anta tayi jikinshi "Nidai Yanzu Babynka yanason yaji d'uminka in kuma aikin office d'in yafi maka shikenan kayi." Mik'ewa tayi ta nufi wani b'angare rufe lap top d'in yayi tare da tattara takaddun waje d'aya ya nufi b'angren da tayi kwance ya iske ta bisa gado tana latsa wayar ta Zama yayi kusa da ita Amma bata fasa latsa wayar ta ba. " Feena." Amma bata d'ago Fuska ta kalleshi shi ba sai ma gyara kwanciya datayi bisa gado yana tsaye yana kallon ta matsawa yayi bisa gadon ya d'ora ta bisa jikin shi. "Fushi ne kike dani Feena Haba my wife ba yanzu na'aje na tafo kinsan fa banason Fushinki." amsar wayar yayi ya aje ta waje guda had'a bakin shi yayi da nata yayi waje guda ya fara tsotsa tamkar ya samu Sweet nan itama ta shiga maida mashi martani na Kissing d'in dayake mata sunyi Nisa cikin Faranta ma ransu rai yana k'ok'arin tafiya wata duniya dasauri ta janye jikinta. Cikin wasu rinanun ido ya d'ago ya kalleta cikin wata Murya. "Feena ya ya hakan." "Bana ra'ayi ne kai baka da aiki kullum sai abu guda d'aya baka gajiya da abu guda na fad'a maka dama bazan iya jurewa ba dama" "Haba Feena nifa Mijinki ina da ikon da zan nemi komai nakeso wajenki fa." "Sai na zauna kuma kamar jaka ka mulke man jiki." Wani kallo tayi mashi tare da tashi ta shige toilet tabar shi zaune. Jiyayi cikin shi yana murd'a mashi dafe cikin yayi yafita b'angaren shi ya nufa toilet ya nufa ya sakar ma kanshi ruwa a tsakiyar kai sai da yaji ya samu relief sannan yafito d'aure da towel ya tsane jikin shi ma'adanar kayan shi ya bud'a ya d'auko wata riga mai gajeren hannu tare da wando bin jikin shi yayi ya feshe da turare key d'in mota ya d'auka ya fito cin karo yayi da ita palour tana kallon television Nigeria film take kallo k'amshi tureren shi taji kawai tasan shi "My Ammar ina zaka ne." Yarasa dalilin da yasa bai iya Fushi da Feena ko yaga laifi ta idan tayi masa wani abu. "Zanje restaurant ne inajin yunwa mezan tafo miki dashi ne.?".. "Kawai ferfesun kaza nakeso katafo man dashi sai ice cream " "Ok sai nadawo Kissing d'inta yayi a gefen Fuska ya juya zai tafi. "My Ammar juyawa yayi ya kaleta. "Na'am My Feena.'' Shagwab'e Fuska tayi "Zan bika muje." "Shikenan d'auko mayafinki.'' Kallon jikinta tayi taga dogon wando tasa wanda ya d'ame mata cinyoyi sai wata riga top wadda ta matse mata jikinta wani siririn mayafi ta d'auko wadda ko ida sauka kafad'ar ta baiyi ba gashi shara shara. Mota suka shiga suka bar Harabar Gidan mai gadi ya wangale musu gate suka fita Restaurant d'in da yake Zuwa cin abinci suka nufa bayan yayi parking din suka fito suka shiga ciki. "My Ammar mutsaya nan muci kawai sai mu tafi da wanda zamu ci anjima." "Ok." Bayan an kawo musu ne suna cikin cin abinci wayar Feena tafara tsuwwa." "My Ammar ina zuwa." Nesa dashi ta matsa sannan ta d'aga wayar Cigaba da cin abinci yayi yana cikin ci ne yaci ance. "Hi handsome guy." Kallon ta yayi shigar Atamfa ce tayi Amma anci mutunchi Atamfar domin duk breast d'inta waje suke gashi babu mayafi jikinta.. Jawo k'ujera tayi ta zauna Kusada shi .. ''Handsome baka bani izini ba nazauna ko.''? Shidai baiyi mata magana ba "Handsome kayi magana mana wallahi tun shigowar ka wajen naji katafi da tunani inason kasancewa dakai ko dako na kwana d'aya ko na yini." D'ago idonshi yayi ya kalleta sannan yace . "Am sorry bana buk'atar hakan.." Murmushi tayi "Shikenan in ba damuwa ina buk'atar phone number ka da kuma name d'inka.. Wani mari taji a fuskar ta tare tunkud'ar da ita gefe d'aya Cikin wani wani wani tsanani kishi tabita da kallo tare da nufar inda take..... ............ [11/3, 10:43 AM] πŸ˜˜πŸ’•: πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) *_Masoyana farin cikina ku ina kuke a fadin duniya ina sonku naji dadi yadda kuka karbi wannan gajeren novel d'in har kunfara cigiya kuyi hakuri munyi rashin wuta ne kwana biyu zamu cigaba daga inda muka tsaya luv you All my fans_* *3&4* Nufar inda take tayi tare da hawa bisa ruwan cikinta "don kutumar ubanki wannan yayi miki kama da colour d'inki da har zaki ce kina buk'atar phone number d'inshi zata kai mata wani naushi taji an rik'eta D'ago Fuska tayi ta ganshi fad'awa tayi jikin shi tare da fashewa tayi da kuka tak'ara shigewa jikin sa kama ta yayi kawai sukaje suka biya kud'in abinci da suka ci wadda ko 3 spoon ba suyi ba Shiga mota sukayi batayi magana har suka isa ko kallon shi bata yi mai gadi yana bud'e musu ko gyara parking bai yi ba ta bud'a ta fita dasauri har mayafin ta ya fad'i Amma bata bi ta kanshi ba Girgiza kai yayi sannan ya gyara parking ya fito ya d'auko mata mayafin ya nufi ciki d'akin ta ya nufa turus! Yayi ganin tasa ma k'ofar key! "Feena!" Amma shiru bata bud'e k'ofar ba ''Feena kinajin ina yi maki magana zaki shareni ko." "Ka koma restaurant ka d'auki budurwarka zata saurereka." "Feena yarinyar da ban tsaya saurere ba zaki ce natafi gunta." "Eh ai da baka bata Fuska ba bazata zauna kusa dakai ba ko." "Shikenan kiyi hak'uri yanzu ki bud'eman k'ofar kinji my honey Feena." Rarrashin ta ya farayi tasowar ta yaji ta bud'e k'ofar turawa k'ofar yayi ya kalleta ta koma bisa gado tayi kwance. Nufar inda take yayi "Haba! My Feena meye na Fushi nifa kwatata banga zamanta ba kusadani sai naji maganar kuma nifa banyi mata magana ba wallahi Haba Honey ta ya kamata kiyardani mana. Kallon shi tayi can kuma ta kauda Fuska "Nasan ko ka canza ne daga yadda nasanka ne." . "Bazan tab'a canzawa ba My Feena ke kad'aice matata kuma wadda zan kula Har abada nayi miki Alk'awarin haka fa." Murmushi tayi tare da matsowa kusa dashi. "Naji dad'in haka daga gareka My Ammar Domin ina maka wani kishi wadda bazan iya misalta maka shi ba Ammar duk mace da tayi k'okarin shigowa gida nan da sunan matar ka wallahi zan iya halakata domin kai _*MIJIN MACE D'AYA*_ ne" Ammar zaro ido yayi jin ta Ambaci kalmar kisa "Feena Kisa fa kika ce?'' "Kwarai kuwa Ammar zan iya kashe ko wacece saboda bazan iya kallon ka da wata mace ba da sunan matar ka face ni domin kai mijin mace d'aya ne in ko har kace zaka k'okarin shigo da wata to tafo da likkafani ta..." Ammar cike da mamaki yake bin Feena da kallo yadda wannna Furucin "Ni naki ke d'aya My Feena."..... *** **** **** "Baffah sannu da dawowa." "Yauwa Dije." Karb'ar ledar dake Hannunshi tayi "Baffah kawo na rike maka ledar." Dariya yayi "Dije wayo zakiyi dai kiji ledar kice to ban manta ledar tsarabar kice." Dariya tayi tare da rufe Fuskar ta "Baffah na nagode Allah yak'ara bud'i ya rufa asiri." "Ameen Dijen Baffah.".. "Baffah bari nakai d'aki sai gama sallahr marigaba sai naci.".. "Shikenan Dije bari nima bani butar nayi sallah."...... "To Baffah". Gun aje ruwa ta nufa ta d'ebo ta bashi yayi Alwallah ya fita itama itada Inna d'aura sallar magribar sukayi suka shiga d'aki...sukayi tasu Bayan Baffah ya dawo ne Dije tana kusa da Baffah yana cin Abinci gyad'a kai yayi "Wannan abinci dakajinsa Dije tayi sa domin naji d'and'an nasa yayi yawa fa. "Haba! Malam kodai jagwalolo domin dai kasan wannan girkin nawa ne shine zaka ce na Dije ne" Dije kallon Inna tayi tare zumb'oro baki "Inna ninayi Miya fa Baffah Miyar tayi dadi sosai ko?" ."sosaima Dije taji maggi sosai kamar kunne na ya cire fa." Dariya Dije tayi daga ita har inna Har Baffa ya kamallah cin Tuwon shi "Baffa na mik'o ma furar kasha?" "Aaa Dije kar cikina ya fashe sai zuwa anjima ko.." "To Baffah." Bayan Anjima kadan Baffah ya dawo daga sallar isha'i ne suna zaune sallamar wani yaro ta katse maganar da suke "Ilu shigo mana meyafaru ne?'' Dama Habu ne kike kira Dije waje." Dije Gaban ta yayi mumunar fad'uwa domin hakan bata tab'a Faruwa gare ta ba gakuma taga yanayi Fuskar sa ta canza "Jeka cemashi gatanan." Juyowa yayi wajen Dije. "Dije dama bakya jin magana ta ne? Meke tsakaninki da Habu?" "Baffah.. dama ..." Kwatsa mata tsawa yayi wadda bata tab'a jin daga gareshi ba." "Amma bazaga laifin ki ba har da mahaifiyar ki domin na fad'a mata hakan Amma kukayi hakan ban isa daku bane..." "Malam karkace haka.." Dakatar da ita yayi tare mik'ewa yafito Habu yana jingine yana jiran Fitowar Dije kawai yaga Baffa durkusawa yayi har k'asa ya gaida Baffah cikin Fara'a ya amsa sannan ya mik'e Baffah jan shi gefe d'aya yayi sukay magana gumi ya k'eto ma Habu Sharewa yayi Har suka gama magana da Baffa ya shiga ciki Dije tana rakub'e tana ganin shigowar Baffah ta mik'e "Kije waje." Cikin sanyi jiki ta mik'e ta fito Habu yana tsaye har ta iso "Habu" D'ago idon shi yayi ya kalleta cikin Fushi ya fara magana "Dije kin cuce ni kin yaudareni kinsan Kina da miji a hannu shine kika b'oye man Kinsan d'an birni zaki aura kika maidani wawa.".. "Habu bangane maganar ka har yanzu wayace maka inada miji kuma d'an binni zan aura?" ''Baffah ya sanar dani ya bada aurenki Ammar jikan mai gari..".. Dije zaro ido tayi tafara tafiya da baya dasauri ta shige gida gaban baffah ta ganta sai hawaye shar!!!!! [11/3, 10:43 AM] πŸ˜˜πŸ’•: πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) *7&8* _Masoyana masu bina wannan labarin kuyi hakuri da rashin jina kwana biyu kuyi ma yar mutan katsinawa afuwa ta dikko d'akin kara kunya gare bamu da tsoro nadawo insha Allah zan dinga yi muku post akan time Ina sonku masoyana_ "Ke wace irin village girl jahila dabba y'ar kauye bakijin horn sai an bankeki ne tund'azu ana miki horn sannan kina neman kija banke ki ko wannan y'an kauye baku da tunani.".. "Kyale ta Luv kema idan akace miki mutum d'an kauye kuma yayi rayuwar cikin ta sai a hankali fa." Aunty hallilos dake gefe tana kallon shi cikin haushi ta kalleshi tace Kenan har da Dad d'in naka kake tunda a kauye yake."... "Honey ka kyaleni da ita bakajin irin Horn d'in da nake mata fa duk bata ji ba.".. Jan Hannun ta yayi suka shiga Mota suka bar Dije tsaye wadda jikin ta duk ya b'aci da ruwan k'asa ga kuma zafin mari da taji da kuma jin Mutunchi da akayi mata sai da taga sun shud'e sannan ta nufi Hanyar gida tana goge hawayen Fuskar ta an kira ta dabba jaka kuma. Inna tana tsakar gida tana bakance gero taga shigowar Dije ga duk kayan ta sun b'aci da k'asa ga kuma sharb'ar hawaye da take dasauri ta mik'e ta nufo Gunta. "Lafiya Dije meya faru dake ne kika shigo haka?" "Dije Ganin inna ta rud'e k'asa fad'a mata bakinta taji ya furta "Inna ina tafiya ne naji nayi tuntunb'e da wani dutsi na fad'i."... "Sannu to badai kiji ciwo ba kou?"... "Eh Inna banji ba " "Shikenan Allah ya kyauta zaki iya d'ebo ruwan ko nasa mu madu ya d'ebo ruwan nashiga makota.?".... "Aaaa Inna ina iyawa fa banji komai ba ba inda jikina ke ciwo.".... "Daukar wani tulun tayi ta nufi rafi ta d'auko ruwa .." _Bayan kwana biyu_ Tafe suke itada Laure sun dawo daga kasuwar garin dake ci duk ranar Lahadi "Dije wai meyasa kwana biyu kindaina biyoman muje rafi ko d'auko itace." "Bakomai Laure aikinsan bakiji dad'in jikin naki shiyasa "... "hakane ai naji sauk'i yanzu in fad'a miki Dije Yaya Ammar matar shi bada mutunchi ko kad'an gata yar rashin kunya shikuma bashi ganin laifin ta.".. Gaban Dije ya fad'i tuno da cin mutunchi da akayi mata tsaye tayi tana kallon ta laure ji tayi ta dafata Dije ko baki gane Ammar d'in da nake cewa ba d'an wajen Kawu kabeer na binni fa.".. "Nagane shi." "In Fad'a miki batajin kunya fa ta rungume shi gaban Kaka tsoho fa ko gaban Hajjo rungumar sa take." Dije zaro ido tayi ta kalli Laure.". "Runguma fa kikace?" "Eh in fad'a miki kota zaune Bisa cinyar shi gashi fa bata mutunta Kaka tsoho da hajjo bare aje gasu Innar mu. Kowa fa bai so aure nan ba don kawai shi yaya Ammar ya nace fa...".Shiru Laure tayi hango Habu tayi tare itama da saurayin ta. . "Dije ga Habu nan tare Amadu fa..." nan hirar tasu ta katse har suka iso wajen su suna tafiya har suka iso cikin gari Laure ce ta dage sai Dije ta bita sun shiga gidansu sannan itama ta rakata domin kwana biyu Inno wato innar ta da ita da hajjo suna tambayar Dije d'in Sun shigo sauren gidan ne Laure ta kwace ma Dije wani gyalen ta Dije tana binta baya zata Amsa laure ta hana ta suna cikin wannan guje guje taji tayi karo da mutum ta fad'a jikin sa kafin ta d'ago ji tayi an buga ta bango wani duhu ta gani tayi luu! Tafad'i cikin wata k'ara Laure ta nufo gunta. dije!!!!!! K'ara rud'ewa tayi ganin jini yana bin goshin ta..... Wayyo Allah Kaka tsoho Hajjo Dije da gudu ta ruga cikin Gida tana Kuka "ya Kashe Dije Kaka tsoho ya kasheta..." .dasauri innar ta fito dawasu mutanen gidan innar ta rike ta Lafiya Laure.?"" "Yaya Ammar ya tunkud'e Dije gatacan soro bata numfashi... Cikin sauri suka nufi zaure tare da mutanen gidan.... [11/3, 10:43 AM] πŸ˜˜πŸ’•: πŸ”· *_MATA KO BAIWA ???πŸ”·_* _REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_ ( *_SHORT STORY_*) _*BY HAFSY BABY*_ ( _*INDON KAUYE*_) *5&6* _Aunty halilos ina godiya sosai da yadda kikeson novel d'inan❣ gashinan nayi Amma fa karki rainaπŸ˜‰_ K'asa magana tayi tana durkushe gaban Baffah sai hawaye shar dake fitowa daga Fuskar ta Inna kallon ta tayi "Lafiya Dije zaki shigo haka kuma ga hawaye na bin Fuskar ki?" Kallon Baffah tayi sannan ta maida idanuwanta ga Inna cikin kyarma murya ta fara magana. "Wa..i ha..bu ne ... Yace...man...d'an binni.. Z an aura. Jika..mai gari Ammar...rushewa tayi da Kuka tana kawo maganar nan ta had'a kanta da gwiwa. Inna kallon Baffah tayi tana niyyar yi mashi magana dakatar da ita yayi "kada kice komai Abinda kikaji hakane Dije jikan maigari zata aura wato Ammar d'an wajen Alhaji Kabeer.".... "Dije fashewa tayi da kuka ta isa gun Baffah ta ta durkusa cikin shashek'ar Kuka "don Allah Baffah kada ka had'ani dashi" "Kiyi hak'uri kinji Dije kamar yadda ki kasance mai biyaya ga iyayenki ki daure kiyiman wannan biyayar kinji ko zaki farin ciki da hakan shekaru biyu da suka wuce mukayi wannan Alk'awarin da Alhaji kabeer kuma kinsan girman Alk'awari shekaru biyu lokacin da aka gina massalci da kuma k'ara gyara makaranta boko da akayi sai isalamiyoyin da aka gina wadda Anan gari Alhaji Kabeer shi ya bani kwangilan kula da kud'in ma'ikatan dake gini ina biyu kuma ina kula da aikin su tun kafin haka dama Alhaji kabeer Abokina ne komawarshi birni karatu ne muka rabu da kuma rayuwar shi da ya koma can Amma duk shigowar dazaiyi k'auye nan muna tare dashi ganin kuma yadda na tsaya na kula da yanayin tsakani yadda nayi aiki tsakani da Allah babu ha'inci komai kuma yadda Mutane ke fad'ar Mutunchi na bayan komai ya kamallah ne muna zaune dagani sai shi yakece man ina neman Alfarma guri na don Allah kada nace mishi A'a nace mishi inda bata kauce shar'ia musulci ba zan mishi. Cewa yayi yana son had'a zur'ia dani don Allah kar nace mishi A'aaaa. sunkuyar da kaina nayi domin kuwa nasan kad'an daga cikin hallayar yaron wajen sa wato Ammar yadda yake kyamatar kauye nan in suka zo yadda yake wulak'an ta mutanen garin don yana ganin su y'an kauye ...sai kuma na tuno mahaifin shi yadda yake rokan Alfarma gareni har da ban iya yi masa Musu saboda ganin mutunchi nawa ya duba shiyasa ya nemi wannan Alfarma waje na nan

Chapter 1 of 11